Makauniyar Kaddara 32

 


Page 32*


............Shigowarta gidan yayi dai-dai da dawowar Khalipha daga yo musu takeaway daya fitayi. Kamar koda yaushe shine ya gaisheta sabida halinta nason nuna isa. Koda ta shigo gidan ta kalli ko'ina sai taga yamata yanda takeson tsaftarsa duk da an cika

matashi, dan Farah mace ce mai tsafta, sannan duk wani abu da mace keyi dan ganin ta faranta ran miji Farah ta iyashi. Matsalarta kawai zafin kishi da hawa kan karatun su Mammah naƙin danginsa, dan tunda Khalipha yazo gidan ta dainama Adnan mafi yawan abubuwan da take masa na kulawa, ita burinta kawai Khalipha yabar mata gida. Shiko ya fita taurin kai yay kunnen uwar shegu da ita. 

         Samun komai yanda takeso yasata batayi ƙorafi ba ta shigo cikin kame kai da tsare gida ta gaida hajiya iya. Yanda take cika da batsewa yasa suma su Jamal gaisheta suna ƙoƙarin kama kansu.

     Ko kaɗan hajiya iya bata nuna mata komaiba ta karɓa mata gaisuwarta hardasu tsokana. Batare data kula tsokanar da Hajiya iyan kemataba ta nufi ɗakin AK tana harar Zinneerah da ƙudirta abubuwa masu yawa akanta. Dan har cikin ranta tanajin kishin zamanta a gidan fiye dasu Bahijja. Bakomai yasata jin sassauci akan su Bahijjan ba sai sanin uba ɗaya suke da AK babu wani maganar aure a tsakaninsu. Sai dai kishin cika mata gida da sukayi. Zinneerah kuwa tasan babu uwar da suka haɗa na shaƙiƙanci shiyyasa takejin zafinta. Itafa sabida shegen kishinta ko ƙawayenta bata yarda su raɓeta balle suzo mata gida. Tafi ganewa ayi catin ko waya yafi sauƙi ƴar nesa-nesa. Suma fahintarta yasasu janye jikinsu gareta suka bita yanda takeso duk da wasunsu ma sunyi aure. Tsaron nata kuma baisa wasu a cikinsu gagarar bibiyar mijin nataba acan waje batare da sanintaba. Danma shi AK ɗin na ƙoƙarin taka musu burki dan ba ɗaukar wargi ko shirme yake ba shima ɗin aƙidarsa tayi yawa.


     Tsaye ta samesa gaban Mirror yana fesa turare. Ta bishi da kallo cike da so da ƙauna da kishinsa mai yawan gaske, wanda ita kanta batasan adadinsaba. Sosai yayi ƙyau cikin pitch suit ɗin nasa da suka dace da kalar fatarsa mai sheƙi da ɗaukar idon mai kallo. Ga abu mafi soyuwa a gareta tare dashi shine kwantaccen sajensa da sumar kansa dake dai-dai misali dan ba tarata yayba da yawan tsiya. Tana nan dai-dai misali.

    Duk da yaji shigowar tata bai fasa abinda yakeyiba. Sai da ya ajiye gwangwanin turaren ya gyara zaman tie ɗinsa sosai da ƙara kwantar da sajensa sannan ya juyo gareta yana zuba mata manyan idanunsa masu cikar gashi da haske. Gasu da kwarjini masha ALLAH tamkar ba namiji ba. Haddace kowanne kalar kallonsa da ma'anarsa ya sakata risinar da kanta ƙasa. Kafinma yay magana tace, “I'm very sorry, bada niyyar kwana najeba zazzaɓine ya rufeni acan ka tambayi Mahma ma”.

         Janye idanun nasa yayi kawai yana girgiza kansa. Ya ɗauka agogonsa ya hau ɗaurawa batare da yace mata komaiba. A hankali ta tako garesa tana kama hanun da ɗage wanda yake ƙoƙarin ɗaura agogon dashi. Sakar mata yayi babu musu ta ƙarasa saka masa. ta sake ɗaukar wasu kalolin gwangwanayen turaren ta fesa masa tana ɗan murmushi, kafin kuma ta rungumesa cike da so da ƙaunarsa.

       Ajiyar zuciya suka sauke a kusan tare. Ya lumshe idanunsa da zagayeta da hannayensa shima yana lumshe idanunsa. Dan da gaske shima yayi kewar tata. Tunda suka dawo daga 9ja taƙi kwantar da hankalinta waje guda ta nutsu kullum da shirmen da take tashi musu dashi a gidan. danma wani abun tana shakkarsa shiyyasa take tsoron aikatawa. Fatan da addu'arsa shidai dama a kullum ALLAH ya gyarata ta koma Farah ɗinta daya sani ta baya mai tattalinsa da son farin cikinsa akoda yaushe.

      Ɗagota yayi yana mai tsare ƙyaƙyƙyawar fuskarta da kallo mai cike da ma'anoni masu yawa. “K baki gajiya dakai ƙarar mutane kullum wajen iyayenki?”.

       Cikin marairaice murya da shagwaɓa duk da ranta fal yake da tsantsar takaicin zaman su Hajiya iya gidan ta sake narke masa. “Ai dai nace kayi haƙuri, kuma kaima kasan a yanayin da nake shiyyasa nake shiga saurin fushi”.

        Kansa kawai yaɗan rausayar yana sauke idanunsa akan cikinta. Sai kuma ya ɗaura hannunsa saman cikin  tare da ranƙwafawa ya sumbacesa sannan ya ɗago. “Dolene inzo naima babyn nan gargaɗi ya bar rikitamin ke kina bani ciwon kai”.

      Karan farko tai ƴar dariya da sake rungumesa tana maijin tsananin daɗi. Dan tunda ta samu cikin nan bai taɓa nuna kulawarsa kamar ta yau ba. Kodan ta kasa kwantar masa da hankaline oho, dan wancan cikin daya zube lokacin da aka sanar masa da samuwarsa tamkar zaiyi hauka dan daɗi, yabi ya rinƙa tattalinsa da nuna zaƙuwar ganin ya fito duniya. Daya zube ɗin kuwa hardasu ƙwalla yayi, yabi ya shiga damuwa sosai, sai zuwan Khalipha gidan ne ya sakashi komawa normal life ɗinsa. yayinda ita kuma suka fara samun matsala daga nan.

        Shima ƙaramar dariyar yayi yana ɗagota. “Uhm kinga barni naje mu gaisa dasu Granny inada meeting 11am”.

     Duk da zuciyarta ta sosu da zancensa sai ta daure ta kanne, koba komai anci mata lokaci ai tunda gashi lokacinta sai ta raba dasu. Da basa gidan kuwa itace zata kasance da shi har lokacin fitar tasa ta cika. A tare suka fito dan tayi alƙawarin sai dai suci lokacin nasu tare itama dan bazata barmusu ba.


         A dining suka iske su Hajiya iyan zasuyi zaman karyawa da abincin da Khalipha yaje ya sayo.  Mai aikin Farah kuma ta shirya musu shi a dining tamkar a gidan aka girka shi. Khalipha na daga tsaye bayan Granny suna magana dan shi fita zaiyi. Juyowa yay saboda jin ƙamshin turaren yayan nasu da takun sa da baya ɓoyuwa ga duk wanda ya sanshi. “Barka da asuba Yayanmu”. Ya faɗa dai-dai suna ƙarasowa wajen.

        Hannunsa AK ya kamo cikin nasa yana faɗin, “Halan yanzu ka tashi kake kiran asuba likita?”.

      Fuskar Khalipha da murmushi yace, “Ai ni harma fita nayi naga gari Yayanmu, kai nedai nake tunanin yanzun ka tashi shiyyasa na faɗa”.

        Kafin AK ɗin yace wani abu Granny dake kallonsu cike dajin daɗi da sha'awar yanda shaƙuwarsu take wanzuwa cikin ƙanƙanin lokaci tace, “Ni nama zata yau bazai fitaba ganin har wannan lokacin bai fitoba. Bayan kuma nasansa shi baya saɓa lokaci”.

        Kallonsa ya maida ga Hajiya Iyan tare da jan kujerar kusa da ita ya zauna. “Yau meeting kawai nake da shi Granny shiyyasa na koma barci bayan sallar asuba. Ina fatan kin tashi lafiya?”.

        “Lafiya lau na tashi, sai dai waɗanan akkunayen da suka cikani da surutu jiya”.

      “Ai kece kika gayyatosu”. Ya bata amsa idonsa na sauka akan Zinneerah dake facing kujerar daya zauna. Tun zuwansa wajen tai ƙasa da kanta tana juya cokalin hannunta cikin abincin da sam ba daɗi yake mataba, wai a hakanma sai da Khalipha ya zaɓo musu wanda yasan zasu iyaci suji daɗinsa tunda ba sabawa sukai da abincin nan ba.

       Janye idanun yayi cike da basarwa yana ɗaukar tea ɗin Hajiya iya ya fara sha. Hakanne ya bama Jamal damar fara gaidashi. Sai Meenal ma ta gaisheshi. Itama Bahijja haka. Zinneerah ce ƙarshen gaishesan batare data yarda ta kalli inda yakeba. 

     Dukansu amsa musu yay kamar yanda ya saba cike da rashin sakewa. Hakan da yayi yayma Farah dake bayansa tsaye daɗi, tai wani ƙasaitaccan murmushi da ɗora hannunta kan kafaɗarsa tana sake matsowa jikinsa. Cike da yanga da ƙasaita tace, “Za kaci wani abune anan ɗin?”.

      “No, shayin Granny kawai ya isheni”. Daga haka ya maida hankalinsa kan hajiya iya ya fara magana ƙasa-ƙasa batare da kowansu yaji mi yake faɗa ba. Hakan kuma sai ya soki zuciyar Farah tabar wajen fuska a haɗe. Khalipha ya danne dariyarsa da ƙyar yana binta da kallo, tana gab da shigewa yace, “Kunga nikam bara na wuce school zanyi latti”.

      Ɗagowa AK yayi ya dubesa. “No ka jira na kammala mu wuce tare kusa da school ɗinku zanje nima”. “Okay thanks you Yayanmu”. Khalipha ya faɗa yana jan kujerar data rage ta dining ɗin ya zauna. 

      Farah ko dake ƙoƙarin shigewa ɗakin jin zancen nasu ya sakata dakatawa. Kamar zata juyo sai kuma mita tuna oho mata ta cigaba da tafiya harta shige ɗakinta tana taunar lip ɗinta na ƙasa da ƙarfi.

    Sosai zamansa shi da Khalipha a wajen ya saka Zinneerah shiga takura, garama Khalipha tana ɗan sakewa da shi. Amma wannan shugaban tsare gidan da ƙasaitar gaba ɗaya tare mata iska yake idan yana a waje. Sai dai kuma takan tsinci kanta cikin jin daɗi dan tana kallon little ɗinta tattare da shi. Yanzunma murmushi ta sake a bazata saboda faɗo mata a rai da Little yayi, dan hutun nan na kwanaki huɗu da tayi ba ƙaramin shaƙuwace ta sake shiga tsakaninta da yaron ba. Har takai tanajin kamar ta ɗakkosa su taho tare. 

    AK da sarai yaga murmushin nata ya ɗan kafeta da kallon sakanni a kaikaice ya ɗauke kansa, a ransa kuwa tambaya yake komi ya bata suga?. Baida mai bashi amsa dan haka ya miƙe dayin ɗan hugging Hajiya iya ta gefe ya sumbaci hannunta daya kamo. “Kimin addu'ar cin nasara, dan zamane mai muhimmanci zanje Granny”. Ya ƙare maganar idanunsa na faɗawa cikin na Zinneerah data ɗago a bazata. Yanda ya juya idanun da wani salo ya sakata saurin maida nata ƙasa ta risinar zuciyarta na matuƙar harbawa.

      Kasancewar babu wanda ya lura da abinda ya faru suka rakashi da addu'ar samun nasara harsu Jamal. Zinneerah dai akan laɓɓa ta fisgo tata addu'ar da ƙyar ta furta. Hayanr fita ya nufa yana saka rigar sanyinsa a saman suit ɗinsa fuska ɗauke da wani ɓoyayyan munafikin murmushi.


     Suna ficewa Zinneerah ta saki ajiyar zuciya. A take su Jamal duk suka kalleta. Hajiya iya kuwa ta saki wata ƴar dariyar data basu mamaki itama, sai dai koda suka maida dubansu gareta sai ta basar. Babu wanda ya sake magana dan dokace hakan ga Granny indai anacin abinci. Sai da suka gama ita dasu Bahijja suka gyara wajen domin taimakawa mai aikin da suke ganin kamar aikin gidan ya mata yawa saboda ƙaruwarsu.


     Yau ma dai hirarsu suka sha tare da kakarsu. Daga ƙarshe Zinneerah ta bama Hajiya iya tsarabar mmn sadiq tare da saƙon zungureriyar wasiƙa da batasan ta micece ba itama. Hasalima sai yanzu da ake buɗe kayan duk suka gani. Jamal ya ɗauka zai buɗe Hajiya iya ta girgiza masa kai da amsa. 

     Babu musu ya bata. Koda ta amsa itama sai ta miƙe taje ta adanata dan tanaji a ranta abune mai muhimmanci a ciki mmn sadiq ɗin ta rubuto, dan dama ɗazun da sukai waya da Baffah yake sanar mata Abbansu Sadiq ya sanar masa yanason ya bashi lokaci zaije har gida suyi wata magana mai muhimmanci. Amma shi yanata juya abin a ransa da tunanin wace maganace haka? Shiyyasama ya sanar mata.

   To a yanzu ganin wannan wasiƙar ya sakata jin maganar da Abban zai faɗama Baffah lallai tanada alaƙa da takardar kenan. Wannan hasashen ya sakata adana takardar sai ta nutsu sannan ta duba dan itama tayi karatun boko duk da bamai tsaho bane a wancan lokacin iyakartama firamare aji biyar aka aurar da ita...............✍

  

No comments

Powered by Blogger.