Rana Daya Complete Book 2


CHAPTER 1 


*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

 

Mun tsaya 

Ba su lura da cewa Aliya tayi mutuwar tsaye ba ne sai da Aisha ta waiwayo da nufin yi mata magana, ta zaci guri ta basu su fara shiga. ” Ta waiwaya ta kalli inda Aliyar take kallo, sai 

taga Shatima zaune ya tasa Salma an gama wanke

mata kai ana tajewa da handrayer…

Wash! Bari in tsaya a nan sai mun hadu a littafi na biyu don jin ya ya za ta kasance?


RANA DAYA 2


Madina, ta ce “Shigo mana Amarya.” Hakan da ta fada shi ne ya janyo hankalin Shatima ga barin kallon gashin Salma, ya kalli inda ‘yanmatan suke. Zumbur! Ya mike da suka hada ido da Aliya.

Da yake Shatima namijin duniya ne, sai ya shanye tsoron da ya tsirgo mishi da mamakinshi, sannan ya dan fadada murmushinsa ya ce, “My love kema kar dai gyaran gashi ki ka zo nan?”

Ta danne tambayoyin da suka taso mata lokaci daya kusan guda biyar a kan wannan yarinyar da ta gansu tare. Ta dube shi da dan fari ta ce, “Eh, gyaran gashi nazo.” Ya ce, “Nayi zaton ke tuni kin gyara naki?” ta ce, “Ban samu lokaci ba ne, sai yanzun.”



Ya kalli mai gyara gashin, “Wannan ma kiyi mata da kyau, don Amaryata ce itama.” Mai gyaran ta ce, “Amaryarka kuma?” Ya ce, “Eh, akwai wasu ma guda biyu.” 

Tayi dariya tare da fadin “A’a wasa ne.” Aliya tana son sanin wace ce wannan, don sai tana ganin kamar ta santa. Ko ‘yar’uwarsu ce? Ta dai san kanwarshi Badi’atu tafi wannan yanzun, don ko sanin da tayi mata a shekara uku baya, ta fi wannan cika ido. Amma bari taji daga gare shi. Cikin salo irin na mata masu wayo ta ce, “Nayi mamakin ganin ka a nan.” Ya ce, “Naga mamakin a fuskarki, amma mamakin me kike yi?” Ta ce, “Na zaci kana can Kano yanzun gurin daurin aurenka da ‘yar’uwata?”

Ya ce, “Ban samu zuwa ba, saboda ‘yar autarku itama ta fito tsaf!” Ya fada tare da dafa kan Salma wadda aka gama gyarawa gashi aka daure.

Daidai lokacin matar ta ce Aliya tazo ta zauna a soma yi mata. Amma ita Aliyar hankalinta yana gurin Shatima, tana son ji daga gare shi don ya sake daure mata kai.

Ta ce, “Wai dama Badi’atu tana da kanwa ne?” Yayi murmushi, don sai yanzun ya fahimci bata gane ba. ya tuna ashe fa bai fada mata cewa akwai Salma ba.

Ya ce, a ranshi bari yayi amfani da wannan damar yayi mata bayani, don haka ya ce, “Zo nan muyi magana.” Ya dubi Salma, “Jira ni simolinsu.” Yayi maganar cikin zolaya.

Jikin motar suka tsaya. Ya ce, “Na manta ban fada miki batun Salma ba, yarinyar nan ina tsananin tausayinta. Na aureta ne don in taimake ta…”

Aliya ta katse shi da cewa, “Kayi me?” Ya ce, “Na aure ta na ce.” Tayi shiru tana nazari, ya dan tsakura mata labarin Salma kadan, ya kuma sake tabbatar mata an fara daura aurensu da Salma kafin su wuce Kano.

Aliya ta danne duk wani kishin Salma da ta ji ya

taso mata. Ta ce, “Amma me yasa ba ka fada min

ba? ko kana zaton zan ja da ikon Allah ne?” Ya tausasa murya. “Nayi kuskure, na san cewa ba zan samu matsala daga gurinki ba.” Ta kirkiro murmushi. “Ita ce karamarmu babbarmu ke nan ko me? Tunda naga aurenta aka fara daurawa.

An ce wadda aka fará daura ma aure ita ce uwargida.” Ta kasa kunne don jin me zai ce. Ya ce, “Fadin Hadisi ko Kur’ani?” Ta ce, “Ina al’adar Malam Bahaushe ce.”

Ya ce, “To ni a gidana ke ce Uwargidana.” Aliya

ta ji dadi a zuciyarta. Amma sai ta danne. Ta ce,

“Kar ka hada husuma, da dai ka bari an bi tsari.” Ya ce, “Tsari ya wuce, nawa. Ni zan tsara gidana, kije ayi miki naki wankin kan saboda lokaci na tafiya.” Ya shiga ciki ya biya kudin su duka, sannan ya ce ma Salma ta gaida Antynta.

Ta russuna ta gaida Aliya da kawayenta, sannan ta fita. Ya dubi Aliya, “Bari in kai ta gida ko?” Aliya ta ce, “To sai anjima.” Yayi sallama kawayenta suka fita. 

Salma tana son taji wace ce wannan? Ya kalleta, “Bakinki yana son cewa wani abu ko?” Ta ce, “Me yasa ka ke gane haka?” Yayi murmushi, “Baiwata ce

hakan. Ki fadi abin da ki ke son fadi.” Ta ce, “To wacece wannan din da ka ce in

gaidata, ‘yar’uwarka ce? Itama tana aure yau ne?”

Ya dan rage tafiya, sannan ya kalleta, “Tana cikin Amarena na yau. Amman ita ba a daura ba, sai an dauro na Kano. Ita ce zata zama uwargidanku.”

Ta tsura mishi ido ta kasa magana. Yayi fakin a gefen titi, sannan ya kalleta. “Idanunki sun nuna rashin gamsuwa da zancena. Me yasa ki ke zaton maganata ba gaske ba ce?”

Ta lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya. Abin ne ni ke ji tamkar ba gaske ba.” Ya ce, “A zantukan da na fada miki, wanne ne ki ke ganin ya yi kama da ba gaske ba? Ko kuma wanne ne bai faru ba? Na ce zan aure ki, kuma na aure ki.”

Ta ce, “Ni ina mamakin da ka ce mu hudu ne, mu hudun ne ban taba ji ba.” Ya ce, “To yau gashi ya faru da ke.” Ya kai yatsan shi ya lakuci kumatunta, “Ke ce kuma autar su. .” Ta ce “Ni na taba ganin wannan matar da kayan Nurse.”

Ya ce, “Eh ita Nurse ce. Yanzun kin yarda ku hudu ne ko sai kun tare kin ga shaida?” Ta ce, “Yanzun dai ina tunanin mu biyu ne, in naga sauran sai in kara hakikancewa.” Ya tada motar tare da murmushi. “To nasan an jima za ki hakikance.” Ya sauke ta tare da yi mata sallamar sai sun hadu a gidan shi.


** KANO **


Can Kano ana ta hada-hadar daura aure, unguwar ta cika makil da manya kuma mashahuran mutane, maroka da makada abin sai wanda ya gani.

An gama daurin aure lafiya, sai dai da dama sun so su ga angon musamman dangin Amarya wadanda ba su san shi ba.

Haka ma cikin gidan su Amarya ya cika makil, Mahaifinta ya kira Mahaifiyar a waya. Ya ce, “Ku 

shirya Amna domin da ita za su wuce yanzun.

Momi ta ce, “Suna kan shiri ne.” Motocin daukar Amarya da ‘yan rakiya tuni an tanade su, ba a jira wai gidan Ango su kawo motocin daukar Amarya ba, domin ita kanta Amaryar motocin ta biyu sabbi dal da aka bata a gudunmawa.

A cikin daya aka dauke ta, dayan aka debo kawayenta, sai sauran dangi da suka jero cikin motoci na alfarma. Zariya suka dira, kamar yanda Hajiya ta tsara cewa duk matan da za a kawo su nan ne gidanta, suma suna da nasu biki da za suyi kafin a kai su gidansu, sai washegari ma sannan za a kai su. Gefen Alhaji aka sauki Amna, dama an gyare

gidan ya sha fenti saboda bikin musamman, gefen Alhaji komai sai da aka canza. Ita da kawayenta ne a ciki kadai, Hajiya tasa an kai musu kayan ciye-ciye na alfarma da karamci.

Don an ce tuwon girma miyarshi nama.

Su dai maza suna gama hallaruwa suka shiga shirin daura auran Nafisa, a gidan Kaka aka daura shi, in da Baban Shatima ya ba da ta.

Shatima yana gurin aka daura nasu da Nafisa, in da suka yi ta daukar hotuna da abokansu da kuma ‘yan uwa.

Daga can suka wuce na Aliya, mutane sun sha mamakin wannan Ango mai mata hudu rana daya. Abin da ya ba Shatima mamaki yanda ‘yan jarida suke bin shi da son jin ta bakinshi, bai san kuma wa ya gayyato su ba. Sabuwar shiga ya sake in da suka tafi walima ta su ta maza zalla shi da abokanshi. Shahararren guri suka kama suka yi walimarsu mai tsari.

Sun taso karfe shida saura na yamma, sai suka yanke shawarar suyi Magriba kafin su je daukar Amare, tunda duk nan dai gidan iyayen Shatima din za a tara su. Nafisa suka soma daukowa, wadda ta ci kuka ta gode ma Allah, sannan aka ɓanbare ta da kyar daga jikin Mamarta, aka sa ta a mota. Ita dakin Hajiyar aka kaita kai tsaye da kawayenta, hakan ya nuna ma kowa ita din ta gida. ce.

Aliya kuwa gefen bakin gidan aka gyara, tare da  bakin da aka sauka a gurin matsugunni, aka kaisu itama da nata kawayen sai dai su basu samu sauka kamar ta Nafisa ba, bare irin ta Amna.

Shatima kuwa da shi aka je daukar Salma, tunda

Hajiya ta karanta mishi wai gidan ta za a kai Amare

kafin a wuce Kaduna, yake tausayin Salma. ba ta zo da kowa ce kawa ba, sai ‘yan uwa da makota. WaYan da suka samu labari, duk Amaryar da ta iso ‘yan uwan Hajiyar da Aminanta suke zuwa suna tarbar su zuwa in da aka yi musu masauki.

Amman da suka iso da Salma babu wanda ya zo.

har shi da kanshi Shatiman ya shigo gidan. Ya kira

Anty Momiyo gefe, ya ce mata “Anty ga Salma fa, 

ita da danginta ba zan so a wulakanta yarinyar nan ba.”

Anty Momiyo ta ce, “kana wucewa da ita, ya

zama laifi a gurin Hajiya ka sani. Bari in tambayo ta muji yanda za’ayi. Suna falo suna shewa Anty Momiyo ta zo mata da batun da suka yi da Shatima. Hajiya ta mike cikin sauri, wai bata gayyar tsiya. > bari taje tayi musu zagin fitar arziki. Nan fa aka hanata, aka bata baki. Ta ce, “Bata da sauran masauki, in shi yana da in da zai sauke ta to ga gidan

nan. Anty Momiyo ta koro masa abin da Hajiya ta ce. Ya ce mata babu komai Anty a kai ta samana kawai,

‘yan uwanta nasa su tafi.” Duk da haka sun rakata

har dakin Shatiman, wanda sai an bi dai ta falon.

Ko gaisuwa basu samu ba ‘yan uwanta bare ruwan sha, su dai suna aje ta suka ce sai sun zo goben don rakata dakinta.

Sun wuce sun bar Salma tsuru zaune a bakin gadon Shatima, fuska lullube ta ci kuka ta gode Allah, tana ma kan kukan suka tafi. Shatima suna masaukin abokansa, sam ya kasa

walwala, hankalinshi yana can gurin Salma,

zuciyarshi ta ki nutsuwa, suna hira yana tsaki. 

Munnir ya ce, “Wai don Allah Shatima lafiya ka ke tsaki?” Ya ce, “Ina tunani ne, yarinyar nan Salma tana can cikin damuwa, koma ayi mata wani abin tun da na san ba a sonta

Munnir ya zabga ma Shatima wata harara, sai ka ce irin yara kanana din nan, sannan ya ja dogon tsaki ya ce, “Ka san Allah har na soma tsanar wannan Salmar, duk ka bi ka zama wani soko a kanta.”

Ya ce, “Munnir ba zaka gane ba ne, da dai na sani da na ce ma Anty Momiyo a hada ta da Aliya nasan zata kula min da ita.”



 Download Complete Here

No comments

Powered by Blogger.