Makauniyar Kaddara 3


 *Page 3*



............Gajeje bata wani jima ba a ɗakin Inna tafito rai ɓace alamar dai wani rikicin suka sake tafkawa. Tana fita a gidan kuwa Inna ta fito a matuƙar hasale itama.

    Ɗakin su Zinneerah ta shiga. Zinneerah dake zaune tana hawaye har yanzun sai jin saukar lafiyayyen mari tayi. Zabura tayi zata ƙwalla ihu Inna ta daka mata tsawa.

      “Munahika yimani shiru kona lallasaki. Dan uban daya haiheki sheri da kikai shirin ƙullamani ashe? Wa billahillazi koda wasa kika sanarma wani a yanda kika bar gidanga sai na lahira ya hiki jin daɗi. Idan kuma kiji ƙarya don ALLAH ki hiɗi masu yanda akayi. Aradun ALLAH ubanki ma sai na ci masa bura-uba bamake kadaiba dan buhun ubanki. Lalatacciya kawai mai shegen nunkuhurci irin na uwarta”.

       Ita dai Zinneerah kuka kawai take jikinta na rawa dan tsoron Inna da takeyi. Sai da ta gama zazzage mata ruwan bala'i iri-iri sannan ta fice a ɗakin.


    Kuka kam Zinneerah ta shashi matuƙa. Ga ciwon da cikinta kanyi lokaci zuwa lokaci. Dawowar Sa'a gidan da kayan ɗanwake ta samu tsagaitawar kukan saboda lallashinta da Sa'a ta zauna yi. Ganin yanda Sa'a ta nuna matuƙar damuwarta yasata shanye sauran kukan nata dan ba yaune farauba a gareta ga halin Inna matar ubanta. 


WASHE GARI. 


       Da safe kamar yanda ta saba kafin tayi tafiya tanayin sallar asubahi ta fito tsakar gida ta hau shara. Duk da sanyin dake busawa na sanyin safiya haka taima tsakar gidan ƙwal da shara, ta gyara turken dabbobin Inna ta zuba musu sabon abincinsu. Sannan tazo ta fara haɗa wuta. Cikin dauriya take komai, dan wani irin zazzaɓine ke ratsa dukkan ɓargon jikinta a hankali. Haka ta cigaba da daurewa harta kammala dukkan ayyukanta wajibabbu a gidan. 

     Babu wanda ya fito a mutanen gidan sai can gyallowar rana. Sa'a ce ta fara fitowa tana mata sannu, sai ga Tinene ta fito itama tana mika da hamma dan sai yanzu zatai sallar asuba. Can sai ga baba ya shigo gidan, da alama tunda ya fita salla masallaci bai shigoba sai yanzun. 

     Dukawa sukai har ƙasa ita da Sa'a suna gaishesa. Ya amsa idanunsa aka Zinneerah da ya kwana da damuwarta a cikin ransa. Murya ƙasa-ƙada dan kar Inna taji yace, “Zinneerah yaya jikin naki?”.

      “Da sauƙi Baba”. Ta amsa kanta a ƙasa. 

    Kafin ya ƙara cewa wani abu Inna ta fito wuff. Da sauri yabar wajen saboda wani shegen kallo mai kama da harara data watso masa. Taja tsaki tana duban Zinneerah dake durƙushe har yanzu.

        “Ki tashi ki ɗebo mani ruwan rahi dan randunan gidanga duk babu ruwa. Kuma na rahin yamma nakeso dan ruwansa yahi garɗi da haske”.

     “To inna. Ina kwana?”.

A takaice ta amsa mata tana karasowa wajen murhun inda wutar da Zinneerah ta haɗa ta kama sosai.

      Fuskar Sa'a babu walwala tace, “Inna dakin barta sai anjima rana ta ƙara dagawa sama, kinga akwai sanyi garin sosai”.

         “To uwata, yanda kikace ai haka zanyi”. Inna ta faɗa a hasale..  

     Shiru Sa'a tayi, dan tasan gatse Inna tai mata.

     Zinneerah dama bata tsayaba, tuni ta ɗauki botikin fenti da hijjab ta nufi ƙofar fita cike da dauriya. Hakan ba sabon abu bane a gareta, shiyyasa fita ɗibar ruwan a yanzu bai dametaba. Kawai yanda takejin jikinta babu daɗine matsalarta. Amma haka ta nausa kanta hanyar jeji domin ɗebo ruwa. Harta isa babban rafinsu da su kansu basusan iyakar inda ya tsayaba bata haɗu dako kare ba. Ta ajiye botikin a gaban rijiyar da aka gina a tsakkiyar yashi wadda bawani zurfine da itaba. Hasalima a gabanta ake duƙawa asa kwano a kwarfo ruwan dake kwance. Bismillah ta ambata tana saka kwanon cikin ruwan, sai da ta kwashe na ciki tas ta watsar waje sannan ta jira ya sake taruwa ta diba a botikin nata. Bayan ta cikashi taf ta miƙe da ƙyar ta ɗora bisa kanta.


         Koda tai sallama Sa'a ce kawai dake wankin baki da gawayi ta amsa mata. Inna ko dake bakin murhu tana yanka tuwon dare daya rage tana jefawa a ruwan data saka a wuta ko kallonta bataiba. Hakama Tinene dake gefen Innar tana shan koko. 

      Sai da ta wanke duk randunan gidan guda huɗu sannan ta juye ruwan ta Sake komawa. Haka ta dinga kai kawo tsakanin gida da rafi ɗibar ruwa. Tun bata haɗuwa da kowa har mutane suka fara fitowa. harma da irinta masu zuwa sakkon ɗibar ruwan na rafi. Duk wanda ta haɗu dashi gaisuwar mutunci ce tsakaninsu. Har ALLAH yasa ta kammala gaba ɗaya.

        Zuwa yanzu Inna ce kawai a gidan, Baba ya fice wajen sana'arsa. Sa'a da Tinene kuwa sun ɗauki tallar gyaɗa da Riɗi da itama tasan tata tallan na jiranta ne.

     Sai da ta gama ɗauraye ƙafafunta da sukai futu-futu da ƙura tazo inda Inna ke tankaɗen garin ɗan-wakenta. 

     “Inna na gama ɗibar ruwan”.

Yanda tai maganar murya na rawa yasa Innar kallonta. Duk da yanayinta ya nuna bata jin daɗi hakan baisa Inna tambayarta ba. Sai ma sake tsuke fuska tayi da faɗin, “Zauna inason magana dake”.

     Babu musu Zinneerah ta zauna duk da ranta fal tsoro.

         Ƙare haɗe fuska Inna tai tana dubanta da ƙyau. A tsawace tace, “Miya maidoki garinga?”.

       Sosai gaban Zinneerah ya ƙara tsananta faɗuwa. Murya na rawa tace, “Inna sune suka koroni. Sunce basa buƙatar baƙauya irina. Kuma saida suka shinhiɗa mani uban bugu da aibantani kahin su bani jikka biyu da rabi su sani a mota....”

      “Munahika, halan wata tsiyar kika ƙulla masu acan? Saboda kina buƙulu da abunda zan samu na hassahi daga kuɗin aikin naki?”.

      “Wlhy Inna ba haka bane. Matar gidance bata sona dai na rantse”.

       “Ruhwa mani baki dan bantan ubanki. Ai hajji Lanti zatazo ne, zanji gaskiyar zance a gareta. Wa billahillazi naji saɓanin abinda kika hiɗi yanzu ina halakaki na halaka banza wohi babu mai sanin yanda akai. Ƴar banza, kinhi son mu zanna ga ƙugunki ga nawa a gida. Sabidda kina kishi dani tunda uwarki bata gida? To mu zanna ga hili ga mai doki ai. Dan uban mutum yayi idan yana iyawa dani ko. Tashi ɓacemin a ido kahin naita tsinarki har se zaman Danya ya gagari ubanki ma bake kaɗai ba”.

       Mikewa Zinneerah tai tana shartar hawaye. Duk da cin zarafi ga inna ba yaune farauba a gareta. Sai na yau ɗin yay mata zafi ainun. Karon farko taji tana kwaɗayin son sanin inda mahaifiyarta ke rayuwa a yanzu.

    Ɗakin kwanansu ta shige, ta faɗa akan yamusashshiyar katifar da Yaya Sa'a da Tinene ke kwana. Dan ita bisa tabarmar karauni take kwana kamar yanda Inna take buƙata. Dauɗaɗɗun kayan dake gefe ta jawo ta shiga rufawa a jikinta saboda sanyi da takeji.

     Sosau ta ringa rawar sanyi tana sambatun zazzaɓi. Har tsahon lokaci babu wanda ya shigo ɗakin. ba kuma ta ƙarajin motsin Inna ba. A haka barci yay gaba da ita mai nauyi.


      “Zinni!! Zinni!!. Wai dan buhun ubanki baki jina inata kware baki?”.

     A firgice ta tashi zaune jin irin kiran da Inna ke ƙwalla mata tamkar ana yaƙi. Ta amsa a kasalance tana ƙoƙari janye kayan data nausama kanta gefe dan ta samu damar mikewa.

       Fitowar tata yay dai-dai da shigowar Yaya Gajeje gidan da sallama. Inna ta sake tsuke fuska tana kallonta. sai kuma ta ɗauke kai ta maida ga Zinneerah dake fitowa tana rawar sanyi da yamutse fuska alamar bata da lafiya.

      “Oh sannu ƴar gata! Ina nan tsaye ke kina can kina jan nashari a ɗaki? To kizo ki haɗa mani wutar ɗan wake kar rana tayi..”

      Da sauri Yaya Gajeje tai saurin tare numfashin Inna, “Haba Inna, wane haɗa wutar ɗanwake kuma kike magana haka? Diba kiga yanda take rawar ɗari da alama bata da lahiya”.

       “Mtsoww!!” Inna taja tsaki. Kafin ta cigaba da magana a hasale. “To ina ruwana da ciwon nata. A yanzu ma wagga duniya waye ke da lahiyar. Gajeje ki hita idanuna, karki kaini maƙurar randa zan maki bankaɗa wallahi”.

      Murmushi Gajeje tai tana kaiwa zaune. Cikin kwantar da murya tace, “To inna idanma kin mani bankaɗa ai kin isane tunda kece kika haiheni. Ni dai kin sanni ban ganin gaskiya na riheta ai. Amma dai kiyi haƙuri ni bara na haɗa miki wutar tunda ita batajin daɗi. Harma sakin danwaken yau nice zan miki Innarmu kwantar da hankalinki”.

    Baki taɗan taɓe. sai dai batace komaiba. Hakan yasa Gajeje fahimtar taci nasara. Tai murmushi da tura hannu a zaninta ta ciro leda dake a lalitarta ta bujen ciki. Goro ne da alawa da biscuits guda biyu ƴan goma-goma. “Innarmu ga kayan suna”. Tai maganar tana miƙa mata.

      Ɗan sakin fuskarta tayi da miƙa hannu ta amsa. “Yo kuma ƙya bani duka. Su su Rabi'u fa?”.

      “Karki damu na ba Salame ta kai musu nasu suma. Wannan nakine. Nima Agali ya bani shi bayan mun hito”.

      “To, to maddala. Ni bamma sami leƙawaba yau na tashi da ƴar mashashshara ne. Sai zuwa anjima zanje nai masu an raɗa suna. Miye sunan ɗiyar ne?”.

       “Ai Hadiza aka samu, sunan Innar Bilkin aka saka”.

     “Tofa ɗigifi. Shi yanzu duk yawan gidansu ya rasa wazai saka sai sunan uwar matarsa?”.

      Ƴar dariya Gajeje tayi tana yafito Zinneerah dake tsaye rakuɓe jikin bango da hannu. “Inna kenan, ashe babu daɗi Lawal ya sakama Ummita sunanki shima”.

     Shiru tai bata tankaba. Dan an ƙure tsoguminta kenan.

    Zinneerah ta zauna tana gaida Gajeje. Cike da kulawa ta amsa mata da kai hannu a jikinta. Jin uban zafin ya sata ambaton, “Ya subahana. Zinni ai masassara ce a jikinki sosai. Kin karya dai ko?”.

      Ƙasa Zinneerah tai da kanta tana haɗiye hawayen dake neman zubo mata. Dan harga ALLAH yunwarma tanajinta mai tsananima kuwa. Saboda Inna batai mata tayin abinciba yasa ta haƙura.

     Shirunta yasa Yaya Gajeje fahimtar bataciba ɗin. Tasan za'a rina. Dan innarsu lamarinta sai du'ai. Bata sake cewa komaiba kamar yanda itama Innar bata tanka musu ba. ta dai miƙe zuwa gindin murhun inda tukunya ke aje saman duwatsun murhun. Tuwone a ciki na dawa da aka yanka aka ɗumama. Duk ma ya zama gutsatstsari alamar masu gidan sunci. Yaya Gajeje da ranta ke mata ƙuna ta ɗauka kwano ta zubama Zinneerah, tare da koriyar miyar kukar dake gefe. Har gabanta takai ta dire tana fadin, “Maza ci na samu mai sayo miki magani nan gidan Rahine idan bata fita tallar kayan koli ba”.

      Jan kwanon Zinneerah tayi gabanta, babu musu ta hau ci dan yunwa takeji sosai..

     Inna dai bata sake tankawaba har Zinneerah ta gama cin tuwon nan. Yayinda Yaya Gajeje ta koma can wajen murhu tana haɗama Inna wutar ɗanwake da ƙoƙarin saka ƙatuwar tukunyar da take amfani da shi.      


            Kasancewar Yaya Gajeje a gidan yau sai ta samu ƴar salama. Dan har Baba daya shigo shima ya ɗan samu sakewar bata kulawa, harda siya mata awara. 

     Washe gari kam Inna bata saurareta ba. Duk da ta fahimci har yanzun bata da lafiya, dan ba'a ƙulla awa biyu Zinneerah bata raɓe gefe tana riƙe cika ba alamar dai cikin na mata ciwo. 

      Sai dai tsabar rashin tausayi ko'a fuska Inna bata nuna ta fahimtaba, daga ƙarshema tallar riɗi da gyaɗa ta sakata ɗauka. Da Sa'a tayi magana kuwa ta hayayyaƙo mata da masifa kamar zata daketa. Dole tai shiru tana maijin babu daɗi da halin mahaifiyar tasu.


★★★


            Yau satin Zinneerah ɗaya kenan da dawowa da ga Katsina. Tun Inna na zuba idon ganin Hajji Lanti ta biyo bayan Zinneerah harta fara sarewa. Dan har ranta ta ɗauki alwashin sai Zinneerah ta koma, bazata taɓa yarda kuɗin data ƙwallafa ran samu su wuceta a banza ba.

       A ɓangaren Zinneerah kam a kwanakin nan daka kalleta kasan bata da lafiya. Musamman yanda ta wani rame sosai. Gashi sam bata da kuzari a jikinta. Yanda ta saba aiki ada da kazar-kazar yanzu sam bata iya hakan. Komai zakaga tana yinsane da sanyin jiki kamar mara ƙashi. Inna tayi masifar harta gaji ta barta, sai dai zagi da tsina ne tana shansa, dan ranar har marinta tayi.

       Yau ma kamar kullum tana gama ɗibar ruwa da dukkan aikinta na gidan tai shirin ɗaukar tallar riɗi da gyaɗa. Tinene kaɗai ta samu a tsakar gida tana suyar wainar fulawa. Inna kuwa ta fice barka wai. 

      Ɗakin Inna ta shiga ta ɗakko ƙaton farin botikin da aka cika da gyaɗa da riɗi, ta sake fitowa tsakar gidan. Cike da sanyin murya tace, “Tinene idan Inna ta dawo ki hiɗi mata na wuce”.

      Kallon banza Tinene tai mata ta ɗauke kanta. Cike da rashin mutunci tace, “Inma wannan allagiran kike mawa kima cire rai yarinya, dan aradu baki cin ko ranyo anan”.

     Murmushi Zinneerah tayi kawai ta fice, dan tasan inhar ta biyema Tinene zama su iya faɗa, itako bata da wannan ƙarfin yanzu kam.

         Dai-dai fitowarta ƙofar gidan nasu gabanta ya faɗi. Tai ƙasa da kanta saboda cin karo da fiska mafi daraja a zuciyarta bayan ta iyayenta. Ba kowa bane face saurayinta Babawo wanda a yanzu ya maida akalar neman auren nasa kan yayarta Karima da yaya Sa'a ke bimawa. Babawo ya sota tun bata san kantaba. Da farko matsin rayuwar data tsinci kanta a hannun Inna dalilin rashin mahaifiyarta a gidansu Babawo yake tausaya mata. Shine silar cigaba da karatunta bayan gama firamare , shine ya tsaya tsayin daka harta shiga makarantar gaba da firamare (Secondary), tana aji ɗaya wani kawunsa ya zo ya tafi da shi kaduna. Bai dawo ba sai da ya shekara. Kamar yanda ta ɗokantu da zuwansa haka shima ya ɗokantu da ganinta. Yazo mata da tarin tsaraba, tare da burin iyaye su shiga akan maganar aurensu, a cewarsa data kammala aji uku na sakandire zasuyi aure. zai wuce da ita can kaduna sai ta cigaba a gidansa har sai taga ƙarshen biro. Hakan yama Zinneerah daɗi a zuciya da ruhi, sai dai kuma a kwana biyu da zuwan Babawo labarin ya canja alƙibla. Dan kuwa bai komaba sai da tsuntsun soyayyarsa ya tashi daga kanta ya koma kan yayarta Karima yar wajen Inna ta uku. Ƙiri-ƙiri ta gaza gane kan Babawon ta, ya canja mata gaba ɗaya. Kosan ganinta bayayi. Taci kuka sosai, ta kuma shiga ruɗani, dan har ciwo tayi. Mutane sunta kace nace akan wannan al'amari, wasu na faɗin asiri Inna taima Babawo ɗin, wasu suce kuma shine dai yake ganin Karima ta fiye masa tunda ita babbar budurwace wadda akema surutu akan rashin samun miji. Dan Karima shekararta sha takwas da wasu watanni, a ƙauyen kuma sa'annin su Zinneerah sune dai-dai aure ƴan sha biyu. Amma sai dai ita ƴaƴan Inna dama sukanyi jinkirin samun miji a ƙauyen saboda mugun halinta, shiyyasa ma har yau babu wacce ta taɓa aure a nan cikin Danya. Gajeje na kauyen Sanni, Atine na can Rimaye. Sai yanzu ga Karima da Sa'a waɗanda duk sun zama manyan ƴammata. Karima nada sha takwas Sa'a na sha shida. Sai Tinene sa'ar Zinneerah itace auta.

         Bayan wucewar ruɗanin canjawar Babawo da shekara ɗaya da wasu wattani, dan har manya sun shiga maganarsa da Karima sai kuma Inna ta haɗata da hajji Lanti da tai sanadin kaita birnin Katsina da niyyar aikatau, inda ita kuma ta gudo ta dawo gida........

         “K! Wai baƙyaji ana miki magana”.

   Tsawar da Babawo ya daka matace ta dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi batare data farga ba. Saurin haɗiye hawayen da suke neman zubo mata tayi tana girgiza masa kanta.

         Ta ɗan risina kaɗan tana faɗin, “Kayi haƙuri Ya Babawo banji bane wlhy”.

      Tsaki yaja yana taɓe baki da jifanta da wani irin mummunan kallo na tsana, wanda a da idan wani yay kuskuren yimata irin wannan kallon sai inda ƙarfinsa ya ƙare. A gadarance yace, “Kiramin Karima nace”.

        Idonta ƙasa-ƙasa tana mai satar kallon yanda ya ƙara ƙyau da cikar zati tace, “Yaya Kareema bata nan, tana Rimaye wajen Yaya Atine, nima ban dawo na sameta ba”.

       Tsaki yaja yay gaba batare da ya sake tanka mataba. Ta bisa da kallo cike da tsananin so da ƙaunar da take masa har yanzun. yayinda ƙamshinsa daya bar mata take jinsa mafi daraja da tsada a cikin iskar da take shaƙa. Duk da ƙarancin shekarunta zuwa yanzu tasan minene soyayya, dan shine ya rene ta akan bigirenta, tun bata fahimta harta fara ganewa da banbancewa, sai gashi rana tsaka rabuwa tazo musu bisa tafarkin MAKAUNIYAR ƘADDARAR da batasan sila ko mafarinta ba, tunda har yanzu bazata iya faɗin dalilin rabuwar tasuba balle dalilin komawar Babawonta kan yayarta.

     Hannu tasa ta sharce hawayenta tana gyara riƙon botikin gyaɗa da riɗinta ta cigaba da tafiya ranta na mata zafi da ƙuna.............✍


No comments

Powered by Blogger.