Makauniyar Kaddara 48
Page 48*
...........Lefe kam yayi sai dai makiyi ya kushe, dan daga na Momie harna Mahma sai dai ace ALLAH ya saka musu da alkairi, da AK yace sunyi yawa akai ɗaya Baffah cayay duka za'a kai, idan yay wasama shima sai ya haɗa nashi dole an haɗa an kai. Dole AK yay gum da bakinsa dan yaga waɗanan iyayen amaryar sai da lallaɓa.
Kamar yanda ake shiri gagarumi a shira's family da gayyatar dangi lungu da saƙo hakama su mmn sadiq suke nasu shirin, dan tuni Gwaggo Maryam ta iso kano sun ɗinke itada ƴar uwarta suna shawararsu, hakama Abba ba'a barsa a bayaba wajen gayyatar dangi da shirya yima Zinneerah kayan ɗaki duk da AK yace basai sunyi komaiba, dan koba shine ya auri zinneerah ba dole shine mai mata kayan ɗaki matsayinsa na babban yaya.
Lokacin daya ambata hakan murmushi kawai Abba yay da sanya masa albarka, a zuciyarsa yana mai jin daɗi da taya Zinneerah samun miji irinsa.
A danya ma baba shirinsa yake da ƴan uwansa batare da sanin Inna ba, dan Baffah da kansa ya kira Baban a waya ya sanar masa hukuncin da hajiya iya ta yanke akan tarewar, baba baiji komaiba yace ALLAH ya kaimu. Daga haka suka fara shirye-shirye.
Akan zuwan su mmn sadiq can kuwa har agama biki sun gama magana da Abba. Dan ana gobe tariya can zataje, danginsu na ɗanmusa ma acan zasu sameta, idan za'a ɗakko amarya washe gari su biyota zuwa kano insha ALLAH.
Zinneerah dai nacam nashan gyaran wajen hajiya falmata lungu da saƙo, ita kanta tasan ta gyaru sai dai Alhmdllh, har tsara yanda zataima su meenal yanga take a ranta tana murmushi. Sai dai kuma iya hasashenta ta rasa dalilin wannan gyara haka, duk da yanda hajiya falmata kan zauna tana mata lectures akan abinda ya shafi aure kan tsunduma zuciyarta a dogon tunani da nazari. Har takan tambayi kanta anya ba aure akai mataba kuwa?. Rashin samun amsa ke sakata jefar da tunanin ta kama wani daban.
A randa Zinneerah ke cika kwanaki shidda gidan hajiya Falmata aka kwashi akwatinan lefenta zuwa gidan Abba. kasancewar ansan da zuwansu sun sami tarba mai ƙyau duk da dai daga nan Danya zasu wuce. Sai da aka buɗe kaya Abba dasu Mmn halima suka gani. Su mmn sakina ma dai sun shiga layin ƴan kallo suna haɗiyar zuciya, daga ƙarshe suna shiga ɗaki Sakina harda kukanta rurus. Ita kanta maman tasu kukan zucin take wanda yafi na fili ciwo dacin rai.
Maƙwafta sun shishshigo suma suka sanya albarka kafin masu binsu Danya su kammala shiri su sake ɗunguma domin kaiwa can. Dole badan mmn sakina tasoba akai tafiyar da ita, itako mmn halima da yaranta biyu ai sune ƴan gaba-gaba, sai maƙwafta da ake gaisawar mutunci da matar Nazifi da suma za'aje dasu.
A ƴan gidansu AK kuwa Mommy ce, sai Adilah data maƙale, sai Momie da Ummi, da su Aunty Khadija yaran Momie na farko su biyu. Sai matar Alhaji Yusif. Sai kuma mahaifiyar Dr Mahmud. Gaba ɗayansu dai mota huɗu sukayi harda ta kaya, suka tafi a jere gwanin sha'awa dan su Khalipha ne masu kaisun, karan farko da zaije tushen Zinneerah.
Anan ɗinma dai ansan da zuwansu, dan sai da safe baba yake sanarma Inna, amaryarsa kuwa tasani kusan kwana biyu, da itama akai aikin abincin baƙin a gidan Gwaggo Laritu harda Yaya Gajeje ma.
Ƙarfe ɗaya da wasu mintuna motocin su Khalipha suka shiga cikin garin Danya. Gidan maigari suka fara isa dan can su Haneef suka sani, daga can aka saka yaro musu rakkiya dan babu wanda yako fito a motama a cikin matan.
Cike gidan yake da ƴan uwa domin amsar lefe, dawowar su Gwaggo Laritu gidan kenan su Mommy suka iso, an musu tarba ta mutuntawa da girmamawa, inna dai shigowar waɗan nan ƴan gayun matama neman birkitata yayi. dan duk iya jarabarta sai gata tai muƙus sai kallo da idanu.
Gidan baba yasha gyara aƴan kwanakin nan, dan ɗakuna ya sake zubawa sabbi aka kuma siminte tsakar gidan tsaf, ga amaryar baba akwai tsafta dan tunda tazo gidan ya ƙara ɗaukar saiti. Musamman yau ma datai masa gyara na musamman ita da Sa'a. Dan jiya akai taron sunan Karima duk da dai baimayi wani armashiba. Sai uwar rigima da aka kwasa tsakanin dangin Babawo dana Inna. Saboda Babawo har yau baizoba yakumaƙi cewa komai, ita kuma idan an tambayeta sai tace bata masa komaiba.
A ƙarƙashin bishiyar gidan aka shimfiɗa musu tabarmi dansu sha iska, aka kawo musu lemuka da ruwan leda da su baba suka tanada domin su kawai. Ba ƙaramin daɗi su Mommy sukaji ba a yanda aka tarbesu da girmamawa da mutunci. Bayan anyi gaisuwa da tanbayar iyalan juna aka shigo da akwatunan da suka saka ƴan uwa fara callara guɗe-guɗen da suka nema jefa Inna a hauka. Dan duk yanda taso ta daure ta kasa sai gata ta shiga zage-zage.
Cikin mamaki da ɗaukarta mahaukaciya su Momie ke kallonta, yayinda su Gwaggo Laritu da sukasan hali basubi takantaba, sai maida hankali a murna da farin cikin Zinni tayi goshi da sukai, suna kuma yaddama Inna habaici akaikaice. Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya sake haukacewa da makwafta da yara ƴan kallo, dole aka maida su Mommy ɗaki dan suma su samu suyi salla. Su dai yanda mutan garin keta arerewa akan wannan lefe nasu sai abin ya ƙayatar dasu ainun, Adilah harda yin video dan ita kam wani ƙayatar da ita suke da sakata nishaɗi, sai washe baki take ranta fes.
A waje ma dai yanda mata ke gudun shigowa gidan da yara sai abin ya dinga saka su Khalipha dariya, da birgesu. Dan suma suna zaune ne a ƙofar gidan a ƙarƙashin bishiya ni'imtacciyar iska na kaɗasu.
Haka suka kasance a ƙauyen danya suna kallon yanda ake kai kawo akan ganin lefe. Sai da sukai sallar la'asar sukai haramar baro garin cike da alkairi da tukuyci, duk da sunƙi amsa Baba yace indai basu rainaba su amsa dan ALLAH. Jin furucinsa yasa dole suka amsa suna mai yaba ƙoƙarinsa da dattako. Daga haka akai musu rakkiya suka shiga motoci suka ɗauka hanyar tafiya kano akan sai kuma ranar juma'a sunzo ɗaukar amaryarsu da zata iso zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu itama.
Koda suka taho a hanya labarin yanda al'amarin ya faru suketayi, dan sun baro Inna ta birkicema jama'a kamar sabuwar kamu a hauka. Duk da dai Yaya Gajeje da Karima na ƙoƙarin tausarta. Gida su mmn halima suka wuce, suma suka wuce nasu gidan inda suka kaima hajiya iya labarin farin ciki. AK na zaune a dining yana cin abinci shi da little yana jinsu, sai dai uffan bai tofaba bayan sannu da zuwa da yay musu.
Adilah ce tazo inda yake bakinta a washe ta sumbaci little da tunda tazo take maƙalle da yaron, cikin sabawa daya farayi da ita ta bashi nata kumatun shima yay mata kiss suna dariya. AK dake kallonsu yay ɗan murmushi kawai batare da yace komaiba.
Zama tayi tana fara bashi labari, tare da nuna masa video ɗin da tayo a waya. Shi kansa abin ya burgesa da bashi dariya. amma sai baiyiba yaɗan murmusa kawai yana ajiye wayar da dubanta cike da kulawa.
“Yaushe zakije ki gaida su Mammah?”.
A take fara'ar fuskarta ya ɓace, ta shagwaɓe fuska idanunta na cika da ƙwalla. “Bro ka barni Please basai najeba, kuma bama kace tana katsina ba tunda mukazo da Mahma?”.
“Kema ai katsinan zakije, gobe idan ALLAH ya kaimu zanje sai muje tare na baroki can ki biyo Mahma ranar biki”.
Hawayen da suka cika mata ido suka gangaro, sai kawai ta miƙe tabar dining ɗin ta shige ɗakin Hajiya iya. Binta yay da kallo kawai yana dariya a ransa. Dama tsokanarta kawai yakeyi, shima yaso zuwan amma Mahma ta hana, tace ya bari ai zata ɗakko su Mammah suzo wajen bikin dan dole suma dangin mahaifiyarsa su kasance ai tunda aure abin farin cikine ga kowacce zuri'a. Yanzu kuma Mammah ɗin kanta a zafi yake zuwansa bazai haifar da ɗa mai ido ba.
_________________________________
A washe garin da aka kai lefe hajiya iya ta samu Zinneerah a gidan Hajiya Falmata ita da Adilah. Yanda Zinneerah ta ƙara canjawa a cikin sati ɗaya ya saka hajiya iya jin daɗi matuƙa, hakama Adilah da sau ɗaya kawai suka taɓa ganin juna a london rungume tayi dan tunda ta ga yarinyar dama ta shiga mata rai, da Hajiya iya ta bata labarin komai kuma shima AK ya bata sai ta ƙarajin tausayi da ƙaunar Zinneerah, tare da ƙara taya ɗan uwanta murnar samun mata dai-dai da shi da zata kawo ma rayuwarsa farin ciki tunda Farah taƙi kwantar da hankalinta ta daina biyema Mammah ta riƙe mijinta kamar yanda ta fara a farkon aurensu.
Daɗin yanda Zinneerah tai ƙyau mai ɗaukar hankali yasa hajiya iya harda ƙarama hajiya falmata kuɗi tana jera mata tagwayen godiya. Cike dajin daɗi itama hajiya falmata tace, “Ai hajiya namaso ace daga gidan nan sai gidan mijinta za'a kaita, amma hakanma babu laifi tare dani zata tafi can ƙauyen muɗan ƙarasa abubuwan da suka rage”.
Hajiya iya taji daɗin wannan karamci na hajiya falmata, dan duk da yanda Zinneerah ta canja kogi bayaƙin ƙari. Da wannan damar hajiya iya ta zauna ta sakema Zinneerah nasiha, a yau kuma ta sanar mata an ɗaura mata aure amma bata sanar mata da waye ba. Share-share sai ga Zinni na kuka da hawaye tana kallon haijiya tamkar wata sokuwa.
Cike da kulawa hajiya iya ta kamo hannunta cikin nata da sigar lallashi tace, “Nasan bamu ƙyauta mikiba Inno, amma insha ALLAH wannan shine gatan da zamuyi miki na har abada. Ki saka a ranki wannan itace taki nasarar cin jarabawar, insha ALLAH nasan bazakiyi kuka ba a wajen wanda muka baki, inamiki fatan alkairi da tarin farin ciki mai ɗorewa a rayuwarki da rayuwar aurenki”.
Kasa magana Zinneerah tayi sai kuka, ta faɗa jikin hajiya iya tana abinta. Itace kuma aka ɗaurama aure bayan taci alwashin bazata taɓa aureba. Gaskiya da anyi shawara da ita da haka bata kasanceba, batason tai aure a gorantama little, batason tai aure a aibantata akan ta taɓa haihuwa a waje. Bata da burin daya wuce yin karatu mai zurfi a rayuwarta, sai dai kuma duk waɗanan burikan nata da farga basu kai daraja da kimar hajiya iya ba a wajenta. Ta cancanci sadaukar mata da komai kodan alkairinta a gareta. Takumayi imani hajiya iya bazata badata ga wanda zata cutuba insha ALLAH, dan haka zatai haƙuri tayi biyayya a gareta insha ALLAHU. Ashe shiyyasa mmn sadiq keta mata nasiha mai harshen damo ita da hajiya falmata.
Lallashinta sosai hajiya iya tayi da sake mata nasiha itama tana hawayen, dan dauriya dama kawai takeyi, amma harga ALLAH tana tsananin ƙaunar yarinyar, wannan kuma hukuncine na ALLAH mai saka soyayyar wani a zuciyar waninsa dominsa badan wani abu dake garesaba. Sannan ta sanar mata yau za'a kaita danya wajen babanta, daga can za'a ɗakkota insha ALLAH zuwa gidan mijinta.
Nanma dai Zinni tayi kuka dajin fargabar tunkarar garin nasu data baro bisa ga dalili mai ƙarfi, takumaji ɗokin zuwa taga babanta da akace ya dawo da ƴan uwanta kuma.
Hajiya iya na gidan har Zinneerah da hajiya falmata suka kammala shirinsu na tafiya, sai Saifudden da zai kaisu wanda ya iso gidan hajiya Falmatan daga baya ya samesu.
★★★★★
Koda suka baro gidan hajiya Falmata gidan mmn sadiq suka nufa domin ɗaukar Gwaggo Maryama, ai ko Zinneerah nayin arba da ita ta faɗa jikinta tana kukaama. Ta basu tausayi daga ita har maman sadiq, to amma wannan shine kawai gatan da zasuyima rayuwarta koda ace babu ransu ta dinga tunawa sun mata gata. Dan little ga mahaifinsa kawai zai kasance itama ta samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya. Lallashinta suka sake zamanyi da mata nasiha, kafin Gwaggo Maryama ta shirya su fito dan da ita zasu wuce danya kafin su Mmn sadiq su biyosu suma daga baya.
Tunda suka ɗauki hanya Saifudden ne kawai ke hira da hajiya falmata da Gwaggo Maryama, itako tayi shiru lafe cikin kujera idanunta a lumshe. Kasancewar tafiyar ba ita kaɗai bace sai taji fargabar tunkarar danyan ta ragu mata a zuciya. Har suka iso gidan mutun ɗaya suka ɗauka hanyar kusada bata buɗe idoba. Sai da taji sun hau hanyar Danya ta buɗe idanu da kallon hanya cike da kewar garinta da tunano abubuwa masu yawan gaske da suka gudana. Isowarsu cikin garin yasa zuciyarta karyewa, sai gata tana hawaye shaɓe-shaɓe.
Zuwa yanzu kam ƴan Danya sun saba ganin yawan shigowar waɗanan manyan motoci, dan haka kai tsaye aka fara ƴan ƙananun maganar cewar angon Zinneerah ne yazo.
Su Zinneerah dai basusan anaiba, dan motar na tsayawa a ƙofar gidansu daya sha gyaran biki da aketa shirye-shiye sai zuciyarta ta ƙara karyewa. Itace ƙarshen fitowa jiki a sanyaye, sai da ta ƙarema anguwar tasu kallo da yara da suka baibaye motar waɗanda takeda tabbacin babu wanda ya shaidata, wasuma basu santaba. Murmushi tayi a karo na farko da ambaton Alhmdllhi cikin matuƙar rauni.
Da sauri ta buɗe idanun nata saboda jin maganar baba dake fitowa yanama Saifudden sannu da zuwa. Juyawa tai a hankali ƙirjinta na harbawa da sauri-sauri. Shima baban tunda idanunsa suka sauka akanta dukkan maganar bakinsa ta gagara fita. Yay tsai yana kallonta zuciyarsa fal wasiwasi. Tabbas fuskarnan dai ta ɗiyarsace, kuma irinta tsohuwar matarsa mafi soyuwa a garesa. Sai dai kuma yana tantama ace Zinneerah ɗinsa ce ta zama budurwa haka tamkar wata jinin larabawa. (Dan gyaran datasha ya sake ƙawatata da ƙyawu mai ɗaukar hankali)
A wani irin slowly Zinneerah ta nufi baba, batama san ta faɗa masa a jikiba ta fashe da kuka ba. Hakan yayi dai-dai da isowar Tinene ƙofar gidan wadda tun ɗazun aka aiketa amma sai yanzu take dawowa gidan, dan yanzu bata samun damar fita yawonta saita hanyar aikan.
Da mamaki take kallon wadda ke runme musu da baba, dan haka cikin sassarfa ta nufi cikin gidan kai rahoto. A zabure Inna data gama yima yarinyar karima wanka ta miƙe, hakama Sa'a dake wanke-wanke. Karima ma madai da Yaya Atine dake a cikin ɗaki sai gasu waje wuff babu shiri. Yaya Gajeje dake can gaban murhu ita da ɗiyar Baba Sabi'u suna suyar naman ragon sunan Karima suma dai duk duban Tinenen sukai, amaryar baba dai datasan ina zancen ya dosa tana ƙofar ɗaki zaune tana gyaran ƙumba da tsohon cikinta, murmushi kawai tayi hankali kwance. Kafin bakin wani ya samu damar furta kanzil sai ga baba ya shigo baki washe yana sharar ƙwalla, hannunsa riƙe da Zinneerah dake kuka rurus. Hajiya Falmata da Gwaggo Maryama biye dasu suna faman murmushin jin daɗi.
Yaya Gajeje ce ALLAH ya bama ikon gane Zinneerah, a take ta saki ludayin hannunta tana ƙwalalo idanu waje da faɗin, “Zinneerah!!”.
Da gudu Zinneerah ta saki hannun Baba tai kan Yaya Gajeje. Bata damu da a yanda yaya Gajejen takeba ta faɗa jikinta suka saki kuka tare. Tuni Sa'a ta saki soson wanke-wanke itama tayo kansu. Su kansu su Yaya Atine da ba ƙaunar Zinneerah ɗin sukeba, kuma tunda aka kawo kayan lefen nan nata ƙiri-ƙiri suka nuna hassadarsu suda Inna basu san sanda suka nufo ƴar uwar tasuba suka haɗu wajen rungumeta.
Hakan da sukai ya matuƙar saka baba jin daɗi, yayinda Inna ta daka musu wata irin gigitacciyar tsawa. Sai dai ina su bama susan tanaiba. Amaryar baba kuwa tashi tai da ƙyar tanama su Gwaggo Maryama barka da zuwa, waɗanda sai yanzu Inna tama gansu. Gabanta ne yay matuƙar faɗuwa datai tozali da fuskar Gwaggo Maryama, dan sarai ta ganeta. A kiɗime tace, “Dangin Hauwa a gidana?”. Karaf kuwa sai a kunnen baba. Kansa tsaye yace, “Hauwarma tana nan tafe a gidan naki”. Ya raɓata ya wuce abinsa dan tabarma zai amsa ya kaima Saifudden.
Ba ƙaramin dukan ƙirjinta furucinsa yayba. Tai baya tana neman faɗuwa ALLAH ya taimaketa ta dafe bango. Babu wanda ya lura da halin da take ciki dansu ta murnar ganin ƴar uwarsu sukeyi.
“Zinneerah kece kika koma haka kamar wata ƴar ƙasar waje?”. Yaya Gajeje ta faɗa tana sharema Zinneerah hawayenta, itako murmushi kawai take ga hawaye shaɓe-shaɓe.
Sa'a dake riƙe da hannunta tace, “ALLAH na gode maka daka nunamin wannan rana da naketa mahwalki da fatan gani, nagodema UBANGIJI daya maido ƴar uwata gida cikin kamala da mutunci harda igiyar aure akanta”.
Yanda take maganar da kuka ya sake raunana zuciyar Zinneerah dasu Gwaggo Maryama da amaryar baba ta sama tabarma a ɗakinta, dan suna jiyosu. Sake faɗawa jikin Sa'a Zinneerah tayi tana sakin wani sabon kukan.
Sai a lokacin baba daya dawo ɗaukama Saifudden buta zaiyi alwala yay sallar la'asar ya ɗauka hanyar komawa ya lura da halin suma da Inna ke ciki. Sallallami ya fara da nufarta, a take suma hankalinsu ya dawo kanta duk suka juya. Ita Zinneerah ma sai yanzu idanunta sukaga Innar.
Ruwa aka yayyafa mata ta farfaɗo, tana buɗe idanu sai akan Zinneerah, ai sai kawai ta fashe da kukan daya bama kowa mamaki da tsoro a wajen. Tashi Baba yay abinsa ya ɗauka butar data kawosa ya fice.
Zinneerah ta matsa jikin Inna tana hawaye da nufin rungumarta, hankaɗeta Inna tai cikin kuka da faɗa. “Munahika karki taɓeni, kinje kin gama yawon tazubar ɗinki zakizo ki goga mana ƙanjamau. To idan uwarki tayo asiri da rufe ido da bakin kowa akan hakan ni na gagareta, asirinta bazai ciniba. Nasan komai kina ikko kina karuwanci, shima shegen da aka ɗaura muku auren ƙaryar abokin cin mushenki ne. ALLAH ya wadatanki tambaɗaɗɗiyar yarinya gantalalla”.
“Kece gantalalliya, ni Sulaiman ban haifi gantalalliya ba”.
Baba ya bata amsa a fusace yana nunata da ɗan yatsa. Ya cigaba da faɗin, “Wlhy kika ƙara aibantamin ɗiya koda da furucin bakine saikin bar gidan nan, bari kuma nahar abada tunda ke bakisan ANNABI ya fakuba mara mutunci kawai.
Wani irin waro idanu Inna tai tana kallon baba, cikin rawar baki tace, “Malam ni kake cewa zan bar maka gida akan Zinni?”.
“Da giduma kuwa, harda jan kati”.
Da sauri Zinneerah ta shiga girgiza kanta tana hawaye. “Baba dan ALLAH kayi haƙuri ka daina faɗi, Inna uwace a gareni, komai ta faɗa a kaina ba laifi bane”.
Baba ya buɗe baki zai bama Zinneerah amsa Gwaggo Laritu da Tinene taje kaima rahoto ta shigo gidan. Zinneerah na ganinta ta miƙe da gudu tai kanta. Sai kuma gasu baba Rabilu suma harda ƴaƴansu. Cikin ƙanƙanin lokaci gidafa ya haukace da sabon murna. Makwafta nata shigowa ganin Zinni. Kafin kace mi zance ya fara yawo amarya Zinneerah tazo kamar an sata a injin gyara mutane ta koma balarabiya.
Haramin da gidan ya ɗauka yasaka kowa mantawa da wata Inna. Har Saifudden ma ya wuce su Gwaggo Maryam basu saniba. Aiko dai a wannan rana Zinneerah bata iya ta samu kantaba har dare, sai can kusan goma yaya Gajeje ta janyeta ɗaki ta bata abinci taɗanci. Daga haka aka zaman sake kafa sabuwar hira dan har zu baba Sabi'u suna gidan har lokacin basu tafiba. Zinneerah ta basu labarin daya sakasu kuka sosai dan tausayi.
Suka shiga godema ALLAH daya saka Zinneerah faɗawa a hannun nagari har ya sadata da mahaifiyarta. Wannan rahamarsace da jin ƙansa ba wayo ko dabarar waninsu ba. Sun kuma tabbatar a katsina aka lalatama Zinneerah rayuwa itama bada sanintaba, saboda a yanda ta basu labarin zuwanta. Inna nata zaginta da tsinarta akan ta mata sharri ita ƙarya Zinneerah tai mata akan cewar itace tasa tabi hajji lanti. Babu wanda yace da ita uffan akan hakan kaf ɗinsu.
Itama Zinneerah tayi kuka jin labarin yanda baba ya kasance, amma tayi farin cikin ƙara aurensa wanda yasa Inna ji kamar ta kasheta, sai dai babu damar yin magana baba ya kafa sharaɗi. Yanda kuwa yayin ta tabbatar zai iya sakin nata akan Zinneerah. Shiyyasa tai gum da bakinta tana binsu da ido, lokaci-lokaci takan fakaici ido ta share hawaye. Dan ga abin faɗa fal a bakinta amma babu damar faɗin sai tsinar Zinneerah dai take kawai.
Murnar dawowar Zinneerah yasa yaya Gajeje kwana a gidan, acewartama sai biki ya tashi kuma kenan. Aiko kusan kwana sukai hira da Zinneerah dan ɗaki ɗaya suka kwana. Hajiya Falmata nason cigaba da aikinta dole ta haƙura, sai dai ta bata abubuwan sha da abinda yake mai sauƙi da bazai takura Zinneerah zaman hira da ƴan uwantaba............✍
Leave a Comment