Sakayyah 2


 📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇


              *SAKAYYAH*

                    Page 2


                          NA

      *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


                *FREE PAGE*

 

*LITTAFIN SAKAYYAH NA KUDINE, WANNAN FREE PAGE NE, ƳAR UWA KI BIYA KI KARANTA CIKIB AMINCI BA HAƘƘIN WANI GABA GAREKI 1k ne kacal kuɗin littafin duk da yawa shi. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, ta nan zaku biya, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. In kuma baki da account ko matsalar Network ZAKI IYA SAYAN KATIN MTN sai ki copy number's ɗin katin ki turo min ta WHATSAPP. 09097853276. Kada ki kirani in kin san ba kayan Ɗa'a kike soba. In dai littafine kiyi min mgn a whatsapp ɗin.*


*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*


_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun da zuƙatan mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida, kai har ma da tan kaɗen gida Shararru kuma ƙasaitattun magungunan matan dans saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata daga hannun. *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Ma'aurats ayau ma na dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki, ko ƙanwarki, ko ƴarki, ko a miniyarli, damake kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Dukansu ƙananan robobin akan dubu uku uku ne kacal Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, koriyar gumba, gumbar madara, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, dukansu a kan dubu uku uku ne ƙananan robobin, sai ta kwalli da ridi da Uku al'khairi da 3 in 1 su dubu biyar biyar ne. Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ta dawo da sabon budurci shi ƴar mitsilar robar 7k ne kana ga masin Daɗi har Maɗigan 5k ne kacal Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, 8k ne  Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, su duka dubu uku uku ne, haɗin Cida kaza, kala biyu ne akwai na 18k shi yanada su tsumi da kwai da rubutu, sai kuma ɗaya haɗin shi 13k ne Ciccibi Abodi, shi 19k ne Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, duk 3k ne kana akwai maganin sanyi sadidan, wanda bani da haufi a kansu set ɗin 10k ne, rabinshi kuma 5k. Ko mai ciki zata shashi baida matsala, infection ko na cikin mahaifane yana magninsa da uzin Allah. Sai su butar sirri, audugar babbar mace,  da dai sauransu...

Sai kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276.  muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci idan kuna ga account no da zaku tura kuɗinku ta ciki masu son kayan Ɗa'an 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276...._



               

      🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,



Cikin fesa sassayyan numfashi, Modibbo ya ci gaba da faɗin.

“Kuji falalar Allahu rabbil samawati garemu, ubangiji yana sonmu yana tausayin mu,  yana kuma jinkanmu."

Ya dire mgnar yana ɗan sauƙe wani numfashi dan Allah ya sani ya fara jin bakinshi ya gaji da mgna. Cikin tattausan muryarsa yaci gaba da cewa.

Daga Abdullahi ibn Busr, Allah ya yarda dashi, yace:

(Ya ma'akin Allah! Shari'o'in Musulunci sunyi yawa a gareni,  saboda haka ka nuna mini wani abu da zanyi riƙon da shi.

Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa.

(Kar harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambaton Allah.

Kuma mai tsira da amincin Allah yace:

(Wanda  ya karanta harafi ɗaya daga littafin Allah yana da ladan kekkyawan aiki ɗaya,  shi kuma kekkyawan aiki ɗaya yana da ladan  misalin goma.

Ba ina nufin Alif lam Mim harafi bane,

A'a.  Alif harafi ne, Lam harafi ne, kana shima Mim harafi ne.”.


Wani irin mayataccen kallo Samira ke bin lips ɗin Moddibo dashi, tana mai kallon dukkan yadda yake motsasu, da yadda tattausan sajensa ke zuba ƙyalli ƙawarta Ikilima Ibrahim ce ta ɗan taɓata da kafa alamun wannan wanne irin kallo ne.

Yayinda gefen damansu kuwa, wata madaidaciyar macece, Hadiza Muhammad Yahaya, wacce take cikin sabbin dalibai.

Kallon da Samira Sani keyiwa Moddibo ne ke bata mamaki.

Shi kuwa Moddibo a hankali yaci gaba da cewa.

Kuma daga Ukbatu Ibn Amir Allah ya yarda dashi yace:

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Ya fito alhalin muna cikin rumfa sai yace:

(Wannene daga cikinku zai so ya fita kullum da safe zuwa ƙoramar Buɗhan ko Aƙiƙ ya  dawo da taguwa biyu masu manyan tozuna ba tare da yayi wani laifi ba ko yanke zumunta ba?

Mukace masa muna son haka.

Yace:

(Ɗayanku yaje Masallaci ya nemi sani, ko ko ya karanta ayoyi biyu daga cikin littafin Allah, mabuwayi mai ɗaukana, yafi masa taguwa  uku ayoyi huɗu sun fi masa taguwa huɗu da kwatankwacin adadinsu na raƙuma.)

Kunga ashe muna ɓarar da damarmakinmu riƙe da waya ba tare da mun samu mun ribaci ilimin da iyayenmu da malanmu suka bamu ba.

Kuma mai tsira da Amincin Allah yace:

(Wanda ya zauna a wani waje, bai ambaci Allah a wajenba, wannan zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah, wanda ya kwanta a makwanci bai ambaci Allah a wajenba shima zai zamanto masa abin bibiya a wajen ALLAH.

Kuma mai tsira da amincin Allah yace:

(Babu wasu mutane  da zasu zauna a majalisi da basu ambaci Allah a cikinsa  ba, kuma basu yi salati ga annabinsu ba, face ya zamo musu abin bibiya, in Allah yaso yayi musu azaba, in yaso kuma sai ya gafarta musu.”

Jujjuya idanunsa yayi fuskarsa cike da shauƙin son Mahaikin Allah Muhammadu Rasulullah, da sahabbansa, 

Wani irin sassayan numfashi ya fesar tare da lumshe idanunsa, wanda yakan shiga wannan yanayi a duk lokacin da yakeyiwa ɗalibansa nuni da al'khairan dake cikin ammaton Allah da bin sunnar manzonmu abinkoyinmu abinsonmu da sahabbansa masu daraja.

Ita kuwa Khausar ƙasa tai da idanunta.

Sai kuma ta ɗan ɗago ta kalleshi jin tattausar muryarsa yaci gaba da cewa.


“Kuma mai tsira da amincin Allah yace:

Babu wasu mutane da zasu tashi daga wani majalisi da basu ambaci Allah a cikinsa ba, face sun zama kamar sun tashi daga kan *mushen jaki ne* kuma zai zamanto musu abin dana sani)”....

Ya ƙare mgnar da haɗe kan yatsunsa duka, kana sai ya buɗasu a tare da ware tafin hannunsa kamar ya sake abu,

alamun ya dasa babbab ɗamba, ya gama da wannan yankin.


Gaba ɗaya hankalinsu tunaninsu duk yana kansa, domin suna matuƙar jin dadin yadda wasu lokutan idan ya shiga aji  yake tunasar dasu mahimman abubuwan da suka cancanci musulmi ya lizamcesu.

Yayinda wasu kuwa da sam baya shiga ajujuwansu cike da son salon sa suke sauraronsa, kasan cewar makarantar nada yalwar malamai kuma shi aiyuka sun mai yawa shisa ba dukkan class da suke dashi yake shigaba.


Shi kuwa Moddibo cikin alamun gajiya da yawan motsa lips nasa da yayi yaci gaba da cewa a gaggauce.

“Mu farka mu ribaci wannan shekarar dukanta kada muce dan wannan wata na Ramadan daya shuɗe, zamu bar wasu ayyukan ibada, mu jure mu zamo dasu ɗabi'armu a kullum domin shi ubangiji ka gafartawa bayinsa, a duk sanda yaso ya ainta wasu daga azaba zuwa rahmarsa madaumiya,  mu wasar da wayoyin nan mu ruggumi Alqur'ani mai girma da tasbihai ya zama dai ita wayar nan sai time to time zamu riƙe ya ke mai karatu dake nake."

Ya faɗi hakan yana nuna gefensu Samira dake buɗe da littafi a gabansu.

Sai kuma ya ɗan gyara saƙale Lapel Microphone din a wuyar jallabiyar jikinsa dan yaji muryarsa tana ƙasa sosai alum yadan zame kaɗan, da ɗan sauri yace.


“Zaku iya duba Muslim (1/554) Abu Dawud (4/264) da waninsa duba Sahihul Jam'i, (5/342). Tirmizi duba Sahihul Tirmizi (3/140) Abu Dawud (4/264) da Ahmad (2/389) duba Sahihul Jami (5/176) Allah shine mafi sani... Abinda nace dai-dai Allah ya haɗamu a mizanin ladan abinda nai kuskure Allah ya gafartamin.”


Ya rufe mgnar da addu'a tare da juyawa ya fita.

Sukuwa gaba ɗaya numfashi suka sassauƙe, yana fitowa Malam Jamil na isowa wurin, dan shi zai shiga ya shaida musu kwanakin da aka ƙara.


Kai Modibbo ya kauda gefe, jin Aminin nashi na cewa.

“Fattanah maza yi gudu ki shiga aji kada in rigagi, shiga, dan in na rigaki nima yau gadin aji zansa kiyi mana”.

Da sauri Khausar din ta juyo tare da kallon shi cikin alamun yanai musu barkwanci tace.

“Malam ko ta window ma zan shiga”.

Murmushin yayi tare da cewa.

“Har yanzu baki girmi shiga ta window ba FATTANAH”.

Da sauri tace.

“Toh ai banyi jikiba, ka gani”.

Kawai sai ta kama jikin window alamun zata zauna ta wajen sai ta juya ta ciki.

Cikin yamutsa fuska Moddibo yace.

“Ke bar nan,”.

Ai da sauri ta diro tare, da nufar ƙofa, tana tura baki.

Shi kuwa Malam Jamil cikin tsananin son yarinyar sabida ƙwazonta da jan da kwanyarta keyi kana da ƙawancenta da ƙanwarsa Asma'u Ahmad ya bita da ido.

Rungume Moddibo yayi tare da yin mgn murya can ƙasa.

“Tuba mukeyi Moddibo ai mana tsawan a hankali ka mance baka cire Lapel Microphone ɗinba, har nima tsawar ta razanani”.

Wani irin nannauyan numfashin Moddibo ya sauƙe tare lumshe idanunsa.

Shi kuwa M Jamil murmushin yayi kana kuma ya sake shi yace.

“Lokaci na tafiya sai na fito na sallami maza kam”.

Kai Moddibo ya gyaɗa tare da sauƙa ƙasa.


Goma  dai-dai aka tashi islamiyan gaba ɗaya duk ɗaliban suka koma gida bayan M Jamil ya musu bayanin dalilin ƙarin hutun, wanda kuma suma sunga hakan.


Ƙarfe ɗaya dai-dai suka tashi daga taron tattaunawa da malaman nasu baki ɗaya.


Bayan sunyi sallan azahar ne, kana duk suka tafi, ma'aikata sukaci gaba da aikinsu.


A gidansu Khausar kuwa.


Khausar ce kwance bisa 3 str daga ita sai yar doguwar rigar material mai taushi a jikinta, Pink collor, sai hular sanyi data sa a kanta, yayinda himilin gashinta yayi tub-tub a ciki.

Da alamun bacci take sonyi.

Cikin sanyi ta buɗe ido ta tare da juyowa ta kalli Momynta dake fitowa daga kitchen ɗinta, hannunta riƙe da plate da  yankakkun fruits  a ciki masu sanyi, gefen ta ta zauna bisa 1 str ta ɗaura plate ɗin kan cinyarta tare kallon Khausar ɗin  data miƙa mata hannu alamun ta bata.

“Tashi kije ki ɗebo Uniform ɗin ku, nasan yanzu ya bushe kizo ki goge muku kafin a kira magriba”.

Numfashi mai ɗan sanyi Khausar ɗin ta fesar tare da miƙewa zaune, ita kuwa Momy tafin sawun ɗiyar Tata take kallo cike da ganin kamannin sawunta dana ahlinta.

Hannu tasa ta ɗauki inabi guda uku. Kana ta  miƙe tsaye tare da juyawa ta fita.

Ita kuwa Momy da idanu ta rakata.


Tana fita a barandar ta tsaya tare da ɗan sa hannunta na dama ta riƙe ƙugunta.

Amina  ce ta fito daga side din Gimbiya Bunayya, mahaifiyarsu kenan, uwar gidan Lamido, 

Wacce daga itana sai Maman su Khausar wacce itace amaryarsa.


Wani irin  kallo Amina tayiwa Khausar tare da cewa.

“Hamshaƙiya, cin abu a tsaye ba koyarwar musulunci bane”.

Fuska Khausar ɗin ta ɗan yamutsa tare da cewa.

“Ngd”.  Sai kuma ta miƙawa Aminu ƙanin Amina wanda yake gefenta.

Da sauri Amina ta kwaɓe hannun yaron da bazai gaza shekara goma sha ɗaya  ba tare da cewa.

“Makwaɗaicin baza, in zakaci akwai a fridge kaje a baka”.

Ido Khausar ɗin ta zuba mata, sai kuma ta sauƙe numfashi dan batayi mmkin hakanba, cikin alamun kasalan da baccin da takeji ya sakar mata, ta nufi wurin shanyan nasu, a hankali take tafiya, dan ganin shanyan nasu yana can  har bayan Part ɗin Hajia Bunayya Umma.

“Wannan daga gani ma aikin Ramadan ne, shine zai zo yayi mana shanya har nan, zaice waɗan can igiyoyin tsawonsa bazai kaiba”.

Ta ƙare mgnar tana nufar can.

A hankali ta fara janye shanyan, har ta isa dai-dai window Hajia Bunayya, cikin mamaki ta ɗan tsaya jin yadda Umman ke mgn da faɗa-faɗa.

“Kada in damufa kake cewa.

Kasan kuwa irin tashin hankali da nake ciki duk sanda na buɗi idanuna na kalli Haiydar a matsayin ɗan Lamido Yariman Gembila kuwa, ko ka mance shine ɗan sa na miji babba, shin baka ganin iyakata da mulki sai dai gani sai hange tunda shine ɗa babba akan Aminu na.

Kai bakaga yadda komai zai juye min ba a gaba, ina gani sarauta zata koma ɗakin Aysha ƴaƴanta ne zasu mulki masarautarmun”.

Sai kuma tayi shiru alamun tana sauraron abin da ake cewa a ɗaya sashin.


Ita kuwa Khausar cike da tsoron halin irin na Umma, gashi dai abinda taji, amman koda zata kwana gayawa mahaifiyarsu bazata taɓa yardaba, domin Umma bata taɓa nuna kishinta a kanta, shiyasa ta ɗauki dukkan yarda ta bata.


Cikin tsananin tsoro Khausar ɗin ta zaro ido ta tare dasa tafin hannunta ta dafe ƙahon zuciyarta, jin Hajia Bunayya na cewa.

“Wallahi tallahi billahil azeem zanyi komai dan ganin bayan Aysha da yaranta, zanyi duk abinda ya kama domin in kauda Haiydar a matsayin yarima mai jiran gado, dan wlh Allah zan iya kasheshi kowama ya huta!...”.

Cikin tsananin kaɗuwa Khausar ta juya da sassarfa ta koma sade ɗin Maminta, tana isa kawai sai ta watsar da kayan bisa kujera.


Da sauri ta kamo hannun mahaifiyar tata tare da cewa.

“Momy! Momy dan Allah ki biyoni zo kiji wani abu”.

Ta ƙare mgnar a matuƙar kiɗime, wanda hakan yasa dole Hajia Aysha ta bita a baya.


Ita kuwa da sauri take jenta, har zuwa bayan window Hajia Bunayya.

Cirko-cirko suka tsaya,

Ita kam Khausar cike da firfito da ido waje take sauraron abinda Hajia Bunayya ke faɗi.


Momy kuwa wani irin...!



A hankali M Jamil yayi parking  a bakin gate ɗin gidansu Moddibo juyowa yayi ya kalli Moddibo dake gefensa yana lallatsa system nasa.

“Toh wazai fita ya buɗe mana gate ne kam?”.

Ba tare da ya ɗago ya kalleshiba ya ɗaga kafaɗarsa ɗaya tare  buɗe tafin hannunsa alamun

Oho.

Kai M Jamil ya jujjuya tare da cewa,

“To bari ni buɗe”.

Kai ya kuma gyaɗa masa alamun.

“Toh”.

Murmushin M Jamil yayi tare da fita ya buɗe gate ɗin, kana ya dawo yaja motar suka shiga ciki.


Parking yayi kana suka fito suka nufi cikin gidan,


 Kai tsaye sashin Innayin suka wuce.


Wani irin yalwataccen murmushin M Jamil yayi tare dayin saurin ya haura kan barandar zama yayi daɓas bisa tattausan carpert ɗin dake shimfiɗe a barandar.

Innayi na kwance yayinda  Ummin Jamil kuwa ke gefenta tana ɓare mata banana.

Itama yalwataccen murmushin tayi tare da miƙawa Moddibo ayaban data ɓaren.

Amsa yayi tare da juyowa ya ɗan kalli M Jamil da ya zame ya kwanta bisa carpet ɗin tare da ɗaura kansa bisa cinyarta, cike da so, ƙauna, shaƙuwa, tausayawa, yace.

“Ummina kin san irin farin cikin da nakeji a raina kuwa in na ganki?”.

Murmushin kawai tayi dan ita bazata iya cewa komaiba a gaban Innayi sabida Jamil shine ɗan ta na fari, kuma su nan Gembila sashine na cikakkun Fulani.


Kawai dai abinda ta sani a baɗini tasan ta fishi farin ciki.

Shi kuwa Moddibo gefen Innayi dake kwance da alamun har yanzu nitsuwarta bai ida dawowa jikintaba, hannunta ya riƙe tare da kallon M Jamil.

“Kai dan Allah ɗagata kada ka karya mana cinyarta da katon kankan nan”.

Ya ƙare mgnar yana gutsuran banana.

Shi kuwa Jamil da sauri ya tashi zaune jin Umminshi na ture kanshi tana cewa.

“Ai kam gskyarka Moddibo”.

Tashin nasa ne, yasa ta miƙe ta nufi kitchen, trayn data shirya kulolin abincinsu ta kawo musu.

Ta ajiye a tsakiyar su,

Shi kuwa Modibbo a hankali ya kamo hannun Innayin tare da tallabota alamun so yake ya ganta a zaune.

Sai kuma duk suka kalli Innayi data buɗe kwayar idanunta jin yana tallabota.

Zaunar da ita yayi cikin kulawa yace.

“Yanzu me yake miki ciwo?”.

Cikin sanyi tace.

“Nima kaina ban saniba, kawai dai zuciyata ke a tsinke tsoro nakeji Moddibo”.

Da sauri Jamil yace.

“Toh Innayi tsoron me kuma kikeji?”.

Cikin sanyi tace.

“Tsoron kada mutuwa tai mini zuwan ba zata”.

Wani irin masifeffen tsinkewan zuciya ne ya riski Moddibo jin Jamil ya ɗan yi yar dariya tare da cewa.

“Kada ki damu Innayi ki dena jin tsoron mutuwa, domin ita wajibinmu ne ita.

Kuma tsufa ba shine hanyar mutuwaba, ba abin mamaki bane ki rayu ni nan Jamilu in mutu in barki, in bar Ummina da rashina, in bar Aminina Moddibo da rashin Aboki kamata, tabbas a al'amarin ubangiji zan mutu in barku a raye da kuma ƙunar rashina”.

Da sauri Moddibo yace.

“Yah Salam wai kai J meyasa ne wasu lokutan kalamanka a baibaisuke? Dan Allah kasan abinda zakana cewa”.

Murmushin mai sauti Jamil yayi tare da cewa.

“Zanfa mutu kam, dole zan mutu to kai dama a gani kake a haka zamu tabbata ne?”.


Da hannu Moddibo ya nuna masa Umminsa da haka kawai taji wasu irin zafafan hawaye sun zubo mata.

Da sauri Jamil yasa tafin hannunsa ya sharce mata hawayen tare da cewa.

“Kada kiyimin kuka kodama na mutu kada ki damu Ummina kinga aminina Aliyu ko to shi zai zame miki madadina”.

Da sauri tayi mishi dakuwa.

Sai kuma yayi dariya mai sauti tare dace.

“Oh su Ummi ana son ɗan fari wato irin bakya son Jamilunki ya mutun nan ko”. Ya ƙare mgnar cikin tsigar wasa kamar dai kakarsa ce,

Hakanne yasasu yin murmushin ganin zata kai mishi duka ya ɗan zille yana cewa.

“Haka kawai wai kunya wai ni ɗan fari bazakice kina sonaba, toh ni kam ina sonki ina sonki ina sonki Ummina”.

Ƙeyarsa ta ɗan buge, kana ta  tura musu plate ɗin dake cike da fruits sai kuma ta mimmiƙa musu fork,


Innayi kuma yar wannan hirar da sukayi yasa ta ɗan sake kaɗan, duk da har yanzu in ta rufe idanunta tana ganin abinda Allah ya nuna mata daren jiya.


Jamil ne ya kalli Innayin tare da cewa.

“Dr  Jamila tazo ta dubaki ko, dan da safe kafin mu wuce makaranta na kirata tazo”.

Kai Ummi ta gyaɗa alamun eh tazo.


Frutis ɗin kawai suka ci kana suka miƙe suka nufu part ɗin Moddibo.

Suna shiga falon,

Cikin sanyi Jamil ya zauna bisa kujera tare da riƙo yatsar Moddibo manuniya, cikin wata iriyar sassayar muryar yace.

“Moddibo kasan ina jin farin ciki na musamman in naga Ummina ko?”.

Sunkuyar da kai Moddibo yayi tare da zuwa aminin nasa idanu cikin sanyi yace.

“J nasani! Na sani dan farin cikin baya ɓuya a fuskarka”.

Cikin Muryar da tafi ta ɗazu rauni ido na ciko da hawaye yace.

“Amman kuma fa farin cikina raggene, duk daɗin da nakeji in na tuna cewa Ummina ba a gidan Dadyna takeba, inajin ciwo mai yawa a raina, inajin takaicin Kasan cewar mahaifiyata bata gidan mahaifina tana can a wani gidan.

Bayan ita tasha wahalar zama dashi cikin talauci,  saida yayi kuɗi dai-dai sanda zataji dadin rayuwa ya saketa, gashi yan uwanta ba masu haliba, mijin da Allah ya ƙaddara ta aura shima rayuwar ba daɗi sabida baida ƙarfi”.

A hankali Moddibo ya zauna kusa dashi cikin ƙarfafa mishi guiwa yace.

“J wanne dadine na kuɗi ya rage wanda bakayiwa Ummi ka tunafa, duk abinda kace kanaso Daddy yana baka, duk kuɗin da zaka nema zai baka, a haka har Makka ka kai Ummi yaranta ka sasu a makaranta mai kyau sanadin su kaƙi kayi aiki a ko ina kace zakayi karantarwa a makarantarsu dan ka tayata basu tarbiyya. Kana kuma yi tunda gashi yanzu sun kusa gamawa, tunda ko Asma'u nanda shekara uku dai zasu gama,  secondary School, kace kuma suna gamawa zaka aurar da Asma'u kana ka ɗauki nauyin karatunta, ta na gaba tana gidan mijinta, shi kuwa Bashir na mijine kuma kace in ya gama so kake ya samu jami'atul Madina, in ya tafi can sannan kayi aure kace kuma kana aure zaka ɗauke Ummi da ita da mijinta Malam Ahmad zaka riƙe su, Jamil to meya rage na jin daɗi da baka samawa Ummi ba, ka gyara mata gidan da take, ka gyara mata ɗakinta”.

Wani murmushin mai sanyi yayi tare da cewa.

“To wai Moddibo da kake cewa haka, rainafa mallakin ubangijine a duk sanda yaga dama zai ɗaukeni daga  wannan duniyar, ko ban gama cikace burukana ba, in babuni a raye wa zai maiye musu gurbina?”.

Cikin tsuke fuska Moddibo yace.

“To dama wa yake da tabbacin rayuwa, yanzu ni in dai naci zan lizanci irin tunaninka Innayi fa bata da kowa a duniya saini.

J ni zaka gayawa mutuwa? Ni Aliyu zaka gayawa mutuwa?”.

Sai kuma duk sukayi shiru suka zubawa juna ido.

Numfashi mai nauyi Moddibo ya fesar kana a hankali yace.


“J ka kalleni mana! In zame maka madubi, gwara kaifa, 

kasan su Ummi kana ganin ta gafa Daddy”.

Da sauri M Jamil ya ri ƙa gyaɗa mishi kai tare da tuno maraicin aminin nasa.

 Shi bai san iyayensu ba ranar da mahaifisa ya rasu, firgicin abin ne ya tadawa mahaifiyarsa naƙudansa, ta haifeshi kana itama tabi bayansa kamar yadda Innayi ke basu labari.

Da sauri M Jamil ya kalleshi jin yana mgn a hankali.


“Ba uwa ba uba ba wa ba ƙani ko ƙanwa ba Baffa ba kawu ba goggo ba Yafendo, yanzu ashe bazaka dubi maraicina ba, sai kai ka godewa Allah ba J kaga ni kuwa idan na tuna duk rashin da nayi in naji ƙunci da ciwo sai in tuna.

Allah ya azurtani da rayuwa da lafiya kana yayi min ni'imar kasan cewa Musulmi, ya bani hankali ya ƙara min da haddar izu settin, da littattafai masu tarin yawa wanda masu iyaye da dama basu samuba, ya bani sa'a a dukkan karatuna mukayi digire har master's har zuwa P.H.D a makaranta mafi daraja a duniya Jami'atul Madina, kana muka samu gurɓin aiki kuma a can.

Wanda ko yau muka koma can da aikinmu a hannu, amman kai ga uzurin daya tsareka, nima kuma da uzurin daya tsareni”.

Da sauri M Jamil yace.

“Astagfurullah! Astagfurullah!! Astagfurullah!!! Alhamdulillah aboki na gari rahama ne, ai kam ni ga uzurin daya tsareni  to amman kaifa Moddibo uzurin menene ya tsareka duk da bana son mu rabu Amman zaso kaje can kayi aikinka da al'bashinka mai daraja”.

Kai Moddibo ya kauda tare da cewa.

“Uzurina ai a fili yake J Innayi na tana son kulawata”.

Da sauri M Jamil yace.

“Ba gsky bane Moddibo karo na forko kenan a rayuwarmu daka ɓoye min abinda ke ranka kaƙi ka gaya min me dalilin ka na zama a ƙasar nan bayan saudia na buƙatar ka, kuma harda daman zama da iyalanmu fa muke dashi a can”.

Kai ya jujjuya tare da cewa.

“J yaushe na zama makaryacin da har mgnata bazata samu karɓuwa a wurinka ba?”.

Da sauri M Jamil yace.

“No wlh ni mai shaidar ka ne har gaban abadan kai ba makaryaci bane, kawai dai ban gamsu da hujjar bane”.

Kanshi ya jujjuya kana ya nufi bedroom ɗinsa,

Shi kuwa M Jamil ɗayan ya shiga.


A can cikin masarautar Gembila kuwa,

Cike da kaɗuwa Khausar ta...


Ta juyo ta kalli mahaifiyarta sabida jin kalaman da Hajia Bunayya ke faɗi.

“Eh Sulaiman a kawo min mashin ɗin lipan mai kyau wanda zaiyi dai-dai da Haiydar, 

A kawo fari dan yafi son komai nasa fari”.

Sai kuma ta ɗan yi jim, alamun tana sauraran abinda ake faɗi a ɗaya sashi, 

dariya mai cike da sakewar zuciya tayi tare da cewa.

“Ai kaima kasan shi na musamman ne, Yarima ne fa, mai jiran gado, kuma gashi sunan Babanmu gareshi, in banji dashi ba da waye zanji”.


Ita kam Khausar cike da mmki take kallon yadda mahaifiyar ke sakin wani murmushi mai cike da yarda da jin daɗin kawaici da ihsanin uwar gidan tata, 

Yayinda ita kuwa Khausar take kallon abun da idanun basira, tana tuna kalaman da taji ɗazu da wanda Umman keyi a yanzu, a sanyaye tace.

“Marching kuma?”.

Daga ciki kuwa sai suka tsinkayo muryar Asiya na cewa.

“Ehye Haiydar ɗan gatan Umma da Lamido, yaron nan kunaji dashi,”.

Murmushin mai cike da manufa tayi tare da kallon inuwar Khausar da Mami  ta jikin window nata, cikin ɗan daga sauti tace.

“Kema ai ɗan lelenki ne,”.

Miƙewa tsaye Asiya tayi tare da cewa.

“Yauwa dan Allah Umma ni zanyi masa albishir”.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.

“Amman ba yauba sai marching ɗin ya iso”.


Numfashi mai sanyi Momy ta fesar tare da kamo hannun Khausar suka juya suka tafi.


Ganin tafiyar sune yasa Hajia Bunayya yin kwaffa tare da cewa.

“Uhum zanyi mgnin kine, shegiyar yarinya mai masifar wayon tsiya da  sa ido, tama fi mahaifiyar tata wayo da fahimtar manufar mutum”.


Su kuwa, suna shiga falon Khausar ta juyo a hankali tace.

“Dan Allah Momy kada ku bari Haiydar yaja marching yayi ƙarami dudu du fa shekarunsa sha 13 ne kawai dan yanada saurin girma”.

Da sauri ta juyo ta kalli Haiydar da yanzu shigowarsa, kanshi ya nuna da yatsarsa manuniya tare da cewa.

“Ni ne ma yaron? To da shekaru nawa kika fini dabino uwar tsufa,  ba shekara ɗaya rak kike bani”.

Yes tabbas kam shekarunsa 13 ne, amman in ka ganshi zakayi zaton yaje 16, domin yanada girman jiki, kuma irin masu wayo da halin girman nanne shiyasa sam bazaka tantance shekarunsa ba, ya fita jiki da tsawo sosai.

Dan in ka gansu zakayi zaton shine babban irin ya bata shekara ukun nannan ne”.

Kai ta jujjuya tare da rumtse tafin hannunta, kana cikin sanyi tace.

“Dan Allah  Momy kada ki bari dan Allah a wannan karon dai ki yarda dani”.

Kai Hajia Aysha ta gyaɗa mata tare da cewa.

“Zan duba."

Cikin kwaɓe fuska Haiydar ya turo baki gaba tare da cewa.

“Plesse Momy kada kibi ta kan mgnar ta”.

Still kai ta gyaɗa masa shima tare da cewa.

“Toh zan duba”.

Cirko-cirko sukayi a gabanta.

Dan dama da haka take yanke musu taƙaddama.

Idanu ta ɗan lumshe jin an kira sallan magrib cikin fesar da sassayan numfashi tace.

“Lokacin salla yayi, maza muje muyi salla”.

Ba musu duk suka juya, shi Haiydar waje ya fita yana cewa.

“Ramadan zomu tafi masallaci”.

Ita kuwa Khausar ɗakinsu ta nufa tana cewa.

“Raudat zomuje muyi salla."

Da sauri kuwa sukabi bayansu.



A can gidansu Moddibo kuwa,

M Jamil ne, ya kalli dun-duniyar sawun Moddibo lokacin da suka fito kan barandar da alamun al'wala sukayi.

A hankali yake taku cikin nitsuwa, yayinda yake motsa laɓɓan bakinsa yana taibihi.


Sai kuma ya maida kallonsa kan sumar ƙeyarsa dake kwance lip-lip tayi irin naɗin nan mai kamar taburma.

Kusan a tare suka sauƙo, 

Hango Ummi da Innayi zaune bisa sallayunsu, da kaskon rushi a tsakiyar su ne, ya sasu juyawa suka nufi waje, sabida tafiya masallaci.


A hankali Moddibo ya zira tafukan hannunsa cikin aljuhun jallabiyar jikinsa, sabida wani irin masifeffen sanyi dake fesowa, duk da rigunan sanyin da suka ɗaura kan jallabiyoyin bai tsare musu sanyi irin na garin Gembila ba, musamman ma, a lokacin da magrib ta ƙarato, wanda lokacin sanire ke sauƙa.


Kasan cewar masallaci babu nisa da gidan ne, yasa suka, tafi da sawu.


A hankali M Jamil ya lumshe idanunsa sabida yadda yake jiyo sautin muryar Moddibo can ƙasa yana zikirin tafiya masallaci.


Shi kuwa Moddibo cikin yanayin sanyin da yakeji yake motsa laɓɓan sa a hankali cikin dadɗan  sauti can ƙasa-ƙasa yake cewa.

اللَّهُـمَّ اجْعَـلْ فِي قَلْبِـي نُوراً، وَفِي لِسَـانِي نُوراً، وَفِي سَمْعِي نُوراً، وَفِي بَصَرِيِ نُورًا، وَمِنْ فََوْقِي نُوراً، وَ مِنْ تَحْتِي نُوراً، وَ عَنْ يَمِينِي نُوراَ، وعَنْ شِمَالِي نُوراً، وَمِنْ أَماَمِي نُوراً،,وَمِنْ خَلْفِي نُوراً، وَاجْعَلْ فِي نَفْسِي نُوراً، وأََعْظِمْ لِي نُوراً، وَعَظِِّمْ لِي نُوراً، وَاجْعَلْ لِي نُوراً، واجْعَلْنِي نُوراً، ألَلَّهُمَّ أَعْطِنِي نُوراً، وَاجْعَلْ فِي عَصَبِي نُوراً، وَفِي لَحْمِي نُوراً، وَفِي دَمِي نُوراً، وَفِي شَعْرِي نُوراً، وفِي بَشَرِي نُوراً، أَللَّهُمَّ اجِعَلْ لِي نُوراً فِي قَّبْرِي... وَ نُوراَ فِي عِظاَمِي، وَزِدْنِي نُوراً، وَزِدْنِي نُوراَ، وَزِدْنِي نُوراً، وَهَبْ لِي نُوراً عَلَى نُوراً

Dai-dai lokacin da yazo ƙarshen addu'ar suka isa bakin masallacin.

Kusan a tare suka haɗa baki wurin yin addu'ar shiga Masallaci.

”أَعوذُ بِاللّهِ العَظِيـمِ، وَبِوَجْهِـهِ الكَرِيـمِ وَسُلْطـَانِه القَدِيـمِ، مِنَ الشَّيْـطَانِ الرَّجِـيمِ، بِسْـمِ اللّهِ وَالصَّلَاةُ وَالسَّلامُ عَلَى رَسُولِ اللّهِ، اَللَّهُـمَّ افْتَـحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتـِكَ“

Kana a nitse suka shiga cikin masallacin.

Shi Moddibo gefen daman sahun forko ya zauna, yayinda shi kuma M Jamil ya nufi wurin kiran salla...


Kasan cewar M Jamil ke ladancin masallacin Moddibo kuma limancin...


Bayan an idar da sallane, Khausar ta juyo ta kalli Raudat tare, da miƙa mata littafin  Dua azkar, amsa tayi kana ta buɗe daga shafin forko ta fara cikin sassayan sautin yarinta.


Ita kuwa Khausar Alqur'anin ta, ta ɗauka tare da fara, rero karatun Alqur'ani cikin zazzaƙar muryarta take biya suratul Nisa'i.


A haka har aka kira isha sukayi kana, suka fito.

A falon suka zauna baki ɗayansu suna cin abinci.


Misalin ƙarfe tara da rabi, Ummi ce zaune gefen Innayi da hijabi  a hannunta alamun ta gama shirin tafiya.

Cikin kulawa da martabawa tace.

“Toh Innayi Allah Ubangijin talikai ya baki lfy yasa zakkan jikine, in Sha Allah gobe koda dare zan zo in kuma dubaki da jiki”.

Kai ta gyaɗa cike da jin daɗin kulawar Ummin Jamil cikin ƙarfin guiwar da ta ɗan samu tace.

“Amin ya rabbil izzati Fatima ngd matuƙa Allah ya raya miki ahlinki yasa suyi miki fiye da abinda kikeyi min”.

Cike da jin daɗin addu'ar tace.

“Amin ya Allah”.

Moddibo kuwa, kai ya tankwara gefe yana kallon kakartasa, sosai ta rame a dare ɗaya da wuni ɗaya.


Haka dai sukayi sallama Jamil ya ɗauke ta suka tafi.


Har bakin gate Modibbo ya rakasu.

Kai ya ɗan juya ya kalli wata motar dake gefen damansa ƙirar BMW irin dai wacca M Jamil yaja sukaje makaranta, sai dai wacce baƙace wannan kuma farace ƙal  mai masifar kyau.

Murmushin M Jamil yayi sabida ya fahimci kallon da yayiwa motar ma magana ce.

kanshi ya juya tare da cewa.

“Lafiyarta ƙalau kawai na barta a nanne sabida nan ya dace da ita, tunda ba gida ɗaya mukeba, Allah ya kiyaye wani uzurin zai iya tashi da dare, kaga kamar jiya da kasan Innayi ba lafiya kawai ɗaukarta zakayi ku tafi hospital ko Ummi?”.

Ya dire ayar mgnar yana kallon Umminsa da shima Moddibo ita yake kallon.

Cikin gamsuwa Ummin tace.

“Sosai ma kuwa”.

Cikin yin ƙasa da kai Moddibo yace.

“Ummi har kema haka zakice, kamar baki san me ake faɗi a cikin gariba, ba cikin gari, bama har cikin gidansu fa, ganin kaskas akemin wasuma ɗaukar abotarmu ta tun yarinta sukeyi a matsayin na maida J saniyar tatsa."

Cikin sanyi Ummin tace.

“To Moddibo ai shi ɗan adam ba'a biye masa”.

Da sauri Jamil yace.

“Yauwa Ummi gaya masa dai kam”.

Cikin tsare M Jamil din da ido yace.

“Motace dai ta hannunka ta ishemu, kuma ga waccar ma, kasan in bawai baka nanba always muna tare”.

Da sauri Jamil ya jujjuya mishi kai tare da jan motar ya tafi.


Sashin  Innayin ya nufa, cike da zurfin nazari.

Tv ya kunnamata tashar Sunna, inda aka sa sautin karatun Alqur'ani mai girma.

Ido Innayi ta lumshe jin nitsuwa da salama na diro mata,

Saida safe yayi mata kana juya ya fita zuwa Part ɗin sa.


Washe gari ranar Alhamis ne, yau babu makaranta ko yan haddan bazasu jeba, shiyasa su Khausar suna gida,

Bayan sallan la'asar Asma'u Ahmad ta shigo falon Momy cikin sakin fuska tayi sallama.

Da sauri Khausar ta fito daga ɗakin Momy tana cewa.

“Wa alaikissalam Giɗaɗo".

Murmushin Asma'u Ahmad Giɗaɗo  tayi, ƙanwar M Jamil kenan da suka haɗa uwa.

Cikin sakin fuska tace.

“Jauro”.

Fuska Khausar ta kwaɓe tare da cewa.

“Wai jauro gsky ni an cuceni”.

Murmushin sukayi baki ɗaya sabida daƙuwar da Mamy tayi musu.

Cikin kunya Asma'u ta ɗan rusuna, tare da cewa.

“Barka da yamma Mamy”.


“Barka dai Asma'u ya Umminki?”.


“Tana lfy tace in gaidaki”.


“Masha Allah Ina amsawa”.


Da sauri ta miƙe tsaye jin Khausar ta kamo hannunta.

Ɗakinta suka nufa, suna shiga suka zauna bisa gado.

Raudat dake kwance kan gadon riƙe da wayan Mamy tana game ne ta miƙe da sauri ta faɗa kan Asma'u.

Ruggumi yarinyar tayi tare da cewa.

“Autan Mamy tsifa ake yi ne”.

Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.

“Eh kuma gashi har yanzu Adda Khausi bata gama minba, tsifanta zafi”.

Hararanta kausar ta ɗanyi tare da cewa.

“Da Allah tashi daga nan, nawama da yaya nake tsifan,  kin samu ma inayi miki”.

Ta ƙare mgnar tana fita daga ɗakin.

Jim kaɗan ta shigo riƙe da filas da kofuna guda biyu bisa tray da kuma kayan tea, kan bed side drower ta ajiye tiran kana ta haɗa musu tea mai zafi, sabida rage sanyin da suke rayuwa cikinsa, yasa tea ya zame musu tamkar ruwa, madadin in kaje baƙunta a baka abin sha mai ɗan sanyi, sai a tarbeka da zazzafan shayi.


“Gidado bar tsifan nan ga tea".

Khausar ta faɗa  tana zama gefenta tare da miƙa mata, kofin.

Amsa tayi tare da kallon Raudat da ta fice da gudu sabida jin Abbansu ya shigo yana kiranta.


Riƙe cup ɗin tayi ba tare da tasha ba,

Ido Khausar ta ɗan zuba mata kana tace.

“Ya dai Giɗaɗo lfy kuwa?".

Numfashi mai nauyi Asma'u ta fesar kana cikin sanyi tace.

“Kamar zan biya ɗazu ki rakani”.

Ajiye cup ɗin hannunta tayi tare da cewa.

“Ina?”.

Murmushin Asma'u tayi tare da cewa.

“Gidan su Moddibo”.

Fuska ta kwaɓe tare da cewa.

“Allah ya kiyasheni, me zai kaini gidansu wannan mugun, mutumin da duk duniya bana da maƙiyi sama dashi, duk abin da nai laifine, ni zanje gidansu yace na kai musu fitsara ya dakani a banza”.

Murmushin Asma'u tayi tare da cewa.

“Yoh ai shiyasa ma ban biyaba dan nasan bazaki taɓa yarda kijeba, kuma dai don shine sarkin masifa da mugunta kawai daga zuwa gidansu sai ya kama dukanki”.

Baki ta taɓe tare da cewa.

“Yoh ai bazanma jeba ma”.

Kai Asma'u ta jinjina a ranta tana raya wata rana zatayiwa Khausar tsiya, ta kwasheta ta kaita.


Ajiye kofin tea  ɗin tayi tare da cewa.

“A'a  dubiyar mara lfy cefa Innayinsa ce ba".

“Can musu”.

Ta faɗa tana kwaɓe fuska

Murmushin Asma'u tayi tare da cewa.

“Toh naji”.


Daga nan sukaci gaba da hira.


Washe gari ranar jumma'a, misalin ƙarfe biyar dai-dai Khausar da ta shigo cikin gidan riƙe da hannun Raudat da alamun kitso ta kaita.

A bakin mashigar gidan nasu tayi kiciɓis da Amina da Samira sani, 


Sun iso bakin ƙofar a tare, dole sai ɗaya ya kaucewa ɗaya kafin a samu wurin wuce.

Wani  masiyacin kallo Samira ta cillawa Khausar tare da jan tsaki.

Ita kuwa Khausar tsuke fuska tayi cikin rashin shakka ko tsoro ta goga kafaɗarta da na Samira duk da kuwa Samira ta girmeta ainun.

Cikin izza Samira tace.

“Ke karere ki nitsu kisan da waye kikeyi”.

Ba tare da ta cire idanunta cikin nataba tace.

“Toh  dodon gori”.

Cikin fahimtar caguben baƙar mgnar da Khausar ɗin ta yaɓa mata wanda yafi abinda ta gaya mata ciwo, tace.

“Ke nifa uwarki zanci”.

Wani bauɗeɗɗen harara da dogon tsaki Khausar taja tare da cewa.

“Raudat mu tafi, kada mu tsaya muji, kukan tsuntsaye marasa tushe da gurbatacciyar tarbiya”.

Daga nan, ta juya tayi gaba.


Samira sani kuwa wani irin masifeffen kallo mai cike da tsana take Binta dashi.

Cikin takaici tace.

“Wallahi na tsani wannan yarinyar sam bana son ganinta, domin ta zame min madakatar nasarata".

Kwaffa Amina tayi tare da cewa.

“Bar shegiyar yarinya zanyi mgninta”.


Cikin tarin tsana Samira tace.

“Kune ma kuka bata dama ai, tana agola sai iyayi take muku, an wani dai-dai ta komai naku da nata, wai hatta makarantarku ɗaya da ita, ni wlh da nice ke sai na zuga Umma ta zuga Lamido tasa an cireta a wannan makarantar, shegiyar yarinya mai kama da ƴan ruwa.”

Kwaffa Amina tayi tare da cewa.

“Bar hegiyar yarinya, zanyi maganinta”.


Ita kuwa Khausar a falo suka samu Mamynsu kishingiɗe bisa carpet saƙale da wayarta a kunne, da alamu waya takeyi, ido ta zuba mata jin tana cewa.

“Eh Hajja Nana in Sha Allah, zata zo, don dama cikin azumi suna hutu to kuma rashin lfyar ne ya hanata zuwa, amman yau suka koma makaranta, kuma an ƙara musu hutun mako uku guda, sabida gyaran da akeyi a makarantar in Sha Allah zata zo, a satin nan,".

Sai kuma ta ɗan yi shiru, na wasu ƴan daƙiƙu, cikin sanyi da girmamawa tace.

“Eh gata nan ma”.

Tayi mgnar tana miƙawa Khausar wayar, cikin kwaɓe fuska kamar zatayi kuka ta amshi wayar tare da karawa a kunne murya ciki-ciki tace.

“Njam ɓanɗu.

Ina yini?".

Daga can kuwa cikin irin isa da kasaita ta tsofi masu iko Hajia Nana tace.

“Lafiyata lau, ki shirya kuna gama jarrabawar jarabar taku ta bokoko a wutan zakizo nan Jauro yaya inada buƙatar ganinki”.

Cikin sauri da alamun akwai zaunanniyar tsama a tsakaninsu tace.

“Toh ai muna da hadda yanzuma da aka ƙara mana hutun, kuma zamuna zuwa leson”.

A faɗace tace.

“Leso mato nace leso mato, ita haddar mu nan ɗin ce miki akayi garin kafuraine, kizo liman Sadu zai baki duk ilimin da kikeso in dai na addinine, na kafurcine dai bamu dashi”.

Cikin takaici tace.

“Nifa ki dena kafurta mana ilimin mu".

Cike da mamaki da al'ajabi Hajja Nana tayi wani dogon salati, tare da sanar da Ubangiji wai itace tana mgn ana bata amsa, ita da mgnar ta take tamkar wahayi a cikin rugarsu kasancewarta itace babba.

Da sauri ta katse kiran tare dasa wayar a Airplane mode,  ta kifeta gefenta sabida kada Mamynta ta gane.


Cikin yin rau-rau da ido tace.

“Mamy dan Allah kice mata tayi haƙuri sai ran babban sallah zanje muyi kwana biyu kafin a koma makaranta”.


Da sauri Momy ta fara jujjuya mata kai tare da cewa.

“Ban isaba Khausar ni dai kam bani da bakin yin taƙaddama da umarni Hajja Nana, ki kwana da sanin can zakije kiyi hutun nan, da kika samu ma bakije kinyi azumi a canba, tun tsawon shekaru takebi tana son hakan kuma bai samuba sabida uzurin da ita kanta ke fadarsa na zuwan ta Umara, bana kuma tace, saboda ke, bazata je Umrar ba, saboda tana so kije ki daɗe kisan yan uwanki su sanki.”

Cikin jan dogon numfashi tace.

“Mamy ni dai kin san ba shiri nakeyi da ita ba, ko zuwa nan tayi a wuni ɗaya sai tayi min masifa da sharri sama da sau biyar”.

Cikin haɗe fuska Mamy tace.

“Kuma dole kan umarnin ta da izininta mizanin muhallin zamanki  yake, ki fara shiri kawai ma in Allah ya kaimu gobe zan gayawa Abbanku, zuwa ranar jumma'a mai zuwa sai ki bisu in sunzo cin kasuwa kije RUGAR JAURO YAYAH tabbas d....!




Littafin SAKAYYAH na kuɗine biya ki karanta cikin Salamah yar uwa.



                        By

       *GARKUWAR MARUBUTA*

No comments

Powered by Blogger.