Makauniyar Kaddara 16

 


Page 16*


............Kamar da wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai Hajiya Iya da gaske take akan amshe Zinneerah daga hannun su Mama. Dan take a wajen ta ɗaga waya tai kiran Alhaji Kabir da dukkan ahalin gidan ke kira da suna Baffah.

     A rayuwa Alhaji Kabir bai haɗa uzirin mahaifiyarsa dana kowaba. Kai bama shi kaɗaiba har sauran ƴan uwansa da jikokin familyn babu mai sakaci da buƙatar Hajiya Iya. Dan ita ko wasan jika da kaka sai taso takeyinsa. 

    A cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi a sashen nata. Hannu ya bama Abba suka gaisa yana faɗin, “Ai bansan ka shigo gidanba Alhaji Isma'il, dana fito mun gaisa”.

       Abba yace, “Wlhy yanzuma na shigo Yayanmu, nazo wucewa da ƙannenka ne, sai kuma ƴayanka dana kawo suma suyi gaisuwa su kuma gaida Gwaggo”.

       “Kai kai masha ALLAHU, lallai yau ka farantamin sosai sosai. Kuzo-kuzo ƴaƴan albarka ga babanku da baku saniba ko”.

     A nutse su Sadiq duk suka nufesa harda Zinneerah. Sai dai ita ta durƙusane daga gefensa kaɗan. Saɓanin su Abdul daya jawo jikinsa ya rungime. Sai da su Sadiq suka gama haishesa ya amsa da kulawa da tambayarsu sunyaensu da ajinsu nawa a makaranta kafin ya maida dubansa ga Zinneerah itama.

     “Ikon ALLAH, Inna wannan ai saikace Inno ta haifeta dan kamanninsu. Ɗiyata yaya sunanki?”.

       Zinneerah da kanta ke duƙe tana wasa da yatsun hannuna tace, “Zinneerah”.

“Masha ALLAHU suna mai daɗi kamar yanda kike ƙyaƙyƙyawa ɗiyata. ALLAH yay muku albarka. Ke ajinki nawa a makarantan?”.

     A take murmushi ya subucema Zinneerah tace, “Abba ss1”.

      “Kai-kai, kice Maman nawa bata wasa bace ƴar boko ce”.

      Barkwancin nasa ya saka dariya suɓucema Zinneerah. Yayinda hakan kuma ya sake saka ƙaunarta a zuciyar Alhaji Kabir dan nutsuwar yaran da tarbiyyarsu ya matuƙar birgesa, musamman Zinneerah ɗin da take mace.

    Kallonsa ya maida gasu Mmn Sadiq yana fadin, “You see. Gashi kun fara tara zuri'a amma basusan kowaba suma. Sai dai ko a hanya naci karo da Zinneerah ai nasan jini nace. Idan akaimin gaddama kuma har kotu zan kai dole a bani abata”.

      Sosai maganar tasa ta saka kowa dariya. Hajiya Iya tace, “Aini kiranma danai maka kenan. Dan nikam dai babu mai rabani da mai kama da Inno tazo gida kenan”.

      “Ina bayanki Innata. Dan haka Alhaji Isma'il dan ALLAH a taimakemu badan halinmuba a bamu Zinneerah, bamason a kalli hakan kuma fin ƙarfi roƙo muke gwiwoyinmu a ƙasa. Ƙila hakan ya zama sanadin gyaruwar zumincin dake neman kufce mana. Amma kuje dai kuyi shawara. Idan kuma akwai matsala dan ALLAH karkuji kunya ku sanar mana kanku tsaye zamu fahimceku insha ALLAH. Kunga ko ba'a bamuba sai take zuwa mana hutu ita da sauran ƴan uwanta lokaci-lokaci”.

        Cike da jin kunyar wannan roƙo nasa Abba yace, “Ai kunfi ƙarfin hakan a garemu”. Yay maganar yana duban Mmn Sadiq data duƙar da kai.

       Daga Hajiya Iya har Alhaji Kabir suma idonsu na kanta. Dan haka Alhaji Kabir yay saurin fadin. “To Alhmdllh, yanzu dai kuje kuyi shawaran nan da kwana uku sai muji yaya ake ciki kamar zaifi”.

      Sam Hajiya Iya bataso jin hakan daga bakin ɗan nata ba, dan sotai take yanke su tafi su barta da Zinneerah, saboda wata irin ƙaunar yarinyarce ta musamman ta shigeta lokaci guda. Amma sai tai shiru dan itama taga cancantar barinsu suje su shawarta ɗin. Amma kuma komai zasuyi tasa a ranta sai Zinneerah ta dawo hannunta da zama dan yarinyar ba karamin shiga mata rai tayiba lokaci guda. shi kansa Alhaji Kabir wani irin kaunar yarinyar yaji a ransa batare da yasan dalilin hakanba.


      Alkairi mai tsoka Alhaji Kabir yayma su Aliyu. kamar yadda aka koyar dasu tarbiyyar godiya haka suka shiga masa godiya da addu'ar fatan alkairi a rayuwa. Sosai hakan yay masa daɗi har cikin rai. Ya kuma kara jin girma da darajar su mmn sadiq sosai. Dan a wannan zamanin bama yaro tarbiyya shine mai matuƙar wahala ga iyaye aynun.


★★★★


       Tunda suka baro gidan babu wanda ya iya yin magana, sai da suna gab da shiga anguwarsune ma Gwaggo Maryama tai ƙarfin halin tambayarsu ina suka baro little kuma?.

      “Gwaggo ai baida lafiya an kwantar dasu a asibiti shida Umma”. Abdull ya bata amsa da damuwa a fuskarsa.

      Saurin juyowa Mmn Sadiq tai ta kalli yaron, kamar zatai magana sai kuma tai shiru ta maida kanta. Fahimtar hakan da Abba yayi ya sakashi faɗin, “Ban faɗa muku bane dan banason raba muku hankali biyu, amma jikin nasama Alhmdllh dan yanzu haka sun koma gida ta kirani cewar an sallamesu ga Naziru yaje zai maidasu gida. Bakomai ke damunsaba kuma sai zazzaɓin haƙora”.

     Addu'ar samun ingattacciyar lafiya sukai masa ita da Gwaggo Maryama. Daga haka suka ƙarasa gidan.


        Sai da sukayi sallar magriba suka huta Maman Halima ta shigo gaishesu ɗauke da Little daya rame sosai saboda yasha jiki. danma ALLAH yayisa mai kwaramniya ga karfin hali da akasan duk yaro da shi.

    Ƙiri-ƙiri sai gashi yana musu ƙyuya. Yaƙi yarda da kowa sai Zinneerah da kunya ta rufe kamar ƙasa ta tsage ta shige. Badan tasoba dole ta amshesa. Aiko ya wani lafe a jikinta yana kallon su Gwaggo Maryama dake jan kafarsa cikin tsokana tana fadin, “Aiko yaro nama fasa auren. Na maka saki goma sha biyu ni da kai baram-baram”.

     Dariya Mman halima tai tana tare masa. Ana cikin haka Maman Sakina ta shigo da yaranta wai zatai musu gaisuwa. duk da bataje can gidanba sai mmn sadiq bata nuna mata komaiba ta amsheta hannu bibbiyu suka gaisa tai musu godiya. 


   ______________,★


      Har washe gari babu wanda ya sake tada maganar komawar Zinneerah gidan hajiya Iya. Dan shi Abba ma ya fice kasuwa abinsa tun safe. 

       Sai bayan sallar la'asar ne Mmn Sadiq da abin keta cin ranta dai ta tunkari ƴar uwarta da maganar. “Maryama nifa inaga kodan matsalar gidan nan zanbar yarinyarnan ta koma wajen Gwaggo, sai dai kuma idan na tuna kar ace dansu masu arziƙi ne mukai haka abin na damuna. Sannan shi kansa Yaya na fahimci baison maganarnan”.

     Murmushi Gwaggo Maryama tayi tana gyara zamanta sosai. “Yaya Hauwa nifa kin ganninan babu abinda ya dameni da cewa ta mutane. Abinda duk ra'ayina ya bani na kuma ji raina ya aminta da shi kuma bai saɓama addinina ko al'adata ba to tabbas yinsa nake dan bama kaina farin ciki. Shi ɗan adam babu wani abu da zakayi a rayuwa ƙyaƙyƙyawa ko mummuna da zai iya gani bakinsa bai tankaba koda kuwa shi a tare dashi akwai abinda yafi naka muni ɗin da ƙyau. Dan haka ajiye batun cewa na mutane muyi abinda ya cancanta. Tun jiya nima cikin nazarin maganar nakeyi da shi Yaya kansa. Shi kawai abinda na fahimta da shi gani yake kamar za'a nuna gazawarsa akan riƙon Zinneerah tunda ba shine ya haifetaba. To amma abinda bai tunaba kuma shine sufa mutanen nan bawai sunsan bama shine ya haifitaba. Sai dai ni har cikin raina na yarda da komawar Zinneerah can gidan kodan wannan fitinanniyar matar tasa dake ganin Yayan ne kawai keda arziƙin da ake zuwa a ci”.

        “Maganganunki duk suna a kan hanya Maryama. Harga ALLAH inason basu ita domin ALLAH da suka roƙa da kuma darajar zumincin da suma sukayi dan shi. sai dai inason tai nesa da su Saude kodan ɓata mata suna da suke a anguwatnan miji zaima Zinneerah wahalar samu. Dan damafa ni ko wannan bata tasoba nayi niyyar ta biki can ku zauna har muga abinda ALLAH zaiyi”.

      “A to tunda hakane a bani abata mu tafi”. Gwaggo Maryama tai saurin faɗa tana dariya. Itama Mmn sadiq dariyar tayi. Haka suka cigaba da tattaunawa har tsawon wani lokaci kafin subar maganar da nufin jiran dawowar Abba yau su tunkaresa da batun.

       Zinneerah da batasan mike faruwaba tana can ɗaki da Little wanda a yanzu yake maƙale mata baya yarda da kowa a gidan sai ita da Gwaggo Halima. Sai su Sadiq idan yaso. Makarantama yau da zata tafi kuka yayta zabgawa sai daga baya ya haƙura bayan yayi barci ya tashi. Wauta da ƙuruciyar dake tattare da ita kuma yasa bata ɗauki hakan komaiba saima tausayin yaron da ƙaunarsa dake ƙara ratsata. Maganar komawa gidan Hajiya Iya kuwa bata damuba ba kuma ta mantaba. Sai dai bata wani ɗaukesa da muhimmanci ba balle taji wani abu a ranta game da hakan.


_________________★


        Koda Abba ya dawo gidan sai da Mmn Sadiq ta bari yaci ya ƙoshi ya nutsu sosai sannan ta tunkaresa da zancen kasancewar yau itace dashi dama. Shiru yay mata tamkar baijitaba. Ita kuma tunanin baiji ɗin bane ya sata sake maimaitawa kai tsaye. Sai dai yanda ya sake tsuke fuska ya saka tasha jinin jikinta kuma.

        Bai kulataba sai da ya mula dan kansa sannan ya fara magana a ƙufule. “Hauwa'u kun shirya hakanne dama saboda abinda ya faru a gidan nan kwanaki shida da suka wuce komi? Shin halin Saude ne baki saniba a gidan nan ne? Da har zaki yanke hukuncin rabani da Zinneerah bayan ni har cikin raina ɗaya na ɗauketa da duk wani yaro dake a gidan nan”.

      “Yaya kayi haƙuri dan ALLAH, sam ba yanda kake tunani baneba. Ni abinda yasama kaji namaka magana saboda mu toshe ɓarakar da dangin mahaifiyarmu ke ganin mahaifinmu ne ya assasata. Su daina ganin tamkar muna gudunsune. Sannan baiwar ALLAHn nan ka duba yanda suka ɗauka Inno, wandama bai saniba zai ɗauka itace ta haifi Hajiya Iyan ai. Wlhy na tabbata da ace banan ta kawo Inno har ALLAH ya ƙaddara rasuwarta ananba da sai munyi kuka bana wasaba akan wannan rasuwar. Yanda zuminci ya taɓarɓare kowa zagayewa zaiyi yabar Buba da gawar Inno, da kuma sun bizneta su kama gabansu su barmu. Amma yanzu kaga yanda suke tururuwar zuwa nan hardama waɗanda bakai zaton ganiban. Amma kayi haƙuri nayi kuskure, dan babu yanda za'ai Zinneerah ta koma can bada yardarkaba”.

      Numfashi Abba ya sauke yana ɗan jinjina kansa. “Maganarki akan hanya take Hauwa'u, ni kaina naji daɗin wannan karamci da suka nuna akan marigayiyar, dan sun nunama sauran dagi su basu manta alkairin Inno ɗinba garesu har yanzun. Badanma ALLAH bai ƙaddaraba kinjifa maganar kaita india da suka fara. Da ace masu kuɗi haka suke daraja zuminci fiye da dukiyarsu dake tsone idonsu lallai da bamu lalace hakaba. Ace dan ALLAH ya baka wani abin jin daɗin duniya kakoma ƙyamar ɗan uwanka baka ƙaunar ya raɓeka. shiko yana gudun raɓar takane saboda karka wulakantashi. Kaiconmu da fifita abinda zai halakamu sama da abinda zai kaimu aljanna”.

       “Amin ya rabbi Yaya. Al'amuran kam sai dai addu'a. Ni kaina halayyar mutanen nan ta zaburar dani wani muhimmin abu insha ALLAH”.

      “Ai haka akeso dama. idan kaga wani ya aikata alkairi kayi ƙoƙarin koyi da shi, ka kuma nisanta kanka ga mai aikata mummuna. Dan masu iya magana kance zama da maɗaukin kanwa shike kawo farin kai”.

         “Sosai kuwa Yaya, ALLAH kai riƙo da hannayenmu”.

    “Amin. To amma nima kuma sai a duba ni dan har cikin raina inason zaman Zinneerah tare damu kodan kansu ya haɗu da sauran ƴan uwanta. Gashi kuma inajin matuƙar kunyar mutanen nan wlhy, yanzu hakamafa ɗazun sai da Alhaji Kabir ɗin ya kirani da kansa akan suna nan dai suna jira”.

       Cike da mamaki Mama tace, “Wai kirafa Yaya?”.

       “Wlhy kuwa, mutanen nanfa mutanen kirkine masu ban mamaki. Toni banda dalilinki ta inama zan ishesu kallo koda a haɗuwar hanyane. Amma ki duba yanda suke da sauƙin kai. Yanzu da wani zaiji nace Alhaji Kabir Shira na kirana a waya ai cazai na zuga ƙarya ko”.. 

     Dariya ta kufcewa Mmn Sadiq, shima Abban ya shiga tayata. “ALLAH kuwa Hauwa'u koni kallon abun nake tamkar mafarki. Ku riƙe bayin ALLAHn da ƙyau bawai dan arziƙin da ALLAH yay musuba, sai don sanin darajar ɗan adam da zuminci da ALLAH ya azurta zukatansu da shi”.

     “Insha ALLAHU Yaya. ALLAH ya bamu ikon gina zuri'armu bisa ƙyaƙyƙyawar tarbiyya muma. Koda sun zama wanu abu a rayuwa sukasance masu sanin mutunci da darajar ɗan adam”.

      “Amin ya rabbi Hauwa'u. To ammafa zan basu Zinneerah ne kawai banda Abdul-Mutallab. Tunda ba wani shayar dashi takeba tabar mana abummu anan. Itama dai su tausaya mana ta dinga ziyararmu akai-akai. dan ɗazun namasa maganar karatunta dan shine babban burina a gareta. Inason rayuwarta ta inganta sosai kodan kaddarar data ziyarci rayuwarta tun tana ƙanƙanuwarta. To shine yake cewa indai karatune sai Zinneerah tace ya isheta da kanta insha ALLAH”.

       “Yaya ALLAH ya saka da alkairi. Dama nima damuwata akan Abdul ɗinne. To amma kana ganin mu sanar dasu gaskiyar al'amari game da haihuwar tata kenan?”.

      “Eh to, bazance miki a'a ba, bakuma zance e ba. amma inaga muɗan bada lokaci taje gidan muga yanayin zaman nata tukunna, duk da har cikin raina bana tunanin wani abu saɓanin ƙyaƙyƙyawa”.

       Cike da gamsuwa Mmn Sadiq ta gyaɗa masa kai.


___________________★


        Washe gari Gwaggo Maryama ta shirya taje yoma Hajiya Iya sallama dan zata wuce itama. Shatara ta arziƙi aka haɗota dashi, tare da driver na ɗaukar Zinneerah, dan Hajiya Iya tace ta gaji da gafarasa bataga ƙaho ba. Da tarema zasu zo da kanta ta ɗauka Zinneerah ɗin sai akai rashin sa'a tai baƙi. Hakan yasa ta haɗo Gwaggo Maryama da driver tace kafin itama tazo, dan tayi alƙawarin dukkan zuri'arta sai sun tako har gidajensu suma insha ALLAH.

       Wannan al'amari ya bama su Mmn Sadiq Mamaki da dariya. Babu shiri tai kiran Abba ta sanar masa. Dole ya baro kasuwa yazo sukai magana. Gashi su kofa Zinneerah basu zaunar akan batunba dan sun yanke da saita samu hutun makarantane.

       Ganin kar Hajiya Iya taga kamar suna mata yawo da hankali suka yanke shawarar barin Zinneerah taje kamar da nufin yin kwana biyu haka. Dan karsu mata gatsau takuma shiga wani hali musamman akan Little.

      Ilai kuwa da suka kirata aka sanar mata zataje wajen Hajiya Iya ta zauna da ita na kwana biyu saboda batajin daɗi sai bata wani damuba. Hasalima taɗanji daɗin tafiyar kodan taje ta huta daga izgili da ƴaƴan mmn sakina da ita kanta maman sakinar kemata a kwanakin nan musamman a makaranta. Shiru kawai takeyi dan karta tada hankalin mahaifiyarta. Amma abin na damunta, dan takai yau har ihu Sakina ta saka akai mata a aji ana kiranta agola ƴar cin arziƙi. Damuwarta ɗaya karatunta da kuma Little dake nane da ita a kwanakin nan duk da ya ƙara samun sauƙi bakamar daba.

     Bayan Mama da Abba sun mata nasiha akan ta kula da kanta da kuma girmama kowa yanda zasuyi alfahari da ita ta ɗauka kaya kala uku kawai abinta tai musu salama cikin dabara ta fito saboda little. Su Sadiq kuwa suna makaranta sai dai su dawo suga wayam bata nan.


      Motane lafiyayya kuma ƙosashshiya. Dan ƙamshin dake a cikintama kansa na musamman ne. (Abinda bata saniba wannan mota ta mai gayyace mai aiki ce. dan Alhaji Kabir motarsa ya bada musamman domin ɗakkota. Haka kawai yarinyar ta shiga ransa yakejinta tamkar ƴaƴansa daya haifa. Ga kuma son daya fahimci mahaifiyarsa na mata itama). Tana a baya driver na gaba yana tuƙinsa a nutse, tai tagumi kawai tana kallon waje da zurfafa a tunanin yanda rayuwarta keta walagigi. Anya kuwa ita tanada farin jini ga mutane? Duk inda zata rayu bata taɓa samun salama hundred percent sai da matsaloli. A Danya matsalarta Inna, Yaya Karima, Tinene. Bayan ƙaddara ta haɗata da mahaifiyarta gakuma su Maman Sakina da ƴaƴanta yanzu suna neman hanata shan ruwa a gidan data samu gata da kulawa. Anya kuwa idan ta dawo daga inda zata yanzu bazata shawarci mamansu akan a maidata boarding school ba ko zata samu nutsuwar yin karatunta cikin salama?.

      Wannan tunanin yasata jin nutsuwa a ranta taketa sakin murmushi batare data saniba har suka iso gaban katafaren milk color ɗin gate ɗin gidan. Sai da driver yay horn maigadi ya wangale gate ɗin ta dawo hayyacinta. Nannauyan numfashi ta sauke zuciyarta na wani irin tsargawa tamkar waccan ranar da Abba ya kawosu. Addu'a ta shiga karantowa a ranta har driver ya buɗe mata ta fito. Godiya tai masa cikin risinawa. Hakan ya sakashi jin daɗi har cikin ransa. Ya miƙa hannu zai amshi jakkar hannunta amma sai ta hanashi. “Haba Yayana, jakkarma kai zan ba ka ɗauka min, ai babu dacewa a cikin hakan, kaine zan ganka da kaya na amsa bakai zaka ganni dasu ka amsa ba”.

     Murmushi ya mata cike da jin ta kuma birgeshi. Shine da kansa yay mata rakkiya har sashen Hajiya Iya. Inda a tafiyar tasu take samun damar yima gidan mai sassa da yawa kallon tsaf. A ranta kuwa raya irin jin daɗi ta masu hannu da manda takeyi. Shiyyasa akace wasu tun a duniya suke cinye rabonsu na lahira. Wasu kuma sai kaga ALLAH ya haɗa musu duniyar da lahirar duka. Ya ALLAH kasa muna cikin masu samun dukan gaba ɗaya.............✍  

   

No comments

Powered by Blogger.