nihaad 9
💖💖 *NIHAAD*💖💖
By _Khaleesat Haiydar_✍🏻
9.....
Nihad na shesshekan kuka tace "Wllh shi inna, kawai an bar sa yana ta abinda ya ga dama a gidan kamar gidan ubansa, duk ya gama rena ni, ko gaisuwa bata hadani da shi" Inna tace "Duk ba wannan ba, yanxu kin kira Aliyun??" Nihad ta daura kanta gefen gadon inna hawaye na sauka idonta tace "Bayan ya ki dagawa" Inna ta dauko wayarta ta mika mata tace "Kirasa da nawa" Nihad tace "Ae idan ba shi da numberka baxa ka iya samunsa ba, ya sa layinsa a Private" Inna tace "Wai ko ba dai Aliyu ɗ'an wajen janaral Habubakar jikamshi ba?" A hankali Nihad tace "Shi..." Inna tace "To wannan dreba duk yanda aka yi tsinanne ne, ko don nace masa ya saki jikinsa yasa ya sake kamar gidan ubansa? to ai ni na xata yaron arxiki ne" Salati inna ta saki tayi tagumi tace "Yau naga dreban jaraba, ashe duk ni na ja komai da nace ya saki jikinsa, to a kira min Ibrahim din tun yamma bai yi ba ya sallamesa" Nihad ta dau wayar inna da sauri ta fara neman number Abba tayi dialing, Inna ta bude baki ta rike ha6a tace "To shi kuma Aliyun banda abunsa garin yaya xai ce sai yayi ma dreba magana mutumin da ba ajinsa ba, ai abinda bai sani ba talakawan nan haka suke da dacin rai kamar mutum ne ya doro masu talaucin, ina shi ina wani basamuden buzun dreba can? To ko a almajiri dai baxa su yarda su ajiye wannan mutumi a gidansu ba balle dreba, su da tun daga titin da ya yanka unguwarsu xaka fara ganin dirka dirkan sojoji har da motocinsu...." Nihad ta turo baki tace "Abba bai daga ba" Inna tace "Ina xai daga, ya tashi ya kawo wani kato gansameme kamar mutanen farko ya dau mota ya basa, ni wllh ranan da na fara ganinsa sai da na tsure, sai fa ya daga mutum ya nanasa da kasa sau biyar bai gaji ba, irinsu ai gadin dogon banki ya kamata a basu ba wai motar mutane ba" Nihad dai tayi tagumi don abinda ya dameta daban, ita yanxu ta ya xata fara shawo kan Aliyu, da yaya ma suka dawo soyayyar, Inna tace "To ko kin san inda ya sauka ki rakani mu je in basa hakuri" Nihad ta kalleta tace "Ji ki kuma, kawai don ki ja min raini?" Inna tace "Wani raini mutumi na nema ya kubuce, wa ke ta wani raini Nihad, idan ma baxa ki shiga ba ni ki rakani ki nuna min hanya in je in samesa" Nihad tace "Aa ke dai kawai duk yanda xa kiyi kiyi Abba ya kori driver din nan kawai" Inna tace "Yo sai ma kin fada, abu har ya kai yana korar ma jikokina samari" Hamid ne ya bude kofar dakin ya shiga yana kallon Nihad yace "Ke don uwarki ni sa'anki ne xaki wuce ni da abokina baki gaishemu ba" Nihad ta turo baki ta koma gefen Inna, Inna dai bata ce komai ba, Yace "Mahaukaciya kawai, uban wa xaki dinga daga ma kai?" A fusace Nihad tace "Kina dai gani babu abinda na masa ya xo ya fara xagina ko inna, ni fa shi yasa bana son xuwa gidan nan wllh, kowa yaje yaji da mugun halinsa" Cikin xafin nama ya nufeta, Inna ta mike ta wangale hannu tana tare Nihad tace "Dokeni to, Hamidu nace ka dokeni" Huci yake yana kallonta, Inna tace "Ai dama ka saba dukan nawa yanxun ma ka duka, ranan da ka biyo Bilkisu ai ni ka jibga ba ita ba" Nihad ko kallonsa bata yarda ta sake yi ba, Yayi wani kwafa ya fice daga dakin, Inna ta kulle dakinta tace "Kinsan korosa aka yi daga can kasar wajen wai wa'adinsa ya kare a can, to kuma sai kayi ta hucewa kan ya yan mutane" Nihad bata san lkcn da ta kyalkyale da dariya ba, Inna tace "Allah haka uban yace min, duk a booth din jirgi aka kwaso su aka dawo" Nihad dai bata ce komai ba, Inna tace "Yanxu ko kin boye number ki baxai daga wayar ba?" Nihad ta mike tace "Ni dai xan tafi inna dama anjima da daddare kice Hamid din ya kawoki nan gidanmu ki samu Abba da kanki" Inna tace "Toh shkkn ma, kawai bari inje in riskesa a gidan ba sai mun yi waya ba, idan ma ya kama ko shi sai ya kira Aliyun ya basa hakuri" Bude baki Nihad tayi, can ta kyabe bakin tace "Ni dai sai kin zo" Daga haka ta fita daga dakin, A bakin gate abokin Hamid ya tare ta da ya faki idon Hamid ya biyota, yana fara magana ta dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu tana yatsine fuska tace "Ina wasa da kai ne malam?" Daga haka ta ja tsaki tayi ficewarta daga gate din, ya bi ta da kallo baki bude, dama Hamid ya gaya masa ya ki ji. Nihad na komawa anguwansu ta yi ido hudu da Khalil dake xaune kan dakali a kofar gida wayarsa na kare kunnensa, yana ganinta bai sake cewa komai ba a wayar da yake kuma bai cire wayar a kunnensa ba, har ta isa dai dai inda yake, tayi masa wani harara ta ja tsaki ta shige cikin gida tayi banging gate din. Abba na tsaye balcony bayan magrib Khalil ya karaso da ladabi yana kallonsa yace "Gani Alhaji" Abba yace "Yauwa pharmacy xan aikeka ka siyo min magani yanxu" Khalil yace "Toh, ya sunan maganin?" Abba na duba wayarsa yace "Yanxu likitana ya turo min ta message bari dai in duba" Abba na shiga message din har ya fara pronouncing sunan maganin kawai ya fasa kar khalil yaje ya masa shirme, yace "Bari kawai xan rubuta maka a takarda kaje ka siyo, idan ka siyo sai...." Abba ya dakata ganin mai gadi na bude gate, sai ga motar Hamid ya shigo compound din, Abba yace "Je ka xan rubuta sunan maganin a kawo maka yanxu" Yace "Toh Alhaji" daga haka ya nufi boys quarters, Inna ce ta sauka daga motar ta nufo balcony, Abba dai na tsaye yana ta tunanin ko lafiya, Tana isowa ganin yanayinta yace "Lafiya inna?" Tace "Ina fa lafiya, mu je parlor baxan iya tsayuwa ba" Sai da ta fara shiga parlon Abba ya bi ta, kanta tsaye ta tafi parlonsa duk yana biye da ita, ta nemi waje ta xauna shi ma ya xauna yace "Ina yini Inna?" Tace "Ibrahim a ina ka samo wannan gansamemen dreban naka?" Abba yace "Wani abu ya faru ne?" Tace "Meye baxai faru ba, ya kora ma Nihad saurayi, d'an wajen Janaral Jikamshi, har yaron ya goge numberta yanxu haka da nake maka magana" Abba yayi shirui yana kallonta as if confused don ya kasa fahimtar xancen nata, Inna tace "A kara min Ac, xafi ya isheni" Abba ya dau remote ya kunna Ac din, yace "Ban fahimta ba Inna" Nan inna ta xauna tayi ma Abba tsari da abinda Nihad ta fada mata da ma wanda bata fada mata ba duk ta dire ma Abba, Abba yace "Ikon Allah, ke yanxu wa ya sanar maki wannan?" Inna tace "Har gida ta sameni tana kuka kamar ranta xai fita, hankalina yayi mugun tashi shine nace da kaina xan taho da daddaren nan, sannan a kira min dreban in ji uban da ya aikosa wajenmu, ni dama ina ganinsa na sha jinin jikina ban yarda da shi ba kawai nayi shiru ne, wa yasan adadin binne binnen da yayi maka a gidan nan yanxu? Huhuhu kana wasa da buzun mutum, Ai irinsu xuwa suke su tarwatse gida kai har ma su talauce mai gidan su saci abinda xa su sata su gudu su koma Nijar, to Ibrahim ko motar nan ma ya gudu maka da shi ai ya cuceka, to yanxu ni dai a kira min shi ko in tafi in samesa da kaina" Abba yace "Aa ba sai kin samesa ba, ai sallamarsa kawai xanyi ya tafi ba sai anyi wani tashin tashina ba" Inna tace "Aa ko xagi ne a bari in masa kafin ya tafi ai" Abba yace "Ke dai nace ki bar komai a hannuna, bari Hamid ya xo ya maida ki gida dare yayi" Tace "Ai Habubakar ne ya sa ya kawoni banda haka waye ubana Hamid xai kawoni, tun fa da aka korosa daga kasar wajen yake jin haushin kowa, to ni nasan sanda ya koma can da xama balle sanda aka korosa, kawai gani nayi ya dawo da manyan jakunkuna, ji yake kamar duk ya kashe mu yanxu haka" Abba yace "Ke wa yace maki an korosa, don Allah ki bar fadin wnn magana a xata da gaske ne" Mikewa yayi ya fita daga parlon ya kira Hamid dake main parlor yace "Zo ka maida Hajiya gida" Yace "Toh Abba" Har mota ya rakata, bata ce xata shiga wajen matansa ba shi ma bai ce ta shiga ba, don da suka fito parlor ma yace Nihal ta kirasu su gaisheta ta hana, yana tsaye compound din har motar ta fita, yana kallon mai gadi dake kulle gate yace "Kai ina Ibrahim?" Aminu bai kai ga bada amsa ba sai ga khalil da mota, Aminu ya kara bude gate din Khalil ya shiga compound din da motar sannan yayi parking a parking space Abba dai ya bisa da kallo, yana sauka daga motar ganin Abba a tsaye, ya nufesa da ledan pharmacy a hannunsa ya ɗan risina yace "Ga maganin Alhaji" Abba yace "Wani Magani?" Khalil ya kallesa yace "Da kace a siyo" Abba yace "Na gaya maka maganin da zaka siyo min ne?" Khalil ya kalli ledan hannunsa da sauri, kawai sai ya rasa abinda xai ce, Abba ya amshi ledan ya bude maganin sannan ya bude wayarsa ya shiga message din da Dr dinsa ya turo masa yaga maganin ne Khalil ya siyo, Abba ya daga kai yana kallonsa daga sama har kasa, kafin yace komai khalil yayi saurin cewa "Ai ka fada min sunan maganin, rikewa nayi a kai" Abba dai bai ce komai ba sai kallonsa yake, Khalil kam ya kasa barin su hada ido, Can Abba yace "Ban gaya maka sunan maganin fully ba" Da sauri khalil yace "Ka tambayi Habibu a can garinmu akwai wani likita da ya bude Kemist na siyar da magunguna, na fi shekara takwas ina jire masa shago yana bani wani abu duk wata, Allah ya bunkasa masa shagon sosai, rasuwa Allah yayi masa shine yaransa suka rufe shagon bayan sun bada sarin duk magungunan da ya bari, wannan dalilin ne ma har yasa da Habibu yayi min tayin wannan aikin na taho kano don ina xaune babu abinda nake, don haka babu wani magani da ban sani ba yanxu haka sai abinda ba a rasa ba..." Abba yace "Allah ya rufa asiri.... Yau kuma me ya hadaka da Nihad?" Khalil ya sunkuyar da kai yace "Bani da masaniyar na mata wani laifin yau, kawai dai abinda na sani saurayinta ya zo zai bani kudi yau da na kai ta babban shago xata yi siyayya, sai na nuna baxan amsa ba, shkkn abinda na sani kenan Alhaji" Abba yace "Kaje xa mu yi magana gobe" Daga haka Abba ya nufi cikin gida, Khalil ya koma gun mai gadi ya zauna letting out a deep breath. Washegari da safe Nihad ta leka window ya fi sau goma wai taga ko driver ya fara harhada kayansa xai bar gidan, amma sai taga ya kai su Sudais da Amina school, kuma da ya dawo taga ya ci gaba da zama bakin gate, kasa samun sunkuni tayi, ta dau wayarta tayi dialing number Inna, yana fara ringing ta daga, tace "Ina kwana inna" Inna tace "An tashi lafiya" Nihad tace "Inna wai jiya ya ku ka yi da Abba da kika xo ne?" Inna tace "Yace xai yi masa koren kare, ai shi bai san haka yake ba, da kyar ma in ya kwana a gidan ki bincika ki ga" Nihad tace "Wani bincike bayan ga mutum can a zaune ina kallonsa" Inna tace "Atoh, Kilan sai yau xai tafi, ai na gaya ma Ibrahim maganganu masu ta6a xuciya jiya, yace min in sha Allahu xai sallamesa, ina jin sai yau din xai koresa don jiya kinga ai dare yayi kar ace mutum bai da imani yayi kora cikin dare" Nihad tace "Sai anjima" Katse wayar tayi ta bude kofar daki ta fito, a parlor ta hadu da Nihal, Nihal tace "Kinsan in two days time xan koma school" Nihad ta tsaya ta kalleta tace "Toh ai baki gaya min ba" Nihal tace "Toh yanxu na gaya maki" Nihad tace "Toh yanxu da Habibu baya nan waye xai kai ki Zaria?" Nihal tace "Ni ma ban sani ba, sai Abba yayi magana" Nihad tace "Don kinga wannan drivern sallamarsa xa ayi yau" Nihal dake ta kallonta tace "Okay" Nihad tace "Ko dai har kinyi shopping din ki?" Nihal tace "Aa probably today or tomorrow, sai yanda Abba yace" Nihad tace "Okay ki min magana sai mu je har da ni" Nihal tace "Okay, baki da lectures yau?" Nihad tace "Toh ko ina da lectures ai babu driver da xai kai ni, but karfe tara nake da lectures" Bata jira cewar Nihal ba ta nufi kofar fita parlon ta fito compound, Backyard din gidan ta nufa kai tsaye gun tsuntsayenta su Saminu na gaisheta duk tayi kamar bata ji su ba, tsaye tayi bata motsin kirki tana kallon cages din birds din da duk suke a bude kuma babu birds din a ciki sai roban abincinsu da ruwa, duk cages din guda hudu a bude suke har na parrot dinta, Dawowa tayi da gudu cikin gida tana kallon Saminu dake shara Shafi'u na watering flowers din gidan cikin tashin hankali tace "Saminu ina tsuntsaye na aka kai min?" Saminu ya mike da sauri haka Shafi'u da yayi dropping watering can din hannunsa, Saminu yace "Suna can cikin kejinsu Hajiya" Ta gwalo ido tace "Wani cage din??" Duk suka nufi inda birds din suke, sai ga su sun dawo suna wuri wuri da ido, Saminu na in ina yace "Wllh Hajiya ko jiya sai da muka xuba masu abinci da ruwa...." Da sauri ta juya ta bar wajen ta nufi gun mai gadi cikin rawan murya tace "Aminu ina aka kai min tsuntsaye na?" Aminu yace "Suna can keji Hajiya" Cikin daga murya tace "Wani Cage din, abinda naje na tarar a bude babu komai ciki" Mai gadi ya mike da sauri yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, babu komai ciki?" Shi dai Khalil na xaune yana danne danne da torchlight phone, Aminu ya nufi inda birds din suke da sauri, Nihad da har kanta ya sara mata ta bi bayansa gabanta na faduwa, can ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo tsakar compound ta rusa wani uban ihu ta daura hannu a ka uwa warce aka yi ma mutuwa, Nihal ce ta fara fitowa a guje ta nufota tace "Nihad what happened?" Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace "Wani yaje ya bude min cage din birds dina duk sun gudu, wayyo Allah na na shiga uku, wllh har sun saba dani Nihal, Parrot din har kiran sunana yake yace good morning" Su Aminu da Saminu dai na can gefe a tsaye sai wuwwurga idanuwa suke, Umma ce ta fito compound din Mumy na biye da ita a baya, Hankali tashe Umma tace "Lafiya Nihad, me ya faru?" Nihad ta nufeta tana kuka sosai ta kamo hannunta tace "Umma wani yayi releasing din min birds dina duk sun gudu babu ko daya" Umma ta saki salati tace "Waye da wannan danyen aikin, yanxu babu ko daya wa ennan tsadaddun tsuntsayen da Abbanki ya siya maki" Nihad na gyada kai cikin kuka tace "Wllh duk sun gudu, bude masu cage din aka yi don su gudu" Mumy dake kallonta tace "Shine xa ki 6ara baki haka ki daga mana hankali Nihad?" Umma ta kalli Mumy tace "Haba Maryam, ko don ba ke kika bada kudin siyan tsuntsun ba, kinsan yanda dabba ke da shiga rai kuwa" Mumy tace "Toh waye ya budesu har suka gudu? Sannan ita me yasa bata xuwa dubasu a kai kai yaushe rabon da taje inda suke" Cikin kuka Nihad tace "Wllh ina xuwa dubasu ki tambayi Aminu, kullum sai naje dubasu" Nihal tace "Toh ko da aka basu abinci ne aka mance ba a kulle cage din ba" Nihad ta durkushe wajen tana kuka kamar ranta xai fita tace "Ni wllh ko ma wa yayi min haka Allah ya isa ban yafe ba, Allah ya tsine ma koma waye, Allah ya isa, shi ma sai an nemasa an rasa wataran yanda na rasa tsuntsaye nahhh" Juyawa Mumy tayi ta wuce cikin gida, Umma ta dagota tace "Ai ba Allah ya isa xa kiyi ba, koma uban wa yayi wannan aika aikan dole a ganosa a hukuntasa, ki bar komai a hannuna kawai" Nihad na shessheka tace "Umma wanda yayi mun haka ya tsaneni ne shi sa yayi haka kuma sai Allah ya tsine masa albarka ya daidaice, Allah ya isana" Nihal tace "Ki daina cewa haka baki san ko..." A fusace Nihad ta mike ta hankadeta har sai da ta kusa faduwa, tace "Shut up plss if have nothing good to say" Bude baki Umma tayi, sae kuma ta kalli Nihal tace "To wuce ciki" Nihal ta ta6e baki ta juya ta koma ciki, Umma ta juya ita ma ta bar wajen, Nihad ta hade rai ganin yanda ma'aikatan gidan ke kallonta, cikin tsawa tace "Uban meye kuke wani kallona munafukai yan iska, ai har da hadin bakin ku aka sakar min tsuntsaye suka bi duniya, to ku sani wllh daga yau sbda ku ni xan dinga shiga kitchen sai in ga d'an iskan da xai xubo maku abinci ya kawo maku, for one week ba ku da abinci wllh a gidan nan tunda har aka sakar min tsuntsu suka gudu" Tana fadin haka ta juya fuuuu ta wuce ciki. Da yammacin ranan Farooq ya shigo gidan daga Abuja, Nihad da abun duniya ya isheta don har sannan Aliyu isn't picking her calls, ga kuma har yanxu bata ga Driver ya bar gidan ba, kuma babu ma wata alamar da ta nuna xai bari, yana nan a xaune tare da mai gadi, ko makaranta bata je ba sbda damuwa gashi har test Husnah tace mata anyi, ta mike daga xaman da take ta yi a parlor ta fito compound jin motar Farooq, tamke fuska tayi ganin Khalil da Aminu sun nufi Farooq, Khalil ya fara basa hannu da ladabi, suka gaisa, farooq dai sai kallonsa yake, Aminu dake ta rawar kafa yana washe baki yace "Ae shine sabon dreban gidan tun bayan tafiyar Habibu, yau kwanansa biyar ina jin a gidan nan" Farooq ya kara kallon Khalil daga sama har kasa, sai kuma yace "Driver??" Sai kuma yayi saurin cewa "Ohk maa sha Allah, ya sunanka?" Khalil yace "Ibrahim" Farooq ya gyada kai yace "Maa sha Allah...." Tuni Mai gadi ya dau jakar Farooq ya nufi cikin gida da shi, Nihad dake tsaye balcony ta hade rai tace "Toh ajiye kayi tafiyarka ko ka aikesa ne??" Aminu ya ajiye jakar ya juya sui sui ya bar wajen, Farooq ya amsa gaisuwan da Nihal ke yi masa ya nufi Nihad yace "What happened Nihad?" Kamar jira take ta fashe da matsanancin kuka, yace "Meye haka?" Cikin kuka tace "Ya Farooq wani axxalumin da baya tsoron Allah ya bude ma tsuntsaye na cage duk sun gudu har parrot din" Bude baki Farooq yayi yace "Garin yaya?" Ta karasa ta rungumesa tana kuka sosai, ta gefen ido khalil ya kalleta kafin ya juya ya bar wajen, Farooq ya dago kanta yace "But how did it happen" Tace "Kawai yau da safe naje basu abinci naga ba komai cikin cage din" Yace "Ow that's bad, bari anjima sai mu je ki siyo wasu" Ta marairaice tace "But how will d parrot get to know me just as the old one?" Yace "Yanda wancan din ya sanki sabon ma haka xai san ki" Daga haka ya kama hannunta suka shiga gidan tana share idonta. Bayan ta amshi nata tsaraban da farooq ya kawo mata ta wuce sama xuwa dakinta, wayarta ta dauka ta sake kiran Inna, yana fara ring Inna ta daga, Nihad tace "Inna har yanxu fa driver din na nan babu inda ya tafi don ma in gaya maki" A fusace inna tace "Ke raba ni da wani shegen dreba an shigo an kwashe min yan canjina wai barin gidan da nayi jiya da magariba, kowa sai ce min yake ba shi bane, to ni na saci abina koko?" Nihad ta tabe baki ta katse wayarta, sai kuma ta ja tsaki tace "Dama ba a abun arxiki dake..." Da daddare tana dakin farooq dake kallonta yace "Toh sai in ce masa me idan na kirasa?" A hankali tace "Kawai hakuri xaka basa a kan abinda driver din yayi masa" Farooq yace "Ba kince layinsa a kulle yake ba?" Tace "Aa ya ta6a saving numberka a gabana ai, ka tuna sanda ya kiraka da baka da lafiya?" Yace "Oh, ohk" Daukar wayarsa yayi ta kira masa number Aliyu yayi dialing, a kashe suka ji wayar, yace "It's switch off" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ki je kawai, gobe sai in kirasa" Mikewa tayi tace "To sai da safe yaya....."
Saura how many page free pages ya kare???
07087865788✍🏻
Leave a Comment