Saran Boye 31-35


 No. 31


..............Ta ƙaramin gate Yoohan yay ficewarsa. Hakan yasa Kubrah data biyo bayansa ta rasa ina ya nufa. Har babban gate taje bayan ta gama dube-dube a harabar gidan bataga wata baƙuwar mota ba duk saina ƴan gidan.

             Yanda ta iso gate ɗin a rikice tana tambayar maigadi sai abin ya bashi mamaki. Amma sai kawai ya bata amsa da cewar babu wanda ya fita.

       “What?! Yama zakace dani babu wanda ya fita a gidan nan? Bayan nasan tabbas idan ba fitaba babu inda zai nufa”.

       “Hajiya Kubrah wlhy babu wanda ya fita kamar yanda na sanar miki. Shin kodai ɓarawo ne ya shigo gidan ban sani ba?”.

      Wani takaicine ya sake tuƙe Kubrah, batare data bashi amsaba ta bar wajen tana zuba masa harara. Shima tsit yayi bai sake magana ba, sai dai zuciyarsa fal saƙe-saƙe.


★★★★


            Yoohan na fitowa waje yay turus dan mamakin ganin motocin gidansu da alamu suka nuna tsayawarsu kenan. Dan yanzu suke ƙoƙarin fitowa. Mamaki yay masifar sake kamashi ganin papa harda d.p.o Emanuel da yaransa. Tsuke fuska ya sakeyi ya nufesu ganin yanda suka tafi kai tsaye ga gate ɗin gidan dan su basu ganshi ba.

       “Papa!” ya faɗa dai-dai lokacin da papa ya kai hannu zaiyi knocking gate ɗin. A kusan tare duk suka juyi garesa domin shigar muryarsa mai amo da kauri cikin kunnuwansu.

        Wata wawuyar ajiyar zuciya suka shiga saki a jajjere, musamman ma guards ɗin Yoohan da suka san suna a cikin gagarumin tashin hankali inhar ba'a samesa anan ɗinba.

       Papa har yi yay tamkar zai kifa dan saurin zuwa ga Yoohan ɗin. Yay wani bala'in rarumosa jikinsa ya rungume yana faɗin, “Thanks you lord. my son are you okay?      

       “Yes Papa! What is happening? Mi kakeyi anan? Miya kawoka kano?”. Yoohan ya jerama papa tambayoyin yana zare jikinsa daga nasa tare da bin guards ɗinsa da ƴan sandan dake zagaye da su da kallon tuhuma suma.

       Sake jawosa jikinsa papa yayi, batare daya bashi amsar ko ɗaya daga tambayoyin ba, ya shiga duba jikinsa sama da ƙasa kamar mai tunanin an masa wani abu. Sai kuma ya kama rigar shaddar jikinsa yana faɗin, “Yoohan minene wannan?”.

      Wani irin luuuu da idanu Yoohan yayi tare da huro iska daga bakinsa. Cikin ƙosawa da abinda ke faruwa yace, “Papa kaya ne mana. Wai mi kukeyi anan wajen ne? Miya kawoka kano?”.

             Cikin tsananin nuna ɓacin rai papa yace, “John! Yau kaine da kayan hausawa a jiki? Mike damun kanka da tunaninka?”.

      Sake shiga wani takaicin shima Yoohan ɗin yayi, dan a take fuskarsa ta sake nuna fusata. Tayaya yana tambaya amma batare da an basa amsaba papa kuma na masa wasu tambayoyi mara kangado sai kace wani ƙaramin yaro. A tsawace ya kalli su Solomon da faɗin, “Mi kukazo yi anan nace?!!”.

       Yanda ya daka tsawar basu Solomon kawai ba, hatta Emanuel da yaransa duk da suke ƴan sanda saida suka razana. Balle kuma ƴan anguwa da suka fara taruwa kallo. Gashi Yoohan yayi maganar ne da yare.

       Solomon ne cikin rawar jiki data baki ya fara masa bayani,

      “Sir! Dama mun zata ko wani abu mara ƙyaune ya sameka. Tunda muka tashi muka fahimci baka a cikin hotel ɗin. Gashi an duba ko ina amma babu alamarka. Ma'aikatan kuma duk sun tabbatar mana basuga fitarka ba, ga kuma wayoyinka mun samu baka fita dasu ba. To shine mukai tunanin ko anyi kidnapping ɗinka ne shine muka kira boss muka sanar masa.......”

        “To da kuka kawosu nan, sune sukai kidnapping ɗin nawa kenan?”. Yoohan ya faɗa cikin katse Solomon.

    Kasa bashi amsa Solomon yayi, dan harga ALLAH ba ƙaramin gulma da munafincin su baba malam sukai wajen papa ba akan gaba ɗaya sun janye ra'ayin Yoohan ɗinma, amma sunyi bakin ƙoƙarinsu suga tun a zuwan farko bai sake zuwa gidanba sai dai hakan ya gagara. Kuma jiya a yanda suka bar gidan yana cikin wani yanayi yasa sukai suspecting ɗin kosu baba malam ɗinne suka turo aka saceshi. Shiyyasa papa na isowa maganar gidan suka fara faɗa shiyyasa yace su kawosa.......


★★


           Baba malam da Kubrah kusan a tare suka shiga falon. Shi ya fitone wajen Yoohan ɗin dan yanason su tattauna ta yanda ya kamata Yoohan ya fara neman ilimin dazai taimakamasa wajen bautar ALLAH. A tunaninsa zuwa lokacin ya kammala cin abincin da Nu'aymah taje kai masa. Dan rashin dawowar tata baisa sun zargi komaiba da ga shi har Umm. A tunaninsu ko bayan takai masan ta shiga sashen Hajjo ne ko kuma Addah.

       Da sauri ya ƙarasa ga N'aymah daya hango ƙasa wanwar, ga kuma falon babu alamar Yoohan ɗin sai ƙamshin turarensa kawai. Tiren abincin data kawo yana a ajiye a inda ta ajiyesa.

       “Ya ALLAH! K lafiya kuwa mamana? Mikikeyi kwance anan haka?!”. Baba malam ya faɗa yana kai hannu ga Nu'aymahn. Da sauri ya zabura dan jin jikinta yayi sanyi ƙalau ya saki. Yay azamar maida yatsunsa biyu wajen ƙofar hancinta. ‘tabbas bata numfashi’ ya ambata a zuciyarsa yana ɗagota gaba ɗayanta.

     Hakan yayi dai-dai da ƙarasowar Kubrah da tun shigowar baba malam tana biye da shi, sai dai shi bai gantaba sai yanzun data ƙaraso garesu da dauri tana faɗin, “Abbah lafiya? Miya faru da ita ne?”.

       Cikin tashin hankali baba malam yace, “Ban saniba nima Khadijah, kinga miƙo ruwa dan bata numfashi”. 

    A hanzarce ta ɗakko masa ruwan da Yoohan yasha ya bari, ya miƙa hannu ta tsiyaya masa. shafama Nu'aymah yay a fuska. sai dai ko motsi batayiba balle ai tunanun zata farko. Hankalin baba malam ne ya sake tashi matuƙa. Ya ɗago idanunsa da sukai jajur ya kalli Kubrah.

        “Khadijah maza kiramin Ahmad ko malam ƙarami ko Omar. duk wanda kakaci karo dashi cemasa ya fiddo mota”.

      Amsawa tai da to tana fita da sauri. Sai dai maimakon ta wuce aiken da akai mata saita samu waje ta laɓe abinta tana wani taɓe baki da sakin murmushin mugunta. Zuciyarta fes take akan halin da Nu'aymahr ke ciki. Ita ta mutu kota rayu hakan ba damuwarta bace a yanzu. Dan ita kaɗai tasan miyasa take bala'in jin zafin yarinyar.


      Baba malam da baisan Kubrah bata tafi aikansa ba ya ɗakko Nu'aymah gaba ɗayanta ya fito. Da sauri Kubrah data hangosa ta sake maƙewa tana zaro ido waje. dan batai tunanin baba malam zai fito da Nu'aymah ba yanzun, a tunaninta ko saita kira ɗaya daga cikin wanda ya aiketan.

    Oho shi hankalinsa ma bai kai gareta ba. Jikinsa na tsuma bakinsa na ambaton ALLAH ya nufi harabar gidan. cikin sa'a kuwa sai hakan yay dai-dai da fitowar malam ƙarami daga sashin su Kubrahn hannunsa ɗauke da leda da key ɗin mota.

      “Abba lafiya? Miya sameta?”. Malam ƙarami ya faɗa a ruɗe yana nufo baba malam dake ɗauke da Nu'aymah.

      Da sauri baba malam ya bashi amsa da, “Maza buɗemin mota malam ƙarami, yanzu ba lokacin sanin mafari bane ba”. Cikin sauri malam ƙarami ya cika umarnin baba malam. ya karasa ga motarsa ya buɗe. Baba malam na ƙoƙari sakata a ciki Kubrah ta ƙaraso wajen. Tamkar an kira Hajjo sai gata itama ta fito daga sashenta ita da Husnah da alama ma fita zatayi.

      A rikice ta nufesu tana tambayar ba'asi. Dan taga yanda baba malam ya saka Nu'aymah a motar tamkar bata da rai. Babu yanda baba malam ya iya dole yayma Hajjo bayani a taƙaice. Kubrah na ƙoƙarin shiga motar dan a tafi da ita Hajjo ta tureta gefe ita ta shi. Yayinda Husna ta ƙirƙira cikin gidan da gudu tana ƙwalama Umm kira tana kuka. Dan ita a zatonta Nu'aymah kota mutune. Yarinyace ƙarama bata wuce 9years ba. Itace autar amaryar Abbah Musbahu.

         Fara fitowar mutanen gidan saboda ihun Husna yay dai-dai da ficewar motar da aka sakata daga gidan. Sai dai suna fitowa idon Baba malam ya sauka akan su Yoohan. Da mamaki ya tsaida malam ƙarami dake ƙoƙarin hawa titin layin. buɗe motar yay ya fita yana faɗin, “Malam ƙarami kuje asibitin ina zuwa. da alama wajen nan babu lafiya dan kamar Yahya ne”.

         Daga malam ƙarami har Hajjo dake baya riƙe da Nu'aymah tana faman jijjigata da tofa mata addu'a basu fahimcesa ba. Sai malam ƙaramin yabi umarni. 

         

        Cikin nutsuwarsa ya ƙarasa garesu tare da yin sallama duk da alamarsu bai nuna na waɗanda ya dace yayma sallamarba. Sai bai saniba ko akwai musulmai a cikinsu. Ai ko cikin sa'a sai gashi wasu daga cikin ƴan sandan sun karɓa masa. Harda ma risinawa suna gaishesa dan darajar da ALLAH yay masa ta babban mutum kuma jagora.

      Ya amsa musu ne idonsa akan Papa da sukema juna kallon sani. Kusan a tare papa da baba malam suka ambaci sunan juna.

     “Pastor Goshpower!”.

“Sheikh Sooraj Hashim!”. 

       Sai kuma kawai sukaga Papa ya kece da dariya yana tafa hannu. Ya sake nuna Baba malam yana faɗin, “Da gaske Sheikh Sooraj nake gani anan?”.

       Kafin baba malam dake kallonsa fuskarsa babu yabo babu fallasa ya bashi amsa Solomon yace, “Sir! Ai shine mutumin da.......”

      Malalacin kallon da Yoohan ke masane ya hanasa ƙarasawa, yay saurin duƙar da kansa ƙasa yana haɗiye sauran maganar.

      Kallon Yoohan baba malam yayi. Sai kuma ya sauke wani lallausan murmushi. Cikin halin dattako irin na masu ilimi da sanin ya kamata yace, “Yahya ka sanshi ne?”.

      Kai Yoohan ya jinjinama baba malam, kafin a hankali yace, “Mahaifina ne”.

         Sosai alamar mamaki ya bayyana ga baba malam, dan fuskarsa ta nuna ƙuru-ƙuru. Yace, “Yahya da gaske?”.

      Kafin Yoohan yay magana Papa da yay matuƙar tsuke fuska ya matso gaban baba malam ɗin yana faɗin, “Mizaisa ya maka ƙarya?”.

      Kamar baba malam zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana sake dai-daita nutsuwarsa. Kusan sakanni goma kafin yace, “Okay! Alhmdllh. Inaga to muƙarasa ciki tunda yau gashi kazo gidana.....”

        “Never!”. Papa ya faɗa cikin saurin katse baba malam ɗin.

     Da sauri Yoohan yace, “Papa saboda mi?”.

     Kallonsa papa yayi da tsananin ɓacin rai. Kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru ya sake maida kallonsa ga baba malam dake murmushi.

        Baba malam yace, “Kayi haƙuri, dan kai yau sunanka baƙona. Ka cancanci na karramaka da masauki da abin ci da sha. Dan koba komai kazo ƙasata ne, yankina, gidana kuma”.

       Tsaki papa ya ja. Tare da kallon d.p.o Emanuel yace, “D.p.o kama shi, inason sanin dalilin alaƙarsa da yarona”.

      “What!!?” Yoohan ya faɗa a zabure yana ƙarasowa gaban papan. Cikin nuna fusata yace, “Papa mi kake shirin yi haka? Dammi zakasa a kamashi bayan ba'a cikin gidansa ka ganniba. Sannan ba tare da shi ka ganni ba”.

        “Rufema mutane baki!!. Karna sake jin bakinka anan. Wannan wasane tsakanin manyan daji guda biyu. Ka shiga mota yanzun nan zamu koma Abuja da kai”.

       “Babu inda zanje papa. Domin aikina ne ya kawoni nan. Banga kuma dalilin dazaisa na barshi ba akan dalili mara tushe. Ku kuma (ya faɗa yana nuna police ɗin) duk wanda yay gigin matsowa koda kusa da shi ne na rantse da ALLAH sai ya rasa aikinsa. Idan kunji ƙarya zaku iya gwada hakan kuma”.


      Tashin hankaline ƙarara ya bayyana a fuskar d.p.o Emanuel. Dan shi kam an sakashi a tsaka mai wuya. Matsayin papaa a garesa ya wuce duk yanda mai karatu zaiyi hasashe. Sannan ɗansa Yoohan basai an faɗaba, yanada faɗa aji ga gwamnatin kowacce jaha saboda rawar da yake takawa akan harkar lafiya dama matsayinsa na babban likita da duniya gaba ɗaya ke ji da gani a yanzu. Dan tabbas yaron yana lokaci da lokacinsa.

          “Yahya! Iyaye nada matuƙar daraja ga ɗa. Ka daina tsaurara harshenka ga mahaifinka kaji. Karka damu da tsakanina da shi, dan a yau a yanzu ya fini gaskiya tunda a wajena ya sameka. Ba'a wasa da iyaye. Dan haka karka sake maida masa magana kaji”. Baba malam ya faɗa idanunsa akan Yoohan dake ta faman haɗiyar zuciya da sauri-sauri.

     Kai kawai ya ɗaga ma baba malam, dan zuciyar tazo wuya bazai iya magana ba. Ya watsama guards ɗinsa wani shegen kallo. Kafin ya raɓa papa da baba malam ya bar wajen batare da yayima kowa maganaba.

             Papa da yasan minene fushin Yoohan yay saurin bin bayansa yana kiransa. Amma ko kallonsa baiyiba balle ya saka ran amsawa. Ya buɗe murfin motar a fusace ya shiga baya, shima Papa ɗayan gefen ya zagaya ya shiga yana cigaba da kiran sunan sa. Hakanne ya saka drivern sa da Solomon saurin shiga suma, sauran guards ɗinsa da su Emanuel da suka sami mafita suma suka nufi nasu motocin batare da suncema baba malam komaiba.


             Nannauyan numfashi baba malam ya sauke lokacin da mitocin suka harba kan titi. Yayinda can ƙasan zuciyarsa ke mamaki da jinjina al'amarin UBANGIJI. ‘Yoohan ɗan Pastor Goshpower ne da gaske? Lallai UBANGIJI mai yin yanda yaso, a lokacin da yaso, ga kuma wanda yaso’. Baba malam ya faɗa a fili. Yasan tabbas UBANGIJI shike fidda rayayye a cikin matacce, ya kuma fidda matacce a cikin rayayye. Amma al'amarin akwai ɗunbin ban al'ajabi a cikinsa, dan yasan abubuwa masu yawa game da papa tun shuɗaɗen lokaci kafin yakai haka.

       Da wannan tunanin baba malam ya koma cikin gidan, inda ya tadda duk jama'ar gidan sun fito sunata tararrabin abinda akace ya faru da Nu'aymah. Su Abban Abdallah ma shirin shiga mota suke zasubi bayansu asibitin.

    Ganin baba malam ya sakasu dakatawa, duk suka nufesa hankali tashe suna tanbayar yaya Nu'aymahn.

        Tausayinsu ne ya kamashi. dan haka cikin taushin murya ya kwantar musu da hankali, tare da sanar musu shima yanzu zai bisu. Basu zauna ɓata lokaciba suka ɗunguma a mota ɗaya Omar ya jasu, akabar su Umm a gida na binta da addu'a.


       Yoohan da tunda suka tafi ya ƙi kula papa daketa so yayi magana yay kwance jikin kujera hannunsa dafe da goshinsa cike da tsananin takaicin abinda ya faru tsakaninsa da Nu'aymah yauma. Yarasa mike jan hankalinsa ga aikatama yarinyar nan wannan banzan ɗabi'ar?. Abinda ba halinsa ba amma yana ƙoƙarin ɗabi'antar da shi a gareta. Saima yaji na yau yafi masa zafi a rai fiye da na jiya.

      Da sauri ya kwanto jikin papa saboda wata hajijiya-hajijiya dake neman kwasarsa. Sake rikicewa papa yayi. A matuƙar ruɗe ya shiga girgiza Yoohan kai kace gani yay baya numfashi.

        Sosai takaici da hayaniyar papa ta sake rufe Yoohan ɗin, amma sai ya daure cikin taushin murya da sanyayata yace, “Papa Please relax. Ina lafiya fa”.

       Da sauri ya rungumeshi yana sauke numfashi a jajjere. Su dai su Solo suna kallon ikon ALLAH daga gaba. A haka suka ƙarasa hotel ɗin da har yanzu akwai sauran yaran Ema... Da taimakon papa Yoohan ya fita, shine ya kamasa har ɗakin da yake. Su kuma su Solomon suka dakata wajen manager ɗin hotel ɗin suna musu bayani akan anga Yoohan ɗin su kwantar da hankalinsu.


         Papa na zaune kusa da Yoohan dake kwance idanu a lumshe, hannunsa har yanzu dafe yake da kansa. Yama rasa wane kalar tunani ya dace yayi akan matsalarnan guda biyu. Alaƙalar Papa da Baba malam. Abinda ya aikatama Nu'aymah a karo na biyu. Buɗe idanunsa yay a hankali kan papa da yay shiru shima yana wani tunani can daban, sai da yay masa kusan kallon sakan goma kafin cikin nuna kulawa ya kamo hannunsa cikin nashi da faɗin, “Papa!”.

       Firgigit ya dawo hankalinsa tare da kallonsa. Yoohan ya sake lumshe idanu ya buɗe a kansa. “Papa dama kasan malamin nan ne?”.

     “Yoohan! Wannan tambayar taka bata da muhimmancin samun amsa. Kai ya kamata nasan minene alaƙarka da shi?”.

       Kamar Yoohan ya faɗi ainahin gaskiya sai kuma wata zuciya ta gargaɗesa dayin hakan. Yunƙurawa yay ya tashi zaune sosai ya jingina da fuskar gadon. Hannunsa ya sake maidawa cikin na papansa, cikin kwantar da murya yace, “Papa akwai abinda nake buƙata a wajensa, shiyyasa na kwantar da kaina nake binsa a sannu harna cimma burina. Sai dai kuma gashi kai kazo cikin mintuna goma kacal kana shirin rusamin shiri na. Miyasa zaka biyema su Solomon da shirmensu? Ai koda suka sanar maka na ɓata ko tunanin inda za'a'a sameni kamata yayi ka jira harna dawo kaji ta bakina. Haba papa da girmanka a ƙasarnan amma kake abu tamkar wani mara.......”

      Saurin katsesa papa yayi ta hanyar ɗaga masa hannu. hakanne ya saka Yoohan haɗiye sauran maganar tasa. Papa ya gyara zamansa sosai da cewa, “Naji nayi kuskure, amma kaima harda laifinka. Miyasa tun tuni baka sanarmin ba, bayan kasan niɗin mai baka goyon bayane akan kowanne irin business naka musamman a wannan yakin”.

       “Nima naji nayi kuskure to. Amma ina da dalilin ɓoyewar ai. Da ace na sanar maka mi nake shirin yi zaka iya ɓatamin aiki dan kanada gaggawa papa. kai kafi son komai da zafi-zafi a lamarinka. Hakan kuma na taɗiyeka daga nasarorinka. Yanzu da ace bakazo ba da cikin satin nan zan kammala aikina. Amma yanzu kaga ka kawo min togaciya dan zai fara kokwanto a kaina. Kaga kenan saina sake sabon ginin da zai ƙara yarda dani hundred percent kamar farko”.

     Cikin tsananin jin daɗi papa ya rungume Yoohan yana faɗin, “I am sorry my sweetheart, kai ɗinne ba'a gane kanka sai kaso. Yanzu dai na maka alƙawarin da kaina zan gyara abinda na ɓata a yau ɗinnan kaji”.

        Ɗagowa Yoohan yay da sauri, yace, “Papa da gaske kakeyi?”.

     “Ƙwarai kuwa my dear son”.

Wani lallausan murmushi Yoohan ya saki najin daɗi. Dan ya fahimci lallai sai ya nunama papa akwai manufa a tafiyarsa da baba malam sannan zai samu nutsuwar samun damar fahimtar ilimin addinin islama da zai kare kansa anan gaba a wajensu dama duk wani dake a cikin ahalinsa da yasan zai kawo masa togaciya. Amma a yanzu yasan duk yunƙurin da zaiyi sai sun taɗesa saboda rauninsa na kasancewa sabo cikin addini mai ɗunbin haske irin musulinci. A yau kawai daya kasance a ciki jinsa yake tamkar sabon mutum. Tamkar darajarsa ta ƙaru. Duk wani nauyin zuciya da ƙunci da yakan tsinta kanshi a ciki a baya yau sai yaji tamkar ansa kwano an kwashesu tas.

       Jikin papa ya sake lafewa tare da lumahe ido. Papa ma dake jin daɗin Yoohan ya fara ɗaukar huɗubarsa ya shiga shafa kansa cike da jin daɗi da annashuwa. Dan shima har zuciyarsa ta gama shirya masa babban aiki akan baba malam tsaf............✍


Tofa masu karatu. Yanzu za'a fara wasan😎 dan haka kumuje zuwa filin daga😉😱🚶🏻.

       



ZAFAFA BIYAR 2021


Hafsat miss xoxo🥰

KIBIYAR AJALI......!

      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

   

          Mamu gee🥰

MIN ƘALB!!😋🤗


        Hafsat rano🥰

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗


        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗


         Bilyn Abdull🥰

SARAN ƁOYE🤗😋


    Duka akan farashi mai rahusar gaske.


Kamar haka👇🏻💃🏻


Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700


Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO 0812652655

ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO

BANK NAME: ACCESS BANK.


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇


0903 234 5899


IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇


  09033181070


💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.



No. 32


............Tun isowarsu asibitin aka fara bama Nu'aymah dake a sume taimakon gaggawa. Sai dai harsu baba malam suka isa asibitin bata farfaɗo ba. Hakan sai ya sake ɗaga hankalinsu. musamman ma Hajjo dake ta faman sharɓar hawaye. Cike da kulawa baba malam ya zauna kusa da ita duk da kunyar ɗan fari dake tsakaninsu. Murya a tausashe da nuna ɗunbin kulawa da ladabi ya fara lallashinta da faɗa mata kalamai masu taushi da nutsuwa irin na masu ilimi. Ya nuna mata koda rasa Nu'aymah sukayi su zama masu haƙuri da godema ALLAH. Dan lokacin da ya basu ita baiyi shawara da suba. A yansu kuwa idan ya karɓeta ya fisu bukatarta ne. 

     Haka ya cigaba da mata nasiha harta samu nutsuwa tai shiru. Abba Musbahu yazo gabanta ya durƙusa tare da saka handkherchief ya share mata hawayen.

     Ana haka Doctor ya fito daga ɗakin da aka sanya Nu'aymahn. Ya buƙaci ganin ɗaya daga cikinsu cikin nuna girmamawa a garesu. Abban Abdallah da Abban su Adawiya ne suka bisa office. Dan baba malam ya nuna kawaicin nasa da ya saba kamar ko yaushe. Amma zuciyarsa cike take da tsoro da rauni. Yana ta dai ƙoƙarin danneta ne da ambaton ALLAH wajen ƙarfafa imaninsa.


       A office ɗin likita kuwa ya nutsu ne wajen rubuce-rubuce a wata takarda kafin ya maida hankalinsa gasu Abbah.

       “ALLAH ya gafarta malam zan fara da muku albishir ɗin farfaɗowarta. Sai dai kuma kamar yanda kuka sani raunin dake a cikin ƙwaƙwalwarta shine ya motsa mata. Kuma gaskiya a bincikenmu yarinyarnan tana matuƙar buƙatar son ganin babban likita. Idan ba hakaba a koda yaushe zata iya fuskantar gogewar komai na ƙwaƙwalwar ta. saboda tana ƙara girma ciwon na daɗa faɗi. Musamman ma daya kasance kamar tana sakama kanta abubuwa masu nauyi a cikin rai. A duk kuma lokacin data shiga ƙunci ciwon na mata kuɗa a cikin kanta, ba dan ma tana samun kulawa da kuma addu'oi ba da gaskiya bana zaton yarinyarnan zata kai wannan shekarun batare data tsinci kanta a ciwon hauka ba. Duk da komai na ALLAH ne, babu wani bawa daya isa canja ƙaddarar wani bawa daga yanda tazo a littafinsa. Amma a wannan karon ayi himmar sadata da likitan daya dace da matsalarta, munan taimako kawai muke bata na dakatar da raɗaɗin a gareta a lokacin daya taso. Amma matsalarta sake hauhawa takeyi gaskiya”.

       Su Abba da duk jikinsu yay sanyi sukaima Doctor godiya sosai. Tare da tabbatar masa insha ALLAHU a wannan karon zasuyi abinda ya dace.

     Yaji daɗin hakan sosai. Ya sake ɗan musu wasu bayanan da suka dace akan yanayin kula da Nu'aymahn kafin ALLAH yasa a dace da samun Doctor ɗin daya faɗa. Dan ya basu note dazai taimaka musu samun ganin makusancin likitan da lokaci-lokaci yake shigowa cikin kano. Baya kuma duba marasa lafiya a ko ina sai a General hospital. Dan haka ya basu abinda zai taimaka musu ganawa da wata likita dake aiki a General hospital ɗin, wadda yake da tabbatacin ta hanyarta zasu iya ganin Doctorn.

     Godiya sukai masa sosai, sannan suka fito. Sai dai basu ma su baba malam bayanin komaiba, a ƙoƙarinsu nason yin wani hoɓɓasa akan jinin yayan nasu da a kullum hidimarsa ke ƙarewa a kan su da nasu iyalin. Suma wannan karon sunason nuna tasu bajintar akan ɗaya daga cikin jininsa guda biyu da ALLAH ya bashi.


________★★


          Ganin lokacin sallar la'adar ya gabato Yoohan ya buƙaci kaɗaicewa dan ya huta. Hakanne ya saka papa fita ya barsa shima ya nufi ɗakin da aka kama masa.

      Yoohan ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana miƙewa. Zuwa yay ya sakama ƙofar ɗakin key. Kafin ya nufi bayi yayo alwala kamar yanda baba malam ya koya masa. Duk da zuciyarsa na kwaɗayin zuwa massallaci yay salla cikin jam'i kamar yanda suka gabatar ɗazun a massallacin juma'a haka ya haƙura ya daure yin tasa shi kaɗai a cikin ɗakin kamar yanda aka koyar da shi.

     Bayan ya idar da sallar a tsanake yay addu'a gwargwadon abinda ALLAH ya hore masa. Waya ya jawo yay kiran baba malam. Cikin sa'a kuwa bugu biyu aka ɗaka. Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke wadda har baba malam ya jiyota.

        “Banyi zaton zaka ɗagaminba Uncle. Nazata zakayi fushi dani bisa kuskuren papa”.

         Baba malam da fitowarsa kenan daga massallacin cikin asibiti sun idar da salla kiran ya shigo masa yay sassanyan murmushi, ƙaunar Yoohan ɗin da ƙyawawan ɗabi'unsa na sake dulmiyasa a ƙaunar yaron. Cikin kulawa yace, “Haba Yahya! Mizaisa nayi fushi da kai? Ai koshi bazanyi fushi da shiba dan ya fini gaskiya. Da farko ina fatan dai ka gabatar da sallar la'asar. Na biyu kuma ina fatan babu wata matsala tsakaninka da mahaifinka a dalilin ganinka da yay a wajena?”.

       Lumshe idanu Yoohan yay a hankali yana jingina bayansa da kujera, cikin so da ƙaunar baba malam dake ratsashi shima yace, “Alhamdulillahi Uncle. Yanzun nan na idar da salla, sai dai banje massallaci ba, ina fatan hakan ba laifi baneba. Dan nayi hakanne saboda ahalina, banason su fahimci ni musulmi ne tun yanzu dan zasubi hanyoyi da dama wajen kaini ƙasa. Amma idan na sami wadataccen ilimin addini musulinci duk ta inda suka ɓullo zan kare kaina”.

          Baba malam dake murmushi ya sauke ajiyar zuciya. “Tunaninka mai ƙyau ne Yahya. Sai dai salla cikin jam'i tanada matuƙar muhimmanci, dan haka kar kayi sakaci da samun ladan dake cikin jam'i kaji”.

       “Zan kiyaye Uncle”.

“Alhamdulillahi haka ake so. Mahaifinka fa?”.

        “Karka damu da shi Uncle. haka yake da zafi, amma da an fahimtar da shi yanada saurin fahimta. Munyi magana da shi ya kuma fahimceni, kafin ma ya wuce zai shigo wajenka yacemin”.

         Hakan ya bama baba malam mamaki matuƙa. Amma sai bai nunama Yoohan ba ya amsa masa kawai. Sannan sukai sallama.


         Lokacin da Yoohan ke waya da baba malam a can papa ma yana ɗakinsa suna waya da Uncles ɗin Yoohan ɗin su Uncle Godwin. Ba akan komai suke wayarba sai akan baba malam. Kamar yanda papa ya girgiza da ganin Yoohan da farko haka suma suka girgiza dajin Yoohan a wajen baba malam. amma daga baya sai bayanin da Yoohan yayma papa ɗin yaɗan sanyaya musu rai.

     Uncle Mike yay wata dariyar mugunta yana faɗin, “Wannan ɗan nakafa shegen kansane, inaga akwai aikin da yakema turawan nan ta ƙarƙashin ƙasa shiyyasa kullum bai damuwa da lamarin kowa sai wannan aikin nasa. A da ba ƙaramin haushi yake baniba akan hakan, amma jin wannan maganar ta yau sai naji ƙaunarsa da son haɗa tafiya da shi. Sai dai matsalar ɗaya ce yaron yanada taurin kai, nasan bazai taɓa yarda musan cikinsa gaba ɗaya ba. Amma ni a ganina mizai hana muma muyi namu aikin akan wannan hausa man ɗin, dan fa multi millions ne. Kawai dai baya nunawa ne”.

         Papa ya kwashe da wata dariya, kafin yace, “Mike! tunaninmu ɗaya, dan haka ku bari sai na shigo Abuja mu tattauna da ƙyau. Yanzu dai matakin farko zanbi shawarar Yoohan zanje har gida na bashi haƙuri. Daga haka na ƙulla alaƙa mai ƙarfi da shi. Sauran bayani kuma sai mun zauna a tebirin shawara”.

    Duk sunyi na'am da hakan suma. Dan haka yay musu sallama ya kashe wayar cike da zumuɗi a ransa. Kaɗan-kaɗan sai ya ƙyalƙyale da dariya. Dan gaba ɗaya zuciyarsa ta gama tsara masa yanda komai zai kasance.


______________★★


         Bayan Baba malam sun shiga sun duba Nu'aymah dake barci suka bar Hajjo da Abba Musbahu a asibitin. Koda suka iso gidan sai su Umm suka shirya su kuma suka tafi duba Nu'aymah. Wanka yayi ya zauna a falonsa yaci abincin da Umm ta shirya masa kafin su wuce. Abincin kawai yake ci a zahiri, sai dai zuciyarsa sam bata tare da duniyar mutane. Yayi zurfi matuƙa gaya a tunanin Pastor Goshpower (Papa). Ba komai ya kaisa ga tunaninba kuwa sai mamakin dama Papa nada babban ɗa a duniya kamar Yoohan? Ga shi dai a zahiri akwai kamanni tsakaninsu, sai dai baisan miyasa zuciyarsa ke kawo masa wani al'amari mai kama da kokwanto a cikin zuciyaba. Musamman da zuciyar tasa ke tariyo masa wani shuɗaɗɗen al'amari daya faru a shekarun baya tsakaninsa da Papan.

       Haka yayta saƙawa da kwancewa har lokaci yaja bai farga ba. Sai da Abban Abdallah ya shigo dubasa sannan ya fahimci yayi zurfi sosai a tunani ashe. Alwala yayi suka fice massallaci dan lokacin sallar magriba ya gabato

    Suna fitowa su Umm na dawowa gidan. tambayar jikin Nu'aymah sukayi. Suka sanar musu har yanzu tana barci, batama san sunje ba balle tahowarsu.

        Baba malam yabi Umm da kallo harta shige. tausayinta mai tsanani ne ke sake shigarsa. Tanada haƙuri da kawaici matuƙa, shiyyasa yake tsananin ƙaunarta fiye da zaton mai hasashe. Yanzu haka inba shi daya gama sanin kayarsa ciki da bai ba bazaka taɓa fahimtar tanada damuwa ba a fuskarta. Ta dake ta shanye komai, baka ganin komai akan fuskarta sai tsananin jarumta da tarin haƙuri da juriya.

     Haka ya tafi massallaci da wannan tunanin na Umm. 


         Bayan idar da sallar isha'i suna shirin zaman karatu kamar yanda suka saba ɗaya daga cikin ƴan agajin massallacin ya shigo ya sanar masa cewar yayi baƙi.

    Jimm yayi alamar tunanin baƙi daga ina a wannan lokacin? Bai gama kaiwa ƙarshe ba ya hango Yoohan dake ƙoƙarin shigowa massallacin. Bai tashi ba, sai ya jira harya ƙaraso inda suke. Yoohan da kallo ɗaya zakai masa ka fahimci damuwa da rashin walwalarsa kamar ko yaushe ya ɗan bama na kusa da shi hannu sukai musabaha kafin ya ƙarasa inda baba malam ɗin yake. Cike da girmamawa ya risina ya gaishesa. Amma sai baba malam ɗin ya kamo hannunsa cikin nasa sukai musabaha kamar kowa. Cike da jin nauyi Yoohan yay masa bayanin tare yake da baƙi, wannan ya saka baba malam miƙewa bayan ya bama ɗalibansa haƙuri ya barsu da Abbansu Abdallah shi kuma suka fito.

       Duk da dai yayi mamakin ganin papa ne sai baice komaiba. Da kansa yay musu iso gidan saukar baƙinsu. Sannan ya kira Umm ta bada abinda ke akwai a gidan cikin su Omar wani ya kawo. 

         Papa dake ta waya tun ɗazun ya ajiye yana kallon baba malam da murmushi, shima bai gazaba wajen maida masa murtani. A ƙasan ransa kuwa yana neman tsarin ALLAH da ga kowanne irin sharri papan ke tare da shi ko yake shirin ƙullawa. Duk da shi mutum ne mai ƙyautatama mutane zato zuciyarsa ta kasa ƙyautata zaton akan papa, dan shi shaidane akan sanin papa bayahude ne na gaske, sai dai bai saniba ko yanzu ya canja daga yanda ya sanshi a da ɗin.

         Hannu ya bashi suka gaisa, hakan yay dai-dai da shigowar Omar ɗauke da basket da Umm ta shiryo abincin motsa baki. Sai da ya gaida Papan, suka gaisa da Yoohan da alamar sanayya tsakaninsu sannan ya fice. Papa ya gyara zamansa yana wani ɗan basarwa, fuskarsa da murmushi har yanzu ya duba baba malam da faɗin, “Kayi haƙuri da kuskurena na ɗazun, ina fatan zaka dubesa akan rashin sani na aikata. Bansan alaƙarka da yarona mai daraja bace irin haka sai bayan mun barka ne yaymin bayanin da har na fahimta, ina fatan zakamin afuwa”.

      Sosai mamaki ya kama baba malam, dan duk zatonsa Yoohan ya ma mahaifinsa bayanin ya musulunta ne. dan haka ya ɗan dubi Yoohan ɗin. Da sauri Yoohan ya girgiza masa kai yanda papa bazai fahimtaba, hakanne ya saka baba malam fahimtar akwai abinda Yoohan ya sanarma mahaifinsa daban kenan. Sai kawai ya murmusa abinsa ya fuskanci papan shima.

       “Karka damu komai ya wuce. Dama kuma ni ban ɗaukesa wani abuba. A inda ya faru anan na zubar da shi, nima ina fatan kaimin afuwa ka kuma fahimci alkairine ya haɗani da Yahya ba sharriba. Sanin shi wanene kuma bazaisa na taɓa cutar da shi ba insha ALLAHU. Saɓanin dake tsakanina da kai kuma bana fatan ya zama sanadin ɓata alaƙata da shi, dan sanin kai ne mahaifinsa bazai canja komai ba daga yanda na ɗaukesa a raina”.

       “Naji daɗin haka, na kuma gode sosai da wannan girmamawa”. Papa ya faɗa yana sake faɗaɗa fuskarsa da murmushin mugunta.

     Daga haka dai suka ɗan taɓa hirar da bawani tsaho taiba, shi dai ma Yoohan ba saka musu baki ya keba, yama maida dukkan hankalinsa ne ga wayarsa kamar baya falon. Kusan awarsu ɗaya da rabi sukai masa sallama suka fito inda su Solomon suke. Sai da baba malam yaga barin motocinsu anguwar sannan ya shiga cikin gida ransa taf da wasiwasi akan wannan ziyara ta Pastor Goshpower, amma sai ya bar abinsa a zuciya bai faɗama kowa ba, ya ma maida hankalinsa wajen kwantarma matarsa hankali akan damuwar ciwan ɗiyarsu.


WASHE GARI.


          Washe gari papa ya matsa akan sai Yoohan ya bisa sun koma Abuja. Badan yaso hakanba ya amince zai bisa, dan dama yau ɗinne zai kammala abinda ya kawosa kanon. Yaso komawa wajen baba malam dansu tattauna game da neman iliminsa amma papa ya tsare ko ina ya hanashi matsawa ko nan da can. Asibiti ma binsa yay sukaje tare, ya kuma zauna a office ɗinsa har sai da ya kammala komai suka fito.

      Da ga asibitin airport suka tafi kai tsaye, sai da jirginsu ya ɗaga sannan guards ɗinsa suka ɗauki hanya suma a motocin.


      Baba malam na asibiti wajen duba jikin Nu'aymah da jikinta Alhmdllh saƙo ya shigo masa. Buɗewa yay ya duba ganin Yoohan ne. Murmushi baba malam yayi saboda ganin abinda saƙon ya ƙunsa, a ransa kuwa yana tsananin tausayi da ƙaunar Yoohan, insha ALLAH yayi alƙawarin zai taimaki yaron nan har ya zama HASKEn da zai zama HASKE ga waɗansu.

    Ajiye wayar yay ya maida hankali ga Nu'aymah da Hajjo take lallaɓawa taci abinci amma sai shagwaɓa take ita ta ƙoshi. Ya ɗan murmusa tare da kamo hannunta cikin nashi. “Mamana daure kici ko kaɗanne kinji, inba hakaba fa kinsan Doctor yace allura zai miki, idan kuma kin fison allurar to sai a kirashi kawai”.

     Da sauri ta shiga girgiza kanta idanunta cike da ƙwalla. “Abba dan ALLAH a'a banaso”.

      “To ki daure kici abincin sai kisha magani ki kwanta ki huta. Kinga kince dama kanki na ciwo har yanzu, Doctor kuma yace kina buƙatar hutune sosai”.

      Kanta ta sake jinjina masa. Hajjo da batace musu komaiba ta miƙama baba malam abincin. Babu musu ya amsa ya fara bata da kansa. Batafi spoon huɗu ba su Ahmad suka shigo ɗakin bayan sunyi sallama an basu izini. Ba Nu'aymah kawai ba hatta Hajjo da baba malam da ɗunbin mamaki suke kallon wanda ya shigo tare da su Ahmad ɗin. Ba kowa bane face Nasir jikan yayar Hajjo.

     Babu kunya idonsa fes akan Nu'aymah da mamakin ganin nasa ya sakata masa kallo mai nisan zango. Hajjo ce ta katse su da faɗin, “Naseru yaushe a gari? Inji maƙi baƙo?”.

          Goshinsa yaɗan sosa najin kunyar kallon da baba malam ke masa. Kafin yace, “Hajjo yanzun nan muka iso”.

       “Kuka iso? To kai da wa kuma?”.

Kansa tsaye yace, “Rufaidah”.

      Baba malam da tun gaisuwar daya amsa musu baice komai ba sai yanzu yace, “Lafiya dai ko Naser? Yau ka tuna damu a duniya”.

        “Ayi haƙuri Kawu, ni ɗin mai laifine kam, mun tahone saboda ga biki nata gabatowa, ganin mun sami hutun makaranta mu duka sai kawai nace bara mu taho maɗan huta ai”.

      “Oh to masha ALLAHU, ALLAH yayi jagora to”.

     A tare suka amsa da amin. Nu'aymah dai bata tanka ba, tama ɗauke kanta tamkar batasan mi akeyiba. Sai da Naser ya tambayeta yaya jikin sannan ta gaidashi batare data kallesanba yanzun ma. Shiko yanata so su sake haɗa ido ko zaiji ɗan sanyi a ransa da ruhinsa.

     Miƙewa baba malam yayi yana faɗin, “To ni bara naje gida hajjo, dan ina saka ran zuwan wasu baƙi ɗan anjima kaɗan idan ALLAH ya kaimu. Idan sun wuce insha ALLAHU zan dawo muji ko zasu bamu sallama, banason zama asibitin nan sam”.

      Amsa masa hajjo tayi tare da binsa da addu'a. Nu'aymah ma ma dasu Ahmad sukai masa sallama ya fice. Hajjo ce ta sake cigaba da bama Aymah abincin, badan yana mata daɗi ba take amsa, sai dai mayataccen kallon da Naser ke mata duk ya sake takureta matuƙa, sannan ya tuno mata da wasu shuɗaɗɗun abubuwa dake tdakaninsu a lokacin ƙuruciyarta, hakan yasa taketa cuno baki gaba da ɓata fuska duk da ƙasan ranta cike yake da mamakin ganin nasa ya dawo bayan barinsu na tsahon shekaru da yayi akanta. 

          Idan bata manta ba shekara kusan takwas kenan rabonsa da kano. Dan tunda tace masa ita Yah Abdallah ne zaɓinta yay zuciya saboda goyon baya da Hajjo ta bama Abdallah a wancan lokacin. Anyi bukukuwa kashi-kashi a gidansu shi kaɗai ne baya zuwa sam.

    Ta ɗan sake satar kallonsa da jijjina ƙyawun daya ƙara da cikar kamala tamkar ba Yah Naser ɗin data sani ba a shekarun baya. Kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yanzu kam kuɗi sun zauna a garesa da hutu, dan sai ɗaukar ido yake kamar gasashshiyar kazar gidan gona.


    *_Naser yaro ne wajen Alhaji Kabeer Usama dake a garin katsina. Jikane ga Yayar hajjo da suke uwa ɗaya uba ɗaya, dan aurene ya kaita katsina ta zuba zuri'a kuma a can mai albarka. Ita kaɗai kuma ta ragema hajjo a yanzun, shiyyasa take ɗaukarta tamkar uwa. Naseer ya zauna a gidan su Nu'aymah sosai, dan rashin yara a gidan lokacin da su Abdallah sukai Accident yasa hajjo ɗakkosa. A wajensu yay primary ɗinsa har secondary. Jami'a ce kawai ta maidashi garin jos. Yaso nu'aymah shima tun tana ƙarama, dan lokacin takara suka dingayi da Abdallah a kanta duk da kowa bai furta ba saboda ƙuruciya. To sai kuma yazam sanda suka furta ɗin ya zam lokaci guda, sai dai Abdallah ya riga Naser. Dama kuma ya fisa nuna damuwa da Nu'aymah. Hakan ya haddasa rigima sosai tsakaninsu, da Hajjo taga lamarin zai girmama ne tai musu shari'a a tsakani da shaidar cewar Abdallah ya riga Naser ɗin. Wannan shine sanadin yin zuciya ya tattara komansa yabar kano ya koma gidansu. Bai kuma sake zuwa ba sai yau ɗin nan da suka gansa tsulum. Har yanzu kuma baiyi aure ba._*..........✍


      To ga dai Naser tsohon masoyin Nu'aymah a kano bayan gudun hijira na shkara takwas da yayi. Ko da wane shiri ya dawo yanzun kuma? Dan da alama kam akwai motsawar tsohon tsumi tattare da shi dama ita kanta, sai mu cigaba da binsa muji YAYA TAKE NE?!!🤗.


ZAFAFA BIYAR 2021


Hafsat miss xoxo🥰

KIBIYAR AJALI......!

      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

   

          Mamu gee🥰

MIN ƘALB!!😋🤗


        Hafsat rano🥰

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗


        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗


         Bilyn Abdull🥰

SARAN ƁOYE🤗😋


    Duka akan farashi mai rahusar gaske.


Kamar haka👇🏻💃🏻


Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700


Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO 0812652655

ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO

BANK NAME: ACCESS BANK.


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇


0903 234 5899


IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇


  09033181070


💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.



*_BARKA DA JUMA'A. ALLAH yasa muna cikin bayin da zasu sami gafara a cikinta😭🙏🏻_*



No. 33


..........Koda suka isa can ɗinma wasu jerin motocinne sukazo tarbarsu tare da bodyguard ɗin papa. Haka suka nufi gida zuciyar Yoohan sam babu daɗi.

     Sun sami tarba da ga ahalin nasu, musamman ma Yoohan da ya jima dama baya ƙasar. Shima yaji daɗin ganinsu sosai, musamman kakarsa data haifi Papa da ƙannen papan su uku mata da yaransu da ya gani sunzo musu, ga kuma kakarsa data haifi Mom itama dai bata komaba har yanzun.

     Madam Chioma sai tattalinsa take kamar ta haɗiyesa dan farin cikin ganinsa, gashi taga ya wani ƙara mata ƙyau da kwarjini da cikar haiba kamar wanda akaima wankan iji. 

     Haka dai ya daure yana biye musu sama-sama dan kamar ko yaushe fuskar dai babu walwala. Ƙasan ransa ma basusan cike yake da tashin hankalin ganin yanda suka cika gidanba tamkar masu biki, musamman da ya san baƙar ƴar tsamar dake tsakanin kakanninsa guda biyu. A yanzu ma haka ya tabbata wannan zuwan na kakar tasu yanada nasaba da zaman mama Deborah Abujan.

     Da ƙyar ya iya zaman mintuna goma a falon ya gudu sama a cewarsa zai watsa ruwa ya dawo. Yana shiga ya ja tsaki tare da dafe kansa. Zama yay cikin kujerar dake ɗakin ya zaro wayarsa a aljihu, sai faman yamutse fuska yake dan har yanzu ransa a ɓace yake akan dawowar dole da papa ya sakashi yi. Wayar ya shiga sarrafawa cike da ƙwarewa. Kansa tsaye yay kiran number baba malam dan yana buƙatar yin magana da shi. Cikin sa'a kuwa bugu uku ya ɗaga. 

           Sai da suka gaisa Yoohan yace, “Uncle mun iso gida, amma nifa gobe zan dawo kano”.

       “Alhamdulillahi, barkanku da hanya. Amma mizaisa ka dawo Yahya?”.

        Fuska ya ɓata kamar yana gaban baba malam ɗin, cikin nutsuwarsa da taurin kai irin na samari masu ji da lokacinsu yace, “Uncle ina buƙatar neman sani akan addinin musulinci. Ta wannan hanyarne kawai zan iya yaƙar duk wani ƙalubalen da nake hange da ga ƴan uwana. Ta hanyar neman ilimin ne kuma kawai zan bautama UBANGIJINA. Ba tsoro nake duk wanda ya sanni yasan na zama musulmi ba. Kawai ina buƙatar kwankwaɗar madarar ilimine nima cikin kwanciyar hankali”.

     Sosai baba malam yay murmushi har Yoohan na jiyo sautinsa. “Yoohan karka damu kaji, bama sai ka dawoba, inason kabi komai a hankali kamar yanda ka faɗa. Akwai ƙanina dake anan zaune abujan amma yana nan basu koma bikin salla ba, dama na shirya masa magana kawai zaka ringa ɗaukar karatu a wajensa tunda anan kafi zama fiye da nan kano, kaga zaifi maka sauƙi ko kuwa?”.

          Ɗan jimm Yoohan yayi alamar tunani, bawai hakan bai masa baneba. A'a tunaninsa shine yanayin aikinsa, dan ya tabbatar a nan abujar ma ba samun zaman yake ba. Yanzu haka kwanaki biyar kawai zaiyi ya wuce Lagos. daga can kuma zai shiga Maiduguri. Yana da tabbacin kuma da wahala ya ƙulla wata guda bai sake barin ƙasarba ma........

       “Yahya ko akwai damuwa ne?”. Baba malam ya katse masa tunaninsa.

    Ajiyar zuciya ya sauke, tare da miƙewa ya taka jiki a sanyaye zuwa bakin gadonsa ya sake zama. “Uncle babu komai. Kawai dai ina duba yanayin aikina ne da baya barina zaman waje ɗaya, sai nake gani kamar hakan zaiyi wahala a gareni. Inba dai ajiye aikin zanyiba kawai na fuskanci karatun.....?”.

       “A'a Yahya bazai yuwuba, duk da bansan ya aikin naka yake ba bazan baka shawarar ajiye aikinka ba. Dan mu musulinci addini ne dake son mutum mai neman na kanka. Ta hakane zaka kare mutuncinka da tarbiyyarka, ka kuma nema halalinka harka tausayama na ƙasa da kai da marayun ALLAH. Yahya karka manta kaifa bawan ALLAH ne mai yawan hidima, sannan bayane goya marayu. Idan ka ajiye aiki yaya masu jira daga garekan zasu kasance kuma?. Kaf Annabawan ALLAH tun daga farkonsu har zuwa MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su tabbata a gareshi, tarihi ya nuna mana nauyin dake kansu na yaɗa kalmar ALLAH baisa sun rayu a rashin neman na kansuba, balle ai tunanin zama daga jiran na wani ko taskar masu mulki. Dukansu sunada sana'oinsu. To inhar mutane masu daraja irinsu sun yi gwagwarmayar neman halalinsu mu su wanene da bazamu tashi munema na kanmu ba”.

       Ajiyar zuciya Yoohan ya sauke. Murya a sanyaye yace, “Hakane Uncle. Tunanin hakan baizo min a rai ba shiyyasa”.

        “Karka damu ALLAH yana tare da mu. Insha ALLAHU mafita zatazo daga UBANGIJIN rahama da jinƙai”.

      “To shike nan Uncle nagode sosai. ALLAH ya ƙara lafiya da tsahon rai. Bara na barka ka huta dan yanzu na sami nutsuwa, ɗazu kam hankalina a tashe yake sosai”.

     Ƴar dariya baba malam yay masa sukai sallama ran Yoohan fes. Da ƙarfin zuciyarsa kuwa ya miƙe ya fara zame kayansa dan son watsa ruwa.


★★★


         Tunda suka ajiye wayar baba malam ya shiga dogon nazari, harga ALLAH yana jin son Yoohan cikin ransa. hakan har mamaki yake bashi wani lokacin. Duk da yasan UBANGIJI kan jefa soyayyar wani a zuciyar wani batare da wata alaƙa ba a tsakaninsu 

      Har yanzu baisan abubuwa da yawa ba dangane da Yaron ba, amma sai ya keji zuciyarsa na tsananin ƙyautata masa zato akan abubuwa da dama na rayuwar yau da gobe. Haɗuwarsu ta uku kenan kacal. Amma ya fahimci wasu ƙyawawan halayya da ko a cikin musulman ma ba kowane ke da su ba. Ga ƙyauttawa da yarda da yaron ke bashi ɗari bisa ɗari.

    Numfashi ya ɗan sauke wani gefen zuciyarsa na sake ƙarfafa masa gwiwa akan alkarin da yake shirin aikatawa. Yayinda can kuma wata ke gargaɗarsa musamman akan ahalin da Yoohan ɗin ya fito.........

         “Malam lafiya kuwa ka zurfafa a tunani haka?”. Umm data shigo tun ɗazun tanata sallama bai jiba ta faɗa tana mai katsesa.

    Ajiyar zuciya ya sauke da sauri tare da kallonta. Gefensa ya nuna mata da hannu alamar ta zauna. Batare da tayi musu ba ta zauna kuwa idanunta a kansa. Hannunsa ya saƙala cikinnata yana ɗan sake furzar da huci. “Jannat wani al'amarine yanzun nan UBANGIJI ya saƙaminshi a cikin tunanina akan yaron nan dana sanar miki jiya ya musulunta. Sai dai kuma wani sashi na zuciyar tawa yana gargaɗina dason jefani a kokwanto game da al'amarin”.

      “Tom nidai a nawa tunanin sai naga kamar shaiɗanne Malam. mizai hana ka bama al'amarin wani ɗan lokaci haka, sai ka duƙufa neman zaɓin ALLAH akan yuwuwarsa ko barinsa”.

     “Eh tabbas kinzo da shawarar hankali Jannat. Insha ALLAHU kuma zanyi amfani da ita. Amma kema inason ki tayani dan ALLAH”.

      “Insha ALLAHU zan tayaka Abban Nu'aymah, ALLAH ya tabbatar mana da alkairinsa”.

      “Amin ya rabbil-alamin”. Ya faɗa cike da jin nutsuwa da gamsuwa akan shawararta”.

    


______________★★★


             Kwanakin Nu'aymah uku a asibiti aka sallamota. Alhmdllh jikinta yayi ƙyau sosai, sai dai haɗarin da Doctor ya tabbatarma iyayenta tana a ciki akan iya fuskantar loosing mamory shine ya jefasu a cikin matuƙar damuwa.

       Yayinda ita kuma da batasan mike faruwa ba sai tata matsalar ta zama Naser. Dan a kwanaki biyun nan daya ɗauka da zuwa gaba ɗaya ya takurama kowanne irin motsinta. Duk da daga gaisuwa babu abinda ke sake haɗasu sai magana kamar kowa. Amma kallon da yake jifanta da shi da tarewa a asibiti da yayi ya tabbatar mata cewar zuwan nasa akwai manufa.

      Tun bayan dawowarsu gida Umm ta taimaka mata tai wanka taci abinci da magungunanta ta kwanta danta huta. Shine ta samu damar yin tunani akan Naser ɗin. Kamar daga sama ta dinga jiyo hayaniya na tashi a gidan, sosai mamaki ya kamata, duk da ta tabbatar hayaniyar bata faɗa bace tasan wannan ba ɗabi'ar mutanen gidansu baceba hakan. ‘To minene ya faru?’ ta faɗa a fili cikin sake zurfafa mamakinta. 

     Kusan mintuna ashirin sai kuma taji hayaniyar ta lafa. bata ko motsa ba balle ai tunanin zata fita ta ganoma idanunta, haka ta cigaba da kwanciyarta tun tana tunani har barci mai nauyi ya ɗauketa saboda a maganin nata akwai na barci daman.


        Kiran sallar magriba ne ya saka Umm shigowa ɗakin Nu'aymah ta tadata. Da ƙyar ta samu ta tashi dan barcin nata yayi nisa sosai. Taimaka mata tayi tai alwala kafin tai yunƙurin fita zata barta.....

     “Umm wai hayaniyar mi naji anayi ɗazun?”. Ta faɗa cikin katse hanzarin Umm dake ƙoƙarin fita.

       Batare da Umm ta juyo ta kalleta ba tace, “Su Abdallah ne, sunma shigo dubaki kina barci”.

      Sosai gaban Nu'aymah ya faɗi, sai dai kafin ta sake cewa wani abu Umm ta fice abinta. Shiru tai tsaye hannunta riƙe da hijjab, dan zuciyarta cike take da tambayoyin miya kawo su Yah Ab ɗin gida a yanzun bayan kuma shine da kansa yacema Hajjo sai bikin su aunty Hajarah daya rage saura kwanaki ashirin cif yau ayi. Ganin bata da mai bata amsarta sai ta saka hijjab ɗinta ta kabbara salla kawai.

       Koda ta idar bata fitaba tai zamanta a ɗaki, sai da tai sallar isha'i da shafa'i da wutiri sanna ta fito falonsu danta ɗansha iska. Umm kawai ta tarar zaune. Ta zauna kusa da ita tare da ɗora kanta a gefen kafaɗarta.

     Ɗan kallonta tayi, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta ɗaura hannunta a wuyanta. Jin jikinta babu wani zafi ya saka Umm sauke ajiyar zuciya da janye hannunta.

      “Umm nafa warke”. Nu'aymah ta faɗa tana murmushi dajin ƙaruwar ƙaunar mahaifiyar tata a cikin rai. Itama Umm Murmushin tayi, ta shafa kumatun ɗiyar tata da faɗin, “Ai haka muke fata Nu'aymah, ALLAH ya ƙara miki lafiya dai damu baki ɗaya”.

      “Amin Umm”. Ta amsa mata zuciyarta cike da damuwa. tasan iyayenta suna cike da damuwar halin data tsinci kanta, basu da damuwa sama da lafiyarta, basu kuma da burin da ya wuce su wayi gari suga ta warke.........

      Sallamar Adawiya ta katse tunanin Nu'aymah. Ta ɗan ɗago daga kafaɗar Umm tana amsawa. Sai dai ganin harda Yah Abdallah ya sata maida kan ta sake kwantarwa zuciyarta najin zafin kishi a kansa.

     Rungumeta Adawiya tayi cike da munafincin data saba nunawa idan suna a gaban mutane. Itama sai Nu'aymah ta tarbeta fuskarta fes. Umm dai cike da jin daɗi take dubansu. Yayinda Abdallah kam kallonsu kawai yakeyi. 

     Bayan sun gaisa da Umm, Nu'aymah ta gaida Abdallah batare data yarda sun haɗa ido ba duk da kuwa shi hakan yake buƙata tun ɗazun. A tunaninta zasu tafi ne, amma sai taga sunyi zamansu sunata hira da Umm. Kusan mintuna talatin basu da ko niyyar tafiyar, takaici ya cika Nu'aymah, dan haka kawai yau itama sai takejin zafin Adawiya akan Abdallah. Shiyyasa hirarma bata saka baki, tana lafe jikin Umm tamkar wata mage.

      Basu bar sashen ba har sai da Baba malam ya shigo gidan, dama shi suke jira. Zama kuwa yay suka gaisa a ransa yana mai jin daɗin ganin yanda Adawiya ta kwantar da hankalinta. Yanda tai ƙiba ta ƙara ƙyau kawai ya isa fahimtar da mai kallonta hankalinta a kwance yake sosai. Barci ne ya sake kwashe Nu'aymah har suka bar sashen bata saniba. Koda Umm datai tunanin anan Adawiya zata kwana amma taga saɓanin hakan sai da ta tashe Nu'aymahr ma ta rakata ɗakinta saboda barcin da tayi.


       Washe gari Nu'aymah ta tashi ne duk a takure. Ba komai ya jawo hakanba sai zuwan su Yah Ab da zaman Naser a gidan. Maƙalewa tayi a sashensu taƙi fita har rana. Sai da Umm ma ta takura mata ɗaukar abincin Hajjo ta kai mata sannan ta fita badan taso ba.

       Tunda taga takalma birjik a ƙofar Hajjo taji kamar ta juya. Amma gudun kar Umm tai mata faɗa sai ta daure tayi sallama. Sai da aka bata izinin shiga sannan ta shiga da wata sallamar a bakinta. Duk samarin gidanne a she. Sai Rufaida da Hajjo. Nu'aymah ba wani shiri sukeyi da Rufaidah ba itama, dan ta girmesu, gata kuma da shegen son girman tsiya, shiyyasa take ganin sai dai su bita. Ita kuma Nu'aymah tsiwa. 

      A tare kawai tace dasu “Ina yinin ku”. batabi takan dawa-dawa ya amsa ba ta nufi Hajjo daketa binta da kallon jin daɗin ganin jikinta ya sake warwarewa.

     “Hajjo barka da gida. Ga abinci inji Umm na”.

     “To takwara sannu kinji, yaya jikin naki?”.

     “Naji sauƙi Hajjo”.

   “Alhmdllh ai haka akeso dama. Tun ɗazun nake tsumayen ganinki amma shiru. Tashi ki duba a firiji na ajiye miki fura”.

     Sosai daɗi ya kanata. Cike da ɗoki ta nufi fridge ɗin hajjo ta ɗakko kofin furar tana sakema hajjo godiya. Har zata fice Naser ya kirata. Badan tasoba ta amsa tare da juyowa tana kallonsa. Ya sakar mata sassanyan murmushi tare da miƙewa ya nufo inda take tsaye. Bayare da yay magana ba yay gaba da mata alamar ta biyoshi.

      Bataso hakanba, amma sai ta bisa kawai gudun kar yaga kamar ta masa wulaƙanci. Ɗaya daga rumfar bunun da aka jera guda uku a harabar gidan ya nufa. Nu'aymah ma dai na biye da shi. Kujera ya ja mata baya yace ta zauna. Nanma bata musaba tayi yanda yake buƙata. Sai da ta zauna sannan shima yaja wata ya zauna. 

     Yana zama Abdallah na isowa wajen kamar daga sama. Daga ita har Naser kallonsa sukai. Yayi kicin-kicin da fuska tamkar zai fasa ihu. Batare da yace dasu uffanba yaja kujerar ɗanyan gefen Nu'aymahn ya zauna suka sakata a tsakkiya.

       ‘Ikon ALLAH ’. Nu'aymah ta faɗa a cikin ranta tana kallonsu da mamaki. 


     “Alhaji lafiya kuwa?”. Naser ya faɗa a lalace yana kallon Abdallah. Murtani Yah Ab ya maida masa cike da dizgi. “Itace ta kawo haka”.

      “Humm!” Naser ya faɗa yana ɗauke kansa daga garesa ya maida ga Nu'aymah da mamaki ke cigaba da nuƙurƙusarta a zuciya.

      “Kayi haƙuri ka bamu waje magana nakeson yi da ita Abdallah”.

     “Wannan isar ce kuma baka yiba. Duk abinda zaka faɗa mata inhar kasan ba mara ƙyau bane ka faɗa a gabana mana”.

       “Mtsoww! Ai kasan baka isa sakani yin abinda banyi niyya ba. Nu'aymah tashi muje can...”

       Batayi niyyar binsaba a yanzu. Tayi niyyar kawai tabar musu wajen. Sai dai tana yunƙurawa zata miƙe Abdallah ya daka mata tsawa. “Koma ki zauna kona mareki!!”. Ya faɗa yana ɗaga hannun tamkar zai maketa.

       Ɓata fuska sosai tayi tamkar zata fasa kuka. Dan ita kam sun sakata a tsaka mai wuya. 

     A fusace Naser yace, “Abdallah karka bari nakai bango da kai, wai shin ina ruwanka dani ne? Naga dai Nu'aymahr nan ba matarka bace balle kace zakama mutane iko. Idan ada kayi ikon saboda akwai alƙawarin aure a tsakaninku yanzu saika tuna babu wannan. Ita ɗin allura ce cikin ruwa mai rabo ka ɗauka........”

     “Nine mai rabon kuma insha ALLAHU!!, dan haka ka kama kanka karka bari a jimu da kai Naseer”. 

       “Hhhhhh! Abin dariya. Sannu Abdallah ubana mai bani umarni. ai ka sani kayi sake tun a farkon dama, a yanzu kuma ta suɓuce maka har avada. A da canma dan ba'a bata dama bane akaso mata auren dole da kai, amma sai UBANGIJI yay dubeta ya hana hakan.....”

        “Naser!!!” 

Abdallah ya kirashi cikin ƙaraji da fusata tare da dunƙule hannu tamkar zai kai masa naushi. Ƴar zabura baya Naser yayi kamar irin yaji tsoro ɗin nan. Sai kuma ya kwashe da dariya ya kuma ɗaure fuska duk a lokaci ɗaya. “Oh to ko dukan nawa zakayi ne?!”.

          Bai gama rufe baki ba kuwa Abdallah ya kai masa naushi. Da sauri Naser ya duƙe naushin yabi iska. Ya sake kai masa wani Baba malam da ke bayansu shi dasu Abbah ya daka musu tsawa.

      “Kai!! wane irin shashanci ne haka kukema mutane a cikin gida da hankalinku?. Ko kunya bakujiba kuka zauna faɗa a gaban ƙaramar ƙanwarku, wannan ai rashin hankaline da sakarci”.

         Duk ƙasa sukai da kawunansu kowa na huci. Abban su Adawiya yace, “Ku wuce muje ciki. Kema Nu'aymah shige”.

        Sum-sum ta wuce tana danne dariyar dake cinta a rai tun fara rigimar yayun nata. Tana shiga falonsu kuwa ta fashe da dariya. Da sauri Umm da Rabi dake a kitchen suna aiki duk suka leƙo.

     “K lafiyarki kuwa kike wannan dariyar ta rashin hankali?”.

      Hannu Nu'aymah tasa da sauri ta danne bakinta, da ƙyar ta haɗiye dariyar tata sannan ta kalle su. “Wlhy Umm su Yah Ab ne suka bani dariya”.

     Batare da Umm ta tsaya jin ba'asi ba tai tsaki ta koma kitchen. Rabi kam sai ta nufota tana tambayarta wai miya faru?. Da sauri Nu'aymah ta haɗe fuska tare da zuba mata harara tabar wajen. Itama Rabin da harara ta raka Nu'aymahn, a ranta kuwa faɗi take, ‘Zaki gane shayi ruwa ne yarinya, shegiya mai kama da ƴaƴan aljanu’.

      Oho Nu'aymah batasan tanai ba. Dan tuni ta shige ɗakinta. Sai dai itama a ranta tana matuƙar mamakin munafunci irin na Rabi. amma sam Umm ta kasa fahimtar akwai wani abu a zuciyar Rabi, dan ita ta jima da fahimtar hakan, harma a ranta tana zargi Rabin da ɗaukar sirrin Umm tana fitarwa. Dan akwai ranar data taɓa ganinta bayan ɗakinsu tare da wanda bata fahimci namiji ne ko mace ba suna magana. Sai dai kafin ta zagaya taga wanene ta iske sunbar wajen Rabin ma harta shigo ciki. Tun daga lokacin ta saka mata kahon zuƙa. Taso fahimtar da Umm amma saita hauta da faɗa akan batason wannan halin banzar, dan Rabi a haife ta haifi Nu'aymah harma wanda ya fita. Kuma tun Nu'aymah na ƙarama suke tare ita bata taɓa ganin wani abu mara ƙyau daga gareta ba.

    Tsaki tayi kawai da kauda zancen Rabi a ranta ta koma tuno su Abdallah. Haka kawai takejin al'amarin nasu na sakata nishaɗi. Ba sai an faɗa ba kowa yasan tana tsananin son Abdallah, ƙaddara ce kawai ta shiga tsakanin al'amarinsu. Amma a yau sai kawai yanda Naser yay sai shima ya birgeta. Har takeji zata iya aurensa duk da zuciyarta bawai tana sonsa bane ba. Amma tunda ta haƙura da Yah Ab zata iya maye gurbinsa da Naser ɗin. Sai dai fa tasan lallai akwai ƙura a cikin faruwar hakan kuma.


★★★


      A ɓangaren su Abdallah kuwa faɗa sosai su Baba malam sukai musu akan abinda suka aikata. Dan a gabansu mafi yawan rigimar ta faru shiyyasa basu bi takan jin yanda akai ba. Sai da baba malam ya tabbatar jikinsu yayi sanyi sannan ya ɗora musu da nasiha kuma, ya kuma sakasu bama juna haƙuri sannan suka sallamesu.

        Suna fitowa kowanne ya wurgama ɗan uwansa harara da jan tsaki.............✍


Kuyi manage Please, inada baƙi😒🚶🏻.




_____________________________

ZAFAFA BIYAR 2021

_______________________

   

                 

Hafsat miss xoxo🥰

KIBIYAR AJALI......!

      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

   

          Mamu gee🥰

MIN ƘALB!!😋🤗


        Hafsat rano🥰

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗


        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗


         Bilyn Abdull🥰

SARAN ƁOYE🤗😋


    Duka akan farashi mai rahusar gaske.


Kamar haka👇🏻💃🏻


Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700


Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO 0812652655

ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO

BANK NAME: ACCESS BANK.


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇


0903 234 5899


IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇


  09033181070


💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.



No. 34


............Abu kamar wasa sai ga ƙaramar magana na neman zama babba. Dan kuwa dai rikici sosai ke wakana a tsakanin Abdallah da Naser akan Nu'aymah. Amma sai suka canja taku yanda iyayensu bazasu fahimta ba. A duk sanda Naseer yasa aka kira masa Nu'aymah sai Abdallah yazo ya tsare. Hakama duk lokacin da Abdallah ya buƙaci ganawa da Nu'aymah sai Naser yazo ya hana hakan ta hanyar zama tsakaninsu kamar yanda Abdallahn keyi.

      Hajjo da mafi yawan rigimar a sashenta akeyi tana kallonsu amma tai kunnen uwar shegu da su kamar bata ganiba. Wani lokacinma da biyu take sakawa a nemo mata Nu'aymah ta zauna a sashenta dan tasan nanne wajen zaman su Naser ɗin musamman da daddare.

       Duk kuma wannan abun dake faruwa Adawiya bata nan, dan kwanansu biyu da zuwa sukai tafiya biki ita dasu Hajarah dangin kakarsu maman su Addah. Da Addah ta ƙarrafa ayi tafiyar da Nu'aymah ma. Sai dai yanayin jikinta yasa Hajjo hanawa. Shiyyasa suka tafi su uku harda Kubrah sai Addahn da sauran ƴaƴanta na ma'auri.

        

      Da farko rikicin nasu Naser nishaɗi yake saka Nu'aymah, amma ganin al'amarin na sake ɗaukar zafi sai hankalinta ya fara tashi. Dan neman birkita mata tunani sukeyi har takan rasa wanene yafi cancanta ta mallakama kan nata?.

     Al'amarin bai sake tada hankalin kowaba a gidan sai randa Hajjo take cema Abdallah dama ya haƙura ya barma Naser Nu'aymah. Tunda shi a yanzu gashi yana auren su Yusrah. A fusace yace, “Indai su Yusrah ne zasu masa katanga da mallakar Nu'aymah to lallai zai rusa katangar”.

     Babu wanda ya ɗauki furucin nasa da muhimmanci a lokacin da yayisa. Sai dai ga mamakinsu bayan sallar isha'i sai gashi da zungureriyar takarda har guda biyu yazo ya dire gaban hajjo.

      Kallonsa tayi fuska a yatsine. “Kai wannan takardun kuma na miye ka ajiyemin kamar wani ɗan saƙon kotu?”. Fuska a turɓune yace, “Hajjo sakamakon katangar da kika tabbatar min zata shiga tsakanina da Nu'aymah ne a ciki. Kinga yanzu sai ki daina min baki ko”.

        Sam hajjo bata fahimci zancen nasa ba, amma sai ta saka Omar dake zaune tare da ita ya duba mata. Ɗaukar ɗaya yay yana murmushin diramar kakar tasu da yayansu. Da sauri ya fesar da ruwan da ya ke sha yana faɗin, “What!?” saboda abinda yaci karo da shi a rubuce.

       A rikice hajjo tace, “Miya faru Umaru?”. Jikin Omar na ɓari ya ajiye kofin ruwan tare da ɗaukar ɗayarma ya buɗe. Nanma dai abinda ke cikin ta farkon ce a ta biyu, ai baima san lokacin daya furta, “Hajjo wlhy Yah Abdallah ya haukace! ko kuma ya fara shaye-shaye ku bincika!. Hajjo sakin Yusrah da Adawiya fa ya yi.....”

      “Saki kuma?!!” Hajjo ta faɗa itama tana miƙewa zumbur.

     “Wlhy kuwa Hajjo gashi a rubuce saki ɗai-ɗai”.

      “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Abdullahi!!. A wlhy gaskiyarka kuwa Umaru Abdullahi ya haukace. Ni Zainabu na shiga uku. Kaga kiramin ɗan malam duk inda yake yazo gida”.

        Ɗan jimm Omar yayi alamar tunani, sai kuma ya dubi Hajjo da ranta ke a matuƙar ɓace. Cikin lallashi yace, “Amma Hajjo inaga kamar dai kiyi haƙuri har ya dawo gida. Kinga yanzu bamusan wane uziri yake kan yiba, kiran da za'ai masa zai iya dagula masa tunani, amma idan kince a kirasan dai sai na kirasa ɗin”.

      “Hakane Umaru! Kaima kayi maganar hankali, amma lallai sai na saɓama Abdullahi fiye da zato a gidan nan. Wane irin wawancine wannan? Ashe hankalin da ake ganinsa da shi da girma bashi da shi ɗin?”.

      “Kiyi haƙuri Hajjo, ALLAH ya huci zuciyarki. Ni kaina ban taɓa zaton hakan daga garesa ba. Kinga wannan ai tushen ɓata zuminci ne, idan iyayen namu basu kai zuciya nesa ba sai kiga al'amarin ya kawo ɓacin rai. Sannan su kansu yaran an saka wani abu a zuciyarsu gurɓataccen. Dan zasu iya tsanar Nu'aymahr da yace dominta yayi, hakan kuma bashi da amfani”.

      Ƙwafa kawai hajjo tayi ranta da zuciyarta na ƙara mata suya da ɗaci. Omar dai yayta lallashinta har sai da yaga ta ɗan kwantar da hankalinta sannan ya fice cike da jimami. Sashensu ya nufa, yaje ya faɗama Momy duk abinda ya faru.

      Sosai itama ta rikice hankalinta ya tashi. Dan ta tabbata Abbansu dama wasu a mutanen gidan bazata fita da ga zarginsu ba, musamman ma da akasan taso ya auri ɗiyar ƙanwarta. Waya ta ɗauka ta shiga neman Abdallah. Sai dai harta tsinke bai ɗagaba. Bata gajiya ba wajen cigaba da jera masa kira, amma yaƙi ya ɗaga.


        Hajjo, Omar, Momy sun yi yinin yau ne cikin tashin hankali da damuwar ɓarnar da Abdallah ya tafka. Duk da sun ƙagara Baba malam ya dawo gidan ransu cike yake da fargabar sakamakon da zai biyo baya kuma.

       Sai bayan sallar la'asar baba malam da Abban Abdallah suka dawo gidan. Dan dama tare suka fita. Sunje wani ƙauyene akan maganar wata katafariyar gona da zasu saya. Sunason gyarata su maidata gidan gona a zuba dabbobi kala-kala na kiwo a ciki. Wannan ma ne dalilin da yasa har yanzu shi da Abba Musbahu basu koma ba. Suna son sai komai ya kammala sannan su ɗauka iyalansu su koma inda suka fito sai kuma biki.

       Kamar yanda al'adarsu take ta fara shiga sashen mahaifiyarsu yau ma hakan suna fitowa daga mota can suka nufa. Yanda suke tafe suna firarsu kowanne fuska ɗauke da fara'a dolene su matuƙar burgeka. Dan a kallo ɗaya zaka fahimci ɗunbin shaƙuwa da ƙaunar juna dake a tsakaninsu.

     Sai da sukai sallama Hajjo da ke zaune cikin ɓacin rai har yanzu ta amsa musu da basu izinin sannan suka shiga. Kallo ɗaya sukai mata suka fahimci tana cikin damuwa. Kusan da sassarfa duk suka ƙarasa gareta kowanne na tambayarta tana lafiya?.

       Batai magana ba, sai wajen zama data nuna musu. Sai dai maimakon su zauna a kujerun sai suka zauna ƙasa tamkar yanda suka saba. Gaisheta sukayi, sannan suka sake jero mata tambayoyi akan yanayin nata.

      Ƙwallar da suka cika mata idanu tasa bakin ɗan kwalinta ta share. Hakan sai ya sake tada musu hankali.

     “Inna dan ALLAH ki faɗa mana minene ke damunki? Mune mukai muki laifi? Ko matan mu? Kokuwa a cikin yaran nan ne wani yay miki wani abu?”.

        Sake share hawayen data matso tayi da cewar, “Ni babu abinda kukai min ɗan malam, Abdullahi ne kawai keson watsa mana gida”.

     Hankali a tashe baba malam da Abban su Abdallah suka kalli juna. Cikin ƙarfin hali baba malam yace, “Innah mi Abdallahn ya aikata?”.

       Takardun da Abdallah ya rubuta ta ɗakko ta miƙa musu. Amsa sukayi kowanne ya buɗe guda ɗaya gabansa na faɗuwa. A tare suka ɗago a razane suka kalli juna da ambaton sunan ALLAH. Baba malam har yana tsallaken kalma wajen faɗin, “Innah shi Abdallah ɗinne ya rubuta wannan takardar?”.

           “Shine ɗan malam, shine da kansa ya rubutasu ya kuma kawo mani. Wai dan kawai jiya na bashi shawarar cewar yay haƙuri ya barma Nasiru Zainabu tunda shi yanzu yana da matansa har biyu. Shine fa yau ya kawomin takardar sakinsu Adawiya wai gashinan ya rushe katangar dana ce masa tana tsakaninsa da Zainabu”.

     Abba da ya gaza cewa komai tun ɗazun yace, “Innalillahi..., wai inna kina nufin su duka biyun ya saka?”.

      “Eh mana Lurwanu, baga takardun nan ba duka biyu na baku”.

      Da sauri baba malam ya amshi ta hannun Abba, shima ya karɓa ta hannunsa. Da gaske kuwa su duka biyun ya saki. A take tsananin ɓacin rai ya sake bayyana a kan fuskokinsu. Abba ya miƙe a fusace zai fice. Kiransa baba malam ya shigayi amma ina zuciyar gadon ta motsa. Dan haƙuri kawai ya bashi batare da ya juyoba ya fice.


          Momy na zaune cikin damuwa da fargabar jiran dawowar mijinta Abba ya shiga. Jiki a sanyaye ta dubesa dan ko sallama baiyi ba 

     Takardun guda biyu ya watsa mata a jiki. “Da saninki ɗanki yay wannan aika-aikar ko?”.

      Gaban Momy na faɗuwa ta ɗauki takardun ta karanta, hawayen da taketa faman dannewa tun ɗazun suka zubo mata a saman kumatu. “Wlhy Abban Abdallah ban sani ba. Nima ina zaune Omar yazo yake sanarmin. na kirashi yafi sau hamsin amma ya ƙi ɗagamin waya ma, kai........”

    Baki ya buɗe zai daka mata tsawa Omar da ya shigo basu sani ba yace, “Abba wlhy babu ruwan Momy, hasalima batasan komaiba akan al'amarin nan sai da nazo na sanar mata. Abba ko kasan dama tunda Yah Abdallah ya dawo gidannan baiyi zaman minti biyar da Momy ba. Da ya shigo ya gaidata da safe bazata sake ganinsa ba sai washe gari. Fushi yake da ita babu gaira babu dalili. Ta sakani na tambayesa amma yacemin idan na sake zuwa masa da zancen Momy sai ya ɓatamin rai. Ita kanta nace zan sanar maka abinda ke faruwa amma ta hanani, wai mu bashi lokaci kozata fahimci abinda ke damunsa”.

        Jikin Abba ne yay sanyi, dan tabbas kuwa ya kula tunda Abdallah ya dawo ƙasar nan bai taɓa ganinsa zaune da Momy ba, da farko yaso tambayarta sai kuma yayi tunanin ƙila sai ya fita suke zaman. Wannan ya sakashi yin shiru duk da kuwa yasan yanda matar tashi take da ƙulafucin ƴaƴa musamman Abdallah.

    Nannauyan numfashi ya sauke tare da zama yana cire hular kansa ya ajiya.....


           A ɓangaren baba malam kuwa Abba na fita waya ya zaro ya shiga neman layin Abdallah. Sai dai kuma abin mamaki switch off. Ajiye wayar yayi ya maida hankali ga Hajjo da ke sharar hawaye har yanzun. Kwantar mata da hankali ya shigayi da bata haƙuri. Yace, “Inna ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, insha ALLAHU mu dai wannan bazai kawo mana rabuwar kawuna ba. Duk inda Abdallah ya shiga kuma na tabbata zuwa dare dole ne ya dawo gida ya kwana ai, insha ALLAHU a daren nan sai ya maidasu su duka biyun”.

        “Ɗan malam bazaka gane abinda nake nufi ba, amma duk yanda kake tunanin sauƙi a al'amarin nan da wahala ya kasance hakan. akwai abinda na sani wanda kai da sauran ƴan uwanka baku san da shi ba a gidan nan. Ina barin masu aikatawar ne kawai kafin ranar da zan masu bankaɗa da tonon silili a gaban kowa. Ni dai abinda zan sanar maka yanzu shine da ga Abdullahi har Nasiru ka zaunar da Zainabu ta zaɓi wanda tafi so tunda abin ya zama haka. Kokuma ta auri wani bare can a zauna lafiya. Sannan inason ka nutsu kayi tsai da hankalinka a wannan karon game da kowa a gidannan, koda baka fahimci duka abinda na fahimtaba zaka fahimci wasu daga ciki. Dan kai ne uba a gidan nan, duk da dama nauyi da girman ya rataya a wuyankane tunbayan rasuwar mahaifinku, ina kuma alfahari da yanda ka riƙe hakan, amma sai randa ƙasa ta rufe idanuna zaka sake tabbatar da girman dake bisa kanka da tarin fituntunun da ke kwance a cikin gidannan wanda ALLAH ne kawai hanasu fallasuwa saboda rahamarsa da ikonsa da kuma ƙarfin addu'ar mahaifinku da har yanzu take biye da ku. Kai dai ALLAH ya ƙara maka haƙuri da juriya kawai. Tashi kaje ka huta, ka kumayi ƙoƙarin tausar sauran ƴan uwanka akan duk ma abinda zai iya biyo baya game da wannan gagarumar fitinar da Abdullahi ya ɗaɗɗago mana”.

       Kasa cewa komai baba malam yayi. Cike da ruɗanin maganganun Hajjo ya jinjina mata kansa kawai da miƙewa ya fice zuwa nasa sashen. Bai iske kowa a falon ba sai Muhammad dake karatun Al-Qur'ani na haddar da aka basu a islamiyya. Yaron bai dakata daga karatun da yakeyi ba, shima kuma bai masa magana ba ya wuce ɗakinsa. 

        Komai tsaf a gyare kamar yanda ya saba zuwa ya iske, ga ƙamshi mai daɗi. A ɗaya daga kujerun ya zube hankalinsa har yanzu baya tare da shi. Dan ransa da zuciyarsa cike suke da tarin ruɗanin kalaman mahaifiyar tasu. Shi kansa yasan akwai abubuwan dake kwance a gidan nan ƙwarai da gaske. Waɗanda da yawansu shi da iyalinsa sun cutu matuƙa a cikinsu. Koma yace suna kan cutuwa. Ya kumayi imani da ALLAH babu wani baƙon ido daga waje da zasuce yana aikata su, dolene mai aikatawar a cikin zuri'arsu yake. Yasha yin tunanin tsananta bincike, amma sai zuciyarsa ta gargaɗe sa da yin haƙuri, sannan yana mai tsananin jin tsoron wanda sakamakon ɓarnar zata tabbata a garesa. A ganinsa gara kawai a cigaba da tafiya a lulluɓen dan UBANGIJI mai ji ne kuma mai ganine akan kowa da komai..........

        Taɓa shin da akayi ne ya saka tunaninsa katsewa. Duban Umm da tun ɗazun take masa magana yay. Fuskarta cike da damuwa tace, “Malam lafiya kuwa? Wane irin zurfafa tunanine haka? lna fatan dai lafiya ko?”.

         “Humm! Jannat lafiyar nan da dauƙi”.

      Saurin zama tayi hannunta riƙe da kofin data zuba masa ruwa tana faɗin, “Miya faru?”.

      Ruwan ya fara karɓa ya sha, ta sake ƙara masa ya shanye sannan ya ajiye kofin ya labarta mata duk abinda ya faru, harma da zancen da Hajjo tai masa.

         Duk da itama ta jima da ji a ranta duk abinda Hajjo ke zargi a kwaishi a gidan hakan bai hanata jin tashin hankali ba. Ita kanta tanason sanin mai aikata musu SARAN ƁOYE a lokuta da dama. Sai dai tsoron wanda zata gani yana aikatawar ke sakata sama ranta haƙuri da barin komai hannun UBANGIJI.


★★★★

    

           A yau dai har dare Abdallah bai dawo gidanba duk jiran da su baba malam sukai zaman yi masa. Dole suka haƙura suka kwanta al'amarin nacin ransu da zuciya.

        Washe gari bayan fitowa sallar asuba baba malam da sauran ƴan uwansa suka hallara gaba ɗaya a sashen mahaifiyarsu. Bayan sun gaisheta suka sake haɗuwa gaba ɗaya wajen bata haƙuri akan abinda Abdallah yayi, suka kuma tabbatar mata insha ALLAH zasu dai-daita komai ba sai yayi tsamari ba.

       Batace da su komaiba dai, sai dai ta musu addu'ar nasara da nemawa Abdallah dama sauran yaran shiriya gaba ɗaya.


       A wannan yinin maganar sakin ta shiga kunnen kowa dake a gidan ciki harda Addah da yaranta dake can suna shan biki. Aiko ba ƙaramin rikita musu lissafi Adawiya tayi ba. Dole babu shiri suka tattaro suka nufo kano zuciyar kowa babu daɗi.

       

      Tunda saƙon saki ya isa kunnen Yusrah kuwa sai wani tarin farin ciki ya kamata. Bama tasan lokacin data shiga dirga tsalle akan gadon ɗakinsu ba. Kafin ta sakko da sauri ta shiga bayi ta ɗauro alwala. Salla tayi raka'a biyu na godiya ga ALLAH daya kawo ƙarewar wannan aure da ko tarewa batayi ba a cikinsa. Dama tunda su Adawiya suka diro ƙasar bata da wani sukuni. Shiyyasa ta koma yinin makarantar Tahfiz ɗin gidansu dan kawai ta gujema ganinsa. Hakan kuwa akayi, dan tunda suka iso sau biyu ta haɗu da shi. Ɗaya da daddare ya shigo sashensu wajen Abba. Na biyu kuma a sashen hajjo taje kai mata abinci. Duka a haɗuwar tasu gaisuwa ce kawai ta shiga tsakaninsu. Yanda baya sakar mata fuska itama bata shiga sabgarsa sam, dan baya wani nuna alamar akwai ko ɗigon haƙƙinta daya rataya a kansa ma. Hakan kuma bai dameta ba, to gashi cikin amincin ALLAH komai ya zama yanda taketa fata a kullum. Ba ƙaramin azumi da ƙiyamullaili tayi ba akan auren nan a cikin watannin nan. Dan ita kaɗai tasan dalilin rashin son auren.


        Duk wannan ruguɗai da akeyi Nu'aymah batasan anai ba ita kam, dan Umm da baba malam babu wanda ya sanar mata. Sashen Hajjo kuma yanzu ba wani shigarsa takeba sosai saboda takurawar Nasir da Abdallah da suka maida sashen hajjo wajen zamansu. Ta gwammaci taita zama a sashensu, idan Muhammad na gidan susha shirmensu, idan kuma ya fita makaranta tayi kallo idan akwai wuta ko su zauna hira da Umm. Wani lokacin kuma tai barcinta dan Doctor ya ce ta dinga yawan barci, shiyyasa ma ya saka mata maganin barci a magungunanta.

           Yauma tana a ɗaki tasha barcin rana har su Adawiya suka dawo bata saniba. Ta fito wanka tai sallar la'asar, shiri ta farayi da ƙudirin zuwa islamiyya yau dan tanajinta Alhmdllh. Tana tsaka da saka kaya ta jiyo kururuwar kuka kamar muryar Adawiya kuma. Saurin ƙarasa saka kayan tayi ta fito, a mamakinta duk ma sai ta iske ƴan gidan a tsakar gida kowa ya fito an rufu kan Adawiya. Gabantane ya faɗi da tunanin ko Accident sukayi a hanya. Da sauri ta shiga bin kowa da kallo sai taga kowa ma yana nan, harsu Aunty Aysha ma basu wuce gidajensu ba nan sukayo.

     Kallon Jafar dake kusa da ita tayi tace, “Jafar miya faru wai?”.

      “Aunty Nu'aymah ban saniba nima. Kawai dai naga Aunty Adawiya na kuka tana cewa wai indai aka rabata da Yah Ab zata mutu”.

       Kafesa da kallo Nu'aymah tai tana son fassara kalaman nasa amma sunƙi fassaruwa. Dubanta ta kai ga Umm dake lallaɓa Adawiya taje sashensu amma taƙi, hakan ya sake tabbatar mata da lallai ba lafiya ba kuwa. Baba malam daya shigo gidan yanzunne ya dakama Adawiya tsawa. Jiki na rawa ta miƙe tsaye.

      “Wane irin rashin hankaline wannan tun daga wajen gate anajin muryarki, tona mana asiri zakiyi da shirme ko mi?. To wlhy bara kuji bama ita ba duk wanda na sakejin bakinsa a wannan maganar saina ɓata masa rai, naga dai Abdallahn a ƙarƙashin ikonmu yake shima, dolene kuma yabi abinda mukeso inhar yana buƙatar gamawa da rayuwarsa lafiya. Kowa ya shige ciki”.

        Jan ƙafa kowa ya shigayi zuwa sashensa. Kubrah ta kama hannun Adawiya suka shige tare. Inda suka bar Addah da bata fitaba nan suka isketa zaune. Babu wanda taima magana a cikinsu har suka zazzauna kowa na ƙannun magana. Batace musu komaiba dai har lokacin, saima jingina da tai da kujera ta lumshe idanu.


          Nu'aymah suna shiga sashensu ta shiga tambayar Umm abinda ke faruwa. Dan ita harga ALLAH bata fahimci komaiba dai har yanzun. A taƙaice Umm ta faɗa mata, sai ko ta zabura a matuƙar razane. “Ya salam. Umm Yah Ab kuwa yana da hankali?! Wannan ai gogama mutane sharri ne da zai ce saboda ni ya aikata saki ga matansa”.

         “Wannan sakaki a cikin da yayi shine ya sake tada mana hankali muma Nu'aymah. Dan zai iya zama wata fitina daban wadda ba'asan iyakar inda zata tsaya ba a gidan nan. Yanzu dai Abbanku ya gano inda yake, ya kuma bashi daga nan zuwa kwana uku idan bai dawo gida ba zai haɗu da ɓacin rai mai tsanani daga garesu”.

         “Ai gara yazo ya kwance wannan ƙullin da yay min nikam, a dalilin mi zai sakani tsakkiya, a barni da abinda ya damenima nikam ya isheni Umm”. Tai maganar tana fashewa da kuka.

        Tausayinta ne ya kama Umm sosai, ta ruƙo hannunta ta sakata jikinta tana lallashi............✍



😩 Yah Ab ya zaka mana haka ne?🤦🏻‍♀️🙆🏻‍♀️

_____________________________

ZAFAFA BIYAR 2021

_______________________

   

                 

Hafsat miss xoxo🥰

KIBIYAR AJALI......!

      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

   

          Mamu gee🥰

MIN ƘALB!!😋🤗


        Hafsat rano🥰

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗


        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗


         Bilyn Abdull🥰

SARAN ƁOYE🤗😋


    Duka akan farashi mai rahusar gaske.


Kamar haka👇🏻💃🏻


Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700


Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO 0812652655

ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO

BANK NAME: ACCESS BANK.


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇


0903 234 5899


IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇


  09033181070


💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.



Ina fatan ansha weekend lafiya? ☺️🤝🏻😘



No. 35


.............Kamar da wasa sai ga Abdallah ya shanye kwanaki ukun da baba malam ya bashi babu shi babu mai kama da shi. Ran baba malam da sauran ƴan uwansa ya sake ɓaci matuƙa, amma duk sunta ƙoƙarin dannewa. Dan hatta Hajjo ranta a ƙololuwar ɓace yake.

          Hankalin Nu'aymah ne ya sake ta shi. Dan koba komai har yanzu tana son Yah Ab, bazata so bari ya cigaba da munana a idon iyayensu ba akan shima son da yake mata. Tunda duk abinda yake aikatawa na laifi a garesu a kanta ne.

          Kuka sosai Nu'aymah tasha akan wannan al'amari. Musamman ma da itama tai kiransa da wayar Umm amma yaƙi ya ɗaga tun a ranar. 

        Yau ma wayar ta sake ɗakkowa ta Umm ta kirasa, sai dai bai ɗaga ɗin ba. Haƙura tayi da kiran, sai dai kuma bayan kamar awa guda kamar an tsikareta ta sake zuwa ta aro wayar again. Test massege ta tura masa, bakinta cike da addu'ar ALLAH yasa ya duba.

    Bayan kamar mintuna biyar kuwa sai ga reply ɗinsa. Jikinta har rawa yake wajen ɗauka ta duba.


       *_“Zan iya amsar gayyatarki akan dalili guda ɗaya, idan kin amince da shi ko yanzu zan iya dawowa gida na fuskanci iyayenmu”._*

        _Dalilin kawai ki amince a ɗaura mana aure ranar bikin su Kubrah._


       Wani irin mugun bugawa ƙirjin Nu'aymah yayi, tai mugun waro manyan idanunta waje hawaye masu zafi na rige-rigen fitowa. A fili cike da karyewar zuciya ta furta, ‘Anya kuwa Yah Ab bai fara shaye-shaye ba jama'a? Na shiga uku ni Zainab, wane irin tsaka mai wuya bawon ALLAHn nan yake ƙoƙarin jefani a gidan nan?’. 

        Kuka sosai ta kuma sha fiyema dana ɗazun, dan sai da taji kanta ya fara sara mata sannan ta haƙura. Har bayan anyi sallar isha'i bata fitaba ta cigaba da zama a ɗaki. Wayar Umm ma da Muhammad ya shigo aran littafinta na *Ahdhari* ta bashi ya kai mata. Yunwa ce ta fara takura mata, dole ta miƙe ta shiga bayi, wanka tayo ta fito, tai shirin cikin wando da riga na barci masu taushi. Tanajin yunwa amma bata jin cin abincin kuma, sha'awar shan lipton ne yazo mata a rai. Dan haka ta miƙe ta ɗauka hula ta saka a kanta sannan ta fito.

      A falo sukaci karo da Rabi ɗauke da ƙaramin jug da alama ma ɗakinta zata. Baki Rabin ta washe ta na faɗin, “A'a uwar ɗakina kin tashi ashe? Kamar kinsan kuwa zoɓon nan zan kai miki dama ko zaki ɗansha dan na sanki da son zoɓo”.

      Ɗan lumshe idanu Nu'aymah tayi ta buɗe akan rabin tana ɓata fuska kaɗan. “No bar zoɓon nan ma dai baba Rabi. Idan ban takura miki ba dan ALLAH haɗamin lipton kaina ciwo yake min”.

       Da sauri Rabi tace, “Ah wlhy babu wani takura uwar masu gida. Kinga zauna bani mintuna biyar kacal, barama nai miki amfani da ganyen shayin baba malam, ina dai kina so ko?”.

        Kai kawai Nu'aymah ta gyaɗa mata dan surutunta ya isheta. A ƙasan ranta kuma tana mamakin yanda Rabin ta amsa dafa mata shayin ɗin babu ko musu balle sukai ga faɗan da suka sabayi kullum.


        Ɗakin Umm Nu'aymah ta nufa kafin Rabi ta kammala, sai dai ta iske tana wanka dan haka ta fito akan idan ta gama zata koma. Fitowarta dai-dai da fitowar Rabi da ga kitchen ɗauke da kofin shayi dake ta turiri. Sai da tai mata godiya sannan take tambayarta ko baba malam ya shigo?.

       “A'a bai shigoba, dan naji Muhammad na faɗin kamar yayi baƙi ne ma”.

     “Okay”.

   Kawai Nu'aymah ta faɗa tare da ɗaukar kofin ruwan zafin ta kai bakinta tana ƙoƙarin kunna television da hannunta na haggu.

      Sosai shayi yayma Nu'aymah daɗi, harta shanye wanda Rabi ta zuba mata itama ta sake zuba sauran wanda ya rage a butar shayin. Tana cikin shan wanda ta zuba ɗinne Umm ta fito...

         “Oh dama kin tashi?”.

“Eh, nama shiga ɗakin na tarar kina wanka. Umm kaina ke min ciwo ALLAH”.

        Cike da kulawa Umm dake dubanta tace, “Ba dole kanki yay ciwoba Nu'aymah, kukan da kikayine ai. Halan ma da kika tafi ɗakin ba barcin kikayi ba?”.

         “Umm barcin nefa bai zoba. Amma yanzu naɗan fara ji, sai dai zan jira Abba ya shigo sannan naje na kwanta”.

          “Wayasan sanda zai shigo, ki tashi kije ki kwanta banason sakarci. Miyasa ke wai sam baƙya tattalin lafiyarkine? Kin fison kullum ki ganmu hankali a tashe”.

      “Kiyi haƙuri Umm ba haka baneba wlhy, dama dan yau duk bamu haɗu da Abba bane shiyyasa. Amma bara nasan insha ALLAHU da safe zamu haɗu. Sai da safe”.

      “Ki tabbatar kinyi addu'a kafin ki kwanta”.

     “To Umm”. 

Nu'aymah ta faɗa tana nufar ɗakinta badan taso hakanba. Kamar jira tana kwanciya sai barci mai nauyi ya kwasheta batare da ko addu'ar da Umm ta gargaɗeta yi ba tayi ɗin.


★★


       Sai wajen sha ɗaya baba malam ya shigo gidan. Koda ya tambayi Nu'aymah Umm ta sanar masa ta kwanta sai ya nufi ɗakinta. Yayi sallama kusan sau uku babu amsa, dan haka ya juyo falo yana faɗin, “Nayi magana shiru, inaga tayi barci ma”.

        “Dama tace barci takeji, amma tsabar fitina wai zata zauna jiranka dan yau duk bata gankaba”.

     Murmushi kawai baba malam yayi, amma baice komaiba.


          Kusan ƙarfe sha biyu saura Nu'aymah ta farka da wani Masifaffen ciwon ciki. Juye-juye ta shigayi a kan gadon tana kiran sunan Umm. Tun abin na mata sama-sama harya fara fin ƙarfin tunaninta. Yunƙurawa tai da ƙyar ta tashi zaune tana ambaton ‘Innalillahi.....’ da ƙyar ta iya sakkowa da ga saman gadon. Sai dai yanda ƙafafunta da mararta suka riƙe sam bazata iya takawa ba. 

       Ƙasa ta durƙushe hannunta ɗaya riƙe da cikinta, ɗayan kuma ta dafe gado da shi tana matse idanu da cije baki. Cikin azabar data isheta ta fara ƙwalla kiran sunan Umm da baba malam tana roƙon suzo su taimaketa zata mutu. Yanda zufa ta jiƙeta sai ka ɗauka ruwa aka watsa mata. Wata gigitacciyar ƙara ta saki lokacin da idanunta ke sauka akan Windown ɗakinta. Gilmawar mutum ta gani, wanda alama ta nuna ya jima a wajen tsaye koma waye. Ai sai kawai ta daddage ta fasa ƙarar da tafi ta farko badan taji tsoro ba sai dan wani irin kartawa da mararta tayi tamkar numfashinta zai bar ganar jikinta a lokacin.......


        A rikice baba malam da Umm da barci ya fara ɗauka yanzun suka farka. Har rige-rigen fitowa sukeyi dan ƙarar Nu'aymah sun jitane tamkar a tsakkiyar ƙwalwar kansu.

    Kwance suka isketa a ƙasa wanwar tana numfashi da ƙyar. Baba malam yay saurin kunna fitilar ɗakin mai haske, Umm kuma ta nufeta tana kiran sunanta. Sai dai ina Nu'aymahn ta suma. Sake rikicewa Umm tayi, ta fashe da kuka itama tana girgiza Nu'aymahn.

       Baba malam daya nufosu shima a rikice yay sauri ja da baya jin ƙafarsa cikin wani abu mai ɗumi. Kallon inda ya taka ɗin yayi. gabansa yay bala'in faɗuwa ganin jini. Cikin rawar jiki ya durƙusa da kai ɗan yatsansa ɗaya yaɗan dangwalo. Tabbas jinine kuwa. Dan haka yace, “Jini kuma?”.

     Saurin kallonsa Umm tayi itama. Tace, “Jini kuma malam? A ina?”.

      Da hannu ya nuna mata, sosai zuciyarta tai masifar harbawa. Tabi jinin da kallo har jikin Nu'aymah da alamu suka nuna daga nan yake fita. Kafin ta iya cewa wani abu sai ga Hajjo da Addah da Momy sun shigo a rikice. dan duk wanda yake a gidan yaji ihun Nu'aymah saboda dare yayi. Sai kuma ga matan Abba Musbahu su maman Yusrah, suma Samarin gidan duk sun shigo sai dai sun dakata a a falo.

       Hankalin kowa ya tashi da ganin wannan jini. Ga dare ya fara.

    Hajjo tace, “Mafita ya kamata mu nema ba wai koke-koke ba. Ya kamata a tado su Ahmadu dan a tafi asibiti”.

       Addah data maida Nu'aymah jikinta ta share hawayen da ke ziraro mata itama da faɗin, “Hajjo inaga a kira Doctor Sale tunda nan kusa yake shi. amma yanzu ko asibiti akaje zaiyi wuya a samu likitan kirki. Gashi yarinyar nan tana ciki wani hali”.

       Dukansu sunyi na'am da zancenta. hakan ya saka Abban Abdallah fita dan ya kiran Doctor Sale a waya. A falo ya wuce samarin gidan tsaitsaye jigum-jigum. Kusan a tare suka shiga tambayarsa mike faruwa?.

       A taƙaice ya basu amsa yana ƙoƙarin kai waya kunnensa.


         Cikin mintunan da basu gaza talatin ba Doctor Sale ya iso. Malam ƙarami ne yaje ya shigo da shi, yay masa iso har ɗakin Nu'aymah. Zuwa lokacin su Momy nata ƙoƙarin saka abu ana kwashe jinin da har yanzu bai dai na zuba da ga jikin Nu'aymah ba. Su baba malam kuma sun koma da ga ƙofar ɗaki. 

      Ko gaisuwa bai tsaya sunyi ba ya shiga. Su Umm duk suka fito aka barsa da Addah da Umman su Yusrah a ciki. Ƙoƙarin tsaida jinin ya farayi, kafin ya fara bama Nu'aymah taimakon gaggawa.

     Kamar wasa sai da ya kwashe awa guda domin ƙoƙarin ceto ta, Umman Yusrah nata gyara wajen, Addah kuma na riƙe da Nu'aymahn har yanzun. Jinin an samu ya tsaya, harma an saka mata ƙarin ruwa bayan an samu ta farfaɗo. Fita yay ya basu waje dan su ƙarasa gyara mata jikinta.

  

         Yana fitowa duk suka yo kansa suna tambayar yaya jikinta. Doctor Sale ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, “Alhmdllh malam ku kwantar da hankalinku. Komai ya dai-daita, sai dai kuma anyi asarar cikin da ke jikinta. Nayi iya ƙoƙarina na ganin cikin bai dalwantaba amma hakan ya gagara, sai dai haƙuri”.

     Ga ba ɗayansu wani irin kallon rashin fahimta suke masa. Cikin ƙarfin hali Hajjo tace, “Kai ɗan nan bamu fahimci zancenka ba. Miya haɗa Zainabu da ciki kuma? Ko kuwa kana nufin wani ciki dai bana haihuwa ba?”.

        Shima ɗin dai kallon mamakin yake mata, kafin cike da son fahimtar da ita yace, “Mama ina nufin ciki na haihuwa mana, ko bakusan tana da shi ba ne?”.

        Kallon juna suka shiga yi ƙirjin kowa na bugawa da sauri-sauri musamman ma Baba malam da Umm da Hajjo. Da rawar harshe Umm tace, “Ya zakace ciki a jikin Nu'aymah?”.

          “Ikon ALLAH! Hajiya wlhy ciki ne da ita ɗan sati shida ma kuwa”.

       Umm zata sake magana baba malam da zufa ke karyo masa ta ko ina a sannan jikinsa yay saurin katseta da faɗin, “Doctor yanzu wane hali take ciki ita?”.

        “Ah Alhmdllh malam, yanzu haka tama farfaɗo, na kuma saka mata ruwa da zai sakata barci, zuwa da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo na sake dubata sai na taho da magungunan da ya kamata tai amfani dasu. Zuwa da yamma idan taji ƙarfin jikinta za'a kaita asibiti dan na sake dubata da ƙyau, a kuma yi mata wankin ciki, dan gaskiya ɓarin yazo mata da matsala kamar”.

      “To shikenan, mungode sosai Doctor, ALLAH ya saka da alkairi”.

      “Amen” Doctor Sale ya amsa saboda jin daɗin addu'a daga babban malami irin baba malam. Daga haka yay musu sallama ya tafi ya barsu da ruɗani.


      Tun fitar Doctor Sale kowa ya kasa yin ko motsi. Sai ma Umm da hajijiya ke ɗauka kaɗan-kaɗan ce ta ɗan zauna jin zata faɗi. Cikin ƙarfin hali Hajjo ta shiga ɗakin Nu'aymahr, ta iske su Addah sun kammala kimtsata harma sun lulluɓa mata bargo, ga ƙarin ruwan da aka saka mata yana tafiya dai-dai.

       “Kunga kuje ku kwanta dare na ƙara nisa. Tunda ALLAH yasa ta samu barci. Suma sauran ku sanar musu suje su kwanta”.

      Babu musu sukai mata sallama suka fita. Su da basusan mike faruwa ba sai suka shiga sake kwantar musu da hankali akan jikin Nu'aymahn da sauki. Hajjo ma tace kowa yaje ya kwanta.

        Su Abban Adawiya ne kawai sukace Alhmdllh, amma babu wanda yay yunƙurin tafiyar sai da Baba malam yay magana. Har kowa ya gama ficewa da ga sashen baba malam da Umm basu iya motsawa ba. Sai bayan kusan mintuna goma sannan ya kama Umm ta miƙe da ƙyar. Ɗakin Nu'aymah suka shiga. Hajjo dake zaune ta zubama Nu'aymah ido ta ɗago tana kallonsu.

     Saurin yin ƙasa da kai Umm tayi, dan sai yanzu me wasu zafafan hawaye suka sami damar ziraro mata. Har ga ALLAH zuciyarta ta shiga cikin matsanancin ruɗanin bayanin Doctor Sale. Wani sashe yana gaskatawa wani sashe na ƙaryatawa. Hakama baba malam a matuƙar ruɗanin yake. Amma da yake shi namijin duniya ne sai ya shanyeshi tsaf dan a ganinsa yana buƙatar lokacin yin tunani akan hakan..........

      Hajjo ce ta katsesu da faɗin, “Ban yarda da wannan maganar ta likitan nanba, duk da kuwa koni jinin ya matuƙar tsoratani tunkan bayaninsa. Sai dai hakan bashine ke nufin mu amince da cewa ciki a jikin Zainabu ba. To ta yayama hakan ta faru? A ina kuma? Yaushe kuma?”.

      Kan baba malam a ƙasa, muryarsa a matuƙar cinkushe da tashin hankali yace, “Inna bazamuyi saurin ƙin gaskatawaba, tunda kinga ai aikinsane hakan”.

      “Duk da aikin nasa ne ban yardaba. Sai an nemo wani likitan ya sake dubata tukunna. Kokuma muje asibiti da safe idan ALLAH ya kaimu”.

       Basu iya mata musu akan hakanba da ga shi har Umm da bata iya furta komai ba har yanzun. 


WASHE GARI


         Da safe Doctor Sale ya dawo gidan zuwa 8:30 kamar yanda yay alƙawari. A lokacin Hajjo ta gyara Nu'aymah da kanta. Yayinda Rabi ta sake tsaftace ɗakin ita kuma.

       Ya dubata yanda ya kamata, ya kuma tabbatar musu komai Alhmdllh dan UBANGIJI ya sauƙaƙa al'amarin. Ita dai Nu'aymah ba wani fahimtarsu take ba, dan batasan ainahin abinda ya sameta ba bayan ciwon cikin da zata iya tuna tayi kafin gushewar hankalinta.

     Ya bada magungunan da zatay amfani da su, da waɗanda bashi da su za'aje a sayo. Daga haka yay musu sallama akan da yamma zai dawo ya sake dubata idan ya taso aiki. Godiya baba malam yay masa. Hajjo da Nu'aymah dai basuce komai ba. Hakama Umm da tun daren jiya da hankalinta yabar jikinta har zuwa yanzun bai gama dawowa ba.


        Baba malam baiso maida hankali akan maganar hajjo na nemo wani likitanba. Amma ganin ta matsa sai ya bi umarninta suka kira wani Doctor Faisal abokin Ahmad. Wajen ƙarfe goma na safen shima ya iso, a lokacin an maida Nu'aymah sashen hajjo.

      Shima dai sun bashi dama yayi aikinsa yanda ya kamata. Kafin daga bisani yay zaman basu bayanin daya matuƙar tada musu hankali akan result ɗin shima. Ya tabbatar musu da gaske Nu'aymah ɓarin ciki tayi ɗan sati shidda da wasu kwanaki, amma babu wata matsala tattare da ita, magunguna kawai zataita sha jikinta zai koma normal.

      Har ya kai karshen bayaninsa babu wanda ya iya motsawa a falon, sai hajjo ce tai ƙarfin halin masa godiya.

     Bayan wucewar Doctor hajjo ta sake tabbatar musu shima bata yarda da nashi aikinba. Duk yanda baba malam yaso fahimtar da ita tace bata yarda ba. A yanzu sai su ɗauki Nu'aymah suje asibiti kawai, kuma na gwamnati take so.

    Ɗari bisa ɗari su Abba Musbahu sun yarda da maganar hajjo, dan suma zukatansu sam basu aminta da maganar ɓarin cikin Nu'aymah ba sam. Sunfi baba malam yawa, dan haka dole yay shiru ya barsu. Amma a ƙasan zuciyarsa bai son sake fitar maganar kuma dan hakan tamkar tonama kansu asirine sukeyi, tunda yasan ba duka likitocinne zasu iya barin maganar a cikinsu ba duk da yasan basusan Nu'aymah bata da aure ba.

           


_____________________


         Bisa matsawar hajjo suka ɗauki Nu'aymah da sam jikinta babu ƙarfi zuwa asibiti. Kasancewar su manyan mutane da ake girmamawa basu wani sha wahalar ganin likita ba, a yanzu kam mace ce ma Doctor Halima. Itama ɗin dai ta gunar da aikinta cike da ƙwarewa. Bayan kamar awa biyu ta basu samako dai-dai dana su Doctor Sale. Dan ta sake tabbatar musu da Nu'aymah tayi ɓarin ciki ɗan sati shida da wasu kwanaki dai, harma ta ɗora da faɗin Nu'aymahr na buƙatar hutu sosai da yawaita cin abinci mai inganci saboda jinin data zubar.

        Ba ƙaramin tashin hankali suka sake tsintar kansu ba a wannan karon kam. Dan ko masu tatsuniya sunce Ƙurun ƙus, anzo ƙarshe. Hajjo mai gardamar bata yardanba a yanzu sai bata iya cewa komai ba. Haka suka tattaro suka taho, dama ita da Ahmad da Naser da Abban su Abdallah da Addah ne suka je. 

        Ganin Hajjo na sharar hawaye Nu'aymah da ke magana da ƙyar saboda rashin ƙarfin jiki ta matsa da son jin mike damun kakar tasu?. Banza tai mata, hakan yasa tunanin Nu'aymah ko hajjo bataji ba ne sai ta sake maimaitawa.

        Tsawar data sakata ɗinke bakinta Hajjo tai mata, ta kuma ja mata dogon gargaɗi akan ta barta taji da abinda ya dameta. Shiru kawai Nu'aymah tai tana kallon hajjon, a ƙasan ranta ko fal tambayoyin mike faruwa ne?.

    Koda suka iso gida Addah ce ta taimakama Nu'aymah zuwa sashen hajjo, inda suka iske Abdallah da ya dawo gidan tare da sauran samarin gidan suna zaman jiran tsammanin dawowarsu.

         Kowa ransa babu daɗi ya shiga yima Nu'aymah sannu, yayinda Yah Ab ya kafeta da idanu kawai yana kallo. Itama dai kallon nasa takeyi. a ƙasan ranta kuma tanajin daɗin dawowarsa gidan. 


      Basuyi zaman mintuna biyar ba baba malam da sauran ƴan uwansa suka shishshigo harda Umm ma da sauran matan gidan dan Hajjo ce ta aika kiran kowa. Sai dai babu yaran gidan da ƴammata. Yaseer ma dake falon zaune tun ɗazun korashi waje akayi, Abba Musbahu yace yaje ya tattara yaran su wuce islamiyya.

         Shiru falon yayi kowa na jiran mi hajjo zata faɗa, Nu'aymah da ganin ita ba'ace ta tashi ta fitaba taita binsu da kallo a ƙasan ido tana mamakin yanda fuskar kowa ke ɗauke da ruɗani da tashin hankali........

       Maganar Hajjo ce ta katsema Nu'aymah tunani.

        “Alhamdulillahi, kamar yanda na buƙaci zuwa asibiti dan tabbatar da abinda zuciyata ta kasa gaskatawa ga shi munje mun kuma dawo. Sai dai abin razanin da tashin hankalin shine babu banbancin magana tsakanin likitocin farko da wadda ta duba Zainabu a yanzu. Itama ta sake tabbatar mana cewar Zainabu ɓarin ciki tayi ɗan sati shidda........”

       “What?!!!”.

Nu'aymah ta katse hajjo a zabure tana miƙewa zaune zumbur tamkar ba itace kejin kamar iska zata ɗauketa ta faɗi ba yanzun. Jikinta na matuƙar rawa tace, “Hajjo ban ganeba dan ALLAH! Wace Zainabu kike magana badai ni Zainab ɗinba?”. 

     Matsananciyar tsawa baba malam ya daka mata, ai bama tasan ta koma ƙasa rib ba ta zube a carpet saɓanin kujera da take kwance a kai ɗazun. Baba malam ya nunata da yatsa yana faɗin, “Zainab!! Wlhy tallahi kinji na rantse, inhar na sakejin bakinki batare da an baki izinin magana ba sai kinyi nadama”.

      Babu wanda ya iya ko motsi, dan jin ainahin sunan Nu'aymah a bakin baba malam ya tabbatar musu da lallai magana tazo iyaka. Ita kanta jin sunan daya kiratan ya saka zuciyarta ƙara gudu da tsitstsinkewa lokaci guda, wani bahagon tsoro da ruɗani suka da ɗa mamaye dukanin gaɓɓanta.

      Hajjo data juyo tana kallonta tace, “Zainabu bama buƙatar wani ja'inja ko rantse-rantse, nan gurin duk zuri'armune babu wani bare a ciki. ki daure ki faɗa mana wanda ya aikata miki wannan ɓarna. Shin da ganganci ne kokuwa fin ƙarfinki aka y? Wanene uban cikin nan da ya salwanta jiya?”.

          Sake rikicewa Nu'aymah tayi, jikinta na rawa tace, “Wlhy hajjo, na rantse da UBANGIJIN al'arshi ban taɓa aikata abinda kuke tuhumata da shi ba. ALLAH shine shaidata ni banda ciki.........”

         Wuƙa sharɓeɓiya Abba Musbahu ya fiddo ya nunama Nu'aymah, sai ƙyalli take da ɗaukar ido, mai kallo daya ganta yasan ta cancanci a kirata da suna GAYAWA JINI NA WUCE.

       “Nu'aymah kinga wannan wuƙar ko?”.

      Kai ta ɗaga masa da sauri jikinta na cigaba da rawa.

       Ya jinjina  kansa da cigaba da faɗin, “Inhar kikace zaki mana wasa da hankali to nan tsakkiyar falon nan zansa su Abdallah su kwantar min dake na yankaki kamar yanda ake yanka ragon layya. Ke dawa kuke aikata wannan shaiɗancin anan gidan.....?”

      Kai Nu'aymah ta shiga girgizawa tana kuka tamkar ranta zai fita. Bakinta kuwa sai wani irin karkarwa yakeyi kamar laɓɓanta zasu zubo ƙasa. Ta buɗe baki zatai magana sai kuma ta sake rushewa da wani sabon kuka.

     

     Kamar daga sama sukaji a bayansu ance, “Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan ita ta gaza baku..........”✍


😱😱To wane majanunun ne kuma wannan?.

No comments

Powered by Blogger.