Makauniyar Kaddara 68


 Page 68*


..........Sai da Zinneerah ta fara gabatar da sallar magrib bayan fitowarta wanka sannan ta zauna ta tsara kwalliya ƴar gaske, tare da baje lungu da saƙo na jikinta da ƙamshin mayun turarurrukan ta sabbin haɗi daga

Hajiya Falmata. Ta ɗakko less da yaji ɗinki mai ƙyau da tsari ta saka tare da kashe kan ɗauri. Awarwaraye da sarƙa ta zuba kai kace wani biki zata. Ta sake ɗorawa da wasu turarurrukan sannan tai zaman sallar isha'i. ALLAH ya sota ƴan biyu suna goye a bayan Yaya Gajeje da Mama A'i.

       Sauri-sauri ta kammala ganin har isha'i su AK basu shigoba. Koda ta fito su Yaya Gajeje wani ihun dariya suka ɗauka da yaba wannan wanka nata. Kunya tasata jan mayafi ya rufe fuskarta. 

      Mama A'i da yake itama a ce, babu yawan magana sai lalata tace, “A'a wannan gayun bai kamata ki kaisa turaka ke kaɗai ba. Bara na ɗakkoma su Alhaji ƙarami kaya a canja musu suma dasu za'a”.

       “Wannan zance nakan hanaya Mma A'i”. Yaya Karima ta faɗa tana dariya. Zinneerah ta tura baki kaɗan tana faɗin, “Gaskiya nai dai a'a, salon su batamin gayu”.

      “Iyee, lallai Zinni binni ta buɗe miki ido da baki, a gabana babu kunya”. Cewar Yaya gajeje tana riƙe haɓa.

     Dariya Zinneerah ta shiga kwasa. Ta faɗa ɗaki tanayi da faɗin, “Yi haƙuri Yaya gajeje na tuba”.

   Suma dai dariyar suke tayata harta ɗakko kayan da za'a canjama ƴan biyu. Su Mama A'i suka shiryasu tsaf sannan Zinneerah ta kwashesu. Dan Yaya Gajeje korata tai wai ta tafi can yazo ya sameta zaifi jin dadi. Su Yaya Gajeje tsoffin masoyane da sukasan takan maza da muhimmancin irin wannan ranar. Aiko shawararsu Zinneerah ta bi. Dan dama itama akwai nata shirin a ƙasa.


          AK bai shigo gidan ba sai wajen tara da rabi na dare. A gajiye yake matuƙa. Dan haka kai tsaye ya nufi sashem Zinneerah ɗauke da little dayay barci. A falon farko ya samesu dan sunfi zama nan, kai shi baima taɓa samunsu a falon ciki ba dan daga shi sai Zinneerah ɗin ke shigarsa da bedroom dinta na ciki, saiko little.

     Mama A'i ta mike tana amsar little ɗin da masa sannu da zuwa. Suma su Yaya Gajeje sannun suke masa. Cike da mutuntawa yake amsa su yana baza idon ganin ta inda Zinneerah zata ɓullo da twins nashi. Ganin dai babu alamarta ya sashi leƙa Inna sannan ya fice.

    Gulmarsa su Yaya Karima suka shigayi suna dariya. Dan yanda yaketa kalle-kalle sunsan matarsa yake son gani, gashi su kuma sun yi gum bama su nuna sun fahimcesaba.


     Shiko harya ɗan shaƙa dan ya zata abinda ya faru tsakaninsu ɗazun da safe ne ya sata fushi. Sai da ya shigo sashensa ya shaki wani mayataccen ƙamshi daya nema karar masa da man kai lokaci ɗaya sannan ya sauke ajiyar zuciya. Taku yake tamkar mara laka a jiki yana bin falon data sakama hasken wuta kaɗan da kallo. Bukatar fara wanka ta sashi nufar bedroom ɗinsa ransa fal waswasin ina ta shiga.

      A bedroom ɗinma ƙamshin da yafi na falo ɗaga masa hankali ya shaƙa. Kasancewar wutar ɗakin a kashe dindim ta sashi fara lalauben makunnar fitilar. Ɗan zabura baya yayi lokacin da haske ya gauraye ko ina a ɗakin. Kyawawan idanunsa kuma sukai masa gani na musamman daya sakashi hangame baki. Zinneerah ce zaune a tsakkiyar gadon lulluɓe tamkar sabuwar amaryar da aka kawo ɗakin miji yau. gefe da gefenta Amaan da Anam ne cikin showals suna barcinsu hankali kwance suma cikin gayu.

      Jiyay gaba ɗaya yana neman daburcewa da salon nata. Ya shiga takawa a hankali zuwa gaban gadon jininsa na tsinkewa tamkar manjan da yaji zafin wuta.

          الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .

*_Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat._*

      _Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika._

اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.

*_Alhamdu lillahi ala kulli halin_*

     _Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali._

       Ya faɗa lokacin da yake kaiwa zaune bakin gadon. “Dan ALLAH ki zauna a haka karki motsa harna fito a wanka, dan wannan sirrin ya wuce na gani da ido kawai ko fatar baki”.

     Zinneerah da duk take jinsa tai murmushi batare datayi ko tari ba balle ta motsa. Bai damuba shima dan mikewa kawai yay ya nufi toilet.

      A yanda ya barta ɗin kuwa haka yazo ya sameta. Tsane jikinsa yake amma ya kasa daina kallonta ita da yaran daga inda yake. Turarurruka ya cuɗe jikinsa da shi da ɗaukar wando fari ƙal iya cinya ya saka da ƙaramar riga armless ya haura gadon

    Zama yay a gabanta ya tanƙwashe kafafunsa suna fuskantar juna. Yasa hannayensa biyu ya kamo bakin mayafinta ya ɗaga sama ƙyaƙyƙyawan fuskarta na bayyana garesa tana neman zautashi da wani sassanyan murmushi.

     Da ƙyar ya iya fisgar numfashin dake neman ƙwace masa yana wani mar-mar da idanunsa dake neman zubowa jikinta. Luuu ta ɗanyi da idanun tasa tafukan hannunta ta rufe fuskarta. Hakan da tai ya bashi damar yin tozali da ƙyaƙyƙyawan ƙunshinta.

        “My Neerat zaki halakani wlhy”. Ya faɗa a wani irin sassanyan sauti da ita kanta sai da tsigar jikinta ta tashi. Hannayensa duka ya ɗaura akan nata yana janyewa daga fuskarta. Cikin idanunta ya zuba birkitattun nasa yana faɗin, “Ina ƙaunarki da yawan yawa My Neerat, zaki zautan ɗan Shira da salonki”.

         Zinneerah dake amsar saƙwanninsa ta cikin idanunsa itama da wata irin muryar da batasan tanada shi bace, “أَحَبَّكَ الَّذِي أَحْبَبْتَنِي لَهُ.

   *_Ahabbakal lazi ahbabtani lahu._*

_Wanda ka so ni saboda Shi, kai ma Ya so ka Yayanmu. Kuma nima ina ƙaunarka”_.

        Gaba dayanta ya cacumo jikinsa ya rungumeta tamkar zai cusata a fata da ɓargon jikin nasa gaba ɗaya. Cikin fisgar numfashi ya shiga laluben bakinta ya manne a cikin nashi jikinsa na wani irin tsuma na zalamar son kasancewa da ita. Bata iya ta hanashi ba. Sai ma haɗin kai data shiga bashi.

    Sai da labarin ya nema yin nisa kuma tsoro ya kamata, dan gasu Anam a gadon karsu taushesu. cikin taimakon da ALLAH yay mata sai Amaan ya farka da kuka. Da ƙyar AK ya iya sakinta yana cizar lip. Itama ta mike da ƙyar daga jikinsa dan tunaninta kar hayesa sukai. Ganin babu abinda ya samesa ya sakata sauke ajiyar zuciya da hararsa. “Ɗan ɗagwai na zatama hayeka akai”.

       Idanu Ak ya buɗe da ƙyar yana duban inda Amaan ɗin yake. Kafin ya yunƙura da ƙyar ya matsa garesa yana dungure masa kai. “Haka kawai ka ɓatamin wasa. Shiyyasama bana Baffan da kai yaro”.

    Murmushi Zinneerah dake kallonsu tayi, ta sauka ƙasa gaba ɗaya tana kai hannu ta ɗaukesa dan tasan yunwa yakeji. Komawa AK yayi ya kwanta dan cikinsa ya ƙulle tamau. Har Zinneerah ta gama shayar da Amaan ta maidashi ta kwantar sannan ta dubesa.

     “Yayanmu ga abinci fa a falo kar dare ya ƙara zurfi”.

    Lumsassun idanunsa ya buɗe a kanta. Akan laɓɓansa da ƙyar ya furta, “Ke kaɗai kin wadatar dani”.

    Dariya zancen nasa ya bata dan tasan dai shi da abinci sai ta ALLAH. Ta miƙe tana fadin, “Nidai daka daure kaci bara na kai su Anam ai musu shirin barci. Uffan bai iya ce mataba harta fice a ɗakin. Bai kuma iya motsawa ba yana a inda ta barsa har kusan mintuna talatin sai gata ta shigo ɗauke da tea. Ajiye masa tai tana faɗin, “Ga tea nanto Yayanmu bara na ɗakkosu.”

    Bai motsaba bai kumayi magana ba harta sake ficewa yanzu ma. Bata jimaba yanzu ta dawo ɗauke da ɗan gadon su Amaan. Ta ajiye ta koma falonsa inda Mama A'i ta rakota da yaran ta amso su sannan tai mata sai da safe dan tama su Yaya Karima sallama.


       Jin ta dawo tana kwantar dasu ya sashi miƙewa da ƙyar zaune. Kofin tea ɗin ya ɗauka ya hau sha dan da gaske yanajin yunwar ma. Sai dai duk inda tai yana binta da kallo harta gama hidimar yaran tai musu addu'a. Dan ma sanye take da zumbulelen hijjabi a saman kayan barcinta.

    Sai da ya kammala yaje yay brush itama taje tayo dan ta kimtso kanta daga can, alwala kawai tayo da brush ɗin ta fito. Tsugunne gaban gadon su Anam ta samesa yana musu addu'a fuskarsa ɗauke da murmushi yana faman shafa kawunan yaran. Ta zare hijjab ɗin nata tana nufar falo ɗakko ruwa duk da ta tabbatar sai yaci abincin nan ko zuwa anjima ne.

    Da kallo ya bita harta fice. Ya sauke ajiyar zuciya yana mikewa daga wajen su Amaan ɗin.

    Tsaye ta samesa gaban mirror yana saka turare. Tana ajiye ruwan ta juyo da nufin masa magana taji anyi cak da ita sai gado. A tare ya faɗa da su yana magana cikin kuneneta. “Wai sokike dai sai na miki kuka yarinyarnan. Sai wani ƙwalele kikemin ni da kayana”.

    Siririyar dariyar data nema zautashi ta saki tana cusa kanta a wuyansa da shaƙar ƙamshinsa itama. Babu shiri ya lalubo bakinta dake ƙamshin strawberry freshener ya manna nasa a ciki. A zalame yake, dan haka cikin zalamar ya shiga sarrafata shima, itama kuma tana amsarsa da zalamar dan koba komai tayi kewa.

     Sai da tafiya tai nisa sosai ta gama shagala a hannunsa da salonsa sai ga idon madam ya raina fata ta koma raki daga karshe. Inama AK ke wani jinta shi a wannan yanayin. Sai da ya more duk ƙwalelen kwanakin da akai masa shima sannan ya koma lallashi yana mata dariyan mugunta.

    Kamar yanda tai hasashe kuwa suna kimtsa jikinsu sai da yaci abinci waishi duk ta sakashi jin yunwa. Murmushi kawai ta dingayi dan dai al'amarin nasa yakanfi ƙarfinta wani lokacin, babu abinda ya damesa ɓaro mata zance yake kansa tsaye kamar ba yayansun nan sarkin mazurai da tsare gida ba. A yanzu haka idan su Jamal na tsogumi akansa sai taita dariya kawai dan tasan dai mazuran iya na waje ne. Itama dai sai da tacin danya tsiyayeta tas ga yaransa a gefe da nasu suma.


      A tsakanin dare zuwa safiya dai sai da Zinneerah ta raina kanta a hannun AK, dan babu kunya ya hanata komawa sashenta yinin ranar shima kuma bai fita ko inaba sai massallaci. Sai dai taje ta ɗauka abu a sashenta ta dawo, su ƴan biyu kam ko ƙofar ɗaki basu jeba suna nane da shi harda little da tunda gari ya waye shima ya taho nan ya tare. Sai da zai wuce islamiyya.

       Babu abinda suke zubawa sai zallar soyayya da nunama juna tsantsar ƙauna a wannan yini. Duk wani motsinta idonsa na kanta. kamar yanda itama dai ta murje nata idon take masa komai dai-dai da buƙatarsa. Sai ta gama ta koma sinne kai wai ita kunya. Hakan na birgesa da sakashi a nishaɗi, dan ji yake tamkar yayi gamo da sabuwar budurwa a haɗuwar farko.

            Washe gari ma duk da ayyukan dake a gabansa tari-tari haka ya lalace wajenta sai bayan azhar ya shirya ya fita. Magribar fari sai gashi ya dawo. Sakawa yay ta shirya ita da yara ya fita dasu wani haɗaɗen joint ɗin cin ƙwalam da maƙulashe, suka shawo ice-creem. Yana ɗauke da Anam tana ɗauke da Amaan. Little na riƙe da ɗayan hannunsa abin sha'awa. Mutane sai kallonsu suke abin birgewa, dan shi kam rashin zamansa a ƙasar sosai yasa bawani saninsa akai a fuskaba da yawa. Sunansa yafi fuskarsa fita ga kunnuwan jama'a. Ganin yanda ake kallon nasu sai kishi ya kamasa ya kuma dinga ɓata fuska. Itama kuma madam ɗin nasa sai kishin ya rufeta ruf saboda yanda ƴan matan wajen ke rawar kai gaban samari dama irinsu AK ɗin duk da suna ganinsu tare da iyalansu (Ƴammata a yi haƙuri inaji daku😂😹😹🙏🏻). Haka dai suka kasance a daddafe a wajen danma vip suke zaune. 

      Daga nan wajen wasan yara suka kai Little dan duk akwai a wajen duk da dare ne. Ya ɗan hau abubuwa yana maijin nishaɗi harda rigimarsa ta aɗora su Anam. Zinneerah tace wlhy bata yardaba. Bata gama dawowa daga maganin naƙudaba ba'a sata kuka.

       Maganarnan ta bama AK dariya. Ya dubeta fuska ɗauke da murmushi har haƙwaransa na bayyana yace, “Haba karki bada mata mana madam, ni har ina murna na sake jefa ƙwallo tsakanin jiya da yau”.

      Cikin ƙwaɓe fuska tace, “Wayyo ALLAH Yayanmu dan ALLAH daina min fatan nan ka tausaya min”.

        Nanma ƴar dariya yayi da sumbatar goshin Anam dake a hannunsa. “My Sweetheart kinji Mamin ku zata mana buƙulun gambo ko? Ku faɗa mata ku kuna son ƙani da wuri Mammah da Mahma, badan kar ace na cika son kai ba sai nace a haɗo da Uncle Ahmad duk lokaci ɗaya, daga baya sai a bani Mommy na da Gwaggo da Baba suma, sai Abbah kuma ya zama auta”.

         Yanda tai sagade tana kallonsa baki a hangame ya sashi dungure mata kai. “Kallon fa?”.

       Kai tsaye tace, “Na tsoro da al'ajabi ne ai. Ƴaƴa bakwai fa kake lissafi daga gama arba'in Daddyn Little”.

        “Oh kinma ɗauka ni na wasane kenan. Yarinya shirya da ƙyau Shirawa yawa suke son ƙarawa, mu babu ruwanmu da wani tsarin iyali”.

       “Aiko na rantse yaji zanzo nayi, danya zan tafi sai nayi wata uku acan”.

       Dariya sosai yakeyi yanzu kam. Yace, “Ai wlhy Baba koromin ke zaiyi, kije wajen Granny kuma kin kai kanki, dan ba ɗaga ƙafa zanba harcan zan biki, gara-garama wajen gwaggo, zanji kunya. Amm nasan itama koroki zatai”.

        A ranta tace, (Zaka iya wlhy Yayanmu) a fili kam cewa tai, “Wannan zance yafi ƙarfina karka lalatani da ƙarancin shekaruna gaskiya”.

        “Lalacewa kuma ta yaushe yarinya, tunda ga ƴan biyuna a hannu ina kallonsu inajin daɗin raina su da babban Yaya takwaran Daddynsa. Zaki gane kuranki bara mu koma gida”.

      Jin haka ya sata yin ɓam da bakinta. Shiko ya samu na tsokana har suka bar wajen bayan yama su Yaya Gajeje takeaway ɗin tasu tsaraban na kayan ƙwaɗayi...........✍


No comments

Powered by Blogger.