Makauniyar Kaddara 40
Page 40*
...........Da farko Baffah yaso kira ya sanarma Hajiya iya komai, sai dai a bisa wani tunaninsa kuma sai yace bara ya bari har zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu da yake da burin yanke hukuncin daya dace ya kuma
san Hajiya iya zataji daɗi sosai. Bai sanarma kowa mike faruwaba a cikin matan nasa, ya dai nema ƙanwarsa Bilkisu a waya sunyi magana, anan nema take sanar masa itama gobe idan ALLAH ya kaimu takeson sake zuwa london ɗin domin duba jikin hajiya iya, tanata neman wayar AK ma bata samuba ashe ya shigo 9ja ne. Tace amma tunda wannan ta taso bara ta dakata harsu dawo daga danya, dan dama tanason su tattauna akan ɓoyema Ahmad rashin lafiyar Hajiya iyan da sukayi.Cike da so da ƙaunar ƴar uwarsa Baffah yace, “Babu damuwa Bilkisu, kiyi haƙuri na kashe wannan ƙurar duk da nasan tawuce kasuwar gobe, dan yanda Adnan ya dage cewar bai aikata wani abu akan samuwar yaron nanba hankalina na tashi, inaji a raina kuma kamar akwai wani abu ɓoyayye da bamu saniba”.
“Gaskiya kam Yaya al'amarin yana buƙatar bincike, baka shaidar ɗan yau amma koni dai inaji a raina Adnan bazai aikataba, to amma jin cewar gwajin DNA ya tabbatar da ɗan nasane yasaka jikina duk yayi sanyi gaskiya. Amma inaga zan shigo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu nan ɗin kawai”.
“To ALLAH ya kaimu da rai, kizo ɗin kozanji sanyi a raina na samu abokin shawara nima”.
Daga haka sukai sallama. Idan barci ya figi baffa a wannan dare sai dai ɓarawo. Hakama mmn Sadiq acan barci ya gagareta. Danma Abba nata mata nasiha da lallashi harya samu taɗan saki jikinta saboda kar matan gidan su fahimci akwai matsala.
*WASHE GARI*.
Washe gari Alhmdllh AK ya tashi garau a zahiri. a cikin zuciyarsa kuwa shi kaɗai yasan mi yakeji gameda son tunano ko ya taɓa aikata wani abu makamancin wanda yake tuhumar kansa akan samuwar little. Sam bai iya tuna komaiba balle ya gano, dan haka ya ajiye komai a ransa yay shiri kamar yanda baffa yace.
Yayi ƙyau matuƙa cikin ɗanyar shadda fara tas da taji ɗinki mai ƙyatarwa da ɗaukar hankalin mai kallo, ya murza hula a kansa wadda ta sake ƙawata tsarin adon nasa da bayyanarsa cikakken bahaushe. Turare ya saka ya fito yana baza ƙamshinsa mai sanyi da daɗin shaƙa. Yayi mamakin cin karo da matasan ƙannensa suma cikin shiri, sai dai baice komaiba ya shiga amsa gaisuwar da suke masa cikin girmamawa.
Baffa ne ƙarshen fitowa sanye shima cikin tashi ɗanyar shaddar, fuskarsa a sake tamkar babu damuwar komai tattare da shi, har hakanma ya bama AK mamaki da tsoro, dan tun yana yaronsa ya gama karantar irin wannan yanayin na Baffa. Idan kai masa laifi ya nuna kamar bai damuba to lallai akwai abinda yake shirya maka kuwa.
Motoci suka shiga, Baffa shi kaɗai sai drivern sa, dan acewarsa zasu ɗauki Alhaji Mansur babban amininsa a gidansa. Sai yazam su Moos'ab sun taru a mota ɗaya su huɗu. AK na shirin shiga wata motar shi kaɗai sai ga Dr Mahmud ya iso. Hakan yasa ya shiga motar Dr Mahmud ɗin kawai da shima dai da alamar shirin tafiyar yazo gidan dama.
Duk da AK cike yake da mamakin wannan gayya sai baice komaiba. Sun dai gaisa da Dr Mahmud ya tambayi yaya ƙarfin jikinsa daga haka sukai shiru, Dr Mahmud nata juya abinda yakeso su tattauna a ransa ya kasa furtawa, dan duk da AK abokinsane yana girmamashi akan wasu dalilai masu yawan gaske.
Sai da suna gab da fita cikin garin kano zasu kama hanyar katsina AK ya sake fahimtar bayan motocinsu uku akwai wasuma biye dasu kusan guda uku. Cikin kasa jurewa yace, “Wai nikam wannan gayyar ta minene Baffah yayi?”.
Ɗan dubansa Dr Mahmud yayi, cikin rashin fahimtar inda zancen nasa ya nufa yace, “Gayya kuma ranka ya daɗe?”.
“Uhm, ko bakaga motocin dake biye damuba?”.
Ta mirror Dr Mahmud ya duba bayansu, a nazarce yace, “To inaga dai ba tafiyarmu ɗayaba gaskiya”.
Shiru AK yayi duk da bai gamsu da hakanba, sai ma ya jawo wayarsa kawai ya shiga daddanawa.
Tafiyar da bata gaza awa ɗaya ba suka iso gidan mutum ɗaya, kai tsaye hanyar kusada suka shiga, a lokacin kuma AK ya sake tabbatar da tafiyarsu ɗaya da motocin nan, amma sai yay shiru bai sake magana ba. Abinka da lafiyayyun motoci ga kuma lafiyayyar hanya cikin ƙanƙanin lokaci suka iso cikin kusada. Basu wani tsayaba suka ɗauki hanyar Danya.
Haka kawai AK ya samu kansa da nutsuwa a kallon hanyar zuciyarsa na masa wasu tunani daban akan rayuwar Zinneerah a ƙauyen, rashin ƙyawun hanya ya ɗan jasu lokaci mai tsaho kafin su shigo cikin ainahin ƙauyen Danya. Duk da ba safiya bace garin akwai mutane sosai, dan lokacine na shigowar farkon damuna mazan garin nata dawowa gida domin haramar noma.
Sosai idanu suka dawo caa akan dalla-dallan motocin kowa na tunanin daga ina haka?. Wasu suce ƴan siyasa wasu suce daga fadar sarkin katsina ne. to basu dai da tabbas, duk da kuwa kai tsaye Abba gidan maigari ya nufa dasu, dan shine jagoran tafiyar tasu. A ganinsa kuma hakan shine yafi cancanta da wannan tawagar tasu dan bayaso ai musu irin wulaƙancin da akai masa a wancan zuwan.
Su maigari suna zaune a bishiyar ƙofar gidansa shi da fadawansa sukaga motoci galla-galla na tsayuwa. Ba karamin kaɗawa hantar cikin maigari da ƴan fadarsa tayiba. Dan duk zatonsa samame aka kawo masa daga fadar sarikin katsina. Duk da yasan baya aikata wani mummunan al'amari ga ƴan garinsa sai da yaji tashin hankali. Bai ƙara rikicewaba sai da su AK suka fara firfitowa.
Daka gansu kaga manyan ƙasa masu ci da tsinin allura, dan duk sun jiƙu cikin shaddoji masu maiƙo da ɗaukar idanun mai kallo. Abba ne ya matsa inda suke yaɗanja maigari dake a ruɗe gefe sukai ƴar magana. a take bakin maigari ya washe ya shiga sakin tagwayen ajiyar zuciya. Bai tsaya jan jikiba yasa ƴan fadar tasa shiga cikin gida suka fara fitowa da tabarmi sabbi ƙal tare da manyan dardumai aka shishshimfiɗa a babban zauren maigari dake share ƙal ga sanyi mai saka nutsuwa gaduk wanda zai zauna.
Duk ciki suka shiga, akabar Baffah da Abba da Alhaji Mansur da Alhaji Yusif a waje suna son yin magana da maigari, dan Alhaji Yusif Mande da Alhaji Mansur Tofa manyan aminan Baffah ne da kowa yasani, tun kuma a daren jiya ya sanar musu abinda zasuzo yi anan ɗin.
Abba ne yayma maigari bayanin nason ganin dangin Malam Sule baduku. Da kuma abinda ke tafe dasu. Jin sunan Zinneerah ya saka maigari jin dunbin daɗi a ransa, dan shi wlhy yama manta da yarinyarnan sam a rayuwarsa. sai dai yau dalilin ambatonta yasakashi farin ciki musamman da yaji dalilin zuwa waɗanan manyan mutane. Bakinsa a washe yace, “Ai Alhmdllh ma kun yanka akan gaɓa Alhaji, dan Malam Sule ɗinma ya dawo garin jiya-jiya, zanma iya cemuku yanzu da safen nan sukabar gabana shi da fitinanniyar matarsa akan rikici data tada dan yazo da sabuwar amarya daga Niger. Inaga yanzu bara na aika a kirashi shi dasu Rabilun ku zauna ku huta”.
Sosai su Baffah sukaji daɗin jin cewar mahaifin Zinneerah ya dawo gida. Dan Abba ya sanarma Baffah cewar wancan zuwan da yayi ya iske bayanan ya bar gari ba'asan inda yakeba.
A take maigari ya aika kiran Baba da su Kawu Rabilu, shi kuma ya shiga gida yasa aka fara haɗa fura da sauran cimar ƙauye domin fitoma baƙi. Bayan ya aika a siyo musu ruwan leda da lemo acan kusada dan musamman ya tada mai mashin.
★★
Baba na ƙofar gida tare da ƴan uwansa yana basu labarin tun barinsa gida ashe Niger ya dosa, acan yayi gamo da wani bawan ALLAH daya taimakesa saboda fahimtar baya cikin hayyacinsa da yayi. Shine ya dage masa da addu'a da neman magani harya samu lafiya acikin watanni shida. Koda yaga ya warke duk da ya tuna komai daya faru sai yace bazai dawo gidaba zaiyi zamansa can neman arziƙinsa. Aiko wannan mutumi yaji daɗin haka. a take ya ɗaurasa akan hanyar sana'a, cikin ƙanƙanin lokaci ALLAH ya amince masa abubuwa suka canja ya fara juya kuɗaɗe duk da bawai masu ɗunbin yawaba. Nadai rufin asirin ALLAH dai-dai gwargwado. Ganin zaman nasa bana ƙare bane mutumin daya taimakesa ya bashi auren ƙanwarsa da mijinta ya rasu bakuma ta taɓa haihuwaba, hasalima shekarunta biyar kacal dayin aure. Ya amsa hannu biyu yayma ALLAH godiya da wannan bawan ALLAHn nan, ya kumayi sa'a Zainaba nasonsa itama. cikin amincin ALLAH basu rufa wata uku ba sai gata da ciki, sunyi murna sunyi farin ciki mara musaltuwa. Da cikin ya tsufane yaga ya dace yazo gida da ita ta haihu a cikin danginsa, shine dalilinsa na ɗakkota suka taho yanzun.
Cikin jin daɗi Kawu Sabi'u yace, “Yaya to yanzu kadawo garemu baki ɗaya kokuwa haihuwa kawai aka kawo yayarmu tayi ka sake gudu ka barmu?”.
Kafin Baba ya bashi amsane ɗan aiken maigari ya iso. Tun anan ya gumtsa musu zancen baƙi. Cike da mamaki suka tashi suka bisa dan su dukansu fes suke cikin shiga ta kamala babu wani damuwa.
Lokacin dasu baba suka iso sun iske an cikama su AK gaba da kayan abinci, duk da dai fura ce da ruwa da lemo, sai zabi da maigari yasa aketa yankawa ana shiga dasu cikin gida dan yacema matansa dan ALLAH suyi maza a gyara a gasasu gashi mai ƙyau.
Fahimtar muhimmancin baƙin ya sakasu miƙewa suma babu sanya suka haɗu da ƴaƴansu suka fara aikin babu wasa. Koda su Baba suka iso Baffah ya buƙaci su zauna a waje suyi magana iyakarsu manyan. Sanin maganace mai muhimci tafe dasu maigari yasa aka sake saka musu tabarma ƙatuwa a zaurensa na biyu dake ƙarami bai kai na farko girmaba.
Bayan duk sun zauna sukai gaisuwa ta mutunta juna. Inda Abba ya bama baba sani. Baba da dama tuni yake masa kallon sani yace, “Haba koda naji, tun ɗazun naketa tunanin wannan fuskar kamar na santa amma na kasa. Kai sannunku da zuwa, sannunku”.
Fuskar Abba da murmushi yace, “Yauwa mun gode sosai Malam Sulaiman. Nasan zakai mamakin wannan zuwa namu, sai dai ba abin mamaki baneba. Kwanaki nazo garin nan amma ban samekaba. Zuwan nawa kuma yanada nasabane da Zinneerah ”.
Da sauri baba ya dubesa jin sunan gudan jininsa abar begensa a koda yaushe. Murya a raunane yace, “Zinneerah kuma Alhaji Abubakar? Ai ina mai baƙin cikin sanar dakai muma nemanta mukeyi tun bayan wani babban al'amari na ƙaddara daya giftama rayuwarta”.
“Eh nasan duk wannan Malam Sulaiman, dan akansama nazo kwanaki, sai dai rashin samunka ya sani komawa. Yanzu dai a taƙaice Zinneerah tana tare damu, dan waɗanan bayin ALLAH daka ganni tare dasu ma a dalilinta sukazo nan. Wannan” ya nuna Baffah. “Shima kawuntane, dan yayane ga hauwa'u, nasan dai bazaka gaza jin labarin dangin mahaifiyarta dake a bauchi ba sanda kuna tare? To Alhaji Kabir Shira yana ɗaya daga cikinsu, sannan kuma yaron wajensa ne ke son auren ita Zinneerah shiyyasa mukazo nan”.
Wani irin daɗi da al'ajabine ya bayyana a fuskokin su Baba da maigari da su Kawu Rabilu. Baba da ƙwalla suka cikama ido yace, “Ashe dama Zinneerah na tare daku? Kai ALLAH na gode maka da wannan ni'ima taka. Nagode maka ALLAH daka bama yarinyata kariya ta hanyar sadata da mahaifiyarta. Sannan kuma nagode muku da kuka zama masu karamci daƙin riƙe baya a ranku kuka jiƙan gudan jinina duk da hanaku ita danai a lokacin da kuka buƙata. Kuyi haƙuri, bansan da wane irin yare ko harshe zan muku bayaniba, amma tunda ba wannan ya taramu yanzuba mu fara maganar da kukazo da ita, waccan zata biyo baya danni na cancanci naje inda kuke muyita. Batun auren Zinneerah kuwa wlhy koda bakuzo inda nakeba kunada iko da damar aurar da ita ga duk wanda zuciyarku ta baku yarda akan ingancinsa da mutuncinsa. Dan haka ni dai a ɓangarena babu matsala na bama wannan yaro Zinneerah halak malak. Ga kuma ƴan uwana nan inada tabbacin bakinmu ɗaya dasu”.
Cikin jin daɗi da farin cikin kalaman baba su Baffah suketa ambaton Alhmdllh bakunansu a washe. Alhaji Yusif yace, “Masha ALLAH, gaskiya munji daɗin wannan karamci, sai dai kuma muna roƙon alfarma ta biyu idan bamu takura muku ba”.
Kawu Sabi'u dake kusa dashi yace, “Alhaji ku ɗauka mudaku duk ɗayane, dan koba komai kuma kunada ƙarfin iko akan Zinneerah, dan haka ba zancen alfarma a tsakaninmu”.
Nanma kowa ya nuna jin daɗinsa. dan haka kai tsaye Alhaji Yusif ya sake faɗin, “To Alhmdllh, dama alfarmar tamu dai bata wuce cewar mufa da shirinmu mukazo nan ba, ma'ana da shirin ɗaura aurenma baki ɗaya muka iso bawai tambaya ba. Muna buƙatar ɗaurin auren ne a gaggauce bisa wani dalili da insha ALLAH daga baya za'a tattaunashi. Fatanmu dai a ɗaura auren kawai”.
Duk da baba yaji daɗin wannan zance sai da yay ɗan jimmm, kafin ya gyara zamansa murya a sanyaye yace, “Amma Alhaji dakun bari dai a fara magana ta fahimta, dan yadace ace kunsan ƙaddarar data afkama yarinyar nan harta kai ga barin gida ta iskeku”.
Da sauri Baffah yace, “Karka damu ɗan uwa, duk abinda kake ƙoƙarin son sanar mana mun sanshi, dalilin sanin nema yasamu cewa a gaggauta ɗaura auren yau, daga baya dukma abinda zai biyo baya sai ya biyo”.
Daɗine sosai ya ƙara kama baba, cikin share ƙwalla yace, “Shikenan mun amince, dan haka ga ƴan uwana nan suke da sauran magana”.
Kowa ya nuna farin cikinsa ananma. Dan haka maigari ya fita cike da farin ciki ya sanarma sanƙira a sanar da ɗaurin aure yanzu idan anyi salla a masallacin juma'a.
Cikin ƙanƙanin lokaci sanarwar sanƙira ta gauraye ƙauyen danya. Kasancewar dama azhar ta taho nan mutane suka fara haramar nufar massalacin juma'a domin yin salla duk da ba juma'ar baceba. Suma su AK da duk basusan mi ake cikiba fitowa sukai sukayi alwala. Mutane sai kallonsu suke tamkar sun sami television. Yara kuwa nata kaima mata labari a cikin gida.
Koda suka shiga cikin massallacin liman sai yaja baya, a mamakin kowa sai gani sukai ya kamo hannun AK ya tsayar a mazaunin liamami.
Kasa magana AK yayi ya tsaresa da idanu, ganin yanda yayi ɗin sai Liman yay murmushi, kansa tsaye yace, “Kai kafi cancanta da ka jamu salla badan nasan kaiɗin wanene ba. Haka kawai zuciyata ta rayamin baka wannan damar, dan haka dan ALLAH karkai musu ko jayayya”.
Baki AK ya buɗe zaiyi magana Baffah ya girgiza masa kai alamar yabi umarni kawai. Dole ya ɓame bakinsa yana wani lumshe idanu da buɗewa a lokaci ɗaya. Dolensa ya juya yana gyara taiwarsa, a ransa rayawa yake da ace baida ilimin addini lallai yau da yaji kunya mai tsanani ashe.
(hummm, jama'a ni kaina sai da na sauke numfashi saboda jin muryar Abdul-Mutallab Kabir Abdul-Mutallab shira dake raira karatu a nutse a cikin salla, dan yanda yake cikin masu jajayen kunne banyi zaton yanada ilimin addini haka ba).
Kasancewar ƙaramin gari jin baƙuwar murya da salon karatun yasaka mata cece kucen anyi baƙon balarabe mai jan salla yau a babban masallaci, a cikin wannan zantuka kuwa hardasu yaya Gajeje dake zagaye da Inna dake kwance rijib babu lafiya tun faɗuwar jiya, da alama dai hawan jini ne ke neman bigeta.
A masallaci kam bayan an idar da salla aka tsaida mutane duk da kuwa dama sunsan da zancen ɗaurin aure da aka sanar dan shine maƙasudin taruwarsu da yawa haka a massallacin tunda akwai kananun masallatai.
Mamakine ya kama su AK jin alinahin liman na sake sanar da maganar ɗaurin aure. AK ya kalli Baffah cike da alamomin tambaya, wani murmushin manya Baffa ya sakarma AK ɗin yana ɗauke kansa ya maida ga Haneef. Magana ya faɗa masa a kunne. A take Haneef ya tashi yana jan hanun Mas'ood suka fita. Cikin mintuna ƙalilan suka dawo da yara ɗauke da kwalayen sweets da huhunan goro da biscuits. Bayan an ajiyesu Alhaji Mansur ya ciro kuɗi ƴan dubu-dubu sabbi ƙal ɗauri biyu ya ajiye a tsakkiyarsu alamar dai kuɗin sadaki ne.
Kai Kawu Sabi'u ya girgiza da faɗin, “Alhaji sunyi yawa, dubu ashirin sun isa matsayin sadaki”.
Baffah ne yay murmushi shima yana girgiza nasa kan. yace, “Darajar ɗiyata ta wuce dubu ashirin, idan tanima za'abi sai sun ƙara mana sadaki wannan yayi kaɗan”.
Kusan waɗanda ke a kusa dasu sai da suka zaro idanun mamaki, Baba yay saurin faɗin, “A'a dan ALLAH ayi haƙuri alhaji, waɗanan ɗinma sunyi yawa kamar yanda Sabi'u ya faɗa”.
“Basuyiba malam Sulaiman”. Cewar Alhaji Yusif. Abba ma yay murmushi da kallon Baba. “Kamar yanda Alhaji Kabeer ya faɗa a barsa haka ɗin kawai ALLAH ya sanya albarka ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba”.
A take aka amsa da amin, tare da shiga hidinar ɗaurin aure kai tsaye. Bayan tsarebe-tsaraben ɗaurin aure da addu'a. Sanƙira ya miƙe ya fara shelantawa ga jama'a an ɗaura auren *_“Alhaji Abdul-Mutallab shira da amaryarsa Zinneerah Sule baduku akan sadaki naira na gugar naira, wuri na dukan wuri dubu ɗari biyu”_*...............✍
*_Tofa, yaufa ake ƙuru-ƙuru, jama'a yaya wannan labari zai kasance a kunnen hajiya aunty mandiya gimbiya Farah uwargida ran gida a gidan Abdul-Mutallab shira. Yaya kuma Mammah zataji? Sai kuma uwar gayya Zinneerah da batasan hawaba batasan saukaba. Shin yaya takene a zuciyar mai gayya mai aiki Abdul-Mutallab Kabir Shira? Moos'ab, Khalipha yaya zasuji da wannan juyin mulki?. Inna dake iƙirarin Zinneerah na birnin ikko yaya zataji?. Amsarku duk tana acigaban MAKAUNIYAR ƘADDARA da nakeda tabbacin yazo muku da sabon salo na musamman 🤏🏻🤓, kumuje zuwa yanzu aka fara wasan_*
Leave a Comment