Najma 5-6
👄👄👄👄👄👄
*NAJMA*
💋💋💋💋💋💋
By maman noorul hudah
This page naku ne masoyan asali da Banda ku ba da Banda niyyar Fara novel yanzu,thanks for always loving me....anty haddy,anty Aisha dahiru,da dai sauransu I appreciate you guys
🅿️5️⃣❤️6️⃣
Bismillahir Rahmanir Rahim
Tace"toh miye dan ance su sake kissa nace suyi ai bani na hadasu ba tun farko bare a had'a ni da shaidani kallon na zoyi in samu ladan gudun da nayi shine za a wani so a zageni
Ya rigada yasan halinta ba kunya ne da ita ba ya kalli delu yace"deluwa jeki gida in ba so kike a Miki duka ba "
Da Ido tayiwa deluwa alaman da karta tafi Kuma ya gani saiya girgiza Kai yayi tafiyarsa Yana Mata addu'ar Allah ya shirya
Cikin d'aga murya tace"Amin ai addu'a kayi "tana ganin yayi Nissa ta dibi kasa ta cika a hanun ta ta dunkunle taje gaban deluwa da sadiya dake Harare haranre juna tace"in kun San kun Isa ba tsoro kuke ba ki d'auki wanan ta hagun ta matsifa ne ta damar ta balai
Dukkaninsu suka d'aki hanunta
Ta buge kirjin deluwa da ta sadiya tace"in kun Isa ku Rama a jikin junanku
Deluwa ce ta Fara kaiwa sadiya Mari tuni dambe ya kacame tsakaninsu,uwani ta koma gefe ta natsu tana kallonsu dambe yayi dambe har zanin deluwa ya kwance ,itako sadiya rigarta ta yage nononta da ba wasu girman ne dasu ba Suka bayyana
Ganin suna son su raba kansu Dan sun gaji yasa uwani sakin Waka tana cewa ku casu arna ku casu, ku casu ba me raba ku
Cikin daga murya tace" ke deluwa karki barta cire Mata hakora,kema sadiya karki barta sai kin fidda rainin "
Har Kan hanya suka hau Dan Jin maganar uwani suke Kamar na uwarsu
Wata tsadadiyar motace ta danno Kai horn ake Kamar za a kurmatasu ganin sun saki juna uwani tace"karfa ku damu da masu motar nan kuyi kamar Baku San dasu ba ku cigaba da damben ku
Cakume juna Sukayi suna son cigaba dukda sun gaji
Bude driver side akayi kafarsa dake sanye da tsadeden halfshoe baka data karbi fatar jikinsa kasancewarsa fari tas,jikinsa sanye da coffee shadda da hula me coffee baground sai milk zare da akayi aiki dashi sai kamshi yake
Fitowa yayi ya zuba musu Ido tare da ciren bakin glass din da ya karbi fuskarsa
Jinjina rainin wayau Yan kauye yake
Dan satar kallonshi uwani tayi kafin tace"ko wanene ya nimi Hana wanan fadar Allah ya tsine Masa albarka,Kuma sai ya ci Mai garinsu ko wanene shi
Shafa Kai yayi ya zuba Mata Ido duk sai ya ganta a fige ma'ana dai kana kallonta ka gan cikkakiyar Yar kauye Mara kunya
Kwafa tayi dan har ga Allah haushinsa take ji dan cak su deluwa Suka tsaya da dambe tayi ta tsaki sai a yanzu Suka ji kunya kasancewarsu ba Kaya ita Kuma sadiya sai Kare kirjinta take
Ganin inda tayi kicin kicin da fuska tana kunkuni
Sai ta bashi dariya ya karaso ya d'auki zanin delu ya Bata ta d'aura da alamu taji jiki Daman kiris take jira sai ta fashe da kuka
Baki sake cikin zigi uwani tace"delu Wai kuka zakiyiwa sadiyar nan ah lallah raini bazai fita tsakanin ku,wawiyya bazaki Kai Mata bugu ba ki nuna kema shegiyar Darin ce
Zuba Mata Ido yayi ganin irin kallon da yake Mata yasa ta Kau da Kai tace
Maman Nur
Leave a Comment