Makauniyar Kaddara 47

 


Page 47*


...........Cike da ɗokin zuwa ganin mmn sadiq dasu Aliyu Zinneerah ta shirya cikin wando da riga na parkistan red and white, sai gyale red data naɗa a kanta wanda ya fiddo mata ƙyawun da fuskrta ta ƙara. Kayan sun zauna mata ɗas a jiki kasancewarta mace mai mulmulallan jiki da ƙyawun surarta ta

ƙuruciya. Babu wani kwalliya a fuskarta, amma ta saka lipstick kaɗan da yayma lips ɗinta ƙyau, dan tanada lips masu ƙyau da tsarinsu ya fita sosai yanda suke ɗaukar jambaki kamar wata babyn roba. Takalmi tasa mai ɗan tudu da igiya, sai side bag ɗinta ƙarama. A yanda tai ƙyau dolene ka kalleta ka sake kallo, ga ƙamshi tana bazawa dan Zinneerah gwanace wajen ɓarnar turare, idan ta samu batai masa da sauƙi. Ƴar jikkar data zuba kayanta kala biyu da tsarabar chocolates ɗin su Abdul ta ɗauka, dama hajiya iya ta fice ita tana falo tuni.

       Hajiya iya kawai ta samu a falon itama tana ƙoƙarin fita, samarin gidan tun bayan breakfast suka fice, hakama ƴammatan, su Jamal kuwa batasan ina suka dosaba. Hajiya iya dake ƙoƙarin fita tace, “Inno kashe tvn nan ki taho nasan Moddibo nacan ya cika da hasahinmu”.

     Da to Zinneerah ta amsa tana ɗaukar remote, bayan ta kashe tvn ta gyara labulolin sannan ta fito, ƙofar ta rufe dan masu aikin Hajiya iya basu dawoba, maybe sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Tafiya ta fara cikin nutauwarta tana ƙoƙarin ɗaura agogo data ɗakko a tsintsiyar hannunta da dosar inda ta hango Hajiya iya da Mommy tsaye da alama harda ita zasuje. Idonta bai lura da AK ba sai da tazo dab dasu tana ɗagowa da shi ta fara tozali yana ɓullowa daga ta gaban motar waya a kunnensa alamar magana yakeyi. 

     Kallon nata yayi dai-dai da saukar nasa idanun a kanta. A take ƴar sakewar data hango akan fuskar tasa ta ɓace ɓat, ya tsuke fuska yana mata kallon data nema kifawa saboda harɗewa da ƙafafunta suka shigayi. Saurin maida kanta tai ƙasa tana cigaba da takowa ranta fal nauyinsa da kwarjini, sai mita take a ranta kuwa. (Haka kawai bakama mutum komaiba yayta hararka, shi wai baya ganin waɗanan idanun nasa manya da ƙarfinsu yay yawa suna tsorata mutane).......

     Da wannan tunanin ta ƙaraso Mommy dake kallonta tana ambaton, “Masha ALLAH ɗiyata irin wannan ƙyau haka”.

    Ƙasa Zinneerah ta ƙarayi da kanta tana murmushi, hakama Hajiya iya murmushi take tana kallonta itama. A bazata sukaji AK ya saki tsaki, cikin faɗa-faɗa yace, “K! Koma kisa hijjab”.

   Ba Zinneerah ba hatta su Mommy sai da suka dubesa, shiko ya fuske ya buɗe murfin motar ma a fusace ya shige abinsa. A sanyaye Zinneerah ta juya zata koma dan shi ba abin wasanta bane, waɗandama suka girmeta da shekaru masu yawa a gidan sunabin dukkan dokarsa balle ita ƴar jiya. Dakatar da ita Hajiya iya tayi ganin yanda tai ƙwalƙwal da idanu kamar zatai kuka, ta kamo hanunta tana matsawa saitin driver da yake zaune. “Haba Moddibo aimata haƙuri tunda ta rigada ta fito, ai kaga gyalen ya rufe mata jiki, kuma naga daga mota sai gida”.

       Shiru yay kamar baiji mi Granny ta fadaba, sai da ta ƙara leƙasa tana faɗin, “Oh nima yarfin daka iya zakamin?”.

    Idanunsa da suka canja launi ya ɗago ya dubi Hajiya iyan, “Amma Granny .......”

      “Dan ALLAH ai nace”. Tai saurin katsesa dan tasan shegen taurin kansa da dagiya akan abinda duk ya kafama sharaɗi. Badan yasoba ya ɗauke kai daga kallonta yan yima motar key. Murmushi Hajiya iya tayi da duban Zinneerah. “Kinga zagaya can kusa dashi ki zauna Inno, mu saimu zauna baya da Mommynku”.

      Kamar Zinneerah ta fasa ihu taji, dan yanda taga fuskarsa batai zaton ya haƙuraba, kawai dai yayi shirune dan Granny ɗin. Amma yata iya, dole ta zagaya tabi umarni. Zama tai maƙure jikin murfin mota, zuciyarta na mata hasashen ko ina little yake? Dan tayi tsammanin dashi zasuje itakam. Yanda AK ya figa motar da ɗan ƙarfi yasata saurin dubansa, sai dai da sauri ta ɗauke idonta ganin wani shegen harara daya watso mata laɓɓansa na motsawa tamkar mai magana komai son cewa wani abu amma ya gagara furtawa.

        “Kai malam wlhy karka zubar damu, dan idan ka kasheni banga sake ganin ɗan inno ba ALLAH ya isa mai kishin tsiya”. Hajiya iya ta faɗa da iya gaskiyarta tana zazzagama AK masifa. Dariya Mommy ta sanya ganin yanda AK ɗin ya hararo Hajiya iya ta mirror.

    Zinneerah kanta sai da zancen hajiya iya ya bata dariya, amma sai tai murmushi kawai tana kauda kanta gefe, dan zuwa yanzu ta fahimci Yayansu da Granny ba'a haɗuwa ba'ai faɗa ba. Kuma itace mai takalar faɗan shi kuma yayta mazurai, idan kuma ya magantu ya rama sau ɗaya yay mata banza.

      A nutse yake tuƙin cike da ƙwarewa da bin dokoki, sai da suka hau titi sosai ya fara amsama Mommy maganar da take masa daga can baya, hajiya iya na tayata. Zinneerah dai bakinta gum, sai strawberry sweet ɗin dake bakinta take ta faman juyawa tana kallon hanya, tana jiran taji ya tambayeta ina suka dosa taga ya ɗau hanyar anguwar kai tsaye. Mamakine ya kamata sai dai babu damar magana, sunyi kusan rabin tafiya taga ya gangara dasu wani super market, sai da ya samu waje yay fakin sannan yay magana batare da ya kalli kowa a cikinsu ba. “Mommy muna zuwa Please”.

        Cike dajin daɗi tace, “A fito lafiya”. 

    Hajiya iya kam baki ta taɓe da ɗauke kai tana maganar da su dake gaba ba jinta sukeba. “Muje”. Ya faɗa yana buɗe murfin ya fice. Zinneerah bata fahimci da ita yakeba sai da Mommy tace, “Ɗiyata fita kuje ku dawo kinji”.

     Sai da Zinni taɗan waro idanunta waje, tace, “Mommy amma.....”  

     “Maza kije karyayi faɗa”.

Mommy ta katseta kafinma tace komai. Dole Zinneerah ta yunƙura ta fita zuciyarta na dukan goma-goma. Idanunta kuwa harsun tara ruwa. Ina ita ina shiga irin wannan wajen da Yayansu, itakam yau tana cikin abba-tuwa, shikenan ya samu damar dazai cimata uwa akan ƙin bin maganarsa na saka hijjab duk da Granny ce tai bell nata dai. 

      Koda ta fito da birkitattun idanunsa ta fara cin karo, ga fuskarnan kamar zatai aman abinda kecin ransa. Ƙasa tai da kanta tana ƙoƙarin haɗiye rauninta dake son bayyana. Ta fiske abinta da takowa inda yake a hankali batare data sake yarda sun haɗa ido ba. Tana isowa wajen ya miƙa mata handkerchief ɗin hannunsa, “Kwashe wannan abun na bakinki”.

    Idanunta dake tara ruwan hawaye ta ɗago ta kallesa. ya zuba mata hararar data sakata amsar handky ɗin babu shiri, cikin ɗan tura baki ta fara kwashe ɗan janbakin dabai taka kara ya karya ba. Handky ɗin ta miƙa masa tana ƙoƙarin haɗiye kukanta. Batare daya amsaba ya raɓata zai wuce da faɗin, “Idan baki shiga hankalinki da saka wannan janbakin ba saina tsinke waɗanan lips ɗin da haƙori mtsoww”.

        Duk yanda Zinneerah taso daurewa kasawa tai sai da ta bisa da kallo mamaki ƙarara akan fuskarta. Ganin bata biyosaba ya sakashi tsayawa cak. Da sauri ta nufesa saboda fahimtar dan ita ɗin ya dakata. Jerawa sukai a tare gwanin sha'awa, dan yanda yake tafiya babu garaje haka itama take tafiyar, amma kasancewar abinda ya faru tana tsoron sake laifi ya ƙara hanzarta tata tafiyar, sai suka samu daidaito dashi dan ya fita kuzari da tsaho.

      Shigarsu wajen ya sake bayyana ɓacin ransa a saman fuska ganin yanda mutane ke ɗan kallonsu jefi-jefi, a bazata kawai taji ya ruƙo hannunta cikin nasa mai taushi da ƙamshi tamkar nata ɗinma, dan zuwa yanzu ta fahimci jin daɗi ke kawo irin wannan baiwar ga fata bawai shafe-shafe ba. A kusan tare ita da shi suka lumshe idanu saboda jin sabon al'amarin dake saukar musu a gangar jiki da magudanar jini, ya sake damƙe hannun da ƙyau yana ƙoƙarin dai-daita kansa gudun kar ayi abin kunya.

    Zinneerah kam ai murus bakinta ya ƙara mutuwa sai sama da ƙasa da numfashinta keyi tana ƙoƙarin fisgosa da ƙyar. Haka tanaji tana gani ya shiga zagayawa dasu yana ɗaukar abubuwa da sakawa a basket ɗin da ɗaya a ma'aikatan wajen ke biye dasu da shi. Itama kuma sai yanda budurwar ke kwarkwasa da wani iyayi a gaban Yayan nasu ya bama Zinneerah haushi ta shiga hararta ta gefen ido tana faman yamutse fuska.

      AK bai fahimci halin da take ciki ba sai da sukazo wajen biyan kuɗi, har lokacin yana riƙe da hannunta tamkar ance za'a ƙwace. ATM ya ciro a aljihun wandon getzner shaddarsa ash zai miƙa budurwar data tayasu takai hannu zata amsa cike da yauƙi, caraf Zinneerah ta kawo hannu ta amsa daga hannunsa tana wani juya ido da sake miskile fuska.

    Yanda tai ɗin ya saka wata dake kusa dasu kwashewa da dariya ita da ƙawarta. A fili tace, “Wlhy yarinya kin birgeni, adana abinki kar ƴan shishshigi suyi miki wuff da shi”. 

     Sarai Zinneerah ta jita, amma sai ko kallon inda suke bataiba tama ɗauke kai gefe. AK ma da sarai yajisu bai nuna yajiba, sai dai ya ɗan dubi Zinneerah ta gefen ido maganar ƴammatan na masa kaikawo a zuciya da ƙwaƙwalwa. 

     Koda aka gama saka musu a leda budurwar bata daddaraba duk da yarfatan da ƙawayenta sukayi da Zinneerah ta sake kai hannu zata ɗauka ledar Zinneerah ta rigata ɗauka da faɗin, “Don't worry, thanks”.

     Kasa haƙuri AK yayi yanzu kam sai da ya ɗan dubeta, mi zuciyarsa ta ayyana masa oho sai gashi da sakin wani malalacin murmushi yana sake damƙe hannunta dake cikin nasa, daga haka ya jata suka fito yana mamakin miskilancinta da kame kai tamkar ba ƙaramar yarinya ba.

         Zinneerah na ganin sun fito ta fara ƙoƙarin zame hannunta a nasa, shima babu musu ya saki tare dayin gaba abinsa. Sai dai kuma abinda sukema gudun su Granny, kuma sun gani. Dan Granny dake bama Mommy labarin da Zinneerah ta bata akan zuwanta katsina aikatau tun bayan fitarsuce ta fara hangosu. Ta taɓa Mommy tana faɗin, “Auta kalla mutanenki”.

       Ɗago kan Mommy yayi dai-dai da sakin hannun juna da sukayi, dan haka ta murmushi kawai da faɗin, “Inna tarkon nan naki fa mai ƙarfine, dan na ƙaramin damƙa yayma ɗana ba, yana dai ƙoƙarin nuna halin nasa na basarwa ne”.

      Baki Hajiya ita ta taɓe da cewa, “Ai sai yayma ubanda baisan halinsaba. Ni tuni na harbosa ai. Itace dai na kasa gane kanta dan itama gidan miskilancince, bansan yanda gidan nasu zai kasanceba an tara masu shegen baƙin rai da miskilanci. Shiyyasa banason a faɗa mata har sai ta tare suje can su ƙarata”.

     Dariya Mommy ta sanya har su Zinneerah suka iso wajen, sai da suka shigo mota ta haɗiye abinta tana musu sannu. Duk amsawa sukai yana tada motar, daga haka sai gidan mmn sadiq da Zinneerah taita mamakin tayaya ya sani?.


    ★★


  Tarba suka samu maiban mamaki daga mmn sadiq da maman halima. ashe hajiya iya ta sanar musu da zuwan nasu, shiyyasa mmn sadiq datai niyyar zuwa dubata yau dole ta haƙura. Zinneerah kam ai tuni ta faɗa jikin mmn sadig tana murnar ganinta ita da mmn halima. hakan datai har sai da ya bama AK mamaki dan baiyi zatonta hakaba. Kasancewar Abba na gida yana jiransu a falonsa aka sauke AK, su Hajiya iya kuwa da mmn sadiq keji kamar ta goya suna a sashenta. 

        Duk yanda mmn sakina taso nuna halin nata garesu saita kasa. Dan wani cika mata ido sukai dole ta kama kanta harda zuwa ɗakin mmn sadiq gaishesu. Ai kam sun amsa mata da fara'a da mutuntawa, hakan da sukai kuma sai ya ƙara musu kima a idonta da shakka. Mmn halima ma cike da girmamawa tazo ta gaidasu, Hajiya iya nata sanya mata albarka dan bata manta da fuskartaba taje mata gaiauwar Inno.

        Saboda zuwa nan hajiya iya dama taƙi cin abinci, dan ta taho da shirin cin abincin gidan ɗiyar tata. Aiko taji daɗin samun masa da mmn sadiq tai musu, sai gashi daga ita har Mommy sunci sosai suna godiya. hakan yasa Mmn sadiq ƙara jin daɗi da nutsuwa. Dan koba komai ai sun bata kimarta. Zinneerah kam tuni tana sashen mmn halima ta barsu dan su sake da kuma kasancewarsu manya a gareta.

    Da wannan damar mmn sadiq da baƙinta sukai hirar zuminci da tattaunawa game da labarin da Zinneerah ta bama hajiya iya da kuma abinda ya faru akan zancen little da maganar ɗaurin aurenta. Harma da shirye-shiryen tariya da a take mommy ta tabatar musu ita ta gama shirya komai rana kawai suke jira insha ALLAHU.

    Hawaye sosai mmn sadiq keyi har sai da hajiya iya ta shiga lallashinta. 

     Sai da akai sallar la'asar Abba ya shigo gaida su hajiya iya tare da AK da shima yaci masa sosai dan yana sonta, ya kuma sha zoɓo shima. Sun gaisa cikin mutunta juna, suka ɗan ƙara tattaunawa har zuwa kusan biyar da rabi sannan sukai haramar tafiya.

    Sai kuma ga Zinneerah tai ƙwalkwal da idanu na kewar hajiya iya da zatayi duk da dai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zata koma. Sau biyu suna haɗa ido da AK da tuni ya shige mota ta mirror ɗin waje, daga ƙarshe dai ta matsa daga saitinsa tana ɗaga musu hannu.


    Tafiyarsu da mintuna basufi talatinba su Sadiq suka dawo gida. Ganin Zinneerah suka haukace da murna suna tambayarya ina little ɗinsu?, su dai sunyi kewarsa dan ALLAH a dawo musu da abinsu. Dariya kawai take musu dan ita dai wannan ba huruminta baneba ai. Tunda batasan yaje canba itama ganinsa tayi.

     Bata samu zama da mahaifiyartaba sai dare bayan yaran sunyi barci, kasancewar ɗakin mmn sadiq ɗin zata kwana suka sami damar yin hira, yayinda mmn sadiq ketama ƴar tata nasiha a kaikaice akan aure da muhimmancinsa da darajojinsa. Ita dai Zinneerah saurarenta kawai takeyi bawai fahimtar dalilin yinsuba. Sai dai suna shiga kwakwalwarta tana kuma ƙoƙarin adanawa da fatan yin aiki dasu a duk sanda ƙaddara ta tilasta mata yin aure dan bata kawosa a lissafinta sam. ita kullum lissafi da budget ɗinta akan karatune mai zurfi kawai.

     Washe gari ma bayan tafiyar su Abdul skull sake zaman hira tayi da mamanta. A yau ɗinma hirar ta kasance kusan duk nasiha da dabarun zaman gidan aure koda da kishiya. Harma dai takai abin ya fara bama Zinneerah mamaki amma saita danne a ranta kawai.


     Karfe huɗu dai-dai sai ga Ni'ima da driver sunzo ɗaukarta, jitai kamar ta fasa kuka. Amma jin mmn sadiq tace zasuje taron biki Danya kuma harda ita nanda kwanaki tara yasa taɗanji daɗi a ranta har fuskarta ta nuna. Bayan ta gama matse-matsen hawayenta ta shirya suka wuce ɗauke da madaidaicin botikin gullisuwa da mmn sadiq ɗin tai musu.

          Koda suka iso gidan cike da murna suka tari juna dasu Bahijja daketa mata ƙorafin basusan zataje wajen mama ba da sun bita. dan sai da su Mommy suka dawo suka sani. Haƙuri ta basu kawai, daga haka suka shiga hidimar cin gwullisuwa kuma.


         Ana idar da sallar magrib hajiya iya tai baƙuwa. Bayan sun shiga ɗaki kusan awa ɗaya aka kira Zinneerah, kai tsaye hajiya iya tace mata ta shirya zasu tafi da baƙuwar gidanta. Mamaki ya kama Zinneerah, amma ganin yanda hajiya iya ta fiske dole itama ta shanye mamakin nata.

     Bayan ta shirya Hajiya iya ta jata gefe tai mata ƴar nasiha da gargaɗin duk abinda akai mata a inda zataje kartai jayayya, karkuma tai wasa wajen koyon komai ɗin. Ta amsama hajiya iya da girmamawa ita dai tana matsar ƙwalla, dan hankalinta ya tashi jin wai sati ɗaya zatai acan, a hakanma hajiya fadi take waje ya ƙure ba haka tasoba.


      Zinneerah naji na gani ta tafi tabar su Meenal tana hawaye suma sunayi tamkar masu rabuwa har abada. Hajiya iya kanta sai da taji kewarta, to amma wannan shine kawai gatan da zatai mata ta miƙata wajen kwararrun mata ta fannin sanin gyaran jiki da wasu sirrika irin su hajiya Falmata su gyara mata ƴar jikallen tata. Dan idan tai dubi da abinda ya faru da kuma kishiya irin Farah saita ƙara jin wannan shine gatan.


      Koda suka iso gidan hajiya falmata bata tsaya sanyaba saboda gargaɗi da sharuɗɗan hajiya iya akan irin salon gyaran da take buƙata aima Zinneerah ɗin, itako hajiya falmata dama aikinta kawai ta sani batasan wasaba. Musamman ma aiki irin wannan na manyan mutane kamar su hajiya iya da suke alaƙa tun zamanin ƙuruciya ba abinda zatai sanya bane. Dan haka tun a ranar ta fara gyara Zinneerah daga isowarsu gidan ko hutawa batama bari sunyi zaman yiba. Tun Zinneerah na kallon abin wani iri hardai ta fara jin yana shiga jikinta da sha'awarsa ganin yanda ta fara canjawa da ƙamshi mai kama jiki da gogewar fata a cikin kwana biyu.

       Babu abinda ke damunta sai kewarsu Jamal da hajiya iya dan ko abinci da ake bata na musamman ne. Hajiya Falmata kuwa nata aikinta da koya mata abubuwa kai tsaye har kunya na neman kashe Zinneerah da ganin hajiya falmata zata iskantar da ita shekarunta basu kai ba. A ranta kuma tana mamaki yanda ake mata magana mai kama da harshen damo akan aure da zamantakewarsa. Ta rasa wannan dalili itakam, takumayi alwashin bazata tambayaba zata cigaba dabi da ido da kuma saurare.


      A Ɓangaren su Hajiya iya kuwa Zinneerah na barin gidan aka ware fara tsare-tsaren biki da maganar invitations dan hajiya iya da Baffah fa shiri suke gagarumi kodan ƙular dasu Mammah dake can hotel suna jiran tsammani daga mai bincike, AK kuwa daketa ƙoƙari akan aikin shinkafarsa yana sane dasu, dan tuni yasa aka bincika masa inda suke, ya kuma shirya ɗaukar mataki akan Farah data bijirema maganarsa. 

     Akan gyaran gidansa kuwa Dr Mahmud da Huzaifa ne tsaye akai duk da gidan bama taɓa zamansa Farah tayiba. Garamashi yankan zauna lokacin da yake shigowa ƙasar a munafunce.

     Ranar da Zinneerah ta cika kwanaki huɗu wajen Hajiya falmata lefen da Momie ta haɗa gudunmawarta ya iso, sai kuma ga Adilah da Mahma daga london suma sun iso da nasu kayan lefen, dan AK na sanar da ita komai bai ɓoyeba, takuma bashi goyon baya ɗari bisa ɗari. 

     Zokaga yanda Adilah ke murna da farin cikin kasancewarta cikin ƴan uwa. mahma kuwa abinci kawai taci anan taɗan huta ta nema inda su Mammah suke, dan bata son ita kanta su san da maganar auren har sai ranar tariyar insha ALLAHU..............✍


No comments

Powered by Blogger.