Min Qalb 26-30

 


MQ 26_*

Zaune suke a Palo itada anty zarah anty zarah na Mata fira Dan sakata nishadi ganin duk tazama so serious Wanda Sam kowa yasan ba halinta bane tafi sabawa da hayaniya shiyasa duk inda take to hayaniya na gurin.,

 

Ana bude qofar palon atare dukkaninsu suka kalla qofar shigowar kowacce fuskarta daukeda murmushin yiwa Dr khalil din maraba Musamman Amatun da murmushinta na yau ya banbanta Dana kullum sbd yau sauran zuciyar Khalil takeson qarasa sacewa sbd ta zamo Tata ita kadai shiyasa yau komai nasa na musamman ne agareta saidai sabanin ganin fuskar Dr khalil zabeera a cikin idanuwan MAHMOUD ZABEERA idanuwanta suka sauka murmushinta me sanyi da tsada akan fuskarsa yafara sauka gabanta yayi mummunan faduwa ta hadiye sauran murmushinta fuskarta na sauya cikeda mamaki da fargaba da sanyin jiki..

 

Tsayawa yayi kallonsu fuskar na bayyanarda mamakinsa daba'a cika ganewaba ganin yanda dukkansu suka waiwayo suka zuba Masa Ido kowacce fuskarta daukeda murmushin daya mugun daukar hankalinsa da sakashi wasi wasin mamakinsu musamman Amatu datafi bayyanarda murmushinta da dukkanin farin cikinta dabai taba ganiba,

Ganin Ahankali Amatu ta dauke idanuwanta dake cikin nasa tana kallon bayansa murmushinta da farin cikinta fiyeda na farko Yana dawowa yasashi dawowa MD dinsa ya sauke boyayyan numfashinda Babu Wanda yaji ya Fara takowa ahankali idanuwansa na sauyawa cikin wani boyayyan yanayin dayake ciki sbd sai alokacin ya fahimci Khalil ne keda wannan murmushi da farin cikin,

 

Zama yayi Kan couch din dakinsa Yana rintse idanuwansa tareda yamutsa kansa yanajin wani irin zafi na ratsa dukkanin jikinsa

Take kuwa zufa ya kakkaryo Masa Tako ina bayan ga kukan AC Nan yanaji yasan a kunne yake....

 

Zarah ya tuno da itama taketa washe baki tana murmushi to idan ita waccar tayi Dan Yana sunan  mijinta to itafa???

 

Jin kansa ya dauki zafi Yana neman saukewa zarah laifin sai kawai ya miqe ya fada toilet yayo wanka yayi clearing mind dinsa ya shirya cikin kayan bacci ya dauki laptop yafara wani aiki Yana basar da tunanin komai da kowama.

 

 

 

Dr khalil kuwa duk yanda yake tunanin Amatu takai cikin ransa sai yanzu yake gane ta wuce Nan sbd wannan murmushin datake jifarsa dashi yagama hargitsa Masa Kai da tunani.,

 

Zama yayi bayan sungama gaisawa da zarah ta wuce tabasu guri ya juyo suna fuskantar juna Yana kallonta cikin kulawa yace"

 

Hw are you AMATULLAH???

 

Zuba Masa idanuwanta tayi har lokacin murmushinta bai daina fitaba tace"

 

Nayi fushi ka koma na barwa Nuratu.

 

Wani irin Dadi yaji ya kamasa me sanyi cikin nutsuwarsa yace"

 

Kishi kikeyi ita tafara tarbona???

 

Harara ta sakar Masa tana cewa''

 

Zanyi maka kuka idan kasakemin maganarta.

 

Kallonta yayi Yana cewa''

 

Ok tom yanzu duk wannan adon sbd zandawo akayisa?

To Meyesa baki shafamin Dan lipstick dinnan naku danaga ana sakawaba Nuratu tasaka ita......

 

Miqewa tayi a fusace tayi dakinta Yana kiranta ko waiwayosa batayiba tana shiga gaban mudubi ta wuce Kai tsaye

Ta dauki janbaki hot red tashafa a bakinta tana kallon madubin saikuma taga tayi kyau saita dauki turare taqara fesawa tadawo palon tana kallon yanayin dayake kallonta fuskarsa na bayyanarda farin ciki sosai sai taji farin ciki yakamata sbd ganin ta kyautata Masa shiyasama take nuna kishin Nuratu sbd ganin hakan na sanyasa farin ciki.

 

Cake din datayi da fruit drink dominsa taje ta dauko takawo Masa Nan suka Fara fira cikin nutsuwarsa yake cin cake din duk da a qoshe yake Amma sbd itace tayi da kanta yakeci cikin alfahari.

 

Sai guraren qarfe goma yabar part din ta rakosa har waje kafin tadawo ciki ta wuce dakinta tanajin farin ciki kamar bazata iya bacci ba yau din.

 

 

Washe gari ataredasu Dr khalil din yayi breakfast kafin suka fita tare harda Dr Salman daya Fara aiki asibitin Dr khalil kafin ya kammala shirye shiryen sa danshi ba anan qasar yakeson aikiba.

 

Gidansu kawu suka Fara zuwa tunda ta Isa gidan kowa ke Mata wani irin kallon burgewa suna tayata murna Wanda yasata sakin baki tana kallonsu cikin mamaki.

 

bakin dakin iyami tagan akwatina a jere tsaf su maman junior sai washe baki sukeyi suna budewa iyami ma yau bakin Nan har kunne sai annashuwarta takeyi tana sake bubbudewa su maman junior kayan suna gani suna shewa.

 

tsayawa tayi tana kallonsu cikeda mamaki kafin ta juyo ta kalli su Dr khalil dasuka tsaya qofar shigowa suna Magana da kawu Wanda shima yau harda saka babbar rigar farar shadda wadda itama Dr khalil ne ya dinko mishi su kusan kala bakwai.

 

Sake juyowa tayi gurinsu iyami da suke Mata barka da zuwa Maman junior kuwa rawa tahau Yi tana janyota tana waqarsu ta yarbawa tana cewa''

 

Amatunmu tasamu mijinda zai Bata farin ciki da suna me girma na mutunci.

 

Kallon rashin fahimta tayi Mata gabanta na mummunan faduwa ta qwace da sauri zatayi Magana iyami datasan Abinda zata iya fada tayi saurin cewa''

 

Kayan Dr khalil ne jiya da daddare aka kawo.

 

Kallon iyamin tayi da sauri tareda juyawa ta kalli inda suke Magana da kawu Yana Dan sato kallon inda suke Dan yaga reaction dinta..

Wani irin farin ciki Mara misaltuwa ya shigeta da sauri ta rungume maman junior tana cewa''

 

Alhamdulillah ya Allah.

 

Dariyar farin ciki iyami ta sake tana sake sakawa Khalil din albarka sbd duk iya bincike kawu yayi akansa Kuma sun Dade da yaba nutsuwarsa da halayensa sbd a wannan zamanin basu taba haduwa da yaro me nutsuwa ba kamar Khalil din,

Shiyasa Babu wani dogon janye janye na al'adu kawu yabasa auren Amatun kawai waliyan Khalil din yake jira idan sun daidaice da khalil din sbd Khalil ya sanar dashi akwai Yar hayaniya a zuriar tasu idan ta lafa zasu zo idan Kuma akasin hakan ne ya amince asamu waliyai a daura musu aure.

 

Zama tayi gefen iyami ta bude kayan tsaf taga abinta tana sake Jin inama gobene ranar auren ayi kowama ya huta.

 

Ciki su Dr khalil din suka qaraso suka gaida iyami tareda gaisawa da sauran mutanen gidan suka koma waje suna jiran Amatun tagama ganin kayan su fito.

 

 

Kusan awa biyu ta Bata kafin ta fito suka wuce asibiti inda ya ajiyeta a office dinsa suka Shiga meeting tayi zamanta tareda miqewa a kujerarsa tana game a wayarsa daya barmata wadda kyakkyawan hotonta yake shimfide lock screen dinsa na ummensa Kuma a main screen dinsa sai hakan yasaka jikinta yin sanyi sbd a rayuwar Khalil yanzu duk Wanda yasansa yasan itada ummensa sune sanyin zuciyarsa da idaniyarsa Amma Kuma gashi Sam ko inuwa daya basa zama a taqaicema ummen Babu Wanda ta tsana a rayuwa kamarta ita Kuma Babu wadda take ganin ta rainawa wayo kamarta

sai kawai taji Bata girmama soyayyar Dr khalil dinba.

 

Sai qarfe uku suka baro asibiti sai kawai suka wuce gurin cin abinci a 5star daganan ma gurin shopping suka wuce sai gab da magrib suka shigo zabeera

Kai tsaye sashen ummensa ya nufa tana ganin sunyi parking bakin flat din tayi saurin kallonsa shima ita ya kalla Yana cewa''

 

Inason ganin Mata biyu masu mahimmanci gareni sun zama daya wannan shine babban fatana,

Amatu please kiyi hkr da duk Abinda umme ke Miki ki Bata dama kigani tanada zuciya me kyau,

Abinda nasani shine duk Abinda nakeso ummina na sonshi bare ke datasan Ina Miki tsaftatacciyar so Wanda bazan iya dainawaba

Dan haka nasan zata soki wata Rana ko Ina Raye ko bana Raye nasan wata Rana saita soki kamar yanda takesona,so please AMATULLAH ki qaunaceta ki kulamin da ita I promise you wata Rana zata daina tsangwamanki zata qaunaceki kamar yanda take qaunata.

 

Wani irin sanyi jikinta yayi sosai saitaji kunyarsa ta kamata ta dago a sanyaye ta kallesa ya da yayi saitaji kamar Bata girmama soyayyarsa ba tunda takasa girmama mahaifiyarsa.,

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali cikin sanyi tace"

 

Inshallah Zan kiyaye zancenka daga yanxu zanyi iya qoqarina gurin kyautata Mata.

 

Numfashi ya sauke ahankali yace"

Thank you AMATULLAH.

 

Fitowa sukayi suka nufi ciki Yana gaba tana gefensa jiki a sanyaye take tafiyar sbd yanayinsa duk ya Gama sanyayata ga wani irin damuwa daya shigeta ga faduwar gaban yanda zasuyi da ummen Amma koma menene tayi alqawarin jurewa sbd shi.

 

A palon farko dasuka shigo take qoqarin zama ya tsaya tareda juyowa ya kalleta yana girgiza Mata Kai tareda cewa''

 

Follow me.

 

Falonta na qurya suka nufa Wanda dagashi sai bedroom dinta Yana gaba tana bayansa.

 

Zaune take tana kallon wani Shirin girke girken larabawa da akeyi a mazzika taji shigowarsa tareda sallamarsa ta juyo fuskarta daukeda murmushin dake bayyanarda girman son datakewa Dan nata sai idanuwanta suka sauka akan wadda ke bayansa ta hadiye sauran murmushinta fuskarta na sauyawa zuwa bacin Rai da fushin ganinta ta tsuke fuska sosai tana dauke Kai daga bakin qofar.

 

Tsayawa Amatu tayi daga Inda take tana sauke Kai ganin irin kallon qyama da tsanar da ummen ke Yi Mata,

 

Qarasowa yayi gefen ummen ya zauna Yana kallon fuskarta data canza yaji ransa yaqara jagulewa ya sauke wani irin numfashi Mara Dadi Yana dafa hannun ummen cikin kulawa da sanyin jiki tareda sautin daya sakasu kallonsa duk su duka biyun yace"

 

Umme Meyesa Zaki dauki halayyar daba naki ba¿

Shin Amatu tanada wani banbanci ne da sauran mutane da Kika zabi qyamarta ita kadai?

Umme Amatu matar dazan aurace sbd Ina sonta da dukkanin zuciyata

Shin umme kodan son datakewa dan naki bazaki qaunacetaba kodan hakan?

 

Girgiza Kai tayi tana danne 6acin ranta ta kallesa tace"

 

Khalil kadaina cewa tana sonka wannan bayan kudi duk duniya Babu yaren datake ganewa,

Wannan Babu wani buri a rayuwarsu Bayan samun kudi ta ko wane halin Yaya,

Kudine kawai agabanta ta yanda zata iya yin komai akan kudi ciki ina fada maka harda mutuncinta zata iya siyarwa akan kudi,

Wlh khalil kaima sbd kudinka take sonka da bakada kudi bazata taba sonkaba

Irin wannan matar kakeson nabari ka aura Khalil???

 

Dagowa yayi ya kalli Inda Amatun ke tsaye cikin wani irin yanayi na damuwa ya sauke ajiyar zuciya tareda cewa''

 

Zo AMATULLAH,

Zo Nan kusada umme.

 

Kallon ummen tayi taga ko kallon inda take Bata qaunar Yi sbd qiyayya ta tako ahankali tazo gefensa ta zauna ahankali Kan carpet din dake gurin tana sauke kai maganganun ummen na sake jujjuyawa cikin kanta.

 

Numfashi ya Kuma saukewa cikin wani irin yanayi na damuwarsa dake bayyane wadda tasa dukansu su biyun kallonsa yasake riqo hannun ummen cikin sanyin murya yace"

 

Ummen banfara son AMATULLAH ba Sai danasan asalin wacece ita,

Nafara sonta ne bayan nasan batada kowa aduniya,

Banfara sonta ba saidanasan a bola ta tashi acan tayi wayo ta koyi gwagwarmayar rayuwa,

Banfara tsananin sonta ba saidanasan irin wahalalliyar rayuwar datayi amatsayin almajiri Mara yanci Wanda ta rayu cikinsu amatsayin namiji bayan tana matsayin mace,

Amatu bakowa mace face yarinyarda wasu bayin Allah suka taimaka suka daukesu Bayan sungama wahalalliyar rayuwa acikin bola da mataccin gidaje da shagunan daba'a gamaba,

Babu Wanda yataba kallonsu da idon Rahama,

Babu Wanda yataba duba yanayin shekaru da jinsinta amatsayin mace ya taimakesu,

Sun kwana da yunwa suntashi da ita,

Sunyi sata dan suci suyi rayuwa,

Maza da yawa sunyi yunqurin lalata rayuwarsu da sunan taimakawa shin umme Wanda yake ciki irin wannan qaddarar Dan yayi sata dan yaci ya Hana kansa Zina illa ne dahar za'a gujesa??????

 

Umme wallahi tallahi ina tsananin son AMATULLAH da dukkanin zuciyata bansan ta Yaya zanyi Miki bayani ki qaunaci Amatu ba,

Na shirya auren AMATULLAH na zamo gatanta itada zuriarta Wanda Babu wani Abu dazai sauya niyata akan hakan,

 

Shin umme kintaba zaunawa kinyi tunanin irin tarin Lada da farin cikin dazaki samu aduk lokacinda Kika kawo murmushi da farin ciki a rayuwar marayu?

Umme tarin ladace me yawa wadda zata iya gyara Miki ko wanke kurakurenki Kuma yabaki nutsuwar zuciya da ruhi....

 

Zuwa lokacin Amatu kuka takeyi sosai sbd Bata taba sanin khalil yasan asalinta ba daduk halinda suka Shiga arayuwa Kuma ahakan yake sonta tabbas yagama bawa rayuwarta girgizar data sauya zuciyarta akansa gabaki daya.

 

Umme ma hawaye takeyi sosai tsananin so da qaunar danta na ratsata...

 

Ahankali ya zamo qasa ya durqusa gabanta tareda riqo hannuwanta idanuwansa dasukai laushi na kallonta a karye yace"

 

Umme ayau gani na durqusa a gabanki Ina roqonki daki ajiye dukkanin wani burin rayuwa ko komawa Allah kodan samun nustuwar zuciya,

Umme Ina roqonki da ki qaunaci Amatu ki da zuciya daya sbd bazan iya ganinku acikin halinda kuke cikiba,

Umme......

 

Bata Bari ya qarasa ba tayi saurin dagosa tana rungumesa hawayenta na qara tsiyayowa tace"

 

Nayi maka alqawari Khalil wlh Babu wani al'amarin duniya dazan sake Bari na 6ata akansa,

Idan dai Amatu ce Kuma wlh na amince maka bazan qara qintaba idan har na tabbatarda har zuciyarta itama take sonka....

 

Rungumeta yayi da sauri Yana cewa''

 

Thank you ya umme.

 

Share Mata hawayenta yafarayi tareda juyowa ya kalli Amatu dake kuka sosai ahankali tanajin Sam Bata cancanci soyayyar khalil ba,

Zuciyarta batayi Mata adalci ba son wani 'da namiji a zuciyarta Wanda ba khalil ba...

 

Ahankali yakamo hannunta ya dawo da ita gefen umme dake kallonta cikin wani irin sabon yanayi ya zaunar da ita ahankali yace"

 

Amatu ga amanar ummi na ki kular min da ita amatsayinki na matar 'danta.

 

Dago jajayen idanuwanta tayi ta kallesa kafin ta kalli ummen ta daga Kai ahankali takasa cewa komai sai binsa takeyi da Ido zuciyarta na karban zazzafan baqon yanayi akansa  Wanda ta tabbatarda sone me zafi.

 

Murmushi umme tasaki ahankali tareda kallon Amatun tana nuna Mata gefenta tace"

 

Kimin alqawarin zaki so shi fiyeda yanda yake sonki??

 

Murmushinsa me nutsuwa ya saki Yana kawar da zancen da cewa"

 

Umme wannan son Kaine zakice ta Soni fiyeda yanda nake sonta sbd bazata iya Sona yanda nake sontaba nawa me girma ne.

 

Murmushi sukayi Banda Amatu dake Jin wani babban al'amari me girma atareda ita hakanan taji gabaki daya nutsuwarta na barinta.

 

 

Haj maryam da Nuratu dasuka jima Bakin qofar palon suna jin dukkanin Abinda yafaru baqin ciki me girma yarufe zukatansu da idanuwansu musamman nuratu data gama zaucewa a fusace ta juya tana qoqarin sakin ihun baqin ciki da zuciyarta dake neman tarwatsewa da gudu Haj maryam tabi bayanta tana cewa''

 

Yau tunda Kika juyamin baya Aisha akan danki kowa ya shirya tashin hankalin dazai biyo daren Nan Dan wlh yau sai takardun asalin Amatu sun kwana a hannun Modibbo da Andi.

##mamuh#

[4/7, 2:51 PM] Zafafa: *_MQ 27_*

 

 

 

 

Ko gabanta Bata gani ta qarasa sashensu tana qoqarin dafe qirjinta dake mugun zafi da radadi kamar zai tarwatse

Tana shiga palonsu ta zube qasa Kan gwiwowinta tareda fashewa da wani irin kuka me tsanani da zafin Rai,

 

Da sauri momynta ta qaraso ciki tana rikota tana Kiran sunanta cikin nata ciwon ran me tsanani da tausayin 'yarta tana sake kamota tace"

 

Nuratu please kada kiyi irin wannan kukan wlh karyamin zuciya zakiyi bazan iya ganinki cikin irin wannan halin ba Dan Allah kidaina kuka zamu samu mafita,

Bazan taba Bari Khalil ya auri wadda bake ba musamman wannan barauniyar karuwar yarinyar Dana Gama alwashin bazata taba aurensaba kodan yanda ya fifita sonta akanki.

 

Tsananta kukanta yayi tana girgiza Kai tana cewa''

 

Momy wlh inoson Khalil fiyeda yanda 'dan Adam zai iya lissafawa,

Zuciyata zafi takeyi sosai bazan iya kallonsa ya auri wata ba,

Gwara na mutu danaga wannan ranar.....

 

Da sauri momyn ta rufe Mata baki tana girgiza Mata Kai cikin tashin hankali tace"

 

Dan Allah Nuratu kidawo hayyacinki ki daina wainnan maganganun

Zan zamo Mana mafitarda zamu Kori Amatun daga rayuwarmu gaba daya da duk ahalin zabeera ma bama Khalil kadai ba.....

 

Dagowa nuratu tayi da idanuwanta dasukai jajir suna tsiyayo hawaye tana qoqarin fahimtar zancen momyn ta zabura da sauri tana tunowa da takardun data karbo hannun manager na kaf asalin Amatun harma da qarin rayuwar karuwanci datasa aka qara Mata akai,

 

Dakinta ta nufa kamar mahaukaciya ta nufi inda handbags dinta suke tahau wargazasu tana neman jakar da tasaka envelope cikin hauka,

Ganin yanda take wargaza Kaya yasa momyn saurin qarasowa tana sake riqota saigashi ta zaqulo jakar

Jikinta har rawa yakeyi ta bude ta dauko envelope din gaba cewa''

 

Momy yau Babu Abinda zai Hanani wulaqanta wulaqantacciyar rayuwarta,

Saina sakata kuka ninkin Wanda ta sakani tun zuwanta zabeera,

Ayau zata San asalin irin girman soyayyar Dana kewa Khalil.

 

Juyawa tayi ta fice tana share hawayenta dasuke sake bulbulowa cikin tsananin zafi da baqin cikin da zuciyarta ke ciki

 

Da gudu momy tabi bayanta tana Kiran sunanta sbd ayanda take yanzu ba acikin hayyacintaba komai lalacewa zaiyi Bata haka zasu tona asirin Amatun ba so takeyi harda umme ta fito cikin zancen....

 

A firgice ta biyo bayan Nuratun tana Kiran sunanta Amma tuni nuratun ta hada da gudu gudu tana sake sakin sabon kuka ta nufi sashen Andi inda tasan Modibbo nacan taredashi a daidai lokacin.

 

Ganin takasa cimma Nuratun data nufi hanyar sashen Andi yasa hankalinta mummunan tashi tuni ta firgice sbd wlh tasan Kwana zasuyi aciki Suma sbd zancen ba qaramin tashin hankali da masifu zai janyo ba,,,

Salman dake qoqarin parking yaga wucewar Nuratu da gudu gudu kamar  tana kuka Yana qoqarin kashe motar ya fito saiga momynsu cikin sauri itama tanabin bayan Nuratun hankalinta amatuqar tashe daga ganinsu yasan ba lafiya ba bare ganin sunkama hanyar sashen Andi koma meyene to ya girmama dan duk Abinda yasa aka wuce Modibbo aka nufi Andi to da matsala babba.

 

Kashe motar yayi da sauri ya fito yana qoqarin bin bayansu saiga Dr khalil ya fito daga sashen ummen tareda Amatu da ummen zasu mayarda Amatu

Da sauri Khalil ya taresa ganin Yana Shirin gudu yace"

 

Lafiya likitan qashi???

 

Kallon hanyar Sashen Andin yayi cikin sauri sauri yace"

 

Inaga akwai matsala ne Naga Nuratu da momy sun nufi sashen Andi kowannensu Babu nutsuwa atare dashi Nuratu ma kamar kuka takeyi...

 

Juyowa yayi ya kalli khalil din cikin fargaba yace"

 

Ina Jin tsoron Abinda zaisa suje gurin anty musamman Nuratu nasan halinta da tsananin fushi da rashin tunani Wanda kowa yasan yawancin fushinta akan Abinda ya shafeka ne

Akwai Abinda yafaru yanzu a tsakaninku ne????

 

 

Dukkaninsu su ukun da sauri suka kallesa cikin wasi wasi da shakku

 

Da sauri umme ta kalli me aikinta dake fitowa dan kawo Mata wayarta dake ringin cikin sauri tace"

 

Shafa'atu Maryam da Nuratu sun shigo sashena bayan shigowar su Khalil????

 

Da sauri cikin tashin hankali duk suka zubawa shafar Ido jiran amsarta

Tace"

Eh da Kuna ciki sun shigo Amma.......

 

Bata qarasaba Salman ya juya da mugun gudu Yana cewa'"

 

Innalillahi-wainna ilaihirrajiun.....

 

Da sauri Dr khalil ya juyo ya kalli umme da zufa ya katse Mata ya kalli Amatu da tuni qafafunta suka Fara daukar rawar tashin hankali ya riqo hannuwansu duka su biyun cikin qoqarin bawa kansa nutsuwa Dan kwantar musu da hankali yace"

 

Umme duk tsanani karku Fadi asalin abinda yafaru na gskiar Abinda yafaru tsakaninku Kika kawo Amatu zabeera,

Amatu komai zai faru karki bude baki kiyi magana nine zanyi Magana ok???

 

Kallonsa umme tayi da sauri tana cewa''

 

Ta yaya Zan tsaya Ina kallonka ka dauki hukuncin Abinda bakaine kayiba...

 

Umme please kuyi kawai Abinda nace ku koma ciki Bari nabi bayansu tun kafin su Isa.

 

Da sauri yabi bayan su Yana share zufan goshinsa akaro na farko dayaji yanawa wani fatar faduwa ya Suma sbd Jin yake inama Nuratu kafin takai tafadi ta suma a hanya..

 

Kasa hakuri ummi tayi takasa komawa ciki ta tsaya gurin tana zarya  cikin tsoro da fargabar Abinda zai biyo baya....

 

 

Bakin qofar shiga momy tayi nasarar damqe Nuratu da sauri tana sauke numfashin wahala da tashin hankali tace"

 

Nuratu kidawo hayyacinki kada kiyi Abinda masifarsa zata qare kanmu sbd wannan alamarin ba Abune me sauqi ba dazamu Bari Modibbo yaji daga garemu ba bare Andi

Maza kawo takardun Nan mukoma muyi Magana a nitse......

 

Qwacewa tayi tareda  tura qofar palon zata shiga har lokacin kuka takeyi sosai tace"

 

Momy yau idan ban tona asirintaba duniya tasan ko ita wacece ba hankalina bazai taba kwanciyaba

So nake ta dandani 'dacin rabuwa da Abinda kakeso....

 

Fixgota Salman yayi da qarfi Yana qoqarin kwace envelope din ta fizge da qarfi tana cewa''

 

Kaima bayanta zakabi aci gaba da barin karuwa tana rayuwa acikin zabeera?

Me take Baku da duk mazan zabeera kuka haukace akanta??

Abinda take bawa sauran mazan waje........

 

Wani wawan Mari salman ya sauke Mata Wanda yasata haukacewa cikin tsananin firgici da masifa tace"

 

Wlh ka sake dasamin tsanarta me tsanani Koda Zan rasa Raina saina tabbatarda Andi da Modibbo sunsan karuwace ita,

Barauniya ce,

Yar bola ce,

Me aikin karuwanci a gidan abinci.......

 

Ba zata Marin dayafi na farko zafi da qara ya sauka akan inda Salman ya mareta

Wannan karon radadin yayi tsananin data kasa riqewa saidata zube a qasa ta dago ta kallesa idanuwanta na qarasa rinewa hawaye masu tsananin zafi da baqin ciki suna gangaro Mata murya na rawa tace"

 

Khalil duk akan wannan karuwar ce??

 

Cikin tsananin bacin Ran dabasu taba ganinsa aciki ba ya bude baki zaiyi Magana akai gyaran murya daga bakin qofar Shiga palon kusan duk atare suka juya cikin firgici da tashin hankali sukaga Andi ne da kansa a tsaye Modibbo na gefensa kowannensu kallo daya zakayi Masa kasan dukkanin fushi da bacin ransu a bayyane yake

Cikin nutsuwa Modibbo ya qaraso gaban Nuratu da itama tashiga firgici ya sanya hannu ya zari envelope din hannunta batareda yace qala ba ya juya yadawo gefen Andi Yana bude envelope din Wanda yasa tuni kowannensu ya shiga rawar jiki musamman momyn tuni ta durqushe qasa tan neman sakin kuka

Andi yayi wa gefenta kallo daya take ta hadiye kukan batareda yafitoba yakoma tana rawar jiki.

 

 

 

Duk inda tashin hankali da sanyin jiki yake Yana tareda Amatu da umme sbd kowannensu yakasa samun nutsuwa ta ja qafafunta dasukai nauyi ta nufi hanyar sashensu idanuwanta na sake kadawa bayan kumburin dasukayi na kukan data gama sha,

 

Tana shiga palon da anty zarah dake zaune tana qoqarin kiranta tayi saurin miqewa ta qaraso gabanta cikin tashin hankali da tsoro take Kiran sunanta tana tambayarta lafiya.

 

Kasa motsi tayi bare Magana sai kawai ta fashe da sabon kuka me shiga Rai tana zubewa qasa...

 

Innalillahi-wainna ilaihirrajiun" anty zarah ke maimaitawa tana zubewa qasan itama cikin tashin hankalin ganin irin kukan da Amatun keyi cikin rudu muryarta na rawa tace"

 

Amatu meya sameki kifadamin tun kafin kisa zuciyata fashewa itama Dan Allah,

Kukanki na bani tsoro tareda sani cikin tsananin firgici Dan Allah kiyimin mgn.....

 

Dagowa tayi ta kalli anty zarah din jajayen idanuwanta na tsiyayo da hawaye masu zafi tanajin tausayin kanta Dana zarah din sbd tasan lokacin rabuwarsu ne yazo,

Abinda Bata saniba shine zarah din zata tsaneta idan taji Abindake faruwa?

Koda zata tafi zatayiwa anty zarah adalcin fada Mata gskia da bakinta ko Dan zallar qaunarta gareta.

 

Wasu hawayen ne suka Kuma tsayayo Mata ta rintse ido zuciyarta na radadin Abinda zata fada ahankali tace"

 

Anty zarah ki gafarceni na zamo  babbar butulu me mayarda alkhairi da cin Amana,

Na cutatar dake ta hanyar wahala akan Abinda Kika saka Rai da burika akansa,

Na hanaki bacci da sukuni gurin dawainiya Dani akan qarya yaudara...

Anty zarah banida ciki ajikina,

Bantaba daukar cikiba,

Bantaba sanin namijiba bare nayi Abinda zaisa nasamu ciki,

Dr khalil ba Mijina bane.........

 

 

Sakinta anty zarah din tayi cikin tsananin firgici da mamaki tayi baya tana zaman 'yan bori idanuwanta na silalo hawayen tsoro da karyewar zuciya ta Fara girgiza Kai tana son yin Magana takasa sai hawaye....

 

Anty zarah bantaba sanin a duniya akwai masu irin tsarkakakkiyar zuciya irin tasu kawu ba sai Dana hadu da Dr khalil dake da salman kuka kawo wani irin farin ciki da sanin mutuncin Kai arayuwata Amma Babu Abinda nakawo Muku sai yaudara da damuwa.....

 

Cikin rawar murya anty zarah dake rawar jiki gaba daya cikin firgici tace"

 

Idan duk Abinda Kika fada hakan ne to meya kawoki cikin rayuwarmu????

 

KUDI"""""tafada Kai tsaye tana sauke Kai hawayenta na qaruwa..

 

Son kudi da burin samunsu kota halin Yaya yasani shigowa rayuwarku

Saidai bayan haduwata daku na fahimci samun mutanen dake sonka da son farin cikinka tareda zama acikinsu shine asalin farin ciki da walwala Wanda kudi baya siya maka suba,

Anty zarah girmanki da qaunarki alqawarine da bazai taba gogewa azuciya da rayuwataba,

Anty zarah idan lokaci yayi Zan fada Miki gaskiyar duka Amma ayanzu iya Abinda Zan fada Miki kenan.

 

 

Miqewa tayi da sauri ganin irin hawayenda anty zarah din keyi tana bin cikinta da kallo burirrikanta akan cikin suna tarwatsewa daya Bayan daya,

Cikinda akai alqawarin Bata Abinda za'a Haifa Wanda tuni tafara kallon kanta amatsayin uwa Nanda lokacin qanqani.

 

Buga kofar da akayi da qarfine yasasu kallon kofar tun kafin su motsa aka sanarda saqone Andi nayiwa Amatu Kiran gaggawa.

 

Rintse idanuwanta tayi hawayen ciki suka gangaro ta juya ta nufi qofa.

 

 

 

 

A tsaitsaye suke Babu Wanda yasamu damar motsawa daga Inda yake sbd tashin hankali kusan mintuna suka share ahakan sbd shock dinda su Andi suka Shiga Bayan Gama sanin wacece Amatu dakuma irin qazamtacciyar rayuwar karuwancin datayi qarshe ta qare acikin zuria mafi tsafta da mutunci,

 

Umme da sauran manyan yaran Andi da Modibbo da tuni aka kirasu suka qaraso Babu wanda ya zauna duk tsaye suke cikin tashin hankali da jimanin abinda zai biyo Andi kawai ake jira yayi Magana.

 

 

Dagowa yayi cikin wani irin yanayi na  tsanani yayiwa Khalil kallon dayasa kowa sake Shiga firgici cikin amo me firgitarwa yace"

 

Kowace tambay amsa daya nakeso,

Ka auri wannan yarinyar??

 

Aa,

 

Acikin takardan Nan anrubuta cewa

Ita din Mara asali ce,

Yar bola ce,

Karuwa ce,

Barauniya ce,

Gidajen abinci,hotels da gidan rawa take aiki,

Babu police station dinda batayi zamaba har gidan yari

Gaskia ne ko qaryane???????

 

Cikin tsananin firgici da tashin hankali muryarsa na rawa yace"

 

Gskia ne Amma Banda.......

 

Hannu Andi din ya daga Masa fuskarsa na nuna dukkanin fushinsa da bacin ransa.

 

Take yace kowa ya watse ya sallamesu ya juya yayi ciki 'yayansa na binsa abaya.

 

Kasa motsi kowa yayi sbd sanin abin bazaiyi kyauba.

 

Daga ciki kuwa kallon alhaji qarami yayi Kai tsaye yace"

 

Yarinyar da mariqanta a daukesu a rufe a central station dinda Khalil zaifi shekaru goma Yana nemansu baigansu ba a sanarda commissioner laifin datayi ta yanda zasusan girman laifin Bata sunan zabeera.

##Mamuh#

[4/10, 7:28 AM] Zafafa: *_MQ 28_*

 

 

 

Cikin nutsuwa da girmamawa Modibbo ya kalli Andi a natse yace"

 

Kama yarinyar da mariqanta kamar su ba'a musu adalci ba sbd da yiyuwar qila bada masaniyarsu ta aikata hakanba kamar yanda shima Khalil Babu saninmu yaje ya kwaso Mana ita..

 

Tsit Sukayi kowa na kallon Andi da yanayinsa sbd maganar da Modibbon yayi ana jiran jin me andin zaice.

 

Zama batareda ya dagoba ya kallesu yace"

 

Alhaji qarami na damqa case din a hannunka a shigar da qara me qarfi akan yarinyar da mariqanta idan ka Gama binciko zancen gaskia ne ko aa akan laifin qage da shirin batawa zabeera suna ta hanyar qage akan cikin qarya,

Hakama asaka likitoci masu kyau suyi bincikenta aduba idan da akwai ciki a jikinta ko Babu,

Kada abari Khalil yasan inda aka Kai case din duk tsanani hakama MAHMOUD ZABEERA kada abari ko kadan yasan Abinda yake faruwa tunda baya Nan sbd acikin minti biyu zai iya saka agano wa Dan uwansa inda yarinyar take.

 

Cikin biyayya alhaji qaramin yace"

 

Angama Inshallah Andi.

 

Sahirtaccen numfashi Modibbo ya sauke zuciyarsa na daci da alamarin sbd baiso komai ya lalaceba.

 

Amatu na isowa sashen motar civil defense din na fakawa bakin qaton gate din ZABEERA

Alhaji qarami ne yafito daga palon ya kalli khalil yace"

 

Ka shiga ciki Andi na zaiyi magana da Kai.

 

Kasa motsawa yayi ya juya ya kalli Inda Amatu ke tsaye yanajin kunyar kansa daya Bari har suka tsintsi kansu a irin wannan Matsin dabai samo mafita ba tuna farko sukai aure tun kafin zuwan wannan ranar.

 

Kallonsa itama takeyi zuciyarta na sake karyewa da wannan masifar

Itadai komai tsananin hukunci da zafinsa zata dauka matuqar ba rabata za'ayi da Khalil din ba.

 

Sake maimata Masa alhaji qarami yayi Yana kallonsa cikin fushi Wanda yasashi dauke idanuwansa daga Kan Amatun yafara takawa ahankali ya nufi qofar palon yashige.

 

Yana shigewa alhaji qarami ya kalli Amatu dake tsayayo hawaye masu ciwo tanajin zuciyarta na sake karyewa ya nuna Mata hanya alamar suje.

 

Da sauri umme tayi gurinta tana qoqarin riqeta anty zarah data biyota tayi saurin rungumeta ta baya tana sake sabon kuka sbd su duka sun San matuqar aka tafi da Amatu ba lallai su  Kuma ganinta arayuwarsu ba.

 

Daga umme har anty zarah din da Amatu kuka sukeyi sosai musamman umme datasan idan Amatu ta tafi rayuwar Khalil dinta na cikin hadarin rasata.

 

Haj maryam ma a katse take har lokacin sbd Basu Gama sanin inda Rana zata Fadi ba gashi dai Nuratun ma kuka takeyi sosai sbd wannan fitinar tasan shikenan Khalil bazai taba sonta ba yanda take fata komai yagama lalace Mata.

 

Matane su biyu da uniform dinsu na civil defense manya manya dasu kowacce tanaji qarfi da rashin Imani sbd Babu kalar bahaushiya acikinsu bare ace musulmai suna qarasowa alhaji qarami ya nuna musu Amatu sukayi kanta suka kana hannuwanta biyu suka Fara janta umme da anty zarah suka bisu abaya suna roqonsu cikin tsananin kuka Amma tuni suka wuce da ita,

Salman kuwa cikin palon yayi da sauri ko sallama baiyiba ya tsaya gabansu Andi ya kalli khalil dake sunkuye da Kai yace"

 

Dan Allah Andi a sassauta Amatu a tsaya a fahimci zancen ta hanyar nutsuwa mace ce ita wlh rayuwarta zasu lalata idan aka Bari suka tafi da ita aka kulleta Dan Allah....

 

Da sauri Khalil ya juyo ya kalli Salman din cikin tsananin firgici bai tsaya gama sauraren Abinda yake fadaba ya turesa ya fice da gudu ko gabansa baya gani.....

 

Ba Andi kadaiba hatta Modibbo Saida ya kidima da wannan alamarin,

Yaransu da Basu taba dago Kai sun kallesuba idan suna musu Magana,

Yaransu da Babu Abinda suka sani arayuwa bayan yimusu biyayya da bin umarninsu Koda baiyi musu daidaiba Amma ayau akan mace kamar abinda sukai shekaru suna Dora 'yayansu akai na neman rushewa,

Yau Andi da kansa Yana zaune ake tafiya abarsa yana magana hakama shima wannan yau shi Andi da kansa yake kalla Yana cewa ba'ayi Abinda yakamata ba....da matsala,da matsala babba ma kuwa.

 

 

Juyawa Salman yayi yabi bayan Khalil Yana fasa maganar da yayi niya cikin 'dacin Rai idanuwansa na sake sauyawa.

 

Koda suka Isa bakin qofar zabeera tuni aka wuce da Amatun motar alhaji qarami nabin bayansu.

 

Cikin tsananin tashin hankali Khalil ke qoqarin bin motar da gudu da qafafunsa Salman yayi saurin riqesa Amma ya fizge yabi motar da gudu Salman da umme na kiransa cikin tashin hankali umme ke cewa''

 

Salman dauko mota da sauri kabisa idan yayi gudu ciwonsa zai tashi Dan Allah kabisa kada kabari komai yasamu Khalil shikadai nakedashi.

 

Ciki yakoma cikin sauri jikinsa har rawa yakeyi yafada mota yajawo da gudu yabi Bayan Khalil din.

 

Koda ya cimmasa harya Fara galabaita numfashinsa yafara sarqewa.

Da sauri ya tsayar da motar ya fito yakamasa yasaka motar ya zagayo ya shiga Yana qara Masa sanyin AC din motar Yana janyo tissue da yawa ya miqa Masa yana qoqarin daidaita muryarsa yace"

 

Dr kada kayi Abinda zai kaika kwance  sbd kana buqatar tsayuwa da qafafunka gurin fitarda Amatu cikin wannan matsalar.

 

Kasa Magana Dr khalil din yayi Yana fitarda numfashi cikin yanayi na azaba ya lumshe idanuwansa dasukayi jajir ahankali yace"

 

Muje gidansu kawu Ina buqatan daukesu daga gidan yanzu.

 

Hanyar gidan suka kama Yana tuqi Yana kallon Khalil din daketa fama da numfashinsa Dan daidaitawa kada yabari yaci qarfinsa.

 

Koda suka Isa Salman ne ya bude Masa motar yafito Yana sake qoqarin daidaita numfashinsa ya share zufansa suka nufi cikin gidan.

 

Zaune kawu yake Yana sauraron radio iyami na zaune gefensa tana shafawa qafarta daya Jan lalle sai gasu sunshigo da qaramar sallama suka qaraso iyami na ganinsu ta ajiye lallen datake qoqarin sawa dayar qafar tana musu maraba da zuwa duk da dai yanayinsu yasata fargaba musamman sbd zufan da kowannensu yaketa sharewa bama kamar Dr daketa fama da numfashinsa Yana dannewa sbd kada agane halinda yake ciki.

 

Kallo daya kawu yayi musu yasan ba lafiya ba

Ya tashi zaune daga kishingiden dayake ya janyo radionsa kusa ya qure murya sbd kada aji zancen dazasuyi ya kalli khalil daya zauna gefensa yace"

 

Likita lafiya naganku kamar 'yan saqon mutuwa???

Salmanu lafiya kuwa??

 

Numfashi Dr ya sauke Yana lumshe ido sbd azabar dayake ji ya kalli kawun cikin taushin murya yace"

 

Kawu zanyi maka bayanin abindake faruwa Amma Dan Allah yanzu inason ku biyoni muje wani guri muyi maganar.

 

Kallon juna kawu da iyami sukayi suka sake maido da kallonsu kansa cikin rawar murya iyami tace"

 

Akwai Abinda yasamu Amatu ne?

Meya faru ne kafara fada Mana mu musulmaine zamu dauki qaddara koma menene.

 

Ajiyar zuciya salman ya sauke cikin sake bawa kansa nutsuwa yace"

 

Ba Abinda kike tunani bane iyami Amma dai yanzu muna buqatar barin Nan ne tukuna.

 

Kallon Dr khalil kawu yayi da kyau kafin ya miqe Yana cewa'

 

Iyami sanyo hijabinki muje na yarda da Khalil fiyeda kowa arayuwata Dan haka koma menene Yana mahimmanci barin Nan din tun sun fada.

 

Jiki mace iyami ta miqe ta wanke qafa dayar dakeda lalle ta fada daki ta sanyo hijabi hannuwanta na rawa sbd  hakanan takejin tashin hankali tun kafin suji koma menene yake faruwa.

 

Babu Wanda suka fadawa suka rufe dakunansu suka fice.

 

A mota Dr khalil yakira babban yaronsa na asibiti Ibrahim ya sanar dashi Yana buqatar gidansa daya Gama be tare ba na kwana biyu,

Cikin sauri yace angama likita.

 

 

Anguwar can take nesa kusan hanyar wajen gari duk da akwai mutane da yawa a anguwar Amma kasancewar dukkaninsu sun Saba da anguwannin cikin gari sai sukaji anguwar wani iri.

 

Gidane qarami me daki biyu sai bayi da kicin a qaramin tsakar gidan sai daki 'daya a hanyar shigowa.

 

Zaune suke akan qatuwar tabarmar da Ibrahim din yakawo suka shimfida kowannensu shiru sunkasa qwaqqwaran motsi alokacinda Dr khalil yagama yimusu bayanin dukkanin Abinda yafaru.

 

Wasu irin hawayen baqin ciki iyami keyi tana sauke kanta sbd tsananin kunyarsu Khalil din ahankali Tace"

 

Bantaba tunanin son kudi da rashin hankalin Amatu yakai har haka ba,

Yanzu wace irin masiface wannan ta dauko wadda bamusan ta Yaya zamu fuskancetaba.

 

Shiru kawu yayi sbd nisa da yayi a tunani Yana Dora dukkanin laifin akansa sbd shine yafara daukar rayuwa da rashin mahimmanci har su Amatun suka dauka shiyasa tayi irin wannan alamarin me girman gaske Wanda ba mutuncin Zabeera ba kawai shi kansa idan zancen ya fita da wane Ido zai kalla mutane duk rashin kunyarsa kuwa.

 

Ganin yakasa magan yasa Salman yashiga basa Magana Dan rage Masa nauyin zuciya Amma sam ko kadan yau bayajin komai bayan qunci.

 

Da zasu tafi Dole yace sutafi dashi gurin neman ofishin da aka Kai Amatun.

 

Yawon ofishin Yan sanda da civil defense suka Fara tun abin na aikin hkr har suka sake Shiga tashin hankali sbd duk inda sukaje ba anan aka kawota ba tuni suka fahimci Alamarin Babu sauqi acikinsa Babu Wanda baishiga cikin mummunan tashin hankali acikinsuba musamman kawu dayake ganin kamar kasheta za'ayi.

 

Wasa Wasa har dare Babu labarin komai daganan suka nufi wata local government din dake kusa canma baa kaitaba.

 

Dawowa sukayi suka ajiye kawun anan gidan Ibrahim gurin iyami suka nufi zabeera cikin sabon tashin hankali.

 

Koda suka Isa Kai tsaye gurin Andi suka nufa inda suka tararda Modibbo acan anan suka zube qasa Khalil din na roqo da ban hakuri abisaga laifin Amma Sam Babu wani sauqi sbd atake Andi yabata umarnin ya rufe maganar case din daga ranar kada Wanda Yakuma tayarda zancen.

 

Kasa komawa ciki Khalil yayi yafice daga zabeera din yaje ya siyo abinci da kayan buqata ya nufi gurinsu kawu.

 

Zaune suke tsakar gidan zaune sunyi shiru Babu me Magana acikinsu kowanne da tunanin dayakeyi yashigo da sallama suka dago suka kallesa cikin sanyi da mutuwar jiki.

 

Qarasowa yayi ya zaune gefen kawu tareda ajiye musu abincin Yana qaqalo qwarin gwiwa yadan Basu Magana kafin ya miqe ya fita yadawo motarsa ya zauna tareda rintse ido sai kawai hawaye suka gangaro Masa Yana dafe kansa yace"

 

Allahumma ajirni fi musibati..

 

Zaune ya kwana cikin mota a qofar gidan kamar yanda Suma ciki su kawu Basu rintsiba iyami kwana tayi sallah.

 

 

Gari na wayewa ciki yashigo anan yayi sallah dakin farko yafito yaje yasiyo musu abinci yakawo haka suka takurasa shima yadan ci kadan yafice zuwa zabeera.

 

Duk yanda yaso ganin Andi ma abin ya gagara sbd hanyar sashensa anrufe  ga Modibbo ma yaqi ganinsa sai alamarin yaqara daukar zafi Yana fitowa daga zabeera Salman yakirasa yake sanar dashi anshigarda qarar maganar sbd gashinan 'yan jaridu harsun buga zancen ya Basu koina alamarin yayi Muni sbd dukkanin inda amatu tayi aiki anbinciko kowa yabada shefar qwararriyar barauniya ce Dan haka yanaga suyi qoqarin sanin inda take ayi belinta kafin case din yashiga Court akwai matsala sbd itada umme ne zasu kwana ciki musamman idan sunan MD ZABEERA yafito amaganar Andi da Modibbo bazasu dauka da saukiba.

 

 

Cikin tsananin tashin hankalin dayafi na farko Dr khalil yasake bazama yawon neman inda aka rufeta ga bangare daya su kawu sun matsa Saida ya maidasu gida saidai tunda suka dawo ake nunasu da Abinda Amatun tayi inda aketa cewa Ashe shiyasa khalil zabeera ya tsaya musu yaketa kashe musu kudi tarewa tayi a gidansu Yana muamala da ita.

 

Duk masifa da fadan kawu yakoma ko  zaman waje ya dainayi sbd maganganun hadda qari da cin zarafi sawa akeyi wainda suke cikin gida dayane kawai suke ganin mutuncinsu har lokacin suna Kuma tayasu baqin cikin wannan alamarin.

 

 

Kwanaki kusan shida kenan Yana bulayi yakasa samunta,

Duk iya inda alamarin yake ya girmama,

Ko abinci baya iyaci sai ruwa idan ummensa ta takura Masa yasha,

Ya rame cikin kwanki shidan yakoma kamar bashiba,

Ya daina zuwa asibiti gabaki daya sai sakin kudi yakeyi koina ana bincika Masa kowace station da office din civil defense Amma Babu haske.

 

Zaune yake gaban kujerar dake kallon insfector Garba acikin office dinsa Yana kallonsa da idanuwansa dasuka shige sbd damuwa ahankali yace"

 

Zanbaka dubu dari biyar kamar yanda ka buqata cikin awa biyar zaka bincikamin dukkanin ofishinku na cikin gari da qauyuka.

 

Murmushi insfector Garba yayi tareda kallon Dr khalil din yace"

 

Mutum me mutunci da girma dai kamar wace irin qaddarace zata kaika batarda kudade masu yawa irin haka akan Amatu da kowa yasan dabadan kudinkaba wlh ko kallo bazaka ishetaba sbd Ina fada maka yarinyar terror ce tasan siririn iya sata......

 

Miqewa yayi Yana katsesa da cewa''

 

Mungama Magana Ina jiranka Nanda awa biyar din.

 

Ficewa yayi ransa abace yabar station din Yana sakejin kamar zuciyarsa zata fashe babu me bude baki yafadi alkhairi akan Amatu duk station 'dinda yaje.

##Mamuh#

[4/10, 7:28 AM] Zafafa: *_MQ 29_*

 

 

 

Zaune yake gefen kawu Yana Shan furarda iyami ta matsa Masa yasha Kiran Insfector Garba yashigo wayarsa cikin sauri ya daga Yana aje ludayin hannunsa

Su kawuma duk shi suka tsurawa ido suna jiran jin Abinda za'a fada Masa.

 

Ahankali ya lumshe ido tareda sakin boyayyan numfashi jin Abinda garban yafada Masa ya katse wayar tareda kallon kawu dayayi zuru zuru cikin farin cikinsa daya kasa boyuwa yace"

 

Tana central ta hanyar zaggen.

 

Ajiyar zuciya kawu yasaki tareda Dan rufe Ido batareda yace komaiba hakama iyami numfashi ta sauke sbd harta yanke hukuncin yau dai zata fadawa usi yasan halinda ake ciki.

 

Miqewa Dr khalil yayi Yana zura takalminsa yana cewa''

 

Kawu muje inshallah yau Amatu agida zata kwana.

 

Zabura kawun yayi dama jira yake ace yatashi din.

 

A mota Dr khalil kasa nutsuwa yayi wani irin yanayi yakeji na tsananin kewar Amatun

Inama ace Amatu mallakinsa ce da tabbas ayau rungumeta zaiyi ajikinsa saiyaji dukkanin kewarta ta sakesa,Amma ko yanzu wannan alamarin daya faru bai barsa da zabin komaiba face na aurenta cikin qanqanin lokaci sbd samun Bata kariya daga kowanne irin barazana.

 

Doguwar tafiya sukayi Mai Dan tsayi takaisu central din inda daqyar aka barsu suka Shiga sbd tsaro.

 

Yana yin parking suka fito kawu na qarewa gurin kallo cikin tsananin tashin hankali ace anan Amatu take zaune akan qanqanin laifi irin wannan Wanda ko zagi da bannar suna da gorin da mutane suke musu aka barsu dashi sun hukuntu,

Amma ace ankawota irin gurin Nan dasai masu laifin babbar kisar gilla ake kawowa sbd kawai tayi Abinda ba laifinta bane,

Wani irin kunci da bacin Raine ya cika zuciyarsa yanajin ba'a taba yimusu rashin adalci ba tun takaicinsu irin wannan,

Yarinya qarama mace budurwa za'a kawo irin gurin Nan?¿

Yanda yakejin tsananin bacin Rai wallahi daba mahaifiyar Khalil ce tasata a wannan halinba wlh dasai yayi shari'a da duk Wanda yake cikin zuriar zabeera sbd arziki ba hauka bane hakama talaka ba dabba bane.

 

Shi kansa Dr khalil Jin yayi dukkanin gwiwoyinsa na sanyi zuciyarsa na cika da baqin ciki da bacin ran ganin anan Amatu take,anan aka kawota cikin masu manyan laifuka sbd kawai tayi qaramin laifinsa baifi ayisa agama cikin gidaba...

 

Babu Wanda ya iya yiwa wani Magana acikinsu sbd halin tsananin baqin cikin dasuka Shiga na ganin irin cin zarafi da wulaqantawarda akayiwa Amatu.

 

 

Koda suka Isa bakin office din commissioner Saida aka Shiga aka isarda zuwansu shima sbd Khalil din 'dan Zabeera ne da Babu wanda zai Bari ko hanyar office din su Isa.

 

Daga cikin office din commissioner kuwa Bayan anzo ansanar Masa da zuwansu waya ya dauka ya dannawa alhaji qarami Kira Wanda akaci sa'a a lokacin Yana gurin Andi.

 

Shiru alhaji qarami yayi bayan yagama sauraran Abinda commissioner ke fada Masa cikin mamaki yace"

 

Ya akayi yayi saurin ganowa Bayan kabada tabbacin aqalla har maganar taje court bazai gano inda takeba.??

Yanzu dai Bari na sanarda Andi saina kiraka kafin ka gansu.

 

Aje wayar yayi ya kalli Modibbo kafin ya kalli Andi cikin nutsuwa da girmamawa yace"

 

Andi khalilu ne yasamu gano inda take Yana bakin office din commissioner ma yanzu haka.

 

Dagowa yayi ya kalli alhaji qarami din da mamaki a fuskarsa kafin ya kalli Modibbo cikin bayyanarda mamakinsa yace"

 

Me Khalilu yakeson komawa ne akan mace????

 

Shiru Modibbo yayi Yana sauke Kai cikin takaici da mamakin Khalil din.

 

Sake bayyanarda mamaki da takaici Andi yayi Yana cewa''

 

Tabbas khalilu Yana buqatar hukuncindazai dawo dashi hankalinsa tunda yazabi wulaqanta hukuncina akan mace..

 

Dan gyara zama Modibbo yayi tareda gyaran murya cikin girmamawa yace"

 

Allah ya huci ranka Andi Amma sai Inaga tunda yariga yayi nisa duk wani hukunci sake tsaurara abin zaiyi tunda Babu wani a zabeera daya taba take hukuncin Manya sai akansa gashi yanzu kowa yafara ankarewa da hakan da azo ayi Abinda zaisa agano bijiewa yayi yayi watsi da hukuncinka asamu masu Goya Masa baya abun yayi yawa.

 

Shiru Andi yayi Yana sauraronsa cikin qoqarin son fahimtar zancensa

Ya dago ya kalli alhaji qarami dakeson Magana shima yace"

 

Kaikuma meye naka hasashen?

 

Gyara zama yayi Yana tausasa murya yace"

 Inaga akashe maganar a idon duniya ma'ana a janye qarar amatsayin munduba maraicinta mun qyaleta idan yaso sai commissioner su saka kudin belin da Khalil din bazai iya biyaba idan yayi yayi Dole zai hkr kokuma ace za'a biya kudin belin Amma saiyayi alqawarin rabuwa da yarinyar

Hakan shine mafita a yanayin da ake yanzu sbd Khalil idan baa janye qararba zai iya dagewa qarshe ya aikata Abinda zai saka zabeera kunya.

 

 

Jinjina Kai Andi yayi Yana na'am da bayanin alhaji qaramin yace"

 

A aikata hakan Amma kafin Nan ayau nakeson Modibbo dukkanin Abinda Khalil ya mallaka na zabeera a karbe.

 

Kallonsa Modibbo yayi da sauri saikuma ya sauke Kai Yana jinjina hukuncin sbd kaf  'yayansa bama shikadaiba kusan duk yayan zabeera da arzikin Zabeera suke tinqaho MAHMOUD ZABEERA ne kawai Babu qwandalar zabeera acikin dukiyarsa da guminsa da wahalarsa yatara arzikinsa,

Idan akace akwace komai na Khalil to motarsa ta hawa da kudaden account dinsane kawai zai tsira dasu Dan kuwa ko asibitinsa dayake tinqaho da ita MAHMOUD ne ya Gina Masa ita amatsayin tayasa murnar zama cikakken likita.

 

 

Koda commissioner yabasu izinin shiga bai nuna musu komaiba suka gaisa kafin Khalil yafara Masa bayanin Abinda yakawosu Babu dogo musu yacewa Khalil din an janye qara  belinta kawai zasuyi akan kudi naira miliyan daya sai kudin tarar bacin suna miliyan daya da rabi duba da yanayin gidan da akayiwa bacin sunan.

 

 

What?????"""Khalil yafada cikin tsananin mamaki da yiwa commissioner din kallon rashin hankali yace"

 

Beli ne wannan kokuwa hukuncin Rai da Raine wannan???

 

Murmushi commissioner yayi Yana gyara zama yace"

 

Dr khalil zabeera zaka iya Kiran lawyer dinka zamu basa komai a rubuce sbd samun qarin fahimta.

 

Kallon bakinsa kawu keyi cikin yanayin tsoron dayafi mamakinsa miliyan biyu kudin beli?gwarama su fito su fada musu bada itane bazasuyiba.

 

Koda lawyer din Dr khalil ya iso aka miqa Masa takardun belin da aka bugo cikin qanqanin lokaci ya karanta yasake karantawa zuciyarsa na tafasa ko ba'a fada yasan shirine akayi Dan quntata Masa shida su Amatun,

Koma menene akayi Dan a cimma bazai taba rabuwa da Amatu ba,

Idan anyi ne Dan aga gazawarsa tabbas bazai taba gazawaba zaiyi komai iya iyawarsa zaikuma qwatar Mata mutuncinta da yancinta.

 

Dagowa yayi ya kalli kawu da idanuwansa sukai jajir sbd tashin hankali saiyaji zuciyarsa ta sake karyewa ya waiwayo ya kalli commissioner cikin yanayin na nuna rashin gazawa yace"

 

Ahada takardun belin su zama ready zuwa gobe zankawo kudin.

 

Kallonsa sukayi da sauri duk su duka commissioner na boye mamakinsa akan Khalil din yace"

 

Shikenan Dr khalil zabeera muna jiranka goben.

 

Miqewa yayi ya fice kawu da Barr Bashir na bayansa kowannensu cikin damuwa Yana Isa bakin mota ya tsaya ya juyo ya kalli Barr Bashir da idanuwansa dasukai jajir yabude busashen bakinsa yace"

 

Barr zankiraka gobe muhadu anan abasu kudin inshallah.

 

Kallonsa Barr yayi cikin kulawa da jimami Yana cewa''

 

Dr khalil kana ganin zamu karbi belin Nan ahaka?

Inaga muje can zabeera aroqi maganar tarar ajanye Mana ita zaifi....

 

Girgiza Kai yayi Yana qoqarin boye rauninsa yace"

 

Ba buqatar hakan zanhada kudin zuwa goben Inshallah.

 

Shikenan tunda zaka iya biya ba damuwa Allah yakaimu goben.

 

Suna Shiga mota yayi shiru cikin tsananin damuwa da tashin hankalin ta inda zai Fara hada kudin sbd dukkanin kudin account dinsa ya rabesu gurin case dinnan cikin kwanaki kadan

Duka duka abindake account dinsa baifi dubu dari bakwaiba Kuma gidan haya yayi niyar kamawa dasu ya ajiye Amatun.

 

Bayan kudin account dinsa da motarsa baida wata babbar kadara sai tsadaddun agogunansa da wayoyinsa,

Asibitin dayake tinqaho da ita bata cikin lissafi sbd tamkar alamar qaunarssuce me qarfi dake tsakaninsa da 'dan uwansa.

 

Kallonsa kawu yayi cikin tsananin damuwa da sarewa yace"

 

Khalilu kada ka takura kanka da hada wainnan kudaden daba haduwa zasuyiba,

Qaddarace wannan me girma ta samemu wadda Allah zai fitar damu inshallah.,

Zamuje muyita addua Allah yabamu ikon cinye jarabawa sbd koba komai munqara bambamce halaye irin na wasu masu arzikin Wanda bayan suna Babu Abinda suka damu dashi,

Farin cikin yayansu da walwalarsu bai damesuba kamar yanda sunansu da girman kansu ya damesu.

 

Ahankali yaja motar suka bar gurin suka kamo hanyar gida har lokacin bai iya cewa ko qala ba sbd nisa da yayi a tunani.

 

Koda suka Isa ajiye kawu yayi ya wuce zuwa zabeera.

 

Parking yayi daidai sashen Modibbo yafito ya nufi ciki jikinsa da zuciyarsa amatuqar sanyaye.

 

Sallama yayi palon yashiga cikin sa'a Modibbon na zaune shikadai Yana kallon labarai Koda yaga khalil din Saida yaji tausayinsa Amma bai nunaba sbd ya dauke Kai Yana cigaba da kallon labaransa.

 

Gabansa ya zube tareda sunkuyar dakai wasu irin hawaye masu zafi suka gangaro daga cikin idanuwansa akaro na farko daya nuna gazawa cikin wani irin sauti Mai tsananin sanyi yace"

 

Modibbo Ina roqon yafiyarku akan dukkanin Abinda yafaru Dan Allah ku   sassautawa Amatu wlh batada laifi akan hakan kuskure ne da rashin sanin ciwon Kai wlh batayi Dan wata manufar Bata suna ko wani Abu ba dabam tayine kawai sbd kudi Wanda tsananin rayuwa yakaita ga hakan.,

 

Modibbo Dan Allah Ina roqon gafara da yafiyarku Dan Allah ku duba maraicinta kada ku tsaurara Mata.

 

Juyowa Modibbo yayi ya kallesa sosai ganin yanda babban namiji jajirtacce kamarsa ke kuka ya sauke ajiyar zuciya Yana cewa"

 

Khalilu zancenka ba'a hannuna yakeba Amma amtsayina na mahaifinka zanfada maka Abu daya,

Kada kayi Abinda zai kawo maka matsalarda bazaka iya tsayawa kaga wucewartaba,

Idan kanason yarinyar Nan tsakani da Allah Dan tallafawa maraicinta to tabbas na amince maka ka aureta sbd aurenta ne kawai zaisa Andi ya iya sassautowa tunda tariga tazama Zabeera Amma idan kasan tsakani da Allah yarinyar Nan batada nasaba to Ina baka shawara kayi gaggawar cireta daga rayuwarka shine kawai sauqi da mafita agareka..

 

 

Da jajayen idanuwansa ya dago ya kalli Modibbon Yana nazartar zancensa wani irin sanyin sassauci na shiga zuciyarsa sbd ya fahimci zancen mahaifin nasa take sabon qwarin gwiwa yasake shigarsa ya sunkuyar dakai cikin sanyi yace"

 

Nagode Modibbo Allah yaqara tsawon Rai.

 

Yana fitowa sashen ummensa ya nufa inda ya tararda ita zaune tayi tagumi kamar koyaushe cikin kwanakin tana ganinsa tayi saurin miqewa ya hanata ta hanyar mayarda ita zaune yana girgiza Mata Kai murya a mace yace"

 

Umme zanbar zabeera......

 

A firgice ta kallesa idonta na cikowa da hawaye zata fashe da kuka yace"

 

No umme karki manta kinmin alqawarin bazakiyi kukaba Kuma kinyi alqawarin bani support adukkanin Abinda Zan yanke.,

Umme albarkanki nake nema a rayuwar dazanyi wajen zabeera dan Allah umme kimin alqawarin bazaki saka kanki cikin damuwar dazata cutatar dakeba.

 

Kasa riqe kukanta tayi ta fashe dashi tana cewa''

 

Khalil Dan Allah kada kabar zabeera kabarni katafi Dani Nima

Wlh bazan iya zama baka nanba,

Katafi Dani duk inda zakaje zanzauna acikinku,

Zan zauna taredaku zanyi renon 'yayan dazaku haifa........

 

Kasa hkr yayi ya rungumeta Yana girgiza Mata Kai Yana cewa''

 

Umme Zaki zauna anan gidan aurenki  sai mutuwace kawai zata fiddaki zabeera.

 

Aa khalil zanbika Dan Allah kada ka tafi kabarni.

 

Ganin yanda ta daga hankalinta yasashi zamewa da sauri ya fice Yana danne zuciyarsa dake neman fashewa yayi hanyar sashensa.

 

Kayansa ya diba a akwati tareda kwashe agogunansa da takalmansa masu tsada sosai da duk abubuwan dazai buqata ya saka cikin mota tareda dukkanin takardunsa yafito yaja motarsa yabar zabeera.

 

Daga zabeera gidan Ibrahim yaje yafara ajiye kayansa acikin dakin farkon Shiga ya rufe dakin da mukulli ya fito yarufe gidan ya wuce.

 

Tareda Ibrahim din sukaje gurin masu Saida agogo akayiwa agogunansa kudi kaf aka shiye suka hada kusan dubu dari uku daganan gurin Wanda zai siye motarsa suka nufa aka Fara cinikin saidai abin son Rai yayiwa mutane yawa Dan siyan wulaqanci sukaiwa motar har kusan mutum shida sukaiwa motar siyan wulaqanci qarshe Dole ya saidata miliyan daya da dubu dari suka karba ya hada hadda kudin account dinsa suka tashi 2.6.

 

Mashin yahau Abinda baitaba hawaba a rayuwarsa ya nufi gidansu kawu anan yafadawa kawu ya hada kudin daga iyami har kawu basusan lokacinda suka fashe da kuka ba.

 

Murmushi me ciwo kawai yasaki batareda yace komaiba anan yayi sallar ishai iyami tasashin tuwon Dole kafin yatashi yatafi.

 

Mashin yasake hawa yakoma gidan Ibrahim Yana Shiga Allah ya taimakesa ana kawo nepa Nan ya tube yayi wanka da ruwan rijiyar gidan da Ibrahim yacika Masa durum da kansa masu shegen tsananin sanyi Wanda Saida suka saka numfashinsa kusan daukewa daya watsasu.

 

Boxer da singlet kawai yasaka yadawo ya kwanta Kan sabuwar katifar da Ibrahim din yasiyo yau yakawo Masa.

 

Kiran salman ne keta shigowa wayarsa Yana qin dagawa sbd duk kwanakin ya tashe duk banyarda salaman zaishigo cikin Al'amarin sbd bazaiso laifin ko wani Abu yasamesaba kodan yanda Amatu ta daukesa kamar usinta.

 

Kiran MD ZABEERA ne yashigo wayar ya qurawa wayar Ido tsawon sakanni kafin ya dauka Yana boye damuwarsa Nan suka hau Maganar shi cikin sanyi MAHMOUD Kuma cikin nutsuwa da miskilanci.

 

Koda asuba tayi daqyar ya iya dafawa ya tashi zaune sbd tsananin sanyin daya Gama shigewa ya Kama dukkanin qasusuwansa.

 

Daqyar yayi sallah ya jingina da bango Yana makure jikinsa guri daya sbd kaf gidan gaba daya koina sanyi yake fitarwa sbd gaf suke kusada ruwa.

 

Daqyar yaga qarfe Tara na safe tayi ya miqe yasake zuwa bayi ya watso ruwan sanyin yafito jikinsa na Dan rawa yashigo daki ya shirya cikin qananan kaya masu Dan kauri ya bar gidan sbd Jin kamar zai iya suma da ciwonsa dake gaf da tashi.

 

A gidansu kawu yaci biredi da kunun tsamiya tareda waina da iyami tasiyo Masa me kyau ta shinkafa.

Kobai fadaba sungama gano halinda yake ciki sbd kada su qara Masa damuwa sukaqi yimasa maganar sai tattalinsa dasukeyi.

 

 

Qarfe goma da rabi a central tayi musu shida kawu suka zauna zaman jira har qarfe goma sha biyu commissioner bai buqaci ganinsuba sai daya da rabi Bayan anyi sallah anfito tukuna aka kirasu suka Shiga.

 

Barr Bashir ne yacire kudin beli da Tara ya bayar akayi rubuce rubucen daza'ayi aka gama kafin akace afiddo Amatun.

 

Lokacinda aka kawota suna ganinta kowannensu idanuwansa suka ciko da hawayen baqin cikin ganin halinda take ciki Amma ita ganinsu yasata qaqalo qarfin hali tana danne azabar cizon sauri da galabaituwar yunwa da dau'dar datake ciki Danma tunda tazo koda Wasa ba'a taba dukantaba Wanda umarnin Andi ne kada a daketa ko so daya.

 

Babu Wanda ya iya mgn acikinsu aka Bata gyalanta da takalmanta suka fito tana tafiya daqyar a galabaice.

 

Suna fitowa titi taga suna qoqarin taron adaidaita ta kalli Dr khalil din da mamaki Kan fuskarta saidai batayi maganaba suka tare adaidaita biyu ita dashi suka shiga daya kawu yashiga daya.

 

Ahankali ya juyo ya kalleta cikin tsananin kulawa da damuwa akan fuskarsa yace"

 

Are you ok?

 

Kallonsa takeyi tana mamakin sauyawar dayayi

Yayi duhu tayi Rama hakama kamar Wanda baida lafiya sai Nishi Nishi yakeyi kamar Wanda yayi aikin wahala.

 

Kai ta daga Masa ahankali tana lumshe ido a wahalce.

 

Koda suka iso gida tuni mutanen gidan suka rude da murna da yiwa Allah godiya take aka hada ruwan wanka masu zafi aka Kai Mata

Maman junior hadda tayata wanka kamar me haihuwa haka aka gasata tasamu 'dan qarfin jiki aka Bata abinci taci tareda magungunan da Dr Khalil din yasiyo Mata ta kwanta take baccin wahala ya dauketa.

 

 

Da daddare kafin ya wuce Bayan yaci tuwon iyami cikin nutsuwa ya zayyanewa kawu duk halinda yake ciki yanxu tareda gabatarda buqatarsa na auren Amatun

Kawu ya sauke numfashi me sanyi yace"

 

Khalilu ko bakayi mgn ba nayi niyyar aura maka Amatu kobabu danginka ko daya sbd aduniya Babu Wanda ya cancanta yazama Dole yazama mijin Amatu idan bakaiba Dan haka wlh khalilu nabaka Amatu amatsayin Mata ka shirya nida kaina zanje masallacin juma'a nayi sanarwa ranar juma'ar Nan Inshallah za'a daura muku aure.

##Mamuh#

[4/10, 7:28 AM] Zafafa: *_MQ 30_*

 

 

 

 

Wani irin sanyin farin cikine ya Shiga zuciyarsa Wanda ya manta rabonsa dashi ya kalli kawun cikin girmamawa yace"

 

Nagode sosai kawu

Allah yaqara girma da Nisan kwana.

 

Amin Amin" yace Yana cigaba da yimasa nasiha akan hakuri da rayuwa komai lokacine dashi wata Rana komai zai wuce.

 

Bai jira sake ganin Amatunba yanayin sallar ishai a masallaci taredasu kawu yayi Masa Saida safe ya wuce.

 

 

Ahanya ya tsaya ya siya cardigan me kauri da sabon bargo me laushi kafin ya wuce gida.

 

Sbd sanyi hatta qafaguwansa da hannuwansa Saida ya sakawa socks bayan yasaka rigar sanyin ya dunqule cikin bargo Amma har lokacin yanajin sanyi na shigarsa hakanan ya daure har wahalallen barci ya daukesa.

 

 

Washe gari da safe ba laifi da kuzarinta ta tashi saidai kawai sauyi sosai data gani daga iyami har kawu Wanda ya tabbatar Mata da fushi sukeyi sosai da ita sai taji hankalinta ya tashi duk yanda taso Basu hakuri ko fuska taqi samu Saida Dr khalil yashigo ne taga sakewar fuskarsu ta kallesa da Ido ta nuna Masa fushi sukeyi da ita yasakar Mata kyakkyawan murmushi Yana nuna Mata Babu ruwansa

Suna Nan zaune saiga salman zabeera yazo Yana ganin Amatu cikin tsananin farin ciki yaqaraso Nan aka hau sabuwar fira inda anan ne takejin dukkanin Abinda yafaru hadda komai da Khalil din ya rasa bayan aikinsa da asibitinsa baida komai yanxu.

 

Jitayi sabuwar soyayyarsa tasake shigarta hartanajin ko bayada komai zata auresa ta zauna dashi Kuma alqawarine ta dauka saita shiryasa da familynsa ta maidasa cikinsu.

 

 

Koda maganar aurensu sati me zuwa ta bayyana tuni kowa yahau murna Nan aka Fara shirye shirye musamman iyami data bada himma gurin gyaran Amatun ga umminsa ma kusan kullum saitazo gurin duba Amatun taso taimakawa sosai Amma Khalil ya nuna kada tayi Masa komai zai iya iya qarfinsa shiyasa Dole tabari sai itama ta maida hankali gurin gyaran Amatun sbd 'danta yaji Dadi.

 

 

Sauran kudaden dasuka rage Masa yaso Kama wani gidan hayar dasu Amma duk gidajen babu Wanda zasu iya zama saiya aje kudin da niyar bayan daura auren Koda da sati biyune zaiyi qoqarin hada kudaden dazasu Samar musu gida me Dan kyau.

 

A bangare daya sanyi yayiwa jijiyoyinsa da qashinsa muguwar shiga a 'yan kwanakin sbd yanxu takai kowane dare Baya iya bacci daurewa kawai yakeyi cikin mutane baya nunawa Amma ciwonsa yatashi matuqa yanajin yanda lungs dinsa sukai mugun laushi baya iya Jan numfashi yanda ya kamata duk iya qiqarinsa yanayi Dan ganin ba'a fahimci halinda yake cikiba.

 

 

 

_GERMANY_

 

Kallon hoton katin Daurin auren da Khalil yaturo masa yakumayi da fararen idanuwansa dasukai wani irin laushi lokaci daya ya lumshe ido Yana sake kallon hoton katin ya ajiye ahankali tareda miqewa ya nufi gaban qaton window din dakinsa dake kallon swimming pool din gidan ya zuba hannuwansa cikin aljihun three quarter din dake jikinsa Yana qurawa waje Ido zuciyarsa na sanyi.

 

Tunani zuciyarsa keyi Amma ya yakuce hakan Yana lumshe ido

Tabbas zai halarta sbd ranar farin cikin Dan uwansa ce.

 

Juyowa yayi ahankali tareda dawowa yadauki wayarsa daya kashe sbd rashin son damuwa ya dannawa PA dinsa Kira Yana dauka Kai tsaye cikin muryarsa me sautin girma yace"

 

Ka shirya Mana komawa gida jibi akwai Daurin auren dazan halarta.

 

Done sir.

 

Kashe wayar yayi ya ajiye Yana sake karanta sunan dake rubuce 6aro 6aro akan hoton katin KHALIL DAHEER ZABEERA da AMATULLAH K SALEH.

 

sake dauke Kai yayi yana lumshe ido tareda sauke ajiyar zuciya ya juya yabar gaban labtop din.

 

 

 

_NIGERIA_

 

da kanta ta shirya tsaf Babu Wanda yasani ta fito suka fita da salman zuwa zabeera mansion.

 

A sashen Andi sukai parking tafito ahankali tana kallon koina komai na dawo Mata sabo tana tuno yanda tabar anty zarah dinta cikin kuka da damuwa take taji idanuwanta sun ciko da hawaye Bata damu da tsaidaduba Saida suka gangaro tasaka hannu ta gogesu ta nufi qofar shiga palon Andi din ta tura tashiga da sallama dama Salman ya tabbatar Mata da a irin wannan lokacin Modibbo na gurin Andi.

 

Modibbo ne yafara gabeta ya zuba Mata idanuwansa masu kwarjini da Khalil da MD suka dauko ta qaraso ahankali ta zube qasa gabansu sai alokacin Andi ya dago ya lura da waye.

 

Cikin tsananin biyayya da nuna damuwarta a fili tace"

 

Ina miqo gaisuwata ga Andi da Modibbo tareda neman afuwar babban kuskuren Dana aikata Wanda ya shafi 'da mafi biyayya da gujewa zuciyarku.

 

Kallon mamakin rashin tsoronta da gwarin gwiwarta suke Mata su duka din ta sauke Kai cikin nutsuwa da girmamawa tace"

 

Wallahi tallahi Dr khalil zabeera baitaba aikata laifin da kuke tunanin ya aikataba koma wane irine,

 

Taimako ya hadani da Dr khalil Kuma shine yasa yayita ajiyata acikin zabeera,

 

Ni marainiya ce kuma Yar bola kamar yanda kowa ke fada Amma Kuma banice nakai kaina bolarba harnayi rayuwa acikinta na tashi acikin

Rayuwa da jarabawar rayuwace takaini wadda itace tabaku girma da matsayi tareda sunan dakuke ganin yafi Dan Adam daraja,

 

Nayi rayuwar maraici da tozarci irinku masu arziki Baku dubemu ba kuka taimaka Mana saidai maigadin makarantane Wanda yake karban dubu bakwai a wata ya taimakemu,

Nayi rayuwar almajiranci Ina matsayin mace sbd kawai na rayu,

Nayi rayuwar wahala da qasqanci duk Dan sbd na rayu,

Munkwana da yunwa muntashi acikinta,

Lokacinda yaranku da jikokinku suke karatu mu bara mukeyi alokacin sbd muci,

Da kaina na koyi yanda zanyi yaqi da maza na qwaci kaina daga sharrinsu tun inada qananun shekaru

Shin nayi dukkanin wannan ne sbd nazama karuwa a rayuwa????

 

Nice na zabarwa kaina yin sata amaimakon karuwanci Dan kawai na rayu sbd sata Zan iya rokon me Abu ya yafemun wata Rana Amma Zina fa???

 

Dr khalil zabeera shine mutum me arziki na farko daya shigo rayuwarmu,

Yakawo Mana walwala da farin ciki a zukatanmu,

Talakawan bangarenmu wainda Dr khalil zabeera yakawo farin ciki akan fuskokinmu da rayuwarmu basa qirguwa,

Meyasa mutum me zuciya irinta Khalil maimakon ayi alfahari dashi za'ayi fushi dashi?

Shin Kuna tunanin ladar aikin Khalil kawai Bata Isa takawo qarin haske da walwala acikin zabeera ba??

 

'yayan da Allah yabaku dukkaninsu amanace agurinku Allah zaitambayeku alaqarku dasu idan da akwai cutatarwa,

'yayanku ne Amma Kuna gudanar da rayuwarsu kamarta dabbobinku kokuma bayinku,

Wasunsu da dama a tauye suke basa rayuwar farin ciki,

Zaman auren Dole da qunci sukeyi duk sbd bin umarni da qaidojinku,

Shin haramun ne neman farin ciki a wani gurin kokuwa musulunci ne ya hana?

 

Shi mutunci da girma Allah ne yake badawa Kuma shiya Baku

Idan Allah yabaku suna duk Abinda wani Dan Adam zaiyi bazai Bata hakanba Koda kuwa me zaiyi.,

 

Nazo zabeera ne sbd son kudina dakuma rashin sanin ciwon kaina Amma sbd tseratar da mutuncinku yasa ya karbi laifi da bacin sunan da baisan lokacinda aka hadosaba,

 

Wallahi niba karuwa bace,

Bantaba aikata zinaba,

Bansan ta Yaya ake aikataba,

Aikin gidajen abinci danayi nayine Dan neman halak Dina Wanda haryanxu Ina alfahari da hakan sbd Allah bai bani matacciyar zuciya ba.

 

Dagowa tayi da idanuwanta dasukai jajir ta ajiye katin Daurin aurensu cikin sanyin jiki tace"

 

Babban burinsa shine aurena yakawoni gabanku Dan neman yafiyarku da gafararku nikuma babban burin danakeson cika masa shine bashi kaina amatsayin mata dakuma sasantawarsa daku iyayensa,

 

Hawaye masu tsananin zafi suka gangaro Mata cikin daci da damuwa tace"

 

Dan Allah Ina roqan gafarar ku yafe Masa kodan kasancewarsa 'da me biyayya da gudun zuciyarku a baya,

Ku basa farin cikin dabai taba samu daga garekuba tun haihuwarsa....

 

Umme dake bayanta tuntuni a tsaye batasan lokacinda tafashe da kukaba tana sake Jin qaunar Amatu ta qaraso gabansu Modibbon ta zube itama cikin kuka tace"

 

Andi Dan Allah ku yafewa khalil kubarsa ya aureta wlh dukkaninsu ba laifinsu bane nice me laifin sbd nice na kawo Amatu zabeera da wata manufarda rashin wadataccen ilimina yabani.

 

Zayyane musu komai tayi sukai tsit Babu me motsi musamman Andi dashi maganganunsa Amatu ne sukafi shigarsa,

Shin dukkanin yawancin 'yayansu rayuwar kunci sukeyi sbd gudun zuciyarsu???

 

 

Tabbas tunda yake tsawon rayuwarsa Babu Wanda yataba kallonsa yafada Masa haqiqanin gaskia sai yau yaringa qanqanuwa daya Isa haihuwar ubanta koma kakanta ta kallesa tafada Masa quncin dayake saka 'yaya da jikokinsa shekaru wa shekaru.

 

Modibbo Kam dama tuni Amatu ta Dade dashiga ransa bazai iya nunawa bane sbd bacin ran Andi Amma tuni yajima da sanin yarinyace me fadar gskia batareda tsoro ko shakkaba.

 

Miqewa tayi ahankali ta juya ta fice tana share hawayenta daketa fita da gudu ta fada mota suka bar zabeera.

 

 

 

Kwance yake yau kwana biyu kenan ciwonsa nacinsa harya Fara cin qarfinsa ko fita daqyar yakeyi sai dare cikin duhu yake zuwa gidansu kawu sbd kada agano halinda yake ciki magungunsa yasiyo dasu inhaler Amma Sam kamar basa Masa aiki sbd kullum sanyi sake shigarsa yakeyi a gidan.

 

Yau laraba saura kwana daya Daurin aurensu Amma abin yaci qarfinsa tuni aka gano baida lafiya sosai sbd Koda Ibrahim yaje gidan tuni ya Dade da fita hayyacinsa hankali tashe ya kwashesa sai asibiti.

 

A asibiti Koda aka karbesa numfashinsa yayi nisa sosai cikin gaggawa akai emergency dashi ana qoqarin saka Masa oxygen.

 

Su kawu Ibrahim din yafara fadawa kafin yakira salman yafada Masa cikin qanqanin lokaci duk suka halarto asibitin hankalinsu duk atashe.

 

 

Kallo daya Amatu tayi Masa hankalinta yayi mummunan tashi sbd lokaci daya sanyi ya kumburasa

Numfashinsa Sam kwata kwata Babu saidai oxygen dinne ke janyo Masa ahankali idanuwansa a rufe fuskarsa tayi haske hakama bakinsa yayi haske sosai ya bushe.

 

Hawaye ne suka kufce Mata ta saki siririn kuka ahankali tana cewa''

 

Meyasa zaka boye bakada lafiya harsaida abin yayi tsanani haka?

 

Zaman rashin hankalin kurame sukeyi a asibitin daga ita har kawu da iyami duk suna asibitin da salman sai ummensa dasu Nuratu dasuka iso kowa cikin tashin hankali bama kamar umme datasha kuka idanuwanta sukai jajir.

 

Sunanan zaune har magriba saiga anty zarah da MD ZABEERA sun iso tana ganin anty zarah suka tsaya kallon juna cikin tsananin kewa da qaunar juna tazo da gudu tafada jikinta tana fashewa da sabon kukan datake ta riqewa tuntuni na ganin har lokacin sai Abinda yayi gaba ajikin nasa.

 

 

MD ne dakansa yaje yayi mgn da likitocin suka sake yimasa bayanin sanyine yayi mugun shigarsa Wanda yasa gaba daya jijiyoyin huhun Jan numfashinsa sun daskare ya tayarda ciwonsa gaba daya harya basa attack Sam numfashinsa yaqi dawowa ta oxygen dinma alamarin sai ahankali.

 

Tsorone yashigesa akaro na farko rayuwarsa

Dawowa yayi dakinda Khalil din yake ya tsaya akansa Yana kallonsa yaji zuciyarsa na neman karyewa da sauri ya juya fice.

 

Anan ta kwana asibitin itada ummensa da iyami har gari ya waye be farkaba zuwa lokacin Kam ko mgn basa iyayi da junansu sbd damuwa zazzaune kawai suke suna rarraba idanuwansu dasuka kode sukai zuru zuru.

 

Da yamma tayo alwalar magriba tazo gefensa ta tayarda sallah tayi tagama tana cikin addua taga kamar ya motsa hannunsa kadan ko shafa adduar batayiba ta zabura ta miqe sai taga idanuwansa a bude sunyi fari tas dasu  cikin tsananin farin ciki ta fada kansa ta rungumesa tana sakin hawayen farin ciki.

 

Umme data fito toilet din dakin tana ganin haka tayo kansu da gudu har sanyin ruwan qafarta na zameta itama fadawa tayi kansa ta rungumesa

 

Ya lumshe ido ganinsu su biyun ba qaramin farin ciki yasashi ba yasake lumshe ido cikin azabar ciwo yanason motsawa Amma sun dannesa

 

MD daya shigo yayi gyaran murya itace tafara juyowa sukai Ido biyu tayi saurin dauke Kai tana maido da kallonta Kan Khalil cikin tsananin farin ciki tace"

 

Dr Dan Allah karka sake rufe idonka.

 

Qarasowa yayi ahankali Yana kallon fuskar Khalil din yau farin cikinsa dai Kam ya bayyana

Shima Khalil din shi yake kallo fuskarsa nason bayyana farin cikin ganinsa Amma azabar ciwo ya hana.

 

 

Cikin sautin murya me taushi yace"

 

Kun sakar Masa nauyi da yawa inaga.

 

Da sauri dukkaninsu suka dagasa kafin suyi wata Magana saiga Andi da Modibbo tareda alhaji qarami sun shigo salman yakawosu take umme da amatun suka saki hawayen farin ciki suna kallon fuskar Khalil din da idanuwansa suka nuna zallar farin ciki ganinsa hawaye masu dumi suka gangaro ta gefen idonsa

Andi da kansa ya matso gefen gadon ya dafa kansa yasaka tissue ya share Masa Yana jinjina Masa Kai.

 

 

Salman da MD ne suka tayar dashi zaune amatu ta hado ruwan zafi da towel suka gyara Masa jikinsa tareda Sanya masa shirt Mara nauyi aka basa tea yasha kadan har lokacin da oxygen a hancinsa Kuma har lokacin bai iya mgn sbd bai iya jan dogon numfashi.

 

Kafin dare yadan warware ba laifi sbd Yana Dan magana ahankali tareda zuwa toilet idan ankamasa.

 

Da kawu yaso daga Daurin auren a gobe Amma Andi yace abarshi kada a daga tunda anriga anyi sanarwa.

 

Da daddaren ranar duk yanda ta nace hanata kwana asibitin akayi akace Takoma gida Salman zai kwana dashi tunda washe garine Daurin auren Dole ta koma bayan tayi Masa bankwana yabiya da Ido cikin kewarta tun Bata wuce dinba.

 

 

A gida duk wani hidimar al'ada sunyi abinsu hatta lalle anyi Mata a blue fox anty zarah takaita akayo Mata tareda gyaran Kai dana jiki Daurin auren kawai suke jira a goben akaita zabeera.

 

Tunda ta kwanta mafarkin Dr kawai takeyi sai kawai ta tashi tayo alwala tazo ta tayarda sallar nafila.

 

Tunda gari ya waye takejinta batada qarfin jiki sbd barin gida dazatayi.,

 

Qarfe daya da rabi dubban JAMA'A suka shaida Daurin auren KHALIL ZABEERA da AMATULLAH SALEH Wanda ya bayarda tarihi me girma sbd itace mace ta farko da aka auro daga waje.

 

A asibiti dagashi sai MD ZABEERA ne Wanda yace zai zauna dashi tunda kowa na gurin Daurin auren.

Bacci yakeyi sbd alluran da akai Masa bada jimawaba sbd jikin daya dawo Masa sosai.,

 

Bayan Daurin auren JAMA'A duk asibiti sukaita zuwa dubasa sai yamma lilis ya farka cikin ikon Allah saiya tashi da qarfin jiki haryana iya Magana tana Kuma fita sosai.

 

Wanka MD ya taimaka Masa yayi ya sanya farar jallabiyar datai Masa kyau matuqa yayi sallolin da ake binsa yazauna kenan saigasu umme da Nuratu wadda idanuwanta sukai luhu luhu sbd kukan data kwana tanayi.

 

Abinci ta zuba Masa ta zauna gefensa ta miqa Masa kanta a sunkuye batareda ta kallesaba.

 

Karba yayi tareda sauke numfashi cikin sanyin muryarsa dake fita ahankali yace"

 

Nuratu inshallah zaki samu Wanda zai wadata rayuwarki da farin cikin Dana kasa baki.

 

Kallonsa tayi idanuwanta na cikowa da hawaye murya na rawa tace"

 

Meyasa kakeson Amatu???

 

Lumshe idanuwansa dasuke a 'dan galabaice ahankali yace"

 

Allah ne yasamin sonta fiyeda komai

Kuma Ina fatar zaki qaunaceta kodan sbd ni.

 

Murmushi me ciwo tasaki hawayenta na sake gudu tace"

 

Zangwada.

 

Murmushi shima ya sakar Mata tareda juyowa ya kalli MD dake amfani da wayarsa yace"

 

Kaifa MAHMOUD???

Zaka gwada qaunar matata ko Dan sbd ni?

 

Juyowa yayi ya zuba Masa idanuwansa batareda yace qala ba.

 

Abinci umme ta matsa Masa ahankali yaci kadan Tasha tea me zafi har zufa yadan karyo Masa aka kunna Masa AC kadan.

 

Ganin yanayin jikin nasa dakuma shi kansa daya nema sallama yasa suka sallamesa bayan sallar magriba zuwa ishai Koda suka Isa zabeera daidai isowar motacin dasuka je dauko amarya Amatu.

 

A gurin Andi aka kaisu duk su duka yayi musu nasiha sosai kafin aka wuce da ita gurin zamanta wato sashen Khalil din Wanda aka sauyawa komai sabo.

 

Iyami da kanta taredasu maman junior suka kawota har cikin dakinta suna jinjina arzikin duniya irin na familyn ZABEERA kafin aka maidasu gida.

 

 

 

Ahankali yashigo dakin datake zaune zugum bakin gado tana tunanin da batamasan tanayiba...

 

Ji tayi anzauna kusada ita ahankali ta juyo sukai Ido biyu dashi gabanta taji yafafi ahankali ta dauke Kai zata sunkuyar ya riqo fuskarta ahankali tareda girgiza Mata Kai ya rungumeta cikin jikinsa ahankali tareda sauke ajiyar zuciya batareda yace komaiba.

 

Sunjima ahaka kafin ya saketa tareda cewa ta tashi suyi nafila.

 

Tashi tayi Babu musu sukaje toilet din tare sukayo alwala suka fito yakama hannunta suka nufi dakinsa.

 

Bayan sungama sallar hannunta ya riqo cikin nasa ahankali yace"

 

Zakici abinci ko wani Abu?

Akwai abinci da umme da antynki suka kawo gashi can a dining.

 

Dagowa tayi ta kallesa ahankali kafin ta girgiza kai.

 

Murmushi yasake ganin yau itama tazama kurma kamarsa tunda yafara ciwon baya iya doguwar Magana.

 

Miqewa yayi tareda tayarda ita tsaye Yana zame Mata mayafinta kyakkyawar fuskarta ta bayyana da kyau cikin qarfin hali yace"

 

Alhamdulillah.

 

Sunkuyar dakai tayi tana qaqalo murmushi ya janyota ya sanya cikin jikinsa ya rungumeta Yana lalubar zib din goguwar rigar Julius Holland din dake jikinta me laushi ya bude rigar ta Fadi qasa tabarta daga ita sai farar bra din dake jikinta da farin under.

 

Saurin rintse ido tayi zata durqushe ya tareda tareda rungumeta cikin jikinsa baida qarfin jiki sbd ciwo Amma hakanan ya cirata tana qanqamesa ya kwantar da ita Kan lafiyayyan gadonsa tareda rage hasken wutar dakin ya zare jallabiyarsa ya hau gadon ahankali tareda jawota jikinsa Yana kallon fuskarta ya Dora bakinsa akan nata tareda 6alle hook din bra dinta Yana cillowa qasa.

 

 

 

Qarfe ukun dare taringa Jin wani irin Nishi sama sama cikin kunnuwanta ta bude idanuwanta ahankali tana kallon inda take saita tashi zaune da sauri tana kallon gefenta a firgice tagansa numfashinsa na qoqarin daukewa cikin tsananin firgici ta diro gadon ta zagayo gabansa tana Kiran sunansa cikin tashin hankali Amma Sam tayi nisa a kidime ta janyo jallabiyarsa ta zura sbd itakadaice zata shigeta alokacin sbd firgici

Sam Bata damu da tsakiyar darene ba ta fito da gudu tayi hanyar sashensu anty zarah dake kusa da nasu a kidime tahau buga musu kofa tana Kiran sunan anty zarah da qarfi.

 

MAHMOUD dake zaune daram acikin Daren yakasa ko rintsawa sbd tsananin ciwon Kai yafara jiyo bugun qofar ya sauko daidai itama zarah tafito daga dakinta Dan taji bugun qofar itama.

 

Shine yafara cewa"

 

Waye??? ta jikin qofar

 

Cikin sauri da tashin hankali tace"

 

Nice Amatu Dan Allah kuzo Dr ne......

 

Tun kafin ta qarasa ya bude qofar yanayin datake ciki yasashi Kama hanyar sashen nasu batareda tagama fadar Abinda zata fada din ba.

 

 

Koda suka iso tuni Dr khalil zabeera yayi nisa shima yau gigitar yashiga ya janyo wata jallabiyar da sauri ya sanya Masa ya daukesa da dukkanin qarfinsa yafito dashi suka biyosa

Zuwa lokacin Amatu kukanma takasa Yi suka fada mota Banda zarah dayace taje hafsatu ta Rakata ta fadawasu umme.

 

 

Koda suka Isa asibiti cikin gaggawa aka karbesa akai ciki dashi zuwa lokacin Amatu idanuwanta neman qanqancewa sukeyi kamar wainda ke bayansu saiga umme da Modibbo harma da Salman sun qaraso asibitin Babu me nutsuwa Hakanan yau ciwon nasa yasasu cikin wata irin rashin nutsuwa da firgici.

 

Dr ashir ne da Dr Fatima suka fito daga dakin emergency din idanuwansu kowanne jajir Dr Fatima tuni idanuwanta suka kawo hawaye rauninta na bayyana Dr ashir ya sauke Kai gaban Modibbo yace"

 

Saidai hakuri Allah ya karbi Dr khalil zabeera.

 

Wuta kowannensu ya dauke musamman Amatu da umme

Amatu qyafta idanuwa tayi kusan so biyu kamar zata makance sbd duhu dake mamaye idanuwanta suka yanke jiki a some kusan atare itada umme wadda Modibbo ya tare ita kuwa MD ne ya tareta ta zube jikinsa dukkanin jikinta ba saki.

No comments

Powered by Blogger.