Sakayyah 7

 


📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇


                    *SAKAYYAH*

                             _Page 7_


                                 _NA_

              *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


     *FREE PAGE NE YAN UWA, BA WAI FREE BOOK BANE! INA GAMA SAKIN FREE PAGE, KO KINGA an fiddashi waje na satane. Na kuma Yaseen ne doguwa. Dan haka ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa biya ki karanta*



*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*


_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace wanda bani da haufi kansa 7k ne kacal sai dai yar musilar robace., Kana masin Daɗi har Maɗigan yana da masigar kyau da tsatstsafo da ni'ima, wlh wasu in sunyi amfani dashi pan biyu sabida yadda zakiyi ta tsiyaya. 5k ne Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa 8k ne, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan wanda wlh koda sanyin cikin mahaifane fes yake wanke shi kuma ko mai ciki zata shashi baida illa, kama budurwa ko bazawara duk zasu iya sha harma da yara. Set ɗin da 10k ne innkuma za'a sa miki komai rabi-rabi ne 5k ne, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._


🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,



Moddibo ta hango zaune a gefen gabas yana fuskantar tata, bima'ana yana kallon yamma, zaune yake  akan wani dutse mai masifar sheƙi kana wasu mutane biyu na tsaye gefen hagu da damansa,

Sannan da buta gabansa bisa alama  Al'wala yayi domin farin yashin daya mamaye wajen daga gabansa a jiƙe yake, kana yana mai fidda wani irin ni'imtaccen ƙamshi maisa ɗan Adam lumshe ido. Baki ɗaya haske ya mamaye ilahirin filin wajen hakan yasa itada Moddibo suna fuskantar juna yayin da M Jameel da Adda Adama matar Baffan Umaru  suma ke fuskantar juna.

Kana lambu dake  can bayanta kuwa yake feso musu iskar yammaci dana lambun suka haɗu waje ɗaya daga sama kuma rana ne yayi Ja yana shirin faɗuwa.

A hankali ta sauƙe numfashi mai nauyi tare da lumshe idanunta.

Da sauri ta buɗe idanun nata, jin wani irin sassayan sautin dariya mai cike da shauƙi da Moddibo yakeyi.

Cike da mamaki duk suka zuba mishi idanu.

Yayinda Adda Adama ma tuni ta fara dariya mai sauti.

Ita kuwa Khausar haka nan taji jikinta yana tsuma tare da sakewa, da sauri ta juya ta kalli  M Jameel ga mamakinta shima ita yake kallo, da idonshi ya nuna mata Moddibo yana mai yin lallausan Murmushi, da sauri ta maida kallonta kan Kekkyawar fuskar Moddibo, wacce tunda take a rayuwarta dashi bata taɓa ganin yayi dariyar da har haƙoransa na gaba zasu baiyana ba.

“Fatabarakallahu fih hasanil khaliƙeen”.

Ta furga a saman lips ɗinta, lokacin da ta sauƙe ƙwayar idanunta kan fuskar Moddibo, da sauri ta kuma lumshe manyan Idanunta sabida wani irin masifeffen sheƙi da ta hango sajenshi dake kwance lip-lip yanayi,

Sautin dariyarsa da har yanzu yake ne yasata saurin buɗe idanun.

“Subahanallah, tsarki ya tabbata ga Ubangiji da ya halicci wannan bawa ya kuma bashi waɗan nan haƙoran”.

Ta faɗa a fili lokacin da taga ƙyellin da haƙoransa keyi har yana ɗauke mata idanunta,

Lobgoɓar da kanta tayi bisa kafaɗarta.

Wani irin sassayan numfashi ta fesar tare da tsaida idanunta a kanshi.


Shi kuwa Moddibo dariya yakeyi mai sayyan sauti wanda yake da daɗin ji, har maƙolloton wuyanshi yana ɗan haurawa yayi sama kana ya dawo ƙasa.

Yayinda ya ɗaura tafin hannunsa kan ƙirjinsa.

Cikin tsananin dariyar ya samu ya ɗan tsagaita tare da furta.

“Astagfurillah watubu ilaik”.

Sai kuma ya ɗago ya kalli M Jameel lokaci ɗaya kuma ya sake sakin dariya mai sauti yana cewa.

“Astagafitillah Wayyo cikina”.


Cikin rage girman idanunta take kallon gashin girarsa dake kwance lip.


Jameel kuwa sai Murmushi yakeyi tare da girgiza kansa.

Yayinda Adda Adama ma dariyar takeyi harda riƙe ciki.

Ita kuwa Khausar gaba ɗaya ta kasa ɗauke idonta daga kansa.

A haka har rana tayi mudun kuyanƙi alamun yana gab da faɗuwa.


amma kafin ya faɗi saiya rabu kashi biyu.

Yayinda Khausar kuwa ke zaune tana fuskantar yamma hakan yasata ganin abin.

Atake hankalin ta ya tashi ganin yanda ranan ya rabu kashi biyu.


Ita kuwa Adda Adama hannu tasa ta dafe ƙirjinta tare da faɗin.

“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n yau mun shiga ukun mu ku dubi yanda ranar tayi fa!”.

Tana faɗin haka duk dariya da murmushin da sukeyi ya tsaya.


Moddibo kuwa daga inda yake zaune ya ɗaga kansa sama tare da juyawa bayanshi kana a hankali yace.

“Ya Salam  ya ilahi ya mujabat da'awati meke Shirin faruwa”.

Cikin tsananin gigita da tashin hankali da firgici Khausar ɗin ta saki kuka mai cike da rauni tare da cewa.

“Innalillahi wa innailaihi raji'un, hasbunallahiwani'imanwakil, mun shiga uku”.

Sai kuma ta juyo ta kalli Moddibo da ya gyara zamanshi kana a hankali yace.

“Babu abinda zai faru wanda Allah bai sani ba, Insha Allah Ubangiji zai mana maganin duk kan abinda yayi tsanani”.


M Jameel kuwa kasa furta komai yayi sai hawaye dake kwaranya daga idanunsa.

ita kuwa Khausar ganin M Jameel na Hawaye kawai sai itama tashiga yin kuka amma ba mai sauti ba.

Cikin wani irin yanayin da bazai misaltuba Moddibo ya dubesa kafin yace.

“Haba J. Kamar ba namiji ba addu'a ya kamata muyi duk kan tsanani yana tare da sauƙi”.

Still dai M Jameel baice komai ba.

Shi kuwa Moddibo cikin sanyin jiki ya fuskanci Khausar cikin wata iriyar murya yace.

“Khausar tausayi na kike ji ne?”.

Cikin kwaranyar hawaye ta gyaɗa mishi kai tare da sakin raunataccen kuka mai cushe numfashi, lokaci ɗaya numfashin ta ya fara cushewa yana ɗauke wa, cikin yanayi wahalar neman numfashi taga Moddibo ya...!

Dai-dai  lokacin kuwa ta farka daga baccin da takeyi ciki  razana tare da kaɗuwa ta dafe kanta da takeji yana jujjuyawa.

Kana duk da sanyi da ake tsulawa a garin wani irin zufane ke tsastsafo mata ta ko ina.

Cikin sauƙe ajiyar zuciya,  ta juya gefen hagunta ta karanta A'uziyya ƙafa uku kana ta canza hannun kwanciyar ta zuwa dama.

Sai dai sam baccin yaƙi zuwa mata, sai ta kama karatun Alqur'ani cikin sassayan sauti,

Cikin ikon Allah ta samu bacci ya kuma yin awon gaba da ita.


Baki ɗaya Wunin wannan ranan akasalance tayi koda abinci ta kasa ci haka zalika koda yawan surutu sai ta rage sosai mafarkin ya tsaya mata arai da zaran ta tuna irin mafarkin da tayi sai taji zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske.


Da daddare cikin ikon Allah data karanta Alkur'ani mai girma tare da bin haddarta da Malam Liman ya bata sai taji sauƙin abin aranta duk da kuwa bawai ta daina jin tsinkewar zuciyar bane amma ya ragu sosai.

Da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare Khausar suna zaune a farfajiya gidan Hajja Nana su uku ita Yaya Abba da kuma Dije suna hira jefi-jefi take sanya musu baki aciki daga ƙarshe ma ta miƙe tace zata je ta kwanta sai Dije ma ta miƙe ganin haka yasa Yaya Abba ya musu rakiya har gida.


Washe gari:Da safe still haka Khausar ta tashi bata da wani ku zari koda abinci ne ta kasa ci iyakacinta tasha Tea ko ruwan kunu sannan ta kasa faɗawa kowa irin mafarkin da tayi domin jikinta ya mutu sosai da mafarkin.

Da daddare ba kinta ɗauke da Sallama tashiga gidan Hajja Nana.

Asaman laɓɓa Hajja Nana ta amsa mata Sallamar tana binta da harara dan tunda taƙi markaɗa mata wake take jin haushi ta.

Ita kuwa khausar bata masan Hajja Nana nayi ba ta nemi waje ta zauna tare da kallon Hajja Nana tace.

“Yunwa nakeji ki bani abinci zanci”.

ta faɗa tana kallon ƙorenta dake jere guda goma sha Uku.


Harara Hajja Nana ta wurga mata tace.

“Gashi ki ɗauka ki ci”.

Kai Khausar ta gyaɗa tare da Matsawa jikin ƙoren tashiga buɗewa ɗaya bayan ɗaya tana dubawa saboda taga gidan Malam Liman anyanka kaji cikin Sa'a kuwa tana buɗe ɗayan taga Jan miyar dage-dage da kuma tuƙeƙƙen tuwon shinkafa.

Ta gyara zamanta tare da wanke hannunta ta fara cin tuwon cikin Mintuna kaɗan ta cinye tass sannan ta kuma janyo wani Ƙoren dan sosai take jin yunwa sannan bata wasa da cikinta dan ita dai ko ciwo bai cika hanata cin abinciba karo na forko kenan a rayuwarta da abu ya tsaya mata a rai har ya hanata cin abinci na kwana biyu son ta Tara yunwar shiyasa.

ta cinye ƙore  biyun tas dan dama tuwon ba wani mai yawa ake samata ba tunda akwai yawan kanukan.


Hajja Nana kuwa juyawa tayi da mamaki ta kalleta kafin tace.

“Yanzu har kin cinye tuwon nan”.

Kai Khausar ta gyaɗa mata tace.

“Na cinye mana kuma yanzu ma ƙarawa zanyi dan yunwa nakeji rabo na da abinci tun shekaran jiya da daddare fa sai dai in ta Shan abu mai ruwa-ruwa”.


Taɓe baki Hajja Nana ta kuma yi tace.

“Toh bubbuga rumbu ga shican ki ƙara ki cinye duka ma in Kinga dama”.

Ta Faɗa tare da tura mata wani akoshin.


Ɗauka Khausar tayi kamar wasa ta cinye dake abincin ba wani da yawa ake sawa aƙoron ba dake sun san cewa ƙorenta da yawa mafi yawan lokuta ma loma ɗaɗɗaya takeyi ako wani ƙoren idan tayi loma sha uku ya wadatar mata a dai cikin tsohuwa ta kuma tsinci nama ta cinye to shiyasa ba'asa mai yawa.


Ita kuwa Hajja Nana ganin yanda Khausar ke cin abinci yasa tayi zaton gatse take mata ta harareta da faɗin.

“Mutum kamar jaki wannan ci haka ki cinye wannan ƙoren ki cinye wancan”.

Ta ida maganar tare da sake tura mata wani ƙoren.


Ita kuwa khausar ta ƙoshi amma saboda ta ƙular da ita yasa ta janyo ta buɗe naman kan abincin ta cinye sannan ta gutsiri kamar loma biyar ta zuba akwanan dake empty.

Wani kwanon Hajja Nana ta kuma tura mata still ta cinye naman ta kuma gutsura ta zuba a sauran kwanon.


Hajja Nana ta dube ta cikin tsareta da ido tace.

“Wai har yanzu baki ƙoshi ba?”.


Khausar cikin yamutsa fuska ta gyaɗa kai kana tace.

“Eyyy ban ƙoshi ba”.

Wani akoshin Hajja Nana ta sake tura mata, Khausar kuwa laluma ta cigaba dayi idan taji da nama ta cinye ta gutsits-tsira tuwon ta bari.


Ita kuwa Hajja Nana kamar wacce akace ta leƙa taga aika-aikan da Khausar keyi da tuwon ta miƙe cikin fushi tace.

“Shegiyar yarinya gantalelliya  ni kike nunawa barikanci, 'yar banza kinje kin zauna gidan Mayu kema kin koma kamar Mayya, sai cin nama kamar kura, wato ma duk naman kike lalubewa dan mayta ai dai na sani in dai ba cikin zanine da keba ai yaci ki ƙoshi”.

Ya mutsa fuska Khausar tayi tare da riƙe ƙugunta tace.

“Naci ɗin idan ni Mayya ce kinsan inda na samu maita, tunda nazo saboda shegen maƙo ko zabuwa ɗaya kin kasa yanka min gaki da Zabbi kamar zasu kashe ki ga shanu kuma aina Babana ne”.


Salati Hajja Nana tayi tare da fashewa da kuka.

Kasancewar duk dare aƙofar gidan ta suke zama yasa Baffa Umaru daya ji sautin kukan ta ya miƙe kasancewar Allah ya bashi kunne komai ƙanƙantar sautin abu ya kan iya ji.


Ganin Hajja Nana na kuka yasa Baffa Umaru nufarta tare da cewa.

“Addah Nana Meya faru?”.

Nuna Khausar tayi  da hannu kana tace.

“Wannan ‘yar Usmanu har zata min gori wai gadon Ubanta na riƙe kaji shegiyar gantalalla yarinya dan ma Allah yayi dan ke macece!”


Ƙasa da murya Baffa Umaru yayi yace.

“Dan Allah Addah Nana kiyi haƙuri kinsan yarinta ke damunta idan ta girma ba zatayi ba”.

Ya ida maganar tare da jan hannun  Khausar suka fice waje.


Bayan sun fita ya juya ya kalleta yace.

“Haba Khausar kidena ki koyi yanda zaki zauna da manya kinga Addah Nana tsufa ya kamata tana buƙatar rarrashi da lallami, kinga duniyar nan ba matabbata bace idan yau kaine gobe ba kai bane ita rayuwar nan bata da tabbas, ki koyi magana mai daɗi ke idan Mahaifinki ina ita fa ɗan ta ne data haifa acikinta kuma ɗan ta mafi soyuwa agareta kada ki sake haka kinji Khausar am”.


Ta gyaɗa masa kai da faɗin.

“Toh shikenan Insha Allah bazan sake ba”.

Ya shafa kanta yana murmushi yace.

“Allah ya miki albarka kizo muje gidana mu kwana zansa ayanka miki Zabbi kici tun da mun gama cin abinci".


Kai ta gyaɗa tare da yin murmushi tace.

“Toh”.

Ya riƙe Hannunta suka tafi suna tafiya suna hira har suka isa gidan bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga gidan Adda Adama ta fito daga ɗaki tare da amsa musu sallamar.


Kallon Adama Baffa Umaru yayi yace.

“Akwai nama ne?”

Adama tace.

“Eh akwai Zabbin da aka yanka da yamma yanzu nake ƙarasa dahuwarsu”.


Yace.

“Toh shikenan ki ƙara sa gyarasu ki kawo ma wannan Kuran Birnin taci”.

Dariya Khausar tayi tana zama akan taburman da Adama ta shimfiɗa musu, shi kuma Baffa Umaru ya zauna daga gefenta yayin da Adama taje taci gaba da aikinta kasancewar farin wata ya haska ilahirin garin.


Anutse Baffa Umaru ya kira sunanta da faɗin.

“Khausar”.

Ta ɗago kanta tana kallon fuskarsa acikin farin watan kafin tace.

“Na'am”.

Idanunsa kanta yace.

“Kinsan kamannin Babanki?”.

Kai ta girgiza masa tare da faɗin.

“A'a bansan kamanninsa ba”.

A sanyaye yace.

“Amma kin san akwai Baffanki ai yayan Babanki Hammadu Ɓadamaya ko?”.


Tace.

“Eh amma Ɓadamaya yake ko?”.

Yace da ita.

“Eh yana can Ɓadamaya dashi da Iyalansa da kuma ahalinsa gaba ɗaya.

 Insha Allah wataran Zakije shida Babanki Uwa ɗaya Uba ɗaya".

Kai ta jinjina da faɗin.

“Eh Mommy na tafaɗa min cewa inada Baffa yana can Ɓadamaya dashi da matarsa da kuma ‘Ya‘yansa”.


Murmushi yayi yace.

“Toh idan kinje zaki ga mai kamannin Mahaifinki sak da sakin  sunan sa Aliyu shine yake kama da Mahaifinki ya gaji Babanki komai da komai kuma shine aka aurawa yayarki Nenne”.

Kai ta gyaɗa tace.

“Toh yaushe zanje in gansa?”

Yace.

“Kinga kamannin Mahaifinki kamar balarabe kinga ba yabon kai ba mutanen Rugar mu duka kyawawa ne amma kyawun mahaifin ki ya fita da ban farin Mutum ne kyakkyawa ga kuma gashin kansa mai tsawo da sheƙi wannan gashin naki ma shi kika ɗauka”.


Idanunta ta lumshe cike da kewar mahaifinta sai kuma ta buɗe su tace.

“Aikam nasan gashin sa na ɗauka ba Mamansa ba da kai agwagwiye".

Murmushinsa ya faɗaɗa da faɗin.

“Ina Addar tawa kike yiwa ba'a itama tsufa ce yasa gashinta kaɗewa”.

Murmushi tayi tace.

“Ai lalle kam”.


Sai kuma ta dai-dai-ta nutsuwarta tace.

“Ku kuma dama nan ne asalin Rugarku?”.

Kai ya gyaɗa mata yace.

“Eh asali nan ne Rugar mu iyaye da kakanni”.

Tace.

“Toh Meyesa ita Hajja Nana ta dawo nan kuma ina ne asalin garinsu Babanmu?”

Murmushi yayi yace.

“Asalin garinsu Babanki yana da nisa lokacin da Addarmu tayi aure ta daɗe kafin tazo ta samu haihuwa to data haifi na farko sai Allah ya sake kawo wasu akan lokaci ta haifi yara uku sai Allah yayiwa kakanki daya haifi Babanki rasuwa,sai ta nemi zata dawo to data nemi zata dawo sai sukace tabarmu su yaran ita kuma tana son yaran sosai sai tace Inde akan dukiya ne tabar musu duka subarta ta taho da ‘Ya‘yanta”.

Zama Khausar ta gyara tana sauransa da kyau.

Shi ko a hankali ya cigaba da cewa.

“Dake dangin Mahaifinki mutane ne masu karamci sai sukace su ba dukiyar su suke buƙatar ba kawai dai suna so suriƙa ganin ɗan uwansu ne sannan ita macece kada subar mata nauyi amma tunda tana son Zama da ‘ya’yanta baza su hanata ba sai suka bata duka gadon Mahaifinki da kuma na Baffanki da ƙannensa mata biyu hadda mai sunanki.


A ranar da tashigo Rugar nan tashigo da aƙalla shanu sun kai ɗari biyu sannan harda raƙuma da tumakai duk gadon sune aka ɗauka aka basu suka dawo”.

Sassayan ajiyar zuciya ta saki tana jinjinawa lamarin.

Baffa Umaru ya cigaba da cewa.

“Toh tun daga lokacin ne zamanta ya dawo nan daga baya Allah yayiwa mahaifan mu rasuwa da gida huɗu ne kacal anan mahaifinmu su suka fara kafata da duk nan dajine mahaifinmu ne ya sare bayan rasuwar mahaifinmu da kuma mahaifiyarmu, 

itace ta zame mana Uwa da uba tun muna yara itace ta renemu nida Mahaifinki mun taso tare atare mukayi wasan ƙasa ta raine mu tare ta zame mana kamar uwa Shiyasa mu awajen mu Adda Nana ba ya bace kaɗai uwa ace a garemu”.


Ita kuwa khausar Ajiyar zuciya ta kuma saki tare da faɗin.

“Ikon Allah Allah mai iko Mabuwayi Gagara misali”.

Murmushi Baffa Umaru yayi yace.

“Kin gane ko mu Addah Nana Uwace agaremu ba Ya ba sannan maganarta Umarni ne awajenmu muda ‘Ya’yanmu babu mai saɓa mata har jikokin mu kinga keda kika zo kina wannan abin sai akaga lallai ta samu karan tsaye”.

Murmushi Khausar tayi tace.

“Lallai dai kam,to amma ina ne asalin su Babanmu?”.

Murmushi yayi yace.

Gobe zan faɗa Miki Idan Allah yakaimu rai da Lafiya zan ƙara sa baki labarin insha Allahu”.


“Toh Allah ya kaimu goben lafiya”. Cewar Khausar


Cikin sauƙe numfashi yace.

“Naji ma Addah Nana na cewa kafin ki koma Abbah zai kaiki Ɓadamaya kije kiga Baffanki da ‘Ya‘yansa”.


“Toh ina kuma ance da nisa?”.

Khausar ta tambaya


“Eh danisa amma ai tafiyar wuni ɗaya ce zaku isa”.

Ya bata amsa.


Miƙe sawunta tayi bisa taburmar tare da cewa.

“Toh shikenan ba matsala, Insha Allahu zamuje, nima ingansa sannan kodan inga mai kama da Babana”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Sannan kuma kafin ku tafi zakuje kiga Addarki ‘yar Baffanki da yake Ɓadamaya tana nan Rugar Fulani dake ma ƙobtanmu Adda Ikki aikin santa?”.

Murmushi tayi tare da gyaɗa masa kai tace.

“Eh na santa ai itakam tana zuwa har gidanmu ta dubani duk dangin Babana ma ita nafi sani”.

Yace.

“Toh shikenan Zakije wajenta kiyi kwana biyu”.

Tace.

“Tun kwanaki nake cewa Hajja Nana zanje in dubata, tace min ba yanzu ba, wai in bari ingama sanin mutanen garin nan”.

Adama dake sauraron  hiransu ta miƙe hannunta riƙe da kwanan da ta gama gashin Zabbin dake ta tashin ƙamshi sannan ta haɗo musu da madara mai ɗumi.

Akan tabarmu ta ajiye musu su duka ukun atare sukaci.


Gyatsa mai sanyi Khausar kana tace.

“Kai gaskiya naci naji daɗi Nagode”.


Bayan sun kammala ne Khausar tashiga ɗakin Adama ta kwanta Adama kuwa ta nufi ɗakin mijinta suka kwanta tare.


Can cikin dare kamar misalin ƙarfe biyu Baffa Umaru ya miƙe zaune, tare da kasa kunnensa sosai wanda hakan ya kasance ɗabi'arsa ne,

domin shine Garkuwar Rugar tasu,  jin motsin tashin sa yasa Adama miƙewa ita ma ta zauna, kusa dashi tana faɗin.

“Lafiya”.


Ajiyar zuciya ya saki da faɗin.

“Naji tsayuwar mota daga can nesa sannan naga haske yashigo har cikin garin nan kamar da akwai wani abu ko dai munyi baƙi ko kuma wani abu!".


Ahankali tace.

“Toh yanzu fita zakayi kenan?”.


“Dole in fita ai Adama idan ban fita ba ‘yan uwana zan bari wani abu yazo ya ritsa da mune ai bazan bari ba dole in fita inga ko menene”.

Ya faɗa a hankali.

Ita kuwa Adama  riƙe hannunsa tayi fuskarta na bayyanar da tashin hankali tace.

“Nikam ina tsoro wallahi”.

Da sauri yace.

“Kada ki damu Insha Allah babu abinda zai faru wanda Ubangijin bai sani ba”.


Kai ta girgiza kana tace.

“Kai rashin network ɗin garin nan yana damun mu wallahi, kaga da akwai network tunda yawanci kowa yana da waya zaka kik kira su awaya kowa ya fito kaga idan yaso sai sufito ku haɗu Atsakiyar garin amma Ni ina tsoron fitarka kai kaɗai”.

Suna cikin Maganar ne sukaji antura ƙofar gidansu anshigo Murfin ya fadi ƙasa Kifff kasancewar ba wani Murfin kirki bane gadon kara ne da gwafa aka haɗa.

Cikin han zari ya mike ya tsaya.


Itama miƙewa tayi da saurin ta riƙe hannunsa tace.

“Fita zakayi dan Allah kada ka fita ka tsaya dan Allah kar ka fita”.

Ya juya ya fuskanceta yace.

“Ya kike so inyi idan ban fita ba kina jifa anshigo gidan nan”.

Yana ida maganar ya fin cike hannunta dake cikin nasa ya fita.

Cikin sauri ta shari gabansa ta fito ya zama na itace agaba shi yana bayanta.


Suna fitowa idanunsu ya sauƙa akan mutanen uku dake sanye cikin baƙaƙen kaya hannunsu riƙe da bindigi da kuma toch ligh mai masifar haske.

Arazane Adama tace.

“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin”.

Ƙaran buɗe ƙofa da kuma sautin Muryan Adama ne ya fito da Khausar daga ɗaki wacce farkawanta babu daɗewa tana fitowa sukayi saurin kashe mata ido da hasken toch ligh dinsu ita da Adama.


Cikin daga Murya suka ce da Adama

“Ki matsa agabansa kada jini ya taɓa ki ki matsa kada mu illataki!”.

Aruɗe tace.

“In matsa agabansa!?Bazan matsa ba, ku suwaye ne? sannan me kuke nema? me kuka zo yimana acikin daren nan?”.


Ɗaya daga cikin sune yace.

“Kashe sa muka zo yi!”..

Cikin tsananin tashin hankali tace.

“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n hasbunallahiwani'imanwakil.

 dan Allah kada ku kashesa,me yayi muku zaku kashe sa?,Meyesa?”.


Ɗaya daga cikinsu ba wanda yayi magana da farko ba yace.

“Saboda yana hanamu rawan gaban hantsi zamu kashe sa muga takan tsiya bashi yace taurin kai ba”.


Baffa Umaru kuwa murmushi yayi mai cike da Jarumtaka da kuma rashin tsoro yace.

“Ni zaku kashe?,To idan kunga na mutu kwana nane ya ƙare,Kuma Ubangiji shi ya ɗauki raina.

 Amma ku baku isa ba babu mai rayawa babu mai kashewa sai ubangiji.

Dan haka raina baya hannunku kuma ajalina baya hannunku idan kunga na mutu ma kada kusa aranku ku kuka kashe ni!”.

Ya ida maganar tare da zabura zai shiga ɗaki dan ɗauko kwari da bakasan.

Ita kuma Adam da saurin riƙesa dai-dai lokacin da suka harbesa  akafaɗarsa na dama.


Ƙaran harbin ne ya tashi gaba ɗaya ilahirin mutanen garin Aɓangaren Hajja Nana kuwa tana tashi daga bacci sanadiyyar ƙaran harbin ta dafe kanta da faɗin.

“Wayyo Umaru na Allah ka kare mana Umaru” domin shine mutum na farko daya faɗo mata arai cikin rawan jiki ta miƙe tare da ɗaukar zaninta ta ɗaura kana ta ɗauki mayani ta yana.


Aɓangaren Baffa Jauro yana miƙewa yace.

“Umaru”.

Ya kira sunan sa cikin daga murya.

Baki ɗaya ‘Yan uwansu da sauran jama'a babu wanda ya faɗo masu arai sai Baffa Umaru ko wannensu daya farka zai ce.

“Wayyo! Umarunmu”.


Shi kuwa Umaru juyawan da zai yi sai suka samu damar sake harbinsa ahaƙarƙarinsa na hagu.

Cikin ƙarfin hali da ɗaga sautin Muryar sa yace.

“La'ilah ha Illallahu Muhammad Rasulullahi(S.A.W) Adda Nana ki yafemin yau kam zasu kashe ni ki yafemin kece madadin Uwa awajena duk abinda nayi ki yafemin yau kam sun kasheni sun kashe ni,Yaya Jauro, Yaya Sadu, Yaya, GarGa, Yaya Liman, Yaya Garba,Yaya Sale yau kam sun kasheni sun cire muku ɗaya cikin goma kun zama ku tara!”.


Adama kuwa Aruɗe ta riƙesa jikinta na kyarma taja numfashi amma ta gagara sakewa.

Ita kuwa Khausar numfashin taja amma ta gagara sakewa saboda tsananin ruɗu da tashin hankali da tashiga kamar zata shiɗe!.

Ihun da kiran sunan da yake yasa suka janye toch ligh ɗin su dake fuskar Khausar da Adama suka mai dashi sama wannan dalili ya bawa Khausar damar kallon fuskokinsu da kyau amma baki ɗaya jikinta ya sandare bata da wani kataɓus ɗin motsawa.


Su kuwa ƙirjinsa suka saita suka sake harbinsa akwai wani ƙaton tukunya agefen  ya ratsa ya ɓula.

Shi kuwa Baffa Umaru ƙirjinsa ya dafe da faɗin.

“Laila Ha'illalhu Muhammad Rasulullahi (S.A.W)” Shikenan rai yayi halinsa.


Su kuwa mutanen garin baki ɗaya gidan Baffa Umaru suka nufo ko wannensu na rataye da kwari da bakansa sukuwa jin hayaniyar mutanen yasa suka ɓulla ta bayan gidansa suka fice tare da zuwa inda suka bar motarsu suka shiga.


Shi kuwa Baffa Umaru ta cikin tukunyar gefensa ya faɗa jini nata ɓulɓula.

Hajja Nana ce farkon shigowa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa tana isa tsakiyar gidan,

Ƙofar dakinsa ta nufa, tana isa inda yake ta janyo gawar ta rungume tana kuka tare da faɗin.

“Umaru! Umaru!! Umaru!!! Yau kuma mai zan gani gawar Umaru zan riƙe ahannuna kamar yanda na riƙe gawar Usmanuna!”.Cikin kuka sosai take maganar.


Su Baffa Jauro da sauran mutanen ne suka shigo sudai Allah Allah suke su ƙarasa cikin gidan suga abinda ya faru dashi sam basu yi tunanin bin bayan mutanen ba.

Ita kuwa khausar hanyar da suka bi suka fita take nuna musu da yatsa ta kasa furta komai bare kuma ta taɓuka wani abun Yaya Abba ne da ya shigo yace.

“Yayane Khausar!?”.


Cikin matsananci kuka da tashin hankali tace.

“Yaya Abba sun gudu sun kashe shi sun gudu sunbi ta nan na gansu sunbi tanan!”.

Azabure Matasan suka bi wajen ina tuni sun shiga motarsu sun gudu sukuma su Baffa Jauro, Baffa, Sadu da sauran rungume gawar ƙaninsu sukayi suna kuka.

Hajja Nana kuwa tattaɓa jikinsa tayi, Sadik yace.

“Baba mu ɗaukesa mu kaisa asibiti”.


Sake rungume gawarsa Hajja Nana tayi tace.

“Saddiƙu wani asibiti zamu kaisa bayan sun kashe sa baya numfashi bashi da rai!?”.

Jauro ne ya karɓesa ya duba shima ya rungumesa ganin ya rasu Baki ɗayan su akan Gawarsa suka kwana.

Ita kuwa khausar gaba ɗaya ta rikice ta duburburce bata taɓa gani ankashe mutum agaban ta ba sai lokacin tayi kuka har ta godewa Allah manyan Idanunta sunyi luhu-luhu dasu ba abinda ke faɗo mata arai kamar yanda sukayi hira dashi.


Washe gari  akaje aka kira 

Ƴan sanda acikin gari suka je sukayi bin cike tare da rubuce-rubucen su na banza da wofi sannan akayi masa sallah aka kaisa gidan sa na gaskiya.

Kana akazo aka zauna zaman makoki, Addar Khausar Ikki da zata je wajenta a Rugar Fulani ce tazo da taji labarin rasuwar Baffa Umaru tana zuwa kai tsaye gidan Baffan Umaru ta nufa duk ‘yan uwan suna can suna karɓan gaisuwa.


Khausar na ganinta ta tashi da gudu ta Rungumeta tana kuka tace.

“Addah Ikki agaba na agabana fa suka kashe shi sun harbesa sun kashe sa ya rasu har lahira!”.

Addah Ikki tace.

Kiyi shiru Khausar duk mai rai mamacine addu'ar mu yake buƙata”.

Kai Khausar ta gyaɗa amma ta gaza tsaida kukan ta Ganin haka yasa Addah Ikki taja hannunta suka fita zuwa gidan Hajja Nana.


Suna Shiga Khausar ta tsaya cikin Muryanta daya dishe da kuka tace.

“Ni ina tsoro bazan shiga ɗakinta ba akwai kuliya”.

Addah Ikki tace to kitsaya na koreta sannan tashiga ɗakin ta fito da kuliyar tasa awani ɗaki ta rufe.

Sai asannan Khausar ta yarda tashiga ɗakin bayan sun zauna Addah Ikki ta zauna ta riƙa yi mata nasiyya tare da kwantar mata da hankali.


Yaya Abba ne ya ɗauki wayarsa ya tafi Bishiyar ƙare zancenka ya kira duk dangi na nesa ya riƙa sanar da su har ya kira Baffa Hammadu na Ɓadamaya ya sanar masa.

Shima washe gari Baffa Hammadu ya ɗauko iyalansa baki ɗaya suka taho da yammaci gab maghariba motocinsi su guda biyu ajere suka shigo Rugar kai tsaye ƙofar Hajja Nana suka nufa sukayi parking motocinsu.


Ita kuwa Khausar na cikin ɗakin Hajja Nana manne da jikin Addarta Ikki suka jiyo Sallama,

Addah Ikki ce ta miƙe da faɗin.

“Laaa Umma na sannan sai Baffanta yashigo daga bayansa kuma wani kyakkyawan matsakaici mutun ne fari ƙal kamar balarabe yayin da Yaya Abba ke biye dasu abaya.


Durƙusawa Khausar tayi tare da fashewa da kuka kalaman Baffa Umaru ne kawai keyi mata suwwa akunne.

Rarrashinta Addah Ikki ta shiga yi tana bata haƙuri da kyar ta tsaida kukan tace.

“Addah Jiya da daddare Baffa Umaru kece min Baffana na Ɓadamaya yana da wani ɗan sa dake tsananin kama da Babana Addah Ikki wannan shine ke kama da Babana?”.

Cikin matsanancin kuka ta ida maganar.


Kai Addah Ikki ta gyaɗa mata alamar Eh.

Ita kuwa khausar kanta ta kife acinyar Addah Ikki ta cigaba da rera kukanta.

Baffan Hammadu  ne ya riƙe hannunta ya cewa.

“Khausar kiyi shiru kada kiyi kukan rashin Uba nima Mahaifine agareki ni zan tsaya Miki madadin Uba ako ina dan dai Banason rabaki da mahaifiyar kice Shiyasa na barki kike zaune tare da ita muddin ina raye zan maye Miki gurbin Uba”.

Cikin raunin murya tace.

“ Baffa Allah hokke sabbugo”.

Ameen thumma ameen suka amsa.k

Kana suka tafi gida Baffa Umarun.


Bayan angama zaman Makoki  Khausar tabi Addarta Ikki can Rugar Fulani tayi kwana biyu sannan suka dawo bayan sun dawo akayi addu'ar bakwai Baffanta na Ɓadamaya yafara shirin tafiya sai asannan Khausar taga sauran ‘ya‘yan sa daya zo dasu harda Mata bayan sun sake ganawa ne suka tafi.


Akwana atashi ba wuya Khausar ta cika Makwanni uku Arugar Jauro yaya yayin da Baffa Umaru keda mako biyu da rasuwa kullum ‘Yan uwansa matarsa  kuma jama'ar gari cikin yi masa addu'a suke domin baza su taɓa mantawa dashi atarihin rayuwarsu ba da kuma irin gwagwarmayar da yayi adomin kare rayukansu.


            GEMBILA


Acan ɓangare makarantarsu Khausar kuwa ayaune aka gama gyara ilahirin makarantar daga nesa idan ka hango ginin ba zakayi zaton cewa a Gembila makarantar take ba koda a ƙasashen turawa ne sai ’Ya’yan wane da  wane saboda yanda aka ƙawata ginin Makarantar fentin ya kasance Maroon and White haka zalika gate din Maroon anda white ne daga sama An rubuta

*Al'ANSAR ACADEMIC SCHOOL* Rubutun ma Maroon and White ne.


Acikin harabar makarantar kuwa Moddibo ne tsaye hannunsa harɗe aƙirji ya yinda manyan idanunsa ke lumshe yana kallon tsarin ginin Makarantar da akayi wani irin Up stair cycle daga cikin harabar makarantar zagaye yake flowers masu kyau da tsari.

M Jameel ne yace.

“Gaskiya Moddibo kayi ƙoƙari makarantar yayi masifan tsaruwa”.


Murmushin gefen baki Moddibo yayi wanda ke ƙarawa fuskarsa kyau yace.

“Masha Allah haka akeso”.

Ya ida maganar tare da juyewa cikin nutsuwarsa yake tafiya har suka fita acikin harabar makarantar suka shiga motarsu dake gefe afake.

Moddibo ke Driving yayin da M Jameel ke gefen mai zaman banza ƙira'an Sudai's na tashi cikin suratul Nisi'i Moddibo kuwa jinjina kai yayi ayoyin na ratsa sa.

M Jameel ya juya ya kalli Moddibo da bakinsa ke motsi alamar karatun yake bi yace.

“Moddibo kamar akwai motar dake bin mu  fa”.

Kai Moddibo ya girgiza yace.

“A'a ba binmu akeyi ba”.

Kai M Jameel ya gyaɗa still yana kallon mirror bai dai ce komai.

Daga nan suka ci gaba da tafiya ganin still kamar binsu akeyi yasa Moddibo ya tsaya.


Ga mamakin su ganin su tsaya yasa wancan motar tayo kansu gadan-gadan...!



*Wasan fa yanzu aka farashi. Bakin zaren labarin sun kai 12 dozi. Kenan. Akwai ababen dake a duhu fa. Saninsu sai kun bibiyu Al'ƙalamin Shatu yar Aliyu Garkuwa. Jikar Muhammad Babayo Maiturare. Kana kuma (BODDIN DEDDE)*




                      By

         *GARKUWAR MARUBUTA*

No comments

Powered by Blogger.