My Lady Boss 10

 


  Last free page

              .......10

     Marubuciyar:

(1)Bafullatnn ruga

(2)Ƴar aikina

(3)Walijaam

(4)Ƴar waye 

(5)Gidan kwarata

(6)Gidan zaurawa

(7)Ƙwaryar sama 

(8)Bintoto

(9)Ƴar maula

(10)Habibi da'iman

(11)Dijama ƴar fulani

(12)kawaliya

(13)Ƙwartn manya

(14)Zuma da maɗaci

(15)Taɓarah

(16) Siyasata

(17)My Lady Boss


*****

_Idan kin San kan ki baxai ɗau abun dake ciki ba,bazaki iya jura ba ,don Allah kar ki karanta ki dawo mun da zancen kutumelesi...ban san wani kitimurmura labarin Romantic ne👌haka kema idan kin san zaki saya ne don ki fitar mun na yafe ki adana kuɗin ki, kar ki fitar mun adawo mun da zancen gntlw.....masoya na billions naji saƙon nin ku gareni ina gdy Allah yabar🫶_


_*Free page ya ƙare daga wannan page ɗin...ku hanxarta wajen biyan kuɗin littafin LADY BOSS domun jin daɗin ku a antayaku a paid grp...kin shirya biya?? Na shirya! To yanda tsarin biyan ya kasance... Regular payment ₦300 vip payment₦500 special payment ₦1000...zaku iya turo da kuɗin ku ta wannan asusun bankin 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank...ko kuma ki tura katin MTN naki ta wannan number 08081202932...Idan Vtu trnsfer ne ki tura ta wannan MTN number 09061466409 sai ki tura da shaidar biyan ku duka ta wannan WhatsApp number 08081202932 asha karatu lafiya...*_


_SADAUKARWA GA MUTAN ZAZZAU gami da godiya ga masoyana billions ko trillions ne gdy duk😍😂_


***


Jin yanda take wasu irin zuban sambatu marasa kan gado yasa Fahad miƙewa yana raba jikin shi da nashi ,hannun shi yasa yana ɓanɓareta daga jikin sa , miƙewa yayi tsaye daga shi sai Boxer kaman ɗan dambe , damtsan shi ka gani a duhu sai ka ruga saboda tsayuwar su ba wasa fuskar sa ɗaure tamau ya fara faɗin " Ke tashi fiche mun daga bedroom apartment. Tsayawa Nuwaira tayi tana don Allah kayi haƙuri ko sau ...wani irin uban tsawa ya daka mata mai maida mutum shiga taitayin sa ,kana yace" You are nonsense , tashi ki fichemun daga apartment. Jikin Nuwaira ne ya hau rawa da sauri ta miƙe tana gyara rigar jikin ta da yayi ƙasa tana wani irin guntun kuka ...Go!! 



Yayi maganan a zafafe tamkar mai shirin duka ,wannan yasata saurin nufan ƙofa , kasa murɗa Handle ɗin tayi ta tsaya , wanda juyowa yayi yana ware lumsassun idanun sa akan ta na shirin tijara , cikin sauri ta murɗa Handle ɗin tana fichewa ...dafe kansa yayi yana jan ƙaramin tsaki mai sauti kana yace "with her untasteful I luv u! Loved Who? mtswww dole yau ta bar gidan nan baxan zauna da jarababbiya a matsayin cook ba. Yana maganan haɗi da shigewa bathroom don watsa ruwan ɗumi. 


****


Zaune Nurse Yusrah a bakin gadon Bilkisu tana nuna mata takardan Sallama don sosai ƙwarai taji sauƙi jiki sarai tamkar ba ita ba...yanda tazo masu a bige yau sarai ta farka . Amsan takardan Bilkisu tayi kana tace " Na gode da kulawan ki Nurse , yanxu zan tafi.  Kallon ta Nurse Yusrah tayi kamin tace " A'a ina Mama? Da sauran ƴan uwa? . Miƙewa tayi tamkar Boss don a tsaye Billy take ga tsawo ga ƙiba ,sai da tasa takalmin ta ,kana ta juyo tana kallon Yusrah tana bata amsa da " Babu su a yanxu Billy ita kaɗai take gudanar da koman ta. 



Tana ƙare maganan tare da yafa ƙaramin mayafin ta , tana faɗin tnx ones again nurse ,till we meet again. Hannun ta Yusrah ta rike tana cewa" Me zaisa ki zauna tare dani?". Muje kiga gida na mahaifina , nima marainiya ce bani da kowa , mahaifin a ya rasu ,haka mahaifiyata , ina da wa namiji amma shima kash bayaji sam yaƙi natsuwa , dangin uban mu basu mana komai , da wannan aikin nawa kaɗai na dogara , mai zai hana ki zauna damu har zuwa lokacin da zaki samu miji kiyi Aure.



Wani irin dariyar basawa Billy tayi kana tace " Billy bata saba zaman gida ba , kuma Billy ba cima zaune bane ,na barki lafiya sai wata jiƙon...tana faɗin haka ta fiche ɗaga asibitin.


Ƙasa motsawa Yusrah tayi kawai hawaye ne taji yana saukowa kuncin ta , dama akwai macen da take irin wannan rayuwar na Bilkisu? Ada Ina tunanin nafi kowa shiga cikin tsananin rayuwa ,amma a yau naga wacce take buƙatar taimako da tallafin iyaye sai dai babu su...kuka sosai Yusrah tayi bata damu da patient ɗin da kowa ke kwance a gadon shi yana kallon ta ba... addu'a kawai take Allah ka shirya masu hali da ɗabi'a irin na Bilkisu.


****


Ɓangaren Madam Sumayya kuwa tana kammala aikin karin kumallon gidan Hjy Juwairiyya ta zauna tana kallon yanda dirning table ya cika da abucucuwa kala-kala . 


Wai yanxu wannan duka za'a cinye a ciki? Taɓ aiko dole na ɗiba mawa Su Safna da Umma na suma ba'a ci basu ba. Zama tayi ta cika babban flsk tana barin gidan haɗi da nufar Gidan su. 


A tsakar gida ne ta cidda Haulatu na shara , wanda ganin ta yasata tsayawa cak tana cewa " A'a ya kika dawo da wuri haka? Kuma kinyi mawa Hajiya maganan zamu zo aikatau ɗin?. 



Humm Sumayya ta nisa tana kallon Haulatu kana tace " Ke ana faɗa maki har yanxu bata sauko ba , tana can sama tana bacci ita da ɗan ta...yanxu abinci na kawo maku ku ci sannan ,Ni Bara na koma... Safna ce ta fito tana amsa kana tace " Wallh ko kamannkn san yanxu Umma ta tashi daga bacci Bara a sa mata ruwa tayi wanka sai taci abincin. To nidai na koma". A dawo lafiya sukayi máta tana fichewa cikin sauri.



****



Bayan koma wanta gidan Hjy Juwairiyya ne ta haɗu da Oruma wanda cikin sauri take cewa " Kije kiyi serving nasu , suna dirning yanxu . Buɗe baki Sumayya tayi cike da mmki tana cewa "Au yanxu abincin ma Ni xan zuba masu suci?. 



Ke Summy ki shiga da sauri , wannan ƴar bala'in Binafa tana nan tana cika wuya. Ganin yanda Oruma ta rude yasa Sumayya nufan falon ,wanda kai tsaye Dirning area ta nufa...wani irin ƙamshi ne ta shaƙa mai daɗin gaske , wanda yayi mata gauraya kaman da wanda tasan ƙamshin sa irin haka............


Cikin sauri ta nufi Dirning ɗin tana zubewa har ƙasa tana gaishe da Alh Y Kumbo Wanda ya kasance mahaifin Khamal , fuskar sa sake cikin fara'a ba izza da mulki ta masu kuɗi babban mutum wanda ashekaru yakai 70 . Kallon Hjy Juwairiyya tayi da take cikin tsadaddan lace black Wanda itace take serving din su tana zuba masu abincin kowa a gaban shi ,  sun san Shi Daddy Kunu ake masa ta gyaɗa da safiya wannan yasa Hjy Juwairiyya tsiyaya masa a wani cup tana risinawa tare da ajewa a gaban shi....Binafa ce da take ta kallon Khamal wanda bai san tana yi ba , yana can yana latsa wayar hannu shi... ɗago da idon ta Binafa tayi tana dalla mawa Sumayya Harara kana tace " Ke meye aikin ki a gidan nan da har sai Momy ta yi srvng ɗin mu ? Ke ba ƴar aiki bace?". Tayi maganan a gadarance cikin faɗa? Jikin Sumayya ne ya hau Rawa ,cikin sauri ta amshi ladle ɗin hannun Mom Juwairiyya tana cewa " Yi haƙuri hjy bari na yi. Humm zama mom Juwairiyya tayi , Daddy ne yace"Aa Binafa kiyi haƙri ƙila wani uzurin ne ya zo mata but yanxu ba gashi tazo ba?".



Talia ce ta zuba masa a platin Gaban shi tana ɗaura masa miyar hanta akai tare da cewa " Yallaɓai Bismillah". Tsam Khamal yayi jin Muryar da baxai manta dashi ba , don duk maganan da suke yi bai tankasu ba ,bai ma sauraren su sai a yanxu . Wuce shi tayi tana nufar Binafa tana ɗaukar ruwan lipton tana shirin aje mata , ɗago da dara daran idanun shi yayi yana watsa su ga sabuwar ma'aikaciya r Momyn tasa....Wani irin shock yayi yana kallon ta gaba ɗaya ƙwaƙwalwa e sa ta tsaya cak....LADY BOSS? Tartstsatsannnnnn kaji Sumayya ta saki cup din tea din tana watsa ma Binafa da tayi zumbur ta miƙe don ruwan zafin ya taɓa ta sosai.....wani irin mari ta ɗauke Sumayya dashi ji kake tassssss ke makauniyace wacce jaka ce?". 



Binafa kina da hankali kuwa? Cewan Daddy cikin ɓacin rai....Daddy zuba mun ruwan zafi tayi fah, Binafa tayi maganan cike da shagwaɓa tana shirin sa kuka. Sumayya ko da nata hawayen ya riga sauka , cikin sauri da gudu ta bar wurin....tana nufan store. Duk da hakan baki ga yarinya ce ƙarama ba? Cewan Daddy cike da damuwa don bai ji daɗin marin da Binafa tayi mawa Sumayya ba . 



Miƙewa Khamal yayi yana barin wurin tare da nufan falon Daddy. Zama yayi shiru yana tunanin abubuwa tabbas dubu ɗari hudun da ta ɗeba masa a wurin sa bai ganin sa a koman komai . Zai iya bata kyautar million bai dame shi ba ,bai kuma ji komai ba , amma maganan da ta yaɓa masa shine baxai iya yafe mata ba...wanin zagaye na ne , xan axabtar dake , zaki san koni waye? Zan saki kuka na dana sani....miƙewa yayi yana nufar store inda yaga ta nufa ..cikin takon sa na taƙama ya kutsa kai dai dai Mom Juwairiyya na miƙa mawa Sumayya takardar sallama daga aiki.....



Na dakatar dake daga aiki anan ɓangare na. 



No mom" Ni na ɗauketa aiki a nawa ɓangaren!.


No comments

Powered by Blogger.