Makauniyar Kaddara 43

 


Page 43*


...........A Nigeria kuwa yau cikin farin ciki AK yay barci rungume da Little, haka kawai wata nutsuwa da farin ciki suka mamayesa. Dukan wani ƙunci da damuwa da tunani

akan samuwarsa suka kwaranye, farin ciki da nutsuwa suka maye gurbinsa, jiyake tamkar ya haɗiye abinsa ya ƙara haifosa tsabar yanda yakejin abun kamar almara. wai shine da ɗa da rana tsaka, ɗan da baisan ta yanda ya samar da shi ba, ɗan da baisan a ina ya samar dashi ba. Shi tsabar ma nazari akan waɗanan tambayoyi. har ji yake ƙwalwar kansa na kuɗa, shiyyasa ya tattare komai ya ajiye gefe ya rungumi ɗansa tare da sumbatar goshinsa yana murmushi. 

      Ya jima barci bai ɗaukesaba yanata kallon little ɗin, sai can kusan ɗaya na dare barci yay awan gaba da shi. ALLAH ya soshi yaron baida fitina. Dan bai farkaba sai gabannin asuba ya tashi yana kiran “Mama ruwa, mama ruwa”.

    A hankali AK ya buɗe idanunsa, ya miƙa hannu ta bayansa ya kunna fitila dake a bedside drawer dan da alama basu da wuta. Zaune ya tashi da ƙyau yana riƙo little dake neman yin kuka yana kiran ruwa. “Oh oh sweetheart i'm sorry ina zuwa”. Ya faɗa da ɗagashi gaba ɗayansa ya maida jikinsa. Kafin ya ɗakko ruwan daya ajiye gefensu dan shima yakan tashi shan ruwan dare shiyyasa baya kwanciya babu shi a kusa. Sosai little yasha ruwan. Yana gamawa ya lafe a jikinsa ya koma barci. Shiru yay yana kallon fuskar yaron mai tsananin kama da tashi, wani lallausan murmushi da ajiyar zuciya suka kufce masa a lokaci ɗaya. Kwantar dashi yay a hankali yaja bargo ya rufa masa shi kuma ya sauka dan yasan bazai iya sake komawa barcinba kuma.


       Harya fita sallar asuba ya dawo little nata barcinsa, shima sake kwanciyar yayi dan barcin yake buƙata.

       Kusan takwas na safe ya farka dole saboda tsalle-tsallen da little ya farka yana masa a jiki, dole ya buɗe idanunsa da sukai nauyi irin na wanda ya tashi a barci. Kamo hanunsa yay ya zaunar a jikinsa yana murmushi tare da kai hannu ya shafi fuskarsa. “Little Handsome ka hanani barci bayan kai kasha naka”.

     Cikin rashin damuwa little yace, “Abba tea”. Dariya AK ya ƙyarƙyale da shi yana miƙewa zaune dashi a jikinsa. “Wato kai yaren abinda kakeso kawai kake ganewa ko? Inga bakin shan tea ɗin?”.

     Babu musu little ya ko wage masa baki alamar gashi. Dariya nanma ya sakeyi da sumbatar goshin yaron wani farin ciki na saukar masa. Huzaifa dake tsaye a ƙofar ɗaki yana kallonsu yay murmushi tare da jin daɗin ganin ɗan uwansa na walwala maiban mamaki, dan ba abu ƙarami bane a rayuwa ke saka AK ƙyalƙyala dariya. Baiyi magabana ya juya abinsa. Shiko AK daba ganinsa yayiba little ya ɗauka zuwa toilet, da kansa yay masa wanka, ya naɗo abinsa a towel ya kawo ɗaki ya ajiye a kan gado. Wayar Haneef ya kira yana tambayarsa sunzoma little ɗin da kaya ne?. Daga can Haneef ya amsa masa da eh bara ya kawo.

      “Okay” ya amsa yana yanke wayar, game ya sakama little a waya ya nufi toilet ɗin shima yin wankan. Shigarsa babu jimawa sai ga Haneef, sai da yayi sallama sau kusan uku, jin ba'a amsaba ya leƙo da kansa. Little kawai ya hango yana kokawa da waya, dan haka ya shigo yana dariya. “My Darling good morning ” ya faɗa yana kaiwa tsugunne gaban gadon. Little dayay busy abinsa ya ɗan ɗago ya dubesa ya sake maida kansa. 

     Yanda yayi ɗin sai ya bama Haneef dariya, ya fisge wayar yana faɗin, “Haba my man ni zakama jama aji danka samu phone?”.

     Ɓata fuska little yay zaiyi kuka Haneef ya maida masa wayar yana dariya. Daga haka ya miƙe ya ɗakko man Yayansu daya hanga a kan mirror yazo ya yayema little towel ɗin da yake a ciki ya hau shafa masa. Sunayi ana kokawa dan little baison ajiye wayar hannunsa. Har dai aka gama. Yana saka masa kaya AK ya fito. Gaidashi Haneef yayi. Ya amsa shikam yana binsu da kallo, dan yanda suke kokawa wajen saka kayan kawai zai tabbatar maka akwai shaƙuwa a tsakaninsu sosai. 

      Haneef na gama shirya little ya ɗaukesa suka fice danya bama Yayansu damar shiryawa. A hankali AK ya sauke numfashi, zama yay a bakin gadon yana ɗan kai hannu ya murza goshinsa, hakan yayi dai-dai da shigowar kira a wayarsa. 

     Kamar zai share sai kuma ya ɗauka wayar dake a kife, duk da ganin Mammah da yayi ɓaro-ɓaro a jikin screen ɗin bai kawo komai a ransa ba ya ɗaga. 

      Sama-sama ta amsa masa sallanarsa, gaisuwa kuwama bata amsaba ta shiga masa magana cikin faɗa. “Yanzu Abdul-Mutallab danka maidani banza harka iya ɗaukar ƙafa ka tafi Nigeria bakako sanar minba!!?”.

      Idanunsa yaɗan lumshe da raunan muryarsa gareta kodan daraja ta uwa da ALLAH ya bata, cikin girgiza kai kamar yana a gabanta yace, “Am so sorry Mammah, nima tafiyar ta dolece wlhy, ki gafarceni”.

     “Dole kace ta dolece tunda ubanka ya gama gayamin magana jiya, aiko yayi da ƴar halak da bazata raga masaba. Dan insha ALLAH yau zan baro london nima zuwa Nigeria ɗin, sai naga munafurcin da kuke son biznewa”.

     Babu shiri AK ya miƙe yana faɗin “Mammah Nigeria kuma?”.

        “Ƙwarai da gaske, ko karnazo ne ubana?!”.

     Bakinsa ya cije dakai hannu ya dafe kansa, zaiyi magana ta yanke wayar ƙitt

             Rasa abinyi AK yayi a ɗakin, ya shiga kai kawo kamar mai ɗawafi. Sam baiso Mammah tazo Nigeria a wannan gaɓar, dan yanda Baffah ya ɗauki zafi wlhy ba raga mata zaiyiba. Shiko baya buƙatar ganin suna shiga irin wannan rikicin dan ƙara nisantasu yakeyi.

      Wayar Mahma ya kira da sauri dan yasan itace kawai zata iya takama Mammah birki. Harta tsinke ba'a ɗagaba, dan haka ya sake kira. Jin an ɗauka ya sauke ajiyar zuciya. Sai dai jin muryar Adilah na faɗin, “Sweet bro surprise”. Ya sakashi maida hannunsa a goshinsa yana murzawa. Ƙoƙarin dai-daita muryarsa yayi yace, “Uhmyim Darling badai kina london ba?”.

      Ɓata fuska tayi daga can kamar tana gabansa. Cikin shagwaɓa tace, “Uhm ai dama nasan yanzu ka daina sona ALLAH, yau kwana biyu ina nemanka a waya saboda dawowana amma bana samunka, na dawo ɗazun nan, saina tarar wai kana 9ja, yanzu haka ina shirin tafiya can gidanka wajen Granny ne, ina jiran Khalipha yace zaizo mutafi idan ya fito school”.

       “Oh parrot har yanzu dai baki canjaba. Ina Mahma ne?”.

     Baki ta tura duk da kuwa bata kasance ƙaramar yarinyaba, dan tama girmi Khalipha da kusan shekara biyu. Cikin shagwaɓa tace, “Haka dai kakeson parrot ɗin nan taka. mahma gata can suna rikici da Mammah akan wai zatazo Nigeria ita da Farah. Wai mike faruwane na isketa sai faɗa faɗa, ni wlhy namaji dama ban dawo ba. Shiyyasa zan tafiyata gidanka dan banason faɗan nan na Mammah taita zagin mana Baffahn mu”.

      Hankalin AK ne ya kuma tashi, atake raunin da yake ɓoyema ƴar uwarsa ya bayyana. Idanunsa suka sake kaɗawa sukai jajur. “Adilah akwai matsalane, amma yanzu sanin tushenta bashine abinyiba. Inason kije ki sace min passport ɗinta dana Farah ɗin duka”.

        “Tab, wlhy Bro hakan dakamar wuya, dan inaga abinda Mahma tai niyyar yi kenan Mammah ɗin ta gani, yanzu hakama gata can harta fito da kayan tafiya shine Mammah ta kulle ƙofan ta canja security”.

       “Thanks GOD”. Ya faɗa yana furzar da zazzafar iska. Hakan da yayine ya sake tayarda hankalin Adilah, dan ta tabbatar Yayanta na cikin damuwa, tambaya ta shiga masa amma bai iya bata amsa ko gudaba, sai ma yanke wayar yayi daga ƙarshe ya zame ya kwanta a gadon yana mai dafe kansa da yakejin ya fara sara masa da ƙarfi.

         

      A cikin gida kuwa little nacan yanata hidimarsa a tsakanin su Baffah hankali kwance. Dan tare yay karin kumallo da Baffah da Mommy abinsa. Hakan harya dinga basu mamakin yanda ya saki jiki dasu sosai. Sai da suka kusa gamawa AK ya shigo falon. Gaidasu yayi sanan ya kai zaune kusa da Mommy. Ta shafa kansa cikin kulawa take faɗin, “Kana lafiya kuwa Son?”.

     Ɗan ɗagowa yay daga kwanciyar da yay jikin kujerar yay mata murmushin yaƙe. “Lafiya lau Momy gajiyan jiyace kawai”.

     “Aiko ya kamata ta sakeka haka. Kodai Daddy nane bai barka kayi barciba?”. Tai maganar tana kallon little dake wasansa hankali kwance. Shima kallon little ɗin yayi yaɗan ɗauke kansa da sakin guntun murmushi. “No Mommy, aishi wannan ko hidimarsa tasa idan ya kwanta bazai farkaba, kawai dai hajiyanne”.

      “Ayya to sannu kaji, taso ka karya saika koma ka sake kwanciya ka huta”. Tai maganar tana faɗa haɗa masa abincin dake a tsakkiyar falon wanda basu jima da gama ciba suma. Baffah dai najinsu amma bai tankaba, sai dai yaji a ransa babu wata gajiya dake damun AK ɗin akwai dai dalili. Dan yanayinsa baiyi kama damai gajiyaba sai damuwa.



*_DANYA_*


     Ba ƙaramin sake rikicewa Inna tai ba da ganin kayan goron ɗaurin aure wai duk na Zinneerah, yarinyar da aka cemata tana can ta kama ɗaki. Kai ina akwai ƙarya a wannan al'amarin. Kawai dai ta fahimci Baba da wani sabon salo ya dawo danya. Kawai yayi hakane dan ace ƴarsa na cikin aminci. To itako zata tabbatar masa ras take kallonsa.

     Da wannan banzan tunanin nata yasa ta wartsake kamar babu abinda ya dameta. Sai ma ƙoƙari sakama kanta wata walwalar dole takeyi musamman idan ƴar barka da gulma suka shigo, dan zuwa yanzu duk zancen ɗaurin auren Zinneerah ya shiga garin na Danya. Wasu kuma badan barkar suke zuwabama yanzu dan son gani da idone da son tabbatarwa da abinda ke faruwa a gidan. Dawowar baba da sabuwar amarya harda tsohon ciki, auren Zinneerah da dawowar Karima gida.

     Aiko dai suna ganin abinda sukazo neman, dan haka duk wacce zata fita saita gumtsi gulma ta fita dashi a baki, duk yanda Inna ke ƙoƙarin nuna ita ta dake ranta kishinta da damuwarta sun kasa ɓoyuwa, sai zabga habaici take wasu Baba da gugar zana. Har takai Gwaggo Laritu na maida mata a kaikaice itama.

     Sai da baba yaga abin zai zama fitina ya lallaɓa Gwaggo Laritu ta wuce gida aka bar Inna da takaici dan kukan zuci kawai take faman yi wanda yafi na zahiri ciwo da cin rai.


___________________★


       Koda AK ya kammala karyawa fita sukai shi da Huzaifa da little, dan yanason rage damuwar Mammah dake cin ransa suk da yaji daɗin abinda Mahma tayi. Sai da suka fita ya samu damar yin waya da Hajiya Iya ta wayar Khalipha daketa ƙoƙarin danne damuwarsa. 

      Sun jima suna wayar da Hajiya iya harma da Huzaifa da little dataji daɗin gani tare dasu dan video call ne. A bakin Hajiya iyan ne ma yakejin wai Farah ta fita da akwati a gidan tun ɗazun, kuma su basusan ina ta nufaba dan bataima kowa maganaba.

     Murmushi AK yayi, cikin rashin damuwa yace, “Karki damu Granny gidan Mammah ta tafi, kuma Mahma zatai maganinta ne ta dawo da ƙafafunta”.

    Baki Hajiya iya ta taɓe da faɗin, “Kai nifa yanzu kam taitayi dan bata cikin lissafina. Tunda ALLAH ya baka ƴar mutunci da nakeda tabbacin zata share hawayenka in ALLAH ya yarda. Fatana dai ka riƙemin yarinya da ƙyau Moddibo, dan wlhy inhar Inno tai kuka akanka kaima sai kayi”.

       Fiska ya ɓata yana wani ɗan yatsinata. Yace, “Oh kukuma naku salon kenan Granny?”.

      “Ai mun wucema haka, dan wlhy bazan baka Inno ba saina shimfiɗa maka dokoki, ko ɗaya ka tsallaka kuwa saika haɗu da fushina”.

      “To lallai naku babbane, nikam sai anjimanki”.

       “Zakaci ubanka Kabirune yaro, bauɗaɗen banza jikan ƴan Morocco”.

     “Ahaka dai kuka gani kuka nane”. Ya faɗa a hasale saboda zagar masa uba da tayi. Itako Hajiya iya dama tayine danta hasalashi ɗin dan haka ta hau dariya. Huzaifa fa ma dai dariyar yakeyi. Hajiya iya tace, “Kaima ai ina zuwa kanka dan uwarka Balkisu, tuzurun banza kana neman tsofewa a gida babu aure. Why bara dai na dawo ƴar kowa na samu aura maka zanyi a dangi, da wani shegen kansa uwa sheƙar angulu”.

      A take shima ya shanye tasa dariyar yana ɓata fuska, “To kin kuma dawo kaina? Kefa ALLAH Granny kinada matsa kiyita zagema mutum iyaye babu laifin zaune babu na tsaye.  Sai ki nema wanda zaki samoma mata a ƙauye badai niba wlhy”.

      “An zageka ɗin mai kama da zucbibin ƴan Lagos, bara dai na dawo kaga yanda zanyi maganinka wlhy, inba hakaba nasa Bashir ɗin yima uwarka kishiya itama wlhy. (Daddynsa take nufi😂) dan haka ya waro idanu waje da faɗin, “Kai! Wai ke Granny miyasa lamarin naki kullum gaba yakeyi?, sam bakison zaman lafiya?”.

     “Oh bama kasan yana yin gaba ba saina dawo Nigeria”. Tai maganar tana yanke kiran.

       “Tsohuwarnan akwai tarin matsaloli a kanta yasin”.

    Cewar Huzaifa rai ɓace. Shi adole yaji haushi ance za'a saka aima Mommy kishiya😹.

     “Ai indai Granny ce ta wuce duk yanda kake tunaninta”. Cewar AK yana wani ɓata fuska shima. Little da baisan anaiba wasansa kawai yake zabgawa. 

      Biyawa sukai ta gidan Dr Mahmud suka ɗaukesa dan gona zasuje duba masu aikin shinkafa, daga na su leƙa company da ayanzu haka an fara zuba aikinsa shima. Kasancewar sun tahoma Little da kayan ciye-ciye ko damuwa baiyiba, sai uban rashinji yake zubawa a gonar alamar yana cikin ƙoshin lafiya.

        Huzaifa akwai son irin wannan wajajen, dan haka ya shiga cikin gonar sosai yana duba aikin da yaba ƙyawun da yayi. Da wannan damar AK da Dr Mahmud suka tattauna akan abinda ya shafesu game da ginin company nin shinkafa da kuma aikin shinkafar, dan a shirinsa so yake ya koma london zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu, kuma da Little yake shirin komawar, baisan kuma yanda zasu kwashe da Baffah ba akan hakan.............✍

    

No comments

Powered by Blogger.