Makauniyar Kaddara 66

 


Page 66*


............Washe gari da yammaci jirginsu ya ɗaga zuwa Birtaniya. Inda al'amari yaso ƙwaɓema Zinneerah. Dan tamkar jira jirginsu na ɗagawa amai ya ringa taso mata. Ganin yanda taketa rintse ido da yamutse fuska yasa AK taɓata. Ido ta buɗe da ƙyar tana dubansa. “Lafiya dai?”. Ya tambaya cikin kulawa.

      “Yayanmu amai nakeji wlhy”. Ta faɗa da ƙyar tana danne bakinta da hannu. Cikin mamaki yace, “Amai kuma?”. Kanta ta ɗaga masa tana miƙewa da sauri domin zuwa toilet. Dole shima ya miƙe yabi bayanta, Hajiya Iya na tambayarsu ko lafiya ma basu jitaba.

       Sosai ta jigatu wajen yin aman, sai da ya taimaka matama sannan suka fito. Ganin yanda duk ta jigata hajiya iya ta shiga salati. “Inno baki da lafiyane dama aka ƙirƙiri wannan tafiyar dake haka?”.

       Kanta taɗan jujjuya mata da ƙyar, murya a sanyaye tace, “A'a Granny lafiyata lau, kawai yanzu ne dai na dinga jin aman”.

        Khalipha dake mata kallon tsaf ya ɗauke kansa yana murmushi da gyarama little dake jikinsa yana barci zama. Hajiya iyama kallon tsaf takema Zinneerah ɗin har wasu mintuna. Kafin tai murmushi da faɗin, “To ALLAH ya rabaku lafiya, ya inganta kuma”.

       “Amin” Khalipha ya amsa mata. AK da duk bai fahimcesu ba ya kalli hajiya iyan sai dai baice komaiba. Harara ta zuba masa tana mita. “Ka wani tsareni da ido minaci ban bakaba to?”.

      Ƙara tsuke fuskarsa yay yana ɗauke kai gefe batare daya tanka mataba. Sai dai har cikin ransa waswasin maganar tata yakeyi. Ya kwantar da Zinneerah jikin kafaɗarsa yana gyara mata mayafinta. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga barci yay awan gaba da ita. Itace bata farkaba sai gab da zasu sauka.


     Abin mamaki sai ga Mammah tazo da kanta ɗaukarsu. Cikin girmamawa kuma ta gaida Hajiya iya tare da rungume Zinneerah da duk alamun rashin lafiya ya bayyana gareta. Khalipha ma cike da kulawa ta amsa masa gaisuwarsa tana dungure kan little da yaƙi zuwa wajenta ya maƙale Khalipha ɗin.

        Har cikin rai AK yaji daɗin canjawar mahaifiyar tasa. Sai dai bai nunaba ko'a fuska. Tunda ya gaishetama sai ya ɗauke kansa ya maida ga waya.

        Sun iso gidansu da suka samu ƙal an gyara, ya kuma san aikin Mammah ne da Mahma. Nanma yaji daɗi. Hajiya iya ɗakin data zauna wancan karon ta sauka. Khalipha ɗakinsa. AK da Zinneerah ɗakinsa. Dan ɗakin Farah ma a rufe yake bai kuma nuna alamun son a buɗeba.

       Wanka ya taimakawa Zinneerah tayi ta kwanta dan zazzaɓi ne rijif a jikinta. Ga yunwa na cinta dan bataci komai a jirgi ba. Hakan yasa AK tsareta taci abincin da Mammah ɗin ta kawo musu. Da ƙyar tai lauma uku, sai gata hanyar toilet da gudu. Duk binta sukai da kallon tausayi, AK idonsa ya kaɗa yay jajur, dan shi ya rasa wannan amai na minene?. Bayan ya taimaka mata ta fito ya kwantar da ita sannan yazo falo yana cema Khalipha yazo suje asibiti dan shi wannan amai ya rasa na miye ko wani abu taci ya bata mata ciki.

         Dariya ta kusa suɓucema Khalipha akan wannan zance, a ranaa yace, (Waken daka batane Yayanmu ya bayyana kansa) a fili kam sai yace, “Uhm ai Yayanmu bara dai na duba mata wani magani kozai taimaketa, amma wannan amai ai na farin cikine bana ɓacin ciki ba”.

       Fuska ya ɗaure tamau yana hararsa, “Shi aman har abin sone?”.

       Mammah da itama dariya ke cinta tace, “Barma yarona mazurai malam, ai gaskiya ya faɗa wannan amai abin so ne, dan kuwa dai na rabone sai dai muyi fatan ALLAH ya sauketa kafiya”.

       Karon farko AK ya ƙwalalo idanu waje yana kallon Hajiya Iya da Mammah dake dariya, ya maida ga Khalipha daketa ƙoƙarin ɓoye tashi. “Nikam ku fiddani a duhu, kuna nufin ciki ne da ita komi?”.

       “Tabbas hakane Yayanmu, Congratulations”. 

    Kasa motsi AK yayi dan alja'ab ko ruɗani zai ce. Sai gani kawai sukai yakai gwiyawunsa ƙasa yay sujuda ga UBANGIJIN talikai mai badawa ga wanda yaso a kuma lokacin da yaso, kafin ya koma gaban Hajiya iya ya rungumeta, ya saketa itama Mammah ya rungumeta, kafin ya koma kan Khalipha.

     Yana sakinsa ɗakinsa ya nufa cikin sassarfa, cikin barci Zinneerah taji an mata wata lafiyayyar runguma ana sakar mata kissis tako ina a jikinta. Ta buɗe idanu da ƙyar tana kallonsa. Jin godiya da kirarin da yake jerama UBANGIJI tare da addu'ar ALLAH ya sauketa lafiya ya sata fahimtar lallai zancem su Yaya gajeje ya tabbata cikine da ita, hawayene suka silalo mata na jin daɗi da tausayin kai. Tayi farin ciki dan tasan koba komai mutane da yawa zasuyi farin ciki ta silar wannan cikin, sannan ta tausayama kanta dan tasan da wahala karatunta bai salwantaba.

       Aman daya taso matane ya sakata samu AK ya saketa ta nufi toilet da gudu. Wani irin tausayinta da ƙaunartane ya kamashi ya dafe kansa yana mai jin kamar inama ace zai iya rage mata wani yanki na raɗaɗin da takeji.


             Khalipha ne ya fita dole ya samoma Zinneerah maganin dazai taimaketa ta ɗan huta da aman duk da dai yasan baizama lallai ta daina duka ba. Cikin amincin ALLAH kuwa tana sha sai barci. Daga haka suka cigaba da farin cikinsu, yayinda labari har ya kaima ƴan Nigeria.

        Zo kaga murna wajensu Meenal da dariyar mugunta wai su Zinneerah an cika zalama, daga shiga harta ƙumso. Sunji inama zasu iya samun wayarta su baɗaɗeta da sheri.

    Mammah ma cikin farin ciki ta komawa Mahma da wannan daddaɗan labari. Sosai itama tai farin ciki da shiga jerama Zinneerah addu'ar lafiya mai inganci. ta sake ɗorawa da yima Mammah nasiha kamar yanda takeyi kullum yanzu tunda suka dawo. Hakkanne ma ya ƙara sakama Mammah nutsuwar zuciya da sake duƙufa neman gafarar ALLAH.

       

      Sabon tattali Zinneerah ta fara gani a london hannun AK da mahaifiyarsa da Mahma. Hajiya iyama duk da tana ƙarƙashin kulawar likita tana binta da addu'a da dabarunsu na tsoffi. Dama little tun kwana biyu da zuwansu ya koma gidansu Mammah ɗan gata. Hakan yasa AK samun damar baje sharafin soyayyarsa a cikin gidannan. Dan Khalipha na musu kawaici da basu fili yaje yay zamansa wajen Hajiya iya susha hira.

     Ita kanta Zinneerah ɗin shegen ƙwaɗayin da cikin yazo mata da shi yasata sake nanuƙema AK, dan babu abinda tafi ƙauna daso kamar ƙamshin turarensa da kasancewa dashi. Randa tai waya dasu Bahijja tasha Sheri, hakama su Sa'a nata tsokanarta.

    Ita dai babu baki dan ya mutu murus. Suna cikin sati na uku da zuwa jikinta yay ɗan mata ƙarfi irin na mai ciki, yau lafiya gobe jangal. Gyaran ɗakin nasa ko nace nasu tai ƙoƙarin yi, tanayi tana ɗan hutawa harta ga yay mata ƙal. Tana cikin gyaran ne sai ga idonta takai kan tsohuwar wayarta da aka sace a ɗakin hajiya iya. Mamaki yasata jujjuya wayar tana kallo dason tunani yanda akai tazo London, london ɗinma ɗakin Yayansu.


       “Malama miya kai idonki nan?”. Taji an faɗa a bayanta cikin dakakkiyar murya. Tasan Yayansu ne, dan haka ta juya fuska a ƙwaɓe tana kallonsa da cigaba da juya wayar a hannunta. Takowa ya ƙarasa yi cikin ɗakin yasa hannu ya amshe wayar fuska a tamke. Ya ɗaga ƙafa zai juya ta riƙo hannunsa da faɗin, “Wai Yayanmu dama kaine ka sacemin waya?”.

     Harga ALLAH yanda tai maganarne yay matuƙar bashi dariya, duk yanda yaso cigaba da pretending ɗin mazuran nasa sai gashi ya saki murmushi da hararta. Ya dungure mata kai yana cije lip ɗinsa na ƙasa. 

      “Yarinyarnan kin fara rainani ALLAH. Ni nema ɓarawo ko?”.

       Hannu tasa ta rufe fuskarta tana murmushi. “Nidai bance dakai barawo ba. Amma idan ta gaskiya za'  sace wayarnan akai na nemeta na rasa”.

     Cak ya ɗagata da ƙasa yay saman gado da ita yana faɗin, “To bara na nuna miki ba satar waya kaɗai na iyaba yarinya”. Ya ƙare maganar da tura hannu cikin ƴar fingilar rigar jikinta da iyakarta cinya. dama ta sakatane dantayi aikin a sake babu takura. Dariya ta shiga ƙyalƙyalewa tana faɗin, “Na tuba wasa nakeyi ALLAH”.

    Kobi takanta baiyiba ya lula da ita duniyar kodumo, dama ita kam duk sanda ya taya tana maraba, inma bai kawo kansaba ita zataje.

    Sai da suka samu nutsuwa aka koma firar waya. Babu kunya yake sanar mata ai tun randa Farah taje Nigeria lokacin da take bama su Mas'ood Number ta yay ƙudirin rabata da wayar, sai dai bayaso yayi gatse-gatse su Granny su saka masa ido ko Khalipha ya fassara abun da wani abu daban. Shiyyasa yabi dare ya sace batare da sanintaba. Dan tana gama waya dasu maman sadiq ta fita tarbosu ya ɗauke wayar yasa a aljihu, ya fito da nufin barin gidan yaci karo da fuskar little.

      Jikinsa ta faɗa ta rungumesa tana dariya. “Kai Yayanmu amma ranar harda tambayata ina take? Sannan duk yanda kaga ina zaune babu waya bakaji tausayina ba”.

    Hancinta yaja yana murmushi, “Uhmyim, salon na barki ki riƙe wani yaymin fashi da makami. Na tabbata Khalipha nema zai fara shiyyasa nai azamar yin maganinku, dan bana haɗa takara da kowa nikam. Duk abinda zuciyata taji tana muradi nawane ni kaɗai insha ALLAH. Dan tun randa kikaimin ihu a ɗaki da kirana aljani kikai wuff da tunanina da zuciyata, shiyyasa duk motsinki yazama akan idona”.

      Ƙarara mamakin maganganinsa suka bayyana a fuskar Zinneerah, sai ga hawaye na cika mata ido, batama san ta ɗane jikinsa da haɗe bakinsu waje gudaba dan daɗi. 


        Soyayyar Zinneerah da AK abin sha'awa. Gwargwadon iko yana bata kulawa. kuma yana so da kaunarta. Sai dai soyayyarta sam bata rufe idonsa ya manta da Farah ba. Tana nan maƙale a ransa yana kuma son kayarsa. Babban fatansa ALLAH ya shiryeta ta gane gaskiya a duk sanda zata sake dawowa rayuwarsa ta dawo a Farah dinta da suka shinfiɗa ƙyaƙyƙyawar rayuwa a baya. Ya kuma yafe mata daga ita har Mammah da Zakiyya, dan koba komai sun zama silar mallakar Zinneerah a rayuwarsa, tare da kusantashi da ahalinsa. Da kuma samun dai-daito tsakanin Mahaifinsa guda biyu, abinda tayta fata a tsahon shekaru amma ya gagara.


______________


      Haka rayuwar London ta cigaba da tafiya cikin jin daɗi da farin ciki, sai dai wataran saɓani da ɓacin rai kanɗan gitta tamkar yanda akasan kowanne gidan ma'aurata. Amma lallai bazasu taɓa iya mantawa da rayuwar london ba dan rayuwace mai tsayawa azuciya garesu. Anci soyayya kamar babu gobe. 

      Sunada wata ɗaya a london matar dake ɗauke da cikin da aka dasa mata ta Morocco ta haihu, sai dai abin ƙaddara ta haifi yarinya mace babu rai, abinda yasa zancenta baiyi tsaho ba ta tabbatar ma su Baffah cewar da amincewarta su Zakiyya sukai komai, ko yanzu suka shirya kuma zata ƙara ɗauka musu wani cikin tunda wannan batazo da rai ba. Godiya kawai sukai mata da bata wasu kuɗaɗe suka barota.

        Duk da kuwa AK yaji baƙin cikin ta yanda aka samar da ɗiyar itama sai da yay hawayen rasuwarta lokacin da aka turo masa hotonta a waya abin sha'awa. Ya sunbaci wayar da jerama UBANGIJI kirari da addu'a a gareta da sauran al'ummar musulmi baki ɗaya. Zinneerah kanta sai taji yarinyar ta shiga ranta. Hakama Hajiya iya dasu Mammah. To amma yaya za'ai da hukuncin ALLAH sai haƙuri.

      Watansu biyu cif suka dawo gida Nigeria domin halartar bikin ƴaƴa bakwai daga zuri'ar Abdul-Mutallab Shira. A lokacin cikin Zinneerah nada watanni huɗu cif. Ya ɗan turo abinsa duk mai lura zai iya ganinsa.

         Aiko sai ta dinga ƙunshe-ƙunshe musamman da taje gidan mmn Sadiq. aiko su Meenal suka dinga mata dariya. Taso zuwa duba Inna kafin a shiga hidimar bikin amma AK ya hana, acewarsa ta bari a gama biki sai suje dan akwai maganar Dr Mahmud ma da Sa'a a ƙasa. 

       Kamar yanda ya umarceta da haƙurin haka ta haƙura aka shiga shagalin bikin su Abidah da aka shiryama bidi'oi kala-kala, danma AK ya zaftare wasu a ciki yanata faɗa.

    Ranar ɗaurin aure a bazata sai ga sunan Khalipha a cikin anguna. An zarga masa igiya uku da ɗiyar Uncle Ahmad Raheenat (Noor). Kowa kam yayi farin ciki da wannan haɗi musamman ma Uncle Ahmad. Shima dai ango da gaske yanaso dan ƙiri-ƙiri ya nuna farin cikinsa. Abin sauƙin ma shima yanada gidansa dama da yake gini, ƴan abubuwane kawai suka rage a ƙarasa dan haka aka hau sauran aiki babuji babu gani. Matar Uncle Ahmad tayi baƙin cikin wannan haɗi itakam, sai dai babu yanda zatai dole ta haƙura. Dan dama taƙi sakin jiki da matan gidan sam. Suko da yake ba kanwar lasa bane duk sai suka watsar da ita suma suka cigaba da sabgogin gabansu.


       A bikin nan dauriya kawai Zinneerah keyi dan batajin daɗin jikinta, hayaniyarma sam bataso, shiyyasa lokuta da dama zaka sameta can gefe a killace. Hakan sai yayma AK daɗi dan bata halarci bidi'a ko daya ba da akai garama kamu da akayi anan cikin gidan. Ana saka kiɗa kuwa sai da tabar gidan saboda ciwon kai mai tsanani. Can gidansu ta koma tai kwanciyarta ta hutama ranta.


       Ansha shagalin biki harna kwanaki uku aka miƙa amare ɗakinsu. Adilah lagos, Safiyya Abuja. Sauran kuma Ni'ima da Abidah duk anan kano ne, sai Noor da aka bari sai nan da kwanaki uku an kammala aikin gidan Khalipha.

     (To amare da angwaye ALLAH ya sanya albarka ya kawo ƴan dugwi-dugwi iyalan baba). 

         Washe garin da aka shashshare daga bikin nan kuma aka kai kuɗin auren Sa'a danya. Inda baƙi suka sami tarba ta mutunci da girmamawa. Inna ga dama ta samu amma babu halin damawa, sai hawayen zuci takeyi. 

   Dan tuni aka maidota gida. Sai dai a duk sanda ta kalli Tinene da tsohon ciki ranar sai ciwonta ya rikice. Hakan yasa suka yanke shawarar maida Tinene gidan Gwaggo laritu harta haihu, dan an ajiye magana randa ta haihu za'a ɗaura mata aure damai cikin tunda ya amsa nasane.

     Daga kai kuɗi baba yace shikam dai baimaga wani abun jeka ka dawo ba a ɗaura aure kawai a huta. Zuwa wani satin ta tare ɗakinta taje tai haƙuri tamkar kowa. Hakan yama Dr Mahmud daɗi, hakama su Baffah da suka kai kuɗin. Nanko take aka zarge igiya uku tsakanin Sa'adatu Sulaiman Danya da Dr Mahmud Dawood. Zokaga baki wajen ango. Aiko AK ya dinga masa sherin kurame yana ramawa shima kamar yanda yay masa. Dan bazai fito kai tsaye yay maganaba sai dai yayi a fisge ya tsuke baki cikin basarwa tamkar bashine yayi ba.

    Cike da farin ciki suka dawo kano da wannan labari, Zinneerah kam tafi kowa murnar wannan al'amari dan har kukan daɗi tayi. 


       Cikin amincin ALLAH sati na zagayowa akai tariyar Sa'a. sai dai Zinneerah bataje Danya ba dan batajin daɗin jikinta kam, Khalipha ma tasa amaryar ta tare a nasa gida da aka kammala. Yanzu kam sai dai mu cigaba dabin kowa da fatan alkairi.

          Tun bayan tariyar Sa'a komai ya sake lafawa, Khalipha ya koma London shi kaɗai domin karasa karatunsa. Zinneerah ma cikin ƙarfin hali AK ya sata zana exam na November/December. Tasha wahala saboda laulayin dake damunta, amma babu laifi tayi ƙoƙari Alhmdllh, sai fata da addu'ar fitowar ƙyaƙyƙyawan result.

       Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Zinneerah na rainon cikinta dake ƙara fitowa yana wahal da ita, duk ta rame sai haske data ƙara kam masha ALLAH. Yanda wahalar tai mata yawa ne ga aikin gida ga little ya fara makaranta, dan yanzu yafi zama anan fiye da ko ina, yawonsa sai weekend, ga gida shiru ita kaɗai yasa Hajiya iya cemasa ya maidota nan gidan sai ta haihu. 

     Babu wani ɓoye-ɓoye ya ɓata ransa. Dan shi dai yafison su cigaba da lallaɓawa a hakan har ALLAH ya sauketa lafiya. Tunda dai bawai kwance take rijif ba. Aikin gida da lalurarsa girki da sauransu duk tanayi. Fitace kawai bata cika sonyi ba dan wahala take sha sosai koda kuwa zuwa gidan su Granny ne kawai tayi ko gidan mmn sadiq. Shiyyasama ta tattara kowanne yawo ta ajiye.

       “Ikon ALLAH, wai ka cika baki da iska! Bazaka maidotan bane komi kake nufi moddibo?”.

       Shiru yay mata kamar bazai tanka ba, sai da yaja wasu sakanni ya dubeta yana ajiye wayar hannunsa. “Granny ki fahimta mana dan ALLAH, taya yarinya na gidan mijinta ace ta taso ta baro. Wazai kula damu ni da Abdul-Mutallab to?”.

        “Owoo, sai ta zauna zaman kula da ku ita kuma ta kashe kanta. Kana ganin yanda duk jikinta ya koma ko abincin kirki bataci sai yame-yame”.

       “Granny duk nasan da waɗanan matsalolin kuma suna damuna wlhy nima, ina kuma yin iya bakin ƙoƙarina na ganin na bata kulawa nima, kuma Alhmdllh jikin natama ya fara sauƙi. Kawai dai idan kin yarda a samo wata ta zauna da ita ni ko nawane zan biya. Kokuma ke ki koma can dan ALLAH ”.

      “Wa? Kama kanka. Kawai sai naje ƙososo na zauna muku a gida raba kanka malam”.

       Murmushi yayi a ransa yana faɗin, ‘Ai wlhy ke zan lallaɓa kije madam, nasan maganinki ai’. A fili kam sai yay mata shiru, daga ƙarshe ma ya miƙe yana faɗin, “Bara naje na ɗauka Abdul-Mutallab a makaranta”.

      “ALLAH ya kiyaye ka gaishesu”.


   Zinneerah na falon farko na sashenta a kwance cikin kujera barci ya ɗan fara figarta daga charting dasu Meenal suka shigo. Kamar yanda Little ya saba duk da kuwa yanzu ya ƙara girma da wayo ga shegen miskilanci kamar sunyi kaki sun ajiye ya nufeta da gudu. Yana ƙoƙarin faɗa mata a jiki AK ya ɗagashi sama dan yanayinta ya nuna masa batajin daɗin jikin. Kuma lafiya lau ya fita ya barta.

     Itama ajiyar zuciya ta sauke ganin ya hana little ɗin faɗa mata a jiki. Ta yunƙura ta tashi zaune tana musu sannu da zuwa. Amsawa yay idonsa a kanta yana kaiwa zaune kusa da ita little a jikinsa.

      “Jikin ne kuma?”. 

  Fuska Zinneerah taɗan yamutse tana kamo hannun little ɗin. “Kawai dai banajin ƙarfi ne amma babu inda kemin ciwo, garama tashin zuciya daketa damuna tun cin kifin nan na jiya da naci”.

      Tausayintane ya sake kamashi, musamman daya tuna yanda taita damunsa da maganar kifin. harma ya dawo gida jiya da nufin bazai sake fitaba ta takura sai da ya fita kusan goma na dare ya nemo mata kifin, gashi kuma taci ta kasa zaman lafiya.

         “Sannu ALLAH yay miki albarka ya saukeki lafiya. Bara na taɓa Mahmud naji kozaki iya shan wani abu dazai baki nutsuwa”.

       “Yayanmu kama barshi zai bari dan kansa. Dan nayi waya da Yaya gajeje tace na samu ɗan kanwa kaɗan nasa a ruwa na sha zai faɗa min”.

        Kafin yace wani abu little da yay kamar ba saurarensu yakeba yace, “Aunty sorry, idan kika haifa mana babynmu zan kaiki makka”.

       Dariya zancen nasa ya basu, dan haka suka murmusa AK na shafa kansa. “ALLAH ya tabbatar ɗan albarka. Yanzu ka muje na maka wanka kaga aunty yau babu kanta”.

    Kansa ya ɗaga masa. Zinneerah tace, “Kama barshi zan iya masa. Bara kaima na haɗama ruwan wankan ga abinci nan na shirya”.

        “Kina fama da kanki kika wani kama abinci? Nace miki duk randa baƙyajin daɗi basai kinyi ba tunda ga gidan Granny sai a kawo daga can”.

    Murmushi ta ɗanyi da kama hannunsa dan ta tura little ɗaki ya kai kayan sa. Ta kwanto jikin hannunsa tana duban ƙyaƙyƙyawan fuskarsa. “Yayanmu nace makafa bawani ciwo nakejiba ALLAH. Kuma idan ban motsa jikin ai sai wani kuma ciwon ya taso”.

    Kanta ya shafa yana rungumota da ƙyau jikinsa. Ya sumbaci laɓɓanta da goshinta yana jera mata addu'a. Itama hannunsa ta sumbata ranta fes ƙaunarsa na ƙara shigarta jini da ɓargo.


        Kwana biyu dayin haka sai ga Mahma daga london. AK yaji matuƙar daɗin wannan zuwa nata, dan dama lokacin bikin su Adilah ta tabbatar masa da cikin Zinneerah ya shiga watanni bakwai insha ALLAH zatazo Nigeria. To shikam ya ƙudiri tunda tazo riƙeta zaiyi har sai matarsa ta haihu.

      Sosai Zinneerah ma ta nuna farin cikinta sosai na zuwan Mahma. Dan-danan ta gyara mata ɗayan ɗakinta na falon farko duk da dama fes yake. Bakuma wani amfani take da shiba garama da ƴan Danya sukazo tariyarar Yaya Sa'a sun kwana a ciki.

     Itama Mahma taji daɗin yanda suka tarbetan, tare da ɗunbin tausayin Zinneerah daketa fama, dan ga cikin nata yayi girma sosai Alhmdllh kamar ba ɗan wata bakwai ba. Kasama haƙuri tayi sai da tace, “Anya cikin nan ba ƴan biyu bane kuwa a cikinsa?”.

     Cike da kunya Zinneerah tai ƙasa da kai tana murmushi kawai. Sai AK dake saurarensune yace, “Ƴan biyu kuma Mahma?”.

       “Eh mana Abdul-Mutallab, ai girman cikin ne masha ALLAH kamar ba wata bakwai ba”.

       Kallon Zinneerah ɗin yayi shima da ƙyau zuciyarsa na fata da tabbatar wannan zance na Mahma. Yace, “To Mahma bamu saniba dai, amma ALLAH ya tabbatar”.

       “Amin to, amma baku dubaba kenan?”.

      “Wlhy Mahma banason wannan bin ƙwaƙwƙwafin, komai ya fito a cikin nan ina maraba dashi da so da ƙaunarsa”.

       “Alhmdllh aihaka akeso musulmi ya kasance Abdul-Mutallab, ALLAH ya rabasu lafiya”.

    Da “Amin” ya amsa mata. Zinneerah kuwa tayi a zuciyarta kawai.............✍


No comments

Powered by Blogger.