Sanadin Zane 15-16

 


πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„ _*SANADIN ZANE*_

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

By maman noorul 

Hudah Paid book


πŸ…Ώ️1️⃣5️⃣🫦1️⃣6️⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


______________

      Duk inda yaso ya Gama duk wasu al'amuran da ya kawosa kasar nan gagara yayi dan sai 6pm Suka fito meeting shima ba ayi concluding ba an bukaci ya jira har architect ya fidda *zanen* building din da za a Masa Dan company yake son budewa,Rai ba Dadi dukda ba Wanda ya Isa yayi masa Dole suggestion Suka kawo  shima yayi reasoning da shawaransu  Haka aka maidashi masaukinsa  


    Ana bude masa ya Fara kokarin fita sai idanunsa ya sauka Kan painting din da aka bashi d'azu 


Alama yayiwa guide dinsa da ya kwaso Masa 


Ciki yayi Yana shiga direct bathroom ya fad'a ya shiga yin uzurinsa sai da ya Gama ne yayi wanka ya fito d'aure da farar towel da wata karama a wuyansa Yana tsane jikinsa 


Zama yayi a stool ya Fara tsane jikinsa bayan ya Gama ne ya shafa cream tare da saka wata farar jallabiya da yayi mugun Masa kyau da alamu dai sallah zai fita yi massalaci Dan an kusa magrib 


     Turarensa me mugun kamshi ya fesa tuni kamshin ya cika ko Ina sanan ya d'au wayarsa ya fita 


       Ya tarar dukkanin aid dinsa na jiransa dan baya  bari ko wannesu yayi missing jam'in balle yanzu da sai sunje nisa da hotel din dole su fita da wuri kar suyi missing jam'in wani  babban massalaci Suka je Basu fito ba Saida akayi isha'i sanan Suka bar wurin suka bar mutane da mamaki wanene shi 


       Yana komawa hotel d'aki ya  shiga ya zauna a bakin gado yana bin missedcalls din wayarsa 


      Wanda yayi saving da first wife ita ya Fara Kira kamar ko jira take ta d'auka da sauri dan sanin kanta ne in har tayi missing calls dinsa ba zai sake Kira ba Kuma ko ta Kira bazai d'auka ba 


     Cikin wani irin shagwab'abiyar muryar da takeyi Dan ganin ta birgesa tace"assalamualaiku"dan akidarsa ne Dole a amsa me Kira da sallama in ba Haka ba zai yanke wayar 


        Da k'yar Kamar bazai amsa ba Dan ya d'au kusan minti daya kafin yace"wa'alaikum mussalam ya kuke"


      Cikin Jin Dadi jikinta har rawa yake tace"fine honey when are you coming back munyi kewarka"


     Cikin takaita zance yace"same here "


Tace"Kana dai lafiya ko ka ci abinci?"


   Yace"Zan ci a gajiye nike ne"


   Tace"but why baby nasan yanzu 8pm tayi a can ka daina Zama da yunwa you might......"


Be Bari ta karasawa ba yace"ok I have to go please sai gobe"


Jiki a sanyaye tace"good night "


Ba tare da ya amsa ba ya yanke wayar da ya so Kira sauran missedcalleds din Amma sai ya fasa 


     Kira yayi  Wanda tea ne kawai dan baya jin zai iya cin abinci me nauyi a wanan lokaci 


           Jawo art work din yayi  ya bude,zaro Ido yayi ganin shine a gidan abinci Yana cin abinci sai ya shafa Yana mamakin how perfect the work is 


D'ayan Kuma ya bala'in tafiya dashi ya jingina da gado Yana  kallo ya kasa d'auke idanunshi even for a minute sai ya gan an rubuta _fannah_ besan lokacin da ya anbaci sunan ba ya Kuma shafa aikin 


Koda aka kawo tea din kin ajiyewa yayi yasa aka ajiye me a table 


       Kusan awa ya d'auka Yana kallon painting me birgewa a ransa sai cewa yake wow 


A fili ya furta this is amazing 


Sai da ya Fara gyangyandi ya ajiye board din ya dan kishingid'a a hankali bacci ya Fara fisgarsa hakan yasa ya kwanta 


         Yana kwantawa ya Fara sana'ar tasa watoh mafalkai mafalkai wanan karon kuwa yaki ake a kasarsa duk an Gama da mutanensa har ya fidda tsammani zasuyi nasara zaiyi saradan sai ga wata irin Guguwa a filin yaki.....sai ya Fara Jin takun  doki kallon direction din yayi sai ya hango wani na zuwa da gudu 


   Rintse Ido yau Dan a tunaninsa ya d'au me zuwan na daya daga cikin abokan gabansu 


     Saidai ga mamakinsu kashewa kawai take ba tausayawa 


    Ya shagala da kallonta mussaman da ya tabbatar yanzu macece ke wanan aikin ji yayi ta jawoshi jikinta tare da cakawa Wanda ya kawo me farkaki ta baya da wuka 


    Cikin izza tace"ba a shashanci a filin daga domin hakan  na iya sanadin rayuwarka  so ka kiyaye 


   Bude Baki yayi yace"wanene keee"


Sai ta gyara mayafin data rufe fuska dashi tace"Babu bukatar sanin 


Tana fadin hakan ta turesa sanan ta bar wurin 


Bude Ido yayi a firgice Yana numfashi sai ya mutsika Ido ya jingina da gado Yana tunanin matsalansa watoh rashin haihuwa,a ce Yana da Mata har uku Amma Babu wacce ta tab'a b'atar wata he don't want to believe labarin da mahaifinsa ya basa na sirikar wanan muguwar matan da ya d'auketa tamkar uwa Amma tayi sanadin mutuwa mahaifiyarsa meyasa zata Masa haka' and on top of that a ce sirikarta ta Zo har gida tayi amfani da maita wajen ganin ta hargitse masarautar Wanda da be yarda ba but gradually ya Fara yarda da maganar mutune Dan a cewar mutane tunda tayi musu Baki masarautar gaba daya ta rasa natsuwarta  shi ya zaga asibitoci ana cewa lafiyarsa kalau Amma matansa ko b'atan wata Basu tab'ayi ba 


   Rintse Ido yayi har yanzu Yana iya tuna inda ya shaku da matar data cutar da ahalinsa ya yarda da ita Ashe dai rayuwarsa take so shida mahaifiyarsa ya tsane tarihin kurma da zuriarta da zai gan yar'ta Aisha zai iya Shaketa har sai ta mutu ya tsane tuna ta   


    Baya Jin zai iya komawa bacci  hakan yasa ya jawo painting da ke gefen gadonsa ya cigaba da kallo 


Sai a lokacin ya lura da farar takkadar dake attarch to the board 


     Budewa yayi ya karanta besan lokacin da ya saki murmushi da ya dade beyi irinta ba 


Ya jawo waya ya kwashi digit din dake rubuce zaiyi dialling sai Kuma ya fasa he is feeling to big a ganinshi downgrading kansa zaiyi ya lumshe Ido imagining how brilliant she most be to make this beautifull painting Yana da paint work dayawa but be tab'a ganin Wanda ya birgesa Haka ba 


      Besan lokacin da ya furta wow ba the work is shaking him 


   Kallon agogo yayi sai ya gan ba Wai ma dare yayi bane is after 9 sai kawai ya mike ya maida jallabiya ya fita Abbas kawai ya Kira Wai zasu site seeing  cikin gari.....sauko Suka fita        __''_____'"


   Maman Nur

No comments

Powered by Blogger.