Sanadin Zane 9-10


🅿️9️⃣🫦1️⃣0️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim


        Watoh shi ga casbi baya kusanta iyali toh be isah ba wallahi aike ba dutse bane 


Kuka kawai sa'a keyi Fahad ya hau fad'a Bata da hankali da kunya take fadin abinda be dace ba "


Kawu yadaka me tsawa yace"barta ta fad'a d'acin Dake ranta a daketa a hanata kuka ya tana da lafiya a maidata katako toh da sake Ni badan Kar yace in dawo me da abinda ya kashe ba da  gobe sai in maka shi kotu yariya  tana da kyau son kowa kin Wanda ya rasa toh meye na wani tauyeta 


      Hafsat tace"kabiru Wai meyasa kake hakane?ka Bari a bi komai a hankali Mana"


   A fusace yace"sai in Koda Miki Mari shashasha ke da baki baccin dare sai kin samu inda kike so watoh ita ta tsaya har bakin ciki ya kashe ta,ta bi Masa a ce ta bi Maza ko toh ba a isah ba"


           Ummi dai mikewa tayi ta shige daki yace"Allah na tuba Shirun naki zai dameni ne mu da muke da kurma a zuri'a karewar shiru ma kenan, Maryam  ke kin haifesu ne Baki San zafinsu ba toh Ni Ina Raye babu Dan iskan da zai tauyesu 


      Kurma ce ta mike zatayi hanyar waje 


   Babu Wanda ya Lura da ita saida ta kai kofa  Kamar ance kawu ya kalli kofar sai ya ganta tana sauri 


Yace"keee Ina zuwa 


Bata jisa ba tafiya kawai take 


Ya mike da sauri Yana cewa Kai jibrin kamo min ita Ina zata da da daddaren


     Ganin jibrin ta taliyarsa yake ya mike da gudu ya bita a zaure ya cinmata cike da haushi yace"Ina.... Ina.... Zaki,


    Kura me Ido tayi Aiko ta had'a maganarsa sai ta Fara me alamu da hannun  


Be Gane  ba yace"ko Ina ne tsaya in d'auko Riga  in rakaki ......,x


Ganin Bata me lokaci zatayi Kuma bazata  taba fahimtar ba yayi saurin d'aukar Riga a kafada ya bita da gudu 


    Yana fitowa ya gan tayi nisa ba Shiri ya bita a guje 


   Sai ganin shi tayi a gabanta yace"Ina Zaki?"


      Wani kallo tayi me yace"matsala na Dake rainin wayau ya wuci wajen wara muje Nima zanci ta arbain 


       Tafiya suke kawu dukda yasan ba jinsa take ba bude murya yayi sai surutu yake itako tafiyarta take ba abinda take tunawa sai fuskar mutumin d'azu sai Jin wani yanayi take Yana ratsata Wanda Bata tab'a Jin Haka akan ko wani mahaluki ba ba Haka Suka karasa gun me awara ta Mika Mata kudi 


Mai waran tace"kurma akwai  layi 


      Dukawa tayi ta d'au biyu cikin basket din waran ta cika yaji ta tura Baki sai lumshe Ido takeyi 


Wuri kawu ya samu ya zauna har aka Kira sallah ya Shiga massalaci yayi Yana idarwa ya fito Yana duba agogon wayarsa ya gan kusan 8:,30 


    Ya tarar an bawa kurma awara sai ci take 


    Yace"halan na d'ari biyu ta siya hauwa?"


     Hauwa tace eh na dari uku ta siya ta Fara cin ta Darin tun Yana wuta wanan na dari biyu ne a hanunta 


Kawu yace"in Jin dai ta biya dan bana son a Zo ana ta tashin hankali irin ta kwanaki da ta ci ta d'ari biyar 



      Hauwa ta dakata da gyara wutanta tace"Aiko cewa tayi zaka biya"


    Wani irin kallo yayiwa hauwa fuska ba alaman dariya yace"tunda Nike zuwa Nan na tab'a cin ta d'ari biyu"


Hauwa ta girgiza Kai yace"Ni bana abinda yafi karfina toh ma da wani baki tace'na dari ukun har Kika Bata"


       Hauwa kamar zatayi kuka tace"alama tayi min ai "


Yace"kina ruwa sundum kusa da kada baiwar Allah daga Ni sai arbain Nima Kuma zanci awara Nima, Dan haka' ki d'auka kinyi sadaka ne Allah Kuma zai Baki lada na ciyar da kurma sai Allah baki lada "


    Kuka sosai ta fashe dashi tana itadai a Bata kudinta

Kawu yace"na ci daga ciki baiwar Allah "


Tace"ah'ah "


Yace"toh miye na niman yimin tsirara akan kudin da ban ci ba riketa ta biyaki"


Kuka hauwa take kurma ta zuba Mata idanu ko a jikinta 


Lura da  zata tara musu jama'a kawu yaja kurma Suka bar wurin 


    Wacece Fannah Yar kurma 



Maman nur

No comments

Powered by Blogger.