Sanadin Caca Book 1

 


*Book 1*

Chp[01]


........"Goje ka saka mana menene haka wai?"

 Uwaisu ya faɗa cike da jumuɗin yanda cacar yauɗin ke shiga masa zuciya.

Dular da take bakinsa ya kawar mai kauri anyi mata naɗin manya,banda tashin hayaƙi babu abinda yake,ga wata hula zungureriyah a kansa,ta fita daga cikin hayyacinta saboda bala'in dauɗar da tayi sosai. Gashin bakinsa duguza duguza kamar gazagi. 

Cikin shaƙaƙƙiyar murya yafara magana,kana jinsa kaji tantiri ɗiban fari.

"Tsoho shin kana nan akan bakarka zakayi cacah dani,kasan fah ba'a wanyewa lafiyah,sannan idan nayi nasara  ko ranka ne billahillaxi saika bani shi,babu abinda ya dameni,naga kuma da alama ko ƙwandala baka maganinta a jikinka"

Hantar cikin Uwaisu ta kaɗa da maganar goje,amma kuma ta wani bangaren yanajin ƙamshin samun nasara,musamman ganin yanda yatara ƴan wasa iri ɗaya a hannunsa,gashi kuma bugu da ƙari goje yasaka shanunsa dayake kiwo jingina,idan ya cinye wasannan yana da shanu fah kenan sukutum.

Goce hular kansa yayi gefe ɗaya tareda gyara zama akan buzun buga cacar,mutane maza da mata ƴan duniya suna zaune kowa na harkar gabansa a wajen.

"Hhhhhh goje kenan ai tunda nake bantaba fara caca na tashi banƙare ba,ko a cini kona ci bana bata baya,gaba na bata bana tsoro kota mutu kokuma tayi rai,ai ninan uwaisu ɗan marka,dan caca muke rayuwa,caca da rufamana kuma da yaye mana bargon asiri,anci mana mutunci kuma an yabemu,a cikinta muka buɗi ido tun kai yana baƙi,gashi har yayi furfura bamu dainaba,dan haka babu jada baya shiga wasa yaro"

Uwaisu yagama faɗa cikeda gadara da kuma yarda da kai,abokinsa Manga sai kirari yake masa.

Shafa ƙeya goje yayi tareda rishe ido yana dariyar gefen baki,kana ganinsa kam kasan yaci dubu sai ceto.

Fara zarar katin yayi yana ajiyewa ɗaya bayan ɗaya har yagama ajiyesu a gaban uwaisu,babu musu kana kuma babu tada jijiyar wuya,kowa yaga wasan indai ya iya wasan yasan goje ya cinye wasan.

Fitar da kwarkwaron wiwi ɗin bakinsa yayi kana ya miƙawa uwaisu dafaffafen hannunsa gabansa.

"Tsoho rai kokuma dukiya,cikin ɗaya dole zaka bada ɗaya yanzunnan bakuma sai anjima ba,dan haka saika hanzarta"

Rawa jikin uwaisu yafara tamkar an jona masa lantarki,don ko ba'a faɗamasa ba daga ganin soyayyun idanun goje toh fah bazai taba haƙura ba sam.

Juyawa yayi ya kalli manga dayake gefensa,suna haɗa ido manga ya kalli wani gefen tamkar bai san Uwaisu na wajen ba.

Bai sare ba dai cikin razananniyar murya ya tambayi Manga.

"Manga yaka juya,domin Allah idan kanaga kuɗi a wajenka ka Taimakamin dashi,zan baka idan mukaje gida"

"Kai kaji wani zance a wajen Uwaisu inada kuɗinne zaka ganni anan ina hamma kaman wani ɗan tsuntsu,sanin kanka ne a gabanka dai wancan satin nasaka injinnawa a caca aka cinyeshi,yanzu bana cass bana ass sai Ladi tagama abincin sana'arta take zubamin bayan tagama yimin tujara."

Duk maganar da suke goje yana jinsu bai motsaba,kana kuma bai ɗauke hannunsa daga miƙashi da yayi ba. 

In ran uwaisu ana ganinsa toda kuwa ya sau fitsari a lokacin,gaba ɗaya tunaninsa ya kulle,shin a ina zai samo kuɗi yabawa goje. 

"Hehehe tsoho kenan,dan kaga ina maka dariya koh,to aradu da kake gani nan ba mutuncine dani ba,ko ka bani kuɗina kwatankwacin kuɗin saniyar dana saka,wato dubu ɗari da hamsin,kokuma na tale ka nan wajen na sutale maka fatar jikinka,kuma banga ɗan matar da zai iya hanani ba kaf garinnan,in kuma kana ganin wasa nake kada ka fito da kuɗinnan yanzunnan"

Shuru uwaisu yayi yana muzurai,sai lalleƙawa yake yana rarraba ido ko zaiga wanda zai kwaceshi a hannun goje,amma babu alamar akwai wanda ya kulada mai suke a wajen.

"Wa kake kallo zatonka akwai mai ƙwatarka a wajennan ne heee,kanama bata lokacinka ne sannan kuma kai baka san dokar kuɗina ba ma,duk bayan minti uku idan ya ƙara toh zan ƙara dubu ɗaya akai,dan haka zaka bani kuɗina ko saina cire maka yatsu tukunna"

Yafaɗa yana ciro wata wuƙa ƙugunsa mai kaifi,har wani lashe baki yake kaman maye yaga nama.

Caraf ya canfki hannun Uwaisu yana shirin cire masa yatsu,wani ihu ya kurma tareda fara dadare,dama gashi da ƴar kibarsa ba ramamme bane kaman gojen,amma yanda ya riƙeshi yakasa kwacewa kasan goje bakaramin bushashshen ƙashi ne dashi ba.

"Wayyo wayyo do Allah ka ƙyaleni wlh zan baka kuɗinka amma kada ka ciremin hannaye,kafadamin bayan kuɗi mai kake so zan baka ka rufamin asiri"

Magana yake yana kururuwa mutane har an fara taruwa,amma kaman kurma yana nan rikeda hannun uwaisu,har yafara saka masa kaifi a hannun na wuƙa,dan dagaske yake haiƙan sai ya yanki hanunnan.

 Taruwa akayi wasu na jan goje wasu kuma suna jan uwaisu daga hannunsa,banda huci babu abinda yake yana sake riƙo uwaisu,idanuwansa sun kaɗan sunyi jawur.


Ranar Uwaisu yaga hairazin kam,don yahada gumi shirkif ta ciki.

Cikin shaƙewar murya na mai taurin kai goje ya yunƙura tareda watsar da mutanen dake riƙe dashi,wawuro uwaisu yayi a karo na biyu tareda cewa.


"Ohh zatonku ina wasane,to duk wanda yafasa rabamun ma ya goya kura ba wando a cikinku,kuma duk mai son uwarsa da haifi wani kokuma ya kwana da pillown ƙasa bana matarsa ba to ya sake zuwa zai rabamu da wannan tsohon najadun"

Yana maganarne yana nuna dukkan mutanen wajen ɗaya bayan ɗaya da wuƙar hannunsa,ɗaya hannun kuma ya riƙe uwaisu camau baya ko motsin kirki,ko ya akayi ma yasamu wannan masifaffen ƙarfin oho.


"Kaikuma shin zaka bani ƙudina kokuma na karbi ranka yan........."


"Tsaya tsaya na baka ƴa ta Sumaimah a matsayin kuɗinka, dan Allah to ka ƙyaleni"


Shuru goje yayi yana zare ido kaman mai nazari,mutanen wajen sunyi mamaki da kuma sakarci irinna uwaisu,wanne irin abune zaisa uba ya dauki ƴar sukutum mai lafiya da kuma hankali yabawa mutum irin goje,hakan ma bata hanyar dadai ba wai fansar kansa yayi da ita a wajen caca. Saidai kuma ta wani wajen hankalinsu zai kwanta,dan da alama goje zai ƙyaleshi da ransa.


Bayan yagama nazarin ɗagowa yayi da sauri kaman zaucacce tareda sake kallon uwaisun,saikuma ya buɗe baki yana jijjiga kai.

"Kai shashasha ka maidani dan kaga ina shaye shaye,a tunaninka ni marar hankaline,taya ƴarka zata fanshi saniyata buleliya da ita ta kiwatu,ina kaita kasuwa kuɗi za'a bani,ƴar ka fah uban wa zai siyeta idan na karbeta,ko sadaki da masu aure ke bayarwa ma dubu ishirinne,saboda ka maidani bunsuru bari ka hadani da mace koh,na maka kama da wanda yahaɗa hulɗa da mata iyeee"


Wannan karon uwaisu kasa magana yayi,sai mutanen wajenne sukayi ta maza.

"Haba goje ba girmanka bane haka ai,tunda har yace zai auramaka ƴarsa a maimakon kuɗinka kayi haƙuri mana,ai mutum yafi kuɗi koh,kaga tunda innarka tafara tsufa basai tana yimuku girki bah?"

Wani a cikin mutanen wajen yafaɗa ta sigar lallashi,da alama kuma hakan yafara tasiri akan sa,dan yaɗan saki wuyan uwaisun ba kaman ɗazu ba.

"Ehh kuma mutum kace wani abun,dama inna kuwa ƙafafunta suna ciwo,bata gama mana tuwo da wuri mutum sai yunwa taci ta cinye masa,saita samu mai mana girki,nizan wuce madakatarmu daga nan,ku wanketa ku kaita gidannamu gobe,idan kuma kasake wata rigimar tasake haɗamu.....hmmmm feɗeka zanyi na bawa su durwa,tsohon banza kawai,gobe ma kasake kasadar shiga caca babu kuɗi,idan ita sa'ar wasanka ce,gajaman kawai"


Haka yagama yiwa Uwaisu tass yashuri wasu takalmin fatarsa yabar wajen yana bobboƙarewa kaman wani mutumin itace. Sudai kowa na wajen ajiyar zuciya yayi,komai yasaka Uwaisu ma yin caca da wannan oho,mutumin da sai yayi wata churr a jeji ba'a ganshi ba idan suka iyo sata  ko fashi. 

Kowa a wajen masu cewa Allah yakara sunfi yawa,yayinda wasu kuma tausayin Sumaimah sukeyi,baiwar Allah tana ganin rayuwa ta wani irin uba da Allah yahaɗasu dashi,abin takaicin dama sauran yaranne aka bawa gojen da sauƙi,amma Sumaimah ya mahaifiyarta zataji,ita kadai ce kaff cikin yayansa ta fitada zakkah na hankali. Kodan yasan ita ba uwarta a gidan,in badan haka ba taya zai fara wannan abun.

Bagazan bagazan babu kunya bare nadama Uwaisu ya shuri shima nasa takalman yana baza uwar riga yayi hanyar gida,lokacin cin abinci yayi,zaije duk wacce takeda girki tagama yimasa tujara ta zuba masa.


            _***_


Leƙawa tayi ganin yamma tayi sosai yasa tafara tattara robobinta na abincinta duk da kuwa bata siyar ba da sauran, dama hakan yakasance al'adar ta ne,bata yarda koda wasa tayi dare a wajen siyarda abincin,yau shakararta ɗaya kenan da fara tallen,tunda akayi auren ƙanwarta Shaheedah itace takeyi yanzu,lokacin da tanaji tana gani tabar karatunta tafara talle tayi kuka sosai da sosai,saidai kuma shin ya zatayi ne,idan bataje tallenba wanene zai bata abinci taci a gidan,ammi ce dama kaff cikin matar mai ɗan dama dama,itace kuma take riƙe da ita,taji daɗi ma da bata gaji da ita ba ai. Sa'arta ɗaya bata tsangwamarta amma kuma bata sakata a zuciyarta kaman sauran ƴaƴan nata. Hmmm wannan jinkirin aurennata yana damunta sosai.

A yanda aka san yanayin dai wacce taƙi kama kanta itace bata auruwa,amma ita kuma anata kaddarar kama kanta da tayi tafita zakkah a cikin gidannasu shine ya hanata auruwa.

Sallama tayiwa abokan tallennata wanda sukam yanzu ma suka fara siyarda abincin,dukkan su ƙannen bayanta ne sosai da sosai. Saboda kowa cewa yake ta rako mata tayi kwantai,amma kuma tasan hakan baya wuce nasaba da tuggun dasu inna lami ke yimata a gida,kasancewar tafi sauran yaransu kyau da kuma soyuwa a wajen kakarsu wacce ta rasu waccar shekarar.

Tafiya take da tunani fal a ranta,haka kawai takejin faɗuwar gaba wacce tarasa dalilin faruwar hakan. Botikin shinkafane akan ta saikuma na miya hannunta ɗaya,gefen kunkiminta kuma ta saƙale bahon data zuba plate da cokala a ciki.

Tazo daidai saitin anguwarsu taji yara sunayi mata magana,amma kuma yafi kama da tsokana,tohh ita kuma ba mahaukaciya ba kai yakawo haka,ko duk rashin aurennata da wuri ne yazamo haka.

Waiwayawa tayi ta kallesu,ba wasu yara bane ƙanana da hankalinsu sarai.

"Yee ga matar goje nan tadawo,ohh kowa yaki aurenta sai goje,shima biyansa kuɗin cacarsa akayi da ita wooo"

Gabanta ne yayi dummm,wannan karon har yafi wanda takeji ɗazu,duk da bazata ce ta gaskata maganar tasu ba,amma kuma tasan hakan abune da zai iyah faruwa,tunda ita kanta tasan halin ubannata,babu wanda bai masa shedar caca ba,hattah kayan ɗakunan iyayensu duk ya ƙararsu a cacah,sunyi kukan sunyi bakin cikin harsun gaji,babu ma ya ita Kaman duk abin ya fi damunta.

Cikin sanyin jiki kaman babu laka a jikinta taahiga zauren gidannsu,gidane na iyaye da kakannu mai ɗauke da ƙofofi da dama,dan su kansu ma sunkusa su talatin yayan vabannasu,banda ƙannen babanta da kuma ƙannensa da kofofinsu.

A gidannsu akwai tsakar gida mai matsakaicin faɗi,duk anan kowa ke fitowa dashi da yaransa yayi harkarsa.

Tana shiga gidan da idanuwa barkatai tayi arba dukka sun watso mata shi,kana gani dai kasan wani abun tabbas yafaru ko kuma yana faruwa.

Sauƙe idanuwanta tayi tai ta maza ta wuce ta gabannsu zuwa ƙofarsu,dan tunda taga dukkan matan a wajen iya amminta ce bata nan,kuma dama itace mace ɗaya a gidan da bata shiga harkar mutanen gidan sosai,badan bataso ba saidan hakan ba halinta bane.tasan duk yanda akayi tana ɗakinta dan haka can ta nufah. Tanajin ƙananan maganganu a cikin kunnenta daga bakunan ayarin matan wajen,amma tayi saurin toshesu a cikin kunnenta,dan a halin da takeji batada ƙwarin wannan zuciyar najin abinda suke faɗa ba yanzu badai tukun ko zataji ma.


Babu kowa a ƙofar tasu,dan haka kai tsaye ta ajiye shirgin hannunta ta nufi ɗakinnasu.

A durƙushe tasamu durƙushe ta ammin ta kifah kanta akan katifar da ita kaɗai ta rage a cikin ɗakin.

Ko ba'a faɗawa mutum ba yasan kuka takeyi na takaici da kuma baƙinciki.

Cikin rawar murya da duk wanda yajita yasan saida akayi jarumta wajen furtata Sumaimah tayi sallama a bakin ɗakin.

Saurin ɗagowa Ammi tayi tareda goge hawayen idanuwanta ta kalli Sumaimah ɗin.

"Ohh har kindawo ne"

Ɗaga mata kai tayi kafin itama ta jefeta da tata tambayar.

"Am...mmi ddd....dagskene baba ya badani ga goje a wajen cacah?"

Shuru ammi tayi tareda runtse idonta,shin taya zata bata  wannan zazzafar amsar tayaya? Saidai kuma hakane dagaskene bazata iya cemata ba haka bane,dukda kuwa abinda zuciyarta keson faɗa kenan.

Ɗaga mata kai tayi tareda saurin kawar da kanta,dan a yanda takeji duk da ba ita ta aikatawa Sumaimah hakan ba kunyar haɗa ido da ita takeji, ji take da tanada iko to zatayi koma menene wajen ganin hakan bata faru ba,saidai wacece ita,tayi magana a goranta mata kan cewar ƴar tace,kawai dan ta reneta. 

Shuru Sumaimah tayi itama tana nata tunanin.

Wani abin ma Ita data  kame kanta daga dukkan munanan ɗabi'u,yanda dan iska bazaizo yace yana sonta ba,to shikuma ɗan kirki koda yana sonta bazaizo ba saboda halayyar mahaifinta da kuma gidansu da bana mutunci ba. Wannan sai taji ma da kwanda tunda ta amince da wani sakaran ba wannan dodon da ake shirin ƙulla rayuwarta da tasa ba.


Siraran hawayene suka zubo daga kuncinta,bata taresu ba bata kuma tsaida su ba,barsu tayi lokacin su ne suyi ta zuba kawai dan in akwai wata ƙofar ma da wani hawayen zai zubo da ta barshi ya zubo........

"Kiyi haƙuri kawai Sumaimah,hakika banji daɗin abinda ya aikata ba,amma kuma banida tacewa akan hakan,dan har yanzu ma ni ban ganshi ba bare yamin bayanin abinda ya aikata,saboda yasan banida matsayin da dole saina sani ne inaga. Kije madafa abincinki yana can,barina yi sallah.


Kashh akan zamu dagata a sabon littafin na sanadin cacah.... Ya kukaji to kuna so?


Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.



DOWNLOAD HERE

No comments

Powered by Blogger.