My Lady Boss 8

 


Free page

              .......8



     Marubuciyar:

(1)Bafullatnn ruga

(2)Ƴar aikina

(3)Walijaam

(4)Ƴar waye 

(5)Gidan kwarata

(6)Gidan zaurawa

(7)Ƙwaryar sama 

(8)Bintoto

(9)Ƴar maula

(10)Habibi da'iman

(11)Dijama ƴar fulani

(12)kawaliya

(13)Ƙwartn manya

(14)Zuma da maɗaci

(15)Taɓarah

(16) Siyasata

(17)My Lady Boss


*****

_Idan kin San kan ki baxai ɗau abun dake ciki ba,bazaki iya jura ba ,don Allah kar ki karanta ki dawo mun da zancen kutumelesi...ban san wani kitimurmura labarin Romantic ne👌haka kema idan kin san zaki saya ne don ki fitar mun na yafe ki adana kuɗin ki, kar ki fitar mun adawo mun da zancen gntlw.....masoya na billions naji saƙon nin ku gareni ina gdy Allah yabar🫶_


_*Free page na dab da ƙarewa,Zai ƙare a page 10 inshallah...ku hanxarta wajen biyan kuɗin littafin LADY BOSS domun jin daɗin ku na cigaba da karanta wannan labari , kin shirya biya?? Na shirya! To yanda tsarin biyan ya kasance... Regular payment ₦300 vip payment₦500 special payment ₦1000...zaku iya turo da kuɗin ku ta wannan asusun bankin 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank...ko kuma ki tura katin MTN naki ta wannan number 08081202932...Idan Vtu trnsfer ne ki tura ta wannan MTN number 09061466409 sai ki tura da shaidar biyan ku duka ta wannan WhatsApp number 08081202932 asha karatu lafiya...*_


_SADAUKARWA GA MUTAN ZAZZAU gami da godiya ga masoyana billions ko trillions ne gdy duk😍😂_



***


Miƙewa Diyana tayi tana fichewa daga Station tana mawa ƴan sandan godiya suma suna mata , tare da jajanta wannan hali nata ,macen zata kawo mijin ta Station a wannan marraba ai abun mamaki ne da kallo.. Diyaana kenan ita take koman ta a cikin gidan mijin ta yarinya ƴar shekara ashirin da huɗu ,ko wani nauyi ita ta ɗauke a wuyan ta.... Hattara mazan wannan zamani masu hali irin na Ɗan Asabe da kuma mijin Diyaana , ba ko wacce mace bane take haƙurarra , wata in tayi haƙuri wata bafa zatayi ba...mu dingi kyautatawa matan mu sai gidajen Auren mu ya dauwama cikin farin ciki da annashuwa .



***



Kwanan su biyu suna tafiya daga Lagos zuwa Zaria , wanda a hanyan su na isowa gab da garin Zaria ne suka ga abin da basu taɓa gani ba, shine Fashi da Rana tsaka .... Salati Sumayya tasa tana faɗin dama na faɗa maku wallahi mu gudu , kuɗin hannun mu zasu ƙwace dama sauran na mutane...Harbin tayan Driver n nasu akayi , wanda don dole suka tsaya moton na wani irin kugggi a kwalta.....Alamu sukayi da su fito , wanda cikin salati tare da kalmar shahada kowa na moton nan yayo waje.....Ciki harda Su Sumayya da suka gama tsarawa kansu abinyi a ƴan sekanni.



Fitowan su ke da wuya , wata mace da ta rufe fuskar ta da Shadow spce ta kalli mazan ƴan uwan ta biyu tana cewa " Ku leƙa ko da saura...jin haka yasa su nufan moton don su leƙa , Safna ne dake bayan ta aƙwance ta miƙe cikin sanɗa tana maƙurar wuyan ta , wanda motsawa takasa yi alama take mawa sauran amma ina sam basu luraba. Sumayya ce ta saɓa Umma suna yankan daji da basu san inda zasu dosa ba.....Laurat tayo bayan su, ganin haka yasa mutane miƙewa kowa yana cin hanya ,wannan ya an ƙarar da sauran ƴan fashi , bugata Safna tayi da moton tana bin hanyar dasu Sumayya suka bi....wani irin harbi suke yi na kisa , don da dama sun sami mutane wasu kuma sun shaaa!



****


Wani irin dariya ne Addiya taji ya ɗauki ɗakin da take zaune ,wanda faɗin ƙawatuwan shi ba'a magana ". Cikin gusassar Muryar sa ta marasa imani da tsoron Allah taji ɗakin ya amsa da amon Muryar sa kaman haka" Hjy Adiyya har kin manta mune gomnati , don kina ɗan wannan matsayin taki ta ƴar majalisa shine zaki turo aga baya na? . Mu da mulki n mu muka baki! Cikin wani irin jan rai da rashin tsoro tare da dakewa tace " Kaci nasara a wannan karon , kasha da rayuwar ka , amma bance maka gaba zaka kuɓɓuce daga hannu na ba.... Wallahi indai ina raye Ni Addiya sai naga bayan malamai matsubbata irin ka ,Ni Addiya ba'a cuta na! 



Ke Addiya ya kamata ki shiga hankalin ki , kar ki manta da Gundumirƙi kike magana , wanda na kashe ki naka kashe banza , baza A tuhumi kowa ba , kuma baki da kowa da zai zauna maki koda zaman makoki ne ya ƙare yana wani sa Dariya na irin azzaluman matsafan nan..... Sai taji ɗiff ɗakunan nata sun bar juya mata . 



Lumshe ido Addiya tayi tana buɗe su ,kana tace " Kayi gaskiya gundumi Ni bani da kowa Ni marainiya ce, a cikin gidan marayu na taso ban san kowa nawa ba , wannan Matsayin da nake kai , da ƙarfi na na ƙwato shi har naxama , don haka Ni mutuwa bata bani tsoro a shirye nake da zuwan ta , indai akan son ganin bayan mugaye irin ku ne.



***



Basai na faɗa maku bana ji ba , ku sani a sahun masu ji! Suka ji Muryar wacce masu yi tsammani ba ya dirarar wa dodon kunnen su ...A matuƙar razane , suka jiyo suna kallon Bilkisuuuu da take zaune a wata itaciya hannun ta babu makami sam ,kan ta kuma a ƙasa. Inalallahi wai'ina ilaihir rajiun , baiwar Allah me muka yi maki? Ki taimaka ki bar mu mu tafi mun haɗaki da Allah. Cewan Sumayya tana ƙara riƙo Umman ta da take bin kowa da kallo.  


Ku bamu kuɗin hannun ku ku tafi cikin salama. Wallh baki isa ba , kin san yanda muka sane shi ne? . Cewan Laurat tana fiddo da idanun ta waje. 



Me yasa kk zaɓi wannan sana'ar zalunci n a matsayin ki ta mace? Mata da tausayi aka sansu bada irin....ke yi mun shiru Nice nan Bilkisu mai gado , ba zaku tafi da kuɗin nan ba indai kun tafi dashi to na tashi daga sunana ne. Kina faɗin Ni macace , a lokacin da yunwa yake damuna da ƙanƙantan shekaru na ,ina kuka ina cewa " Su bani abinci ko ruwan sha basu bani ba , da ƙarfi na na ƙwata daga hannun su , na zama sarauniya a fadata , na zama tantitiyar mara ji na fara fashi , yanxu sai ku kawo mun Allah ɗaya ne...ku bani kuɗin kona gwada maku damtse.



Shiru sukayi Idon su kaf ya kyakyashe babu mai iya kuka , Sumayya ne tace " Da hakan kika yi da yafi mana ,idan kin cika Bilkisu ki amashe kuɗin nan daga gare mu , ba  tare da makami ba , kawai ƙarfin naki , yanda ki ke taƙama kin wahala ,muma duk a wahalcen muke......wani irin zafi maganan Sumayya yayi mata wanda yasa ta miƙewa tana tun karo ta kai tsaye....zagaye ta sukayi suka rufa mata dambe suke na ƙwatan rai ,tabbas sun ji jiki a hannun Bilkisu , wanda Sumayya ce ta buga ta da bishiya nan take ganin ta da jin ta ya ɗauke , ɗaukar Umma tayi suna neman hanyan barin jejin....



****



Saukar jirgin yayi dai dai da fara saukowan Fahad cikin shigar ƙananan kaya da suka amshi fatan shi ƙwarai , ɗaga kai yayi yana hango Sir Khamal da yake sanye cikin shigar Trac suit arsh colour abin ka ga farar fata baƙaramin kyau sukayi mashi ba...Nufo inda yake Fahad yayi yana bashi hannu , suna gaisawa ba tare da kowa yace komai ba suka shige moton haɗi da barin airport ɗin take.....


****



Me napep ne ya kalli su Sumayya yana cewa " Hjy ina za'a kai ku? .shiru su duka sukayi don Basu san ko ina anan ba! Sumayya ne tace " Kai mu layin masu kuɗi a Zaria. 



Me napep ɗin ne yace" Aƙwai G.R.A , aƙwai Tukur Tukur , aƙwai kuma ƙaura...wanne ciki za'a kai ku? . Laurat ne tace " Yi mana bayanin ko wacce a ciki ya tsarin wurin yake?. 


Me napep ɗin ne ya basu amsa da" G.R.A. Nan ne unguwan masu kuɗi alhazan Zaria mny ƴan siyasa da sarakuna.


Ƙaura a cikin City yake unguwan masu mulki da sarauta kenan da ƙafarta , kuɗin akwai amma ƙaryar su tasha ƙarya....



Tukur Tukur unguwan matasan masu kuɗi yara samari da masu shekaru dai dai....kuɗi boko ƙaryar komai ya haɗaa

 A wannan layi . Aaa'aaa'aaaa kai mu Tukur Tukur cewan Safna da Sumayya suna haɗa baki a tare. Nan take me kafu babur ya kwana yana nufar tk road.



****



A tangaɗi ta Nufo Asibitin A.B.U tudun Wada...cikin tangaɗi take tafiya wanda kowa darewa yakeyi  yana bata wuri , kai tsaye inda likitocin ke zaune Bilkisu ta nufa ,kanta na xubda jini kaman jinin jikin ta zai ƙare....da sauri wata nurse tayo kanta don taimakawa ,amma sai ta ɗaga mata hannu alaman a'a .



Zama tayi a kujera wanda likitocin da ganin ta gaban su ya faɗi ,don ko ba'a faɗa ba sun san wannan tantiriya ce lamba ɗaya.  Kowa kasa tunkarar ta yayi sai Nurse Yusrah dake shigowa , cikin wani irin sauri ta nufo ta tana kama fuskar ta tana cewa " Nurse a bani bandeji da auduga ...cikin zumma suka miƙo mata , hannun ta takai tana fara masa treating raunin da taji , kana tace " Ina ƴan Uwanki ina Mama da ƙanni? Yusrah tayi maganan tana kallon Bilkisu , wanda cikin murya ta barasa alamu bayan abin ya same ta sai da tasha tayi nak sannan ta nufo asibitin...Nuna Yusrah ta hauyi da hannun ta kamin tace " nine Uwana nine uban kaina kuma nine ƙani Yayan kaina".



Wannan wani irin shashanci ne? Cewan Nurse Yusrah tana jan tsaki , tana cigaba da aikin ta don ganin ta tsaida jinin. Hannu Bilkisu takai tana amsan Almaka shin tana caka shi a raunin goshin ta da shima yake jini....wani irin rintse ido duka sukayi ,kamin tace" rana ta farko dana nema abu ya kuɓce mun , ina xan same wa'annan yaran? Dole na gansu naji su waye su? Taya suka samu kuɗin nan..... Cewan Bilkisu tana caccakar kanta da almakashin , jini ke da zuba cewan Yusrah cikin tsoro da tausayawa don ta fahimci a maye Bilkisu ke maganan.



Wai me kkce waye iyaye na? To babu ! Amma ke zaki iya zama iyaye na inkin damu da gani na a haka , shegun likita baku iya komai ba sai saka fararen kaya na banza da wulaƙamci , duk wacce bata zo inda nake ba sai......keeee waye sunan ki? 



Yusrah tayi maganan cikin fusata . Cikin Muryar ta da ya fashe tace " Bilkisuuuuuu . 



Yusrah ne ta amshe da cewa" jubiki fah Kaman ba mace ba ,waye zai taho inda kike a haka? Waye mahaukaci? Dole suyi baya , kince baki da iyaye , Ni na zama iyayenki , to naji duk da kasancewar kin girmemun indai zaki daina abun da kikeyi na wannan shan barasar a matsayin ki na mace , to ki zo gidan mu ki zauna dani , idan kuma kina da iyaye ina roƙon ki ki koma gare su......Sauran numfashin Bilkisu yasa Yusrah fahimtar bacci ne ya ɗauke ta saka makon allurar da sukayi mata. 



Sauran likitocin ne aka hau kallon kallo ,na shin da gaske Yusrah zata ɗauki wannan bugaggiyar takai gidan su ,ita da ke cida kanta ?". 


Ku ɗauko gado a sata , ku Kaita room 24 . Suka tsinkayi Muryar Yusrah ya katse su ,wanda cikin sauri suka fara cika umarnin ta....



****



Kallon mai hayan Safna tayi kamin tace " Ka taimaka mana dai ashekara dubu ɗari....mlm sabo ne yace " A'a indai yayi maku ɗari da hamsin to , saboda gidan nan fa duka ku zaku zauna ciki ku kaɗai ai hakan yayi ashekara.



Himm to bdmwa Laurat ku shiga mana da kayan ku mu fara gyarar gidan , ga kuɗin mlm sabo mun gode cewan Sumayya tana bashi kuɗin a dunƙule...washe baki sabo yayi yana godiya ". 



Safna ki zauna keda Umma mu bari da Laurat mu shiga kasuwan gari n nan mu haɗo mana kayan abinci ,kana na dawo mu nemi gidan aiki , don Ni dai aikatau zanyi ban san kan garin ba tukunna .mlm sabo zanyi ma magana ya nema mun gidan aiki sai mun dawo. 



A dawo lafiya Safna tayi masu tana shigewa ɗaki da Umma".



****



Gidan malam Ilu babu masaka tsinke saboda jama'a cike harda masu lapo dasuka zo zasu sai da gidan tare da tafiya da Sumayya....Ganin ɗaki babu kowa har kayan su wannan yasa su fahimtar Sumayya ta gudu....Ɗakin Lauratu a ka duba ganin ƙofa a buɗe ko ta ɓoye cike ne , nan da shiga aka ga ɗan Asabe tsirara ƙwance a sume haihuwar uwa n shi...Salati su Rita da Mmn mujahida suka sa suna fitowa da gudu maza na shiga ɗakin don  ganin halin da Ɗan Asabe ke ciki rai a hannun Allah warwassss.....


Mama Atine ce ta shigo zaf zaf itace uwar lapo tana cewa " gafa kuɗi tun jiya Sumayya ta aikomun da dubu ɗari da hamsin sharrrr....ɗari da Hamsin???? Matan gidan suka haɗa baki cike da mmki ,kamin suce to ina Sumayya na ?.




To ai wannan ban sani ba ,ku za'a tambaya Sumayya nidai nawa kuɗi kuma ta kawo mun tayi maganan tana masu lapo kuɗin su....suna amsa suka juya.




Ɗan Asabe aka ɗauko tarai-tarai kaman gawa ana fita dashi , mlm Ilu na watsa do muchiyan da aka buga masa tsakar gidan , dariya wasu suka gimtse ,wasu kuma na jajanta masa.



*****



Kwana huɗu a Zaria kuɗin Sumayya ya ƙare a cefane kuɗin moto dana kama haya...wannan yasa safiyar talata ta miƙe tana sa hijabi don fitowa neman aikin gida shara girki ko wanke wanke . Mlm sabo ne yayi mata rakiya zuwa wani gida kana yace kunga gidan idan zaki shiga a akwai wani inji da sai ya lacceki tassssss sAbosa tsaban dukiyar da Allah ya basu. Mai gidan yayi gomna yanxu haka ministar ne ,ki shiga da addu'a Allah yasa ki samu , to suna da yara? Ta tambaye shi kai tsaye... Eh kaman ɗan su ɗaya a duniya shima baya ƙasan nake tunani. 



To Mlm sabo na gode. Sumayya tayi maganan tana nufar tamfatsetsen gidan kaman hotel saboda girma da tsaruwa ....Sai da masu tsaron gidan suka gama mata tambaya da lacce sannan suka nuna mata hanyar sasan matan gidan... A farfajiyar gidan ne tana can tana tafiya tana mmkin wannan wani irin daula ce da dukiya aka zuba a gidan nan kawai taji tayi kiciɓus da mutum , waya na faɗi ƙasa nan take ya tarwatse.....




Oh God! Matsalar ƴaƴan talakawa kenan duk idan suka zo wuri a Sara ce , taji wata murya cike da masifa ta ɗirar mata. Saurin kai hannun ta ƙasa Sumayya tayi tana cewa " Kiyi hƙr ta ɗago ta na miƙa mawa  BINAFA wayar ta, wanda hankaɗe Sumayya tayi tana nufan moton ta tana shigewa , don kun san ta dawo Gidan Hjy Juwairiyya da zama.....


 topa! ƙaƙaƙaƙaƙa.......koya abun zata kasance ,shin mahaifiyar Sir Khamal zata ɗauki Sumayya ko ko? Ya kuma zata kasance tsakanin Sumayya da Khamal?




_Free page na dab da ƙarewa ki hanxarta wajen biyan kuɗin littafin LADY BOSS...._ _Littafin na kuɗi ne normal group ₦300 vip group ₦500 spc ₦1000 zaki iya turo da katin MTN ta wannan number 08081202932 ko ki tura ta wannan account details...6037312299 Mohammed A'isha keystone bank Idan Vtu trnsfer ne kiyi ta wannan number 09061466409 zaku na iya fara payment ɗin cox free page ba da yawa xanyi ba..._

No comments

Powered by Blogger.