Min Qalb 36-40

 


MQ 36_*

 Umme da kanta tabata abinci abaki taci tana qara jinjina zancen Dr Fatima data fada Mata kafin shigowarta akan inda aka tsaya da maganar matsalar,

 

Ita kanta Amatun a sanyaye take sbd rashin sanin makomar abindake cikinta,

Allah yasani tanason babynta Kuma tanason samun Abinda Bata fatan tayi wahalar banza shiyasama tunda sunce saita kwantarda hankali babyn zai samu shima lafiyar da akeso tafara iya qoqarin kwantarda hankalin saidai Kuma Sam tsoro da shakkar halinda babynta ke ciki ya Hana hankalin nata kwanciya.

 

Iyami ce ta miqa mata kofin maganin tsiyayewar zaqi tana cewa''

 

Karba ki Dan Sha ko kadan ne zai taimaka idan haihuwar ta taso gaba data.

 

Kallon kofin tayi tareda karba ahankali ta kurba tana rintse ido sbd rashin dadinsa ta ajiye cup din tana girgiza Kai tace"

 

            Iyami bazan iya Sha da yawa ba wannan ya Isa Yana sakani zafin zuciya da yawa.

 

Fura me sanyi anty zarah ta zuba Mata ta miqa Mata Wanda itace ke cewa tafisonta da sanyi sosai idan ba hakaba Bata iya Sha abin Sha idan baida sanyi Sam.

 

Karba tayi ta shanye atake tana cewa aqaro Mata saidai aka miqa Mata jug din daya Gama daukan sanyi shima.

 

Shan furar takeyi sunata kawo Mata firarraki kala kala Dan dauke Mata hankali kota cire damuwa da tsoron kwata kwata,

Sai dare dukkaninsu suka watse aka barta daga ita sai iyami sai anty salamatu dasuka Zo taredasu maman junior dasu maman basiru Dan dubata kowanne dauke da kularsa ta kayan gargajiya na marmarin me ciki,

Maman junior sakwara da jar Miya ta kawo Mata wadda taji yaji sai maman basiru data kawo Mata danwake dayaji salad da kwai anty salamatu ma taga soyayyar gyada ahanya da Madara gasassa ta siyo Mata duk saitaji idanuwanta sun cicciko da hawaye har batasan lokacinda tasakesu tana sunkuyar da Kai sbd ayau tasake tabbatarda ba jininka ne kawai Dan uwankaba wani Dan uwanma yafi na jini,

Bata damu da son sanin asalintaba ko jininta wainnan bayin Allahn sune Yan uwanta sune jininta sbd suna qaunarta tamkar jininta Dan haka Bata buqatan sanin inda ta fito Dan kula kawu da iyami tareda usinta sune asalinta hakanma ya Isa rayuwa Alhamdulillah.

 

Share Mata hawaye anty salamatu tayi tana cewa''

 

To meyene na kuka Bayan Dr tace ko damuwa ba'a so bare Kuma kuka,

Wannan abin damukeyi duk yiwa Kai ne sbd mu tamkar zuria daya ne idan baki manta ba yawancinmu dake gidan bamuda zuria,bamuda dangi mune Yan uwan junanmu Dan haka meye abin damuwa aciki.

 

Iyami dai batace komaiba sbd ita wani lokacinma ayanda takejinsu aranta har mantawa takeyi da ba itace ta haifesuba sbd har cikin ranta take qaunarsu a haqiqanin gaskia.

 

Take suka cika dakin da hayaniyar gida dasuka Saba ana tuttuna baya da irin fadace fadacen dasuka sabayi Wanda haryanxu ba dainawa sukayiba Nan take ta sake saigata ta washe acikinsu tana walwalarta harda dariya da qyaqyatawa

Taci sakwara kadan hakama Dan waken taci sosai shikam kafin ta Dora da masararta tanaji suna firarsu Basu bar asibitin ba sai goma da wani Abu kafin suka tafi anty salamatu ta rakasu kafin tadawo Amatun tayi bacci cikin nutsuwa Wanda ta kwana biyu batayiba.

 

Washe gari da Dr Fatima ta auna BP dinta taga ya sauka sosai sai abin yabata mamaki takalli iyami cikin Jin Dadi tace"

 

Tayi bacci ne sosai jiya?

 

Eh Kam jiya tasamu bacci Dan sallah ma saidai da safen Nan tayita.

 

Masha Allah gskia idan da zata riqa samun hakan to da Inshallah komai zaizo da sauqi yanda mukeso.

 

Jin hakan yasa iyami ta aika salamatu tayiwasu maman junior Magana akan su riwa zuwa Dan Allah suna kawowa Amatun firar dare

Ba musu suka amince sbd Suma zasuso tasamu lafiyar.

 

Aikuwa tuni asibitin Takoma majalisar 'yan gidansu Dan kuwa idan sunayi dariyar Amatun har qofan daki anaji umme ma data ga hakan saita qarawa zuwan nasu armashi ta aiko musu da lafiyayyan abinci da pepper chicken na kaji kullum aikuwa Suma ganin wannan dadin yasa suka sake dagewa da kullum gida suke kwaso abinsu sai sun iso gida araba abawa kowa nasa Kuma kajin ba 'yan kadan ba ga drinks gakuma kudin abin hawa da anty zarah ce itakuma ta Basu Wanda zasu riqa amfani dasu Dan da farko kawu ne duk sukazo yake Basu na komawa sai anty ZARAH ta dauke Masa wannan nauyin.

 

 

Kwananta takwas a asibitin ranar na Tara ta tashi da wani mummunan ciwon kai wanda yasanya jini da ruwa 6alle Mata take hankalin dukkanin likitocinta tashi musamman Dr Fatima

Su kansu su umme dasu kawu kowa yashiga tashin hankali musamman ganin yanda take wani wani Abu kamar jijjiga haka aka kwasheta akai labour room da ita aka barsu tsaitsaye suna Kai kawon jira cikin rashin hankali.

 

Kafin qarfe hudu na yamma dukkanin 'yan uwanta da wasu daga cikin familyn ZABEERA suna asibitin Babu me wata walwala acikinsu sbd har lokacin Babu wani labari daga likitoci sai yawo ake ana fita ana shiga.

 

Dr Fatima ce ta fito Bayan tayi waya da Modibbo ta sanar Dasu komai na halinda ake ciki ta kalli kawu da umme da iyami dake gabanta cikin office dinta dake cikin labour room cikin tsananin damuwa da sanyin jiki tace"

 

Wato Abinda ake ciki shine Amatu bazata iya haihuwa da kanta ba sbd lokacin haihuwar baiyiba gabanta ko kadan bai Fara budewaba gashi baza'a iya jiraba sbd qarfinta zai qare hakama babyn ruwan dayake ciki kowane lokaci zasu iya tsiyayewa Wanda hakan na faruwa hadari ne Mai matuqar girma Kuma barazana ce ga rayuwarsu su duka,

Dan haka bazamu Bata lokaci ba na sanarwa su Modibbo zamuyi Mata aiki saidai Abinda zata Haifa din zamu sakasa a kwalba sbd rashin isarsa haihuwa idan Allah yasa andace...

 

Tsit sukayi kamar wainda sukaji mugun labari,

Koda yake kusan hakan ne Dan umme tuni tafara hawaye sbd tasan rasa babyn zatayi kamar yanda ta rasa Khalil dinta.

 

Numfashi kawu ya sauke cikin jarumata yace"

 

To shikenan likita ba damuwa ayi aikin Allah yasa hakan shine mafi alkhairi yasa Kuma ayi cikin sa'a.

 

Amin tace tana qoqarin amsa wayarta da Kiran MAHMOUD ZABEERA ke shigowa Dan takirasa dazun bai dagaba.

 

Itace tafara Magana sbd tadan fahimci bai cika maganaba yafi saurare Dan haka Bayan ta Masa ya aiki saita Fara koro Masa bayanin halinda ake ciki ta Dora da cewa''

 

Modibbo yace Kaine zaka saka hannu a file din gashi Kuma bakanan and bazamu iya wuce Nanda 20min ba bamu Shiga da itaba ba sbd.......

 

Kai tsaye cikin wata murya me sanyi ya katseta da cewa''

 

I will be there in 10min yanzu nake baro airport.

 

Kafin tayi Magana ya datse wayar ya ajiye gefensa ya sauke sanyayyan numfashi tareda rufe Ido ya bude ya kalli Mal Umar yace"

 

Mal Umar Yi parking.

 

Ba musu yayi parking din saiyaga ya fito daga Bayan motar ya zagayo gurin sit din driver ya bude yace"

 

Fito ka koma baya zanyi tuqin.

 

Fitwo Mal Umar yayi da sauri batareda yace komaiba duk da Yana cikin mamaki Amma dai sanin ba Abinda yafi tsana wani lokacin kamar tambaya yasa baice qalaba ya zagaya ya Shiga dayan gefen ya zauna.

 

Batareda ya kalli gefen mal Umar dinba Bayan ya shiga ya tayarda motar yace"

 

Saka seat belt dinka.

 

Da sauri ya janyo ya saka.

 

Wani lafiyyan speed yabawa motar Wanda yasa Mal Umar saurin hade qafafunsa Yana hadiye yawu tareda damqe qofa Yana zazzare idanuwa dan ba halin Magana bare ya nuna tsoronsa,

Allah ya kaimu inda zamu lafiya yafada cikin ransa Yana satar kallon MD din dake sake bawa motar wani mugun speed din Wanda yamanta rabonsa da irin wannan tuqin qila tun Yana cikin samartakarsa idan Khalil ya matsa Masa Akan suyi tseren mota a Sudan idan yaje gurinsa.

 

 

Fitowa Dr Fatima tayi daga labour room sanyeda kayan CS tana duba agogon wayarta datakeson kashewa kafin Shiga CS din taga minti Tara kenen da wayarsu da MD Amma haryanxu shiru ga kowa jigum jigum shi ake jira yazo yasa hannun ga Modibbo ma ya iso asibitin Amma baisaka hannunba yace ajira MAHMOUD din tunda yace abasa mintuna kadan...

 

Kamar daga sama har zata juya cikin room din saigashi ya doso gurin cikin tafiyarsa me nutsuwa da cika Ido take kowa ya juya Yana kallonsa Yana tahowa in calm Sam baka ganin gaggawa ko sauri ko firgici ataredashi shi mutum ne daya iya controlling yanayinsa duk qwaqwarka baka ganewa saidai idan ka kalla cikin idanuwansa kake iya gane Abinda yake ciki saidai Sam ganin idanuwansa ba Abune me yiyuwaba ga kowa Dan baya Bari.

 

Yana qarasowa ba wata Magana Dr Fatima ta miqa Masa file da biri yayi signing tareda juyawa zuwa blood bank dinsu sbd tun a waya yafada Mata basa buqatan jinin asibiti.

 

 

Anshiga tiyatar da qarfe biyar na yamma shiyasa gabaki daya ward din cike yake da familyn ZABEERA ko biyowa ta gefen ba'a yi sbd ba'a buqatan hayaniya suna buqatan silence sbd suji da damuwar dasuke ciki,

Damuwar iyami da kawu tsakaninsu da Allah tafi karkata ne Akan su samu 'yarsu tukuna kafin suyi maganar abindake cikin shiyasa sukafi kowa damuwa ga USI da Dr Salman sai Kira sukeyi sun Hana kowa sukuni qarshe ma dai kusan wasu kashe wayoyinsu sukayi wasu Kuma suka sanyasu silent.

 

MAHMOUD na tareda Modibbo a office din Dr khalil zabeera Wanda haryanxu wani bai shigaba tukuna suna jira Modibbo ne Dai ke wayoyinsa shikuwa MD ZABEERA Yana zaune ne yayi crossing legs idanuwansa a lumshe yana karkada qafa.

 

Ana fitowa sallar magriba nurse na fitowa daga theatre ta cikin labour room fuskarta daukeda da murmushi da farin ciki tun Kan ta qaraso duk suka miqe suna kallon bakinta tasake sakin murmushi tace"

 

Ansamu baby boy.......

 

 

Masha Allah, Masha Allah, Masha Allah alhmdlh, alhmdlh"  Sune kalmomin da suka karade gurin atake kowa na fada Yana washe baki

Umme Kam tana fada idanuwanta na cikowa da hawayen farin ciki hakama iyami da kawu daya kasa zama guri daya yafita waje yadawo.

 

Anty zarah kuwa karo na farko dataji idanuwanta kamar zasu ciko da hawayen kwadayin samun dukkanin Abinda Amatu ke samu musamman irin wannan soyayyar daga kowa ga Kuma babynta tasamu.

 

 

Hamdala Modibbo yayi lokacinda nurses biyu suka fito da jaririn dunqule cikin wani qaton farin bargon jarirai acikin kwalba.,

 

Babu Wanda aka Bari yashiga dakin kwalbar jariran sai Modibbo da MAHMOUD din sbd jaririn baida lafiya sosai Dan gabaki dayama kalar fatarsa ta Dan sauya saidai tubarkalla jaririn Yana haske sosai da dogon hanji kamar dukkanin iyayensa.

 

MAHMOUD Modibbo ya miqawashi Yana tayasu murnar samun qaruwa tareda addua ya fice yabarsa.

 

Shiru yayi akaro na farko yaji hannuwansa na rawa game da daukar Abu sbd kaf rayuwarsa Yana sakaran wannan ne karo na biyu daya taba daukar jariri sbd baida Wanda zai haihu yabasa danshi ya dauka,

Karon farko daya taba daukar jariri shine lokacinda wani babban abokin kasuwancinsa ABDUL LAYE da matarsa ta haihu suna Greece shine yayi Masa huduba ma sbd shaquwarsu sai yau da Allah yabasa ikon daukar 'dan Dan uwansa Wanda yake shine ubansa yanzu Koda kuwa ace Khalil din na Raye yasan shine zai Masa huduba bare yanzu dayakeda gaba daya responsibilities din na yaron,

 

Fuskarsa yadan bude ahankali ya kalla wani sanyi da nutsuwar zamowa uba na shigarsa

Sai yanxune yakejin Abinda zarah ke fada nason zamowa uwaye suma wata ran,

 

Haka kawai sai yasamu kansa da murmushin dayasa nurse din dake tsaye kusan sumewa tana kallonsa da dukkanin girman idanuwanta kamar zata cinyesa baki sake.

 

Dagosa yayi yakai fuskarsa gurin kunnen jaririn ya karanto Masa Kiran sallah da addua tareda Sanya masa dukkanin albarkarsa dakuma yiwa Khalil addua.

 

Saida ya Dan jima kafin ya miqawa nurse din aka maidashi cikin kwalba ya fice.

 

Office din Dr Fatima data gama sauyawa tagama signing na fitowa tiyata tana zaune tana harhada kayan tafiya gida saigashi yashigo Nan tasake Masa bayanin Alhmdlh Amatu insha Allah komai lafiya data wartsake shikenan ba wata damuwa saidai jaririn Kam baida lafiya sosai saidai yanzu ita matsalar jaririn ba nata bane yanzu Dr fatihu ne zaiji da matsalar jaririn shizai Basu bayanin komai zuwa da safe Dan haka tana tayasu murna da fatan Allah yakawo abin da sauki.

 

Kusan atare itada MD din suka bar asibitin zuwa gida Dan ko dakin da amatun take bai jeba ya wuce gida Modibbo ma tuni ya wuce.

 

 

Sosai suke ta hidimar kulada Amatun tun cikin dare data farka tuni nurses suka sake gyarata aka kimtsa komai Koda qarfe goma na safe tayi kowa yazo ya tararda ita a zaune sai abin nasake Sanya kowa farin ciki.

 

 

To kusan dai murna komawa ciki takusa Yi sbd bayanin da Dr fatihu yayi musu dangane da jaririn Wanda yanzu haka da oxygen yake numfashi kadan kadan baya iya shaqar numfashi da kansa,

Sanyi ne da rashin motsawar jijiyoyin yawon jini ajikinsa sukai Masa mugun qarfi gashi ko qarfin kuka yarin baida a taqaice dai Yana buqatar blood transfusion.

 

Babu Wanda yakai MAHMOUD da Amatu tashin hankali sai umme ma da abu yadawo na damuwa shiyasa duk abin yakoma ba murna kamar ba haihuwa akaiba.

 

Ahankali ita ta warware tasamu sauki sosai Dan kullum da kanta take zuwa dakin da yake tadubosa,

Kwana shida dayin CS din ta murmure matuqa sai Dr Fatima tabata sallama Amma sbd jaririn sai jinyarsa ta dawo musu sabuwa saidai kullum tana zuwa gidansu tayo wanka ta huta tadawo.

 

Batareda sanin kowaba MAHMOUD ya bincika wani qwararran asibitin Yara dake Greece take yasa ayi musu Shirin tafiya

Ya sanardasu Modibbo Nan Suma sukai na'am da hakan Dan dama tuni Andi shima yafara bincikawa wasu qasashen.,

 

Da Amatu da anty salamatu sai umme datace zata aka hada tafiyar shi MAHMOUD zasu rigasa zuwama sbd baya iya tafiya da Mata sam.

 

Andi dayazo har gidan kawu da kansa da Daren laraba ya gyara zama Kan tabarmar da aka shimfada Masa bakin masallacin qofar gidan yace"

 

Mal Saleh maganar tafiyar yaran Nan inaga zaifiwa kowa kwanciyar hankali idan aka daura auren kafin sutafi sbd su samu isashen lokacin nemawa KHALIL qarami lafiya daga Nan har lokacinda Allah zai basa batareda mu munshiga wasi wasiba Suma Basu Shiga takuraba

Shiyasa nace amatsayinka na mahaifinta Zan Sanar maka idan ka amince a daura Bayan sun dawo sauran abubuwan sa biyo daga baya.

 

Numfashi kawu ya sauke Yana muskutawa cikin jinjina kai yace"

 

To Nima dai da bakazoba inada niyyar zuwa da safe sbd zuciya data kasa yardarmin tafiyar hakanan sakaikai duk da ba ita kadai bace Amma hakanan nayita wasi wasin su sauran idan sungaji dawowa zasuyi abarota ita kadai sai hakan bai wani kwantaminba gwara a daura Kam Nima yafimin nutsuwa.

 

To shikenan nagode sosai Mal Saleh Kuma Inshallah gobe za'a aiko kudin auren idan Allah yakaimu juma'a sai a daura tunda ranar juma'ar da daddare zasu wuce shikuma MAHMOUD din asabar da safe zai wuce.*_MQ 37_*

 

 

*_kina da burin koyon sana'a wadda zaki yita daga gida a sauqaqe_*

 

*_kin jima kina sha'awar yadda yake hada BIRTHDAY CAKE DA DECORATION amma kin rasa wajen da zaki koya?,ko FARASHIN YA MIKI TSADA?_*

 

*TOFA MATA!*

 

*_Ga dama ta samu_*

 

*_UMMU AYMAAN KITCHEN ta shirya tsaf don koya muku yadda ake hada gangariyar BIRTHDAY CAKE wanda ya gama hada dukkan gamayyar kayan dadi masu sanya harshe su motsa,gefe guda kuma ta koya miki yadda zaki qawata waje da walwali da kuma walainiyar KAYAN ADO DA QAWA na wajen gudanar da SHAGALIN BIKI SUNA TARON BIRTHDAY WEDDING ANNIVERSARY da sauransu_*

 

*_ba'a nan UMMU AYMAAN KITCHEN YA TSAYA BA,tana da ajujuwa na musamman don koyar da mata nau'in girke girke MAIDA TSOHUWA YARINYA,hakanan tana karbar kwangilar abincin taro kowanne iri_*

 

*_ta fannin kayan maqulashe na fulawa ta samar da abubuwa kamar haka_*

Cake perfait

Cup cake

Samosa

Springrolls

Meatpie

Doughtnout

 

*SIYAN DAYA KO SARI*

 

*_za'a koyar dake BAKING AND DECORATION QIRI DA MUZU ta sigar zancan nan da hausawa kance GANI YA KORI JI,gani ga malama_*

*_sa'an nan kuma akwai tanadi na musamman ga masu sha'awar koya ta hanyar yanar gizo wato ONLINE,duka kan farashi mai rangwame_*

 

*_ZA'A IYA SAMUNTA A UNGUWA UKU,LAYIN MAI FATA ZARIA ROAD*

 

KO A TUNTUBETA A WANNAN LAMBAR WAYAR

08032964266

 

*_ZA'A GUDANAR DA KOYARWA NE ON 5&6,GARZAYA MAZA KI REGISTER*๐Ÿƒ๐Ÿพ‍♀️๐Ÿƒ๐Ÿพ‍♀️๐Ÿƒ๐Ÿพ‍♀️๐Ÿƒ๐Ÿพ‍♀️

 

 

 

 

 

Bayan tafiyar Andi gyara zama kawu yayi Yana fiddo wayarsa cikin babbar rigarsa ya Danna Kiran USI Dan sanar dashi komai sbd shi dama iyalinsa sune abokan shawarar sa.

Kamar yanda tsammananta Usman din yayi na'am da ayi auren kafin sutafi zaifi bawa kowa nutsuwa dan haka take suka qara tattaunawa suka Kai qarshe Bayan dawowarsu ayi walima saita tare shikenan.

 

Cikin gidama Yana Shiga Kai tsaye dakin Amatun ya wuce dan tadawowarta gida take kwana duk da komai nata na zabeera har lokacin sbd bawai ansallami Khalil qarami bane Kuma Nan gidansu yafi Mata sauqin zuwa asibitin kullum akan zuwa daga zabeera.

 

Kallonta yayi tana waya da umme ahankali sbd gabaki daya ciwon Khalil ya karyar Mata da jiki da zuciya sai tanajin tsoron rasashi kaman yanda ta rasa babansa shiyasama ta dauki burin samu waraka akan tafiyarnan dazasu Yi a matse take dasu tafi sbd ganin takeyi dasun tafi Khalil dinta zai samu lafiya.

 

Ganin tana waya yasa yafasa mgn ya qyaleta har zuwa gobe yayi dakinsa inda ya tararda iyami ita Kuma tana kunna musu tsintsiyar qamshi bayan tagama gyara dakin Wanda tsafta kyakkyawar dabiarta ce Sam Bata rabo da gyara da qamshi.

 

Zama yayi Kan babbar daddumar tsakar dakin bayan ya cire babbar rigarsa ya sauke numfashi Yana cewa''

 

Iyami zoki zauna Magana zanyi dake akan 'yarki.

 

Juyowa tayi ta kallesa taga Babu alamun fitarsa daya same ataredashi saita kunna sauran dayar tsintsiyar qamshin ta sokata a jikin qofar shigowa ta qaraso gefensa ta zauna Yana cewa''

 

ALLAH yasa lafiya dai wannan nutsuwa danaga kayi¿

 

Nufinki banda nutsuwa iyami?

Wato dai haryanxu duniya batai Miki darasin yiwa miji biyayya ba kokuwa dai sbd kin Raina........

 

Katsesa tayi da sauri da cewa''

 

Dan Allah Yi hkr ya Isa kada mu komawa halin dare ne ana jinka har maqota,

Munyi jika yanzu wani abin dai Dole mu barshi Dan haka Yi hkr ba nufina kenan ba.

 

Shiru yayi kamar yafasa maganar tsawon mintuna kafin ya sauke ajiyar zuciya yasake kallonta yace"

 

Andi ne da kansa yazo dazun Nan

Sunxo nemawa MAHMOUD auren Amatu abisaga suna neman alfarma sbd basa barin matan yayansu su fita wani gurin dabam suyi aure

Kuma dai ba laifi Nima na yaba da shawarar su sbd kwata kwata bana fatar Amatu tadawo gida ta zauna munsamu tayi aure zata samu ingantacciyar rayuwa saigashi Ashe mijin bame kwanakine agaba ba......

 

Kasa barin ya qarasa zancensa iyami tayi ta katsesa cikin tsananin mamaki da fargabar maganarsa da cewa''

 

Mijin Zarah fa kuke maganar aurawa Amatu idan dai MAHMOUD din Dana sani kuke Magana akai.

 

Wani kallo kawun yayi Mata cikin rashin fahimta yace"

 

Eh shifa mijin Zarah din ake Magana wani abin ne?

 

Ta Yaya kuke tunanin hada zarah da Amatu kishi fisabillah bayan kunsan yanda suke matuqar qaunar juna ga kishi mugun Abu ne Dan Allah ku sauya shawarar Nan idan basaso Amatun tabar zabeera gaba daya Baga Salman Nan ba sai ahadasu Amma Dan Allah Ina Amatu Ina auren mijin Zarah......

 

Kallon mamaki da shashanci yake yimata cikin 'yar hasala yace"

 

Meya kawo maganar kishi da rashin yuyiwa?

Shine yafi kowa cancantar ya riqe iyalin Dan uwansa dakuma zamowa uban Muhammadu Khalil mu shi muka duba bawai kishi ko wani tunaninku na Mata daban ba,

Yanda suke qaunar junan nasu ai shikenan sunsamu damar zama tare har abada Kuma bawai anyi ne Dan cin zarafin ita zarah din ba anyi ne sbd ganin hakan ne ya kamata,

Shi MAHMOUD tun ranar farko da akayi zancen gabansa akayi Kuma bai musaba Dan haka ni me 'ya mace bazai yiyu ace ansamu tangarda ta gurina ba Dan gaka ki aje maganar kishi da rashin yakamata a gefe tun kafin Amatun taji ta samu qarfin ji daga gareki,

Sannan Banda abinki shin ba abin farin cikinmu bane da Jin Dadi tareda kwanciyar hankali ace mun aurar da yarinyar Nan ba adaidai irin yanxu datafi buqatan Wanda zata jingina dashi amatsayin Miji Kuma uban danta,

Kina tunanin duk yanda zabeera suke qaunarta da Bata kulawa idan tana gida zaune wata ran sai ta fuskanci juyin rayuwa wani Kai tsaye zai sheganta danta,wani akan 'dan sai afasa aurenta shin kin manta irin rayuwar data fito ne bayan tsanani da jajircewar Dr khalil aka samu ta watsar da komai shine yanxu zamu vari me tadawo zaman banza Wanda bama fata amma komai zai iya faruwa.,

Ki aje maganar shaquwarsu da yakamatanki mu fuskanci ci gaban yarmu Dan kuwa aure gareta yanzu shine babban rufin asiri.

 

Numfashi ta sauke me nauyi kafin tace"

Dukkanin bayaninka naji amma bana saka ran wannan auren Abune da Amatun zata karba Dan kuwa Ayanda nasan tanajin zarah to zata gwammaci mutuwa ba aure data auri mijin Zarah.

 

Wace irin maganace wannan iyami kike fada?

 

Wlh maganar gskia kenan nake fada maka

Amatu bazata yarda da auren mijin antyntaba nake fada maka

Tun wuri kafin Azo aji kunya kayi Magana da ita kaji Dan Nafi kowa sanin ba amincewa zatayiba

Ai ana barin wani halak din ko Dan kunya,

Amatu tafison koba soyayya tsakaninta da salmanu ta auresa idan anyi Mata tilas dadai ta auri MAHMOUD.

 

Shiru kawu yayi zancen iyami na sanyasa nazari,

Idan Amatu ta bijire ta dage tabbas zasuji kunya Kuma dai Allah yasani yafi buqatar tayi aure ayanxu data zauna zaman zawarci Kuma,

Gskia bazai Bari hakan yafaru ba zai tabbatarda ta amshi wannan auren hannu bibbiyu Amma kafin Nan bazai sanar da ita komaiba sai andaura auren Inshallah ta yanda kotaqi kotaso bazata iya kubucewa aurenba.

 

Kallon iyami yayi Yana tattaro dukkanin hankalinsa yace"

 

Kada ki sanar da ita komai dangane da hakan yanxu sai Bayan auren

Kin fahimta ko?

 

Da mamaki tace"

 

Meyasa??

 

Sbd kada asamu damuwa.

 

Shiru tayi ta danyi nazari kafin ta jinjina Kai tana cewa''

 

To shikenan Amma dai dakun sanar da ita tukuna zaifi..

 

Zan aurar da ita amatsayina na ubanta Bayan auren Zan Sanar da ita alokacin danaga ya dace Dan haka na rufe zancen daga Nan.

 

 

 

Washe gari kamar yanda Andi yace da yamma sun aiko da kudin aure tareda sadakinsu da katin daurin auren Wanda aka bugo da safen sun karba tareda adduar zaman lfy me dorewa ga auren.

 

Take maganar Daurin aure ta Bazu koina sbd fitar katikan Daurin auren ga Kuma sanarwa agidanjen radio da talabijin musamman daya kasance auren mutum me suna kamar MD ZABEERA guda,

 

Take abokanan hurdarsa manyan mutane suka Fara Kira suna tayasa murna tareda saka zuwa Daurin auren cikin mahimman aiyukansu na washe gari.,

 

Umman zarah ce tafara Jin wannan mugun labarin Wanda ya sanyata cikin tashin hankali da rashin nutsuwa saidata Kira zarah din wadda daga bakin umman tata itama tafara Jin wannan mummunan labarin daya sanya qafafunta qasa daukarta ganinta ya dauke ta sulale agurin ta Fadi zaune tana qoqarin Kiran sunayen Allah Amma suna bace Mata sbd tashin hankali daqyar ta iya cafko sunan Allah daya ta furta tana lalubar wayarta tareda shiga social media take kuwa ta ringa cin karo da hotunan  katikan Daurin AUREN dakuma masu cewa zasu sako hoton macen datai sa'ar shiga rayuwar MD ZABEERA akaro na biyu bayan matarsa ta farko wadda haryanxu duniya batasantaba.

 

*MAHMOUD DAHEER ZABEERA* da *AMATULLAH K SALEH* sune sunayen datake ta maimaitawa akan hoton Daurin auren idanuwanta nason kawo ruwa Amma tashin hankali da tsoro yaqi Bari.

 

Sama ta nufa dakin MAHMOUD din Wanda tun rana daya dawo ya shige bai fito ba Ashe sbd yasan fitinar daya dauko ne,

 

Babu bugawa yau Kai tsaye ta bude kofar palonsa ta shigo ta nufi bedroom dinsa ta tura ta shige zuciyarta na wani irin harbawa da sauri sbd gaf kwanyarta take da zautuwa,

Bayani kawai takeso daga MAHMOUD din kokuma Amatun sbd wata zuciyarta takasa yadda da wannan Abinda saitana kallon abin tamkar a mafarki Sam takasa gasgatawa.

 

Kwance yake Kan gadonsa ya qure AC idanuwansa a rufe daga gani ba bacci yakeyiba saidai Kuma batada tabbacin idonsa biyu,

Farin wando da farar rigace Mara hannu ajikinsa sai fararen qafafunwa dayau bai sakawa safa ba sunyi fari tas dasu tafin qafar kamar Baya taka qasa fuskarsa sai annurin kwarjini yake fitarwa take taji hankalinta yasake tashi da kishinsa duk da tasan bama Abune me yiyuwaba mijinta yaso Amatu sbd halayensu sunyi gabas da yamma sam Babu Abinda zaisa ma ya iya kula Amatun amatsayin Mata.

 

Qarasowa kansa tayi ta tsaya zatayi Magana sai kawai kuka ya kufce Mata Mai Dan qarfi batasan lokacinda ta durqushe agurinba tana rufe fuskarta kukan na qara tsanantuwa.

 

Bude idanuwansa yayi dasukai jajir sbd pressure dayashiga shima akan wannan auren Wanda yayi Magana dasu Modibbon sun nuna babu fashi kawai yaje yayi Shiri,

Bai iya hayaniyaba bare gardama da manyansa shiyasa kawai ya taho sbd bazai iya tsayawa hayaniyar gardama ba dasu Modibbo musamman da Andi yafara daukar zafi kamar zai Dora laifin akan Modibbo shiyasa kawai ya taho yabarsu suyi yanda suka dama din,

Yaso yayiwa zarah bayani Amma sbd Koda yashigo yaganta cikin walwala saiya share da nufin idan yadawo tafiya zaifada Mata idan Kuma taji shikenan saisuyi mgnar.

 

Tashi zaune yayi ahankali tareda miqewa tsaye Yana zuba Mata idanuwansa dasukai jajir ahankali yaringa nazarinta sautin kukanta na fita ahankali Yana shigarsa sai kawai yaji zuciyarsa da jikinsa sunyi sanyi tausayinta na sake kashe jikinsa ahankali ya durqusa ya kamota ya dagota tareda sanyata cikin jikinsa ya rungumeta sosai Yana Dan bubbuga bayanta batareda ya iya cewa komaiba.

 

Kusan mintuna da dama suka shanye a tsayen Yana sake Bata kyakkyawar runguma harsaida kukanta ya rage Takoma ajiyar zuciya tana sake shegewa cikin jikin nasa.

 

Zaunawa yayi bakin gado tareda zaunar da ita Kan cinyarsa ya kwantar da kanta Kan kafadarsa Yana hade hannuwansu cikin na juna suka damqe ya dago ya kalli cikin idanuwanta da itama shi take kallo ya sakar Mata wani kyakkyawan murmushin daya saka jikinta mutuwa ya bude baki ahankali yace"

 

Zarah kada ki taba tunanin bana son ki sbd irin rayuwar zaman damuke,

All my life Babu abin Dana sani Bayan kadaici,

Bansaba rayuwa da kowaba,

Bansan ta Yaya Zan sake cikin mutaneba nayi rayuwar walwala ba acikinsu,

Mutanen waje sune wainda na Dan Saba dasu sbd sune mutanen dasuka Saba Jana ajikinsu batun yanzuba shiyasa su nake iya sakewa acikinsu,

 

Khalil was the only family dana dauka inadashi sai Modibbo Wanda shima tsakanina dashi umarni ne kawai da bada oda,

Khalil shine kawai Dan uwana Dana sani Wanda yake tsananin qaunata da damuwa Dani tun Muna Yara harya rasu yabarni ni kadai nasake komawa tamkar banida kowa again,

 

Shigiwarki rayuwana da farko na dauka kamar takurawane Amma daga nabawa alaqar dama da mahimmanci saidai daga gareki ke bakya min kallon miji abokin rayuwar dazamu sake kamar kowane normal couples kina min kallon abin tsoro,

Abin shakka dakuma son muyi rayuwa kamar yanda kowannenmu ke buqata wato ta rashin shiga takurawa kowa Wanda yasani Barin muyi irin rayuwar da Kika zaba Mana wato kowa yayi nasa since you don't want to give it a chance.,

 

Zarah kadaki dauki wannan auren cin Amana ko cin zarafi daga garemu mu duka sbd you know me Sam Banda sha'awar wani Tara Mata,

Dagani har ita yarinyar ma Babu Wanda akai Magana dashi wannan umarninsu Modibbo ne and na amince da umarninsu sbd Inada raayin cigaba da kula da yarinyar da Muhammad so please kadaki ga laifin kowa akan maganar Nan ki mu duka muyi accepting sabon canjin dazamu samu banason doguwar damuwar dazata kawo hayaniya anan,

Idan kin kwantarda hankalinki is nothing compared to ace wani labarin ne na daban kiyi sbd kanki kiyi sbd ni Kuma kiyi sbd ita me zuwan sbd kowa ya zauna lafiya,

Kinsaba zama da ita ai so Kinga ba sabon Abu bane.

 

Wani qaton Abune yazo ya tsaya a maqoshi kamar zai toshe numfashinta idanuwanta dasuka Fara kumbura sukai jajir ta qurawa fuskarsa Ido tanajin da ace da Hali data cire sonsa aranta ta huta da Abinda takeji kamar zata shide,

Sai dai kamar yanda yace kowa ya dauki dangana sbd azauna lfy bazata tayarda hayaniyaba saidai tana buqatar kasancewa ita kadai yanzu sbd tunanin Abinda yakamaceta Dan kuwa idan har Amatu ce za'a aurawa MD din tanajin kamar bazata iya daukaba gwara a aura Masa kowama Banda Amatu bazata iya kishi da Amatu ba zuciyarta bugawa zatayi.

 

Sakinsa tayi ahankali tareda zare hannunta tana kallon cikin idonsa dashima ita din yake kallo kamar bashine yayi dogayen maganganuba yanzu din,

Sakinta yayi shima ta miqe tana share hawayenta dasuka kasa tsayuwa ta bude baki zatayi Magana saikuma ta kasa tayi saurin juya Masa baya ta tattaro jarumta ahankali ta iya bude baki ya furta"

 

Inshallah bazaka samu damuwaba akan hakan ta gefena saidai ka tayani da adduar cigaba da jurewa hakan.

 

Da sauri ta fice ta sauko da gudu ta nufi dakinta tana Shiga ta zauna tsakiyar dakin tareda fashewa da wani irin kukan tsananin baqin ciki tana rufe bakinta sbd kada ya sauko yajita.

 

 

Amatu kuwa kawu da kansa yasameta har daki cikin Daren ya zauna Kan daddumar dakin Yana kallonta da kyau cikin sauti Me nuna matuqar mahimmancin zancensa a natse yakira sunanta ta dago ta kallesa dakyau tana amsawa gabanta na tsananin faduwa..

 

Amatu bani na haifekiba Amma wallahi inajinki tamkar 'yar Dana Haifa ta jinina,

Kisani duk Abinda Zan iya zartarwa akan 'dan dazan Haifa Zan iya zartarwa akanku ku biyun sbd irin qauna danake muku keda Usman,

Ni ubane da bazanso ace 'yata tadawo gabanaba tana zaman jiran wani yazo gareta,

Kinyi aure cikin zuriar dasuke tsananin qaunarki da ganin mutuncinki tareda matuqar qaunar 'danki Wanda har suka kasa hakurin jure tafiyarki ki barsu,

Amatu amatsayin na na uba gareki kamar yanda na dauki kaina na zarce hukunci akanki batareda na nema shawarar kiba sbd tunanin ke din Zaki karbi duk wani hukuncina da Isa dazan nuna akanki.

Mahaifan Khalil sunzo nemawa 'dansu aurenki sun roka alfarma nakuma amince musu gashi min yanke shawarar tunda tafiya zakuyi gwara adaura auren sbd samun nutsuwar kowa duk da bataredashi zakuyi tafiyarba goben.....

 

Kalmarsa ta qarshe tasanyata sauke wata qaqqarfan ajiyar zuciyar da saura kadan zuciyar Tata ta buga Jin yace batare zasuyi tafiyarba kenan ba MAHMOUD bane kamar yanda ta zata da farkon zancen na kawu Wanda saura qiri ta zunduma ihun dabata shiryaba Dan tuni zuciyarta tafara harbawa ashe bashi yake nufiba

SALMAN""zuciyarta ta ayyana Mata take tayi saurin rintse ido saidai kalmomin da kawu yayi amfani dasu da farko na ikonsa akanta yasa ta sauke ajiyar zuciya Kai tsaye Dan gajarta zancen tace"

 

Shikenan kawu duk Abinda ka yanke akaina wallahi na amince maka Kuma Dan Allah kadaina cewa bakai ka haifemu ba sbd mu bamuda Wanda yahaifemu agurinmu idan bakaiba,

Ni yarkace zaka iya yanke kowane hukunci akaina batareda ka tambayeniba,

Tunda Dr khalil ya rasu walh Banda raayi gameda zaben miji sbd ra'ayina ya rasu tareda Mijina Dan haka Banda zabi sai Wanda kayi.

 

Da zallar mamaki iyami da kawun ke kallonta saidai tunda ta gajarta zancen ta amince Babu amfanin dogon bayani Bari abar zancen ahaka har zuwa bayan Daurin aure agani.

 

A daran kukan rashin Dr Khalil yadawo Mata sabo tayi kuka kamar mutuwarsa na sabuwa,

Ayau itace zata auri Salman mutumin data dauka aboki Kuma Dan uwa ta Yaya zatai rayuwar aure da wanin Dr dinta,

Wayarta ta janyo ta Kira anty zarah ki zataji sanyi Amma Bata daukaba kusan Kira bakwai no answer

Miqewa tayi tayo alwala tazo tahau nafila tana jaddada adduar ta ga ubangiji akan yabata juriya da hkr na rashin Dr tareda sanyawa wannan auren dazatayi dawwamร mmiyar albarka.

 

 

Koda gari ya waye anata Shirin Daurin aure itakuma da anty salamatu sunata Shirin tafiya sbd jirgin qarfe biyu zasubi Daurin auren Kuma daya da rabi ne after jumaat.

 

Ba wani dogon noqe noqe iyami ta hakura hakanan ta babbata wasu Yan magungunan masu kyau da qarfi tareda yimata gyaran jikin gaggawa Wanda Sam duk basa gaban Amatun hardai qarfe daya tayi aka wuce gurin Daurin auren daya Tara dubban JAMA'A aka shaida akan sadaki naira dubu hamsin kacal.

 

Koda Yan Daurin auren suka dawo su Amatun sungama Shirin komai na tafiyarsu sbd qarfe biyu zasu tashi shiyasa Koda kowa yadawo Dan kada asamu Yan kanzaki akayi airport dasu cikin shirinta na doguwar rigar jallabiyar Kuwait datai mugun yimata kyau Muhammad khalil na hannun anty salamatu suka fito cikin mota a airport din wayarta tayi ringin saiga sunan Dr salman zabeera ajikin wayar take taji jikinta yayi sanyi waifa yanzu mijinta ne ta sauke ajiyar zuciya tareda daukar wayar zatai magana ya rigata da cewa''

 

Congrats Mrs MAHMOUD DAHEER ZABEERA.

 

Ciro wayar tayi daga kunnenta ta kalli sunan Wanda suke wayar takuma mayarwa kunnenta tana cewa''

 

Salman ne??

 

Eh Mana nine kokina jiran Kiran mijinkine MD ZABEERA yanzu yabar zabeera Yana hanyar airport yafasa zuwa daga baya tare zasu tafi.....

 

Salman me Keke cewa yimin bayanin dazan fahimta waye aka daura aurena dashi kaine kokuwa sbd banason boye boye fadamin.....

 

Mezaisa adaura Miki aure Dani Kuma?

Da MAHMOUD ZABEERA dai aka daura muku aure........

 

Juwace ta dibeta tayi baya gabaki daya jikinta asaki taji antarota jikin babbar rigarsa Fara qal dabai cireba ta Daurin aure.

##Mamuh#*_MQ 38_*

 

 

 

Anty salamatu da umme dake qoqarin fitowa mota jikinta duk a sanyaye itama da wannan auren Dan ganin yau anwayi gari wani ya aure iyalin Khalil dinta,

Yarinyar da Khalil dinta yafiso fiyeda komai wadda ya yarda yarabu da kowa da komai akanta yau tazama mallakin wani

Wani abin sai mutuwa Dan kuwa da Babu Abinda zai raba Khalil da Amatu idan ba mutuwarba,

Amma tunda har MAHMOUD ne ya aureta damuwarta qalilance sbd MAHMOUD dinma mutum ne me matuqar mahimmanci da girma a rayuwar Khalil Dan haka take musu fatan farin ciki me darewa a wannan auren.

Fitowa motar taqarasa Yi itada anty salamatu sukai gaba.

 

Qoqarin dawowa tunanin ta takeyi ga bude Ido ta rufe taga tabbas shi din ne take cikin jikinsa da qarfi ta yunqura ta qwaci jikinta tana sake kallon kyakkyawar fuskarsa dayaqi kallonta ya juya Yana cewa Mal Umar ya fiddo Masa luggages dinsa daga mota.

 

Sake tariyo maganar datayi da Salman tayi cikin kanta tana Dan girgiza Kai tana qoqarin yakice zancen cikin kanta sbd bama zai yiyuba ace anyi tunanin hadata aure da MAHMOUD ZABEERA Rabin ran Anty zarah,

Sam bazaima yiyuba wannan hadin Bayan ansan tsakaninta da antynta Sam Sam......

 

Wayarta ta daga hannuwanta na rawa sbd tashin hankali da tsoron Abinda zataji ta lalubo numbern iyami ta Danna Kira tayita ringin no answer

Da sauri ta lalubo ta kawun tayita kira shima bai daga ba kasa hakuri tayi cikin tashin hankali ta nufi su umme dasukai gaba sosai ganin Bata sauri yasa ta Fara gudu tana kiran sunan umme cikin ficewar hayyaci Dan gabaki daya kanta ya kunce gabaki daya so kawai take a qaryata Mata zancen salman zabeera a tabbatar Mata daba mijin anty zarah aka daura Mata aure dashi ba.....

 

Hannunta aka damqo tareda birkitota tadawo baya gaba daya cikin jikinsa akaro na biyu wannan karon cikin tsananin masifa ta juyo zatai magana idanuwanta suka Shiga cikin nasa daya zuba Mata Wanda ke bayyanar da seriousness dinsa ya bude baki bayan ya Dan kalli mutanen dake wucewa suna kallonta yanda tafara keta gudu ga jallabiyarta very attractive sbd irin me shape dinnan ce Kuma gyalen jallabiyar kawai ne tayi rolling dashi sai handbag dake hannunta...

Murya a daqile yace"

 

Nan ba gurin Wasa bane kokuma Zabeera you better behave yourself....

 

Kasa hadiye Abinda ya tsaya Mata a maqoshi tayi ta kallesa cikin masifar da batamasan tanayiba tace"

 

Hakama rayuwata ba abin Wasa bace kokuma Zabeera dazaka shigo batareda sani ko damata ba,

Nafasa tamabayar kowama kaga agabana Kai Zan tambaya tunda mune abin yashafa inason tabbatarda da cewan da waye aka daura aurena ayau din?

 

Sakinta yayi batareda ya kalletaba ya wuce Yana cewa''

 

She's crazy.

 

Biyo bayansa tayi tana sake nanata tambayar Amma ko inda take baida alamun kalla saima agogon hannunsa daya kalla yaga time yayi ya wuce Kai tsaye su umme ma tuni suka shige.,

 

Ganin zata Tara Masa attention na mutune dasuka Fara Binsu da kallo suna Magana qasa qasa gashi wasu sunfara ganesa Kuma da alama akwai 'yan Media agurin yasan good days dinshi sunzo qarshe dama tunda aka daura Masa aure da wannan crazy yarinyar gashi ranar farko ma zata Bata sunansa a idon mutane...,

 

Juyowa yayi ya fizgota da qarfi tareda kallon fuskarta Yana Kai bakinsa daf da kunnenta cikin bacin Rai Mai tsanani yace"

 

I swear idan baki nutsu kindawo hankalinkiba Zan tabbatarda kinyi nadamar sanin zabeera sbd right this moment Zan rabaki da Muhammad ki koma gida keda ganinsa saina tabbatarda baimasan kece mahaifiyarsa ba..

 

Cikowa idanuwanta sukai da wasu irin kwallar baqin ciki cikin rawar murya tace"

 

Bakada Imani Rabin ran Anty zarah.

 

Sakinta yayi tareda dagowa ya juya ya kalli yanda mutane ke kallonsu suna washe baki sbd sun burgesu sun dauka soyayya sukeyi yayi gaba batareda ya tsaya ya kalleta ba jiki amace zuciya na tafasa tabi bayansa tana ayyana irin tashin hankalin dazai biyo baya sbd har abada Babu maganar aure tsakaninta da mijin Zarah.

 

Acikin jirgi seat dinta ne gefen na umme sbd shi Yana first class

Tana zama ta rufe fuskarta wani irin azababben kuka ya kufce Mata ta rufe baki tahauyi zuciyarta na wani irin quna da qarfi.

Umme tasan ayi hakan shiyasa ma batai yunqurin rarrashinta ba sbd tana buqatan kukan ko taji sanyin Abinda akai matan Dan kuwa da tsananin ciwo da kunya Mara iyaka tareda nauyi a aura maka mijin Wanda ya yarda dakai tareda baka qauna Mara iyaka,

Duk su dukan Kam sai hkr Amma zarah ce tafi kowa cancantar ban hkr sbd kishiya ba Dadi musamman irin wannan ta bazata Kuma da wadda baka taba kawowaba

Gashi Amatu mace ce daba kowane namiji zaisamu ya iya Bari ba sbd ita kanta shaida ce tagani akan Khalil dinta tanadai fatar Allah yabasu rayuwa me albarka acikin wannan zaman nasu.

 

Ganin kukan yaqi qarewa gashi lokaci yaja tafiya tayi nisa yasa umme dafa kanta cikin kulawa da taushin murya tace,

 

Amatu wannan kukan dakikeyi Babu sauki ko mafitar dazai kawo Miki acikin wannan alamarin,

Aure dai anriga andaura Kuma banajin akwai abindazai warware hakan Dan haka amatsayina na tamkar uwa agareki Ina baki shawara da umarnin ki daina wannan kukan da duk wata masifa ki aje gefe neman lafiyar danki mukazo ki maida hankali mu dage muga munsamu Abinda mukazo nema,

Ki aje komai muyi Abinda yakawo mu idan yaso Bayan munyi nasara idan ankoma gida sai ayi maganar auren kinji.

 

Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya me qarfi akai akai sbd qarfin kukan datasha Wanda har lokacin zuciyarta Bata daina Mata zafi da ciwo ba tunanin anty zarah da halin datake ciki da irin kallon datake Mata sun kasa barinta sukuni saidai kamar yanda ummen tace su maida hankali Kan Abinda yakawosu neman lafiyar Muhammad khalil idan sun koma za'a yi Yanda za'a yi a warware auren kokuma tun anan zatasan yanda zatayi ya sawwaqe Mata tun anan suna komawa gida kowa yakama hanyarsa.

 

Share hawayenta tayi ahankali tareda dago idanuwanta dasukai jajir suka kumbura sbd tsananin kuka ta kalli anty salamatu taga bataga Muhammad din a hannunta ba ta bude maki cikeda mamaki zatai magana antyn ta rigata da cewa''

 

Yana gurin MAHMOUD.

 

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda mayarda kanta ta jinginar tana rufe idanuwanta tana tuno zancensa na cewa zai rabata da Muhammad take taji kamar tsoro yanason kamata saidai Kuma ita ba anty zarah bace batajin tsoronsa tafison daganan har qasar sin tabisa akan 'danta duk inda yakaisa.

 

Bacci ne ya Dan dauketa sbd ciwon Kai me tsanani daya saukar Mata sbd kukan datasha har jikinta sai daya dauki zafi Wanda da wuya idan ba zazzabi bane ya damqeta ga tashin hankali,ga kuka,ga pressure,ga fargaba da tsoro duk sun hadu sun dabaibayeta Dole zazzabi ya damqeta me qarfi kuwa.

 

Koda jirginsu ya sauka saidai anty salamatu ta riqota suka fito sbd jiri jiri take gani.,

 

Basusan Yaya akaiba sai ganin wata white jaguar XK120 tayi parking gabansu yanayin motar kawai yasa umme gane MAHMOUD din ne sbd kusan duk Wanda yayi Masa farin sani yasan irin motocin dayake hawa ko a Nigeria ko aqasashen waje.

 

Zagayawa tayi tabude gaban motar tacewa salamatu" Zo sakata anan salamatu.

 

Qwacewa tafara qoqarin yi Jin ance zata shiga gaban motar umme ta kalleta ba Wasa a fuskanta tace"

 

Salamatu zoki shiga mutafi tunda ita Bata tashi tafiyarba.

 

Jin kamar ran ummen yafara baci yasa ta shiga gaban motar ahankali  tareda rufewa tana jinginar da kanta tana kallo gefe zuciyarta na sake cunkushewa.

 

Shiru dukkaninsu Babu me Magana har suka isa wani kyakkyawan building din dake jerin wasu Athens self-contained flats.

 

Parking yayi acikin qatuwar harabar kafin suka firfito shine yafara wucewa gaba kansa na juyawa sbd  baisan ta Yaya zai zauna da mutane acikin gidansa ba Sam baya iya zama da mutane musamman ana inda yake sakewa yayi rayuwarsa gashi harda umme.

 

Forth floor ne nashi Dan haka suna fitowa lift din forth floor da sunansa baro Baro dake rubuce akan qofar shiga sukaci karo *_MD ZABEERA_*

 

da security password yabude qofar yafara shiga tareda kunna fuse na wutar gidan take komai ya kawo haske anty salamatu ta bude Ido da baki tana kallon aljannar duniya tashigo tana kallon sama idanuwanta kaman zasu fado,

Haduwarsu da familyn ZABEERA yasa idonsu suka Dan bude da ganin rayuwar masu kudi da Kuma ganin daular masu kudi Amma anan Kam taga Abinda duk kyau da tsari tareda dukiyar zabeera Bata gani acan ba.

 

Umme ma data Saba da yawon qasashe Saida Nan din ha burgeta sosai ta yaba saidai flat din 2 bedrooms ne bayan master bedroom dake Dan daga gefe saman qananun stairs Wanda aka zagaye da glass door.

 

Sauran 2 bedrooms din Kuma sune suke kallon juna daga gefen hanyar dining can umme tace su nufa sbd ganin can ne masaukinsu danshi tuni yayi hanyar master bedroom dinsa yashige qofar glass din kafin ya nufi qofar asalin bedroom din.

 

Umme ce tashiga dayan bedroom din Amatu da salamatu suka Shiga daya bayan salamatu ta kwantar da Muhammad toilet tafada da sauri sbd fitsarin datake ji tun acikin jirgi Amma tsoro ya hanata ko motsawa bare tayi Magana.

 

Amatu kuwa bakin gado ya zauna tareda rafka tagumi tana dafe kanta dake tsananin Mata ciwo ga tunanin duniya daya kasa barinta.

 

 

Dayake dare ne Babu Wanda yadamu da wani abinci salloli kawai sukai bayan wanka suka kwanta.

Dadin AC da qamshi me sanyaya zuciya tareda gajiyar dake taredasu yasasu samun bacci me Dadi da nutsuwa.

 

 

Qarfe takwas na safe qarar doorbell yasasu fitowa kowanne a shirye sbd zuwa asibiti.

Breakfast ne umme tayi odar daga wani restaurant data bincika online Dan haka Babu Bata lokaci sukaci Wanda suka iyaci Amatu da salamatu suda Basu taba fita waje ba.

 

Bayan sungama anty salamatu batareda kowa ya sataba ta tashi tahau gyaran koina tana gamawa me gidan na fitowa sanye cikin qananan Kaya hannunsa daukeda key din mota da wayarsa sai zuba qamshinsa yakeyi ba kowa a palon sai anty salamatun Dan haka suna gaisawa yace ta sanarwa Amatu Yana mota tafito da Muhammad.

 

Yana ficewa tayi daki ta tararda ita zaune tana hawaye bayan Gama wayarta dasu kawu da iyami da wayar umme da layinta na qasar sungama qara Mata zafi da maganganunsu akan auren.

Kallonta tayi ta fada Mata saqon MAHMOUD din ko kallon anty salamatun bataiba ta miqe ta dauki Muhammad ta fice zuciyarta a cunkushe.

 

Suna barin gidan umme takira yayarta Prof zainab zabeera tace a aiko driver yazo ya dauketa bazata zauna a gidanba sbd irin wannan auren na Amatu da MAHMOUD suna buqatan abarsu su kadai Dan asamu su fahimci juna su bawa auren dama sbd so take kafin sukoma komai ya daidaita tsakaninsu duk da ita sati biyu zatayi Takoma tabarsu anan din.

 

Anty salamatu dataga ummen zata tafi duk sai taji wani iri za'a barta ita kadai tsakiyar amaren duk da umme ta jaddada mata akan ta bada himma matuqa gurin taimakawa komai yatafi daidai tsakaninsu.

Bayan tafiyar ummen wanka tayi itama ta kwanta bacci bayan ta rufe dakinta.

 

A asibiti duk wasu formalities sun cike anyi komai an kwantarda Muhammad din yabiya komai da komai anan zasubarshi saidai su riqa zuwa dubasa shine qaidar asibitin, basubaro asibitin ba sai maraice inda yunwar cikinta ta isheta  gashi asibitin da nisa sosai.

Ahanyarsu ta dawowa Babu me mgn saishi dayake amsa waya akai akai tanaji hadda anty zarah yayi waya.

 

Wanine ya damesa yanason ganinsa akan project dinsa na Nan Athens daya tsaya sbd wata babbar matsala Dole ya juya Kan motarsa ya nufi private joint dake cikin babban hotel din Athens din Yana daukar baqin mirror goggles dinsa ya sanya daidai lokacinda suka shigo gurin Wanda matakan tsaronsa da securities dinsa sukai yawa sbd girmansa da haduwarsa ga mutane sai abubuwan gabansu sukeyi.

 

Shine yafara fitowa Bayan yayi parking kafin yagama fitowa security ya bude Mata motar itama bataso fitaba sbd bataga dalilin zuwa da itaba Amma tsoron gurin da yanayin yanda gurin yake yasata fitowa ta tsaya gefensa yagama waya kafin suka nufi cikin gurin Yana sake amsa wata wayar.

##Mamuh#*_MQ 39_*

 

 

Direct wani kebantaccen guri suka nufa daga bayan joint din inda aka tanada domin VIPs itadai komai na gurin bai burgeta ba ko dogon kallo bai ishetaba sbd damuwar dasuke Wanda sukazo gurin tare,

Sam ta rasa walwalar rayuwarta tun jiyan data samu sanin shine mijin da aka daura mata aure dashi.

 

Da sauri Jan baturen yataso Yana Masa sannu da zuwa tareda miqa Masa hannu sukai shaking Yana kallon fuskar Amatu dake daure ba alamar fara'a ko wata walwala ya maida kallonsa Kan MD din Yana sake washe baki zaiyi Magana MD din ya katsesa a gajarce Yana zama yace"

 

My wife.

 

Da sauri Mr Jeremy yasake kallonta Yana sake sakin fuska da murmushi yace"

 

Nice to meet you Mrs ZABEERA.

 

Kallonsa tayi ta Dan daga gira daya kadan alamar amsawa ta zauna nesa dasu tana kallon gurin ba cikin dadin raiba sukuma suka zauna tareda fiddo laptop ya kunna yafara nunawa MD din aikin dayakeson nuna Masa.

 

Sauraron Mr Jeremy yakeyi Yana Kuma fahimtar Abinda yake Masa bayani daidai hankalin nasa ya rabu Kashi biyu ne,

 

Waiter""ya furta ahankali cikin nutsuwa daidai lokacinda wani Waiter ya nufo VIP din.

 

Yes sir""Waiter din yafada cikin Yar rusunawa.

 

Amatu ya nunawa waiter din Yana cewa abata menu ta zaba Abinda take buqata.

 

Koda aka miqa Mata menu girgiza Kai kawai tayi batareda ta juyo ta kalli gefensu ba.

 

As you wish"yafada Yana dauke hankalinsa gabaki daya daga kanta ya maida Kan aikin gabansu.

 

Awa daya,awa biyu har uku taga aikin bana qarewa bane ga uwar yunwa kamar zata illatata ta waiwayo ta kallesa akaro na kusan hudu Amma ko inda take baya kallo kamar ma ya manta da ita gabaki daya..

 

Cikowa idanuwanta sukai kamar zatayi kuka sbd baqin ciki da takaicin yimasa magana takeji Amma haka ta miqe jiki a mace ta nufesu tana sassauta damuwarta sbd kada takaici yasa ta zuzzuduma Masa zagi ayi Mara kyau.

 

Jin mutum tsaye akansu yasa Mr Jeremy dagowa Yana ganinta ya washe baki Yana bata hakurin riqe Mata Miji da yayi itadai ko kallo bai ishetaba ba MAHMOUD din take kallo Wanda ko motsawa baiyiba bare ya juyo ya nuna yasan da mutum agurin

A hasale tace"

 

Ka maidani gida sbd Banga amfanin zamana anan dinba.

 

Juyowa yayi ya zuba Mata fararen idanuwansa dasuka sanyata saurin dauke Kai zuciyarta na bugawa da sauri.

 

Fuskarta ya kalla dakyau batareda yace qala ba Jin shiru yasata juyowa zata Kuma mgn idanuwansu suka sake hadewa sbd rikicewa batasan lokacin datace Dan Allah ka maidani gida wallahi yunwa nakeji kaman Zan mutu ana wlh.....

 

Dan bude idanuwansa yayi irin da gaske kike bayan anbaki damar cin abincin kince AA.

 

Dauke Kai tayi zuciyarta na qara Dan daukar zafi saidai Bata sake cewa komaiba ta juya ta nufi hanyar mota.

 

Juyowa yayi ya kalli Mr Jeremy daya Gama washe baki Yana kallonsu cikin burgewa yayi gyaran murya Yana cewa abar sauran aikin sai zuwa gobe zai kirasa.

 

Miqewa yayi tareda karban copies na takardun aikin tareda wucewa yana kunna wayarsa daya kashe tun dazu.

 

Jikin mota ya tarar da ita fuskarta amatuqar tamke tun Kan ya qaraso ya bude motar ta shige ta rufe.

 

Yana shiga ya Dan rage sanyin ACn motar sbd sanyin daya Dan Fara saukowa kafin yaja motar suka bar gurin Yana amsa wayar Modibbo data shigo Masa.

 

Suna Isa gida ta fice motar dayake zata gane tuni tayi gaba Koda ya shigo tana tsaye gurin dining tana kwankwadar grape juice ko sanyi baida Amma Bata damuba sbd gigitar da yunwa tai Mata.

 

Gaisawa da Anty salamatu kawai yayi ya wuce hanyar dainsa bayan ya ajiye odar abincin dayayi tun suna hanya ya hade da delivery man din a qasa ya karba.

 

Tana ganin alamar abinci ne ya ajiye ko daki bai qarasa shigewaba ta nufi ledocin to hau budewa jiki na rawa ta dauki box daya tafara ci duk da abincin kamar zataiwa kanta kuka sbd rashin ma'anarsa Amma hakanan ta tuttura Tasha lemu ta saki qyasa tareda sauke ajiyar zuciya ta kalli anty salamatu dake kallonta cikin mamaki da 'yar dariyar sai alokacin tace"

 

Anty salamatu wlh bandauka Zan iya shigowa da qafafu naba sbd yunwa.

 

Murmushi antyn tayi tareda Fara gyara gurin tana cewa''

 

Amatu kenan.yanxu Wanda yafita da miji kundawo da yunwa maimakon kifara cire Masa ki Kai Masa Amma kin zauna kin qoshi abinki.

 

Anty salamatu kenan

Wane miji Kuma?

Ina umme ko bacci takeyi?

 

Dining anty salamatu ta nufa da abincin tana cewa''

 

Umme ta tafi gidan yarta tace da Dan nisa daga Nan acan zata zauna sai ankwana biyu zata Zo.

 

Kallon tsoro takebin anty salamatun tana cewa''

 

Meyasa zata tafi to?

Da Ina Nan wlh can zanbita nayi zamana acan Nima.

 

Abincin anty salamatu ta jere Masa a dining din bayan ta diba ta wuce daki batareda tacewa Amatun komaiba sbd takaicin zancenta na cewar zatabi ummen.

 

Itama miqewa tayi jiki a sanyaye ta nufi dakin saita tararda anty salamatu ta maida Mata kayanta dayan dakin da umme tabari sbd yafi girma ta jere Mata kayanta tsaf a wardrobe ta sake gyare dakin.

 

Tubewa tayi tayo wanka tazo tayi sallah Tasha maganin ciwon Kai ta kwanta take bacci yayi gaba da ita.

 

Wanka yayi shima ya fito Bayan yayi sallah ya zauna dining ya dauki box din chips daya yaci da Burger yasha energy drink ya dawo Palo ya zauna ya kunna news Yana kallo sama sama Yan amsa wayayo har tsawon lokaci kafin yakoma bedroom dinsa.

 

Washe gari Babu Wanda yagansa acikinsu sbd bai fitoba kwata kwata sai yamma lis yafito ya fice bayan fitarsa ya aiko da mota aka kaisu asibiti Basu jimaba aka dawo dasu.

 

Washe garima hakan ne yafaru ankaisu asibiti Kuma Basu sakashi a Ido ba,

Kwanaki suka Fara tafiya Amma Babu wani sabon alamari a rayuwar zaman gidan,gabaki daya Basu cika ganinsa ba sai jefi jefi sbd baya zama idan Kuma Yana Nan bai cika fitowaba,

Kullum ana kawo musu abinci so uku a yini har Anty salamatu tagaji dacin na wajen tafara Dan yimusu dubarun abinci dayake ta iya girki sai suka koma cin nata ganin sunfi son na gidan sai yasa akazo aka dauki anty salamatun aka kaita shopping din komai na abincin dazata iya girkawa.

 

Yanayin zaman yafara gundurar anty salamatu sbd Sam ko gaisuwa Bata Shiga tsakanin Amatun da MAHMOUD din saitaji duk ta tsargu da zaman gidan ta sanarda Amatu tafiyarta zatayi yabi umme inda take idan har Bata sauya ba ta ringa gaida MAHMOUD din har dakinsa Koda bai fitoba.

 

Da farko share zancen antyn tayi Amma dataga alamar da gaske antyn tafiya zatayi Dan harta Kira umme saita Fara zaman Palo tana kallo ko wayoyi idan yadawo kokuma idan yafito zai fita takan gaishesa batareda ta kallesa.

Ta bangaren Muhammad kuwa suna ganin cigaba sosai sbd sauki yafara samuwa Dan yanzu Yana kuka sosai kamar sauran babies wani lokacin idan taje asibitin sukan batashi tabasa nono da kanta basai ta tatsa Masa a roba kamar yanda ake Masa ada Kuma Yana 'dan kamawa yanzu ba laifi.

 

Yau zaune take a Palo ita kadai tana kallon wayarta data gama waya da USI tanason Kiran anty zarah Amma kamar koyaushe tanajin kunya da nauyinta takasa Kira sbd batasan ta inda zata Fara yiwa anty zarah din bayani ba.

 

Bude qofa taji ahankali cikin nutsuwa  sbd baya komai cikin hayaniya yasa tagane shine yafito daga dakinsa

batai niyar juyawa Amma ta daure ta 'dan juyo a sace ta 'dan kalli qofar.

 

Sanye yake cikin qananun kayan Shan iska sky blue me haske sosai sai slippers farare dake qafarsa da keys din mota da waya a hannunsa da alamu gurin Shan iska zaije.

 

Anty salamatu ce ta fito sanye da riga da skirt na atampa ganinsa da yanayin shigarsa yasa tadanji kunya tana dauke Kai tareda yaba kyau da kwarjini irin na MAHMOUD,

Har zata koma daki cikin Jin nauyi data Zo ta darshe tsakanin amare Kuma qanne saita Dan tsaya batareda tajuyo gaba daya ba tace"

 

Inason zuwa gurin umme nai Mata kwana biyu shine nace ko za'a kaini?

 

Zulum Amatu ta miqe tana kallon anty salamatun cikin mamaki da firgici tace"

 

Nima zanje Bari nashiryo.

 

Ko kallonta Babu Wanda yayi acikinsu ya nufi qofar ficewa Yana cewa''

 

Muje na ajeki da kaina.

 

Ko Kaya anty salamatu Bata tsaya daukowaba sbd kada Amatu tafito Basu tafiyarsu ba tabu bayansa da sauri.

 

Aikuwa kodata fito cikin Shiri tana gyara zaman gyalen jallabiyar dake jikinta taga ba kowa a palon ta nufi qofa da sauri ta fito ta hau lift zuwa qasa tana Isa suna  barin harabar building din ta tsaya tana bin hanyar gate din futa da Ido tanajin wani Abu aranta na baqin ciki Amma hakanan ta hkr ta juya Takoma ko daki Bata shigaba a Palo ta zauna baqin ciki da damuwa na cinta ta Yaya zasu tafi su barta ita kadai a gidan daga ita sai shi.

 

Har kusan qarfe goma sha biyun dare baidawoba tana daki duk da kwance take hankalinta na qofa taji shigowarsa sbd Sam takasa samun sukuni ita kadai cikin gidan aqalla dai taji motsin mutum cikin gidan zai rage tsoronta.

 

Sai qarfe daya saura taji shigowarsa ta sauke ajiyar zuciya daga kwancen tareda juyawa ta gyara kwanciyarta tana rufe Ido.

 

Washe ma haka ta wuni ita kadai gidan bataga dawowarsa ba sai cikin dare ahaka sukai kwana uku take hankalinta yafara tashi sbd tun tashinta Bata Saba rayuwa gurinda Babu hayaniyar jamaa ba Sam Bata taba ma zama ita kadaiba sai abin yake Bata tsoro shiyasa ranar kwana ta biyar tana kwance cikin damuwa tunda safe taji fitowarsa ba Shiri ta wuntsulo daga Kan gadon ta fito ko wula da suturar arziki Babu ajikinta tana futowa shikuma Yana zama Kan Kan dining da cup din ruwan tea a hannunsa sai jinta yayi kwasam akansa ya dago idanuwansa ahankali ya zuba mata ganin suturar dake jikinta take ruwan tea din dake cikin  bakinsa suka Dan sarqesa ya dauke Kai Yana Dan tari ahankali batareda ya juyo yakuma kallontaba ya miqe zai bar gurin takuma saurin Shan gabansa tana cewa''

 

Bazan iya zama anan ba inason zuwa gurinsu umme.

 

Tsayawa yayi cak tareda juyowa ya kalleta da idanuwansa dasukai 'dan ja sbd tarin da yayi Yana kallon fuskarta yace"

 

Su umme nada damar barin Nan ke Kuma akan dalilin me Zaki bar Nan?

 

Sakin baki tayi tana kallonsa Kai tsaye tace"

 

Akan dalilin ni kadai nake rayuwa kamar Mara galihu,

Inason zama tareda mutanen dasukan darajata sukasan su......

 

Idon daya watsa Mata yasa maganarta yankewa tana Dan sauke Kai daga kallon idanuwansa qasa qasa tace"

 

Nagaji.

 

Ringing din wayarsa yasashi dauke idanuwansa akanta ya dauka Yana cewa''

 

I will be there in 10min and the ticket make it 2.

 

Wuceta yayi Yana cewa''

 

Kije ki shirya.

 

Juyawa tayi ta koma daki tana cewa''

 

Dadai yafi sbd nagaji da wannan zaman rashin yancin gwara ka kaini gurinsu Kona farfado rayuwata.

 

Tsayawa tayi gaban madubi zata tube tayi saurin kallon jikinta tana Dan fiddo idanuwa sbd ganin kayan jikinta tana furta taslimah...

 

Rigar bacci ce ajikinta gajera sosai wadda ko cinya Bata Gama hawaba Kuma irin me gidan nonuwan nan ce agabana yadin me sulbi sosai gashi rigar baqace saita fiddo kyan farar fatarta.

 

Dafe goshi tayi tana sakejin damuwar abin tareda kunya me tsanani kafin dai ta tuben ta nufi toilet.

 

Wanka tayo ta Dan shafa man jaggins kadan sai spray da body mist data shafa ya sanya doguwar Turkish gown royal blue tayi rolling gyalen tafito da handbag dinta qarama sai wayarta.

 

Qoqarin zama takeyi saigashi yafito sanye cikin qananan Kaya blue black shima sai qamshinsa ya doke nata ko kallonta baiyiba ya nufi kofa Yana duba agogon hannunsa.

 

Mr Jeremy ne yazo daukarsu atunaninta gidansu ummen zasu Amma taga sunzo asibiti suka Gama Abinda zasuyi kafin suka nufi gurin shiga train Wanda yasata bude idanu tana kallon tsarin gurin suka shige first-class tun kafin su zauna aka Fara gabatar musu da jaridar karatu da abin sha,

 

Wayarsa ce tayi ringing Yana dubawa yaga video call ne zarah ke kiransa Abinda Bata taba ba

Da farko yaso qin dauka Amma ya dauka daidai lokacinda Amatu ta juyo zatai Masa Magana saigashi idanunsu sun gane musu juna itada anty zarah baro baro jikin waya take kowaccensu gabanta yayi mummunan faduwa sbd ganin Yar uwarta musamman ganin irin adon dake jikin kowaccensu

Amatu ce tayi saurin sauke Kai zuciyarta na harbawa da qarfi adon anty zarah din na cika Mata Ido sbd kwalliya ta musamman anty zarah tayi cikin wasu qananun Kaya ba komai akanta sai gashinta data zubo sbd kawai ta burge mijinta.

 

Itama Kuma anty zarah idanuwanta Basu sauka akan komaiba sai akan fuskar Amatun data canza sosai tayi fresh kamar tana cikin kwanciyar hankali da amarci.

 

Shikuwa ganin yanayin shigar zarah din tun kafin tayi Magana ya datse Kiran Yana kashe wayarsa gabaki daya sbd kada aganar Masa iyali.

 

Take Amatu taji tafiyar tafita ranta jikinta yayi matuqar sanyi batasan lokacinda ta juyo ta quresa da kallo ba tanason karantar yanayin dayake ciki da Abinda yafaru yanzu din ba.

 

Jin idanuwanta akansa yasashi Dan kallonta yaga batada niyar barin kallonsa

 ahankali cikin cool muryarsa me taushi yayi gyaran murya

Ta dauke kanta ahankali har lokacin zuciyarta Bata daina bugawa da qarfi ba.

 

Tafiyar awa daya da rabi sukayi saigasu awani gari dayake da tarin sanyi da qarancin mutane Wanda daga gani garin shaqatawar Yan honey moon ne sbd yanayin tsare tsarensa.

 

Wani boyayyan hotel suka sauka Wanda ya tsarinsa yasa take tunanin shine babba agarin sbd komai nasa farine.

 

Aiki yakawosa shiyasa suna shiga suite dinsu ko zama baiyiba ya fice yabarta bayan yayi odar abinci dakomai yasa akawo Mata.

 

Itakuma zama tayi bakin gado jikin asanyaye sbd har lokacin Bata daina ganin anty zarah da kallon datake Mata a idonta take tasakejin matsuwar gobe tayi sukoma kodan Takoma gurin Muhammad dinta da akace za'a iya Basu sallama kwanakin

Gabaki daya Jin haushin komai taji tanasake yi

Daqyar tagama Abinda zatayi ta kwanta Bayan ta sanya riga da wandon bacci masu Dan nauyi da aka kawo musu set na mace Dana namiji ta rintse idanuwanta tana son bacci ya dauketa.

##Mamuh#*_MQ 40_*

 

 

 

Kasa daukarta bacci yayi Kuma ko juye juye takasa tadaiyi lamo cikin lullubin duvet tana tunanin inda rayuwa ta daukota tun kuriciya da inda zata kaita kokuma inda yakawota yanxu,

 

Auren mijin wata Sam baya cikin mafarkinta ko tunaninta sbd itama tafison ta bugi gaba da mijinta natane bawai na wata tazo ta aura ba Wanda koma dai yayane mijin wata ta aura za'a ce,

Babbar damuwarta yanxu shine rashin sanin makomarta a wannan auren yanxu,

Tarigada tasani tabbas yaudarar kanta take da tunanin rabuwa da Rabin ran Anty zarah sbd a zabeera Kam ba Maganar saki sai bisaga girmammiyar qadda ko mutuwa,

To ita ga mutuwar ma ta raba Amma Basu barta ta tafiyarta ba an daureta da auren Wanda takewa kallon ya haramta gareta sbd Yana mijin Zarah....

 

Motsin bude qofa taji Wanda yasata sake rintse idanuwanta tana sake yin tsit sbd sanin shine yadawo

Bata tunanin iya kallonsa sbd dai ba tantama a daki daya zasu kwana dan haka gwara ta lafe gari ya waye su Dan inda dare yamusu.

 

Kallonta yayi yaga yanda take lullube har Kai sai bai damuba ya nufi closet ya tube yafada toilet yayo wanka Yana fitowa shima kayan baccin ya dauka ya sanya tareda fesa mist ya nufi gadon ya hayewarsa ya kwanta tareda Dan Jan lullubin ya shige a gajiye yake shiyasa Yana kwantawar bacci ya daukesa ba Bata lokaci.

 

Mamakinsa takeyi ta yanda ba wani tunani ya hau gadon ya kwanta bayan yaganta akai kwance,Abinda Bata saniba shi Sam baima San wani Wai ka kwanta qasa ko Kan kujera ko wani dakin Kan kowane dalili ba Abu daya yasani baya sauya gurin kwanciyarsa akan komai,

Ko agida zarah ce ma idan ta fahimci Yana tattareda gajiya wani lokacin take komawa dakinta ta kwana tabarsa ya huta shikuma tunda raayaintane wannan baitaba hanata tafiyar ba saima sakewa dayafi Yi da hakan wani lokacin

Tana cikin tunane tunanen bacci yayi awon gaba da ita.

 

Da asuba saidata Gama sallah ya tadata ta tashi tayo alwala da jallabiyarta tayi sallar tana gamawa ta cire Takoma tayi kwanciyarta Takoma bacci abinta sbd itamadai bazata iya takura kanta sbd shi ba musamman ma data lura idan ta takura kanta din ko ajikinsa.

 

Shima tana jinsa yagama wayoyinsa yazo ya kwanta kusan atare bacci Yakuma daukesu Basu farkaba sai guraren 10 na safen.

Itace tafara bude idanuwanta ta sauke akan fuskarsa dake fuskantar tata tafara kallonsa ahankali tana tuno haduwarsu ta farko data biyu data uku duk agun sata ne take taji kunyar abin nadawo Mata har batamasan tana rufe fuskarta ba tana girgiza Kai saijin tayi cikin muryar bacci yace"

 

Kadama kifara wani banzan tunani akaina I can smell your blushing..

 

Zaro Ido tayi da sauri cikin wata sabuwar kunya Amma saidatace"

 

Wane tunani zanyi akanka dazaisani Abinda kace kanaji?ni bana tunanin komai....da sauri ta yunqura ta tashi zaune zata sauka ya riqo hannunta Wanda yasata saurin juyowa ta kallesa zuciyarta na Fara bugawa da qarfi shima ahankali ya bude idanuwansa dake rufen bacci baigama dakinsu ba ya sauke akan fuskarta tayi sauri dauke Ido zuciyarta na tsananta bugu har kirjinta na sama da qasa

Ya gangaro da idanuwan nasa Kan kirjinta dake sama da qasa da sauri alamar zuciyarta ce ke harbawa da sauri batareda yayi Magana ba sai ya saketa ta dira da sauri ta shige toilet batareda tasan abinyi ba sai kawai ta bude sabbin brushes din data gani ta dauki daya tafara brush tana kasa kallon fuskarta ko a madubi sbd Jin wani iri kamar kunya kamar fargaba da tsoro.

 

Murtsike kunyarta tayi ta fito tana daure fuska ta tarardashi zaune Kan sofa Yana kunna wayarsa daya kashe da asuba ta nufi fridge ta bude ta aduko lemun carrot da lemon ta zauna a wata kujerar ta bude tafara Sha ahankali batareda ta kalli inda yake ba.

 

Yana cikin toilet aka kawo musu breakfast din dayayi oda da kayan sawa ta karba tareda ajiyewa tana qoqarin duba kayan sbd jeans ne da riguna take gani Abinda takeda burin yiwa Dr khalil zabeera kwalliyarsa har saiya manta da kowace mace duniya Bayan mahaifiyarsa Amma Ashe basuda wannan rabon.

 

Astaghfirllah" tace tana ajiye kayan daidai fitowarsa

Taso Fara cin abincin Amma gabaki daya Babu Abinda ta taba gani aciki bare tasan ya akecinsu shiyasa ta haqura harya Gama Jan ajinsa da ja Mata Rai yazo ya zauna Kai tsaye tace"

 

Nifa yunwa nakeji bansan wanne ne naciba wanne ba'a ci Yi sauri ka nunamin....

 

Baisan lokacinda ya juyo gaba daya Yana kallonta ba wato yamayi sauri...

 

Irin yanda take kallon abincin yasashi sakin wani boyayyan murmushi akaro na farko

Jin shiru tafara hasala tace"

 

Nifa yunwa nakeji nace fa.

 

Baisan lokacinda bakinsa yace"

 

Ok" ba

 

Fara zuba Mata tea yayi ya miqa Mata kafin yafara zuba Mata egg source cikin boiled veggies sbs taji dadin ci Amma Ina tana shanye tea din taci spoon daya na abincin taji zuciyarta na neman tashi ta ajiye tana kallonsa tana girgiza Kai alamar bazata iya ciba.

 

Tea din yasake zuba Mata kafin yasanya spoon yacire komai na cikin tsakiyar burger dinsu ya miqa Mata yana nuna Mata Tasha da tea din.

 

Kaf tea din ita tashanye shi sbd shikadaine Abinda zata iya sawa cikinta shikuma tana kallo yanacin abincin cikin kwanciyar hankali ganin abin zai tayar Mata da zuciya yasa ta miqe ta shige toilet wanka.

 

Bata San yanzu akeyintaba Saida tagama wanka ta daura towel takasa fitowa ta zauna ciki ta shafa Neutrogena oil din data gani aciki tazo jikin qofar ahankali tace ya miqo Mata kayanta...harta juya ta tsaya cak sbd tuno hadda bra zai miqo kenan saiya taba Mata gidan nono da sauri ta fito tana cewa''

 

Barshi barshi nafito Zan dauka da kaina,. tsayawa tayi tana Masa kallon mamaki ganinsa zaune ko alamar ma zai miqo Mata kayan beyiba kamar yanda ta zata kenan da barinta zaiyi a toilet din tayita zaman jira.

 

Takaici yasanyata daukar kayan da qarfi tana daure fuska zuciyarta na zugata akan tabi takan qafarsa ta take Amma ta share ta nufi wardrobe ta bude ta dauko undies dinta tana juyowa taga bayanan kenan yashige toilet a fili taja guntun tsaki tana cewa''

 

Anty zarah kinada qoqari gskia.

 

Turarensa ta fesa kafin ta shirya cikin kayan ta tsaya tana kallon kanta tanajin wani iri sbd irin pencil jeans dinnan ne yakama Yan dogayen siraran cinyoyinta har gwara rigar is loose me Fadi ce sosai Amma ba wani tsayi gyalen jallabiyarta ta daura akai bayan tagyara Daurin talwataccen gashinta daya dan yamutse gurin bacci.

Zaunawa tayi abinta tana lallatsa wayarta sbd dama can ita Allah beyita da nuku nuku ba Kuma burintane samun wayayyar rayuwar Jin Dadi da sakewa, Bata samu daga Wanda taketa mafarki da buri ba wato Dr khalil dinta yanzun dinma bawai tana maida burinta akan MD bane kawai dai zata sakewarta ne bazata takura kanta ba shiyasama batai wata doguwar damuwar akan kayan ba.

 

Dagowa tayi Jin motsinsa idanuwanta suka sauka Kan budadden jikinsa dake tsiyayar ruwan wanka qugunsa Kuma daureda towel brown da sauri ta dauke kanta tana Dan Sosa kanta daya dau qaiqayin bazata.

 

Ganin da gaske shiryawa zaiyi gata a zaune yasata saurin miqewa Takoma gaban TV ta qurawa Mata idanuwa ko qyaftawa batayi tana jinjina ko inkularsa lallai wannan mutumin dasuke gani a zabeera Basu sanshi ba.

 

 

Tsaf ya shirya cikin qananan kayan wainda suke kalar nata sky blue jeans da farar transparent shirt ko zama beyiba ya kalli Inda take yace ta tashi suje.

 

Da sauri ta miqe zata dauko jallabiyarta yace no need for that

Aiko tabiyosa suka fice.

 

Wata kyakkyawar mota ya karba daga hotel din tareda driver suka fita.

 

Gurin abokanan aikinsa suka Fara zuwa wani hotel dake kusada wani ruwa acan suka kwasa sukai bakin ruwan taredasu da abokin nasa mr folaye da matarsa me sabon qaramin ciki daya 'dan fito kadan.

 

Sakewa tayi da meenat matar folaye sbd yanda tayita janta ajiki take suka Fara sabo anan ne ma taci abinci sbd na Nan yanada dama sosai akan na hotel dinsu sbd akwai chips da noodles akwai pasta duk tasamu taxi daga Nan suka kwasa zuwa wani farm house inda Nan ma sunyi ciye Amatu tasamu abokiyar ciye Nan tasake suka ringa cin duk Abinda bakinsu zai iya daukar dandanonsa Dan itama meenat zuwansu na farko ne Nan da mijinta yayi da ita.

 

Basu Fara Shirin komawa ba sai dare sosai inda taji tafison masaukinsu meenat yafi Dadi ba kunya ta roqesa su koma can ga mamakinta kuwa baice komaiba Amma saigashi anyi musu folaye yasa anmusu reserving suite sukai kwanciyarsu anan.

 

Washe gari sukaso komawa Amma suka shiririce itada meenat wani gurin shopping da aka kaisu gashi yau dinma qananun kayan ne ajikinsu na yau sunfi daukar kalar fatarsu da yimusu kyau sbd black ne gashi ba laifi dukkaninsu sunada hasken fata matuqa

 

Suna zaune a wani snacks and coffee restaurant dake bakin ruwa saiga Kira yashigo wayarsa Yana dagowa yaga video call zarah na Masa.

 

Sam baisan meyasa zarah yanzu take Masa video call ba Bayan shi tunda sukai aure bai tana cewa sunyi video call.

 

Dauka yayi a natse saigata ta bayyana kyakkyawar fuskarta dataji simple makeup na Masa murmushi

Ahankali ya sauke numfashi Yana amsa gaisuwarta da dorawa da cewa''

 

You look great.

 

Wani irin Dadi ne yakusa kasheta sbd baitaba yaba kwalliyarta ba sai yau din ta washe baki tana kallon kyakkyawar fuskarsa dake fidda wani sirrin kwarjini da kyau tace"

 

Thank you,ya kake?ya Athens?

 

Dan kallon wuyanta dake bayyane sbd fadin wuyan rigar jikinta yayi ba laifi yanayin shigar ya burgesa baisan yaushe zarah  tafara koyan saka irin kayan Nan ba ya bude baki a hankali yace"

 

Alhmdlh..

 

Amatu dake hotuna da meenat tunda yafara wayar hankalinta ya Dan koma kansa tafara qoqarin sharewa gano da anty zarah yake wayar meenat ta kalleta tana cewa''

 

Da waye MD ke video call and he seems to be relaxed and cool da yanayin wayar?

 

Numfashi Amatu ta sauke tana murmushi tace"

 

Da matarshi yake waya antyna.

 

Kallonta meenat tayi dakyau tana sake duban MD dako inda suke baya kallo sai kawai tura Amatun kansa da qarfi tana cewa''

 

Oh I'm so sorry I lost my y balance.

 

Kyakkyawar faduwa tayo ajikinsa sbd Saida gaba daya qirjinta ya hadu ya manne da nasa dayake shima a bazata yajita jikinsa saiya riqeta sbd karsu Fadi qasa daka Kan kujerar dayake.

 

Anty zarah maganar da zatayi bace Mata tayi sbd ganin Amatun jikin MD ba qaramin raunana ganinta da zuciyarta yayi ba ta maida kallonta Kan kayan jikin Amatun saitaga komai iri dayane Dana MD din banbanci nata na Mata nashi na maza hakama budewar wuyan rigar Amatun yasa taji tana kamo nata tana rufewa sbd Abinda taji Yana danne maqoshinta Kai tsaye ta kashe Kiran da kanta tana barin hawayenta saukowa ta kife Kan gadon datake zaune tareda fashewa da wani irin kuka Mai ciwo.

 

Su kuwa can Amatun ce tafara sakinsa ta sauka daga Kan jikinsa tana qin kallonsa sbd yanda taji hankalinta ya tashi da yanda anty zarah ta gansu wani bangaren na zuciyarta Kuma wani irin nauyi takeji saitaji gurin ya gundureta ma gaba daya ta wuce batareda tacewa kowa komaiba.

 

Washe gari Koda qarfe dayan Rana tayi sundawo harsunyi Shirin zuwa asibiti sbd ranar ne ranar sallamar Muhammad shiyasa duk damuwarta ta kau cikin tsananin farin ciki take su umme ma sunyi waya zasu hade a asibitin gurin daukosa sbd zumudi tarigasa fitowa Yana saukowa suka fada mota suka nufi asibitin.

 

Koda suka Isa sun tarardasu umme

Kallo daya umme tai Mata tasan komai yafara daidaituwa sbd yanayin 'yar walwalarta daya Fara dawowa.

 

Bayan dogon formalities aka sallamesa aka Basu dansu murna agurin kowannensu ba'a mgn saidai anbasu kakkauran sharadin kada aringa barinsa sanyi na shigarsa sosai sukace sunji.

 

A gida sasai aka ringa kiransu ana murnar samun nasara saidai anhana ashigo jirgi dashi saiyayi qwari sosai yasamu lafiya shiyasa ana sake kwana  biyu umme ta tahowarta shima MAHMOUD din wata tafiya takamashi aka bar Mata anty salamatu.

 

Ahankali suka Saba da zaman qasar da Jin Dadinta tareda Fara sanin gurare Dan suke Kai kansu siyayya da sauran wasu abubuwan musamman dasu meenat Suma sundawo garin saita haihu zasu koma,

Ga Muhammad tuni ya warware yayi girma abinsa yanzu Yana samun nono koyaushe take ya canza yafara girma gashi hadda jiki sosai yayi gwanin sha'awa,

MD na kiranta lokuta da dama Amma iyakacinsu gaisuwa sai ya tambayi Muhammad wani lokacin ma anty salamatu yafi Kira.

Abu daya ne matsalarsu a garin shine rashin turancin arziki tayiwa kawu mgn saigashi kawu yaje har zabeera da kansa yayiwa su Andi tunin alqawarinsu na barinta karatu Allah yasa MAHMOUD din na Nan sai sukai Masa maganar yasanyata makaranta acan da zaman banzar.

 

Tunda anty zarah taji tafiya zaiyi zuwa Greece taji hankalinta nason tashi Amma ta danne sbd ba laifi ya Dade sosai a gida wannan karon saita danne harda saqon gaisuwarta ga Amatu sbd har yanxu tunda akai auren basuyi mgn ba sbd kowa bai Gama daidaituwa da al'amarin ba.

 

Zaune suke a Palo itada Muhammad dake koyan zama anty salamatu Bata Nan taje gidan meenat dake Dan zazzabi sosai ta tayata hidima.

 

Riga da guntun skirt ne ajikinta Wanda bai kamata ba ko kadan sai hular babies dake kanta Bata Gama rufe Mata gashin Kai ba Wasa takewa Muhammad sosai Yana dariya taji bude qofa batareda anyi knocking ba ta juyo da sauri cikin mamaki sai idonta ya gane Mata shi batasan lokacinda ta saki baki ba tana kallonsa da dukkanin zuciyarta.

 

Shima ita din yake kallo yanda Takoma kamar wata yarinya qarama Babu me cewa itace uwar yaron gabanta tafi Kama da yayarsa ta kusa bama ta nesa ba.

 

Muhammad dake bangala dariya ya kalla har baisan lokacinda ya sakar Masa kyakkyawan murmushi ba yana nufosu.

 

daukarsa yayi Yana kallonsa cikin tsananin qaunar yaron yace"

 

Muhammad you're looking great and handsome.

 

Kallonta yayi ta sauke kanta tana cewa''

 

Sannu da zuwa.

 

Bai amsaba bai Kuma dauke idonsa akantaba saima kissing Muhammad da yayi a fuska Yana cewa''

 

Thank you.

 

Bedroom dinsa ya nufa daukeda Muhammad Yana cewa''

 

Ko Zaki gyaramin dakin bazai rasa quraba.

 

Bayansa tabi da kallo tana mamakin kyawun daya qaro da wani irin haske

Kodan ta Dade Bata gansabane.

 

Akwatinsa ta tura zuwa dakin nasa ta kallo sbd shine shigarta na farko

Dakin komai na cikinsa farine Wanda ta fahimci shi din yanason farin Abu ta dauko mop da bucket da sweeper ta a ajiye tafara gyaran dakin bayan ta sauya Masa zanin gadon ta goge komai Yana palo tafito Bayan tagama komai ta karbi Muhammad ya wuce bedroom.

 

Da daddare Koda anty salamatu tadawo ta tararda zuwansa tunda tashige daki Bata sake fitowaba Saida safe shima tana Gama shirya musu komai ta wuce gidan meenat sbd zasu sake komawa asibiti da ita yau.

 

Dakansa ya dauketa yaje ya Samar Mata admission da komai na makaranta ya damqa Mata daga can gidansu meenat sukaje dubata.

 

Dagacan gurin cin abinci suka biya sukaci kafin suka dawo gida.

 

Kwanansa takwas a qasar kafin yatafi da kewar Muhammad daya shaqu dashi cikin kwanaki qalilan Dan kullum a hannunsa yake Rabin kwana sai dare sosai yake maidasa hannun mamansa.

Itama bayan tafiyarsa yabarsu da kewarsa sbd kwanakin kullum Muhammad na taredashi.

 

Sosai ta nitsa cikin karatunta gadan gadan musamman dayake me wuyane karatun sbd medical ne tana karantar gynecology sai yazamto hankalinta nakan karatu yanzu fiyeda komai,

USI yazo Mata tareda Dr Salman har so biyu Wanda yasata Jin Dadi fiyeda tunani musamman usi daya dauki Muhammad a hannunsa ji yayi kamar zai hadiyesa sbd so da qauna,

 

Kawu da iyami ma kullum cikin waya suke Gama umme Anty zarah ce dai har yanzu ba wani sauyi sbd takirata har so kusan uku Bata taba daukar wayarta ba shiyasa ta Dan dakata tukuna.

Ta bangaren MAHMOUD ZABEERA kuwa Babu wani sauyi a rayuwarsu saina qaunarsu data zama kamar daya akan 'dansu sbd tunda Muhammad yayi wayon sanin babansa yake zuwar musu akai akai sbd yaron dako yaushe dadynsa yakeson gani Dan tuni yayi wayo sosai Dan kusan shekararsa biyu kenan harda watanni.

Duk Wanda yasanta abaya yanzu bazai iya ganetaba idanba farin sani kayi mataba,

Ta sauya sosai daga Amatun blue fox Takoma AMATULLAH zabeera,

Sam halayyarta da yanayinta sun sauya,

Yanzu ita mace ce me nutsuwa da Kamala,

Mace ce me aji da ilimin Boko ya shigeta yake Kuma bayyane atareda ita sbd ko zaman awa daya kayi da ita zaka fahimci da likita kake zaune musamman gashi suna shekarar qarshe ta kammala karatunta,

Amatse take data samu hutun wannan shekarar taje gida sbd tayi masifar kewar iyayenta Dan tunda tazo bataje gida ba

Har gwara anty salamatu taje gida harta Dade sosai kafin tadawo gashi ko yanzu tana Shirin zuwa ganin gida Kuma tareda Muhammad zataje wannan karon,

Ga USI ma yagama karatunsa yanzu yadan Fara aiki a asibitin zabeera.

 

Yau su Anty salamatu da Muhammad suka wuce tana dawowa daga rakiyarsu airport ta shige daki ta tube tayi wanka tana fitowa ta sanya three-quarter pink da farar riga Mara nauyi ta daure gashinta da band ta saka qaramar hula ta nufi kicin ta hado flakes da sabuwar madarar ruwa me sanyi ta fito Palo tanasha taji ana qoqarin bude qofa Kai tsaye tasan MD ZABEERA ne ya shigo qasar sbd tasaba da duk zuwansa saidai suji bude qofarsa kawai baya knocking kamar sauran baqi.

 

Juyowa tayi gaba dayanta daukeda mug din hannunta ta kallesa da fararen idanuwanta kafin ta qyafta idonta saiga anty zarah ta fito daga bayansa tana shigowa tareda rufe qofar take kofin hannunta yaso kubucewa tayi saurin taresa hannunta na rawa.[

No comments

Powered by Blogger.