nihaad 10

 


πŸ’–πŸ’– *NIHAAD*πŸ’–πŸ’–

By _Khaleesat Haiydar_πŸ“–✍🏻


10......


Khalil na xaune yana waya a bakin gate mai gadi ya karaso wajen daga boys quarters, Khalil ya saka wayar a aljihunsa bayan ya gama, Aminu da har ya xauna ya mike yace "Aa bari in baka waje ka ci gaba da wayarka...." Khalil yace "Na gama" Aminu ya dawo ya xauna yana kallonsa yace "Na lura baka son kayi waya a gaban mutane saboda hayaniya ko?" khalil yace "Haka ne" Aminu yace "Ina can tare da su Saminu muna ta jajanta lamarin tsuntsayen nan da suka gudu, abun da mamaki da al'ajabi, sun kusa shekara daya da rabi fa a wajen ba a ta6a nemansu an rasa ba sai yau" Khalil yace "Ai gwara da suka gudu kar xunubanta ya dinga shafarsu su ma" Aminu ya kyalkyale da dariya yace "Wllh baka da dama, ni tashin hankalina abincin da tace xa a hanamu, in an hanamu abinci ya xa mu yi? Ba fa kanta kenan, duk da nasan uwarta baxata yarda da hakan ba, amma makira ce tana iya biyomu ta kwace idan an kawo mana" Khalil yayi murmushi kawai, Aminu yace "Amma fa kana bani tsoro da mamaki yanda kake nuna mata baka shakkarta, akwai wani littafi da na ta6a saurara a shafa labari, kaga yanda ta sa ka gaba haka? To haka ita ma yarinyar littafin ta sa mutumin gaba yana aiki a kampanin babanta ita kuma ita ce manaja a kampanin, tayi ta masa walakanci da rashin mutunci daga baya ta xurma sonsa in gaya maka, To sai...." Dakatar da shi khalil yayi yace "Me kake nufi?" Aminu ya gyara xama yana washe baki yace "Toh wa ya sani ko hakan xai iya faruwa wataran, barin taga sambalele me dogon hanci, ka fa san matan nan ba alkibla garesu ba...." Khalil yace "Ta wahala.... banda abun ka ina ita ina talaka? Sai dai kuma bata san wani talakan ma ko da kudi aka hadasa bazai saurareta ba, in dai kamar ni talakan yake wllh ko kallonta baxai yi ba" Aminu ya gwale ido, sai kuma ya tuntsire da dariya yace "Yanxu kana nufi misali yau ace maka gata nan ka aura baxa ka aura ba?" Khalil yace "Misalinka ba me yiwuwa bane har duniya ta nade, don kuwa da in aureta gwara na aura Krista, ko kuma in dauwama ba auren, kai kasan darajan da Allah yayi ma Ι—an Adam kuwa? To bari kaji ko da kudi wannan yarinyar baxata tsaya inda budurwata take ba, ga ta dai yar talakawa kamar ni amma ita wannan fitsararriyar baxata tsaya inda xata tsaya ba wllh...." Aminu yace "Aa dole xaka ji haushinta wllh, nima kuma ina taya ka jin haushinta kullum, ji tijaran fa da tayi maka daxu, banda yanayin rayuwa a ina xata ganka har ta cakume kwalar rigarka tana dungure kanka tana maka munanan xagi, a Ζ™alla ai xaka bata kusan shekara goma na sani, amma ta maka wnn cin mutunci da tijara gaban Nihal da kawarta, ba ma wannan ba ji yanda ta dau bahon ruwa gaba daya ta juye maka a cikin jama'a" Khalil yayi wani Murmushi bai dai ce komai ba, Aminu yace "Ni dai yau ace min ga ta in aura xan yarda in aureta ko don kudin babanta da kuma halaccinsa, sai kuma in saita mata xama...." Daga sama har kasa khalil ya kalli Aminu, bai san sanda yayi dariya ba yace "Kai ta kudin kake kenan" Aminu ya washe hakora, Khalil ya girgiza kai yana Murmushi, Aminu yace "Wllh ni fa naji dadin bude kejin nan da aka yi tsuntsayen suka gudu, Allah ne ya bi min hakki na abinda ta min jiya a kan su" Khalil yace "Ku kuka bar mata tsuntsayen suka kai har warhaka a gidan ai" Daga haka ya mike ya bar Aminu a wajen xai je yayi alwala kafin a kira isha'i.  Nihad na komawa dakinta taga missed calls din Husnah da yawa, ta xauna gefen gado ta kirata, yana fara ringing Husnah ta daga, Nihad ta dinga jin hayaniya tace "Kina ina haka?" Husnah tace "Mozida suite" Nihad tace "Me ake yi a nan?" Husnah tace "Wllh na manta ban gaya maki ba shekaranjiya a schl, Abokin saurayin Naf ne ke birthday, nayi ta kiranki tun daxu baki daga ba dama wai in gaya maki" Nihad tace "Toh ai tun jiya ya kamata ku gaya min, kuma yanxu kinga dare yayi" Husnah tace "Kashhh, kinga ke matsalarki kenan Nihad, karfe takwas din ne dare?" Nihad tace "Toh ta yaya ma xa ayi in taho babu me kai ni, kinsan wawan nan har yanzu Abbanmu bai koresa ba wa yasani ma ko asiri yayi ma yan gidan duk suke supporting dinsa, Umma ce kadai ke bayana a ko da yaushe, throughout na xuba ido yau in ga ko xai tafi ban ga ya tafi ba" Husnah tace "Kinsan abinda zai faru?" Nihad tace "Aa" Husnah tace "Yanxu xa mu fita mu karo wasu wine, kawai ki san duk yanda xa ayi ki fito mu hadu a wannan katon supermarket din na anguwarku" Nihad tace "Kar fa ku bar ni inyi ta jira Husnah" Husnah tace "Haba wani jira, bayan gashi nan yanxu ni da Naff da Sumy za mu fito" Nihad tace "Okay, bari a shiga masallaci sbda yan sa ido, sai in fito" Husnah tace "Sai mun hade, kar kuma kice ban gaya maki ba, A abokan celebrant din har da 'ya yan gwamnoni, shiga ce ta kece raini xa ki yi, duk da nasan ki ba wasa" daga haka Husnah ta katse wayar. Nihad ta mike ta shiga bandaki tayi wanka a gurguje jin ana kiran isha'i, ta dauro alwala ta fito da sauri, tada sallah tayi bayan ta idar ta fito da wani ubansun gown dinta ja wanda Aliyu ne ya siyo mata daga kasar waje ta saka, ko make up bata yi ba duk ta harhada kayan make up din da turarruka a wani babban jakarta da xae iya daukan hijab da takalmi da tarkace da yawa, tana jin an tada sllh sae da ta jira aka yi raka'a daya snn ta fita da sauri bayan ta sa ma dakinta makulli, tayi surveying parlor don tabbatar da babu kowa a ciki, ko wa na dakinsa, dama kuma gidan ana magrib kowa ke shigewa daki babu me shiga privacy din wani, sai kuma washegari idan an hadu wajen breakfast, yawanci da yake a bangaren Umma dakinta yake, Umma kan shigo taga ko tana waya kuma da wa take wayar, to dai ta sa ma dakin makulli ko taje xata shiga xata ji sa a kulle, da sauri da sauri ta fito compound nan ma ta ci sa'a babu kowa, duk suna masallaci, kan kace me ta bar compound din ta kama hanyar inda supermarket din da Husnah tace ta jirasu yake, tana isa wajen ko minti biyar ba ayi ba sai ga motarsu Husnah suka dauketa suka wuce, Husnah tace "Yanxu da Habibu na nan nasan da kansa zai xo ya daukeki idan aka gama partyn ko karfe sha biyun dare ne, yanxu dole kinga sai mun ajiye ki a nan after the party in ba dai saurayi kika yi a can ba" Nihad dai ta xuge jakarta ta fara gyara fuskarta xata yi light make up. Wajen partyn ya hadu iya haduwa kamar yanda Husnah ta fada ai kam ya yan manya ne suka cika wajen, very dim light ne kunne a inda suke birthday din, babu abincin da babu da abun sha tun daga ruwa, lemo, wine, alcoholic drinks, kai komai da akwai a wajen, gasassun rago biyu aka bankare wajen, ga manya manyan pepper chicken... cake din da budurwarsa tayi masa ma kadai abun kallo ne... duk hayakin cigarette ya turnike wajen, an sha shagali iya shagali a birthday din nan, abinda Nihad bata yarda da shi ba shine ta sake ma maza fuska a wajen, xata dai shige cikin kawayenta mata amma bata xama cikin maza, ko da kana ta shisshige mata ma banxa xata yi da kai tayi ta danna waya, Husnah ta kwankwade glass din wani alcoholic wine, glass na biyu kenan ta sha, su Naf da sauran yan matan wajen su ma duk wine din suke sha, Husnah na kallon Nihad dake rike da cinyar kaza da wani can drink a gabanta tace "Wllh ki Ι—an dana wine din nan ya fi na wancan ranan dadi sannan shi wannan babu abinda xa ki ji idan kika sha, wllh soo cool" Nihad tace "Aa baxan sha ba drink din nan ya isheni" Zully tace "Ke dadina dake kwabsin ki yayi yawa, don Allah ki Ι—an kurba idan bai maki ba sai ki bari kar ki sha, nima kinsan ai ban fiye son wines haka ba, amma tunda kika ga ina shan wannan ya kamata kisan ba karya" Nan duk suka mata caaa akan cewa ta Ι—andana idan bata ji dadinsa ba sai ta bari, Husnah ta cika mata glass din gabanta tace "Kiyi sipping first ki ji" Nihad ta dauka ta kai baki ta kurbi kadan, bayan few seconds ta wara ido tana kallonsu tace "Waow its really nyc, it tastes good" Husnah ta kyalkyale da dariya tace "Ba na gaya maki ba da kin tsaya kin kwabsawa" Nan Nihad ta kwankwade wine din, Husnah ta kara cika mata glass nan ma ta shanye, Naff sai dariya take tana cewa "Wllh ki bar ta haka Husnah tam ni dai na gaya maki" Husnah tace "Toh meye a ciki ai baya wani bugarwa" Haka dai Nihad ta sha wine tayi nak, party din da ba a karasa da ita ba kenan tayi ta masu layi a wajen, banda dariya babu abinda suke mata, Husnah tace "Kaii amma jininta ma bai da karfi wllh, Ι—an wannan wine din shine xai bugar da ita" Nan suka ci gaba da shagulgulansu, Nihad kuwa ta kife kai a wajen sai bacci, ba a tashi birthday din nan ba sai karfe dayan dare, Husnah ba irin tashin da bata yi ma Nihad ba amma ta ki tashi, da ta dagota xata koma ta kife kai, wani abokin celebrant din yace "Na kama daki a nan why not kawai ku barta ta kwanta ta huta" Husnah tace "Aa nasan halinta tana farkawa xa mu samu matsala da ita, kawai dai kamata yayi mu ma a kama mana dakin dama dare yayi ba lallai a bari mu shiga schl ba yanxu, idan ya so duk sai mu kwana a nan" Ba don ransa ya so ba haka nan ya kama masu dakin, suka ciccibi Nihad sai dakin suka kwantar da ita saman gado, Husnah dai na ta kaffa kaffa da Iphone din Nihad a wajen tunda ta san halin wasu daga yan matan dake wajen. Sai kusan biyu suka kwanta a dakin bayan duk sun yi wanka.     

Karfe hudu da rabi Nihad ta farka da wani axababben ciwon kai, da kyar ta mike xaune tana bin dakin da kallo, sai kuma ta sauka tana layi ta nufi kofar dake dakin wanda bandaki ne, ta kuma sani tunda sun saba lodging a wajen ita da su Husnah, tana shiga bayin bayan tayi fitsari taji wani amai ya taho mata, nan ta dinga kwarara aman tana rike da cikinta dake juya mata, da kyar ta wanke bakinta bayan ya lafa mata ta fito, bata sake komawa baccin ba sbda ciwon kai me tsanani da ya takurata, ganin biyar ya kusa ta ta6a Husnah da kyar, ta fi minti goma tana tada Husnah dake xuba minshari kamar wani kato, kafin ta bude ido cikin magagin bacci tace "Wai ya aka yi Nihad?" Da kyar Nihad tace "Don Allah wa xai yi dropping dina gida kafin yan gidanmu suyi noticing bana nan, asuba ya riga yayi" Husnah ta ja tsaki tace "Tsakar daren nan wa xai wani kai ki gida kowa na bacci, ki bari gobe kawai" Nihad tace "Ke asuba fa yayi ki duba agogo ki ga, wllh na manta yayanmu na gida zai iya xuwa bedroom dina yace xai tasheni inyi sallah, idan yana gari duk yana tashin mu...." Husnah tace "Ohh God Nihad ki barni inyi bacci mana, haba" Daga haka ta juya ta ci gaba da baccinta, tashi Nihad tayi da kyar ta bude jakarta ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta bude kofar dakin ta fita, babu kowa reception din hotel din sai tv dake aiki, ta fita haraban wajen, wani mutumi ta gani xaune yana ta xukar ta6a a waje, ganinta ya kashe ta6ar, ta nufesa tana kallonsa ganin bahaushe ne tace "Bawan Allah idan babu damuwa ina son taimako wajenka don Allah" Daga sama har kasa yake kallonta yace "Taimakon me?" Tace "Nasarawa GRA nake son ka ajiyeni pls, kawayena da muke tare da su bacci suke ni kuma ban xo da motata ba" Yace "Ohk babu damuwa, bari in dauko makullin motata" Tace "Toh Nagode, nima xan dauko jakata" Daga haka duk suka koma ciki, ta shiga dakinsu, shi ma ya shiga nasa, ta tattara komai nata a jakarta, wayarta ne kawai bata gani ba, zaro ido tayi lkci daya hankalinta ya tashi ta fara tashin Husnah a rikice tace "Husnah ina wayata??" Da kyar Husnah dake ta snore kamar doki ta bude ido, a fusace tace "Ohh my God Nihad ki kyaleni mana inyi bacci, me yasa kin fiye takura ne wai" hankali tashe Nihad tace "Dalla can ina wayata??" Husnah ta ja wani dogon tsaki ta daga pillow dinta ta zaro wayar ta ajiye mata a gefe sannan ta ci gaba da baccinta, Nihad ta sauke ajiyar xuciya sannan ta dau jakarta da wayar da sauri ta fita, Tsaye ta gansa a haraban hotel din yana jiranta jikin motarsa, bayan ta shiga motar shi ma ya shiga, suna fita daga suite din yace "Ku ne ku ka yi birthday jiya?" Gyada masa kai tayi kawai, yace "Gaskiya ne, birthday din na manya ne" Duk surutun da yake Nihad ba tankasa take ba, banda tashi babu abinda xuciyarta yake, she was so uncomfortable, a haka ta dinga daurewa tana masa kwatance har suka isa dai dai inda su Husnah suka dauketa daren jiya, yace "Ina gidan naku?" Ta nuna masa wani layi dake a rufe tace "xan karasa da kafa, kaga gate din a kulle yake" yace "Ohk amma ya sunanki?" Cike da karfin hali tace "Aysha" yace "Maa sha Allah, Aysha ki bani digit dinki mana" ta gyada masa kai kawai, ya mika mata wayarsa ta amsa tayi dialing wani old line dinta dake a kashe tace "Wayar a kashe yake sai na shiga gida na kunna" yace "Toh shkkn nagode Aysha ni sunana Mustapha" tace "Nagode, sae anjima" daga haka ta bude motar ta sauka, cike da karfin hali take tafiya don jiri ke dibanta, ta shiga layin da ta nuna masa, sae da ya ga tayi nisa sosai a layin sannan yayi reverse ya bar wajen, tana waigowa taga ya wuce, ta juya da sauri ta dawo ta fita daga layin sannan ta dau hanyar nasu layin, gani tayi kamar an idar da sallah bayan ta iso kusa da gate din gidansu, da sauri ta bude karfen inda aka xagaye da flowers a kofar gidan nasu ta shige bayan flowers din ta buya tana maida numfashi, don har an fara fitowa daga masallaci, tana jin aka shiga cikin gida aka kulle gate, Sai kuma ta sake jin an bude gate din, Muryar Abbanta taji yana amsa gaisuwa nan bakin kofar gate din, sai da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta, ta kara yin lamo a cikin flowers din duk da ant da taji suna cizonta bata damu ba, ta fi minti bakwai a haka bata sake jin motsin kowa ba bakin gate din, hautsinewa cikinta ke yi taji amai na taho mata, kokarin fitowa take yi daga flower din don ta samu ta shige cikin gida, kawai taga mutum xaune a dakalin dake kusa da inda take labe, sai da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta don duk xatonta ya Farooq ne don shi ma ya kan xauna a waje idan aka idar da sallah, ya daga kai jin motsi, sai kuma ya mike tsaye da sauri, komawa baya yayi yana kallonta with surprise, ita kuwa tsabar tsorata aman da take rikewa ya taho mata, ta durkusa ta dinga kwarara aman a wajen, kauda kansa yayi bayan yayi perceiving din aman da take yi, ya sake kallonta this time around da wani expression a fuskarsa, duk sae da ta amaye sauran liquor din cikinta sannan ta mike da kyar, ko kallonsa bata yarda tayi ba ta shige gate din gidan, ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, ko second ashirin ba ayi da shigarta ba sae ga mai gadi da gudu ya fito waje yana kallon Khalil yana zare ido yace "Ina me tabbatar maka bata kwana gida ba, dawowarta kenan daga duk inda ma taje wllh" Khalil dai bai ce komai ba, mai gadi ya yamutse fuska yace "Ni warin giya ma nake ji, ko kai baka ji ba don Allah?" Khalil ya juya ya shiga gate din gidan ya xauna nan saman bench dake gefen dakin mai gadi with numerous thought running his mind, mai gadin ma ya shigo ya zauna yace "Ni fa sai nake ganin ma kamar warin giya take ko kai baka ji ba?" Khalil ya kallesa yace "Amma baka wanke bakin ka ba ko?" Mai gadi ya Ι—an zaro ido, sai kuma yayi yake yace "Ai shi xan wanke ma na fito yanxu..." Tashi yayi da sauri ya shige dakinsa, Khalil ya kalli hanyar gate din, sai kuma ya mike ya fita, jakanta da ya hango cikin flowers da ta bari ya dauko ya shige cikin gidan sannan ya nufi chalet dinsu, A parlor ya tadda Su Saminu sun yi dai dai duk suna bacci, ya ciro makullin daki a aljihu, ya bude dakin sannan ya shiga ya kulle kofar, xaunawa yayi gefen gado ya bude jakar, takalma heels ya fara cirowa da kayan kwalliya da turarruka, sai iphone dinta da ya gani, ya dinga jujjuya wayar don a lock yake, sai kuma ya ajiye ya ci gaba da ciro sauran kayan jakan, bai san sanda ya bude baki ba ganin kwalban Codeine, can ya ajiye a gefe, ya bude wani zip dake cikin jakar, still yayi ya dinga kallon abinda ke wajen babu ko kiftawa, ya kai hannu a hankali ya cirosu gaba daya yana jujjuyawa, prophylactics ne na maza da na mata, ya ajiye su a gefen gado ya mike ya nufi window din dakin yana kallon waje babu ko kiftawa.

Nihad na fitowa daga wanka aka bude kofar dakin, sae da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta don tsoro, Umma ce ta shigo dakin ta rufe kofar murya can kasa tace "Daga ina kike Nihad?" Nihad ta daburce tace "Ni Umma?" Umma tace "Aa ban son karya ba yanxun nan naga giftawarki ba na fito daga parlon Abbanku?" Nihad tayi narai narai da ido tayi shiru, Umma tace "Gaya min gaskiyan inda kika je" A hankali tace "Wata kawarmu ce ke birthday Umma" Umma tace "Ki dai nutsu, in ma xaki birthday ae sai ji gaya min ni baxan hanaki ba, amma baxa je makarantar yau ba bacci xa kiyi ko?" Tace "Aa xan je" Umma tace "Toh sai kiyi ki shirya karki makara" Daga haka Umma ta juya ta fita, Nihad ta sauke ajiyar xuciya, sai yanxu da ta sake wani aman da xata yi wanka taji ta Ι—an fara dawowa dai dai, kanta ya daina juya mata, tana gaban madubi tana shafa mai ta tuna da jakarta, xaro ido tayi ta mike da sauri ta dau hijab dinta gogagge ta saka sannan ta fito daga dakinta, downstairs ta sauka ganin Farooq a xaune dining area tace "Yaya ina kwana?" Yace "Kina jin ina Knocking ki ka ki bude kofa daxu?" Tace "Aa yaya ina bandaki ne, ai na tashi sannan ma" Bai ce komai ba, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ta bude kofa, yace "Ina xa ki?" Ta marairaice tace "Xan je in duba ko Allah xai sa tsuntsayen sun dawo" Murmushi kawai yayi ta juya ta fita, da sauri ta nufi gate, taji dadin ganin mai gadi baya bakin gate din, sannan khalil ma baya wajen, tana bude gate ta samesu su biyu xaune kofar gidan, suna hada ido da khalil ta daburce, sai ta hau kame kame, bata amsa gaisuwar da mai gadi ke mata ba tace "Aminu a layin nan babu inda zan samu katin waya?" Aminu yace "Inaa, Hajiya ai sai an fita can supermarket" Tace "Ohk" Da gefen ido ta dinga lekan cikin flowers din dai dai inda ta buya amma bata ga alamar jaka ba, nan hankalinta ya tashi sbda wayarta na ciki, bata san lkcn da ta karasa wajen ba tana kara dubawa da kyau, Aminu yace "Wani abu kike nema ne Hajiya?" Wani shegen kallo tayi masa tace "Toh ina ruwanka?" Khalil dai na ta danna er karamar wayar hannunsa, ta saci kallonsa.

07087865788✍🏻

No comments

Powered by Blogger.