Makauniyar Kaddara 33
Page 33*
............A ɓangaren Farah kuwa tabbas a cikin tsananin tashin hankali take. Tana ƙoƙarin dannewa ne kar a samu matsala. Amma lallai zuwan waɗannan yaran gidan nan bazai haifar da ɗa mai ido a gareta ba, dan bawai
zuwan nasu bane kaɗai matsalarta. Wannan itace dai-dai gaɓar da zata nisanci gidan nata da mijin ma ta koma zaman Morocco saboda killace ɓoyayyen sirrinsu, dama shirin yanda zasu saka AK maida Hajiya iya Nigeria sukeyi da zaran Mammah ta dawo daga China, sai gashi kuma wasu sun ƙaru. Gashi batama san iya adadin kwanakin da zasuyi ba. bata kuma san randa itama Mammah zata dawo ba.A take hawaye masu zafi suka silalo mata. Ta jawo wayarta domin ƙara gwada kiran Aunty Zakiyya. Tun jiya take nemanta amma wayan yaƙi tafiya. Ta tura mata saƙo babu reply. Yanzunma dai switch off.
‘Na shiga uku ni Farah, aunty ina kika shigane dan ALLAH?’. Ta faɗa a fili hankalinta na sake tashi. Har zatai wurgi da wayar sai wani tunani yazo mata. Cikin hanzari ta shiga fara neman babbar ɗiyar aunty Zakiyya. Cikin sa'a kuwa sai ga tata ta shiga. A take bakinta ya washe da murmushi, taja wani dogon numfashi ta fesar da ƙarfi.
Ana ɗaga wayar ko amsa sallamar yarinyar batayiba tace, “Ameera ina aunty?”.
Cike da shagwaɓa Ameera tace, “Aunty tana ɗaki, yanzu suka dawo daga Niger ita da Daddy”.
“Niger kuma? Kinga kaimata wayar”.
Ameera ta nufi ɗakin mamanta tana cigaba dama Farah surutun da ba fahimta takeba sam, burinta kawai taji muryar Aunty......
“Assalamu alaiki auta”.
Muryan Aunty Zakiyya ta katse mata tunaninta. Batare data amsa sallamarba ta fara magana, “Aunty ina kika shiga kwana biyu, damuwa na nan zata kasheni lokacin mutuwata baiyiba. Wlhy akwai matsala babba aunt, muna kukan targaɗe ga kuma karaya ta samu”.
Babu shiri aunty dake kwance tana hutun gajiyar da suka kwaso a hanyar Niger ta miƙe zumbur tanama Ameera nuni data je. Koda Ameera ta fita ƙofar ɗakin ta murzama key kafin tace, “Auta miya faru?, kinsa zuciyata na neman bugawa wlhy”.
“Wlhy aunty ni tawama saura ƙiris ta buga. Muda muke burin tafiyar tsohuwarnan jiya sai ga wasu huɗun sun ƙaru, harda shegiyar yarinyarnan data tureni naji ciwo, aunty kinsanfa wannan watanne ya kamata na taho nan ko naje Morocco.......”
“Kinga nutsu kimin bayani yanda zan fahimta Farah, wai ƴan gidansu ne suka sake zuwa nan london ɗin?”.
“Eh”. Ta bata amsa tana jan numfashin kuka. Kafin ta faɗa mata duk yanda sukai dashi akan zuwan su Zinneerah.
Itama kanta Auntyn hankali tashe tace, “Aiko bazai yuwuba Farah, kinsan dai wannan shine wata na biyar da samuwar cikinki, ya kuma zama dole kibar London dan Abdul-Mutallab ba mahaukaci bane ba. Yanzu babbar matsalarmu da Mammah bata nan, amma na tabbata itama ai lissafin cikin naki na'a ranta bazata wuce satin nanba zata komo nan london ɗin, ki kwantar da hankalinki karki ja ya fahimci wani abu. ko ita tsohuwar ta fahimta”.
“Aunty taya zan kwantar da hankalina. Wlhy na mugun tsanar yarinyarnan da har yanzu bansan alaƙarsu ba. Dan inaji a jikina akwai aure a tsakaninta da shi, n.......”
“K dalla rufama mutane baki, wai ke Farah wace irin banzar yarinyace. Ana ga yaƙi kina ga ƙura. Ki fuskanci abinda keda muhimmanci a gareki kin wani zauna tunanin kishin banza da wofi akan yarinyar da ƙilama bata ishesa kallo ba, cayay miki yana sonta ne? Haba dan ALLAH, kishin nan duk muna dashi muma dan ya zame mana tamkar gado, amma ke kam naki ya fara zama na hauka dan kina gaurayashi da zargi. Inda Abdul-Mutallab zai ƙara aure na tabbatar da tun sanda ake dabin ya ƙara tunda baƙya haihuwa daya ƙara ai. Amma yanzu ki maida hankali wajen abinda zai kawo miki mafita kinama mutane shirme bayan ke da bakinki kince yarinyar bama ta wuce shekara sha bakwai ba. Ubanmi zaiyi da sa'ar Ameera shida ke da ke mtsoww, ni kinma bani haushi wlhy sai anjima”. Ta ƙare maganar da yanke wayar.
A fusace itama Farah tai wurgi da wayar tata zuciyarta na mata zafi da maganganun auntyn ta. Miye laifinta idan tayi kishin mijinta? Ta yaya zata kasa fahimtarta bayan tasan ƙudirin waɗan nan mutanen akanta, ƙilama da biyu suka ɗakko yarinyar suka ajiye saboda mijin nata. Su dan basusan halin wannan munafukar tsohuwar dake nuna kamar bata gane komai amma tsaf idonta buɗe yake. Ita zama ta iya cewa a wajenta AK ya gado nuna halin ko in kula akan abu koda kuwa yana sane.
Haka ta cigaba da kai kawo a ɗakin har tsahon lokaci duk da tana jiyo motsinsu da hirarsu a falo taƙi fita.
★
A ɓangaren su Hajiya iya kuwa babu wanda ya damu da rashin sake ganin Farah a gidan. Hirarsu suka sha yau ma, salla kawai ke tashinsu har Khalipha ya dawo musu da abinci shima ya zauna aka ɗaura hirar da shi. Babu jimawa shima AK ya dawo gidan. Koda ya shiga yayo wanka shima dawowa yay cikinsu ya zauna ransa fes da farin cikin ganinsu cike da gidansa, abinda yayta fata da mafarkin gani a shekarun baya amma hakan bata kasanceba sai yanzun, duk da ba saka baki yake a hirarba sai ya gadama zaka fahimci yana tare da jin daɗin zaman. Hasalima aikinsa yaketa famanyi a lap-top kamar baya a wajen. Dan shima rashin ganin gilmawar Farah a gidan yasashi tunanin ko bata nan.
Sai kusan gab da magriba sai gata ta fito da alamun barci ta tashi. Sosai yake binta da kallon mamaki. Itako tayi kicin-kicin da fuska cike da takaicinsa. Kenan har takai ya dawo gidan bazai nemetaba saboda yana tare da ƴan uwansa. Batare da tayi magana ko kula gaisuwar dasu Meenal ke mataba ta juya ta koma ɗakinta hawayen takaici na zubo mata. Da kallo duk suka bita harta shige.
Fuskarsa na nuna alamun ɓacin rai yace, “Dama tana gidan?”.
Babu wanda ya iya bashi amsa a cikin su Jamal. Sai Hajiya iya ce tace, “Nima duk zatona ta fice ai, dan tunda kuka bar gidannan wani cikinmu baiji ko motsinta ba. Lafiya kuwa take Moddibo? Ya kanata kaje kaji”.
Maida kansa yayi ga aikinsa yana gyaɗama Hajiya Iya kai kawai, dan shi bazaiso ɗan sauran mutuncinta ya ƙarasa zubewa a idonsu ba. cikin son danne takaicinsa dason rufa asirinta, Ya miƙe yana faɗin, “Inaga to jikin natane babu daɗi. Granny wannan babyn naku na bama matata wahala ya kamata ku tsawatar masa”.
“Kai kai Moddibo kana nufin ciki ne da ita?”. Hajiya iya ta faɗa cike da zumuɗi saboda jin firucinsa.
Ƙayataccen murmushi ya saki yana kallonta. Hakan da yayi ya saka su Bahijja miƙewa suka hau murna da rawa. Yanda sukai ɗin sai ya sakashi jin ƙarin daɗi a cikin rai, a bazata suka haɗa ido da Zinneerah da take murmushi har haƙoranta na bayyana, ita dai tana daga zaune bata tashiba. Saurin maida nata idanun tai ƙasa tsigar jikinta na tashi, dan yanda yay murmushin ba ƙaramin sake fiddo kamanninsa da Little yayiba. A hankali shima ya janye nasa da raɓasu ya wuce zuwa ɗakin Farah ya barsu hajiya iya na jero godiya ga ALLAH da kirarin farin ciki Khalipha da Zinneerah na amsa mata da amin. Dan su Bahijja shirmen da suke na murna yasa bajin mi hajiya iya take faɗa sukeba.
Sai da suka bari yaja wasu ƴan mintuna da shiga sannan suka miƙe suma domin zuwa dubata. Sallama suka farayi ya amsa musu da cewar su shigo sannan suka shiga. kusan Zinneerah ce ƙarshen shigowa.
Farah na kwance a gadon. shi kuma yana zaune kusa da ita gab hannunta cikin nasa. Dan tunda ya shigo zuciyarta ta bata shawaran cewar tai amfani da wannan damar kawai tace bata da lafiya. Hakanne kawai mafitarta gudun samun matsala. Sai kuma akai sa'a shima ya shiga tambayarta mike damunta? Shine ta sanar masa da zazzaɓi ta yini da ciwon kai. amma tasha maganin da Doctor ya bata.
Kukan da tasha yasa idanunta kumbura dama gata fara. Ta ɗagosu da ƙyar tana ɗan dubansu da amsa sannu da addu'ar da suke mata. Koda idanunta suka sauka akan Zinneerah dake can ƙarshe bayan Khalipha sai da taji wani tuƙuƙin baƙin ciki. Ta janye idanunta dake sake cikowa da ƙwallar jin kishin kasancewar yarinyar a garesu, tanajin tsoron ganin wata mace da aure zai iya shiga tsakaninta da mijinta ta raɓesu, shiyyasa zaman Zinneerah a gidan yafi na kowa damunta a yanzu........
“Da alama ma dai yinin yau bakici komaiba?. ko kina da buƙatar wani abune a nema miki ƴar albarka?”. Maganar hajiya iya dake shafa mata kanta ta dawo da ita hankalinta. Kafin tace wani abu AK dake jin daɗin kulawar da Hajiya iyan ke nunawa akan matar tasa yace, “Nima abinda nake mata magana kenan kafin ku shigo, ya kamata ko tea tasha”.
“Banajin cin komai ne ALLAH”. Ta faɗa a hankali cike da shagwaɓa tana kallon AK ɗin da shima ita yake kallo har yanzu hannunsa cikin nata.
“A'a bazai yuwuba Farah. Zinneerah jeki ki haɗo mata ko tea ne da wani abin dan kinfi waɗanan nutsiwar yin abu”.
Kai Zinneerah ta jinjinama Hajiya iya da nufar ƙofa. Duk da tanajin Farah na cema Hajiya Iyan ta ƙoshi bata dakataba ta fice. Dan ita dai har cikin ranta tausayin Aunty Farah taji ya shigeta. Ta ɗanɗana wahalar ciki tasan mi akeji, shiyyasa da ance ciki na wahalar da mace sai taji tsananin tausayinta.
Bata wani zaman ɓata lokaci ba ta haɗa tea mai daɗi dan komai akwai, har kayan abinci akwai duk da ba irin wanda suka sani bane, dan mafi yawansu na gwangwanine da sauransu, taɗan ɗiba mata cake da Khalipha ya kawo musu ɗazun ta haɗa dashi ta koma ɗakin.
Duk suna tsaye har yanzun, batare data yarda ta kalli kowa ba ta nufi gaban gadon, tana niyyar ajiye tiren a ƙasa ya riƙosa batare da yayi magana ba. Ita kuma batai tunanin shiɗin bane dan haka ta ɗago, saurin sakar masa tiren tayi saboda shigewar idonta cikin nasa. cikin ɗan daburcewa ta miƙe daga ranƙwafowar da tayi a gabansu taja jikinta baya.
Da wani irin tashin hankali Farah ta tashi zaune tana duban Zinneerah ɗin dan komai akan idonta ya faru, zatai magana AK daya gama karantarta yay azamar katseta. Ganin yanda yay da fuska yasata haɗiye abinda tai niyyar faɗa akan Zinneerah ɗin, da wannan damar ya kalleta cikin ido yana jefa mata gargaɗin ki kama kanki.
Tare da ɗaukar kofin shayin ya miƙa mata. A cinkushe tace, “Ni nace na ƙoshi”.
“Ni kuma nace sai kinsha”. Ya katseta a kausashe.
“Haba-haba Moddibo minene abin faɗa kuma anan, kaga bani ni na bata da kaina. Kai sam baka iya lallaɓa mutumba wlhy”. Hajiya iya da batasan dalilin kaushin nasaba ta faɗa. babu musu ya miƙa mata kofin shayin.
Akan dole Farah tasha shayin da cake ɗin badan tasoba. Dan har wani ɗaci-ɗaci suke mata a maƙoshi. Musamman da idanunta suka sake gano mata AK na kallon Zinneerah da kanta ke a ƙasa tana latsa wayar Jamal hankalinta kwance. Ita kanta da take mace sai da taga annurin fuskar Zinneerah ɗin musamman yanda hasken wayar ya haskata ga kuma wani ɗan murmushi bisa fuskar tata dake da nasaba da abinda take gani a wayar. Itako Zinneerah ba komai yasata murmushin ba sai hoton Little da take gani a wayar Jamal ɗin.
Khalipha daya fahimci inda Farah ɗin ke duba rai ɓace ya sakashi cewa suje falo, duk da shi baiga kallon da Yayan nasu kema Zinneerah ɗinba sam. Bama shiba kowama ba lura da AK na kallon Zinneerah ɗin yayiba, dan itama ɗin dai shegen zargi dabin ƙwaf-ƙwaf ɗintane ya kaita ga hango abinda yake neman saka zuciyarta bugawa.
Fita sukai suka barta da hajiya iya da Yayan nasu. Koda suka dawo falonma Zinneerah shigewarta tai ɗaki acewarta lokacin salla yayi. Tanason kuma tayi tilawar karatu yau dan ta kwana biyu batayiba.
Suma ganin lokacin sallar yayi sai duk basu zaunaba suka nufi ɗaki, har Meenal dake fashi binsu tayi kawai...........✍
Leave a Comment