Min Qalb 31-35

 


MQ 31_*

 

 

MAHMOUD ZABEERA ma yau dukkanin jarumta da qarfin ransa ji yayi Yana kakkaryewa daga zuciya har gangar jikinsa, tarota kawai yayi Amma shima Jin yake kamar faduwar zaiyi,

Dr Fatima tayo gurinsa da sauri tana hawaye ta tattaro Amatun jikinta tana Kiran nurses da duk asibitin jikin kowa da zuciyarsa tayi sanyi da rasuwar Dr khalil zabeera Wanda ya zamto cikakken mutum sbd kyawawan halayensa dasukeda wuyar samu acikin mutanen yanzu.

 

Dr ashir kuwa ganin dukkaninsu kowa neman zauce musu sbd tsananin tashin hankali da sauri ya dauko kujera yakawo wa Modibbo daya tare ummen data Suma,

Kiran wasu nurses yayi aka Kama umme itama akai ciki da ita aka kwantar gadan dake gefen Wanda aka kwantarda Amatu cikin sauri aka Fara Basu taimakon gaggawa dansu farfado tinda suma.

 

Su Modibbo kuwa zaunar dashi MAHMOUD yayi dukkanin jikinsa na rawa idanuwansa sunyi jajir ko mahaifin nasu yakasa kalla

Jin yanda jikinsa ke rawa sosai yasa Modibbo dagowa da jajayen idanuwansa ya kallesa tareda dange hannunsa Yana rintse ido tareda jinjina Masa Kai alamar sai hkr.

 

Dr salman zabeera kuwa kuka yakeyi sosai kamar mace sbd rasuwar Khalil din tamkar saukar tsawa sukajita kwatsam Babu Wanda yakawo tunani ko zancen mutuwa yanzu ba'a kansaba kosu Andi dasuke tsofi Basu kawo tunanin mutuwa akansuba.

 

MAHMOUD ne yayi qarfin hali da jarumtar karban wayar Modibbo yakira Andi dake zaune cikin tsakiyar Daren Yana salati sbd baccin dayaji haka kawai ya dauke daga idanuwansa Kiran farko na asuba  dayaji anyi yasashi miqewa zaiyo alwala yafara ko nafilfili wayarsa tadauki haske alamar Kira.

 

Juyowa yayi ya kalli wayar yana mamakin Wanda ke iya kiransa a wannan lokacin saiyaga sunan Modibbo

 ya sake shiga mamaki ya dauki wayar tareda dauka cikin nutsuwa yayi sallama.

 

Daga can asibiti Saida MAHMOUD ya tattaro qarfin halin iya bude bakinsa cikin rawar muryar dabai taba ba arayuwarsa yace"

 

Muna asibine taredasu Modibbo da umme Allah yakarbi Khalil cikin Daren Nan.

 

Tsit Andi yayi tsawon mintuna Yana qoqarin kakkamo zancen dazai fada yafara da Kiran"

Innalillahi-wainna ilaihirrajiun.

 

Kashe wayar yayi tareda ajiyewa yakoma bakin gadonsa ya zauna Yana sake maimata taslima Yana jinjinawa al'amarin ubangiji dayakeyin yanda yaso alokacin da yaso,

Ya dauke Khalil bayan cika masa burinsa na kwana daya tal,

Wannan shine cikakkiyar ikon ubangiji da Babu Wanda ya Isa ya sauya sbd yau da ace dukiya da mulkinsu nada iko meya hada Khalil da mutuwa a ranar yau da ko awa ashirin da hudu aurensa baiyiba.

 

Astaghfirllah" yafara maimaita tawa Yana rintse idanuwansa ya sunkuyar dakai cikin tsananin jimamin rasa yaro me tsaftatacciyar zuciya da tausayi tareda tawakkali irin Khalil.

 

Allah yayi maka rahama yabaka hasken kabari da sakamakon gidan aljanna KHALIL.

 

 

Koda asuba tayi akai sallar asuba tuni rasuwar Khalil ta yada zabeera da familynta nako Ina da ko Ina tuni kuku ya sauka a zabeera sbd mutuwar ta girgiza kowa sbd Babu Wanda yayi tunanin mutuwa Kuma tasa adaren,

 

Koda gari yayi waye sosai tuni family suka Fara halarta zabeera tafara cika tun kafin akawo gawar tasa gida dama wainda sukazo biki Kuma dama Basu tafiba tunda a Daren jiyan aka kawo amarya Ashe basasu koma daga bikinsa ba saisunyi zaman makokinsa,

Duk Wanda ya iso saiyayi kukan wannan babban rashin na khalil zabeera sbd kowa Yana shaida kyawawan halayensa da nutsuwarsa wadda tasa yakeda jamaa ciki da wajen zabeera.

 

 

 

Ahankali tabude idanuwanta ta rufe tasake budewa tana qyaftasu

Da fuskar usi dake rungume da kanta tafaracin karo ta rufe idon ta bude taga shi din daine ta zabura da sauri ta tashi zaune har tana zamewa saura kadan ta fado qasan gadon iyami da maman junior da idanuwansu sukai jajir musamman iyami da har lokacin hawaye Basu dauke daga idanuwanta ba sukayi saurin tarota ta kallesu da manyan idanuwanta dasuka firfito sun bushe sai wani irin ja dasukayi tafara qoqarin miqewa qafafunta da hannunwanta tareda muryarta dasuke wata irin rawa tana cewa''

 

Ina...ina..Ina khalillll????

 

Sunkuyar dakai sukayi Banda iyami datayo kanta tana neman rungumeta tayi saurin qwacewa tana nufar qofar dakin asibitin USI dake kuka sosai yayi saurin tarota Yana kuka yace"

 

Amatu Ina zakije antafi dashi gida muke jira ki farko muma muke gidan.......

 

Zamewa tayi ta zube qasa tareda sakin wani irin gigitaccen kuka me qarfi dayasa asibitin suka qara daukar  shiru kowa na sake rafka tagumin rashin Khalil din dakuma kuka da tashin hankali dazata shiga idan ta farka Wanda suka shirywa Sha dama.

 

 

Tsayawa sukayi kowannensu na nasa kukan me tsananin cikin tausayinta da Kuma zafin rashinsa Suma daya bugesu  Babu Wanda yayi yunqurin hanata sbd kuka Kam yariga ya sameta abarta tayisa ko zataji sassucin radadin ZUCIYA.

 

Irin kukan datakeyi ne yasaka hankalin duk Wanda ke asibitin tashi sbd kukan nata taba zuciyoyinsu yakeyi Yana sake tuno musu da Dr khalil sbd rashinsa ne kawai yasa take wannan kukan Dan kuwa da Yana Raye Amatunsa bazatayi irin wannan kukan ba matuqar ba al'amari yafi qarfinsa bane.

 

MAHMOUD ne da kansa Modibbo yasashi yadawo asibiti yadaukosu Amatun tunda yashigo asibitin yaji tsit Yana Kama hanyar dakin datake yafara jiyo kukanta dayasashi tsayawa cak qafafunsa da zuciyarsa na qara daukar nauyin rashin Dan uwa mafi soyuwa garesa.

 

Jin kukan na kakkaryasa yasa yayi jarumtar qarasawa dakin ya tura ahankali yaci karo da ita zube bakin qofar tana kukan idanuwanta kamar zasu zazzago qasa.

 

Saurin juyawa yayi yacewa su iyami su kamota sutafi gida.

 

Daqyar suka tattarota suka saka mota suka nufi zabeera inda take cike tundaga farkon layin anguwar talakawane tako Ina bulbulowa sukeyi dukkaninsu yawanci mutanensa ne da taimako ya hadasu.

 

Ko a anguwarsu kawu jama'ar dasuka halarto dan jana'izarsa basa qirguwa

Hakama ko anguwar gidan Ibrahim daya zauna Saida yayi mutane sbd ko acikin rashin Saida ya taimaki mutane da dama.

 

Sashen Modibbo akayi da ita inda gawarsa take shimfide an lullubeta su Modibbo da Andi taredasu alhaji qarami da kawu dake gefe zaune Yana tsiayayar hawayen dasuka kasa tsaya masa,wallahi ayau ki yakeyi tamkar 'dan daya fito daga tsotsonsa ne ya rasa sbd Khalil yarone daya shiga ransa Wanda yakejin inama ace haddashi ya tsinta lokacinda ya tsinto su Amatu da Usman.

 

Kukan umme ne dake zaune gaban gawar ta daga qafafunsa tana addua tana kukan da bayama fita sbd disashewa da muryarta tayi hakama ko gani batayi sosai ayanzu sbd kumburin da idanuwanta da fuskarta sukayi.

 

Tun kafin ta iso gaban gawar tasa qafafunta suka kasa daukarta ta zube tana sake sabon kukan dake taba dukkanin mutanen dake palon tafara rarrafowa tanajan jikinta ta matso gaban gawar tana kallon fuskarsa dake bude tayi fari fes Yana sheqi kamar zaiyi murmushi.

 

Qoqarin daukewa numfashinta yafarayi Salman da USI sukayi kanta suna Kiran sunanta anty juwairiyya dake palon itama tayi saurin tarota tana shafa Mata fuskarta zuwa bayanta numfashin na Dan daidaituwa.

 

Cewa akayi su fita za'a yiwa Khalil din wanka sbd lokacin jana'izar yayi sabon kuka Amatu tafashe dashi tana kallonsa tana Kiran sunansa ganin zata karya musu zuciya yasa Andi yace juwairiyya tayi cikin gida dasu itada umme wadda sai anriqeta sbd sosai Bata gani komai sai dishi dishi.

 

MAHMOUD ne yabiyo bayansu bayan sun fito Yana rintse idon damuwar tambayar dasu Andi suka turosa yayiwa Amatun ya tsaya bayansu kadan yayi Dan gyaran murya kadan yakira juwairiyya ta tsaya tareda juyowa tana kallonsa da jajayen idanuwanta

Ya Dan kalli Amatu da umme dake hawaye Babu me lakkar qwaqqwaran motsi acikinsu a taqaicema baya tunanin zasu fahimci Abinda zai fada ya Dan dauke Kai cikin qaqalo nutsuwa yace"

 

Zaki tambayetane ko da akwai janaba atare dashi.

 

Dummm taji itama juwairiyyar tareda sauke Kai ta gyada Kai tareda matsawa gurin Amatun dake tafiya tanajan qafa jiki a sake ta riqota tana kallon fuskarta datai ja ahankali tace"

 

Amatu wanka za'a yi Masa anason sanin idan da akwai janaba ataredashi¿

 

Cak Amatu ta tsaya tareda juyowa ta kalli anty juwairiyya da jajayen idanuwanta dasuka Fara bushewa taji  sabon kuka na zuwar Mata sbd tun yanzu taqara tabbatarda mutuwa tonon asiri ce, Amma tunda tariga ta rasashi meya rage Mata tun yanzu tafara ganin tonon asiri ahankali ta juyar dakai tana qoqarin wucewa ta 'dagawa anty juwairiyya din Kai Wanda yasa MAHMOUD ZABEERA dayaga amsar data bayar juyawa ya koma Yana qoqarin Hana mutuwar jikinsa bayyana, cikin sanyin jiki ya  sanardasu Andi Nan aka Fara yimasa wanka,

Suna gamawa aka shiryasa cikin farin likafaninsa aka shimfidesa tsaf aka sake aikawa matarsa da mahaifiyarsa sukazo sukai masa adduar data Kuma Kai Amatu ga Suma akai ciki da ita aka dauki gawarsa aka fito da ita inda dubban mutane ke jira Wanda yasa iyayensa da Yan uwansa mamakin lokacinda yayi wainnan jama'ar a waje wanda yawancinsu talakawane da marasa lafiyarsa Wanda yasa Andi Jin kunyar kansa alokacin dasuke zaune suna zuba mulki da oda alokacin 'yayansu nacan suna taimakawa talakawa da marasa qarfi,

Ya tabbata koshi ya mutu yanzu bazaiyi jama'ar Khalil ba Wanda sukewa fatan ya dace tun anan.

 

 

Anyi jana'izar Dr khalil zabeera ankaisa kwancinsa na qarshe andawo anci gaba da karban gaisuwar da aketa ganin mutane kala kala a zabeera Wanda yaketa saka iyayensa da Yan uwansa alfahari da Jin sasssaucin zafin rashinsa sbd ganin Inshallah ya dace tunda kowa yazo da alkhairin dayake fada akansa.

 

 

Acan cikin gida kuwa a sashen umme ake karban gaisuwar

Umme ko Magana Bata iyawa idan anmata gaisuwa saidai daga Kai kawai Dan ko mutanen Bata ganewa sosai,

Amatu kuwa zazzabine me qarfi ya rufeta bayan anty juwairiyya da anty zarah sun taimaka Mata tayi wanka ta gyara jikinta tareda sallar asuba aka kwantar da ita a quryar bedroom din umme anty zarah ta zauna tareda ita tana shafa kanta sbd irin ajiyar zuciyar datakeyi Babu qaqqautawa kuka tuni idanuwanta suka bushe ko zuwa bayayi sai ajiyar zuciya da idanuwan datake zarewa.

 

Nuratu kuwa hajiya Maryam tafi kowa shiga tashin hankali bayan iyayen Khalil din da matarsa sbd Nuratu da abin ya buga sosai sai zabura takeyi tana somewa qarshe dai ankira likita yace saisun tafi da ita asibiti fatarsu alamarin bai taba qwaqwalwartaba.

 

 

Da daddare Amatu sashenta aka maidata tareda iyami da da anty salamatun gidansu da zasu zauna da ita kafin agama zaman gaisuwar asan abin yi.

 

Bedroom dinsa tashiga ahankali ta kunna wutar dakin tana juyowa ahankali da jikinta da Babu qarfi ko kadan idanuwanta suka tsaya akan shimfidar dasuka kwana a Daren jiyan ta qurawa jinin dayake Kan shimfidar ido tafara takawa ahankali ta Isa bakin gadon ta zube qasa tareda jawo zanin gadon ta qanqame tana sake kuka ahankali tana tuno Daren na jiya wanda yayisa a cikin yanayi na ciwo da rashin qarfin jiki sosai kamar Wanda rabo ke cizo Kuma kaman  yasan rabuwa zasuyi, gwara da Bata hanasa kantaba Ashe datafi kukan datakeyi ayanzun.

 

Cukuikuye zanin gadon tayi cikin jikinta tana shaqar qamshin jikinsa dake jikin zanin cikin kuka tace"

 

Jiya kana taredani Dr meyasa zaka tafi??????

 

Kuka take fitarwa me qaramin sauti a bakin gadon har wahalallen bacci ya dauketa zaune a qasan.

 

Sai asuba ta bude idanuwanta dasukai nauyi sbd kumburi ta tashi tana gyara zamanta kafin ta miqe ahankali tana kallon zanin gadon dake jikinta ta sake kallonsa kafin ta nannadesa ta nufi cikin wardrobe din dakin tayi Masa kyakkyawan boyo ta fito dakin takoma dakinta inda su iyami suke sanyin AC yasa wani irin dogon bacci ya daukesu,

 ta shiga toilet tayo alwala tana fitowa iyami na farkawa ganin alamar alwala atareda ita dakuma Jin ana sallah a masallacin cikin zabeera yasa tasan asuba ce ta tashi zaune tana qoqarin saukowa gadon ta nufi bayin itama.

 

Sallah Amatun ta tayar kanta na tsananin ciwo kamar zai tsage qarshe dai a zaune tayi sallar.

 

Guraren qarfe Tara na safiya aka kawo abincin safe aka jere musu a dining tareda sabuwar me aikin da aka iko ma Amatun.

 

Anty zarah ma tunda safe ta iso sashen ta gaidasu iyami dake zaune Palo jigum sbd Amatun ta rufe kanta a dakin Khalil din tanata kuka ita kadai taqi fitowa.

 

Duk yanda anty zarah tayi qin fitowa Amatun tayi salman da USI ma sunxo  sunyi sunyi taqi bude dakin Saida akaje aka sanarwa umme.

 

Ummen na zuwa qofar bedroom din nasa kasa Magana tayi itama sai kawai ta fashe da sabon kukan daya daga musu hankali

Amatu dataji kukan ummen hankalinta yaqara tashi ta rarrafo ta bude qofar tareda fadawa jikin ummen tanajin kukan ummen har cikin ranta kamar yanda idan Dr na Nan tasan zaiji kukan ummensa.

 

Daqyar juwairiyya dasu anty zarah suka sallashesu aka fadowa su Modibbo saiga Andi dakansa ya zauna yayi musu nasihu masu karya zuciya da saka tawakkali Nan suka dauki qaddara suka dangana.

 

Anty zarah ce da iyami suka Bata abinci Dan Dole Tasha tea kawai sai guntun slicebread anty zarah takaita ta watsa ruwa ta sanya doguwar riga da hijab suka dawo Palo ta zauna cikin mutane.

 

Dukkanin kulawa da cinta da yanayinta anty zarah ce takeyi sai su iyami dasuke kwana yimata addua suna tofa Mata sbd yanda take firgita cikin bacci idan ya dauketa.

 

Anyi adduar uku anyi ta bakwai an watse kowa yakoma inda yafito sai anty salamatu da sabuwar me aikinta da aka bar Mata tayi zaman takaba Wanda taso takoma gidansu tayi umme ta ringa roqonta kada ta tafi tabarta Dole akace ta zauna anan tayi takaba tukuna.

 

 

 

****

Rayuwa me sauyawa kamar yanda mutuwa take Dole hakama dangana daci gaba da rayuwa yake Dole.,

Kusan sati hudu kenan yanzu da rasuwar Dr khalil zabeera Wanda tuni wasu suka manta suka koma harkokinsu Banda Amatu da mahaifiyarsa da har abada mutuwarsa bazata taba sakinsuba,

 

USI yakoma makaranta daqyar sbd kasa tafiya yayi yabar Yar uwarsa alokacin datafi buqatarsa Amma itace da kanta ta tuna Masa cewa burin Dr khalil ne yayi karatu me zurfi Dan ya tsayu da kansa ya tsaya musu wataran kamar irin yanzu da basuda Khalil din tabbas sunyi Rashi Dan yanzu zasu koma Matsin rayuwarsu ne na dah.

 

Sosai anty zarah da anty salamatu ke kula da ita hakama kullum umme saitazo da kanta ta dubata musamman saka mutuwar arai datayi  arai sosai sai lafiya take neman gagararta sbd kullum cikin zafin jiki da zazzabin dare take,

 

Modibbo da kansa kullum yake Kira yaji lafiyarta da kansa ba saqo ba shikuwa Andi kullum saiyayi musu aikin idan da Abinda Amatun ke buqata saidai Kuma MD ZABEERA baibar ko wace irin qofa dazasu buqaci wani abinba koyaushe buqatarsu cikakkiyace daga garesa duk da baitaba zuwa inda takeba rabon daya kalli ko inda sashen yake tun ranarda ta dawo.

 

Rasuwar 'dan uwansa ta dakesa sosai harsaida hakan ya taba himmarsa da jajircewarsa a aiki shiyasa take dukkanin iya qoqarinsa gurin cire tunanin wanzuwarta a zabeera yariga ya damqawa zarah komai na buqatar Amatun harta fita takaba Dan haka yagama komai baida sauran tunani akanta saima busy daya qara saka kansa zama Dan yanzu tafiye tafiyensa sundawo dama sbd Khalil ne dake takura Masa yasa yarage tafiye tafiyensa Amma yanzu Kam sai ya qarawa kansa yawan tafiye tafiyen.

##Mamuh#

 

 

*_'yan uwa inaga anan zamu tsaya sbd duba da azumi daya riga yazo inshallah saimu Bari idan Allah yabamu yawancin ran kaiwa bayan sallah saimu qarasa Inshallah._*

_NAGODE_*_MQ 32_*

 

Gyara zama anty zarah tayi tana sake qurawa fuskar Amatun datayi haske sosai Ido tana maida kallonta zuwa hannuwanta dasukai haske sosai har wani yellow yellow sukayi taji hankalinta nason tashi gabanta na faduwa ta maida kallonta Kan fuskarta tanabinta da kallo ko Ina har zuwa qasanta ta ajiye cup din furar da Amatun tasa aka kawo Mata tana cewa''

 

Amatu yanayinki na bani tsoro da rashin nutsuwa sbd yanayinki na nuna kamar bakida jini,

 

Ruwa idanuwanta ke qoqarin kawowa tana kallon fuskarta Amatun dake zaune ka kwantarda kanta jikin sofa idanuwanta a lumshe Wanda yanzu hakan yazama tamkar dabia gareta sbd aduk lokacinda ta zauna tayi shiru idanuwanta take lumshewa sbd tunanin rayuwarta data juya Mata kamar upside down Dan kuwa sai yanzu take sake tabbatarda rashin Dr khalil zabeera arayuwarta babbar gibi ce ga rayuwarta sbd shine farin cikinta, walwalarta,gatanta,burinta,alfaharinta, nutsuwarta gatanta dama asalinta gaba daya...

 

Hawayen datake riqewane suka gangaro daga cikin rufaffun idanuwanta Wanda yasa hankalin Anty zarah sake tashi tunanin qilan eh da gasken Amatun batada jinin tunaninta ya zama gaskia ta dafe goshi tana rintse ido cikin tsananin damuwa da firgici tace"

 

Amatu Dan Allah ki bude Ido kiyi magana wannan kukan naki na zuci Yana wahalardamu masu qaunarki,

A zabeera kaf gaba daya yanzu Babu Wanda akeji dashi ake tsananin qaunarsa fiyeda kowa kamarki sbd kece Abinda duniya gaba daya ta shaida Dr khalil zabeera naso fiyeda komai har rayuwarsa,

Damuwarki damuwar kowa ce,

Kukanki baqin cikin mune,

Amatu Dan Allah kiyi hkr ki dauki dangana tareda daukar qaddarar rashin Dr Khalil sbd ganinki ahaka na karya dukkanin qwarin gwiwar ummen khalil,

Yanzu Amatu bansan yazanyiba gaki da rashin lafiya ajikinki ta zazzabin dare kullum Amma kinki ko karban magani gashi yanzu Ina sakaran ko jini na neman gagararki Amatu meyasa,meyasa......hawaye ne suka katse Mata takasa qarasa maganar ta miqe da sauri zata bar gurin Amatu ta riqo hannunta ahankali tana bude idanuwanta dasukai jajir ta zubawa fuskar anty zarah din dake hawaye tanajin qaunarta tako Ina tana shigarta tareda tausayinsu su duka.

 

Jawota tayi ta maidata zaune tana kallon fuskarta ta tashi zaune ahankali tareda sake hannun anty zarah din tana dauke idanuwanta daga kallonta ahankali ta bude baki cikin yanayi na karyewar zuciya tace"

 

Anty zarah meyasa kike qaunata har haka?

Meyasa keda Dr kuke min irin wannan son haka?

Anty zarah kinsan arayuwata bantaba samun soyayya irinta Dr khalil zabeera ba,

Shine ya koyamin sonsa alokacinda zuciyata batasan wata soyayya ba saita kudi,

Shine yabani sunan mutunci da martabar mace,

Dr khalil zabeera yazabi soyayyata fiyeda komai da kowa,

Yasa zuciyata takamu da zazzafar soyayyarsa me wuyar Bari bare mantawa Amma yatafi ya barni a daidai lokacin da zuciyata batasan komai da kowaba bayanshi,

Meyasa yatafi yabarni anty zarah Ina tsananin buqatarsa.......

 

Rufe Mata baki anty zarah tayi tana girgiza Mata Kai hawayenta itama suna gudu tace"

 

Amatu kada kiyi sa6o ki dauki dangana shima da ana bada zabin mutuwa da bazai taba zabin barinki ba sbd bazaiso ganinki cikin irin wannan halin dakike cikiba yanzu..

Kiyi hkr ki rungumi hukuncin ubangiji akanku hakan da yayi shine daidai kizama me godewa ubangiji aduk halinda Kika tsintsi kanki.

 

Sauke Kai Amatun tayi hawayenta suka Gama gangarowa ta dago tana sharewa ta kalli anty zarah datake kallonta cikin tsananin damuwa ta sauke ajiyar zuciya ahankali tareda lumshe ido ta bude ta miqawa anty zarah din hannu tana kallon cup din furar data kawo Mata.

 

Da sauri anty zarah din ta dauki cup din ta Bata tana bayyanarda Jin Dadinta na sassautowa da Amatun tayi cikin guntun zumudi tace"

 

Thank you AMATULLAH.

 

Da sauri Amatun ta kalleta tana fasa Kai cup din bakinta sbd duk duniya Dr khalil dinta ne kawai ke Kiranta da cikakken sunanta AMATULLAH.

 

Fuskewa anty zarah tayi tana qaqalo murmushi ganin tana neman dawo da gaba baya tace"

 

Banma iya fadar sunan yayi Dadi ba kaman yanda ake fada.

 

Ganin tashiga kame kamen fadar sunan datayi yasa Amatu sake sauke ajiyar zuciya tana Kai cup din bakinta  tana kurba ahankali ta lumshe ido tana gyara jinginawarta  sbd dadi dakuma karbuwa dataji bakinta da cikinta sunayi da furar saita saki jiki tanasha ahankali furan na sake sanyata lumshe ido.

 

Anty zarah ganin yanda furan tasamu karbuwa sosai agun Amatun yasata miqewa da sauri ta nufi fridge ta dauko gaba daya jug din furan ta dawo dashi ta ajiye gaban Amatun tana cewa''

 

Kawo cup din aqara zubawa Kisha

Dama nasan zakiji Dadinta sbd har sabuwar Madara na zuba Miki aciki.

 

Qara Mata tayi takuma shanyewa Saida ta shanye kusan cup uku kafin tace ta Isa abarta haka.

 

Cikin Jin Dadi anty zarah tagyara zama tana Mata fira ahankali tana matsa Mata qafafunta dasuka Dan kumbura sbd zama guri daya

Ahaka har bacci ya dauketa cikin nutsuwa Wanda rabonta da irinsa tun kafin rasuwar mijinta sai yau.

 

Gyara Mata kwanciya zarah tayi kafin ta zame ta fice daga part din gaba daya takoma nasu Nan ma wani aikin tahau sbd MAHMOUD datake saka ran  dawowarsa ayau din duk da gaba daya yinin ranar basuyi wayaba dama itace tafi Kira to itakuma yau ganin yanayin sauyin jikin Amatu yasa hankalinta yadan dauku ko yanzu tana ganin kamar hasashenta gaskia ne Amatu na buqatar ganin likita jikinta bai nuna tana lafiyaba

Dole zata fadawa umme kokuma MD idan yadawo yau asan nayi kada wani ciwo ya kamata basuda masaniya.

 

Aikin gyare gyare da girki suka hau Yi itada hafsatu sbd tuntuni ta zauna tayi nazari zata dauki shawarar Amatu ta kawo gyara arayuwar aurenta da tsakaninta da mijinta,

Zata cire shakku da tsoron mijinta ta fuskanci reality rayuwar aure sukeyi ba zaman darasiba Dan haka zata sauya kanta ta sauya zamantakewarta da MAHMOUD ZABEERA kada tayi sake lokaci ya qure Mata.

 

Sai yamma suka Gama komai tayi wanka ta sanya doguwar riga ta atampa tareda yafa qaramin qyale akanta ta hada abincin data dibarwa amatu ta jera a tray hafsatu ta dauka suka nufi can.

 

Koda suka shiga futowarta wanka kenan itama ta sanyo riga da skirt na atampa ta sanya.,

Abin mamaki maimakon taji kayan sun Mata yawa sbd Rama saitaji kamar skirt din ya kamata hakama rigar.

 

Kallon anty zarah dake kallonta cikin yanayi na tunanin dabasanma na menene ba haka kawai idan tana kallon Amatu wani lokacin saita Shiga tunanin yanzu saime Kuma zaizo gaba a rayuwar Amatun.

 

Anty zarah kina ganin na qara jiki ne kokuwa nece naji hakan?

 

Numfashi anty zarah din ta sauke tana matsowa gaban Amatun ta Dan ja rigarta daga gefe gefe taji ba wani space tasaki murmushi tana cewa''

 

Gskia baki wani qara ba inaga sbd dai kin Dade baki sakasu bane shiyasa gashi bakida wasu tsofin kayan bare kisaka Amma kiyi hkr kiyi manage tunda ba abin ado bane Kuma ba fita zakiyi ba bare kice Zaki takura.

 

Gyada kanta tayi tana sanyawa kanta hula Mara nauyi ta Dan saki fuska ta qaqalo murmushin yaqe sbd faranta ran Anty ZARAn tace"

 

Anty zarah wannan qamshin na Rabin ranki ne?

Sbd nasan shi kadaine akewa wannan Shirin na musamman.

 

Kasa boyuwa farin cikin anty zarah yayi ta saki annushuwa sosai tana cewa''

 

Amatun kin bawa MAHMOUD sunan Dole Wanda harya zauna cikin kaina Nima RABIN RAN ANTY ZARAH.

 

Falo suka fito suna cigaba da Dan fira sama sama sbd karta zaqe da yawa ganin Amatun tafara sakewa.

 

Suna zama tace"

 

Anty zarah kokinsan meyasa idon mutum ke nauyi wani lokacin kamar zasu juye ga ciwon Kai me tsanani???

 

Kallonta da kyau zarah tayi kafin tace"

 

Kinajin hakan ne?

 

Gyada Kai tayi ahankali tana cewa"

 

Qila sbd kukan danakeyi ne koyaushe.

 

Aa Amatu ba lallai hakan bane ni nafi zargin rashin ishashen jini atare dake kibari Akira likiti ya dubaki.

 

Ba buqatan hakan anty kawai daima yanzu Kwan biyun Nan nadainajin nauyin idon ciwon Kai me tsanani yafi damuna idan akwai maganin ciwon Kai kawai kiban danasha shikenan zanji sauqinsa Inshallah.

 

Akwai ibuprofen agurina Yana maganin ciwon Kai sosai yanxu idan na koma xan aiko hafsatu takawo Miki kisha kafin ki kwant kafin safe zakiji wasai.

 

Nagode anty zarah Allah yabarki da Rabin ranki yabaki zuciyarsa.

 

Wata Yar dariyar farin ciki tasaki tana qoqarin dasawa zuciyarta zancen ta hanyar cewa amin saidai Kuma wani sashen na zuciyar na ganin kamar da wuya samun zuciyar MD ZABEERA koba agurinta ba ko agurin kowama.

 

 

Salman ne yashigo palon daukeda babbar ledar fresh fruits da ledar gasassun kifin dasuka gasu cikin source din veg chips sai qamshi sukeyi.

Da kallo dukkaninsu suke binsa har su hafsatu suka karbi kayan hannunsa sukai kicin dasu Dan zubowa a tray ya qaraso ya zauna gefen anty zarah Yana kujerar dake kallon ta Amatu Yana kallonta cikin yanayi na tsananin kulawa Yana tambayarta Yaya take

Ta amsa Masa cikin yanayin sake bawa kanta qwarin gwiwa sbd su masoyanta dasuka damu kansu akan damuwarta.

 

Maida kallonsa yayi Kan anty zarah dake yankawa Amatu kankana cikin fruits dinda su hafsatu suka kawo bayam sun sake wankowa yasaki murmushi Yana cewa''

 

ZARAH Ashe MD yadawo yau.

 

Dagowa tayi tana Masa kallon mamaki da tambaya tana miqawa Amatu kankana a qaramin plate da fork.

 

Ganin alamar batasaniba akan fuskarta yasashi karban plate din dashima take miqo Masa ya gyara zama yafara Sha kafin yace"

 

Kafin nafita da yamman Nan Naga shigowar motarsa an daukosa daga airport Amma sashen Modibbo Naga motar ta nufa Kuma acan mukayi sallar magrib tare agun Modibbon Amma dai by now inaga yabar sashen Modibbo.

 

Kallonta Amatu tayi tana sake murmushi ahankali cikin nutsuwa tace"

 

Barka anty zarah.

 

Itama murmushi ta mayar musu tana gatsa apple ahankali zuciyarta na shiga yanayi na 'yar damuwa tana basarwa sbd qilan yakirata bayan dawowarsa din Dan tabar wayar acan sashensu tana charging.

 

Ganin hankalinta bai Kan Yar qaramar firar dasukeyi yasata miqewa tareda Yi musu Saida safe daidai fitowar anty salamatu daga dakin dayake zaman nata a zaman dazatai agidan kafin sukoma inda suka fito.

 

Qarosowa tayi suka gaisa da zarah dazata fice kafin ya qaraso ta zauna gefen Dr salman suna gaisawa Yana janta da Yar firar dasuka Saba tun amatu nasaka musu baki hartayi shiru ta lumshe ido tana saurarensu sbd kanta dake sarawa.

 

Shigowar hafsatu ce data dawo tasata bude idanuwanta ahankali ta saukesu akan hafsatun tareda karban maganinda anty zarah din ta aikota takawo Mata ta juya ta fice.

 

Miqewa tayi da kanta ta nufi kicin ta bude fridge ta dauko ruwa ta bude tareda ballo maganin Tasha ta maida sauran ruwan tareda fitowa tayiwa salman Saida safe ta wuce daki direct tayi sallar ishai ta kwanta sbd tsanani dataji kamar Kan nata nayi Dan har jiri jiri take gani.

 

 

 

Zarah kuwa bayan tabawa hafsatu maganin takaiwa Amatu direct sama ta nufa dakin MD bayan tasake fesa turare ta daura dankwalin kayan jikinta tana sake gyara zaman curves din rigar taje ta hado Masa abincin sukai Masa marasa nauyi a tray ta Isa qofarsa tayi knocking so daya kafin ta tura qofar tashiga bakinta daukeda sallama cikin yanayi na nutsuwa.

 

Fitowarsa wanka kenan Yana tsaye gaban mirror Yana goge ruwan jikinsa ahankali ya dago ya kallota ta jikin madubi da fararen idanuwansa ya amsa sallamar ahankali cikin muryarsa data kashe jikinta Nan take.

 

Kallonsa takeyi da dukkanin idanuwanta da bakinta da hancinta da nutsuwarta da komaima nata sbd wani sheqi da jikinsa yakeyi na hutu dayake samu.

 

Jin shiru yasashi juyowa ahankali ya kalleta yaga yanda duk ta sake gurin kallonsa ya dauke Kai ahankali tareda bude wardrobe ya janyo jallabiya Mai tsantsi da taushi brown ya saka tareda fesa spray dinsa na imperial majesty ya nufa kujera ya zauna Yana daukar wayarsa dake kashe ya kunna tareda dagowa ya zuba Mata manyan idanuwansa ya bude baki ahankali yace"

 

Nasameku lafiya?

 

Dan firgita tayi da tareda dauke idonta akansa cikin tsananin Jin nauyin mayen kallon datazo ta tsaresa dashi batareda yimasa ko sannu da zuwaba bare gaidashi.

 

Cikin Dan Jin kunya ta qaraso gefensa ta zauna ahankali ta ajiye tray din akan table tana saita kanta cikin Jan mutuncinta a natse tace"

 

Barka da dawowa,ya hanya?

 

 

Ajiye wayarsa yafarayi bayan ya saka silent ya Dan juyo ya kalleta cikin nutsuwa har zuwa adon datayi dominsa ya sauke ajiyar zuciya ahankali kafin ya dauke Kai Yana Dan sakin fuska yace"

 

Alhamdulillah,

Ya kuke?

 

Sake kallonsa tayi sbd yanda gabaki daya ko awaya yawanci tambayoyinsa suka koma Mata kalmar KU.

 

Jin shiru yasashi dagowa ya kalleta ya sake maimaita tambayarsa da cewa''

 

Kuna lafiya???

 

Zuba Mata Ido yayi sbd amsa yakeson ji.

 

Akwai matsalane acan gefen??

 

Sai alokacin ta kallesa cikin Ido sbd sai alokacin ta fahimci Amatu yake nufi ta saki ajiyar zuciya tareda sake murmushi tana gyada Kai tace"

 

lafiya kalau Nake su Amatu ma lafiya kalau suke saidai duk da Bata fadaminba inaga kamar batada lafiya sbd sauyawar datayi ga ciwon Kai me tsanani datace tana........

 

Tari me qarfi ya sarqesa na abincin dake bakinsa,

Spoon din faten dankalin daya maida cikin plate batareda yakai bakinsaba kamar yanda yayi Niya yasata kasa qarasa fadar Abinda take fada tana kallonsa ta kalli abincin cikin mamaki da fargaba tace"

 

Ya salam,

Sorry,

Lafiya?

Akwai wani Abu ne tareda abincin?

 

 

Dan lumshe ido yayi tareda budewa batareda ya kalletaba yace"

 

I lost my appetite.

 

Cikin damuwa ta matsosa da sauri Yana dafasa cikin kulawa tace"

 

Bakada lafiya ne?

Ko akawo wani abincin?

 

Numfashi ya sauke Yana sake kallonta yace"

 

No I just lost the need to eat karki damu.

 

Kasa hakura tayi ta zubo Masa coconut drink dinda tafi awa biyu tana hada Masa sbd sanin Yana qaunarsa ta zubo a cup ta miqa Masa cikin sauri da kulawa daidai kiran Salman zabeera nashigowa hannun dayayi niyyar karban drink din datake basa shi ya wuce dashi ya dauki wayar Kai tsaye Abinda bayayi Kiran farko ya daga waya,

Yanaji a rayuwarsa daga Modibbo sai Khalil ne kawai ke Masa Kira daya ya dauka.

 

MD Amatu ce ba lafiya sosai she's ko numfashi batayi and she is bleeding ba kakkautawa am taking her to hospital...

 

Aje wayar yayi Yana qoqarin saita nutsuwarsa

Saikuma kawai ya miqe tareda daukar wayarsa da key din mota yafice.

 

Bayansa zarah tabi da kallo kafin tabi hannunta dake sangale da cup din data miqa Masa bai karba ba tanaji wani nauyi na danne zuciyarta Wanda yasa idanuwanta cikowa da hawayen dabatasan Kona menene ba.

#Mamuh#*_MQ 33_*

 

 

 

Ahankali ta sulale zaune hawayen datake qoqarin maidawa suka gangaro,haka kawai zuciyarta kejin zafin Abinda yayi Mata din a yanxu

Aqalla koma menene tunda ba mutuwa akace Amatun tayi ba ya kamata yayi Mata mgn kokuma ya karba Abinda take miqa Masa din,

 

Share hawayen tayi tareda ajiye cup ahankali ta miqe ta fice tana qoqarin cire damuwar abin kwata kwata cikin ranta sbd idanma ta barshi cikin ranta itace zata fi kowa wahala.

 

Bedroom dinta ta nufa tareda sanyo gyale ta dauko wayarta ta fito tana latsa Kiran anty salamatu.

 

Cikin sanyin jiki da kulawa tace"

 

Anty salamatu menene yasamu Amatun?

Kuna Nan kokuwa anwuce asibitin?

 

Numfashin damuwa anty salamatu ta sauke cikin tsananin damuwa tace"

 

Wlh haka kawai muka dinga Jin nishinta da salati Koda mukazo harta some ga jini ba qaqqautawa sai zuba yakeyi gamu dai muna isowa asibiti yanzu tareda MD da Dr salman.

 

Katse wayar tayi ahankali tareda sauke numfashi tana sake bawa kanta qwarin gwiwa da hkr ta nufi sashen umme tana amsa Kiran mominta data Kira tana Mata barkar dawowar mijinta lfy.

 

Tana shiga umme na fitowa da jaka a hannunta Nuratu na biye da ita hankalinsu a matuqar tashe musamman umme dako lulluba gyalenta daidai takasa tadai ratayosa a wuya ta gyara cikin mota idan tashiga.

 

Fadawa motar tayi itama tace zata bisu zuwa asibitin suka wuce sbd zumudi ma Nuratu ce ta tuqa motar sbd bazasu jira shigowar driver ba daga main gate tunda akwai tafiya daga gate din farkon zuwa ciki.

 

A mota umme ta kalli zarah datai sanyi tana cewa''

 

Zarah menene yafaru ne? ko bayan magriba dinnan nayi waya da ita najita lafiya kalau har Ina godewa Allah danaji muryarta tafara sakewa da walwala,

Shin da akwai matsala ne tuntuni daban saniba kokuwa yanxune kawai abin yasameta?

 

Numfashin damuwa anty zarah ta sauke ta kalli ummen cikin sanyi tace"

 

Lafiya kalau nabarta bayan magriba dinnan tadaice tanata fama da ciwon Kai me tsanani sai jiri hakama gskia ta sauya sosai Dan saima ni nakega kaman batada jini sbd yanda tayi fayau fayau,

 

Kallonta umme tajuyo tayi gaba daya zuciyarta na bugawa daidai isowarsu asibitin suka fito suka nufi hanyar dakin dasukasan Dole tanacan sbd asibitin mijintane aka kawota,

Cikin tsananin damuwa da firgici umme ta kalli anty zarah bayan sun iso qofar dakin sun tarardasu salman a tsaye suna jira cikin rashin sukuni

Tace"

 

Zarah meyasa baki fadamin dukka wannan ba sai yanxu?

Shin Bayan jiri da ciwon Kan metace Miki tanaji?

 

Dan jujjuyawa tayi ta kallesu ganin kowa ya juyo ya zuba Mata ido Yana jiran amsarta Jin tamvayar da ummen tayi Mata MD ma dawowarsa kenan daga amsa wayar Modibbo ya qaraso Yana kallon yanda sukai cirko cirko.

 

Cikin kulawa tace"

 

No Kan ne kawai da jiri take min complain to saina Bata Ibuprofen maganin ciwon Kai........

 

What??????

 

Dr Fatima data fito dakin tafada cikin tsananin firgici tana qarasowa tace"

 

Ibuprofen?

Wayace kibata Magana batareda taga likitaba ya rubuta Mata?

Shin kinsan maganin dakika batane yasata cikin wannan hadarin gashi tana qoqarin rasa cikin dake jikinta......

 

Mene????umme tafada da tsananin qarfi tana zaro idanuwanta

Ta juyo gun zarah cikin kidima tace"

 

Meyesa Zaki Bata magani bakisan aikinsa ba?

Meyasama baki fadawa kowaba zaki dauki magani kawai kibata zarah?

Innalillahi Dr Fatima meza'ayi yanzu Dan Allah kada kubari cikin Nan ya zube Dan girman Allah ku taimakamin ku tsaida cikin Nan.

 

Nuratu da anty salamatu ma kusan duk acikin shock sukace Dr Fatima Dan Allah ataimaka.

 

Salman ma cikin tsananin damuwar yace"

 

Maganin da hafsatu takawo Mata dazun shine Kika aiko Mata?

 

Dafe goshi yayi cikin damuwa yace"

 

Dakin Fara tambayana na duba kafin kibata tunda Ina Nan I cud have checked.

 

Mutuwar tsaye zarah tayi tana rarraba idanuwanta a tsakaninsu cikin tsananin firgici da tashin hankali kowa na jeho Mata tambayar meyasa meyasa.,

Shin suna tunanin kaman da gangan tabata maganin ne? kokuwa suna tunanin zata iya cutatar da Amatun be?

 

Cikin muryarsa data sanyata juyowa ahankali ta kallesa taji ya fuskanci Dr Fatima cikin murya me nutsuwa yace"

 

Na menene ibuprofen din?

 

Na ciwon Kaine Amma irin strong din Nan kwata kwata masu ciki basa shansa infact kamar abortion pills ne ga masu ciki marasa qarfin jini ko kadan,

Gskia this is serious sbd gashi ta zubarda jini sosai har jini ma Muna buqata gskia but yanxu dai we are trying our best mugan mun tsaida jinin.

 

Kai tsaye yace"

 

Wat are the chances na cikin?

 

I can't say sir but just pray and have faith we will try all the best we can Dan muma Muna son cikin

Sai Maganar jinin daza'a saka zamu Kira blood bank dinmu mu....

 

No bana buqatan na blood bank din afara Shirin diban ledan jinin kawai.

 

Kallon cikin idanuwansa zarah keyi tanason ya kalleta ta karanci yanayinsa da yanda ya karbi zancen itace tabawa Amatun maganin Amma yaqi kallontan saima qoqarin juyawa dayakeyi yaga Andi da kansa tareda Modibbo a bayansu suna kallonsa cikin nustuwa,

 

Cikin alfahari dashi Modibbo ya jinjina Masa Kai yace"

 

Abinda kace shine daidai bama buqatan jinin wani gurin dabam munada wainda zasu bada jini da dama...

 

Andi na kallon fuskarsa dake sunkuye Yana karantar yanayinsa na kulawa da damuwa da yayi akan iyalin Dan uwansa Khalil alokacinda baya rayen ya jinjinawa qoqarinsa cikin yabawa yace"

 

Bama buqatan jinin kowa acikin dangi ma tunda uban Dan gashinan a tsaye bazai rasa jinin bayarwaba.

 

 

Office din Dr ashir suka nufa acan yasake musu bayani tareda Basu tabbacin Inshallah komai zai daidaita kafin suka tafi.

 

Iyami da kawu ma tuni suka iso asibitin

Hankalin kowa nasake hargitsa musamman yanxu da kowa yaji zancen da akwai ciki kowa yaji batareda dogon nazari ba saiyace meyasa zaa Bata magani ba tambaya

Hakan yasa anty zarah komawa gefe ta zauna cikin yanayi na tsananin damuwa da danasanin Bata maganin duk tasan cikin rashin sani tayi Amma yanda firgici kesa kowa tambayar Yana sata muzantuwa duk da Suma ta musu uxuri sbd tasan firgici ne da tsoron Abinda zai biyo baya.

 

Iyami ce tadawo gefenta ta zauna tana qoqarin danne damuwarta ta kalleta tace"

 

Karki damu zarah ko zubewa cikin yayi qaddararsa ce,

Koni da agabana take kowane irin magani Zan iya Bata na ciwon Kai tunda bamu sani ba.

 

Daga Mata Kai kawai zarah din tayi batareda ta iya ko magana ba

Duk Wanda zaiga gangancin Abinda tayi bazata damuba mutum biyu kawai takeson su fahimci niyyarta da rashin saninta,

Daga MAHMOUD sai Amatun

Amma sai zuciyarta na ganar mata zaiyi wuya MAHMOUD yayi Mata kuskuren fahimta sbd yafi kowa sanin Abinda zata iya aikatawa musamman akan Amatu da kowa ya shaida da zuciya daya take qaunarta.

 

Cikin ikon Allah ansamu anshawo Kan matsalar jinin ya tsayu cikinma ya tsayu saidai Kam Babu dogon aiki ko motsin dazai iya taba lafiyar cikin Dan haka hutu ne kawai akeso tayita yi jinin ma ansaka Mata roba daya Kuma alhmdlh jikin bai wani Yi baiyiba tafarko har so biyu anty salamatu da iyami na Bata tea sbd sune suka kwana anan.

 

Hankalin kowa ya kwanta musamman umme da tunda safe Takoma asibitin kusan tareda zarah suka iso Dan motarsu atare tashigo harabar asibitin Kuma kowanne da kayan breakfast ya iso.

 

Gaisawa sukayi suka Isa dakin tare alokacin anfito da ita wanka kenan iyami nasaka Mata doguwar riga mara nauyi.

 

Gaisawa sukayi umme na zama kusada Amatun tana qarasa gyara Mata Sanya rigar sai kaffa kaffa takeyi Wanda yasa Amatun kallonta tasaki guntun murmushi tareda riqe hannunta tace"

 

Umme bafa fashewa zanyiba kiketa Yi kaman kwai.

 

Babu Wanda be bayyanarda murnarsaba a fili da Abinda tafada sbd tun bayan rasuwar Khalil yau ne farko datai Abinda yake asalin dabiarta wato yanko Magana ba taunawa.

 

Dariyar farin ciki umme tayi bayan tagama gyara Mata zaman rigar ta zaunar da ita an jingina Mata pillow tace"

 

Ni ummen Kuma ake fadawa haka Amatu.

 

Murmushi tayi tace"

 

Umme ji nayi kamar kina min susa ne Yana sani waiwayi.

 

Kallon anty zarah tayi zatayi Magana saiga MD ZABEERA yashigo atake imperial majesty yacika gurin da sanyin qamshi Wanda yasakata lumshe ido sbd qamshin daya samu karbuwa daga yanayinta na ciki

Anty zarah ma lumshe ido tayi cikin yanayi na damuwa sbd jiya baikoma gidan ba sai dare sosai yanzu da safe Kuma tana tashi tahowarta asibiti tayi kawai sbd tayi tunanin Yana Nan din Ashe sai yanzu yake isowa gashi haryanxu basuyi Magana ba tana buqatan Magana dashi taji nasa tunanin akanta.

 

Ahankali ya qaraso ciki Yana gaidasu umme da iyami kafin ya maida kallonsa kadan akan gadon Amatun wadda ta bude idanuwanta adaidai lokacin sukai Ido cikin Ido

Da sauri kowannensu ya dauke idanuwansa shi Yana basarwa itakuma tana Dan tsuke fuska.

 

Kasa hkr zarah tayi sbd tanason Jin bakinsu su biyun akan alamarin ta juyo ta fuskancesa cikin tausasa harshe tace"

 

Ina kwana?

 

Kallonta yayi a natse ya amsa Yana qoqarin juyawa ya fice tace"

 

Ba laifina bane Abinda yafaru jiyan inatason inyi bayani Amma kamar kowa yakasa fahimtata.

 

Tsit dakin sukayi sbd Jin zancen nata musamman Amatu datakejin zancen yanzu.

 

Umme ce tayi saurin kallon Amatu kafin ta maida kallonta Kan zarah din tace"

 

Ba kasa fahimtarki akaiba zarah Amma ta Yaya Zaki yanke bata Magani without any consulting?

Da idonki Kinga Abinda yafaru da ita akan hakan,

Bai kamata ki kasa fadawa kowa Abinda yake damuntaba tun farko you should have told me ko Kuma MAHMOUD.

 

Cikowa idanuwanta sukai da hawaye bayan sunyi jajir ta dago ta kalli MAHMOUD din daya juya baya din bai fita ba yanajin saukar maganganun ummen har cikin ransa sbd idan har zarah tayi Dan kulawa ga Amatun bai kamata suga laifinta ba saidai ba halinsa bane tsayawa hayaniya.

 

Kallonsa zarah tayi ahankali tace"

 

Kana tunanin hakan kaima?

 

Rintse idanuwansa yayi tareda juyowa ahankali ya kalli Amatun da itama idanuwanta sukai jajir kafin ya kalli zarah din cikin radadin Abinda zai fada yace"

 

U could have asked kafin kibata maganin tunda Salman na Nan kokuma kifadawa ummen tun farko

This is irresponsible of you zarah...

 

Cikin bayyanarda tsananin damuwarta Amatu tace"

 

Me kukeyi wa anty zarah haka?

Kallonsa tayi Ido cikin Ido tace"

 

Kuna tunanin anty zarah zata iya cutatar Dani ne ko me? Ni banganeba,

Nice nace anty zarah tabani magani idan tanada bayan haka idan anty zarah tasan Ina tareda wani Abu atare Dani wlh bazata taba bani Abinda zai cutatar daniba bama haka wlh na tabbata a duniya idan akwai meson Abinda yake taredani bayan ni da mahaifinsa da Yana Raye to anty zarah ce idan da ace tasani,

Meyasa zaku dasa ayar tambaya akanta Bayan dukkanin shedarta yakamata ku bayar,

Umme kadaki zargi anty zarah akaina ko Abinda yake taredani Dan Allah ko anan gabane hakan Yana karya zuciyar me hakuri wlh,

Zaku iya dasa Mata wani tunani na dabam Bayan ba haka takeba kunfi kowa sani musamman Kai zatafi Jin zafi idan kayi Mata wannan tunani""taqarasa fada tana dauke idanuwanta daga cikin nasa daya zuba mata Yana kallonta da idanuwa a bude sbd akaro na farko ta tayasa fadar Abinda yake cikin zuciyarsa sbd shine yafi kowa sanin zarah bazatayi ko kusan hakanba Akan wani bare akan wannan silly yarinyar.

 

Numfashi ya sauke ahankali tareda kallon cikin idanuwan Amatun kafin ya juyo ya kalli zarah da idanuwanta sukai jajir cikin kulawa da taushin harshe yace"

 

Lets go.

 

Kallonsa tayi zuciyarta na narkewa,fushinta na wankewa sbd yanda yayi ya nuna kulawarsa gareta tareda nuna damuwarsa akanta

Cikin sanyi tace meyasa nakesonka sosai hakane MAHMOUD DAHEER ZABEERA?

 

Ahankali ta sauke idanuwanta daga kansa tana cewa''

 

Nakawo Mata breakfast inason zanbata da kaina.

 

Wani irin kallon are you kidding  me?yayi Mata Yana mamakin halinta na rashin Jin zafi.

 

Murmushi tasake cikin sanyi tareda daga Masa Kai

Ahankali yace ok tareda juyowa ya fice zuwa office din Dr Fatima.

 

Qoqarin zuba Mata abinci umme tayi Amatun tayi saurin hanawa tana kallon anty zarah cikin murmushi tace"

 

Umme antyna ce zata bani abinci da kanta Dan Allah.

 

Kallon zarah din umme tayi cikin Jin nauyi kadan duk da ita Bata dauki maganarsu cin fuska ga zarah din ba sbd tun farko yakama kafin kabawa wani magani kabari likita ya rubuta Masa Mana.

 

Iyami ce taqara dorawa da bawa zarah haquri tareda matsa Mata ta matso Dan bawa Amatun Abinda takawo Mata.

 

Cikin farin ciki da cire damuwar Abinda ya wuce din ta zubawa Amatun kunun gyada da plantain ta miqa Mata tana cewa''

 

Kici sosai sbd kisamu qarfin haihuwa idan lokaci yayi Dan karki manta da alqawarin da kukaimin keda Dr khalil  na cewa zaku bani Abinda zaku Haifa tun a wancan cikin na iska.

 

Dariya kowa yayi a dakin Banda Amatu da kewar Dr da tunaninsa ya dawo mata.

 

Yamma sosai aka sallameta Salman ya kalli su kawu da iyami Bayan dukkaninsu sun fito harabar asibitin za'a tafi gida yace"

 

Kawu muje saina saukeku a gida su Kuma su tafi a motar umme ga Kuma motar zarah MD ma Yana cikin asibitin Naga shigowarsa kafin ayi sallamar inaga Yana tareda likitocin.

 

Kallon salman din kawu yayi kafin ya maida kallon gun umme da Amatu yace"

 

Ai Amatu tafiya zanyi da ita tayi takabarta tareda renon cikinta a gida sbd hankalin iyami rabuwa zaiyi da ni kaina....

 

Zaro idanuwa waje umme tayi hakama zarah dashi kansa Salman din.

 

Cikin rawar murya umme tace"

 

Kawu kayi hakuri Amma bangane ainihin Abinda kake nufi ba.

 

Ina nufin tunda dai dama gida zata dawo ko Bayan takaba gwara Takoma can din tayi zaman idan yaso bayan haihuwar sai asan nayi......

 

Bayansa dukkaninsu sukabi da kallo Babu me iya Magana sbd girgizar zancensa

Ganin suna kallon bayansa yasashi juyawa sai sukai Ido biyu da MAHMOUD dake tunkarosu cikin tafiyarsa me nutsuwa.

##Mamuh#

 

 

*Littafin Nan na kudine kabiya ka karanta cikin nutsuwa da aminci.**_MQ 34_*

 

 

 

 

 

Fuska kawu ya sake bayan isowar MD yace"

 

MAHMOUD sannu da qoqari mungode sosai Allah yasaka yayi muku albarka duk ku duka Allah yaji qan Khalilu yayi Masa rahama tareda albarkar Abinda yabari a baya.

 

Amin kowannensu yace jiki a sanyaye kafin umme ta Dora da fadin"

 

MAHMOUD kayi Magana da kawu Dan Allah yabar Amatu harta haihu tukuna ayi maganar tafiyarta.

 

Miqawa zarah takardar dake hannunsa Wanda Fatima tabayar kafin ya kallesu cikin rashin son Jan dogon zance yace"

 

Kutafi zamuyi mgn da kawun Zan wuto da ita idan angama.

 

Kallonsa umme tayi tana miqa dukkanin yardarta akan cika maganarsa na zai dawo da Amatun zabeera idan sun barta.

 

Ahankali ya gyada Kai Yana Dan rufe Ido.

 

Kallon Amatun umme tayi jiki a matuqar mace tace"

 

Ina jiran dawowarki Amatu.

 

Gyada Mata Kai tayi tana murmushin Bata qwarin gwiwa kafin ta kalli anty zarah da ita tayi wani iri tace"

 

Anty ZARAH saki fuskan Mana saikace Rabin ranki ne akace za'a tafi dashi.

 

Guntun murmushi anty zarah din tasake tana Dan hararar Amatun tace"

 

Kina tunanin MAHMOUD zai barni yatafi wani gurin bayan tafiye tafiyensa?

Kece dai abin jimamin sbd ba'a shiga Zabeera family a fita saidai mutuwa""taqarasa tana dariyar Amatun qasa qasa.

 

Tafiya sukai suka bar Amatun taredasu iyami dasu kawun Nan kawun da MAHMOUD suka kebe sukai magana sai gashi sun wuce a motar Salman sun barta tareda MAHMOUD din

Batareda yayi Mata kallo biyu ba ya nufi motarsa bayan yace suje.

 

Drivernsa ita yafara budewa mota tashiga kafin ya zagaya ya budewa MD din yashiga ya rufe yafada motar shima ya tayar sukabar gurin.

 

Jinginar da kanta tayi baya tareda lumshe ido ta sauke numfashi ahankali sbd imperial majesty dinsa daya gaurayu da AC dakuma qamshin motar saiyake Bata nutsuwa sbd dadinsa.

 

Shikuma wayarsace datai ringing ya dauka yafara waya cikin nutsuwa a harshen turancin dayasata Dan bude Ido kadan ta saci kallonsa sbd ya tuno Mata da Dr khalil dinta idan Yana turanci zaunawa takeyi ta zubawa bakinsa Ido cikin burgewa da son koya sbd abin na matuqar burgeta tana sha'awar zama Yar gayun Yar Boko me zuba turanci Wanda tasan da Dr na Nan da yanzu tafara karatu Inshallah.

 

Ajiyar zuciya ta sauke afili Wanda yasashi Dan waiwayowa kadan ya kalli gefenta kafin yaci gaba da wayarsa.

 

Har bakin qofar palonsu motar ta tsaya direban yafito da sauri ya zagayo ya bude Mata batareda ta juyo ta kallesaba tace"

 

Nagode""ta fice ta shige palon tana sauke numfashi sbd atakure take cikin motar ko dogon motsi bakada ikon Yi kamar an takura Masa ne shiyasa ko matarsa zarah wata ran basa kwana tare sbd yawan juye juyenta da motsi Wanda ke hanasa bacci ko kadan hakan Kuma na saka Rabin kansa ciwo.

 

A palon ta tararda anty salamatu na qoqarin ajiye abincinda tafito dashi daga kicin akan dinning itada shafa'atu me aikinta.

 

Wecewa tayi dakinta Kai tsaye tayi wanka da ruwan dumi sosai kafin ta fito ta sanya jallabiya tayi sallar magriba da akayi suna hanya tayiwa mijinta addua sosai cikin farin ciki da walwala take sbd cikin jikinta ya dawo da duk wani farin ciki datake tunanin ta rasa Dan kuwa Dr khalil dinta Jin take kaman yadawo sbd tasamu Abu mafi soyuwa daga garesa.

 

Shafa cikin tayi bayan ta miqe ta zauna bakin gado ahankali ta tuno da cikin qaryarsu Wanda shauqin abin alokacin yayita shigarsu itada Dr Ashe ita kadai zata qarar da zuwan ranar,

Idan namiji na Haifa baida sunan daya wuce na mahaifinsa inshallah.

 

Wayartace tayi ringing ta juya ta kalla screen din wayar taga sunan USI

Tasaki murmushi me Fadi tana daukar wayar kusan atare sukace"

 

Lallaima.

 

Dariya suka saki lokaci daya Jin bakinsu yazo daya tace"

 

Allah USI nakusa gayawa kawu ya yafewa Yan can Kai,

Yanzu duk yinin yau sai yanzu kake kirana.

 

Dadina dake masifa ko numfashi bazaki Bari mutum ya saukeba,

Yaya jikin to?

Nayi waya dasu kawu yace ansallameki sunkoma gida.

 

Eh da magribar Nan nadawo.

 

Amah nayi Magana da kawu akan Zaki koma gida sbd zaifi Mana sauki harzuwa lokacin haihuwarki tunda ko haihuwa Kikai bana sakaran zasu karba Abinda aka Haifa din saiyayi wayo sosai kokuma idan Zaki koma makaranta

Dagani har kawu Amatu karatu yanzu mukeson kiyi.

 

Numfashi ta sauke tareda gyara zamanta tace"

 

USI Nima naso komawa gidan saidai Kuma yanada wuya su Bari nabar Nan din shiyasama kawai nabari Bayan haihuwar saina koma gida tunda koba komai Ina haihuwa na fita takaba ba sauran dalilin zamana anan din Amma dai kawu yace zaizo gobe zasuyi Magana dasu Modibbon idan sun Bari din zankoma gidan idan Kuma sun buqaci na zauna harna fita takaban duk Babu illa tunda dai lokacin zaizo.

 

Numfashi ya sauke cikin nutsuwa yace"

 

To Allah ya saukeki lafiya shine fatanmu akan komai.

 

Amin ya furta afili kafin suka shiga cikin zancen karatunsa dayayi nisa yanzu gashi Yana bada himma sosai Dan tuni ya goge cikin masu qoqarin makaranta.

 

Da daddare umme da kanta tazo tayi musu fira har kusan qarfe goma kafin ta tafi anty zarah dai ce Bata sake gani ba sai washe gari anacan ana soyewa da Rabin Rai.

 

 

 

Washe gari qarfe goma sha daya na Rana kawu ya iso zabeera tareda Dr Salman dayaje ya daukosa akan maganar komawar Amatu gida

Dama Suma su Modibbon suna jiransa sbd tun jiyanma da MAHMOUD yayi musu bayanin Abinda kawun ya buqata sukaso zuwa har gida su samesa tun cikin Daren saigashi yace yace zaizo a yau din.

 

Babban palon Andi suka Isa inda andin da Modibbo ke jiran isowar kawun

Gaidasu kawai dr Salman yayi ya ficewarsa ya barsu suka Fara tattaunawa.

 

Cikin nutsuwa Andi ya kalli kawu zaifara Magana saiga MD yashigo batareda yasan kawunma naciki ba.

 

Cikin nutsuwarsa da girmamawa ya gaidasu tareda sanarda Modibbo zaiyi tafiyane yau takamasa Kuma zai kwana biyu kafin yadawo.

 

Kallonsa Andi yayi cikin nazari harya miqe zai fice yace"

 

MAHMOUD dawo ka zauna Magana zamuyi akanka da Dan uwanka marigayi tareda Abinda yabari.

 

Maida kallonsa yayi Kan kawu cikin nuna Masa girma amatsayinsa na mahaifin 'yar dasuke son abarta cikin zuriar 'ya ko 'dan da zata Haifa yace"

 

Mal Saleh tun jiya nakejin saqonka bakin MAHMOUD

Da tun jiyan mukaso ganinka saikuma dai muka Bari yau din tunda yace kace zakazo din akan maganar,

To Mal Saleh munji zancenka amatsayinka na mahaifin AMATULLAH Kuma bamu katsi hanzarinkaba amma maganar barin AMATULLAH kwata kwata zabeera Bata tasoba sbd koba komai dai ga rabo Nan ya ratsa a tsakani Kuma bayan hakan ma tun asali zabeera shiyasa ba'a auren waje sbd irin hakan duk da qaddara ce da Babu me gujewa saidai kuma tunda AMATULLAH tashigo zuria mezaisa ta futa Dan mijinta ya rasu bayan munada Wanda zai Kare mutunci da haqqin iyalin 'dan uwansa ko ayanzu da babu ran nasa?,

 

Mal Saleh Kai ubane,bazaka so 'yarka Takoma gabanka ta Dora sabon zama na zawarci duk da Allah ne yaso hakan shiyasa muke fatan kaima kazabi barin 'yarka a killace cikin inuwar aure sabanin komawarta gabanka,

'yayanmu idan mazajensu sun rasu suna fita takaba da qanqanin lokaci muke aurar dasu ga Yan uwa mafi kusanci na mazajensu sbd dorewa acikin aure shiyasa ba alfahariba bamada tarin zawarawa acikin zuria sbd zawarcin ba Dadine dashiba,

 

Maganar aure ga me takabar dake cikin takaba haramun ne shiyasa bazamuyi maganar auren AMATULLAH ayanzu ba Amma dai muna roqonka a matsayinka na mahaifin AMATULLAH daka barta anan tayi renon cikinta ta haihu bayan haihuwarta zamu nemawa Dan uwan mijinta mafi kusanci agaresa aurenta wato MAHMOUD Wanda Inshallah aranar sunan Abinda ta Haifa tareda radin suna zamu daura musu aure Inshallah idan harka bamu dama tare Kuma da amincewa.

 

Numfashi me qarfi kawu ya fitar a fili tareda jinjina Kai sbd shima kamar yanda suka fada duk duniya Babu ubanda zaiso yarsa tadawo gabansa ta zauna ta dasa sabon zaman zawarci sai abisa qaddara,

 

Qaddara ce ta saukarwa Amatu Kuma Dole sunkarba hannu bibbiyu saidai tunda tasamu wani tayin auren gskia bazaiqi amincewa ba tunda dama suna tunanin tattarawa ne subar gidan sukoma inda Amatun zatafi sakewa da Abinda zata Haifa to tunda har mutanen nan na qaunarta harda basa iya barin ta fita wani gurin dabam tayi aure Babu Abinda yafi Masa wannan saidai tunda ba halaccin maganar neman aure akanta ayanzu zai tafi da ita still idan lokacin haihuwarta yakusa tunda zata dawo daga baya.

 

Aje numfashi yayi tareda koro musu nasa bayanin bayan amincewarsa akan idan takusa haihuwa Zata koma gida ta haihu gaban uwarta.

 

Ba wani dogon sharhi suka amince akabar maganar akan Babu Wanda za'a sanarwa yanda aka aje zancen sai bayan haihuwarta idan lokacin Daurin auren yayi.

 

Komai bai iya cewa ba sbd zancen baiyi Masa Kama da zai yiyu dinba idan har za'a tambaya ra'ayinsu kafin Daurin auren idan lokaci yayi.

 

Sallama yayi musu tareda 'yar godiyar da batakai cikinsa ba ya fice Yana duba agogon hannunsa sbd yakusa lattin Isa airport.

##Mamuh#

 

*_Dan Allah kuyi hkr kuyi manage inada uzurin fita ne amma Inshallah next pg saikun gaji da karantawa sbd tsayi_* 😁*_MQ 35_*

 

Godia kawu yasake kafin ya sake gyara zama bayan fitar MD yace"

 

To akwai 'yan burirrika dakuma kamar sharadi zance kokuma dai nace alfarma damuke nema bayan auren.

 

Cikin jinjina Kai Andi yace"

 

Muna sauraronka Mal Saleh Allah yasa me dubuwace wannan alfarmar ko sharadin.

 

Eh wato gskia Amatu dai na sha'awa dakuma ra'ayin zurfafa karatun zamaninta wato na bokon Nan

Tajima da wannan burin bama ita kadaiba wannan burinane akansu tun suna Yara gaskia saidai Kuma Hali na rayuwa baibari tasamu ilimin bokon ba sosai,

Shi kansa mijinta Allah yaji qansa kafin aurensu yayimin alqawarin barinta tasamu wadataccen ilimi bayan aurensu saigashi Allah bai basa iko ba Dan haka nake bayarda wannan buqatar ta barinta ta ilmantu acikin Boko Dan shi na addini Banda haufi akanta tasamesa yanda yakamata Inshallah,

Wannan shine buqatata

Idan MAHMOUD daku iyayensa zaku Bata wannan damar to Ina godiya da hakan.

 

Tsit sukayi suna nazartar zancen nasa sbd maganar haqiqanin gaskia yaransu Mata basa karatu anan musamman masu auren sbd qasarmu na daya daga cikin qasashen da Basu dauki Mata da daraja ba idan angansu suna yawon neman ilimi makaranta musamman akan matan aure da akafi buqatar fasikanci dasuba ayanzu akan 'yan matan shiyasa suka zabi gwara sukai yaransu qararda ba'a sansu ba suyo karatunsu su dawo,

Amma babbar matsalar anan itace ana maganar karatun Amatun ne bayan aure Kuma har wata qasar.

 

Muskutawa Modibbo yayi ya kalla Andi cikin nutsuwa yace"

 

Inaga Babu wata illa ko abin damuwa musamman tunda shi MAHMOUD din nada gida acan yawancin qasashen saita zaunama acan din shikenan.

 

Numfashi Andi Yakuma saukewa kafin ya jinjina Kai ya kalli kawu yace"

 

Yanxu duk ba lokacin wannan neba yanxu idan lokacin yayi zamuyi maganar insha Allah.

 

Sake goggodewa juna sukayi tareda maganganu dangane da gadon da Khalil yabari shidai kawu baida tacewa hakadai suka kammala kafin aka Kira Salman ta waya yadawo ya daukesa Dan maidashi gida.

 

 

***Ahankali tasanyawa kanta hkr ta rungumi qaddarar rasuwar mijinta tareda rungumar Abinda Allah yabata ta maida hankali gurin renon cikinta Wanda kusan yanzu tsakanin itada umme da iyami da anty zarah sai oga kwata kwata MD ZABEERA ba'a San yafi qwallafawa cikin Rai ba,

 

Iyami tuni tafara siyan robar wankan jariri dasu kujeran zaunawa akai ayi Masa wanka harma dasu kayan yajin abincin me jego Wanda kullum lissatafinta kenan,

 

Umme ma Kam tuni akai nisa gurin tariyar kayan jarirai hardasu kayan wasansa,

Anty zarah kuwa kayan me jegon tafi maida hankali gurin Dan siya

 

Sai oga MD ZABEERA Wanda ya damesu ya shanye gurin Tara siyayyar kayan jarirai har wainda sai ya iya tafiya da gudu kafin yayi amfani dasu dan sunfi qarfin jariri Wanda daki guda ake Tara kayan acikin sashen Amatun duk yayi tafiya yadawo scan ake Kai kayan Wanda yasa Tunanin Yama fisu zautuwa wannan Rabin ran Anty zarah din.

 

Tsakaninta dashi gaisuwa ne shima sai idan anci sa'a sun hade by mistake sbd saitayi fiyeda wata ko wata biyuma Bata gansa ba sbd sosai yanzu yarage zama sai yawan tafiye tafiye,

 

Dr Salman kuwa yayi tafiya baya qasar tun cikinta na wata hudu yayi tafiyar Amma kusan kullum ayini shida USI batasan Wanda yafi wani kiraba,

 

Cikinta yanzu Yana wata na bakwai Wanda yayi girma Dan daidai ba laifi Wanda yasa qafafuwanta Dan kumbura kadan shiyasa ma kullum ake fita da ita haraba tana Dan zagayowa sbd Dr Fatima tace taringa motsawa tana Dan zagayowa.

 

Duk wani bayani da update Akan lafiyar cikin Dr Fatima MD ZABEERA take Fara Kira sbd agurinsu tamkar shine mahaifin Abinda za'a Haifa din and kowa yasan irin shaquwarta da qaunar dake tsakaninsa da 'dan uwansa kafin ya rasu so koba a fada musu ba sunsan Babu Wanda zai dauki responsibilities na cikin Bayan shi barema Kuma shine yabada wannan odar ta komai asanar dashi har ranar haihuwar ma'ana EDD dinta duk yasani.

 

Zaune suke apalo itada anty salamatu da sai umme datazo dubata and kwana biyu tunda tashiga wata na takwas take fama da ciwon Kai me tsanani Dr Fatima tayita dubata ta sanar musu da tana fama da matsalar high BP ne Wanda Dole suyi monitoring dinsa sbd idan bai sauka ba yakoma normal to yanada wahala ta iya haihuwa da kanta saidai CS.

 

Magani umme ta miqa Mata ahankali ta karba tareda karbar robar ruwan dake gabanta ta bude ahankali tana Dan lumshe ido sbd ko Ido ta bude sosai kanta kamar zai tsage,

Maganin ta shanye tana ajiye robar daidai Dr Fatima na shigowa palon daukeda sallama suka juya dukkaninsu suka kalleta suna Mata sannu da zuwa Banda Amatun data kasa ko bude idanuwanta dake lumshe sai kawai taji hancinta na shaqo Mata qamshin imperial majesty sama sama,

Bata bude idanuwanta ba sbd tasan baitaba shigowaba Kuma tasan baida dalilin dazai sashi shigowa din dan Daman da cikin yadamu bawai ita ba to Kuma Dr Fatima ma kafin tafada musu komai dangane da cikin saita fada Masa tuntuni haka suke Dan haka Bata sakaran akwai Abinda zai taba sanyashi shigowa....

 

MAHMOUD Kaine da kanka yau?""maganar umme data sanyata bude rufaffun idanuwanta cikin rashin sa'a sai acikin nasa daya zuba Mata akaro na farko daya kafeta idanuwansa Yana kallon cikinta daya Gama girma.

 

Cire idanuwanta cikin nasa tayi akaro na farko wata irin tsananin kunyarsa ya kamata sbd ganin irin kallon dayakewa cikinta

Ta 'dan muskuta ahankali tareda Dan Jan wuyar rigarta sama sbd budadden wuyane Dan doguwar rigace Mara nauyi Sam hannunta ma qarami ne irin na shimi.

 

Ahankali ya dauke kansa Yana zaunawa a kujerar dake fuskantar Tata ya kalli umme ya bude baki cikin yanayinsa na nutsuwa cikin sauti me taushi yace'

 

Barka da yau umme,

Na sameku lfy?

 

Lafiya kalau,

Yaushe kadawo ne Dan last time Dana tambaya zarah tacemin kana Turkish.

 

I came back this evening.

 

Allah sarki to sannu da hanya.

 

Thank you umme""ya furta cikin qaramin sauti sbd Sam kwata kwata rayuwarsa bai Saba da a nuna Masa kulawaba musamman daga gareta shiyasa yaji abin wani irin har baisan Yaya zai amsa Mata dinba Bayan da qananan kalmomi.

 

Kallon anty salamatu data kawo Masa drinks yayi tareda Dan girgiza Kai Yana cewa''

 

No thank you bana buqatan komai am ok.

 

Maida kallonsa yayi Kan umme cikin nutsuwa batareda ya kalli Amatu ba yace"

 

Umme Dr Fatima tayi bayanin komai dangane da yanayin da ita take ciki wanda yakamata asan asalin menene yasa takasa kwantar da hankalinta kodan sbd lafiyan Abinda yake tareda ita,

Meyasa bazaku fada Mata ta kwantar da hankalinta ba sbd high BP dinnan is a very serious issue and I can't.....sai yayi shiru yakasa qarasa fada ya 'dan kalli gefenta kadan tareda maida kallonsa Kan Dr Fatima yace"

 

Please make her understand illolin BP game ciki please.

 

Kallonsa Dr Fatima tayi kafin tajuyo ta kalli Amatun datake mamakin yanda Ashe dama Yana Magana haka sosai saidai maganar tasa tafi Kama da kamar ransa A 'dan bace yake.

 

Cikin damuwa ma umme itama tace"

 

Hakane kam Amatu Dan Allah ki cire damuwar idanma damuwar tsoron haihuwar kika saka aranki ki cire Zaki haihu lfy munanan munata Miki addua.

 

Idanuwanta be suka ciko da hawaye har suka Fara gangarowa Wanda yasa kowa zuba Mata idanuwansa cikin mamaki da damuwa,

 

Dr Fatima ce ta Kama hannunta tajata  daki tareda ce musu karsu damu zata Magana da Amatun zataji matsalarta.

 

Daki suka Shiga tareda rufo qofa suka bar su ummen zaune tsit cikin tsumayi.

 

Kiran wayarsa akayi ya miqe ya fice a natse tareda daukar wayar Yana Magana kamar bayason Yi ya nufi hanyar sashensu.

 

Kallon Amatu Dr Fatima tayi cikin nutsuwa da kulawa tace"

 

Amatu karki damu ni likitarki ce duk Abinda na tambaya kada kiji komai karki boye ki fadamin sbd lafiyanki da abindake cikinki mukeso Kuma kema nasan bazaki so komai yasameku ba, kinada matsalar da kikeji ne dangane da cikin?

Kokuma a jikinki?

 

Numfashi ta sauke tareda sauke kallonta daga Dr Fatima din ta bude bakinta dayayi nauyi tace"

 

Dr Fatima kaina ne ke tsananin ciwo sai Kuma kamar na daina Jin motsin cikin tun jiya.....

 

Kallonta Dr Fatima tayi da sauri cikin 'yar razana amm zamtowarta likita saita saki murmushi cikin kulawa da kwantarwa da Amatun hankali tace"

 

Jiya tun yaushe ne bakiji motsin ba?

 

Tun da yamma danaji bansake ji ba.

 

Sake wani murmushin me sauti tayi tareda dafa hannun Amatun tace"

 

Kinga wannan ba wani matsalane babba ba zamu duba mugani inshallah baby lafiyansa kalau

Bayan wannan menene Kuma matsalar?

 

Dagowa tayi ta kalleta kafin tayi qasa da Ido cikin damuwa tace"

 

Ciwon Mara saikuma gashi dazu Naga jini kadan kadan kaman Yana zuwa.

 

Kama ne kokuma kingani din?

 

Nagani""tafada Kai tsaye tana bayyanarda damuwarta.

 

Ok Amatu kinaji karki damu sosai Dan akan wannan insha Allah yanzu zanje dake asibiti zandubaki acan sbd Kinga gskia lokacin haihuwarki bai Isa yiba ana haihuwane at 36weeks zuwa 40weeks harma fiye amma ke Kinga yanzu kina cikin 33weeks atleast Koda za'ayi haihuwar gaggawa ne Kikai ko 35weeks haka so yanxu zanje dake asibiti zamu duba matsalar mugani Amma kema saikin taimaka kin rage damuwar komai aranki sbd Kinga damuwace tasaka BP dinki rising and hawan BP Kuma na iya leading to komai so please Amatu kicire damuwa inshallah komai zaizo yanda ake so ake Kuma fata kinji ko??

 

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali kafin ta daga Kai tana cewa Inshallah Dr.

 

Dr Fatima ce kawai ta fito tabaro Amatun cikin daki dan tashirya tafito su tafi.

 

Zama Dr Fatima tayi ta fuskanci umme data zuba Mata Ido tana tsumayin jiran Abinda zata fada musu 

ta Dan sauke numfashi cikin yanayi na damuwa kadan tace"

 

Gskia akwai matsala dangane da yanda tace batajin motsin cikin gakuma zuban jini datace Dan haka inaga asibiti zamu Bata gado ta kwanta mufara monitoring BP dinta da lafiyar babyn har musamu takai lokacin haihuwar saidaima bazance ga komaiba yanzu sainaje asibiti munyi scanning munkuma dubata mungani musan meye abinyi.

 

Ajiyar zuciya umme ta sauke jiki a mace yace"

 

To Allah yasa miji alkhairi

Min barwa Allah komai

Allah yayi Mana jagora.

 

Amin anty salamatu da Dr Fatima sukace Suma jiki amace.

 

Dr Fatima ce ta miqe tafara ficewa tana latsa Kiran MD Dan sanar Masa halinda ake ciki.

 

Cikin doguwar rigar jikinta ta fito sai dogon hijabin data sanyo.

 

Fitowa sukayi umme na riqeda hannunta sbd qafafuwanta dasuka kumbura sosai daqyar take takasu ga mararta datai nauyi tana Mata ciwo.

 

Baqar JUGUAR RANGE ROVER suka tarar pake a bakin qofar palon akunne sai qyalli take tana aiki duk da Basa ganin Wanda ke ciki kowannensu Saida ya ayyana MAHMOUD ZABEERA ne sbd shikadaine ke dukan irin wainnan motacin a zabeera duk da kowa na dukan kalar nasa arzikin.

 

Shine da kansa yake tuqa motar

Umme ta bude baya Amatun tashiga ahankali Yana kallonsu ta mirror kafin anty salamatu tashiga

Umme tace suje zataje ta shirya zatazo daga baya.

 

Jan motar yayi suka wuce Yana tuqin ahankali kamar Wanda ya dauko me naquda.

 

Koda suka Isa Dr Fatima ta shirya komai Nan take aka karbeta akai nufi labour room da ita Dan acan zasu dubata suyi Mata scanning.

 

Anty salamatu ana Shiga da Amatun ta daga waya takira kawu tafada Masa tana kashewa saiga Kiran iyami cewa gatanan zuwa.

 

Tashin farko suna Gama dube dubensu suka gano ruwan dake riqeda babyn saura kadan su Gama tsiyayewa gashi lokaci baiyiba Dan ko kadan Bata Fara budewar haihuwa ba  suna saka ran saidai CS gashi Kuma lokaci baiyiba da saura Dan haka mun yanke zamu riqeta anan muna kulawa da lafiyarsu har zuwa Nanda sati biyu tashiga 35to 36weeks sai ayi aikin saidai gskia babyn zaizo ba qwari muna fatan yazamto rashin qwarin kawai sbd irin hakan babies din yawanci na zuwa da matsaloli"""Dr Fatima ce take fadawa MAHMOUD ZABEERA hakan acikin office dinta bayan tabaro Amatun gurin nurses suna shifting dinta zuwa dakinda zasu ajiyeta.

 

 

Zanyi tafiya Nanda 5 days but Inshallah I will be back before time din yacika Just do the best you can atare matsalar.

 

Karka damu Mr zabeera Inshallah zaka dawo kasamu both the mother and the baby lfy.

 

Thank you"yace tareda miqewa Yana dorawa da cewa''

 

Stefan zaiyi clearing bills na komai zuwa anjima.

 

Kamar zaije dakin datake saikuma ya dakata tareda kallon qofar kawai ya wuce daidai isowar su iyami suka gaisa ya fice asibitin gabaki daya.

 

 

Da daddare iyami ce kawai ta kwana tareda ita anty salamatu ranar gidansu ta wuce dan dama tanada niyyar zuwa gidan yau yin wani Abu saiga zuwa asibiti ya kamasu.

 

Umme da Haj maryam ne suka Zo da daddare suka kawo musu abinci

Anty zarah ma tazo takawo wa Amatun furar datake so,

Gaba daya Kwanakin busy take da hidimar gidanta data MAHMOUD da yanzu ta dage sosai take farautar soyayya da kulawar mijinta Wanda Amatun ke sake zugata da Bata qwarin gwiwa Kuma alhmdlh tana samun ci gaba Dan ko last month tare sukaje UK sukaga wani likita Akan matsalar rashin haihuwar ta Wanda itace ta nuna tanason ganin likita cikin sauki kuwa ya amince Mata sukaje UK din daga can Sudan suka wuce Saida sukai kusan wata daya kafin suka dawo wanda tafiyar tasa tafara fuskantar asalin irin rayuwar da mijinta MD ZABEERA takeso wato rayuwar turai shida iyalinsa Wanda duk wayewarta ita Kuma takasa koyawa kanta sbd Sam ita  saka qananun Kaya basa gabanta tafi ganin kyan kanta da burge kanta idan ta hade cikin kayanta na yarenta har gwara dogayen rigunan jallabiya taba sakawa sosai saigashi taga yanda yake rayuwa kamar asalin bature idan yabar qasarsa wato wasu irin personalities garesa boyayyu na burgewa ga wasu irin kyawawan manyan 'yan Mata masu aji dasuke huldar business dashi suna jansa da fira sosai Kuma ba laifi Yana 'dan sake musu shiyasa ta Raina kanta suna dawowa tafadawa Amatu damuwarta Wanda hakan ya sanyaya jikin Amatun itama saita Fara zugata akan ta zabure tafara duk Abinda tafara lurada yanaso tunda harta Fara samun Clue.

No comments

Powered by Blogger.