Makauniyar Kaddara 34

 


Page 34*


............WASHE GARI ta kasance babu inda AK zaije. Khalipha ma sai yamma zaije school bakuma zai daɗeba zai dawo. duk sai da suka shiga sukaima Farah sannu da jiki, sai dai

kuma hajiya iya yanda taga Farah ragal yau sai abin yaso bata mamaki, gashi ita dai idonta bai gano mata wani alamun mai ciki tattare da Farah din ba, saurin kaudashi tai a ranta da danganta hakan da kowa yanada irin salon laulayin cikinsane. To maybe itama Farah nata salon kenan tunda gashi duk zamanta gidan bata taɓa fahintar Farah na laulayiba sai a jiya. Koda yake bama tasan dai cikin wata nawa bane. Amma da alama dai kamar yanda take hasashe ƙila bazai wuce ɗaya zuwa biyuba.

      Haka taita saƙawa da kwancewa har AK ya fito ya tuna mata yau fa zai kaita taga likita, yama zata zai iske ta shirya. Lallai ta shafa'a da cewar zataje ganin Doctor yau, amma da yake tsaf take dama sai kawai ta saka Bahijja ta ɗakko mata mayafinta a ɗaki. Dan Zinneerah da Meenal suna ɗaki su basu fitoba, dama ita kaɗaice a falon sai Bahijja da Jamal. Khalipha ma duk yau babu wanda ya gansa. Garama su Zinneerah sun fito sun gaida Farah da jiki sun kuma taya mai aikin gidan da aiki.

           Duk da baiga su Zinneerah ɗinba baiyi maganaba, saima kama hannun Hajiya iya da yay suka fice.


★★


     Bayan tafiyar su Hajiya iya da kusan awa ɗaya da rabi su Zinneerah suka fito, zamansu babu jimawa a falon sai ga Khalipha ya fito riƙe da waya yana magana alamar video call yakeyi. A bayan Jamal yaɗan ranƙwafo yana kanga masa wayar yanda zaiga mai magana. Cike da farin ciki Jamal ya ɗagama Moos'ab hannu yana faɗin, “Hy Yah Moos'ab”.

    Jin haka yasa Bahijja da Meenal tasowa duk suka dawo kusa dashi, suka sakashi tsakkiya Khalipha na bayansu. Duk da Zinneerah na falon ƙin tasowa tai, sai dai yanda suketa surutu da ihu yasata kallonsu tana murmushi, jin kuma suna ambatar sunan little ya sata jin ɗokin ganinshi amma ta kasa tashi taje garesu duk da Meenal nata kiranta. Daga ƙarshe ma saita miƙe ta nufi kitchen da ake hango komansa ta falon saboda da glass kawai aka rabashi da falon, duk abinda kakeyi acan zakaga na falo shima zai ganka. Shayi ta fara haɗama kanta dan yunwa takeji ko karyawa batayiba yau, sam abincin da ake kawo musu gidan baya mata daɗi, balle yau ma mai aikin gida ta haɗa musu breakfast ɗin tunda babu wanda ya fita tsakanin Yayansu da Khalipha masu sayo musun.

      “Gata nan na biyota da wayar ai Yah Moos'ab, kasan mutunuyar taka da miskilancin tsiya”. Ta tsinkayi maganar Bahijja a bayanta. 

          Tana juyowa Bahijja ta kamo hannunta ta ɗora mata wayar ta juya tabar kitchen ɗin tana dariyar shakiyanci. Dansu tuni suka fara harbo jigin Yah Moos'ab ɗin akan Zinneerah, sai dai suna tsoron faɗa ya ci musu kaniya.

       Wayar Zinneerah ta ajiye jikin wani ɗan maƙali dake a basket ɗin da kayan shayin ke ciki, fuskarta ɗauke da murmushin jin kunya ta dubi Moos'ab ɗin dake faɗin, “Gimbiya a rage wannan jan ajin mana Please”.

     “Kai Yah Moos'ab wane irin jan aji ana zaune ƙalau, ina fatan kuna nan lafiya?”.

        “Lafiya lau muke, dan ganima tare da Little Handsome tun safe na ɗakkosa daga wajen Gwaggo yau a gidanmu zai kwana insha ALLAH”.

     Idanu ta ɗan waro na mamaki, “Baka tsorin yay muku kuka Ya Moos'ab?”.

     Maimakon ya bata amsa sai ya karo mata fuskar little ɗin yana dariya. “Hy Gentleman kalla Aunty a waya tana maka magana”. Ya faɗa yana sunama little wayan. Ɗagowa kuwa Little dake kokawa da chocolate yayi ya duba wayar, sarai ya gane Zinneerah dan haka ya washe baki cike da ɗoki yake faɗin, “Aunty! Aunty”.

     Dariya sosai ta kama Zinneerah cike da jin daɗin ganinsa mai tsanani, idonta na tara ƙwalla tace, “Uhm su malami an ƙara wayo ashe?”.

     A dai-dai nan Farah ta shigo kitchen ɗin cike da tafiyarta ta ƙasaita da isa. Dama kuma hango Zinneerah a kitchen yasata shigowa dan tanason jamata winning akan shigo mata kitchen. Wani irin mahaukacin bugawa ƙirjinta yayi lokaci guda har takalmin ƙafarta na neman kadata a ƙasa. Tai azamar dafe kitchen cabinet jikinta na rawa. 

    Harga ALLAH da farko ta zata AK ne akan waya saboda yanda Moos'ab ya sakama little wayar kusa da fuska sosai, sai dai data ƙara matsowa taga wannan yarone. Amma duk da haka wani irin jiri-jiri taji yana neman kwasarta saboda ganin matsanancin kamannin. Babu wani neman excuse ta ɗauka wayar cikin hannunta tana faɗin, “Wannan yaron wanene haka?”.

       A yanda tai maganar, da tsoratar da Zinneerah tayi dan batasan da shigowarta kitchen ɗinba yasa Moos'ab maido da wayar kansa yana ɗaukar little ɗin yasa bisa cinyarsa tana ganinsu su biyu. Batare da tunanin abinda zai faɗa zai iya zama matsalaba yace, “Hy Auntynmu yaronmu ne. Bakiga yana kama da Yayanmu ba, shi ya haifa muna baku sani ba”.

     Harga ALLAH cike da barkwanci Moos'ab yay wannan furuci, sai dai ya zoma Farah a bahagon tunani, dan babu shiri ta nema sakin wayar a ƙasa sai da Zinneerah ta tarota ALLAH yasa bata kai ƙasaba. Itako a take takai ƙasan saboda santain tiles dana takalmin ƙafarta. Wata irin gigitacciyar ƙara ta saki wadda ta saka su Khalipha da sam hankalinsu baya kansu maido dubansu wajen, kusan a tare suka kwaso da gudu zuwa kitchen ɗin duk da su basajin mi suke faɗa. Ihun Fara ɗinma dan tayi da ƙarfi ne yasa sukajita, gashi kuma tana ta wajen saitin ƙofa ne ma.

      Shigowarsu tayi dai-dai da kaiwar Zinneerah durƙushe kanta, a kuma dai-dai lokacin numfashin Farah ya bar gangar jikinta alamar dai suma tayi. Ƙara ruɗewa Zinneerah tayi ta shiga jijjiga ta tana shafa fuskarta da kiran sunanta. Suma su Meenal duk ƙasa suka kai durƙushe suka shiga taya Zinneerah jijjigata ta.

     Khalipha da shi kansa yake a rikice duk da ya fahinci suma tayi yama rasa taimakon da zai bata, sai da Jamal yay hikimar ciro ruwa a fridge shima a ruɗe ya mika masa sannan.

     Yana ƙoƙarin ɓalle murfin gorar ruwan Hajiya Iya da AK suka shigo. Kuka da ihun su Meenal ya sakasu nufo hanyar kitchen ɗin cike da sassarfa. 

     “Ya ilahi, kuko yaran nan miya faru kuka cika gida da ihu haka dan ALLAH?”.  Hajiya iya ta faɗa tana isowa inda suke.

    Khalipha ne dake ƙoƙarin ɓalle murfin goran ruwan har yanzu ya kasa dan tsabar ruɗewa yace, “Granny Aunty Farah ce ta suma wlhy”.

      “Suma?”.

Cewar AK da shima ya karaso inda suke. Ganinta kwance a jikin Zinneerah da har yau take jijjigata tana kuka ita dasu Bahijja ya sakashi tabbatar da e da gaske suman kuwa tayi, amsar ruwan hannun Khalipha ɗin yayi ya zuba a hannu ya ranƙwafo ta bayan Meenal ya shafa mata ruwan akan fuska har bisa hannun Zinneerah dake shafa fuskar tata.

     A take ta kawo wani irin nannauyan numfashi. Ganinsu a kanta ta miƙe a zabure jikinta na rawa. Babu zato babu tsammani sukaga ta cakumi wuyan Zinneerah ta shaƙe. “Tsinanniya matsiyaciya. Dan ubanki yau sai kin faɗamin wacece ke? Ta gidan ubanwa wancan yaron ya zama ɗan mijina kuma?”.

         Wani irin kakari Zinneerah ta shigayi dan ba ƙaramin shaƙa Farah tai mataba, ga Hajiya Iya na ƙoƙarin janye hannunta dasu Bahijja amma sun kasa. Cikin rufewar idanu AK ya sauke mata mari dan ganin tana neman masa kisan kai a gida, bayan yanzu ya gama ganin yarinyar na kuka iya iyawa saboda shigarta wani hali.

     Azabar zafin mari ya saka Farah sakin Zinneerah babu shiri ta ƙwalla wata irin gigitacciyar ƙara da ta sakasu toshe kunnuwansu babu shiri. Banda Zinneerah datai baya ta zube riƙe da wuyanta tana ƙoƙarin jawo numfashi da ƙyar.

     Saurin riƙota Khalipha yayi, yayinda Hajiya iya kuma ta riƙo Farah da take neman fita hayyacinta saboda gigitar mari da abinda kunnuwanta suka jiye mata yanzu a bakin Moos'ab.

      “Wai nikam mike faruwane haka? Farah ki nutsu ki mana bayani, ya mun tafi mun barku lafiya kuma mu iskeku a wannan harmutsatstsen yanayin abin ban tsoro”.

     Kasa magana Farah tayi, sai jikinta ke wani irin rawa ga hawaye na rige-rigen sauka, yanda ta tsire AK da kallo tana sake hango tsananin kamanninsa da yaron ya sake harmutsa tunaninta, sai kawai ganinta sukai a ƙasa ta sake sumewa.

     Sake rikicewa sukai gaba ɗaya, dan shi kanshi yanzu al'amarin nata ya fara bashi tsoro. Duk da yasan halinta ta iya ɗaukar abu da girma amma na yau ɗin kamar yafi na kullum. Hajiya iya ce tace ya ɗauketa suje ɗaki kafin a ƙara saka mata wani ruwan. Baiyi musuba ya ɗauuta gaba ɗayanta zuwa bedroom ɗinta. Hajiya iya da Khalipha ne kawai sukabi bayansu, su kuma su Meenal suka kama Zinneerah suka tayar zuwa falo.   Jamal kuma ya ɗauka mata ruwa a fridge yabi bayansu zuciyarsa fal mamakin miya kawo wannan tashin hankali haka?. Baida mai bashi amsa, bai kuma zaton samun amsar ga Zinneerah a halin yanzun ba.


      A can ɗaki kuwa ruwa aka ƙara shafama Farah ta farfaɗo, sai dai tambayar duniya sunyi mata taƙi cewa komai sai uban kuka take dirza. Data kalli fuskar AK kuma ta hasaso ta little sai ta sake fashewa da wani kukan.

       Sanin halin Farah da AK yayi ne ya sashi jan tsaki tare da daka matsa tsawar data sakata shanye gumjin kukan da take ɗin. “Ki nutsu karki maidamu wasu ƴan iska mana, ya ana taroki kina zillewa sai kace wata karamar yarinya?”.

        “Wlhy bazanyi shiru ba, har sai an faɗamin ƴar iskar data haifi wancan shegen yaron da Moos'ab ya kira da naka, har wannan matsiyaciyar yarinyar ke magana dashi ta waya.....”

       A fusace ya zuba mata wani shegen kallo daya sakata haɗiye maganarta babu shiri ta ƙanƙame hannun Hajiya iya dake riƙe da nata. duk da bai fahimci inda zancenta ya dosaba sai da gabansa ya faɗi, juyawa yay ya sauke idonsa akan Khalipha.

      “Mike faruwa?”.

Kai Khalipha ya girgiza masa. kansa tsaye yace, “Wlhy ban saniba Yayanmu, nidai Moos'ab ya kirani ina ɗaki kwance yace na bama su Meenal waya su gaisa. na kawo musu ya gaisa dasu Jamal sai aka kaima Zinneerah wayar kitchen dan tana can kuma tare yake da little. Daga haka bamusan miya faruba sai ihun Aunty Farah mukaji kawai dan ko wucewarta kitchen ma ni wlhy ban ganiba”.

       Batare da yace komaiba ya maida dubansa ga Farah dake kuka har yanzu kamar zata shiɗe. “Meya faru ke da kika shiga kitchen ɗin?”.

        Wani irin kuka ta kuma fashewa da shi, tace, “Miya faru kuwa bayan ganin shegen ɗanka da nayi wanda kake ɓoyemin karna sani, a duk sanda nai maganar kanacin amanata da wasu matan a waje ka balbaleni da bala'in ina zarginka. Sai gashi ALLAH ya tona maku asiri ɗan uwanka yau ya fallasamin, ALLAH ya nunamin shege ɗan ƴar iskar yarinyarnan na waya dashi. Wlhy bansan haka kakeba Abdul-Mutallab, dana gwammaci dawwama banyi aure ba akan ganin wannan baƙar ranar........”

       “Haba kekuwa ƴarnan wane irin kalaman rashin ɗa'a ne haka kike jefar mijinki dasu? Ni wlhy saima yanzu na fahimci daga ina matsalar take, halan yaron nan na wajen Hauwa'u ta gani?”.

          Khalipha ne ya bata amsar cewa, “Eh shine kuwa Granny, dan Moos'ab ne yake can gidan ya ɗakkosa. To inaga sanda suke magana da Zinneerah ita kuma ta shiga kitchen ɗin ta gansu. Amma aunty Farah ya kamata kiyi haƙuri ai miki bayani, yaron nan baida wata alaƙa da Yayanmu sai ta zuminci, kamannine kawai da ga ALLAH b........”

       “Ƙarya kakeyi munafukin ALLAH ta'ala, idan kai kaƙi faɗar gaskiya ai shi Moos'ab ɗin da bakinsa yace ɗansa ne”.

       Hajiya iya da mamakin Farah ke neman kasheta tace, “Shi Moos'ab ɗin ya faɗa miki yaron na Moddibo ne?”.

      A gadarance tace, “Ƙwarai kuwa”.

   Yanda tai maganarne ya saka AK kaima bakinta bugu. sai dai da sauri Hajiya iya ta kare tana faɗin, “Kull da wannan ɗabi'ar, karka sake ka aro halin da ba nakaba kayi haƙuri abi komai a sannu harta fahimta. Kai Khalipha kiramin Moos'ab a waya yanzun nan”.

       Amsa mata Khalipha yayi yana fita falo domin amso wayarsa a wajen su Zinneerah. 


      Dai-dai lokacin da Khalipha ke ƙoƙarin kiran Number Moos'ab kiran Baffah ya shigo wayar AK. Cike da ƙarfin hali ya ɗaga, sallama yay yana mai ƙoƙarin dai-daita muryarsa dake a cinkushe. Sai dai kuma yanda yaji muryan Baffah sai ya bashi mamaki. 

        “Kaga Babana haɗani da Inna”.

“Baffah lafiya kuwa?”.

     “Karka damu lafiya lau, haɗani da ita”.

      Cikin sanyin jiki ya mikama Hajiya iya wayar yana faɗin, “Baffah ne”. Amsar wayar tayi takai kunnenta. Batare da sunsan mi Baffah ya faɗa mataba ta miƙe ta fito daga ɗakin. Hakanne yasa AK miƙewa shima ya fito domin jin ko Khalipha ya samu Moos'ab. Dan shi kaɗai yasan irin hukunci dazai masa idan har yaji gaskiyar zancen.

       Kamar jira suna fita kira na shigowa wayar Farah. Kamar zata share sai kuma ta duba wayar tana sharce hawaye. Wani irin zabura tayi saboda cin karo da sunan Mammah akan fuskar wayar alamar ta dawo kenan..............✍

No comments

Powered by Blogger.