Makauniyar Kaddara 5

 


Page 5*


..........Lallai da gaske shirin biki ake na ƴar gata. Dan bama Inna kawai ba hatta da Atine dake aure Rimaye ta shiryama bikin. Ko kayan ɗakin Karima daga can akayosu. Ita dai Yaya Gajeje bata biye musu. Sai ma nuna musu illar ƙulla wannan aure takeyi. Dan ta tabbatar an cuci Zinneerah

. Tun abin bai kai hakaba take ma Inna magana amma bata saurarenta. Sai ɓacin rai dake biyo baya a tsakaninsu akan hakan. Zuwa yanzu kuma data tabbatar sunyi nisa saita zuba musu ido. Dan akwai ranar ƙin dillanci ai. Kuma nasihar baba ta shigeta. Dan shima da kansa yace ta barsu karta sake cewa komai akan auren. Inhar an cutama Zinneerah ne akan hakan ALLAH na nan baya barci.

         Tun ra da aka kawo lefe lafiya taima Zinneerah ƙaranci, a haka ta daure take komai na rayuwarta data saba. Harma ta ida zana jarabawarta ɗaya data rage ranar litinin. Sun kammala junior secondary school kenan suna jiran result kuma ya fito aga abinda ALLAH zaiyi.

         Biki kam dai shiryashi ake sosai kamar yaune aka fara aurar da ƴa a gidan. Ita dai Zinneerah nata ido ne kawai, sai idan ta keɓe ne takan sha kukan zuci. A randa aka saka Karima a lalle jikinta yay tsanani, har takaita da kaiwa kwance dole.

      Cike da damuwa Yaya Gajeje ta takura mata taci alala da suka girka a gidan saboda baƙi da sukazo daga marabar musawa dangin Inna. Da ƙyar Zinneerah ta iya cinye guda ɗaya sai amai. Kowa ya tausaya mata anata mata sannu. Harma wata ƙanwar Inna na cewa shawara ce a nemamata sassaƙe tasha. Itadai bata iya magana sai amsawa da kai harta samu ta koma ɗaki ta kwanta.

     Cikin tsoffin da sukazo daga maraba ne ɗaya ta dubi Yaya Atine dake gefenta tana shayar da ƴarta da take goyo. “Niko nace Atine”.

      “Na'am Gwaggo ladi”. Yaya Atine ta amsa tana kallonta tana maido hankalinta gareta. Wadda aka kira da Gwaggo Ladi tace, “Wanan ƴar uwar taku tayi aure ne dama bamu da labari?”.

      Da mamaki a fuskar Yaya Atine tace, “Gwaggo wai kina nufin Zinneerah? Indai itace batai aureba. Yaya zatai aure baku jiba”.

     Cikin waro idanu na alamar gulma tace, “Kanjakar ubancan kayyasa. To lallai idon Asabe a rufe yake a gidan nan bata bahimtar komai daɗa”.

      “Gwaggo miyasa kika hiɗi haka”. Yaya Atine ta sake faɗa tana duban Gwaggon nasu da ƙyau.

     “Uhm-uhm babu komai Atine. Kawai dai naga abinda yafi ƙarhin ganina ne. Dan wannan ɗiyar ciki ke ga jikinta, harma ya tasa gashi nan”.

      A razane Atine ta saki ƴarta ƙasa da dukan ƙirjinta tace, “Gwaggo ciki?!! Zinni ɗince ke da ciki!!?”.

     Yanda tai maganarne ya jawo hankalin sauran mutanen dake a gidan kansu. Ga ƴarta data saki ƙasa ta tsage da kuka saboda zafin faɗuwar da taji..

            Yaya Gajeje ma a ruɗe ta saki kwanon data ɗakko zata saka a sayoma Zinneerah kunu ko zata iya sha. Ta ƙaraso gasu Atine da sassarfa tana faɗin, “Atine wannan wane irin mugun alkaba'ine kike hiɗi dan ALLAH?”.

        Da sauri Atine tace, “A'a yaya Gajeje bafa ni na hiɗi ba....”

     “To waya hiɗi?”.

Gajeje ta katse ƴar uwar tata.

         “Kunga bafa zancen hayaniya bane ba Gajeje. Ku kira yarinyar tazo nan”. Gwaggo Ladi duk ta katsesu.


       Zinneerah na ɗaki kwance tana sauke numfashin wahalar amai da tayi wata cikin ƴan bikin ta shigo ɗakin tana ƙwala mata kira. Miƙewa tai daga kwancen da take a razane tana dubanta batare data amsaba.

    Matar tace, “Kinga taso ana kiranki a waje”.

         Batare da tunanin komaiba Zinneerah ta miƙe ta biyo bayanta cike da dauriya. Tana fitowa gabanta ya faɗi ganin kowa na gidan ya zubo mata idanu, har waɗanda ke a cikin ɗakin Inna duk sun fito tsaye cirko-cirko. Rasa ina zata dosa tayi dan ruɗiya. Sai da yaya Gajeje tai ƙarfin halin kiran sunanta cike da tashin hankali. Dan ita kanta kam zuciyarta ta fara gaskata zancan tsohuwar saboda wani irin canjawar da Zinneerah tayi, wanda ada sam hankalinta bai taɓa bata abu makamancin ciki ba akan canjin....

     Ƙarasowar Zinneerah inda suke ne ya katse tunaninta. Tsohuwa Gwaggo Ladi ta kamo hannun Zinneerah ta buɗe tafin tana kallo, ta kuma ɗago fuskarta ta gwale mata idanu nanma. Sai kuma tace ta buɗe bakinta ta turo harshenta waje. Ita dai Zinneerah babu musu komai yi take cike da tunanin ko wani ciwone ya kamata. dan a watani uku ɗin nan data dawo gida ƙwarai da gaske tanajin canji sosai a jikinta wanda batasan kansa ba.....

       “Wlhy wannan yarinyar ciki ne da ita Asabe. idanma baku yarda ba ku kaita ayi gwaji wajen likita”.

     Zancen Gwaggo Ladi ya katse tunanin Zinneerah. Yayinda a take gidan ya harmutse da salllami da gulma. Sam Zinneerah bata fahimci komai a zancen Gwaggo Ladi ɗinba, duk da yanayin mutanen dake gidan ya sake sakata a tashin hankali.

     A haukace Inna tazo ta kai hannu zata kai mata maguza wata ƙanwarta ta tare tana janye Zinneerah ɗin. “Haba Asabe, ita dake cikin wannan halin zaki kaima wannan bugun? Kamata yayi a bita a sannu asan inda al'amarin ya hito ai ko?”.

         “A ina ya hito banda wajen yawonta na tazubar Haule. Idan na hiɗi ya rinyarnan nabin maza sai ace sheri nake mata dan ban haiheta ba. Kwanan nan fa tahiya tai babu wanda yasan ina taje kusan mako huɗu sannan ta dawo. Amma da yake ubanta shashasha ne bai ɗauki wani mataki a kantaba. Wace irin makauniyar rayuwace wannan? Na rantse da ALLAH bata zaunamin gida da cikin rariya. Sai dai ta koma can gidan wanda ya ƙunsa mata masihwar su ƙarata tambaɗaɗɗiyar yarinya”.

      Yanda Inna ke masifa kamar zata haɗiye harshentane ya saka gidan yin tsit kowa yana saurarenta. Yayinda hajijiya take juyama Zinneerah garin a hankali. Babu zato sai ganinta kawai akai ƙasa ta zube.

     Babu wanda yay yunƙurin taimaka mata sai Sa'a dake kuka tun farkon fara maganar, ta taho da gudu ta durƙusa gabanta tare da ɗagota jikinta tana jijjigata. Tsawa inna ta daka mata akan ta tashi a wajen kota tsine mata.

     Cikin kukan Sa'a ke girgizama Inna kanta. “Haba Innarmu! Haba Innarmu!. Wlhy Innarmu Zinni ba ƴar iska bace. Wlhy Zinni bata iskanc......”

    Ta kasa ƙarasawa saboda kukan daya sarƙeta. Yaya Gajeje ce ta tako inda suke itama tana share hawaye da bakin zaninta. Ta durƙusa ta kamo kan Zinneerah dake a jikin Sa'a ta maido kan cinyarta tana fashewa da kuka maiban tausayi.....


         Bayyana irin tashin hankalin da Zinneerah ta tsinci kanta a cikin wannan rana da duk wani masoyinta ma ɓata lokacine. Hatta da maƙiyan nata jimami suke nunawa a zahiri, a baɗini kam ransu fari tas musamman ma Inna da ke ganin fatanta ya tabbata.

       Kamar yanda Zinneerah ta yanke jiki ta faɗi sai da aka zuba mata ruwa haka Baba ma da labarin ya riskesa tamkar saukar aradu ya zube babu numfashi sai da aka zuba masa ruwa ya farfaɗo da ƙyar.

      Kafin wani dogon lokaci garin ya ɗauki zance Zinneerah tayi cikin shege. Tofa abin nema ya samu ga masu ƴancin faɗin albarkacin baki. Wasu suce mugun alkaba'in Inna ne ya kamata, wasu suce wahalar da Innar ke batace ta kaita da fara bin mazan ai. Wasu suce babu wani dama halintane. Dan kawai tana shan wahala a gidansu sai ta bi maza.

     Kowa dai da inda nasa furucin ke sauka. Duk da ba yaune ainahin ɗaurin aure ba sai ga mutane na tururuwar shigowa gidan gulma da son ganin ƙwaƙwaf. Ƴammata kam harda waɗanda Karima ma bata gayyata zaman ƙunshin ba sai gasu.

      Inna kam tanata zabga bala'i sai Zinneerah ta bar mata gida ƴan uwanta na tausarta. Yayinda Zinneerah ke a ɗakinsu tare da Baba da Yaya Gajeje da Sa'a. Sai wasu ƙanen Baban maza su uku da mace ɗaya sun turketa akan saita faɗa musu a ina ta samo wannan jidalin?…

      Kuka Zinneerah keyi tamkar numfashinta zai rabu da gangar jikinta. A karo na babu adadi ta sake faɗin, “Wlhy! Ta-kwaran-kwatsa Kawu ban taɓa aikata iskanci ba. Wlhy ni banda ciki.”

       Cikin daka mata tsawa Kawu haruna yace, “Kinci uwarki Zinni. Su waɗanda sukace kinada cikin zasu maki ƙarya kenan? Bayan duk ga alamomin mai juna biyu tattare da ke. Idanfa baki hiɗi mamu wanda kukai wannan lalatar to kuwa kina barin garinga kije can ki nema wasu iyayen bamuba. Dan bamu zama da mai halin banza cikin zuri'armu kau...”

        “Ai bama barin gariba ni nan da kake gani rami zansa amani na bizneta da ranta har sai ta mutu idan bata hiɗi mamu gaskiya”.

     Tirƙashi. Tunfa su kawu nabin Zinneerah da lallami akan sanin gaskiyar magana har takai Kawu Sabi'u da fara bugunta amma ta kafe akan itafa bata taɓa aikata abinda ake tuhumarta ba. Tsabar tashin hankali kowa kansa ya ɗauki zafi. Baba ma ya kasa magana sam.

     Ganin suna neman halaka yarinya wata a cikin ƴan uwan Inna dake aure a kankia tace, “Kunga karkuce ta wannan hanyar zaku tuhumi yarinyarnan. Sannan har yanzu babu tabbacin cikinne a jikinta ko saɓanin haka. Kamata yayi ku sami likita yay mata gwaji, idan an tabbatar cikinne sai a bita ta hanya mai sauƙi a binciketa bawai ta kwakwazo da azabtarwaba. Dan yanzu idan cikinne ai sai kuyi mata lahani ita da shi k.......”

       “K Halima bamu son tsarin banza da wohi. Kinason hiɗin ita Yaya Ladi ƙarya tayi kenan da tace akwai cikin? Bayan duk wanda ya kalla wannan sheɗaniyar yarinyar zai tabbatar da alamomin mai ciki tattare da ita...”

       “Ba haka nake nihi ba yaya Asabe. Tayaya zan ƙaryata Yaya Ladi ni kuwa. Ni dai ina nuna maku muhimmancin bin komai a sannune. Yanzu wannan ruɗama yarinyar tunani da bugun nata da akeyine zaisa ta hiɗi gaskiya? A ganina idan anbi komai a sannu sai a kamo gaskiyar al'amarin da mahwarinsa basai anbi hanyar ilatata ba a dawo kuma ana dana sani”.

    Inna zata sake magana Yaya Gajeje ta katseta. “Maganar Gwaggo Halima gaskiyane. Ya kamata mubi komai a sannu kawu. Dan kowa yasan halin Zinni bazata aikata wannan al'amari da ganganba inma har ya tabbata hakane. Ba muba ko jama'ar gari idan zasu hiɗi gaskiya sunsan Zinni yarinyace mai nutsuwa da haƙuri. Wlhy inaji a raina inhar da gaske ciki ne a jikin Zinni sai dai ɗayan biyu ne ya hwaru. Kodai wani la'ananne ne yay mata wayo ya ɓata mata rayuwa. Ko kuma acan inda ta baro wani yay mata hin ƙarhi ya aikata mata wannan zaluncin. Ku tunafa yarinyarnan nemarta akai aka rasa rana tsaka. sai kuma gata ta dawo babu zato. Abin mamaki kuma tamkar an rihe mana bakuna har yanzu bamu sake bi takanta muji yaya akai tabar garinga ba ta kuma dawo? Miya hwaru da ita data tahi? Ina taje? Waye silar hitar tata? Duk bamu binciketa b..........”

       “Gajeje!!!” 

  Inna ta faɗa da wata irin mahaukaciyar tsawa tana nunata. Ta cigaba da faɗin, “Na rantse da ALLAH idan baki hita batun wannan ƴar iskar yarinyar ba daga yau sai na tsine maki a gidan nan ke da Sa'a. Har uban waye zai hiddata a gida da gari banda abokan iskancinta wanda ga sakamakon abibda takeyi ɗin nan ya bayyana kowa ya gansa”.

      Dubanta Gajeje tayi zatai magana. Sai kuma mita tuna oho tai shiru kawai tai ƙasa da kanta tana sharce hawayen dake sakko mata.


        Har dare gidan ya gagara komawa dai-dai. Zinneerah kam tana can ƙuryar ɗakinsu ta ɓuya tana cigaba da kukanta. amma duk da haka bata kasa jiyo yanda ake aibantata a tsakar gidanba ita da mahaifiyarta a bakunan wasu a cikin dangin Inna. Yayinda ƴammata masu zaman ƙunshin Karima suka fara raira mata waƙa cikin habaici da izgili kamar yanda Karima ta sakasu.

     Babu wanda ya hanasu, dan Yaya Gajeje tabar gidan tun ɗazun. Baba kuwa yana zaune daga can bayan runbunsu shiba mai rai ba shiba gunki ba. Sam zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa basa aiki irin na mutane.

        Duk da ƙarancin shekarunta yinin yau ya sake tabbatar mata da rayuwa ta sake kaita wani ajin jarabawar da yafi zaman gidansu ƙunci da tashin hankali. Ita dai ko Al-qur'ani aka bata zata iya rantsewa da shi akan bata taɓa aikata iskanci ba, amma sai gashi yau an wayi gari ita ake kira da suna mai ciki, cikinma cikin shege. Ta sake fashewa da kuka mai cin rai.


★★★


        Zamu iya cewa a wannan dare barci ɓarawo ne kawai ya saci Zinneerah kasancewarsa gwanin iya sata. Amma badan taji sha'awar yinsaba ko buƙata.

      A kiran sallar farko ta tashi, taji daɗin jin gidan shiru alamar kowa bai tashiba. Ta lallaɓa ta fito zuwa bayi. Bayan ta kammala lalurarta tai alwala ta sake shigewa ɗakinsu. Daga haka bata sake fitowa ba har sai da rana ta haska. Zuwa lokacin gidan ya cika da hayaniyar baƙi da yaransu. Kamar jiya dai kowa da zancen cikin nata ya tashi a baki, hakan yasa ta sake maƙurewa a ɗaki taƙi fitowa.

    Tana zaune kanta cikin gwiwarta taji muryar Gwaggo Laritu ƙanwar su baba na kiran sunanta. Kanta ta ɗago muryarta data sha kuka a dusashe tana amsawa. Fuskar Gwaggo Laritu a haɗe tace, “Taso ki hito”.

       Sosai gabanta ya faɗi, sai dai babu damar musu dole ta miƙe tana rangajin yunwa da damuwa. Kamar jira ake ta fito tsakar gidan yay tsit idanu caahh a kanta. Tai ƙasa da kai zuciyarta na tsitstsinkewa dan tashin hankali...

      “Munahika, ƴar iskar yarinya. Ƙyahwa ta duƙar da kai kamar balamar tunkiya tunda kin kwaso mamu abin kunya”.

    Inna ta faɗa tana jan tsaki. Ita dai Zinneerah kanta a duƙe bata yarda ta kalli kowaba. Ta kuma kasa ɗaga ƙafarta dan batasan ina zata dosaba. 

        Sa'a ce ta taso daga inda take zaune tazo ta kama hannunta, itama muryar tata a dasashe alamar tasha kuka tace, “Muje Zinni, su baba na jiranki a zaure”.

     Da ƙyar ta iya ɗaga ƙafafunta tabi Sa'a har zauren. Baba na zaune shi da su Kawu Haruna. Ƙasa ta zube cikin rawar murya tana gaishesu. Babu wanda ya karɓa mata, sai Gwaggo Laritu ce tace, “Ya kamata mutahi kar rana tai tsaka tunda ta hito”.

     Nanma babu wanda ya iya cewa komai, sai miƙewa da su kawun sukai amma banda Baba da kansa ke ƙasa. tunda Zinneerah ta fito ko motsi baimayiba. Koda sukai masa sallama zasu tafinma bai motsa ba. Bai kuma ce uffanba har suka tasa Zinneerah gaba suka fice.

      Mashina biyu dake jiransu suka taras a ƙofar gida. Kawu Sabi'u da Kawu Haruna suka hau ɗaya. Ita kuma da Gwaggo Laritu suka hau ɗaya batare da tasan ina suka nufa ba. 

         Ƙasa zinneerah tai da kanta har suka baro cikin garin Danya. Wanda tasan tunda kasancewar safiyane kowa yaga tahowar tasu, waɗandama basu ganiba zasu samu labari ga waɗanda suka gani ɗin.

          

      Har cikin Kusada masu mashinan nan suka kaisu babban asibitin Kusada. Kasancewar ɗan mashin ɗin daya goyo su Kawu babban ɗan Kawu Sabi'u ne shine yay musu shige da ficin komai har suka sami ganin likita kusan sha ɗaya na rana. Duk da a matuƙar tsorace Zinneerah take bataƙi amsa tambayar da duk likitan yay mata ba. Bayan ya gama mata tambayoyin yasa aka kira masa wata matashiyar budurwa. Zinneerah ya nuna mata yana faɗin, “Maryam kuje da ita tai hitsari akaima Bashir”.

      Budurwa daya kira da Maryam ta amsa da to a girmame tana duban Zinneerah. Tashi Zinneerah tayi ta bita zuciyarta na ƙara shiga damuwa da firgici. Bayan ta kaita wani banɗaki tayi fitsari a wata roba suka fito. Zinneerah wajensu Gwaggo Laritu ta dawo. ita kuma Maryam ta tafi cika umarnin likita.

     Sunyi zaman kusan mintuna arba'in Maryam tazo ta wucesu zuwa ofishin likita. Dansu tuni sun dawo waje sunba sauran marasa lafiyar damar shiga suma.. Kusan mintuna goma Maryam tazo tai kiransu.

     Kamar ɗazu daga ita sai Gwaggo Laritu suka shiga. bayan sun zauna likita ya dubesu da murmushi yana faɗin, “Masha ALLAH mamana ga sakamakon gwajin hitsarin da mukai mata ya hito. Duk da dama dai kafinma hakan na fahimci ciwon na ƙanwata abin so ne. Amma duk da haka dai nafi yarda da'a gwada ɗin......”

       Cikin ƙosawa Gwaggo Laritu tace, “To madallah, mike damunta?”.

       Sake faɗaɗa murmushi likita yay yana duban Zinneerah da kanta ke a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta. “A'a Inna ba wani abu baneba face ƙaruwa muka samu. Tanada ciki na kusan watanni huɗu. Kuma Alhmdllh yana cikin ƙoshin lafiya kamar yanda itama alamomi suka nuna tana cikin ƙoshin lafiya, sai dai kuma ya kamata a ringa kula da abincin da zataci saboda shima yaron cikin nata ya samu nagartaccen raino.......”

     Sam Gwaggo Laritu da Zinneerah ba fahimtar bayanin likitan sukeba tunda ya ambaci ciki. Dan Zinneerah ma wani irin hajijiya take gani. Tun ofishin na juya mata har ta koma ganin duhu a cikin idanunta. Sai kawai ganinta sukai a ƙasa daga ita har kujerar robar da take zaune a kai.

       “Ya subahana”. Doctor ya faɗa yana zabura saboda faɗuwar Zinneerah. Hakan kuma yay dai-dai da dawowar Gwaggo Laritu datai suman wucin gadi itama hayyacinta. Yayinda su Kawu Rabilu suka shigo da gudu saboda jin sallalamin da likita da budurwar nan Maryam keyi akan Zinneerah da alamomi suka tabbatar da suma tayi............✍



“Hummmm!!!! Turƙashi, masu karatu wannanfa shi ake kira da ANA DARA GA DARE YAYI. shin yaya akai hakane? Yaya kuma za'ai? Mi kuma zai faru?. Gadai likita ya tabbatar da ciki a jikin Zinneerah baiwar ALLAH. yayinda Zinneerah ta tabbatar mana kuma bata taɓa iskanci da kowa ba. Shin tayaya aka samu ciki idan babu mahaɗi? Shin wanene uban wannan cikin? Ta yaya aka samar dashi? Da sanin Zinneerah ko fyaɗe ne? Mi Inna ta sani akan barin Zinneerah gida? Anya kuwa babu lauje cikin naɗi masu karatu? Ina mahaifiyar Zinneerah? Yaya Baba zai kasance da tabbatuwar wannan cikin dake jikin ƴarsa dake a matsanancin rayuwa a gidansa? Yaya jama'ar garin Danya zasu cigaba da ɗaukar Zinneerah yanzu? Yaya rayuwar Zinneerah zata cigaba da kasancewa a gidansu da garinsu?.


Wannan amsoshin duk suna ƙumshe a cikin littafin MAKAUNIYAR ƘADDARA da zai zo muku akan naira 300 kacal insha ALLAH. Dan girman ALLAH ina roƙonki ƴar uwata. Kibi ta hanyar data dace domin mallakar naki cikin kwanciyar hankali. Idan kin zama mai shigewa gaba wajen girmama sana'armu kema sai ALLAH ya ɗaga darajar taki komai kanƙantarta. Idan kin zama jagora ko mai burin ruguzamu UBANGIJI ya fimu sanin ke wacece.. Fatanmu kowa ALLAH yay riƙo da hannunsa akan neman halak ɗinsa. Dan ALLAH kuzo ku saya kafin ku karanta. Dan ALLAH idan kin saya karki zama ɗaya daga cikin masu fitar mana dan kawai ganin mun koma baya ko kuntata mana. Ku tuna da tarin alkairinmu na baya gareku, koda bazaku rama manaba karku cutar damu dan girman ALLAH mun roƙeku dan shine kaɗai zamu iya haɗaku da shi🤓🙏🏻.


ALLAH kai mana jagora. Yanda zamu fara lafiya ALLAH ya bamu ikon gamawa lafiya. Masoyanmu da basu gajiyawa wajen sayen hajarmu da mun fitar muna sake godiya a gareku, ALLAH yabar zuminci. Masoyanmu da basu taɓa sayaba kuma ku garzayo dan bana Zafafa shiri sukai na musamman domin farin cikinku. Masu jira a fiddo ku karanta kuma dan ALLAH kuzo ku biya ku mallaki naku a wannan karon kuma sai ALLAH ya kawo muku Customers akan naku kasuwancin. Mun gode. Mun gode irin trillions ɗin nan😘😍😘😍🤗😊😉.


*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*


Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.


No comments

Powered by Blogger.