Namijin Zuma 2

 


Free page 2

Tafiyar 10mnt ta kaisa wani katafaren gida na fitar hankali, gate din gidan golden light color ne, ,Kai daganinn get din gidan kasan na wadanda sukaci suka tara ne, sunfi karfin

yau dinsu.   Hon daya yayi aka wangale masa get sbda ganin lambar motarsa da akayi, me tambarin AS da ARMY ta sama.. Danna hancin motar yayi cikin gidan ya isa packing space yayi packing ya fito se Wani murmushi yakeyi idanuwansa sun cika da kwad'ayin san ganinta, kusan 2month kenan yau besata a ido ba sede waya kawai sukeyi a Kai a kai.  daya bar garin Ayyuka ke masa yawa over, duk ayyukan da yakeyi Amma cikin waya suke da ita komi zeyi seya gaya mata,ko kaya ze siya seya tura mata ta zaba masa wanda takeso. Tsayawa yayi ma'aikata suka shiga zuwa suna tsugunnawa suna jero masa gaisuwa, yanata amsawa fuska cike da fara'ah, haka kawai yaji a jinin jikinsa kmr ana kallonsa, juyawaar dayayi zuwa  window ya hangota tsaye tana kallonsa. "Wow! You are always beautiful, kyauma dole ya gaidaki mommahma,,,," ya fadi a hnkali yadda bame jinsa, ya sakar mata murmushi itama murmushi ta sakar masa Hadi da matsawa daga jikin window yadena ganinta. "First Darling..." ya fadi yana me dafe saitin zuciyarsa, a kullum zuciyarsa na yawaita bugu in har ya ganta ko in ze ganta, yasan soyayyace ta uwa dayake mata take sashi jin hakan a kanta. Ba tare daya gama Amsar gaishe gaishen ma'aikatan gidanba ya wuce abinsa zuwa babban falon gidan,  Bakinsa dauke da sallahma ya turo kofar falon ya shigo, tsaye take ta jingina bayanta da bango, sanye take  da rigar Material red me  flowers Green and goolden.   From down to up ya fara kallonta. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" Ya fadi can kasan zuciyarsa, kyaunta ya shahara ubangiji ya loda mata lodi-lodin kyau ,fara ce ita sol harda rodi rodin red-red a jikinta, kafafuwanta tamkar bata taka kasa, bul-bul sun ciccika tanada zara zaran yatsu, A kalla size dinta baze wuce 37-36 ba. Tanada cikakkiyar fuska O face ce da ita, dara-daran idanuwanta tamkar zasu fado kasa Dan girmansu, Tanada yalwal gashin Ido dana gira, yayinda girarta ta hade da juna har xuwa goshinta cike yake taf da gashi , tanada dogon hanci sosai, bakinta dan mitsitsi kai bakace yatsa ma ze iya wucewa ta cikin Bakin nata ba, tanada da kyau, kyaun daban taba ganin me irinsa ba duk duniyar Nan, tanada Dimples din gefen Kumatu, ta cikin bakinta kuma tanada kananun hakora kmr na yara, yayinda takeda siraran wushirya sama da kasa,   matsakaiciyace a fannin tsawo, ita ba doguwa bace, ita ba gajera ba, sannan bata da kiba kuma ba siririya bace Amma Aeezad zeyi biyunta a jiki Sam bata da jiki, normal-normal, Amma hakan be hana siffar jikinta bayyana ba, tanada cikakkun nonuwa yayinda suka cika kirjinta taf-taf, cikinta a shafe yake, ta kasa kuma kasanta cike yake da uban hips bata da zungurun duwawuka sosai, sede hips ne da ita na fitar hankali, duk iya, iya hassadarka da makircinka da fasikancinka da gulmarka baka isa ka hango  muni a tattare da ita ba, a kallah shekarunta sun kai 32yrs amma baka isa ka gano shekarunta ba zaka rantse da Allah yar 20yrs ce , kyaun jikinta ya shahara, ita irin matannan dasukeda wuyar samu Benu ce ita Sam bata tsufa, karamin jikine da ita. "Kin tsaya kinata kallona ta window ko mom...." Cewar Aeezad, Nabeelah batace masa komi ba. Kmr an tsungukeshi yace ", Kinada kyau na Izaya mommy ...."Aeezad ya karashe fadi da cooling voice dinsa, smiling tayi masa yayinda seda wushiryarta ta bayyana Hadi da Dimple dinta. Batare datace komi ba ta karasa kan Daya daga manya manyan royal chairs din falon ta zauna, ta dago ta kallesa ta sakar masa karamin murmushi  Cikin zazzaka zukekiyar voice dinta me sanyi ta fara magana "Jarumi na mommynsa, kuma nanny dinsa..!'' ta kauda mgnrsa dacewa hakan domin Sam bataso yanace mata tanada kyau, dukda a kasansu take Amma sam bata daukar raini tanada rike mutumcin kanta, gani takeyi in yanace mata tanada kyaunnan ma alamomin raini vnw iya shigowa inta saki jiki. Wani sanyi yaji a zuciyarsa, sbda sunan data kirasa dashi, Nan da Nan ya narke, kmr me Shirin fashewa da kuka. "Inasan sunan Nan kinfi kowa iya fadinsa first Darling..." Cewar Aeezad da yayi mgnr fuska bawani nishadi. Tsura masa Ido tayi tin shigowarsa data lekasa ta windowo ta kula da damuwa a tattare dashi, duk duniya ba wanda ya kaita sanin wayeshi, tasanshi ciki da bai, tin batasan kanta ba ta rainesa tin yana jariri da hannunta, sanshi dake zuciyarta daban ne ji takeyi tamkar ita ta haifesa da cikinta, daukar cikinsa ne da haihuwarsa kawai batai ba, amma tasan San da take masa ko mahaifiyarsa iya abinda zata masa kenan. "Mommyna Aunty hafsa dasu Asmah da Noor  basa Nan ne?"cewar Aeezad. Daga masa Kai tayi still dara-daran narkakkun idanuwanta na kansa ta bude Dan karamin bakinta tace "AUNTY HAFSA  Ta tafi office, su Asmah da Noor suna school kasan yau monday....." Yana daga tsaye yayindaya zubo mata idanuwa shima kmr yadda itama ta zubo masa cikin nazartarsa. "Okay,,," cewar Aeezad.  "Zoka zauna Babyna Wani Abu na damunsa ka gayamin inji waya tabomin dan nabeelah ." Nabeelah ta fadi cikin tarairaya da kwantar da hankali, ta karasa ta zauna kan kujerar 2ctr. Ai kamar Aeezad na jira ya karaso ya zube kasan carpet ya daura kansa a kan cinyoyinta, ya fashe da Wani irin kuka kamar jariri Dan goye, besan meyasa ba, inde yana gabanta seya dinga jinsa kamar wani karamin yaro Dan 2yrs Sam beda dauriya inde a gabanta ne. Yadda yake kukan ya daga mata hankali Nan da Nan ta daburce ta gigice ta kid'ime ta shiga dimauta, uwa uba ma seda taji hawayensa na taba cinyoyinta ta kara rudewa , yadda hawayensa ke sauka a cinyoyinta tamkar a zuciyarsa yake sauka, Nan take garwashin tashin hankalin da damuwa ya ruru a zuciyarta. Yadda yake kukan ya tabbatar mata dacewa ya jima yana jure abubuwa a zuciyarsa, har cikin kasan room and farlo din zuciyarta takejin kukan nasa, jikinta ya mutu murus yayi sanyi karai, inside itama knr tasa kukan takeji batasan kukansa kwata-kwata. "Bana yafiya ga duk wanda yasamin Kai kuka babyna, Dan Allah kayi hakuri banasan abinda ze taba zuciyata, tamkar barazana ce ga lafiyar jikina..." nabeelah ta fadi yayinda muryarta ke cracking itama ji takeyi tamkar ta fashe da kukan,batasan kukansa sam, batason bacin ransa,ta tabbatar san da take masa ko uwarsa ke raye iya abinda zata masa kenan wallahi, a wani fanninma setafi uwarsa sansa. "yi Shiru Jarumi na Nabeelah,kasan kukanka namin zafi a kasan zuciyata, turiri zuciyata kemin..." Ta fadi a dimauce yayinda ta lumshe idanuwanta ta sake budesu a kan kansa dake cinyoyinta, cusa hannunta tayi cikin sumar kansa, still se kuka yakeyi ,shi da kansa yasan batasan kukansa, amma besan me takejiba in taji kukansa daya sani da ta tabbata bazeyiba, shi dayake kukan tafishi shiga tashin hnkali da damuwa in Yana kuka,,. "Dan Allah kayi shiru ka gayamin waya tabaminkai babyna, please na rokeka kayi shiru Dan Allah kukanka barazana ce ga lafiyar zuciyata, kasan uwa batasan jin kukan d'anta,da kayi kuka sau daya,  wallahi kwara ni nayi kuka sau Dari  ..."ta sake  fadi da sanyayyiyar muryarta dake cike da  tashin hankali,yayin data shiga kokarin dago fuskarsa, ta rike fuskar tasa da tafukan hannayenta biyu, still har yanzu kuka yakeyi, ya kureta da idanuwansa daketa zubda kwallah sunyi red irin red dinnan sosai, ganin hakan ya kara rud'ata. "Banasan kukanka haba jarumina Dan gatan mommynsa, haba babyna, haba Nurul Aini na nabeelah..." Ta fadi hakan da sigar rarrashi sosai. Tsagaitawa yayi da kukan nasa, sbda kirarin ya ratsashi over, shiyasa in yana cikin dmwa ita kadai ke saitasa,ta iya rarrashi over., takai yatsunta biyu ta share masa duka hawayen dake kan fuskarsa, ta sakar masa murmushi me kwantar da hankalin me kallo. "Yawwah ko kaifa Dan gata na nabeelah, toh ynzu Gayamin waya tabominkai jarumi na nabeelah...." Ta fadi yayinda takejin kmr ta bude cikinta ta maidasa sbda SO da kaunaR datake masa baze misaltuba, ko sauro bataso ya kusancesa. Ai kamar Aeezad na jira ya fara jero mata damuwarsa tamkar ze fashe haka yakejinsa. "Mommy yanzu abinda na'eema takemin ta kyauta kenan ? Sbda Allah fa? Gaba daya tazama yar  shegiya,  Wannan wani irin Aure ne tsakanina da na'eema, tinda mukayi aure yanzu kusan 2yrs kenan bata taba 1month a gidana ba, nace tabini abuja taki, kuma inna dawo bana samunta a gida kullum tana gidan mommy,  Mommy na turata kasashe kasashe tana saro mata kaya, gabaki daya ba aikin hankali a lamarinnan,, babban bacin cikina ma duk cin da nake mata har yanzu ko bari bata taba yiba, hajiya mommy ce  tace wai karta haihu inta haihu waze dinga zuwa mata kasahen waje saro kaya? Hmmm,, This girl na'eema jiya Dana kirata wai harni take gayama itafa bata daukeni a bakin komi ba,tafisan uwarta dani,, taso mafa ta zageni a kan gaskiya ta Jiyannan ,kawai dannace Se Allah yasakamin a kan yawo datakeyimin da igiyar Aurena a Kanta,, totally yarinyar Nan ta rainani mommy wai ace kamar ni ina matsayin commander din Army , wai yarinya  karama da bata wuce 19yrs ba yanzu ni take gasawa maganganu, Ga raini kmr sa'nta,, ....nayi nadamar auren Na'eema a rayuwata,  tinda na Aureta ban samu kwanciyar hankali ba, gashi Sam ban isa da ita ba, hajiya mommy ce  ke  controlling dinta, kuma ita ke controlling min Aurena da ita, kmr yadda take controlling daddy haka  take controlling aurena dani da na'eema,,Sam na'eema bata gayamin zata fita, sede in dawo katsina inga bata Nan inna kirata tace tana Egypt ko Landon ko America,,  kinsani de da kanki mommy Allah ya jarabce ni da soyayyar na'eema wallahi ji nakeyi kmr bazan rayu in bata ba...abin ya isheni ne shiyasa na gaya miki mommy nagaji, ynzu ma daga gidan nake inaso muyi mgna da daddy mommy taki bari, se daga baya ma nayi tunanin kawai kwara na barwa zuciyata saboda kona gayawa daddy  baze amfanamin komi ba, tinda shima se abinda mommy tace, Sam daddy bashi da katafus a komi nasa,... nagaji wallahi mom, kuma gashi kin hanani bin mata...'' ko numfasawa beyiba seda ya Kai Aya, zuciyarsa na Kuna   ya langwabe Kai a kan cinyoyinta masu azabar laushi,,kawai yasa ne Amma ba iya damuwarsa ba kenan, kai dagani kasan akwai sauran abubuwa dasuke cinsa inside.  Nabeelah ta tsuresa da Ido tinda ya fara mgna har zuwa yanzu kallansa kawaii takeyi yayinda tausansa ke shigarta, daman ai ance duk wanda yase rariya yasan zata zubda ruwa, kullum problem din Aeezad na'eema da hajiya mommy.  Ajiyar zuciya nabeelah ta fara saukewa a hankali kana ta fara magana cikin nutsuwa da hankali. "First de kmr yadda na saba fada maka a kullum kayi hakuri please, komi na duniya dan hakuri ne, kuma komi me wucewa ne, shiyasa akeson hakuri da juriya da dauriya a kan komi na duniya, balle lamarin Aure wannan ai dole se kayi hakuri,  kaga ita hajiya  mommy matsayin uwa take gareka, so kaga Uwa kuwa lallabata akeyi a gama da ita lafiya, kaga hakurin zaka ci gaba dayi kawai, dan Allah banasan abinda ze tabamin zuciyarka kwata-kwata Aeezad na nabeelans..."  Aeezad yayi  hanzari amshewa da "Hakuri hakuri kullum mom, saboda Allah fa,inni nayi hakuri a zahiri ai Wani abun besan hakuri ba,,,saboda Allah nan kiri-kiri kika hanani komi, inada beb dina Esther mom kika hanani zama da ita kika sani na Rabu da ita, kuma mom kinga saboda kar in dinga ciye-ciyen gindinayen mata yasa nayi Aurennan da wuri ba tare dana nuna ba, ban tafasa ba, ban isa aure ba, Amma nayi hknan, toh kinga Auren yadda ya kaya wallahi kwarama babu,kawai ni yanzu na yanke hukuncin zan dawo muci gaba da rayuwata da beb dina Esther kawai se in kyale mommy da yart...." Kafin ya karasa tayi saurin rufe masa baki Hadi da hade Rai kmr ba ita ba, Nan da nan ta chanza kamar bata taba dariya ba , ta shiga sirfafo masa jaraba da masifa. "Zina kakeso ka koma kaci gaba dayi kou?zinar ma da kafura mara tsarki najasa,  Wadda kayi ada bata isheka bane? Me kakeso ka maida rayuwarka ne Aeezad? Kasan illolin zina kuwa Aeezad? Kai kawai dadin kake hange kou?"  ta fadi cikin kunar Rai murya cike da ruwan matsifa da bala'i, in yayi maganar zina setaji kmr ta dauko bulala ta rusa da Dan banzan duka.


No comments

Powered by Blogger.