Makauniyar Kaddara 27

 


Page 27*


...........Alhmdllh an samu daidaituwar jikin hajiya iya, amma bawai tana a cikin hayyacinta yanda ya kamata baneba. Shiyyasa shima AK ya kammala dukan

shirinsa akan tafiyar da ita. A wannan karon Baffah baiyi yunƙurin hanashiba. Sai ma taimaka masa da yay da wasu abubuwan kasancewar tafiyar ta zama ta gaggawa.

        Duk wanda ya kalla shirawa a yinin yau yasan lallai an taɓa musu wani babban jigonsu, dan kowa idanu jajur. Daga masu kukan zuci har masuyin na zahiri irinsu Zinneerah. Dan ita dasu Bahijja haɗe kawuna sukai sukaita rusar uban kuka sai da Yah Haneef yayta lallashinsu da ƙyar da nuna musu sumata addu'a sannan suka ɗan nutsu.


        Haka suka kasance yau yini guda a asibiti likitoci nata ƙoƙarin su, yayinda AK keta shigi da fici na ganin sunbar Nigeria a yau insha ALLAH. Yau ko ƙwaƙwaran abinci babu wanda ya samu yaci a cikinsu, sai ruwa da ƴan kame-kame. Salla kawai ke tashinsu.

     Yah Adnan bai farga da babu matarsa a asibitinba sai da zasu koma gida domin shiryawa. Ransa ya ɓaci matuƙa amma ya daure ya shanye har suka isa gidan. Kamar yanda yay hasashe kuwa a gidan ya isketa wai taji ciwo a ƙafa saboda turewar da Zinneerah tai mata da asuba, ga kuma zazzaɓi tanaji. Duk da ya lura da yanda take alamar kuka ta zauna tasha baibi takantaba ya hau shirya musu kaya da kansa batare daya mata bayaniba. Yana gamawa kuma fiwowa yay zuwa ɗakin hajiya iya. Inda ya iske Zinneerah zaune tanashan sabon kuka. 

     Tsaye yay kawai shiru yana kallonta batare dayayi maganaba tsahon lokaci. ita kuma batasan da shigowar tasaba kanta na a cikin ƙafafunta ne. Yaɗan furzar da huci da cije lip ɗinsa yana ƙarasa takawa cikin ɗakin da ƙyau. Gyaran muryar daya saka Zinneerah ɗagowa yayi. Kallon cikin ido sukaima juna sai kawai ta fashe masa da kuka. Idanunsa ya lumshe yana ɗan kauda kansa gefe. 

         “Dan ALLAH Yayanmu kaje dani duk inda zaku kaita”. Ta faɗa kukanta na kuma tsananta. Baice mata komaiba ya nufi bathroom ɗin ɗakin dake gyare tsaf duk da yau babu wanda yabi takansa. Ruwa mai ɗumi ya tara a botiki ya fito, inda ya barta anan ya isketa tana cigaba da kukan nata. “Tashi kije kiyi wanka”. Ya faɗa yana nufar inda littatafan hajiya iya suke na addini batare daya sake kallontaba.

     Jin abinda yacene ya saka Zinneerah miƙewa da saurinta duk zatonta ƙorafinta ya karɓune. Littatafan ya gama ɗauka da wasu ƴan abubuwa na Hajiya Iyan yasa a ƙaramar jikka. a saman gado ya barta ya fice domin zuwa shima yayi wankan.


     Sauri-sauri Zinneerah tahau shiri bayan fitowarta wanka kasancewar ba salla takeba. Tana gamawa ganin jikkar daya ajiye akan gado itama ta jawo akwati tahau haɗa nata kayan. Tana tsaka da neman wayarta da tun jiya bayan ta kira mmn sadiq bata sake ganin wayarba, har so tai ta kirata yau ma ta sanar mata halin da ake ciki amma sai bataga wayarba.  

      Shigowar AK ɗakin da sallama ciki-ciki, Baba Rahi biye da bayansa ɗauke da tire ya sata dakatawa da leƙe-leƙen neman wayar da takeyi.  Juyowa tai tana kallonsu, yanzu kam shima yayi wankan dan yana sanyane cikin ƙananun kaya sai uban ƙamshinsa ke tashi dan yama danne nata turaren data saka. Shiko kallo ɗaya yay mata ya ɗauke yana maidawa kan akwatin data haɗa kaya. Baiyi maganaba sai zama da yay  cikin sofa ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana sauraren Baba Rahi dake lallaɓata ta zauna taci abinci.

      “Baba Rahi na ƙoshi, ALLAH bana jin yunwa”.

       Manyan idanunsa da launinsu ya canja gaba ɗaya a yunin yau ya ɗago ya zuba mata cike da gargaɗi, babu shiri ta amshi kofin shayin da Baba Rahi ke miƙo mata tai ƙasa da kanta tana kaiwa baki badan yana mata daɗi ba, dan bakintama ji take yana wani ɗaci-ɗaci. Ɗauke idanun nasa yay ya jingina da kujerar yana mai lumshe su. Sai dai kuma yana kallonta ta ƙasan idon. 

       Baba Rahi ce ta cigaba da lallashinta har taɗanci abincin shima kaɗan ta ture idanunta cike da kwalla tace ta ƙoshi, Batare da Baba Rahi tace komaiba tahau tattare kwanikan zata fita da su ya dakatar da ita. “Baba barsu anan jeki abinki”.

       Amsa masa Baba Rahi tai tana maido tiren ta ajiye, Zinneerah kuwa kallon inda yake ta ɗanyi kamar zatai magana sai kuma ta maida kanta ta duƙar. Shi kuma batare daya tashi koya buɗe idanunba yace, “Tashi ki ɗauka maganinki da abincin kizo nan”.

       Ita tama manta wai bata da lafiyane. Shakkarsa yasata miƙewa ta ɗakko din tayi yanda yace batare data musa bin umarninsa ba. Ɗagowa yay daga yanda yake a zaune ya buɗe abincin da kansa ya sake tura mata gabanta. “Na baki 10minutes kawai ki cinyesa”. Daga haka ya koma a yanda yake kamar ɗazun. Cika idanun Zinneerah sukai da ƙwalla. Taja abincin gabanta tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallar tata dan bataga wajen yin wargi ba. ALLAH ma ya sota abincin ba wani mai yawan tsiya bane dan baba Rahi dama ta santa bawani cin abincin take sosai ba. Sai da ta gama tasha maganin sannan ya sauke ƙafarsa da gyara zamansa yana faɗin, “Zonan”.

     Babu musu ta miƙe zuwa garesa. Sai dai inda ya nuna matan ta zauna ne yasata jin shakku tatsaya tana duban gefen nasa. Harar daya balla mata ce ta sata zaman babu shiri daga can ƙarshen kujerar duk da tazarar ba wata mai tsaho bace a tsakaninsu.

        Ƙasa tai da kanta tana wasa da yatsun hannunta, ji take ba'a taɓa saka rayuwarta a takuraba irin ta yau ba, dan kwarjininsa da ƙamshinsa gaba ɗaya sun sakata jin ɗakin ya musu kaɗan. Shiko ko a jikainsa kallon hanunta da taketa faman cuɗawa a juna kawai yakeyi cike da nazari. Mikuma ya tuna oho masa sai yay saurin kauda kansa. Kusan mintuna uku suna a haka shiru kafin ya sake dubanta.

        “Kikace zaki bimu?”.

Ya faɗa ciki-ciki idanunsa ƙyam akan fuskarta.

     “Eh Yayanmu dan ALLAH”.

  Ta bashi amsa itama murya na rawa. Kwarjininsa na sake tsumata dan ta kasa ɗagowa ta dubesa. Tamkar bazai sake cewa komaiba sai kuma yaɗan girgiza kansa. “Idan kin bimu karatunki fa? Ko kin jinginesa kenan?”.

     Idanunta da suka ciko da ruwan hawaye ta ɗago a karo na farko ta kallesa, sai gasu a cikin nasa dan shima ita ɗin yake kallo. Yanda ya tsatstsareta dasu ne ya tilastata maida nata ƙasa hawayen cikinsu da batasan na miyeba na gangarowa. Sai dai tana danganta zubar tasu da takurar da tayi na kasancewar su zaune a waje ɗaya yanda mafalkinta bai taɓa kaiwaba.

    Ya sake maimaita mata cewar, “Nace karatunki fa idan kin bimu?”.

      Muryarta na rawar kuka tace, “Yayanmu nidai kaje dani dan ALLAH, idan na dawo naje makarantar, inason na kasance da Granny kawai”.

        “Saboda karatun baida muhimmanci a wajenki ko?”.

     Kasa cewa komai tayi a wannan gaɓar, hakan ne ya sakashi sauke murya ƙasa da alamun lallashi a ciki yace, “Bazaki bimu yanzuba, dan shi ilimi abune mai muhimmanci ga mai nemansa, adalci ɗaya zan miki shine idan kunyi hutu zakizo ki ganta ok”.

      Sharrr hawaye suka sake ɓalle mata. Ta ɗago zatai magana ya miƙe abinsa yana faɗin, “Na gama magana ki tashi ki saka mata kaya kala biyu a wancan jikkan dana ajiye, sai abubuwan da kika sani masu muhimmanci da take amfani dasu yau da kullum. Wannan kayan naki da kika haɗa kuma ki kaisu sashen Momie dan zaki koma da zama can wajenta”. 

       Daga haka ya fice abinsa ko waiwayenta baiyiba duk da yaji kukan data fashe dashi. Kansa kawai ya girgiza yana ƙara jinjina ƙuruciyarta da shagwaɓa a ransa.


       Karo ya kusanci da Farah wadda ke ƙoƙarin shigowa ɗakin alamar biyosa tayi, ya ɗan bita da kallon mamaki kamar zaiyi magana sai kuma ya ɗauke kansa da raɓata ya wuce abinsa. Har tayi kamar ta shiga ɗakin Hajiya iyar taga mi yayo a ciki tun ɗazun sai kuma ta fasa tabi bayansa da sauri. Yana shiga ɗakin itama tana shigowa. Zama yay cikin kujera ya hau haɗa shayin daya saka Baba Rahi dafa masa shima. Sai da ya kammala zai fara sha sannan ya kalli Farah data zauna kusa da shi ta wani tsatstsaresa da idanunta manya.

      “K kina ganin abinda kikayi yau shine dai-dai? Kowa yana asibiti ke kina gida kwance?”.

       Cike da isarta tace, “Amma dai kasan nima banda lafiya ne ai. Sannan wannan shegiyar yarinyar sanda ta shigo ɗakinan ta ɗauka wayoyinka turenifa tayi a ƙasa amma ko waiwayena batayiba. Jiba kaga yanda ƙafata ta kumbura”. Tai maganar tana nuna masa ƙafar da cigaba da faɗin, “Wlhy yanda ta sani jin azabarnan itama sai na sakata taji wadda ta fita dan saina karyata kafin nabar gidan nan”.

       Ɗauke idanunsa yayi daga kan ƙafar kamar baiji mita faɗaba. Duk da masifar data cigaba dayi akan Zinneerah ɗin bai tanka mataba harya gama shan tea ɗinsa sannan ya miƙe. Hakan da yay ya ƙona ran Farah, sai dai ganin ya ɗakko man zafi ya dawo ya zauna da kama ƙafar tata ya ɗora a jikinsa ya sakata sauke ajiyar zuciya.

     Duk da ya jita baice uffanba ya hau shafa mata maganin a wajen yana ɗan dannawa kaɗan-kaɗan itako tana zuba shagwaɓa. Sai da ya tabbatar maganin ya shigeta sannan ya ajiye ƙafar yana dubanta cikin ido. “Yau zamu wuce”.

     Mamaki ƙarara a fuskarta tace, “Ina?”.

       Kansa tsaye yace, “London, Granny zataga Doctor acan”.

     Jitai kamar an daɓa mata mashi a ƙirji. ta tattaro yawun takaici ta haɗiye muƙut tana dubansa, “Amma my Hero duk likitocin ƙasarnan har sai an kwashi kamar Granny dake fama da jikin tsufa an wahal da ita zuwa wani waje”.

       “Ke kika kallesa a fuskar wahala. mu neman sauƙi zamu insha ALLAH ”.

       Harara ta zuba masa a kaikaice zuciyarta nayi mata zafi, cikin ɗan rawan murya tace, “To sai dai kuje ni kasan dai babu inda naje. Bazai yuwu na shigo ƙasarnan ba kuma ban ziyarci kowaba”.

        Juyiwa yay ya kalleta cikin ido fuska a tsuke ainun, cike da gargaɗi da barazanarsa yace, “Da zaki taho ai nan aka turoki, dan haka iya nan ɗin zaki tsaya. Nan da awanni shida jirginmu zai tashi”.

       Yanda ya tsareta da idanun ya hanata iya cewa ƙala, dan tasan mi wannan kallon nasa ke nufi a gareta. Dole ta tsuke bakinta hawaye na rige-rigen sakko mata. Batare dayabi takantaba ya miƙe ya fice dan yanason yin magana da Baffah.

     Miƙewa tai a harmutse itama ganin ya fice tana masifar bazata yarda hajiya iya ta bisuba. Dan babu yanda za'ai a jajubar musu gayya a takurawa rayuwarsu. Khalipha ɗinma ta ɗauki alwashin wannan karon bazai koma mata da zama a gidaba. Sai dai ya koma hostel kamar yanda Mammah ta faɗa. Haka taita masifa tana kuka da neman wayar Mammah amma taƙi shiga. daga ƙarshe sai auntynta ta samu ta kira sukaita masifar tare, Auntyn ta ta katse wayar ta kirashi. Yana ganin kiran sanda yake tare da Baffah yaƙi ya ɗaga dan yasan zancen dai bai wuce mai hali tayi halin nataba...........✍


No comments

Powered by Blogger.