Sakayya 12

 


📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇


                   *SAKAYYAH*

                       _Page 12_


                             _NA_

             *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*Littafin SAKAYYAH na kuɗine wannan Free page ne ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 saura shafi huɗune kacal ana biyar na gama Free page*




Da sauri Modibbo ya rintse idanunsa, tare da shafa sajensa domin, badan glass dake tsakani ba da akan tattausan sajensa  sumbatar zata sauƙa.

Shi kuwa M Jameel cikin sauri ya lumshe idanunsa tare da gyara zamansa yana fuskantar  ta da kyau.

Ita kuwa Khausar hannu tasa tare da gyara zaman ɗaurin ɗan kwalinta, sai kuma ta canza Baitin da take ji zuwa.

 Waƙar Lamba tana marming tamkar zabia kai kace itace ta raira waƙar, bin baitukan takeyi tana jujjuya manyan idanunta, tana mai girgiza jikinta zuwa  ƙugunta.

lumshe manyan Idanunta kumayi tare da fitar da sautin zazzaƙar muryanta a fili ta tace.

“Kai zan yiwa kalamaina.

Kai zan baiwa muƙamai na. Ungo makullaina ka riƙe.

Ta ida bautin tare da nuna saitin fuskar Moddibo da yar yatsarta ma nuniya.

Wani irin shu'umin murmushi M Jameel ya sake tare da sa hannunsa ya riƙon hannun Moddibo da ya yunƙura zai ɓalle karfin motar.


Ita kuwa Khausar, cikin azama taci gaba da bin waƙar cike da zazzafan shauƙi tace.

“Ni ban furta da wasa ba, samari dukka basu kai ba, kana nan banganin kowa da ido, dan  basu isheni kalloba”.

Tayi mgnar bisa alamu daga ainihin cikin ranta take bin waƙar, M Jameel kam murmushi yakeyi cike da shauƙi.

Modibbo kuwa ya cika yayi fam dan har ransa yakeji yarinyar ta tarainashi gani yake kai tsaye ma dashi takeyi, gashi kuwa M Jameel ya riƙe masa hannunsa ƙam-ƙam.


Ita kuwa Khausar mazari uwar rawa, ƙugunta da ƙirjinta take motsawa a slowly tana mai ci gaba da cewa.

 “Kai zaka zauna adamana, kuma ka bani gurin kwana, wannan shine fassarar mafarkin da nake kullum cikin baccina”.

Wani irin yar-yar Moddibo yaji tsikar jikinsa na tashi domin suna jinta ras kasan cewar Glass ɗin bayan motar a suna ƙasa kaɗan.

Ita kuwa Khausar 

ida baitin tayi tana mai nuna Moddibo dake kwance jikin kujeran Idanunsa alumshe da yatsan hannunta tana murmushin dake ƙarawa fuskarta kyau.


Shi kuwa Moddibo Cikin fushi ya fuzge hannunsa daga riƙon da M Jameel yayi masa tare da sanya tattauaan tafin hannunsa da niyyan buɗe motar.

Shi kuwa M Jameel cikin sauri ya riƙe tafukan hannunsa da ƙarfi tare da girgiza masa kai alamar ya bari suga iya gudun ruwanta.


Ƙwafa Moddibo yayi tare da jingina bayansa da jikin kujeran ya cigaba da kallonta.

Ita kuwa rawanta ta cigaba dayi tana Girgiza jikinta ganin abin nata ba mai ƙare wa bane yasa Moddibo buɗe motar cike da tsananin  fusata.


Kamar walƙiya ko wanda ya diro daga sama haka taga Moddibo a gabanta,

Cikin tsoro, mamaki, da kiɗima  kalli fuskarsa cikin zare ido ta tayi ƙasa da kanta,

domin bata tsammaci  da mutum aciki ba.


 Shikuwa Moddibo cikin nutsuwarsa da kuma kamala ya fito daga motar tare da tsaida idanunsa akanta yana mai ƙara tsananta suƙe fuskarta da ya ƙara razanata.


Ita kuwa cikin tsananin ruɗu da tashin hankali mara misaltuwa ta ɗaura hannunta akai.

 tare da zubewa akan gwiwoyinta tana mai girgiza kanta gaba ɗaya ta gaza cewa komai.


M Jameel kuwa gefen Driver ya buɗe tare da fitowa yana dariya mai sassayan sauti,

dai-dai lokacin da Ummi da Asma'u suka fito  daga cikin gidan zuwa harabar gidan.

 Idanu Ummi ne suka sauƙa akan Moddibo da M Jameel kafin kuma ta maida ganinta kan Khausar dake durƙushe ta kama kai da hannunta duka biyu,

cike  da mamaki asaman fuskarta Ummu  tace.

“A'a ikon Allah Khausar lafiya ya dai haka!?”.

Kasa cewa komai Khausar tayi, still hannunta na kanta haka zalika ta kasa ɗago kanta banda bugawa da ƙarfi babu abinda zuciyarta keyi da ƙarfi.


Ganin Ummi da tambayar da take yiwa Khausar yasa Moddibo basarwa kamar baisan da ruwan ɗigon Khausar dake tsugunne gabansa ba,

cike da nutsuwa da kuma takun ƙasaita ya janye ƙafarsa da ya ɗaga da niyar zaiyi wasan ƙollo da Khausar ɗin yana mai maida fushinsa ya haɗiye ya juya ya nufi gaban Ummi.


Murmushi Ummi tayi Idanunta akan Moddibo tace.

“Sannun ku da zuwa  Babana, dama yanzu nake shirin zuwa unguwa  zanje duba jikin Maman Khausar”.

Ta ida mgnar ta maida kallonta kan Khausar da har zuwa yanzu take durƙushe sai dib dab dib dab da sautin zuciyarta ke badawa,  cikin kula tace.

“A'a Khausar yaushe kika zo? ya jikin Mommyn ki?”

Ita dai Khausar bata ɗago ba bare kuma ta motsa, gani take aduk lokacin da tayi kuskuren ɗaga kanta Moddibo zai iya kifeta da azabebben marinsan nan mai sa mutum ganin taurari masu wutsiya.

Cikin kula Ummi ta juya ta kalli Moddibo dake tsaye hannunsa na acikin aljihu  murmushi tayi kana tace.

“Allah yayi zaku zo ku sameni, kuzo mushiga daga ciki”.

Kai suka jinjina tare da wuceta, ita kuwa Ummi juyawa  tayi zuwa gaban Khausar ɗan tsugunna tayi tare da riƙo hannun Khausar tace.

“Duk cikin gaishe da Malama ne har haka Khausar? to taso mu tafi”.

Sai asannan Khausar ta ɗago kanta tare da sakin wani  nan-nauyan ajiyar zuciya, ganin Moddibo bai nan cikin mutuwar jiki tabi Ummi falon.

 Suna shiga Khausar tayi saurin janye hannunta daga cikin na Ummi, kana ta kama na Asma'u suka nufi Bedroom ɗinta”.


Suna shiga Bedroom ɗin Khausar ta janye hannunta daga na Asma'u ta zauna agefen gadon Idanunta cike da ruwan hawaye ta dafe ƙirjinta tare da cewa.

“Asma'u nashiga ukuna!nikam yau naga ta kaina, Allah yana jarabtana ta hanyar haɗani da Moddibo a bauɗaɗɗen yanayi,

zuwa na kenan naji wata waƙa tamin daɗi na tsaya ina bi uwa zabiya.

 Kuma kin sanima fa ni ban fiye jin waƙa ba, sannan bai dameni ba amma kawai ɗazu naji wata waƙa MP din Haiydar Wai ita Buga da Lamba kuma wallahi nasan Haiydar ne ya haxa min da bai bani aron MP ɗinsa ba ai da banjita ba bare inji yamin daɗi,  kawai na kama rawa tamkar yar gala,

ashe Moddibo na kallona nikam bansan irin hukuncin da zai minba gobe amakaranta, ƙilan ma ya sake sakani kaɗe ɗan kwali nikam nashiga Ukuna! Laifi kan laifi gashi gyale na yafa ga uban turaren dana zumbuɗa ga rawa dajin waƙa Wayyo ni Batula Faɗimatuzzahara naga ta kaina!”.


Ta gumi Asma'u tayi tare da kallon, Khausar da tayi narai-narai da ido kana tace.

“Ke kam dai Khausar kamar saɓani Allah yake haɗaki dashi”.

Narai-narai tayi da ido tare da dafe kuncinta da hannun biyu kana tace.

“Mummunan saɓani ma kuwa, na sharri ma ya Allah kashiga tsakanin na gari da mugu, Allah kara bani dashi ya Allah kada ka bashi ikon zalunta na, tun da dai arashin sani nayi kuma babu wanda yafi ƙarfin kuskure ai seya min uzuri ko?”.


Janye mata tagumin Asma'u tayi tana dariya tace.

“Kece Khausar wani zubin sai ahankali, kawai daga zuwa saiki hau rawa kamar mazari da anyi magana ki wani ce Allah yashiga tsakanin na gari da mugu sannan da kike maganar uzuri a'a ba'asi za amiki ba uzuri ba kuma waye mugun waye na garin”.


Sheƙeƙe Khausar ta ɗago kai tare da tsirawa Asma'u Idanu kana tace.

“Nifa na lura dake tun ba yanzu ba, kinfi ƙaunar Moddibo dani wato har kina goyon bayan sa akan ni kin zaɓe sa kin barni? Yoh shine mugu mana ni ta gari”.

Ware idanu Asma'u tayi tare da langwaɓar da kai tana dariya tace.

“Haba ƙawar arziƙi matsayinki yafi haka, dan Allah kada ki sake faɗan hakan aise kisa ayimina dariya”.


Taɓe baki Khausar tayi tare da faɗin.

“Kinsan gwara in gane matsayina ai tun wurima,

idan kinfi ƙaunar Moddibo insan matsayina”.

Dariya mai sauti Asma'u tayi da faɗin.

“Maida wuƙar ranki shi daɗe Fattanah”.

Murmushi Khausar tayi tare da kishingiɗa akan gadon.


Acan falo kuwa bayan Moddibo da M Jameel sun sake gaisawa da Ummi ta miƙe tashiga kichen ba daɗewa ta fito hannunta riƙe da babban tray dake ɗauke da Warmers ta ajiye musu.

Murmushi Moddibo yayi yace.

“Sannu da gajiya Ummi”.

Murmushi tayi tace.

“Yawwa Babana”.

M Jameel kuwa miƙewa yayi yashiga kichen ya dauko musu Plate da cups guda biyu kana ya dawo ya zauna.

Kulan ya buɗe, da sauri ya gyara zamansa jin wani ƙamshi mai daɗin ya ratsa hancinsu.

M Jameel ya lumshe ido tare da zuba musu akan Plate.

Moddibo ya matso tare da tsirawa Pride rice ɗin da yaji vegetables da naman kaza amsar spoon ɗin da M Jameel ke miƙa masa yayi, cikin fesar da numfashi Moddibo ya ɗibi abincin ya kai bakinsa, lokaci ɗaya yaji daɗi ya mamaye masa baki, kallon Ummi yayi tare da faɗin.

“Ummi wannan girkin yayi daɗi”.

murmushi tayi tare da tsiyaya musu tea mai ɗumi.


Bayan sun gama ci.

M Jameel ya goge bakinsa da tissue kana yace.

“Ummi ɗazun ina zakije dama?”.

Tana matsar da Flaks ɗin tea tace.

“Wallahi Maman Khausar zanje dubawa, bata da lafiya shekaran jiya a asibiti suka kwana jiya ne aka sallame su da safe”.


Girgiza kai yayu kana yace.

“Ayyah Subhanallah Allah yabata lafiya Allah yasa zakkan jikine”.

Amin Ummu tace.

Yayinda  shi kuwa Moddibo Aransa yace. “Uhhhm yarinyar kamar aljana ita da mahaifiyar ta babu lafiya har ankwantar da ita a asibiti jiya-jiya aka sallame su, amma yau har ta gararo yawo, har tana rawa agidan mutane kamar wacce aka yiwa bushara da Aljanna, ita kuwa wannan daɗin me takeji”. sai kuma ya taɓe baki takaicin halayyar yarinya yasa bece musu komai amaganar ba.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin.

“Toh Ummi mu zamu tafi”.

Ummi ta juya ta kallesa da murmushi afuskarta tace.

“Da wuri haka Babana?”.

M Jameel ne yace.

“Ai dama a gaggauce muka zo Ummi, dan kwana biyun nan naga ya maida hankalinsa akan rubutun da yake inagama ya kusan gamawa”.


Ummi kuwa kallonta ta mayar kan Moddibo kana tace.

“Masha Allah Ubangiji Allah ya taimaka, ya kuma baku sa'a ka kusa gama wa kenan?”.

Cike da nitsuwa Moddibo ya amsa da.

“Ameen”,Kana yace.

“Eh Ummi na kusa gamawa, amma waɗan da na tura ƙasar Ɓadamaya ma tukunna wanda na turawa, Sheykh Jabeer ya duba min su har yau basu dawo ba, to inaso kawai na haɗa wa'annan ma dake wancan bugun Hafs ne wannan kuma Warash ne”.

Yai da mgnar tare  sauƙe numfashi kana ya cigaba da cewa.

Warash ne nake rubuta wa to inaso idan nagama rubuta wannan ɗin na tura masa, wala Allah ya tuna mishi da duba wancan ɗin.

Nasani abubuwa ne suka masa yawa da yake ya wanci yakin arewacin nan duk wanda ya rubuta Kur'ani shi ya ake turawa sai ya duba yagani toh zanyi ƙoƙari na gama rubuta wannan ɗin sai ahaɗa akai gaba ɗaya ko zan samu ya haɗa min su lokaci ɗaya idan ya duba ingancin su”.


Jinjina kai Ummu tayi cike da yabawa jajurcewarsa da kuma ƙoƙarin sa tace.

“Masha Allah Allah yatemaka  Allah ya bada sa'a abu yayi kyau Allah yabar mana irinku Moddibo Allah yayi jagora”.


Moddibo kuwa cikin jin daɗin addu'ar ta yace.

“Ameen Ummi Allah ya amsa Nagode”.

Miƙewa M Jameel yayi idanunsa akan Ummin sa yace.

“Ummi zamu tafi”.

Tana ƙoƙarin kwashe Plate da sukayi amfani dashi tace.

“Toh Nagode Allah ya muku albarka”.

Suka haɗa baki wajen faɗin.

“Ameen”.

kana suka fice.


Bayan sun ɗauki hanya M Jameel ya dubi Moddibo wanda shike Driving ɗin yanzu yace.

“Ni ka sauƙe ni agida”.

Moddibo da still hankalin sa ke kan Driving yace.

“Ba zamu tafi tare ba?”.

Girgiza kai M Jameel yayi kana yace.

“A'a nasan rubuta zaka je kayi sannan Abba ya kirani akan batun yana so naje Ɓadamaye batun Company sa akwai sabbin Injina da aka kawo, za'a saka kaga na daɗe ban jeba, amma wannan karon ko naje baze wuce kwana biyu zanyi in dawo ba”.


Moddibo kuwa jinjina kai yayi kana yace.

“Toh yaushene tafiyar?”.

Kai M Jameel ya Girgiza tare da faɗin.

“Toh dai ban sani ba tukun”.

Moddibo dake ƙoƙarin shan kwana yace.

“Yawwa zanyi ƙoƙari inga na gama rubutunan idan zaka tafi sai ka tafi min dashi”.


Shi kuwa M Jameel Kai ya gyaɗa cike da gamsuwa da maganarsa yace.

“Toh shikenan hakan ma yayi Allah yatemaka”.

Moddibo ya amsa da.

“Ameen”,tare da parking motar bayan ya isa ƙofar gidan su M Jameel.

Sauƙa M Jameel yayi tare da yi masa sai anjima, kai Moddibo ya gyaɗa kana yaja motar ya tafi.


Yana isa gida bayan yayi Parking motarsa ya wuce Bedroom ɗinsa kasancewar yana da alwala yasa ya ɗauko abubuwan buƙatar sa na rubun Alkur'ani da yakeyu kana yaciigaba da rubutu, saida aka kira sallar La'asar sannan ya tashi yaje masallaci ya gabatar da sallan la'asar, bayan ya dawo kuma, yazo ya cigaba da rubutun, yana yi yana karantar Suratul Kahfi  kasancewar yammacin jumma'a ne, sai misalin ƙarfe biyar kafin ya ajiye Kur'ani.


Acan ɓangaren Innayi kuwa zaune take akan kujera ’yar tsugunno acikin kichen tana juya miyar zogala wanda yaji namar Rago da kuma wadataccen man Shanu da wake yana tashin ƙamshi bayan ta sauƙe miyar ta ɗaura Ruwan shayi daya ji na'ana, kaninfari da kuma ɗanyan citta yana tafasowa yana ƙamashi mai daɗin shaka.

 Flaks guda biyu ta ɗauka ta juye sannan ta ɗauki ɗaya ta nufi sashen Moddibo dashi.


Acan gidansu Asma'u kuwa bayan tafiyar Moddibo da M Jameel Khausar ta miƙe tare da fitowa falon Idanunta akan Ummi tace.

“Toh Ummi mu tafi ba dama kince gidan mu zaki jeba”.

Jinjina kai Ummi tayi tace.

“Eh Khausar inaso naje na duba jikin Mommyn ki”.

Ba tare data zauna ba tace.

“Toh Ummi mu tafi”.

Kai Ummi ta jinjina kana ta miƙe suka fita su ukun Bashir ƙanin Asma'u ne kaɗai suka bari agida Ummi da kanta take Driving Khausar da Asma'u na baya suna hira.


Acan ɓangaren su Hajiya Bunayya kuwa Kallonsu Boka Kar'uzu yayi cikin wata razananniyar tsawa yace.

“Wannan maganin ya riga daya ɓaci, ta lalata komai yanzu sai anyi aikin dai-dai-ta fuskarta ma tukunna kafin azo ayi aikin jawo hankalinsa, yaran nan biyu da kuka gani kuke magana akansu yarane dasu na tsaye da sunan Allah da riƙo da Ibada, musamman ma Moddibo  da kuke magana akansa kwata-kwata baya rabuwa da alwala ajikinsa ka masa zaiyi wuya”.

Cikin tashin hankali Hajiya Bunayya ta juya ta kalli Hajiya Lami da duk tagama shiga ruɗu.


Boka Kar'uzu kuwa cigaba yayi  da cewa.

“Yanzu sai munyi aikin wata uku kafin fuskarta ya dawo dai-dai sannan sai tabar Sallah na tsawon watanni shida kafin mu samu mu fara aiki shiko aikin za'ayi na tsawon watanni shida kafin ta fara nuna masa muradanta”.

Kana ya maida kallonsa ga Hajiya Lami data zabga uban tagumin tana kallon sa cikin Muryansa Mara daɗin Amo yace.

“Kema naki hakanne sai tayi wannan watannin”.

Dafe ƙirji Hajiya Lami tayi tare da zare Ido kana tace.

“Har Watanni shida shida Boka kafin wannan lokacin fa har sun kusa gama Ss 2 ma zasu tafi 3 awannan lokacin daka ɗiba mana”.

Cikin tsawa da hargagi yace.

“Dole sai anbi wannan ƙa'ida idan ba haka ba babu abinda zaku samu ya tafi dai-dai!”.


Ta gumi Hajiya Lami ta rafka kana tace.

“Shikenan Babu damuwa Indai burinmu zai cika tunda ai makarantar basu gama ba zamu bi ahankali”.

Ya yamutse fuska tare da watsa musu wani kallo da jajayen Idanunsa cikin wata murya mara daɗin Amo yace.

“Ƙa'idah ne yanzu zata je tayi ta aiki da wannan maganin na tsawon watanni ukku fuskarta zai koma dai-dai a Idanunsa sannan bayan wannan kuma tsawon watanni kar kuyi sallah daga nan kuma zan fara haɗa magani na tsawon watanni shida kafin su tun kare su daga magana”.


Murmushin Hajiya Bunayya tayi tare da gyara zamanta tana fuskantar Boka Kar'uzu da kyau tace.

“Toh shikenan ba matsala. 

Amma fa ciki ya zube aiki yayi kyau!”.

Wani irin mahaukaciyar dariya mai matuƙar razanarwa Boka Kar'uzu ya saki da faɗin.

“Ai dama dole aiki zaiyi kyau idan kun bishi da ƙa'ida wannan ma ku kuka je kuka ɓatashi!”.


Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.

“Godiya muke Boka ana gaba zamu kiyaye”.

Kai ta gyaɗa kana yace.

“Toh ya batun aikin toshe mahaifar!?”.

Kai Hajiya Bunayya ta Girgiza tare da faɗin.

“Boka muga ma da batun aikin Amina tukunna, kaga ga yayar ta ma tana zaune ba tayi aure ba, sannan ga itama Aminan ta girma shiru, amma ita kace rabonta ne yayi nisa abin ya ɗaure mana kai mun rasa yanda zamuyi har wajen ƙan wata na tura ta Aƙasar Khautal ko zata samu rabonta acan amma acan ɗin ma shiru kuma kaga ta dade da gama karatu amma  har yau Auren bai samu ba zamu jona mata wani makarantar ta fara zuwa jami'a kawai, tunda itama kanta Amina dan wasa da karatun take da tayi shekaru biyu da gamawa amman sai aikin maimaita aji gashi har shegiyar yarinyar nan ta kusan cimmata”.



Kai Boka Kar'uzu ya ɗago daga bugun ƙasar da yake tare da cewa.

“Babu matsala ita Aseeya rabonta yana nan tafe”.

Cike da jin daɗi Hajiya Bunayya tace.

“Godiya muke Boka Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu Mugu Uban mugaye Hatsabibi Uban Hatsabibai!”.


Wata mahaukaciyar dariya Boka Kar'uzu ya kece dashi cikin jin daɗin kirarin da ta masa yace.

“Aikin ki zai tabbata ƙaramar la'ananniya  Aljani ɗan ƙundalu mai ido Atsakiyar kai zai cika miki burinki ku fita da ƙafar hagu ta baya!”.

Miƙewa sukayi suka fice kamar yanda ya faɗa ransu fesss suna tsalle da kafar hagu kamar kutaren agwagi...


Acan ɓangaren su Ummi kuwa bayan sun isa gidan su Khausar sun gama gaisawa da Mommy da kuma Hajiya Ruƙayya da har zuwa lokacin suke tare.

Mommy tana murmushin tace.

“Ummi ya fama rigimar Khausar, ɗazun nan tace zata je ta duba ki ashe kina hanya”.

Dariya Ummi tayi tace.

“Ai lalle dai kam Hajiya Aysha babu ruwan Khausar ai”.

Murmushi Mommy tayi tace.

“Kina dai karate ta Amma Khausar ba dai rigima ba?".

Aunty Ruƙayya tayi Dariya kana tace.

“Ai Khausar bata da rigima ita dai baza'ayi gulma agaban Idanunta bane, sannan ba za'a cakake ta ta haƙura ba, kunga kuwa ai da gaskiyar ta”.

Dariya Ummi tayi tace.

“Aikam de lalle da gaskiyar ta”.

Ita kuwa Mommy Dariya tayi kana suka cigaba da hira.


Washe gari Asabar suka koma makaranta Khausar kuwa cikin tsoro da fargaban abinda Moddibo zai mata ta zuciyarta ya riƙa bugawa da ƙarfi lokacin da yashigo raba musu questions pepar  tayi zaton zai mata hukunci sai taga baima kalli inda take ba.

 Shikuwa Moddibo kawai ya fita sabgarta ne ganin alamar bata da cikikakkiyar nutsuwa in ya biyata zata zarar dashi.


Akwana atashi haka al'amura suka cigaba da tafiya komai yana wakana Moddibo ya kammala rubutun Kur'aninsa ya bawa M Jameel ya tafi wa da Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Joɗa na Adamawa.

 Satin M Jameel biyu ya dawo tare da shedawa Moddibo ya karɓa harma ya fara dubuwa Insha Allah nan kusa zai turo masa.

Karatun su Khausar na tafiya komai na tafiya dai-dai yanda ake buƙata Anyi gasar musabaƙa jihar Taraba Makarantarsu Khausar Al'ansar Academic school_ shine yazo na farko Khausar ce tazo na ɗaya a haddar Izu arba'in yayin da Asma'u tazo na biyu Aishatu Abdullahi tazo na uku ,A haddar Izu biyar Raudat ce tazo na ɗaya kyaututtuka masu yawa suka samu kana suka dawo cike da nasarori.


Yanzu karatu na tafiya akwana atashi babu wuya wasa gaske yanzu Khausar suna Ss2 

thirth term suna shirye shiryen fara Exam gashi kuma Ramadan ya kawo kai yayin da ake ta shirye shiryen shiga Ramadan tuni Gwamnatin Jaha ta rarraba malamai zuwa inda ko wanne zaiyi Tafseer kamar yanda aka saba Moddibo da M Jameel antura su Babban Masallacin juma'a dake ƙofar sarki Gembu anan zasuyi Tafseer ɗin su na Ramadan.

Lokaci natafiya karatun su Khausar na sake tafiya yanda ake buƙata tsakanin Amina da Khausar babu wani jituwa hasalima gaba ce domin har gobe M Jameel na sake nuna kulawa ta musamman akan Khausar yayinda Moddibo kuwa kwata-kwata baya lura da al'amuran Khausar hasalima idan tayi laifi zai yanke mata hukunci fiye dana kowa wannan dalili yasa basa shiri kana babu wata jituwa atsakaninsu.


Alhamdulillah ayaune Khausar suka rubuta exam na ƙarshe kuma da Geography suka rufe.

Taro Moddibo yasa aka haɗa kamar yanda aka saba a kowani ƙarshen hutu ko baki ɗaya Malaman sun haɗu awajen zamansu haka ma ɗalibai Khausar da Asma'u na zaune awaje ɗaya.


Shi kuwa Moddibo cikin nutsuwarsa da kuma kamala ya nufo wajen as usual cikin shigar sa kaman ko yaushe sanye yake cikin Jallabiya fari kansa naɗe da hirami idanunsa sanye da ɗan siririn farin glass daya ƙawata kyawun fuskarsa yalwataccen sajensa  zuwa gemunsa ya kwanta luf-luf yana sheƙi.

Cikin tsantsar nutsuwa da sanin darajar kansa ya gyara zaman microphone ɗin tare da hura iska kaɗan kana yayi gyaran murya yace.

_“Bismillahir Rahmanir Rahim, Innalhamdulillah nahmaduhu wanasta'inuhu wanastaghfiru wa'nazubillahi min shururi anfusna wamin sayyi ati a'amalina, man yahdillahu fala mudillahlah waman yudlil fala hadiyala, Wa'ash hadu Allah ilahalillahu,  Wa'ash hadu anna Muhammadu Abduhu wa Rasulullah (S.A.W)”._


Sai kuma ya ɗan lumshe idanunsa tare da sauƙe Ajiyar zuciya kana ya cigaba da cewa.

“Duk kan yabo da godiya su tabbata ga Allah subhanahu wata'ala mai kowa mai komai, da yakawo mu wannan lokaci da muke shirin karɓan hutu saboda gabatowan wannan wata mai falala, haƙiƙa watan Ramadan wata ne mai falala da rahma wanda duk kan musulmi yake da burin ganinsa.

 

Baki ɗaya wajen shiru yayi kowa ya maida nutsuwarsa zuwa garesa yayin da Samira kejin aduk lokacin data mallakesa babu macen da takaita sa'a a faɗin wannan duniya tamu ta bani adam.

 Malam Arɗo kuwa Aransa yake jin Moddibo ne Garkuwa kuma ginshiƙin makarantarsa.

Moddibo kuwa cikin yanayin sanyin Muryar sa mai cike da nutsuwa ya cigaba da cewa.

“An abu Huraira ta radiyallahu anhu,

_Manƙama Ramada Imanan Wahtisaban gufra lahu mata ƙaddama min zambi muttafaƙun Alaik”_


Ma'ana ankarbo daga Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda, yana cewa Duk wanda watan Ramadana ya kama yana mai Imani da kyautatawa ana kankare masa zunubansa da suka gabata”.


 Ya sauƙe sanyayyar Ajiyar zuciya mai sanyi kana ya cigaba cewa.

“Wannan kaɗai zai iya nuna maka muhimmanci da kuma darajar wannan wata hakika wannan watar ba wata bane na wasa watane daya kamata mu tsaya mu miƙa lamuranmu ga Ubangiji Mabuwayi gagara Misali, sannan mukasance masu yawan Karatun Alkur'ani, Istigfari, hailala da kuma tasbihi, ba sai na tsawaita ba ko naja duk abinda zance kun sani”.

Sai kuma ya maida kallonsa ga sauran Malaman yace.

“Koda akwai mai magana?”.


Duk suka girgiza kai alamar babu Moddibo kuwa M Jameel ya miƙawa microphone ɗin kana ya koma ya zauna shi kuwa M Jameel bayanai ya ƙara akan na Moddibo kana ya sanar dasu Bayan Sallah da sati ɗaya zasu dawo.

Yana gama Maganar ya juya tare da kallon Khausar da ita adai-dai lokacin Idanunta na kasansa cikin Sanyayyar Murya yace.

“Lelewal zoki rufe mana  da addu'a!”.

Anutse Khausar ta gyaɗa kai tare da miƙewa.

Shikuwa Moddibo kallon mamaki yabin M Jameel dashi amma baice komai ba.

Amina kuwa jitayi tamkar zuciyarta zai buga saboda baƙin ciki da kishi.

Ita kuwa Khausar cike da tsoron Modibbo dake sa ta nemo nutsuwa ta amshi microphone ɗin cikin zazzaƙan Muryanta tayi addu'a kana aka tashi kowa ya watse dalibai nata murnan hutu kowa ya koma gidansu cike da farin ciki.


Da daddare Khausar na zaune akan 1sitter hannunta riƙe da wayar Mommy yayin da Mommy kekan 3sitter ta miƙe ƙafafunta Hannunta riƙe da kofin tea.

Anutse Mommy ta ɗago kanta tare da sauƙe Idanunta dake kan Khausar Wacce baki ɗaya hankalinta ke kan wayar da take dannawa ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

“Khausar tunda an baku hutu ko dai za kije Jauro Yaya kuyi azumi tare".

Da sauri Khausar  ta ajiye wayarta tare dasa hannu ta dafe ƙirjinta tace.

“Nashiga Ukuna! Dan Allah dan darajar Annabi Mommy Kar kiyi Wannan maganar, kibar tsohuwar nan tunda dai bata ne maba”.


Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.

“Toh shikenan yanzu azumi saura sati amma nasan zaiyi wuya acikin satin nan idan bata neme kiba”.

Marerece fuska Khausar tayi kana tace.

“Allah yasa karma ta nemeni duk da garin yamin daɗi Mommy amma inaso in tayaki aiki”.

Murmushi Mommy tayi kana tace.

“Toh shikenan ba matsala hakan ma Allah ya zaɓa Mana abinda yafi zama alkhairi”.


Acan ɓangaren su Hajiya Lami kuwa zaune take afalon Hajiya Bunayya tare da Samira Sani da kuma Amina.

Kallon Hajiya Lami Hajiya Bunayya tayi kana tace.

“Yanzu dai saura mana watanni biyu mu gama cika Umarnin Boka Kar'uzu na watanni shida daya ɗiba mana kada muyi Sallah, kafin na ƙarshe da zamuyi muje mu karɓi maganin su zo suyi aiki dashi”.

Murmushi Hajiya Lami tayi tare da jinjina kai tace.

“Eh haka ne bayan Sallah da sati Uku zamu gama”.

Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.

“Gashi kuma azumi ya gabato amma acikin wannan azumin ma ace ba zamuyi sallah ba kuma watan falala da ibada!?”.


Wani kallo Hajiya Lami tayi mata kana tace.

“Idan ke zakiyi sallah ki ɓata aikin da kikayi to kinyi na wancan watannin shida da kika samo fuskar ’yar ki ya dawo dai-dai a idanunsa, sannan yanzu wata ɗaya da rabi daya rage ne zaki ɓata ba zaki iya jira ba. Agaskiya nikam zan cika ƙa'idata domin in samu cikar burin ‘yata”.


Samira kuwa zama ta gyara tana fuskantar Hajiya Bunayya da kyau tace.

“Agaskiya Ummah kar muyi wasa da wannan damar da muka samu idan yaso idan muka gama sai mu rama bashin sallah dake kan mu!”.


Ita kuwa Amina Kallon mahaifiyarta tayi tare da ƙanƙance Idanu kana tace.

“Yanzu ke Ummah wasa zakiyi da wannan damar da muka sha wahala tsawon watanni muna yi!?”.

Zare ido Hajiya Bunayya tayi tare da nuna kanta da yatsa tace.

“Ina waya faɗa miki ko an faɗa miki daɗi nake ji ga yayarki azaune gaki kuma kema azaune”.

Ta ida maganar dai-dai lokacin da Asiya ta fito daga Bedroom bayan ta gama sauraron duk abinda suke faɗa zama tayi akan 1 sitter dake fuskantar Hajiya Bunayya cikin sanyin murya tace.

“Gaskiya Ummah!, Gaskiya Ummah!! Kada neman duniya yasa mu rasa ƙiyama tare da rahamar Ubangiji, Ummah sallah da arayuwar duniya itace farkon abinda za'a bin ciki mutum dashi aranan gobe hisabi idan tayi kyau abin cika sauran abubuwa idan kuma ba tayi kyauba, baza ma aje ga sauran abubuwan ba”.

Tayi ƙasa da Idanunta ganin shegen kallonda Umman take bin ta dashi bata damu ba ta cigaba da cewa.

“Ummah aduniya Allah ya Umarceki da kiyi sallah da Azumi amma Boka La'anannen yace kada kiyi, sannan ki biye masa har ki yarda sannan ki riƙa ɗaura ‘yarki akan gurɓatacciyar hanya nikam wannan al'amari yana tayar min da hankali, wannan al'amarin sam bai yi ba yanzu dama akan wannan turban kuke tafiya?”.

Ta saki Ajiyar zuciya tare da gyara zamanta kana tana ƙoƙarin maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata cikin dauriya ta cigaba da cewa.

“Shiyasa tun da na dawo sati biyu banga kinyi alwala ko Sallah ba?, Ni nayi zaton ma al'ada kike yi,Itama Amina naga bata sallah dana tambayeta saita kama yimin rashin kunya”.


Amina dake jifanta da mugun hararane tayi saurin katseta tare da cewa.

“Anyi miki rashin kunyar keda ba kyabin Ƙa'ida da Umarnin Bokan baga ki har yanzu baki auru ba!sai shegen iyayi da kwainane!”.


Asiya da Idanunta suka ciko da ruwan hawaye ta kalli ƙanwar nata cike da mamaki sai kuma tayi murmushi mai ciwo tace.

“Wannan Allah ne bai nufaba, idan Allah ya saƙƙo da lokaci zanyi shi domin Aure da mutuwa lokacine”.

Atsawace Hajiya Bunayya tace.

“Rufe min baki, keda ma can ba'a haɗa shiri dake ya tafi dai-dai, dama ke da magautana kike tare kina nan kamar wancan matar ce ta haifeki”.


Asiya ta danne kukan dake neman kufce mata tace.

“Ba haka bane Ummah zanso mu gudu tare mu tsira tare ne, bazan so ganin ku cikin halaka ba Umma kuyi tunani akan wannan rayuwar da kuka jefa kanku".


Hajiya Lami kuwa cikin fushi tace.

“Wannan dai akwai gantalelliyar yarinya shegiya mai shegen mugun halin jaraba, duk yanda akayi wancan gafalalliyar kishiyar Uwar taki ta baki nononta kinsha”.

Kallonsu kawai Asiya keyi cike da mamaki.


Hajiya Bunayya kuwa Afusace tace.

“Bana son gaskiyar taki ki riƙe abarki.

 ki gudu ke kaɗai mu ma mu gudu mu kaɗai kiga wanda zai riga isa tsakanin mu da ke”.

Cikin tsananin tashin hankali Asiya tace.

“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n.

 Allahumma Ajirni fi musibati wa'ahlif khairan minha”.

Ta ida addu'ar tare da miƙewa ta shiga Bedroom ɗin su akan gado ta faɗa tare da dafe kanta tace wannan wani irin Masifa ce Ummah ta jefa kanta.


Acan falo kuwa Ummah suka cigaba da tattaunawa tare da tsaida matsaya akan idan sun kammala aiki zasu biya Sallolin da ake binsu.


Washe gari.

Da hantsi misalin 12:00 Khausar na kwance A Bedroom kamar daga sama tajiyo Sallamar Hajja Nana da sauri ta miƙe tare da zama Atsakiyar gadon ta kasa kunnenta dan tabbatar wa shin ita ɗin ce ko kuwa.

Aikuwa Muryan Mommyn ta taji tana cewa.

“A'a Hajjar Allah Maraba sannu da zuwa Allah raine Jaɓɓama,Jaɓɓama Yottu,yottu”.

Ita kuwa Khausar wani irin zare ido tayi sai kuma ta miƙe da sauri ta fito abakin Bedroom din ta tsaya Idanunta akan Hajja Nana da Dije dake tsaye agefenta.


Jan zuciya Khausar tayi tare da tsaida idanunta akan Hajja Nana tace.

“Kece?”.

Harara Hajja Nana ta watsa mata da faɗin.

“Toh ki koreni wato ba kyason ganina!?”.

Tura baki Khausar tayi tace.

“A'a".

Sai kuma ta juya tare da kallon Dije dake tsaye tana kallon falon da dugu ta nufi Dije tana cewa.

“Oyoyoo Dije nayi kewarki ya gida ya Goggo Nanne?,Ya Yaya Abba?,Ina Sadik?, Yasu Baffa Jauro?, Baffa Sadu?,Baffa Liman?, Baffa Garga? Ina Bishiyar Ƙare zencen ka ina Rafi?”.


Murmushi Dije tayi kana tace.

“Duk suna lafiya kuma sunce agaisheki da kyau da kyau”.

Tayi murmushi tace.

“Allah sarki nima nayi kewarsu sosai”.


Cikin sakin fuska Mommy ta fito daga kichen hannunta riƙe da Flaks da kuma kofi biyu ajiyew tayi, kana ta koma ta ɗauko fruits duk ta ajiye agaban Hajja Nana data hakimce akan kujera sannan ta zauna still fuskarta da Murmushin daya kasa ɓoyuwa tace.

“Sannu Hajja kunsha hanya ya mutanen gida?”

Ta ida maganar tana tsiyaya mata Tea a kofi.

Amsa Hajja Nana tayi ta kai bakinta.

Mommy kuwa miƙewa tayi ta shiga kichen dan haɗa mata abinci.


Hajja Nana kuwa juyawa tayi tare da kallon Khausar dake maƙale da Dije kana tace.

“Wato ba zaki gaisheni ba, Dije ce kikayi farin cikin  ganinta ni bakiyi farin ciki da ganina bako!?”.


Ya mutse fuska Khausar tayi tace.

“Tun ɗazu nake ta gaisheki kina fama da ciye-ciye baki jini ba”.

Sake baki Hajja Nana tayi tare da riƙe haɓa sai kuma tace.

“Ubanki nake baciye-ciye ba” 

Hannu Khausar ta buɗe da faɗin.

“Ɗanki kika zaga dama kin barsa ya kwanta cikin kabarinsa acikin salama da yafi”.

Ta ida mgnar idonta na ciko da hawaye dan Allah ya sani bata son a zagar mata mahaifi.

Hajja Nana ta ajiye Kofin shayin dake hannunta ta nuna Khausar da hannu tace.

“Ki kiyaye nifa,Ki kiyayeni fa Khausar”.

Tura baki Khausar tayi kana tace.

“To ai gaskiya na faɗa”.


Ita kuwa Hajja Nana na ɗaukar kofin shayinta tace.

“To ya miki kyau koma mene ki ƙarata can, yanzu kishirya ki haɗa kayanki tare zamu tafi zamu je muyi azumi acan”.

Kallonta Khausar tayi kana tace.

“Mu tafi ina?”.

Hajja Nana tace.

“Eh mana Khausar mu tafi Jauro Yaya”.


Da sauri Khausar ta maida kallonta gareta kana tace.

“To ai muna zuwa hadda”.

Hajja Nana tace.

“To ai wannan ba abin damuwa bane idan muka je sai Malam Liman ya riƙa ƙara miki”.


Kai Khausar ta girgiza kana tace.

“Baza ki gane bane, inada abubuwan da zanyiwa Mamana ɗin nan da kike gani ina taya ta aiki”.


Hararanta Hajja Nana tayi da faɗin.

“Dama kece mai taya ta aikin ina masu taya ta aikin?”.

Zare ido Khausar tayi kana tace.

“Tayi cikin shege ankoreta ta koma ƙauyensu.

 Mai gadin muma ana canza shi saboda shi ya mata ciki”.

Da mamaki Hajja Nana tace.

“Ash'sha Subhanallahi ashe gidan naku babu tsaro kenan, ashe ku gidan bayan maita hadda rashin tsaro a'a maza-maza shirya mu tafi”.

Dai-dai lokacin da Mommy ta fito girgiza kai tayi tace.

“Kai Khausar bakyajin magana maza ki ɗauka wa Dije abinci ku wuce ɗakin ki”.


Kai Khausar ta gyaɗa tare da wucewa kichen ta daukawa Dije abincin sannan suka wuce Bedroom ɗin.

Mommy kuwa zama tayi agefen Hajja Nana tare da ajiye mata tiren abinci cikin sanyin murya tace.

“Hajja Nana kiyi haƙuri da halin Khausar zaku tafi idan hakan kike so”.

Kai Hajja Nana ta gyaɗa kana tace.

“Toh babu damuwa amma tace min baki da lafiya da gaske ne?”.


Kai Mommy ta Jinjina kana tace.

“Eh wallahi kwanakin nan duka ban cika jin daɗi ba bansan meke damuna ba!”.

Jinjina kai Hajja Nana tayi kana tace.

“Subhanallah Allah ya sawwaƙa Allah ya yaye.

Kuma da gaske ne mai aikin ku ta haihu cikin shege?".


Dai-dai lokacin Hajiya Bunayya da Amina suka shigo falon.

Ɗaga kai Mommy tayi tare da kallon Hajiya Bunayya data zauna tace.

“Hajiya ga Kakar Khausar”.

Murmushi Hajiya Bunayya tayi Idanunta akan Khausar tace.

“Ai na ganeta Hajja Nana sannu da zuwa ina yini ya gajiya kunzo lafiya?”.


Ita kuwa Amina batare data ƙarasa shiga falon ba ta ɗaga sautin Muryanta da faɗin.

“Khausar!, Khausar!! Khausar!!!,”.

Daga ciki Khausar tace.

“Me?".

Afusace Amina tace.

“Bana son rashin kunya ni zaki yiwa rashin kunya? ina kiranki kina jina ba zaki fito ba aikin san dai tunda na kira ki ina da ɓuƙatar ki!”.

Jin surutan da take yasa Khausar ta fito tare da tsayawa daga bakin ƙofa ta riƙe ƙugunta kana tace.

“To ai tunda ke kike da ɓuƙatata kinsan inda dakina yake sai ki shiga ki sameni”.


Cike da kirsa Hajiya Bunayya tayi dariya tana kallon Khausar tace.

“Kudai in Kun hadu bakwa rabuwa da faɗa kamar wasu ƙananun yara Allah dai ya kawo muku sauƙi kuna na  kamar wuta da Auduga”.

Juyawa Hajja Nana tayi ta kalli Khausar da Amina kana ta taɓe baki tare da cewa.

“To ai kinsan haka al'amarin yake, mu zuriyarmu  bama gani mu ƙyale sannan bama ji muyi shiru, sannan su kuma mayu haka suke basason mai baki shiyasa baza'ayi shiri ba”.

Hajiya Bunayya tayi saurin cewa.

“Hmmm Hajiya ai tsatsonne na mayu su basu tsotsaba dan mu atsarkake muke”.

Kallon mamaki Mommy tayi mata kana tace.

“Hajiya har ke kin yarda da kalmar kenan?”.

Hajiya Bunayya ta taɓe baki kana tace.

“Ha'a abinda ake faɗa musu acikin gari mun isa mu hana ne?”.

Atake fara'ar dake fuskar Mommy ya gushe cikin rashin jin daɗin abinda Hajiya Bunayya ta faɗa tace.

“Wallahi sukam ba Mayu bane har dake ki yarda kefa komin yaya, ita Uwa ce agareki kuma kakar ’ya'yanki kuma Inde har za'ace suna ciki to mijinki ma yana ciki”.


Hajiya Bunayya kuwa cikin sauri tace.

“A'a mijina atsarkake yake.

 Uwarsa kuwa ba zan musan ta mata ba yawwa a duniya idan kaji an cewa mutum maye ba zaka musanta masa ba kawai dai abinda na sani mijina ba yayi nima banayi kuma 'ya'yana na basayi.

 Hajja Nana gaskiya kika faɗa taje can ta ƙarata da baƙin halinta inma tanayi can mata inma ba tayi can mata amma abinda gari dai ake faɗa tana yi, kuma mutum bashida hujjar da zaiyi musu akan hakan, gwara ma hujjar da mutum zai ɗabbaga tunda ga alamu ke yanzu ko cikin ki dake yawa zubewa bakya ta Allah ƙashi da ita!?”.


Cikin sauri tare da ɗaure fuska Mommy tace.

“A'a nikam Allah ne ya ƙaddara min zubewar ciki babu wani wanda ya zubar min da ciki”.

Murmushi Hajiya Bunayya tayi aƙasan ranta tace can miki ƙidahuma.


Khausar kuwa kallon mamaki tabi Hajiya Bunayya dashi kana aƙasan ranta tace lalle Hausawa sunyi gaskiya da suka ce iya ruwa fidda kai”.

Amina dake tsaye ta watsa Khausar Harara kana tace.

“Abbah ke kiranki kizo kakar taki tazo da wasu maza suna waje sai kije ku gaisa”.

Ta ida maganar tare da juyawa ta fice.


Ita kuwa khausar cike da farin ciki ta juya ta fice ta nufi coumpund kasa ɓoye fara'ar fuskarta tayi ganin Yaya Aliyu tsaye yaron Baffanta na Adamawa tare da Yaya Abba cikin jin dadi ta ware manyan Idanunta cike da farin ciki tace.

“Yaya Aliyu sannu da zuwa ku ƙara so”.

Ta faɗa tana yin gaba zuwa Falon Lamiɗo dake saukan baki.

Bayan sun shiga falon sun zauna ta dubi Aliyu still Fuskarta da murmushi tace.

“Yaya Aliyu yaushe kazo?".

 Gyara zamansa yayi yana fuskantar ta kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

“Baffanki ne ya tasoni wai sai na kawowa tsohuwar sa kayan azumi shine kuma yanzu Hajja Nana tace sai munzo”.

Khausar kuwa murmushi tayi kana tace.

“Hajja Nana rigima"

Sai kuma ta maida kallonta kan Yaya Abba dake latsa waya tace.

“Yaya Abba ya karatu?”.

Ahankali ya ɗago kansa da murmushi afuskarsa yace.

“Karatu ya ƙare yanzu wannan karon tare zamu tafi da Aliyu can Adamawa idan Allah ya nufa idan munje zan samu aiki Insha Allah tunda kinga Baffan Jimeta yana da hanya da manyan mutane Insha Allah za'a samu”.


aSaki murmushi tayi kana tace.

“Masha Allah abu yayi kyau”.

Lamiɗo ya shigo suka gaisa bayan sun gama gaisawa ya fita, Khausar kuwa Anutse ta miƙe tace.

“Ina zuwa”.

sannan ta fice.

Kai tsaye kichen ɗin su ta nufa ta ɗauko Babban Warmers da faranti ta fita.

Hajja Nana ta bita da kallo baki sake ganin Uban kula me kyau da tsari da tafita dashi.

Ba daɗewa Khausar ta dawo ta sake ɗaukan Flaks da kofuna.


Har takai ƙofa Hajja Nana data kasa haƙuri tace.

“Kede akwai Jaira mara kirki tunda nazo kike wani shan ƙamshi kamar baki so zuwa na ba, ko arzikin gaisuwa ban samu ba bare insa rai da ruwan sha, amma wa'annan saboda 'yan uwanki ne jiki na rawa kin wani kinkimi Uban kula kin fita yanzu kin dawo kin ɗauki Flaks”.

Kallonta Khausar tayi tare da taɓe baki tace.

“Kinga sai anjima Ni sauri nake”.

Tana gama fadar haka ta fice bakinta ɗauke da Sallama tashiga falon.

Amsawa sukayi tare da kallonta.

Zama tayi tare da buɗe Warmers din ta ɗauki babban Plate ta zuba musu shin kafa da miyar  da yaji naman kaza sai kuma haɗin coslow kana ta zuba musu shayi dake tururi.

Yaya Abba yayi Murmushi yace.

“Da'alama wannan girkin kine saboda wannan ƙamshi”. 

Murmushi tayi amma batace Komai ba.


Acan ɗaki kuwa bayan ankira sallan Azahar Mommy takai Hajja Nana har toilet ɗin ta tayi alwala kana ta fito ta gabatar da Sallah bayan ta idar tayi adduo'i.

Ta juya ta kalli Mommy dake riƙe da carbi ahannunta tace.

“Aisha”.

Cike da girmamawa Mommy tayi ƙasa da kanta kana tace.

“Na'am”

Hajja Nana kuwa gyara zamanta tayi tare da tattara duk kan nutsuwarta zuwa kan Mommy tare da cewa.

“Magana ce mai muhimmanci ta kawoni”.

Cikin girmamawa Mommy da kanta ke ƙasa tace.

“Toh ina sauraronki Hajja Nana”.


Hajja Nana kuwa Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

“Magana ce akan Khausar da kuma ɗan Baffanta wato Aliyu”.


Jinjina kai Mommy tayi cike da ladabi tace.

“Toh Hajja Nana ina jinki”.

Hajja Nana ta gyara zamanta tare da cewa.

“Toh zuwa yanzu dai inaga Khausar ta girma, sannan inaga ta gama karatun ta yanzu idan ma bata gama ba to ta kusa”.

Jinjina kai Mommy tayi kana tace.

“Eh ta kusa Insha Allah yanzu kam Shekara ɗaya yarage bayan sallah Insha Allah zata tafi ajin ƙarshe na gama makarantar gaba da primary”.


Cikin jinjina kai Hajja Nana tace.

“Masha Allah Ubangiji ya taimaka”.

Mommy ta amsa da.

“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

Hajja Nana kuwa duk kan nutsuwarta ta tattara tare da cewa.

“To ai yanzu dai ta samu ta kori jahilci ta yaƙesa, yanzu batun aurenta za'ayi.

 Ga kuma Yayanta kuma ɗan Uwanta za'a aura Matashi magana ya ƙare sannan kuma idan karatun take so ta cigaba idan sunyi aure zata yi acan jahar Adamawa tunda suna da makarantu manya-manya acan dan haka yanzu batun aure ne ya kawo mu nazo dashi za'a haɗa bayan sallah in Allah ya yarda”.

Akuma dai-dai lokacin Khausar ta shigo ɗakin, cike ka ɗuwa Idanunta na kan Hajja Nana cikin sauri tace.

“Wai me naji kina cewa?”.

Cikin isa, gadara, Hajja Nana ta wurga mata Harara kana tace.

“Batun Aurenki nakeyi”.

Arazane Khausar ta zare ido kana tace.

“Wa.....!





*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*


Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara. 


Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.


Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida.



  GARKUWAR MA'AURATA


                           By

     *GARKUWAR MARUBUTA*

No comments

Powered by Blogger.