Min Qalb 16-20

 

MQ 16_*


Zaune take gaban madubin dakin daya zama Mata tana kallon fuskarta datayi haske sosai tareda duka fatar jikinta har wani qyallin samun hutu da kayan gyara masu tsada da mutunci zuwa qirjinta daya ciko shima yayi daram dam  sabanin dah banbancinsa da shafe idan tasaka brazier ne push up.


Mayarda kallonta tayi Kan cikinta tana miqewa tsaye ta Dan matse rigarta tana shafa cikin sai tasamu kanta da sakin murmushi karon farko datai shaawar dama ace cikin gasken ne da ita da zaiyi mata kyau Kuma da duk wahala da dawainiyar anty zarah baza taje a banxa ba,


Dan sake dafe cikin tayi tana cewa''


To idan ace cikin gske ne to waye zai zama babansa?


Dr??


Girgiza Kai tayi tana cewa''


Ummen sa bazata Bari ba.


Amma dai duk da haka shine zaifi iya bawa babyna kulawa Amma dai kamanninsa kuwa anty zarah nakeson ya dauko sak sai Kuma......


Shiru tayi takasa qarasawa


Daga bayanta taji ance' sai Kuma me maman bby?


Juyowa tayi tana kallon ZARAH din kafin ta juya ta qurawa cikinta ido ta cikin madubin ahankali tace'


Sai Kuma inason ya dauko hancin MD.


Zarah dake qoqarin zama bakin gado tsayawa tayi ta kalli amatun tana karban zancen a baibai saidai kawai tasan duk irin shirme shirmen Amatun sai kawai tasaki murmushi tana janye Amatun daga gaban madubi tana cewa"


Zoki zauna zaki gaji da tsayuwa gashi yau zamuje scanning anjima kadan 

MD nake jira ya kirani na sanar Masa zamu fita nayita Kira baya dauka tun safe bayan fitarsa.


Ki qyalesa anty zarah mu tafiyarmu kawai tunda Dr na can Yana jiranmu a asibitin tun dazu yake Kira bamu fitoba.


Bazaki gane bane Amatu dokar MD ce baya barina fita Babu wani babban dalili me qarfi sbd shi mutum ne me buqatar sirrintacciyar rayuwa Mara hayaniya shiyasa bayason ko iyalinsa ace kowa ya sansu a haka dai zance MD mutum ne me tsananin kishi.


Dibar zancen na anty zarah tayi ta watsar da baki tana cewa"


Anty zarah to nidai gskia muje karki tsaya jira tunda yaga Kiran naki fa na tabbata,

Kuma nidai bazan Bari Dr yayita jiraba tunda Modibbo da Andi sunsan da zancen fitar muje kawai Dan Allah.


Miqewa anty zarah tayi tana nufar qofa tana cewa'


Amatun 6acin ran MD ba kyau bazan iya take dokarsaba 

Zan iya fita yanxu wani Abu yafaru wlh bazan iya daukar fushinsaba kiyi hkr Bari nasake gwada kiransa kozai dauka....


Takaici yasa Amatun dafe ciki ta durqushe tana cewa''


Wayyo Allah anty zarah cikina marata ciwo sosai 

Dan Allah anty ki taimakeni kada cikina ya samu matsala Ina sonsa banason ya zube.....


Da gudu anty zarah ta dawo tana Kiran sunanta cikin tashin hankali tana riqota 

Ita kuwa Amatu sai wani murqususu takeyi tana sako hawayen qarya tana Daman cewa''


Anty ki taimakeni banaso cikina ya zube.


Tsabar tashin hankali da firgici tareda tausayin Amatun me tsanani ZARAH batasan lokacin data fashe da kuka ba tana kamota jikinta tana qoqarin muqar da ita tana kwalawa hafsatu Kira Dan tazo su kamata suyi asibiti.


Kamata sukayi suka saka mota a gigice anty zarah ta yafo gyalen jallabiyar dake jikinta ta fada motar ta jasu suka fice tana cewa hafsatu"


Hafsatu maza Yi sauri ki Kira Dr khalil ki sanar Masa Abinda yake faruwa gamunan zuwa.


Shiru Amatu tayi daga kukan qaryan datakeyi jikinta na yin sanyi da yanda anty zarah ta daga hankalinta sai hawaye takeyi tana Mata sannu Amma Babu yanda ta iyane itama sbd Dr yace Mata komai zatayi ta tabbatarda sunxo asibitin sbd yabasu scanning din daya shirya Dan ita din idan basuxo asibitin ba to tabbas wani likita ummensa zatasa akawo har zabeera din Dan kawai ayi komai yafito fili

A bangare daya Kuma ga USI da shima zasu hadu duk a asibitin shiyasa tayi hakan,


Ahankali ta kamo hannun anty zarah din bayan har sun iso asibiti Khalil ya karbeta sun shige yayi duk yanda zaiyi ya hado scanning din aka kwantar da ita office dinsa tareda 'yan magungunan vitamins sai alokacin hankalin zarah yadawo jikinta ganin Amatun tadawo daidai ciwon ya daina.


tana kallon anty zarah din bayan ta riqe hannunta ganin har lokacin da sauran damuwa a fuskarta itama cikin sanyin murya furta"


Nagode anty zarah,

Nagode da matsayin da Kika bani na qanwa tamkar wadda kuka fito ciki daya,

Anty zarah wlh kece mutum ta uku da Kika taba qaunata tsakani da Allah ba qyamata ko wulaqantawa Dan haka kinada babban matsayi a zuciyata da har abada bazan mantaki ba.


Kasa cewa komai anty zarah tayi sbd har lokacin Bata Gama fitowa cikin shock din halinda Amatun tashigaba 

Dan wato da ace wani Abu yasamu cikin bazata taba yafewa kanta ba.


Shigowar Dr da USI a bayansa yasata miqewa zaune da sauri tana washe dukkanin haqoranta cikin tsananin farin ciki takira sunansa tana qoqarin saukowa gadon Dr khalil yayi Mata gyara murya Yana kallonta 

Take ta kallesa tana dawowa nutsuwarta saita waske ta hanyar cewa"


Anty zarah ga qanina usman.


Kallonta anty zarah tayi irin da gasken Nan kike?


Daga Mata Kai tayi murnarta na sake bayyanuwa ta jawo Usman din gaban anty zarah tana cewa"


Usi ka gaida anty zarah.


Da sauri cikin girmamawa yace"


Anty mun wuni lafiya?

Ya gida Yakuma qoqari?

Mungode sosai sosai fa anty

Allah ya saka Miki da alheri

Ya biya Miki buqatunki na alkairi.Murmushi anty zarah tayi tana kallon yanda jikinsa har mazari yakeyi gurin gaidata Yana fiddo dukkanin girmamawar dayake ji akanta sbd duk yanda take qaunar Amatunsa tafada Masa shiyasa shima tun baigantaba yake Jin qaunar halayenta da ganin girmanta.


Kallon Amatu dake cikin dokin ganin usman din tayi tana cewa''


Amatu me Kika fada Masa yaketa wannan addua haka?

Usman karka ji komai ba komai Amatu tamkar qanwar da kuka fito ciki daya nake jinta 

Saidai kayi Mata nasiha ko zataji Amatu Bata zama kurum kodan halin datake ciki gashi yauma sbd tasa damuwar fitowa Dole yasa akaso samun matsala har muka qare kwance a asibiti.


Anty zarah ki ringa doketa kokuma ki Fara hanata kayan Dadi zata dawo hankalinta.


Dariya sosai anty zarah tareda Dr suka saki harda ita Amatun tana kaiwa usi mugun duka a baya tace"


Ni zakayiwa baqin ciki usi?

Zakasan dawa kayi sai nasa kawu ya aura maka qanwar maman junior data maqale maka.


Cab wannan ai koni tafi iya sanin yanda ake sanfewa Dan wlh koke duk qwarewarki saita sanfeki

Kisa ranarda aka kawota ta sanfe Dan cinikin iyami da kawu kejin yanzu yafara zamowa sahun masu abun Kai kawu ya kwana ya debewa auren albarka.


Dariya suka saki gaba dayansu hadda anty zarah da batasan meye sanfewarba dagasu sai Dr ne kawai suka sani shima sbd yayi bincike sosai akansu ne Kuma sun zauna dashi su kawu da USI din Basu boye Masa komaiba gameba rayuwarsu sbd sunriga sun daukesa kamar jininsu.


Ta Dan saci kallon Dr da ita yake kallo shima zuciyarsa na samun nutsuwa da yanda yake ganinsu cikin nishadi zuciyarsa na sake samun nutsuwa

Ta juya ta harari usi tareda take Masa qafa da qarfi har Saida ya zabura tayi saurin dafesa Dan kada anty zarah tagane qasa qasa tace"


A gaban Dr baban babyn nawa kake tayarda maganar qwarewata a sata ka  shirya kwanciya a asibitin Nan Dan saina fasa maka baki da haqora idan anty zarah ta fita.


Kallon Dr yayi da Ido Yana cewa''


Ka ceceni matarka zata fasa bakina Wai.


Kamar zaiyi Magana sai ya fasa Yana sakar Mata murmushi sbd idanun data zuba Masa tana jiran jin Abinda zai ce ta mayarda rigimar kansa.


Ikon Allah anty zarah tayita kallo a tsakaninsu sunata raha da nishadinsu cikin tsananin qaunar junansu ga Dr da tuni dama yazama 'daya daga cikinsu gabanta harsu iyami aka Kira da kawu a wayar Dr Nan aka Dora wata sabuwar hayaniyar sbd labarin fadanda kawu yayi dasu maman basiru ya dauko motar yan sanda biyu aka kwashe gidan kaf harda alhaji mande daya iya shigar sani infika.


Dariya sukeyi sosai musamman da iyami ke fadawa Amatu kawunta ya zabure yanzu tunda yaga ya 'dan tsayu hakama insfector Garba na Nan Yana bibiyar kawun akan maganar aurenta.


Nishadi sosai suke saka anty zarah tayi zugum tana kallonsu suna burgeta hakanan taji inama acikinsu take itama data samu farin ciki kamarsu,

Abu daya tasani shine Koda take cikin wadata ta taso cikin tun tana gidansu Basu San wani Abu Wai sakewa cikin nishadi kayi rayuwarka ba,

Tun a gida sun Saba bin umarni ne kawai da oda suka sani 

Iyayensu basa jansu ajiki Wai da sunan tarbiya da kadasu lalace

Shiyasa yawancinsu Basu wani cikin walwala saidai kawai suyi rayuwa cikin daular Amma Babu wani walwala saigashi wainnan bayin Allan sunada duk wani nishadi da walwala suna rayuwarsu hankali kwance,

Tabbas shi nishadi da farin ciki ba siyansa akeyiba Allah ne yake baka

Gashi ayau duk da tarin daular datake ciki rayuwar wainnan talakawan tana burgeta harma tanajin inama acikinsu take.


Anan sukai kusan Rabin yinin sai yamma suka fito gabaki dayansa tana Jin kewar usi dasu kawu tun Usin be tafi Amma hakanan suka rabu shida Dr suke tafi a motar Dr sbd yakaisa gida itakuma suka tafi a motar anty zarah da hafsatu.


Suna tafe suna tana kallon titi cikin nishadi sbd tunda tashiga zabeera tsawon wata biyu sai yau tafito,

Gskia dai ma Ashe wani lokacin masu kudin rayuwar takura kawai sukeyi kullum a killace Wai sbd kar mutane su dameka,

Ita Sam batason akoma gidan yanzu yawo takeso tadan sakata ta Wala.


Qaramin tsoki taja a fili Wanda yasa anty zarah kallonta tana cewa''


Yaya dai Amatu?


Bata fuska tayi tana yamutsawa tace"


Anty zarah Dan Allah muje blue fox na taba yin aiki acan 

Muje kibiya madam dinmu kudi yau da kanta zata wanke min Kai da qafafu tasan Nima bayan ta koreni aiki nayi gaba ba bataba.


Murmushi tayi tana cewa''


Amatu ba dama.


A blue fox wani shaqiyanci ta dinga yiwa madam bell din tana cewa ga Abinda da Abinda takeso 

Haka dai suka ringa yimata Abinda tace sbd ganin wadda sukazo tareda ita din she's from zabeeras.


Gyaran Kai akai musu itada anty zarah din tareda kyan qafa da gyaran fuska take suka koma tamkar wasu amare musamman amatun da Bata taba irin wannan gyaran ba take suka hau wani irin sheqi.


Daga nan restaurant din blue fox din ta matsawa anty zarah suka shiga Nan tayi odar kayan dadin dataci harta Bar saura sbd sunfi qarfin cikinta suka fito nanma matsawa anty zarah  tayi suka nufi wani qatoton shopping mall datace tanada kwadayin son shigarsa.


Suna shiga mall din me hawa biyu batasan lokacin data saki tsallen murna ba tana rarraba idanu cikin gurin farin cikinta a bayyane.


Sama suka hau gurin kayan babies antyn na cewa kayan baby kawai zasu siya

 Nan anty zarah tadan zaba kayan babies suka sauko Amatun nata zare Ido tarasa abin dauka sbd duk kayan Dadi da maqulashen dake gurin akwaisa a gida hakama sutura Bata buqata sbd Dr kusan kullum cikin kawo Mata su yake hakama anty zarah

Idan turarukane duk tanadasu a gidan hakama takalma,

Ita Kam da a dah ne tazo wannan gurin da saita sace kusan kayan dubu dark saidai suje station

Amma ko yanxu ba damuwa Dan saita yiwa Dr tsarabar dazai ringa tunata.


Wani tsadadden agogon Rolex tagani Yana qyalli take ta hango kyanda zaiyi a hannun Dr 

tasaki murmushi tana kallon anty zarah dake qoqarin Ciro card dinta tabayar gurin payment ta faki idanuwansu ta zaresa tareda sakawa cikin aljihun doguwar English gown din dake jikinta tana waskewa tahau 'yan juye juye tana latsa wayar anty zarah dake hannunta.


Suna Gama payment din suka fito har zasu shiga mota aka tsayar dasu da sauri ana cewa su dawo ciki anason ganinsu.


Tsayawa anty zarah tayi tana kallonsu cikin mamaki kafin ta kalli time har anfara Kiran sallar magrib tace"


Lafiya?

Sauri mukeyi munyi dare fa.


Dayan ne me sanyeda suit kamar ma shine babbnsu yace"


Haj wani Abu mukeson kugani da idanuwanku kafin muyi mgn please.


Qaramin tsoki tasaki tana cewa''


Amatu ku jira a mota Ina zuwa.


Aa hajiya da ita zakuzo duka muke buqatar ganinku.


Ba musu suka koma ciki har office din managern gurin suka zauna take aka kunna musu Abinda footage na CCTV camera 

Mutuwar zaune anty zarah tayi cikin mamaki da kunya 

Amatun ma cikeda kunyar anty zarah ta dago ta kalleta kafin tayiwa manager kallon takaici

Bataji kunyarsa ba ko kadan ita anty zarah ce kawai abin Jin nauyinta itama dandai na farkone datayi a gabanta.


Bude baki anty zarah tayi Yana Mata nauyi zatayi Magana kenan saiga Yan sandan da aka Kira mota guda har sun iso Nan take aka gargadosu zuwa mota anty zarah tsabar rudewa da tashin hankali ko magana ma takasa Yi.

Wata baqar Mercedes-Benz beymach30745 2020 ce tashigo harabar gurin tayi parking

Tareda wasu motoci guda biyu manya na asalin me mall din dasukazo Dan duba gurin zai siye tareda estate din dake bayan mall din.

 saidaya dauki lokaci Yana qarasa wayar dayakeyi kafin yafito 

Lokacin su alhaji bayo din yafito tareda P.A dinsa dukkanin ma'aikatan gurin sunyo gurinsa suna Masa barka da zuwa hakama ganin MD ZABEERA taredashi yasasu qara bada girmamawa suna Masa barka da zuwa barema daman sunji shine zai siye gurin.

##mamuh#

ZAFAFA BIAYAR


SIRADIN RAYUWA

safiyya huguma


MIN QALB

mamuhgee


YANKAN BAYA

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Pay @09033181070

Or 09032345899

[3/26, 7:46 PM] Zafafa: *_MQ 17_*

_Mg_Ana qoqarin turata motar Yan sandan ta hangosa tareda mutane Yana waya har lokacin kamalarsa na sake fita dabam acikinsu batasan lokacin data washe baki ba tana cewa''


Anty zarah bazan Bari kije station ba da mutuncinki,

Fizge hannunta tayi daga hannun 'yar sandar mace ta maraice da fuska kamar zatayi kuka tace"


Officer madam Dena riqeni da qarfi cikine Dani Kuma....


Kallonta anty zarah tayi duk da tsananin baqin ciki da kunyar datake ciki Bata fatan Abinda zai samu Amatun sbd cikin jikinta 

Zatai Magana idonta ya sauka kan MD dasuke qarasowa daf dasu zasu shiga mall din 

Wani mummunan tashin hankali ya shigeta tai saurin fadawa motar Dan kada ya ganta bazataso mutuncinsa ya zube agurin ba da zarar angano ita matarsa ce

Barema sanin dokarsa da Abinda yafi tsana shine iyalinsa suzo budadden gurinda za'a Gama ganesu kamar wasu marasa daraja.


Amatu na ganin haka ta 'dan daga murya tace"


Ku bamu damar Kiran wani daga gida

Sbd daga babban gida muka fito wato ZABEERAS.


Cak ta 'dan tsaya bai juyoba saidata qara Kiran sunan zabeeras din tana sake Dan daga murya sbd ganin ya tsaya 

Kai tsaye ya juyo idanuwansa suka sauka kanta a bakin motar 'yan sandan Babu alamar kunya ko Jin nauyi atare da ita 

Kai kawai ya dauke zai tafiyarsa saikuma ya tsaya cak sbd kamar matarsa ya hango cikin motar 

Saiya kasa juyowa tsawon seconds kafin ya juyo cikin nutsuwa ya kalli cikin motar 

Zarah dince kuwa a zaune tana sunkuyar da kanta

 take wani irin dacin Rai me mugun tsanani ya rufesa Amma idanba Wanda yasansa ba bazai iya ganewaba

Rintse idanuwansa yayi dasuka sauya atake yana controlling nutsuwarsa ta sakan hudu kafin ya budesu ya sauke Kan managern gurin cikin muryarsa me taushi da nutsuwa yace"


Meyake faruwa anan?


Bayani tsaf manager ya koro Masa Yana qarawa da cewar"


Ranka ya Dade wannan itace asalin wadda tayi satar inaga ita waccan me ajewa ce wato shugabarta Kuma.........


Hannu ya dagawa managern Yana qara controlling fushinsa da idan yasakesa agurin fasa gurin zaiyi gaba daya Dan bazai iya daukar fushinsaba.


Yana daga wayarsa dake ringing yace"


Ku sakesu suje

Abar zancen daganan

Zanyi handling komai da kaina.


Okay ranka ya Dade angama

Officer ku sakesu su tafi 

Ke hajiya fito 

Allah ya taimakeku MD yasa baki ku wuce karku sake zuwa Nan sbd next time bazaku samu wannan damarba ta kubuta Dan munsan yanda muke dealing da qananun barayi irinku..


Zuwa lokacin kuka anty zarah keyi sbd maganganun dayake jefa musu dakuma sanin yau taqare Mata tsakaninta da MD Dan ita kawai ke iya hango _rage_ din dake fuskarsa gasu tafito bada izininsa ba,

Takai dare a waje ga wani irin bacin suna da aka ja Masa Danma ba'a gano ita matarsa bace.


Daqyar take Jan qafa jikinta na mugun rawa ga hawayen datake sosai ta nufi mota Amatu na binta jikinta a macen itama sbd ganin halinda anty zarah din ke ciki Wanda Bata taba ganinta acikinsaba.


Suna shiga mota daqyar anty zarah din ta iya tayarwa suka bar gurin Babu me iya ko dogon motsi a motar har suka Isa Kuma har lokacin hawayen anty zarah Basu tsayaba.


Suna barin gurin ya daga wayarsa daketa ringin Kai tsaye yace"


Dr duk Abinda kakeyi ka tabbatarda matarka tabar gidana acikin Daren Nan.


Kashe wayarsa yayi Yana Gama fadar hakan kafin yajuyo ya kalli P.A dinsa yace"


Faruk handle this for now

Gida zanje gobe zaka bani details din yanda akayi.


Juyawa yayi Kai tsaye ya nufi motarsa ya fada tareda janta da kansa yabar gurin sai alokacin suka fahimci da matsala sbd yanda yaja motar yabar gurin.Suna shiga Palo tayi saurin Shan gaban anty zarah tareda zubewa qasa da qarfi Kan gwiwoyinta tana sunkuyar dakai cikin tsananin nadama tace"


Anty zarah kalmar hakurina bazata canza komaiba gameda tozarcin Dana janyo Miki yau din

Dan Allah anty zarah kiyi hkr wallahi bantaba Jin kunya da takaicin halinaba sai ayau,

 wlh sbd ke yau naji na tsani wannan halin nawa Dan Allah anty zarah kiyi hkr wlh banyi Dan tozarta.....


Saukar wani lafiyayyan Mari taji a fuskarta Wanda yasata qarasa zubewa zaune tana taba fuskarta amatuqar gigice ta dago a zuciye zatai Magana idonta ya sauka cikin nasa idanun dasuka kada sukai jajir....


Da sauri zarah ta zube qasa itama zatai Magana ya daga Mata hannu batareda ya kalletaba yace"


For first time ayau naji nayi takaicin amincewa da aurenki,

Hw cud you zarah,

Bakisan mutuncin kanki da Wanda ya ajiyeki bane dazaki fita in the first place batareda izini ba 

Ever this stupid being came here nasan zaayi haka wata Rana sbd wannan ba mace bane she is just a shame,

Sata rayuwarta ne 

Shi aka reneta dashi sbd Abinda tasani shine kawai sata da yawo cikin maza with no shame,

A hausance banma san sunan dazan kirataba sbd idanma ankirata da abin kunya an Bata sunan mutunci

Amma ke this is the last thing I expected from you...


Banason hayaniya I prefer rayuwata ni kadai yafi nutsuwa da kwanciyan hankali so please ku duka just park ur things kubar Nan 

Ni kadai nakeson zama anan just I think kowannenmu need a break.......Wani irin kuka Mai taba zuciya anty zarah tasaki tana qoqarin basa hkr ya juyawarsa zai haye sama Amatu ta miqe da saurin Tasha gabansa tareda sake zubewa tana tsiyayo hawaye masu tsananin 'dacin kalaman daya furta akanta saidai komai 'dacinsu zata hade bazata Bari laifinta ya lalata auren anty zarah ba kodan yanda tasan shine rayuwar anty zarah din.


Akaro na farko a rayuwarta datake qwallan cin zarafi da akai Mata sabanin da ko ajikinta Dan ko damuwa batayi barema ada Babu Wanda ya Isa ya tsareta ya iya fada Mata haka Bata saka an Masa zanen yorbawa a fuskar ba.


Sabbin hawaye suka gangaro Kan fuskarta ta bude baki muryarta a matuqar sanyaye tace"


Dan Allah kayi hakuri anty zarah batada lai...


Ko kallon inda take baiyiba ya wuce tayi saurin rarrafawa zatasha gabansa  cikin tsananin 6acin Rai ya daga qafa zai wuce da ita aka saka hannuwa biyu aka tare qafar

Ya tsaya cak kallon Dr daya riqe qafar tasa cikin tsananin mamaki da sabon takaici.


Dr daya jima tsaye Yana sauraran duk Abinda MD din ya fada suna dukan zuciyarsa duka me tsananin daya karya gwarin gwiwarsa.


Baice komaiba sai kawai ya sauke gwiwoyinsa qasa gaban MD din tareda sunkuyar da Kai cikin tsananin rauni da damuwa me nauyi murya a sanyaye yace"


MAHMOUD karka hukunta zarah akan laifin amatu na roqeka da sunan Allah,

Itama Amatu Ina roqonka daka yafe Mata Koda  hakan zai zama alfarmar qarshe dazakamin arayuwata to Dan Allah ka yafe Mata ba laifinta bane laifina ne Dana kasa bar Mata duk Abinda yakamata nabar Mata......


What???Khalil Kama San waye wannan yarinyar kuwa?

Tun farko bansan me kagani na hankali atareda wannan yarinyarba harka iya sabawa iyayenka ka aureta,

And now kana durqushe a gabana duk sbd ita 

Khalil Kama ganin daidaine hakan?


Rintse idanu Dr yayi a sanyaye Yace"


Abinda nasani yanxu arayuwata shine indai sbd itane zanyi har Abinda yafi durqusawa sbd tsirar Mata da mutuncinta,

Kai Dan uwanane mafi kusanci agareni Wanda kalmomin batanci mafi Muni suka fito daga bakinka kan macen danafi so da qaunar Kare martabarta shiyasa na durqusa gaban nake neman afuwarka sbd ita,


Cikin sake kunnasa da Khalil din yayi da maganganunsa hakanan kawai yaji mugun zafinsu 

Yau Khalil ne ke fadar kariya da martabarta 

Rintse ido yayi suna qara rinewa ya kalleta 

Sautin kukanta na fita ahankali sbd maganganun Dr sungama sanyata cikin nadama me tsanani

Take zafin zuciyarsa yafara loosing control ya juya zai wuce Khalil ya miqe tareda Shan gabansa yace"


MD matuqar haryanxu matsayina na Nan a zuciyarka da rayuwarka inason ka tabashi biyu kabani nida Amatu sbd wlh ni itace tawa rayuwar,

Zakaimin alqawarin yafe Mata tareda Bata mutunci amatsayinta tawa,

Idan bakayi Dan ni ba kayi kodan jinina dayake jikinta Wanda yake shima naka jinin,

MD Ina fatan zakamin wannan alfarma ko bayan idona.Kasa kallon Khalil din yayi sbd baqin ciki da takaicin duk akan mace ya zare haka macen ma ba kamar matan mutunci ba haryana kirarin idan yana qaunarsa saiya qaunaceta 

Ra'besa kawai yayi ya haye sama tun kafin shida Khalil din ta 6aci akan yarinyar.Bayansa Khalil yabi da kallon harya shige kafin ya saki numfashi a sanyaye tareda juyowa ahankali ya zauna gefen amatu dake kuka qasa qasa takasa ko motsi.


Kallon zarah dake nata kukan yayi zaiyi mgn ta miqe tabar gurin tayi dakinta ta rufo sbd itama kukan takeso tayi sosai ko nauyin zuciyarta zai ragu.


Cikin sanyin jiki ya maido da kallonsa Kan amatu yafara lallashinta Yana Mata nasiha hartayi shiru da kansa ya dauko ruwa a fridge yabata Tasha ya rakata har dakinta kafin ya wuce zuwa nasa part din jiki da zuciyarsa amatuqar sanyaye.


Sallolinta tayi ta zame ta kwanta Kan dadduma a inda tayi sallar yau ba Maganar cin Dadi

Amma datayi awanni a kwance taga bacci ba zuwa zaiyiba sbd yunwa hakanan ta miqe ta fito taje kicin taci fruits dinta da yoghurts ta qoshi tazo ta kwanta tunanin Dr na dawo Mata bangare daya Kuma damuwar da anty zarah take ciki.Washe gari tunda safe Dr khalil yazo sbd yasan shikenan MD zai Fara rashin 'dan zaman dayakeyi a gidan fita tinda safe dawowa sai dare qarshema yasan zai iya tafiya yabar qasar yakoma wata qasa sai yaga dama ya dawo.


MD na ganinsa ya kallesa Yana watsar da tunanin abubuwan jiya din sbd shi ba mutum ne me aje hargitsi cikin kansa ba Sam ko maganar batason a tayar sbd kar asashi cuwon Kai.


Kallonsa Dr khalil yayi Yana qaqalo murmushi yace"


Good morning MD ZABEERA.


'dan kallonsa MD din yayi Yana maida kallonsa Kan agogon hannunsa cikin miskilanci yace"


Morning Dr khalil zabeera.


Murmushi Khalil din yayi Yana cewa''


Sorry MD.


Kallonsa ya 'danyi kafin yaci gaba da duba wayarsa.


Bai kamata nama Magana irin yanda nayi maka a jiyan kayi hkr.


Karka damu I can't even recall Abinda yafaru a jiyan.


Numfashi Khalil ya sauke Yana gyara tsayuwa kafin yace"


Amma akan Amatu inakan duk Abinda nafada Dan haka Ina riqon alfarmarka sbd abin dake cikinta please kabata damar dazan gyarata kodan 'yayana su samu uwa ta gari.


Gaba daya MD din ya dago ya kallesa wannan karon tareda 'dan lumshe fararen idanuwansa yasaki wani sahirtaccen numfashi kafin yace"


I hope you know wat u're doing.


Motarsa ya fada tareda cewa''


Mu yini lfy Dr.


Murmushi Khalil yayi Yana cewa''


Zan dauki wannan amatsayin amincewa da roqona thank you.


Ciki ya qarasa gurinsu sbd Suma yanason mgn dasu musamman zarah bayason tasamu matsala da Amatu akan wannan alamarin sbd ita kadaice yasan Amatu is safe a gurinta.


Cikin sa'a kuwa Zarah din na dining tana qoqarin jera breakfast tayi 'dan adonta duk da ba walwala sosai a fuskarta duk sbd taqara bawa MD hakuri.


Cikin sakin fuska yakira sunanta 

Ta juyo tana yaqen Dole suka gaisa 


Suna cikin mgn saiga Amatu ta fito jiyo muryarsa 

A sidade ta qaraso tana kallon fuskar zarah a raunane.


Ganin yanda tayi din sai anty zarah din taji rashin Dadi ta saki 'dan guntun murmushi tana cewa''


Amatu Zo 

Kinci abinci jiya da daddare kuwa?da maganinki ma kinsha??


Wani sabon girma da qaunar anty zarah dinne suka rufeta batasan lokacinda ta qarasa gurinta da sauri ba ta rungumeta tareda sakin wani siririn kuka tana cewa''


Anty zarah Dan Allah ki yafemun wlh nayi nadama me tsanani akan Abinda na ja miki.


Karki damu Amatu qaddarane Kuma yariga ya wuce tunda kince bazaki sake ba.


Zama tayi gefen anty zarah din ta share hawayenta tana sunkuyar da Kai tace"


Anty zarah kunyarki nakeji haryanxu sbd tun yanxu nafara saka Miki da Abu Mara kyau akan alkairi da qaunar da kike mini,


Ayau naji gida nakeson komawa inda nafito,

Cikin mutanenda nafito,

Cikin rayuwar damuka saba da qanqancin da muka Saba dauka sbd nafara gane ban cancanci zama cikin mutane masu mutunci da daraja kamarku ba,


Anty zarah daukar abin wani yazama tamkar qaddaratace sbd saimun dauki abin wani muke iya ciyar da cikinmu abinci wata Rana,

Rayuwa da mutanen cikintane suke tilastamu ga aikata wasu laifukan wata Rana,


Nida usi muntaso cikin bola muka rayu acikinta mukayi wayo,

Acikin bola muka Fara sanin yanda zamuyi fafutuka mu gudanar da rayuwarmu,


Bayan Tasha shine gurin kwananmu

Shine muhallinmu a lokacin,

Tun munada shekarun da bamu Gama sanin bambamcin jinsuba aka lalatawa usi rayuwa ta hanyar Masa fyade,

Fyaden da shine sanadin farko na qarin tabarbarewar rayuwarmu,

Alokacin mukasan ba tausayi atareda mutanen cikin duniya,

Munkoyi data Danmu ci mu tsira mu rayu,


Anty zarah bamu qara fuskantar qasqancin halin rayuwa da mutanen cikintaba sai alokacin da nida USI aka kamamu a gaban idonsa aka yaga tsumman sutura dake jikina za'ayi mini fyade Wanda yayi sanadin haduwarmu da mutum na farko daya Fara yima kallon muma 'yayane Kuma mutane 'yan Adam,


Kawu ya gabatar Mana da sabuwar rayuwar almajiranci wadda nayita acikin maza da siffar maza ta hanyar rayuwa usman namin aski,

Munyi almajiranci na wahala Wanda yasamu baqin jini acikin almajirai Yan uwanmu,

Munyi kukan sarari munyi na fili saidai bamuda tudun dafawa har Saida rayuwar wahala da garari ta aure mu kafin kawu yasake kallonmu da idanuwansa na rahama da jin qai ya zamo uba garemu,

Ya bamu uwa me qaunarmu tamkar 'yayanta iyami,


Mezamu ce arayuwar Nan bayan wahala da rayuwar garari a jininmu take shiyasa ko a gidan kawu tsanani da Matsin rayuwa be qare Mana,


Muna kwana da yunwa mutashi da ita Kuma muyi rayuwarmu,

Munshiga masifu iri iri da rayuwa ta jefamu aciki saidai Babu wani mahaluki 'daya daya taba kallonmu da zuciya me kyau 

Kowa nada buri Mara kyau akanmu Wanda ya dangantamu da irin wannan rayuwar da ake qyamarmu sbd ita,

Rayuwa ta zabar Mana gwagwarmayar samun Abinda zamucu kota halin Yaya alokacinda 'yaya kamarmu suke makaranta suna karatu shin anty zarah bawa shi yake zabarwa kansa qaddarane??


A tsawon shekarun ban bantaba Jin nadamar daukar abin waniba sai a jiya Dana jawa macen data Soni tsakaninta da Allah batareda ta hada komai daniba,


Anty zarah a shirye nake Dana bar Nan sbd zamana anan masifa zai janyo Miki ba alhe.......


Rungumeta anty zarah tayi da sauri Yana sakin sheshekar kukan datakeyi na tausayin Amatun da usman tareda su kawu dasuka taimakesu bayan Suma taimakon suke nema.


Tabbas Amatu sbd Allah nakesonki tun ranar da kikazo Nan,

Kinmin laifi Amma ban riqeki a raiba sbd sanin ajizanci irin na 'dan Adam,

A da Ina zaune dake amatsayin matar Dr dakuma Amana da aka bani Amma daga yanxu zan zauna dakene amatsayin qanwa da muka fito ciki 'daya.


Zamewa Amatun tayi da sauri tana share hawayenta ta saki qaramar dariya tanason kawar da kukan anty zarah din tace"


Anty da gaske?


'daga Mata Kai tayi tana share hawayenta itama.


Anty zarah karfa wata Rana kice aa alqawari kikamin munzama kamar ciki daya muka fiyo.


Dariya antyn tayi har lokacin hawayenta Basu Gama tsayawaba tace"


Amatu nayi alqawari ba canzawa 

Amma kema kinsan kinyi alqawari zakiban babynki idan kin haihu"" tafada cikin tsokanar Amatun.


Da sauri ta kalla Dr dayayi mutuwar zaune da tsananin so,qauna, tausayi tareda ganin girman Amatun 

Ta dafe cikinta tana cewa''


Dr kaji anty zarah Wai zamu Bata babyn.


Yana kallonta cikin tsananin shauqi yace"


Idan har kin amince zaki Bata ni Kuma idan har nine dadynsa nayi alqawari da hannuna zanbatashi.


Murmushi yasaki tana shafa cikinta ahankali tace"


Inama inada cikin wlh Dana baki anty zarah.


Qasa yayi da murya daidai kunnenta yace"


Karki damu watanni kadan ne yarage mufita wannan dilemma din zamu bawa antynki da MD baby.


Kallonsa tayi da sauri tana boye dariyarta Dan batasan yajitaba ganin yakasa daina murmushi yasata miqewa da sauri tayi hanyar dining tana cewa''


Anty zarah mijinki yagama ci muzo muyi namu party din a dining Dan wlh har yunwar jiya saina fanshe abuta.


Murmushi sukeyi suna Mamakinta ganin tabbas Bata aje al'amarin duniya a ranta sbd karta wahalar da kanta a banza sbd me gatane ke tsayawa kuka da damuwa Dan a lallashesa suda basuda ko daya sunyi futo na fito da kuka da damuwa tareda abin kunya Sam baya damunsu.

##Mamuh#ZAFAFA BIYARπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡SIRADIN RAYUWA

safiyya huguma


MIN QALB

mamuhgee


SARAN BOYE

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Pay @09033181070

Or 09032345899

[3/26, 7:46 PM] Zafafa: *_MQ 18_*

_Mg_
Koda anty zarah tace yazauna suyi breakfast tare baiso karya Mata qwarin gwiwaba amma Dole yace Mata MD yariga yafice tun dazu so karma su jirasa suyi abinsu shima bai tsayaba sbd yau umme tace taredashi zatayi breakfast ya fice ya nufi can tun kafin rashin zuwansa ya shafi Amatu Dan Babu ranarda Bata tsinewa ranar data Fara haduwa da amatun.


Shiru anty zarah din tayi a sanyaye Jin MD baya gidan ya fice.


Dafa hannunta dake zuba chips Amatu tayi tana murmushi tace"


Anty karki damu zai hakura inshallah,

Nice nayi laifin Kuma nice zan gyara

Inshallah Allah saina sa Rabin ranki ya yafe Miki Dan haka ki daina damuwa Amatu zatai Miki handling komai.


Qasa tayi da murya Yana cewa''


Saina Fara sashi yasan dawa yakeyi kafin Nan,

Shine jiya haddasa Dr ya durqusa agabansa Yana wani daddaure fuska Yana Shan qamshi to zaisan yasa Dr da anty zarah damuwa indai nice Amatu saiya sani.


Me kike cewa Amahh.


Cika baki tayi da chips da kwai tana cewa''


Bance komaiba anty zarah 

Zauna kici abincinki karki Hana kanki abinci sbd soyayya.


Zama tayi tana murmushi tace"


Amah samun Wanda kakeso yanada Dadi hardai idan shima Yana sinks,

Kinga kamar ke da Dr.


Tea ta kwankwada tana cewa''


Yanxu ni da Dr son juna muke??


Eh Mana gashinan a fili Muna gani musamman Dr bayada damuwa sai Taki,

Farin cikinki da walwalarki sune nasa

Kina gani yanda baya iya dauke Ido a kanki koyaushe kece first priority dinsa.


To ni anty banajin wainnan abubuwan da Kika fada nadai San acikin maza banida kamar su uku shi da kawu da usi,

Yanda kakejin usi hakan nakejin Dr zan iya komai Dan farin cikinsa da kula dashi.


Bakyajin faduwar gaba duk lokacinda Kika jiyo muryarsa kafin ya iso gareki??


Sake cika bakinta da soyayyan qwai tayi tana cewa''


Banaji Amma Kinga Rabin ranki Dana jiyo ko qamshin turaran Nan Masa me qarfi gabana faduwa yake sbd masifarsa.


Tsit anty zarah tayi tana kallonta kafin tasaki murmushi tana cewa''


Shikenan karki damu zankoya Miki yanda zakiso Dr matuqa kamar yanda yake sonki.


Anty zarah inason nazama wacce zata bawa Dr farin ciki da dukkanin wata soyayya..


Bazaki iya basa farin ciki ba sai kin basa dukkanin zuciyarki da soyayyarki.


Zanbasa sbd shine kadai a duniya cikin maza ya cancanci zuciyata

Koda zuciyata batasan meye so ba zanbada ita saiya koyar da ita da kansa.


Taso bawa maganganun amatu nutsuwa Amma ta watsar sbd Amatun kanta batasan abubuwan datake fadaba Dan haka ba amfanin nazarinsu.Suna Gama cin abincin Palo suka dawo anty zarah ta zauna tana waya da ummanta ita Kuma Amatu dakinta Takoma Dan watsa ruwa.


Wanka tayi ta sanya riga da skirt na atampa coffee kala ta tsaya gaban madubi Yana duba kanta tana sauke ajiyar zuciya sbd ganin Masha Allah yanxu ita da kanta sha'awar kanta takeyi sbd mulmulewa da jikinta yayi da hutu da kayan gyara jiki da fata.Akan cikinta dake shafe kamar bashi yake daukar uban kayan Dadi da abincin datake zuba Masa ba ta shafa ahankali tana gyara tsayuwa

Hakanan kawai yanxu tsananin son cikinta ya shigeta duk da tasan ana Magana ne akan Abinda Babu kwata kwata saidai ita zancen yashigeta musamman idan tayi tunanin ganin babyn a hannunta tana Masa Wasa Yana murmushi irin na Dr.


Dankwalin kayan jikinta ta zare tareda nadawa ta saka cikin rigarta daidai cikinta saita saki rigarta cikin yataso ya zauna daidai tareda qarawa tsayinta kyau sai tayi kamar sabuwar amarya me qaramin ciki

Batasan lokacinda tasaki murmushi ba tana shafa cikin saiga anty zarah tashiga tana cewa''


Amatu baki gama Shirin bane gurin Modibbo zamuje gaisuwa tunda kikazo bakije kin gaishesaba hakama umme sune fa iyayen mijinki....


Tsayawa tayi da maganar lokacinda idonta ya sauka kan 'dan matashin cikin na jikin Amatun take dukkanin farin ciki da Jin Dadinta ya fito fili ta qaraso da sauri tana cewa''


Kinga Amatu yanxu cikinki yafito sbd kinsaka riga da skirt dogayen rigunan Nan boye cikin sukeyi gaba daya..


Kallonta Amatu keyi tana murmushin ganin yanda ganin fitowar cikin kawai yasaka anty zarah wannan farin cikin to ranar da aka haifesa fa ta daukesa a hannunta.


Anty zarah Inshallah kema zaki dauki ciki ki haifi 'yayan kanki Dana Rabin ranki.


Allah yasa Amatu 

Sbd babbar adduata a yanxu shine samun haihuwa tareda MD sbd haihuwa ce kawai zanyi na tabbatarda MD ZABEERA yazama nawa,nasamu muhalli acikin zuciyarsa da rayuwarsa.Gyale coffee ta yafa akanta suka fito zuwa sashen Modibbo,


Kamar Wasa saigasu sun 'dan jima agurinsa sbd yanda Amatun ta zage tana basa labarin qanxon kurege na aurensu da Dr daya sake tambayarta,


Hakanan sai ta 'dan shiga ransa sbd Jin yanda sukayi gwagwarmaya itada mahaifiyata baba Jamila.Daganan sashen umme suka nufa Kai tsaye Amatu nata sake bude idanuwanta da zabeera din koina kallo takeyi cikin burgewa tana sake tantance asalin girma da wadatar Zabeera din.Kwankwasa qatuwar qofar shiga palon umme sukayi 

Tsawon mintuna hudu kafin me aikinta tazo ta bude musu suka shigo Amatu na santin kallon qayataccen palon da qamshi tareda sanyin AC suka cikasa.


Zama zukayi jiran saukowarta saidai shiru shiru Bata saukoba Nan Zarah da aka Kira tayi baquwa ta tafi tabar Amatu na zaman jira.


Saidata shafe awa kusan biyu a zaune kafin ummen ta fito cikin shigar alfarma tana waya Kuma dagaji da Dr take wayar sbd yanda take amsawa da Dan sauran haushinsa dabai Gama sakinta ba

Saidata shigo tsakiyar palon ta lurada  Amatu dake zaune tana kallo tana Kira ruwan lemu da aka kawo Mata hankalinta kwance Dan wuce guri da volume bai ishetaba ta dauko remote taqara tana shigaba da kallonta remote din a hannunta sai murmushin Abinda take kalla takeyi.Ko sallama da Khalil din batayi ba a wayar ta kashe tana cewa"


Uban waye zaune har cikin palona?


Juyowa Amatu tayi tana aje cup din hannunta da murmushi Kan fuskarta tace"


Haj Mama nice Amatu matar khalil nasan zuwa yanzu kinmantani.


Cikin quluwa ta daka Mata tsawa tana cewa"


Uwar matar khalil din ce ba matarsa ba

Zoki fice kafin nasa kiyi nadamar zuwa Nan.


Matsowa Amatu tayi da sauri gabanta tana cewa''


Umme Dan Allah kiyi hkr da Abinda yafaru ba laifina bane bakuma laifin Dr bane qaddarane Kuma nidai na karba qaddarar nan da hannu biyu ta zama matar Dr wlh inaso.....


Ganin tafara loosing patience dinta batason tayiwa Amatun komai yanzu sbd tanadin datai Mata tukuna shiyasata fixgota a wulaqance ta jeho ta waje daidai isowar Nuratu  wajen ta tareta daga faduwar dazatai saidata dago taga Amatu ce aikuwa ta saketa amatun tayi muguwar faduwa akan hannunta na dama take ta samu kurdewar qashi tasaki wani razanannen ihu tana qoqarin tashi Amma takasa dafawa sbd azaba take wani zufa ya karyo Mata ta kalli Nuratu a masife tace"


Ita waccan data jeho ni nasan dalilinta kekuwa da kikaimin haka meye naki dalilin??


Dalilina shine cikin jikinki""tafada cikin tsananin tsana da takaicin ganin cikin jikin Amatun.


Miqewa tayi da qyar tana dafe hannun cikin azaba tace"


To ke meye ruwanki da cikina kokuwa kema cikin 'yan koren uwar Mijina ce sbd dai bakida alama da 'yan zabeera daga Ina malama???


Baqin ciki maganar Amatun tai Mata tana sake quluwa tace"


Ni ba matsiyaciya bace kamar ki wadda Babu Wanda yakeda tabbacin ba karuwa bace Khalil ya fada tarkonta ta auresa sbd kudi 

Wama yakeda tabbacin wannan cikin nasane Kona wani qa........


Wani gigitaccen Mari ya sauka akan fuskar Nuratun dayasa gefen bakinta 'dan fashewa 

Ta dago da sauri tace"


Ni Kika Mara???


Zuciya data gama ciyota kukan kura tayi tai Kan Amatun zata mareta aka riqe hannunta ta bayanta ta fizge zata Kuma Yi Kan Amatun ya sake riqe hannunta tareda zagayo gabanta kyakkyawar fuskarsa ta jinin zabeera tana fidda sheqi 

Tace"


SALMAN????


Sakeni,

wlh saina koyawa wannan mummunar karuwar hankali..


Saukar wani Marin ne a fuskarta yasata qarasa zaucewa tana qwacewa tace"


Wlh yau sainaga ubanda ya tsaya wannan tinkiyar...


Sakinta Salman din yayi tareda kallon Amatu da mamakinta yagama kashesa yana cewa"


Lallai Nima zanso ganin Wanda take dashi daya Bata wannan qwarin gwiwar me ban mamaki da burgewa 

Ina buqatar saninsa Dan basa jinjinawa ta musamman.


Kallonsa Amatu tayi ganin Yana qarawa wutar masifar fetur tace"


Amatu itace tsayayyiyar kanta Bata buqatar tsayawar wani gurin nunawa  kowa matsayinsa,


Ki zauna ki nanatawa tosashiyar qwaqwalwarki ni Amatu nariga Masha gabanki 

Idan har akwai Amatu har abada Dr khalil zabeera bazai taba kallonki ba

Kai da kake Dan uwanta saika taimaka Mata gurin fahimtar hakan 

Amatu ba tsarar yinki bace.


Tana Gama fadar hakan ta wuce Yana shafa cikinta Dan qara qular da Nuratun 

Cikin mugun baqin ciki da takaici nuratu ta juya a zuciye tabar gurin tana fidda huci kamar zuciyarta zata tarwatse idanuwanta har wani cikowa da hawayen baqin ciki suke 

Dama can Kuma halinta ce saurin fusata.The great ORTHOPEDIC Dr Salman zabeera kuwa gabaki daya Amatu tagama basa mamaki lokaci daya da burgesa sbd sanin darajar kanta datayi takuma nuna batareda tsoro ba,

Koma wacece Amatu shi tagama burgesa shiyasa yakasa dauke Ido daga kanta harta bace.


SARAN BOYE

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Pay @09033181070

Or 09032345899[3/28, 11:48 AM] Zafafa: *_MQ 19_*
*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*


*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*


*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*


*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*πŸ’†πŸΎ♀️πŸ™ŽπŸ½♀️


*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaΙ—a ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*πŸ‘―πŸ½♀️πŸ‘―πŸ½♀️


*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*

*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*


*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*


*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*


*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*🀞🏾🀞🏾🀞🏾🀞🏾
**********

Doguwar tafiya tayi har zuwa sashensu tana Jin tsananin azabar radadin da hannunta keyi ta daure ta iso tana rintse ido cikin uwar azaba ga zufa sai karyo Mata yake shiyasa tana isowa tun a Palo ta zube Kan kujera tana kallon hannun da harya Fara kumbura

Sanin anty zarah na dayar palon tareda baquwarta yasa ta sulala tayi dakinta ta kwanta Dan kada ta dagawa anty zarah din hankali saidai ita kadai tasan uwar azabar datake ciki shiyasama takira usi 

Yana daga wayar sai alokacin taji hawaye sun ciko idanuwanta sai Kuma takasa mgn ta kashe wayar ta ajiye tana gani yanata Kira takasa dauka sbd karta daga Masa hankali kawai.Duk yanda take tunanin zata iya riqe ciwon takasa sbd sosaine tasamu gocewar qashin hannun sai kumbura yakeyi har takai tafara kasa motsasa sbd tsamin daya dauko.


Har dare tana dakin Taki fitowa sai bayan magrib baquwar anty zarah ta tafi 

Itama anty zaran dakinta ta nufa sai datayi sallar magrib da ishai tukuna ta fito palon saidai rashin ganin amatu a palon yasa ko zama batayiba ta nufi dakinta.


A kwance ta taddata Idanuwanta a rufe tanajin anty zarah din ta tashi zaune tana rintse ido alamar ciwo 

Nan anty zarah din ta qarasa bakin gadon da sauri tana dafa Hannun me azabar Bata saniba 

Wani irin zabura Amatu tayi cikin tsananin radadin dataji tana tana cewa''


Anty hannuna ya karye.


Da sauri anty zarah ta kalli hannun batasan lokacin data zaro ido ba ganin ya kumbure sul a rude tace"


Amatu meye wannan nake gani?

Garin Yaya hakan yasame ki??


Sai alokacin hawayenta suka gangaro tace"


Anty wannan me son Dr din ce ta tureni na Fadi a hannun.....


Mene??""anty zarah tafada da qarfi tana maida kallonta Kan cikin Amatun da har lokacin Bata cire cikonba tace"


Ta ture ki batada hankaline bataga Abinda ke jikinki bane ko so hauka ne Bari nakira Dr yanxun Nan yazo 

Ita Kuma Nuratun I will deal with her later wannan ai ganganci ne.


Dr najin Abinda yafaru hankalinsa ya tashi gashi wani mahimmin meeting sukeyi sbd gobe shida wasu manyan likitocin asibitinsu zasuyi tafiya zuwa china gurin wani program na sati biyu.


Tunda zarah takirasa tafada Masa hankalinsa ya rabu biyu 

Meeting din kawai suke Amma Rabin hankalinsa na gidan sanyi daya dayakeji aransa shine SALMAN yananan yadawo kwararren likitan qashi ne yasan basa buqatar zuwa koina.


Sai guraren 8:40 suka fito gashi Kuma yanada wani Wanda yayiwa alqawarin ganinsa idan yafito hakanan yakoma office dinsa

Koda ya Isa office din mutumin na kiransa Nan suka Fara mgnar dazasuyi ahankali yanayi Yana shafa qirjinsa da numfashinsa ke Dan sauyawa tun safe yakejin hakan Kuma yasan alamace ta ciwonsa zai iya tashi ko wane lokaci Amma meeting din yasa baisamu damar amfani da inhaler gashi idan yataso duka Dole saidai oxygen Wanda duk lokacinda aka saka Masa oxygen rayuwarsa tana cikin mugun hadari ne sbd oxygen din nabawa lungs dinsa matsala sbd dama can basuda qarfi lungs din tun haihuwarsa shiyasa shida likitocinsa sunriga sunkai qarshe akan karya taba Bari ciwonsa natashi gaba daya harya tafi qarfin inhaler ta riqesa.Qoqarin Kama numfashinsa dake son qwace Masa yakeyi Yana dagawa mutumin Kai sbd Magana tafara son gabatarda ya dago daqyar ya kallesa Yana dannewa yace Masa yaje zai nemesa idan yadawo daga tafiya zasuyi Magana.


Mutumin na fita ya dafe qirjinsa cikin tsananin azabar rashin fitar numfashi idanuwansa sunyi jajir jijiyoyin kansa sunfito sosai 

Hannunsa na rawa ya jawo drawer office din nasa ya Fara laluba baiji inhaler dinsa ba,

Firfito da duka kayan ciki yayi Yana watsowa cikin sauri da tsananin azabar dayake ciki baiganta ba gashi yafara loosing control din kansa sbd idanuwansa sun Fara gani dishi dishi

Da sauri ya miqe ya dauki wayarsa da keys din motarsa ya fito Yana riqeda kurkinsa ya nufi motarsa ya fada Yana tayarwa yafito asibiti saidai abin yaci qarfinsa gaba daya zuwa lokacin sbd numfashinsa daya dawo gaba daya bakinsa tuni motar tafara qwace Masa.Daga government house yafito daga wani guntun meeting dayayi da deputy governor akan investing dasuke sonyi a sabon ZABEERA LTD dinsa dake Bangkok,

Shida malam Umar ne a motar shike tukasa 

Gaba daya hankalinsa nakan wayarsa dayake duba tarin misscalls din da akaita Masa Wanda duk yawanci daga  mutanen hurdarsa ne sai sauran daga family wainda yasan dukansu bazai wuce buqatar kudi daga garesaba Wanda Sam shi ko mamakinsu baida lokacin tsayawa yayi 

Misscal din zarah guda hudu ne ya kalla numbernta dayayi saving da ZB wato zarah zabeera,

Sam Bata gajiya da Kira ita duk da tasan bako yaushe yake dagawa Amma Sam taqi sabawa da hakan 

Wasu mutanen suke aikata Abinda zai 6ata ransu,

Abinda tasani ya koya a rayuwarsa shine kayi rayuwa akan mizanin dazai baka nutsuwa da ease 

Baya tunanin har abada zai iya jefawa ko Kai kansa ga Abinda zai baqanta ransa ya Bata Masa Rai yayi iya qunci da baqin cikin dazaiyi tun Yanada quciya Dan haka wannan babin na damuwa akan alamarinda wani zaisaka ya Dade da wucewa agurinsaMD ga wannan kamar motar Dr khalil ce Kuma kamar dai ba lafiya ba Dan.....


Bai qarasa yayi saurin over taking motar Dr din sbd wani junction dazata nufa ta buga.


MD din ne da kansa yafito ya nufi motar Yana budewa idanuwan Khalil din na qoqarin rufewa da zafin nama ya fizgosa daga cikin motar tareda taimakon malam Umar suka kamasa zuwa motarsa da kansa ya qara sanyin AC din motar tareda fitowa cikin sauri ya zagaya ya bude gaba cikin sauri yabude can qarqashin sit din driver saigashi yaciro inhaler da sauri ya zagayo ya dago Kan Khalil din Yana shaqa Masa Amma Ina Sam ko Shiga batayi sbd numfashinsa ya tsaya gaba daya.


Kasa mgana yayi yafito idanuwansa na sauya ya karbi mukulli hannun malam Umar ya zagaya ya figi motar cikin mugun speed din dayasa Mutanen gurin watsewa da sauri sbd gudun tsautsayi shikuma Mal Umar yashiga motar Dr din yaja yabi bayansu.Zabeera ya nufa Kai tsaye

Securities suna hango motarsa da yanayin da yake tahowar cikin speed yasasu saurin wangale Masa makeken gate din da mutum uku ne ke iya rufesa

Yana isowa yashige gate din Yana qara gudun motarsa yabi bangaren dama inda tacan gefen hanyar zuwa part din Khalil din yake.


Yanayin parking bakin part dinsa yafito ya nufi wata qatuwar flower vase dake bakin qofar shiga palonsa inda anan yasan Khalil din na aje keys dinsa.


Ya a budewa da bedroom dinsa ya nufa Kai tsaye sbd yasan inda allurar take 

Tun daga cikin dakin ya hadota yadawo motar Yana shiga ya daga hannun Khalil din ya soka Masa tareda dannata da sauri ruwan suka shige jikinsa take yayi wani irin yunquri tareda Jan numfashi me qarfi da qara kafin jikinsa yakoma yasaki.


Sai alokacin MAHMOUD ya sauke ajiyar zuciya Yana 'dan dafe goshinsa tareda lumshe fararen idanuwansa dasuka sauya kala.,


A duniya idan akwai mutum daya dazai iya sadaukarwa Koda rayuwarsace to shine Khalil,

Khalil ne kawai weakness dinsa a duniyar Nan sbd shikadai ne yake shiga tashin hankali akansa aduk lokacinda yaga ciwonsa yatashi sbd hakan na razana jarumtarsa Dan Khalil shine mutum na qarshe dayake baya iya tunanin ma rasawa,

A rayuwarsa he has only two dear ones,

Na farko mahaifiyarsa da har yanzu take cikin qasan ransa daya kasa cire kewarta,

Sai na biyun shine khlail,Wanda bayada wani Dan uwa dayake gani amatsayin jininsa kamarsa.

Tsananin mataki da kulawar daya daukarwa ciwon Khalil din yasa dukkanin motocinsa da office dinsa yanada ajiyayyar inhaler dayake ajewa sbd Khalil din Dan Koda ta kwana irin haka.Ahankali yaji an dafa hannunsa 

Saida yaqara rinste idanuwansa yasaki qaramin numfashi kafin yabudesu akan hannunsa da khalil din ya dafa a wahalce.


Kallon fuskarsa Khalil yayi tareda sakin wani wahalallen numfashi ganin duk duniya idanba ubangiji daya halacci MAHMOUD din ba Babu me iya gane kowane yanayi na MAHMOUD da Abinda yake ciki sbd fuskarsa Bata taba nunawa,farin ciki ko akasin hakan.


Kallonsa yayi da jajirtaccin idanuwansa cikin nutsuwa yace"


Koma me kake tunanin kanayi zaifi idan kadawo kanka,

You know this is stupidity right??

Menene amfanin aiki da gwagwarmayar idan Babu lafiya you better come back to your damn senses.


Girgiza Masa Kai Khalil yayi tareda qoqarin fitowa motar Amma bazai iyaba sbd jikinsa ba qwari Dole MAHMOUD din yakamasa suka fito yakaisa har cikin bedroom dinsa kafin yayi amfani da wayar khalil din yayiwa umme txt akan bayajin Dadi.


Harzai juya ya fice Khalil din ya riqo hannunsa Saida ya fidda numfashi ahankali na marasa lafiya kafin ahankali ya furta"


Thank you.


If you want to thank me be careful about your health,

Next time idan kayi Wasa irin haka yafaru ka shirya rabuwa Dani sbd i can't take this stupidity,

U're unbelievable Khalil 

Kana likita Amma Kaine kake Wasa da lafiyarka har kake tunanin yin tukin mota cikin wancan yanayin,

Menene cikin kanka dayafi kula da lafiyarka mahimmanci????


Amatu.


Tsit MAHMOUD yayi sbd Jin zancen na Khalil a bazata.


Kallonsa yayi cikin zallar mamakin irin like seriously??


Lumshe ido yayi Yana sake maimata sunan Amatun a gajiye

Yadora da fadin"


MAHMOUD wallahi Amatu itace tunanin kulawa da ita yafimin lafiyata,

Acikin yanayin danake ciki Babu Abinda nake tunanin cimmawa kamar na iso gida gareta sbd tana cikin halin buqatata akusa,

Banajin yanayina kawai Abinda nakeso na iso gida alokacin.


Zame hannunsa MD yayi tareda miqewa Yana qoqarin barin gurin sbd idan baiyi nesa da Khalil ba tsaf zaisa a binciko Masa the best psychiatrist Dr taduba Masa shi.


Tashi zaune Khalil din yayi cikin dasasshiyar murya yace"


Amatu amanata ce idan kana qaunar 'dan uwanka zaka kulamin da ita aduk lokacin da bana kusa 

Shine kawai Abinda nake roqanka a matsayin alfarma ta har iya rayuwa.


Cak ya tsaya tareda kasa juyowa zuciyarsa na juya Abinda Khalil din yafada Wanda yasashi Jin wani iri saidai kawai ya wuce batareda ya juyoba Kuma baice kala ba ya ficewarsa daidai isowarsu umme tareda Nuratu da tuni hankalinta yayi mugun tashi Jin Khalil dinta bayajin Dadi.
Zaune zarah take a Palo tana jiran isowar Khalil din sbd tayita kira daga bayan nan wayarsa a kashe 

Allah ma yasa Amatun tasamu bacci ya 'dan dauketa.


Yana shigowa ta dauka Khalil dinne tayi saurin miqewa zatai Magana saitaga MAHMOUD ne fuskarsa daukeda wani yanayi na kasala da sauri ta qaraso gabansa tana cewa"


Sannu da dawowa¿


Kallonta yayi tareda kallon agogon dake palon yasake maido da idanuwansa kanta yayi Mata kallon minti biyu cif ahankali ya daga Mata Kai alamar amsawa cikin sautinsa me sanyi yace"


Haryanxu kina zaune a Palo

Akwai matsala ne?


Kallonsa tayi wani irin sanyin Dadi na kwaranya cikin zuciyarta harsaida murmushinta ya bayyana ta kalli cikin idanuwansa ya dauke Kai sbd Sam bayason ana kallon cikin idanunsa ahankali tace"


Dr nake jira nakirasa tuntuni yanzu Kuma wayarsa akashe 

Amatu ce ba lafiya taji ciwo sosai a hannunta.....


Cak ya tsaya daga tafiyar dayakeyi batareda ya juyoba saikuma ya tafiyarsa Yana cewa'"


Shima bayajin Dadi bazaiso damuwa ba yanzu shima Kuma gobe tunda safe zaiyi tafiya so just handle her situation for him.


Wucewa yayi yabarta tsaye dafe da goshin tunanin mafita da abin Yi.


Ganin Amatun tasamu bacci haka ta lallaba itama taje ta shirya tayi dakin MD din saidai duk Rabin hankalinta na qasa gurin Amatu.
Dr Khalil kuwa asubar farko lafiya kalau yatashi da qarfinsa kamar baisamu attack din ba ajiyan,

Qarfe Bakwai na safe jirginsu zaitashi Dan haka qarfe shida da rabi yafito a shirye driver din umme zai kaisa airport

Yaso ganin Amatu Amma yasan lokacin Basu tashi ba hakanan ya hakura ya wuce bayan yayiwa zarah text tareda transfer din kudi masu kauri na kulada duk Abinda amatun ke so kafin sati biyun yadawo,

Hakama bai wuceba Saida yayi Magana da Salman akan zaije yaduba Amatu yasan matsalarta da Abinda za'ayi Mata.

Tun qarfe hudun asuba ta tashi tayita juye juyen azaba tun tana daurewa harta kasa tafara hawayen azaba tana juye juye Dan haka Koda gari ya waye anty zarah tashigo tuni idanuwanta da fuskarta sungama kunburewa sbd kukan azaba aikuwa tana ganin anty zarah din ta sake sabon kuka 

Da sauri zarah ta rungumeta tana rarrashinta da Mata sannu kamar zatayi kuka.


Hannun har wani qyallin kumburi yakeyi shiya qara daga hankalin zarah ta kamota suka fito Palo tana cewa'' 


Dr yayi tafiya Bari nafadawa MD zamuje asibiti.


Tana qoqarin juyawa saiga qwanqwasa qofar Salman tareda usi bayansa Wanda Dr khalil ya roqesa akan yadaukosa aje dashi yaduba Amatu sbd tun jiyan data kirasa taqi Magana hankalinsa yake atashe.


Aikuwa amatu na ganinsa tasaki sabon kuka 

Da gudunsa yayo gurinta hankalinsa a mugun tashe Yana cewa''


Amatu??


Zama yayi kusa da ita Yana kallon hannunta sai kawai yaji shima idanuwansa sun ciko da hawaye kamar mace saigasu suna gangarowa.Dr salman zabeera sai suka basa dariya ya zauna Yana duba hannun Yana cewa"


Zarah kina ganin mutuniyarki tasa oga Usman kuka saikace ba namiji ba,

Usman dama jarumtar taka a baki take kenan.


Matsa hannun nata yayi da qarfi take tasaki wani razanannen ihu tana damqe hannun dataji akusa da hannunta dake Kan hannun kujera


Shikuma da saukowarsa kenan basusan dashiba ba yazo wucewa yaji an damqe hannunsa ya tsaya cak batareda ya juyoba sbd ko bai juyoba yasan itace sbd zafin ciwo ta riqesa batareda tasani ba 

Saidai Kuma samun kansa yayi da tsayawa batareda ya qwace hannunba  yana gane radadin datake ji ta hanyar yanda ta mugun matse hannunsa.

##mamuh#
ZAFAFA BIYARπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


SIRADIN RAYUWA

safiyya huguma


MIN QALB

mamuhgee


SARAN BOYE

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Pay @09033181070

Or 09032345899

[3/29, 11:34 AM] Zafafa: *_MQ 20_**_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*


*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*


*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*


*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*πŸ’†πŸΎ♀️πŸ™ŽπŸ½♀️


*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaΙ—a ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*πŸ‘―πŸ½♀️πŸ‘―πŸ½♀️


*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*

*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*


*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*


*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*


*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*🀞🏾🀞🏾🀞🏾🀞🏾

*************

Jin mutum ta bayansu a tsaye yasa anty zarah Dan dagowa tana qoqarin juyawa Amatu tasaki wani sabon ihu dayasata dawo da kallonta Kan Salman cikin damuwa da tausayin Amatun tace"


Salman please ka danyi Mata ahankali kodan juna biyun jikinta.....


Daga salman din har MD cak tunanin kowannensu ya tsaya da maganar da Zarah din tafada,


Zame hannunsa yayi da sauri tareda barin gurin kansa na Dan sarawa sbd ihunta daya cika part din gaba daya,

Yana fita qofar gym dinsa dake maqale data shigowa palonsu yashiga Yana qoqarin clearing mind dinsa da cewa''


Khalil wane irin shirme kasani aciki¿¿

Matarka ce and she's pregnant....

MAHMOUD just stay out of this.


Geamin din dayazo Yi yafara Yana komawa asalin MD ZABEERA dinsa.


Salman kuwa shiru yayi Yana nazarin kalmar a cikin kansa duk da dai ba yanzu ne yasani ba tun kafin yadawo Nuratu ta sanar dashi komai 

Kawai abin rudewar anan shine shedan dake saka Masa wasi wasin hakan sbd Amatun data shiga kansa hakan kawai yake jin bazai Bari Nuratu ta cutatar da itaba Koda Bata ciki,

Abu daya daya sake tsaya Masa arai shine Sam idanuwansa da iliminsa na likitanci duk da bana mata ba sun kasa gasgatar Masa da akwai ciki a jikin Amatun.


Kallon fuskarta yayi ahankali yasaki murmushi ganin hawaye shabe shabe a fuskarsu su duka ukun,ita da usi harda anty zarah din ma.


Handkerchief dinsa dayake daukeda tambarin asibitinsa da sunansa ajiki yaciro daga aljihunansa ya miqawa usi yace"


Usman share Mata hawayenta.


Daqyar da fitina da koke koke ta ihu da komai aka dubata yasa Usman yaje motarsa ya dauko wasu magunguna da allurai yayi Mata da kansa yabata maganin Yana Mata sannu tareda tsokar yanda idanuwanta suka kumbura sbd kukan raki.


Saidata ci abinci da sauran maganin yaga anty zarah takaita daki ta kwanta tafito tace Masa tayi bacci kafin yatashi suka fito tareda usi dakejin kamar karya tafi yabarta ta bangare daya Kuma kallon koina yakeyi Yana jaddada daula da dukiya irinta wannan ahalin zabeera.


Sashen Salman din suka nufa cikin motarsa sbd kowane sashe zuwa sashen akwai 'yar tafiya shiyasa duka yawancinsu da motacinsu suke zuwa sashen juna sai dai idan kaso motsa jiki kaje da qafa.


A palon Salman din suka zauna Nan USI yaqara ware Ido Yana kalle kalle badan yayiwa Dr khalil alqawarin bashi ba abin wani har abada ba da yau Allah ne kadai yasan abubuwan dazai sanfe daga cikin zabeera dinnan Dan tun a part dinsu anty zarah yaga abubuwan dauka Amma hakanan ya hadiye ya dauke Kai sbd karya kunyatar da Dr khalil.


Abinci lafiyayye aka aiko daga part din mahaifiyarsa Haj Maryam aka jera Masa a dining suka zauna ci shida usi dasukai sabo cikin qanqanin lokaci sbd gano tsananin qauna da kulawa dake tsakaninsu shida Yar uwarsa Amatu.


USI na Ido biyu da kayan Dadin dake jere a dining din take yaji hakurinsa na Kama mutuncin Kai ya qare take ya washe baki Yana cewa''


Allah ya taimakeni saura kadan yau nadauki azumin alhamis da Dr ya doramu akai nidasu kawu 

Kawuma yau dayaji Dr yayi tafiya wlh win dauka yayi yace mu huta kwana biyu kafin Dr din yadawo sbd duk litinin da alhamis taredamu yakeshan ruwa acan gida.


Dariya sosai Salman yayi Yana sakejin Usin na burgesa sbd baya boye boye yace"


Kace yau dai akwai ciye ciye sai ciki yakasa dauka.


Lumshe ido USI yayi bayan yazuba kakkauran soyayyan kwai cikin bakinsa dayaji kayan qamshi da albasa take yasaki murmushi Yana sakawa Dr khalil da adduar samun nasara a rayuwa Dan komai suke samu a rayuwa sbd shine

Yagama Basu duk wani Abu da suka kasa samu a rayuwarsu ta kadaici, talauci,garari da rashin sanin daraja.


Sosai salman yaji tausayi da qaunarsu tareda son samun Lada da adduar da Dr khalil ke samu daga garesu sbd kyautatawa da kulawar dayake Basu amatsayinsu na wainda basuda shi,


A iya firar da yayi da USI ya fahimci su din talakawane masu tsananin buqatar taimako Wanda yasa Dr Khalil shigowa rayuwarsu ya taimakesu har suke ganinsa a Wanda yafi musu kowa da komai,

Idan baiyi kuskuren tunaninba yanasa ran sbd tallafawa rayuwarsune yasa ya auri Amatun batareda sanin iyayensu ba,

To Amma Kuma a yanda labari yazo a zuwan Amatu zabeera ance batada mahaifi ita din marainiyace,

To shi kawu waye tunda ba'a ce sunada kawun ba a takaice cewa akayi basuda kowa,

Gashi yanzu yanatajin sunan kawu a bakunansu,

Da akwai inda wani Abu ya maqale to,

Akwai Abinda dagasu sai Dr ne suka San abinsu koma dai menene yasan Dr khalil ya boye ne sbd wani dalili me kyau.


To gashi shima Amatu da USI sunshiga ransa alokaci daya,

Yaji yanason kasancewa acikin farin ciki da walwalar da Amatu da ahalinta zasu samu.


Bayan sun Gama cin abinci shigewa yayi ya kwanta yabar USI yanata faman kallon wani action film Yana cin wani lafiyyan dabino me laushi daya Gama daukan sanyi a fridge.


Sai azabar salman din yatashi bacci zuwa lokacin shima usi ya Dan miqe a kujera yayi baccinsa sanyin AC na hudasa hankali kwance.


Tayar dashi salman yayi tareda nuna Masa dayan bedroom dinsa yace yaje yayi wanka zai kawo Masa Kaya.


Dakinsa yakoma ya hadowa usi din manyan kayansa designers masu kyau da tsada kusan kala shida da takalma na alfarma da agogai ya hado Masa tareda wata qaramar akwati yasa aciki yakawo Masa

saiga usi yayi wanka ya shirya tsaf cikin qananan kayan dasuka fiddo da ma'anarsa da kyawun dayake dashi shima hardasu feso turaren da duk ya shaqa a jikinsa saiya saki murmushi abinsa Yana sake godewa Salman da yiwa Dr khalil addua.


Dasuka fito Saida suka koma yasake dubo Amatu zuwa lokacin har ta tashi bacci itama tayi wanka taci abinci tasha magani tana zaune Palo anty zarah na gefenta tana miqo Mata yam balls datasa akai Mata tana ci tana tunanin Dr Khalil da har lokacin basuyi Magana ba.


Kwankwasa qofa akayi hafsatu tazo daga kicin tabude suka shigo suna yar fira kamar wainda sukai shekaru atare duk da Dr salman ne me jan usi din da firar sbd yasake sosai dashi Dan dama can shi Dr Salman yanada Magana sosai da son raha da Wasa.


Tunda taga USI da kayan dake jikinsa ta sake baki tana kallonsa cikeda mamaki tana cewa''


Usi a Ina ka......


Da sauri yace"


Dr Salman ne ya......


Katsesa shima Salman din yayi da cewa"


Wai Kai itace yayarka ko Kaine yayanta da kake Jin shakkarta ne.,


Sosai Kai usi yayi Yana murmushi yace"


Dr bakasan Amatu bane da zafin Rai yanzu Nan saitace zata fasamin Kai ko baki.


Dariya Dr da anty zarah suka sake 

Anty zarah tace"


To lallai Nima naji tace zata fasa maka Kai da baki yafi so goma Amma bantaba ganin anyi ba.


Kallon Amatun usi yayi Yana cewa'


Anty zarah dafa tanayi yanxune anan batama ganni ba bare tayi 

Amma ada tsaf zata saka wata Jakarta me kama data wanzamai ta kwadamin akai ko baki 

Jakar Nan yanda kikasan da qarfe akayita tsabar qarfi.


Dariya duk su duka suka sake sosai hadda hafsatu dake jera abincin Rana a dining 

Itama Amatu dariyar tayi tana cewa''


Usi tashi kabar Nan kafin na fasa maka baki wlh...


Kinji ko anty zarah tasake fada

Ai a yini tana cewa zata fasa bakina da kaina yafi so ashirin

Kawu ne duk ta fada sai yayi sadakar ruwa wa qadangaru su Sha Wai yana fidda Mata baki kada fada Babu cikawa ya fado Mata.


Filon kujerar datake ta dauka ta jefa Masa da qarfi tana cewa''


Kamar anyi a kunnen kawu 

Kuma Allah saina fadawa Dr yau bakayi azumi ba dan Banga alamarsa atare dakaiba yanda nasanka kamar mace da mugun Jin azumi.


Kallonta yayi da sauri kafin ya kalli Dr Salman yana Dan nutsuwa yace"


Idan Kika fada Masa to kisani banine kawai banyiba 

Kawuma ya ajiye yace wlh saiya huta.


Zaro Ido tayi itada anty zarah tace"


Kawu ma ya ajiye?


Eh Mana iyami ce kawai ta dauka abinta sai kwadayayyun gidan dasuka Saba duk akayi ana raba musu abubuwan abinci basusan yayi tafiya ba sunacan duk sun dauka.


Shiru Amatu tayi tana sakin murmushi kewa da tsananin qaunar Dr khalil da girmansa na sake cikata sbd ya kawowa gidansu rayuwa me inganci da samun tsira,

Duk litinin da alhamis yakeyin azumi harya koyawa su kawu 

Suma sauran Yan gidan tuni suka dauka sbd duk litinin da alhamis din Yana kawo kayan abinci a raba gidan Dan Shan ruwa Wanda wasu suna musu kwana biyu Basu qareba,


Da farko sbd samun kayan dayake kawowa suke azumin Amma yanzu kusan dukkaninsu abin yafara zama jikinsu Kuma kowannensu yasha ruwa takanas sukewa Dr khalil adduarsa ta daban sbd yakawo sauyi da walwala a rahuwarsu gidan gaba daya.


Anty zarah ma cikin jinjinawa Dr khalil tace"


Allah ya biyawa dr buqatocinsa na alkhairi sbd wannnan aikin ladar dayayi.


Amin Amatu tace tana kallon Dr Salman dashima yaji yana sake ganin girman Dr khalil zabeera tareda yiwa kansa kwadayin Lada da kyautawa su Amatun.


Anan sukaci abincin Rana taredasu Amatu kafin suka fito suka wuce Salman zai maida usi gida.


Bayan tafiyarsu cikin kulawa anty zarah tace"


Nagode Amatu.


Juyowa Amatu tayi ta kalleta cikin rashin fahimta tace"


Anty zarah me akayi?


Murmushi tayi tana kallon Amatun gaba daya tace"


Amatu kinkawo dariya da walwala acikin rayuwar kadaicin Dana samu kaina acikin gidan nan,


Tsawon shekarun aurena Banda ranar Dana taba zaunawa acikin gidan nayi fira nayi dariya harda qyaqyatawa saida Kika shigo cikinsa,

Banda abokin fira,abokin nishadi acikin gidana,

Maimakon nakawo sauyi da walwala acikin gidan Nan da rayuwar MD sai Nima kadaici da rashin walwala da rashin farin ciki suka aureni sai gidan yaqarasa zama cikin duhun dayake ciki tuntuni.,


Amma zuwanki amatu yakawo walwala da annushuwa acikin gidan Nan Wanda ko hafsatu datake amatsayin me aiki na hango walwala atareda ita bayan zuwanki cikinmu

Shiyasa nake Miki godiya sbd ko ahaka kin shayar damu yanda walwala da nishadi sukeda Dadi a rayuwa.


Murmushi tasaki tana gyara zama tace"


Anty zarah banbaki kwatan Abinda kikamin arayuba,

Kin qaunaceni a yanda nake Kika Kuma karbeni hannu biyu bayan kingama sanin waceceni,

Kinbani matsayin qanwa kamar ta jini bayan baki hada komai Dani wannan shine babbar kyautar Dana samu a rayuwata ta samunki keda Dr khalil,


Dr khalil shi yariga yazama wani jigo atare Dani da bazan iya Babu Shiba Wanda nake fatar dagake harshi mutuwace kawai zata rabamu,


Farin ciki Kuma Babu Wanda yake bawa wani farin ciki a rayuwa sai Allah saikuma Kai da kanka idan ka ture komai ka bawa kanka mahimmanci,


Anty zarah kece da kanki zaki kawo walwala da sauyi a gidan aurenki idan kinso,

Bansan meye zaman aureba tunda banzauna da Dr ba saidai ni nawa tunanin daga lokacinda Kika auri mutum to duk mulkinsa da dukiyarsa da muqaminsa da duk wani Jin kansa to fa anzama daya 

Idan bai aje Dan kansa ba ke zaki aje masa,


Anty zarah kinsa tsoro da shakkun mijinki fiyeda sonsa acikin ranki Wanda shike sa kiga an tsufa da jikoki da 'yaya da komai saikiga mace mijinta na Mata fada ko dixgawa a gabansu Wanda ita ta daukar Masa hakan tun anada kuriciyar aurensu.,


Mijinki mijinkine baida wani suna bayan wannan hakama kema bakida wani suna bayan na matarsa ko bayaso Dan haka anty zarah ki aje tsoro da shakka ki gyara rayuwar aurenki sbd bazan zauna Nan dakuba dazanta kawo dariya a fuskarki kece zaki kawo dariya a fuskarki data mijinki,

Dan haka Dan Allah anty zarah ki gyara sbd kada lokaci ya qure Miki.


Zugum tayi tana sauraren Abinda Amatun ke fada tanajin kamar da wuya al'amarin.


Murmushi Amatu ta sake tana cewa''


Anty zarah tunanin me kikeyi?


Miqewa tayi tana cewa''


Sam ni Banga abin tsoro ko shakku ba  agun Rabin ranki a takaice ma ni tsaf zan gyare Miki zamansa matsalar da aka samu itace ni ko qamshinsa na jiyo gabana faduwa yakeyi sai naji zuciyata tana bugawa da sauri kamar zata fito daga qirgina,

Idan na kalli fuskarsa kuwa rasa nutsuwata nakeyi,

Bansan meyasaba shikadaine nakejin hakan akansa,

Shi kadaine bana iya yiwa fuskarsa kallo biyu sbd dukan da zuciyata takeyi,

Meyasa idan.........


AMATULLAH"""yakira sunanta gaba daya batareda yasan yayi hakan ba sbd zantukanta dake juya kansa da tunaninsa....


Juyowa sukayi su duka hadda anty zarah datai qaramin suman zaune Jin abubuwan da Amatu ke fada akan MD Wanda idan shedan ya Rudi fahimtarta to zata ce ne wannan so ne me zafi.....


Saurin girgiza kanta tayi tana Dan bugawa tace"


Tunani ne 

Amatu matar Dan uwan MD ce

Tanama daukeda cikinsa

Bazata taba son wani ba bayan Dr khalil bare Dan uwansa MAHMOUD tunanin banxana ne kawai.


Ganin Dr Salman ne yakira sunanta yasa anty zarah sakin ajiyar zuciya a boye 

Ita Kuma Amatun murmushi ta sakar Masa tana cewa''


Harka dawo¿


Gabaki daya kansa juyawa yakeyi Wanda hakan har akan fuskarsa ya nuna confusion sai kawai ya miqa Mata ledar hannunsa daya siyo Mata tarikicen kayan chocolates dasu cookies ya juya baice ko kala ba.


Yana fita Saida ya zauna cikin motarsa ya yamutsa kansa Yana cewa''


Amatu MD ZABEERA takeso bayan tana matsayin matar khalil zabeera kokuwa kansa ne bai fahimci yanda abin yakeba????


Kasa yadda yayi yaja motarsa yana qoqarin yakice tunanin dama duk Abinda kunnuwansa sukajiyo Masa.Bayan fitarsa kuwa cikin farin cikin abubuwan daya kawo Mata din tazauna gefen anty zarah suna bubbudewa suna cin wasu suna dauko wata firar tasu maman junior tana bawa anty zarah din labari suna dariya hankalinsu kwance.


Sasai Tasha chocolates din Wanda har Saida anty zarah tace ta daina sbd ciwon Mara Amma haka ta share tunda tasan ba wani ciki ajikinta sasha kayan zakinta harsai dataji cikinta kamar zai Yi ciwo ta aje sauran cikin fridge.


Da daddare tana qoqarin zama bayan futowarta daga wanka ta shirya cikin riga da wando na bacci masu Dan akuri ta saka wularsu sai qamshin turaren Dr khalil takeyi Wanda yabata datace tanason qamshinsa saiga kiransa yashiga saidatai wani wuntsilawa sbd farin cikin ganin kiransa sbd dazu yakira da numbernsa tacan tayi saving.


Tana dauka tafara zuba Masa qirafin da batai Masa dazu ba sbd gaban anty zarah ne tace"


Nifa ban daina fushiba katafi kabarni zabeera ni kadai.


Murmushi me sauri yayi Yana qara Jin sonta har cikin ransa a natse yace"


Baga zarah Nan ba.


Shiru tayi kafin ahankali tace"


A cikin zabeera da wajenta a yanzu Babu inda nakejina cikin tsaro da kulawa idan har bakanan,

Dr kariga ka koyar Dani Jin rashin tsaro idan baka kusa Dan Allah kadawo da wuri tsoro da fargaba nakeji idan baka kusa.


Nutsuwa maganarta ta qara Masa yaji sanyi Yana qara samun nutsuwa yace Mata"


Inshallah Amatu idan Ina Nan kina cikin tsarona Babu Abinda zanbari yasameki sai qaddara.


Nasani Dr""""tafada tana Dan yamutsa fuska sbd mararta data Fara murdawa gashi dama ita qa'idane duk wata saitayita baqar wahala idan zatayi period,

Tunda tazo zabeera Dr khalil sbd cikin da akace tanadashi Yana gano tana ciwon period yake kaita asibiti duk wata tana ganin Dr Fatima ana Yan dubaru har tagama period din tukuna.


Fira sukeyi tana daddaurewa ahankali sbd ciwon marar gadan gadan yakeson taso Mata sai alokacin tagane Abinda anty zarah ke nufi data daina cin zaqi.


Jin kamar tanajin bacci yasa yayi Mata addua kamar yanda ya Saba duk dare kafin ya kashe wayar saidai hakanan yakejin kamar ba lafiya takeba.


Lallabawa tayi ta kwanta tana juye juye hardai abin yataso Mata sosai Nan tafara hawaye tana Kiran sunan Allah.Bayan kusan awa biyu da Gama wayarsu ya yakasa samun nutsuwa ya  kalli agogo yaga yanzu su can a Nigerian dare yayi sosai sai ya janyo wayarsa yashiga massage yayiwa zarah text yasan tana tareda MD Amma dai idan har tagani zataje ta dubo Amatu tagano masa.


Anty zarah na dakinta yau bataje dakinsaba sbd yanda yadawo tasan a gajiye yake bazaiso a takurasaba shiyasa tayi kwanciyarta dakinta tanata juye juye cikin tunanin daukar shawarar Amatu Amma tanajin shakku, 

Saiga massage dinsa yashigo tana karantawa ta miqe sanyeda kayan baccinta riga da wando irin na Amatun sak ta nufi dakin da sauri.


Salati tasaki me qarfi tana Shiga dakin cikin tashin hankali tayi kanta ganin tanata juye juye riqeda ciki tana wani irin numfashi da kukan azaba.


A rude takira Dr tana fada Masa cikin tashin hankali yake dama daya duba yaga yaune date din period dinta da sauri yace"


Kira umme Dan Allah ta taimaka Mata  takira Mata Dr Fatima.


Umme Kuma"""

Anty zarah tafada cikin mamaki sbd sanin kowa yasan umme Bata qaunar Amatu da Abinda yake cikinta.


Shikuma sanin umme ce kawai tasan Amatu batada ciki yasa yace aje gurinta sbd yasandai bazata tonaba yanzu.


Eh Zarah Kira umme Dan Allah Yi sauri.


Jiki na rawa ta Danna Kiran numbrn umme Saida tayita ringin kusan Kira biyar sai ana shida ta daga cikin bacci.


Umme zarah ce

Gamunan Amatu batajin Dadi zaki Kira Mana Dr Fatima ne Wai.


Wani qaton ashar ummen ta gundumo tana cewa''


Uban Dr Fatima zankira muku,

Zarah Kika sake kirana cikin Daren Nan saina mugun Bata miki wlh.


Kallon wayar da ummen ta kashe Mata tayi cikin mamaki da tsoron Ina mafita gashi idanba idonta yayi Mata qaryaba saitaga kamar jini a jikin dogon wandon Amatu din.


Wani razanannen qaramin ihu tasaki tareda jefar da wayarta tana fitowa da gudu tayi sama dakin MAHMOUD cikin sa'a Yana zaune yana aiki a laptop da cikin tashin hankali da rudewa tace"


Amatu ce ba lafiya kamarma jini cikinta zai lalace.....


Cak ya tsaya tareda dagowa ya kalleta ta daga Kai cikin rudewa tana kasa Magana.


Kallon agogo yayi batareda ya motsa yaga dare be

Zata sake Magana ya aje laptop din gefe tareda miqewa ya zura jallabiya Fara qal Kan singlets da short dake jikinsa ya dauki keys ya sauko zarah din na bayansa.


Kamar bazai Shiga dakinba saikuma ya Shiga daidai tayi wani juyin azaba zata fado qasan gado ya tareta da hannunwansa biyu 

Unfortunately sai idanuwansa suka sauka kan stain din jinin dake jikinta 

Ya rintse ido da sauri tareda dauke Kai Yana shawarar daukanta saikuma ganin halinda take ciki yasashi daukarta cak gaba daya yafito Yana cewa''


Zarah ki Kira zamu dawo zuwa da safe.


No comments

Powered by Blogger.