Makauniyar Kaddara 13

 


Page 13*


............A zahiri dai Zinneerah ce ta haifi Abdul-Mutallaf. Amma dukkanin abinda ya shafi yaron ƙiri da muzu ta sakarma Maman Sadiq. Musamman daya kasance ba abincinsa yake sha ba yanzu sai madara. Idan ka gansa a hannunta ko tana masa wata hidima to Mama Sadiq na wajen Abba ne ko tana aiki, yaran kuma basa gida.

      Wanda bai saniba ma idan yazo gidan saiya ɗauka Maman Sadiq ɗince ta haifi yaron. Tsabar ƙwarewa a shahara wani lokacin idan tace Zinneerah tai masa wani abu tata kumbura baki kenan. Ita maman Sadiq ma abin har dariya yake bata. 

        Itako Zinneerah ba komai ke ɗawainiya da itaba sai tsabar shirme da ƙuruciya, sannan har cikin ranta ta rigada ta saka cewar yaron ɗan aljanune suka ajiye mata. Bawai bata sonsa bane, sosai take son abinta kasancewarta mai son yara dama can, dan a hankanma wani lokacin haka zata zauna taita satar kallonsa, idan kuma Mama ta fita a ɗakin takan ɗaukesa kota zauna tana kallonsa tana murmushi da shafar kansa, kai har kiss idan ALLAH ya cidashi yimasa akeyi ko rawa.


      A yau kusan shine ma ya tadasu da asubahi da kukansa, dan a daren jiya tsautsayi ya saka Maman Sadiq tsare Zinneerah ta shayar dashi akan ko za'a dace yanzun tunda tana shan maganin. Sai gashi a cikin rashin dacewar cikin yaron ya kumbura kamar yanda ya ringayi a asibiti. Abba daya dawo daga masallaci ya shigo yana faɗin, “Yaya dai wai nikam?. Mi akaima abokina ne yau a gidan nan?”.

      Maman Sadiq dake bashi maganin da aka dinga bashi sanda suna asibiti idan hakan ta faru ta ɗago tana dubansa. “Wlhy Yaya tsautsayi yasa na sakata ta shayar da shi jiya da daddare dan tausayi yake bani, ace jinjiri kamar wannan babu abincinsa sai madarar banzar nan. Tofa shine kaga cikin dai ya kumbura kamar yanda yakeyi”.

      Amsarsa yayi a hannunta bayan ta goge masa maganin daya ɗan ɗisa masa a wuya. Ya sakashi a kafaɗa yana hura masa kunne da shafar bayansa. sassauta kukan ya farayi kaɗan-kaɗan, kafin ya koma ajiyar zuciya. Kusan mintuna biyar suna a haka yaron ya saki gyatsa mai ƙarfi. Su dukansu sai da suka sauke numfashi. Su Sadiq dake zaune duk cikin damuwa Abdul yace, “Abba Little yaji sauƙi (dan haka suke kiransa saboda Abdul ɗin).

       Fuskar Abba da murmushi yace, “Insha ALLAH yaji sauƙi gashi yayi gyatsa. Da alama kuma barci ma zaiyi, sai a goyashi”. Ya ƙare maganar da kallon Maman Sadiq.

       Miƙewa tai tana faɗin, “Tazo ta goyashi ɗakinka zanje na gyara, dan sakarci duk wannan ihun da yaron nan keyi tana ciki tana jinmu amma ko leƙe, tun a ɗakinma luf tayi ita a dole barci take bata jimuba”.

     Dariya kawai Abba yayi batare da yace komaiba. Maman Sadiq kuma ta shiga kwalama Zinneerah da duk tana jiyosu daga ɗakin kira. Fitowa tai sum-sum-sum kamar wata munafuka. Abba yace, “Koma ki ɗakko zani kizo ki goyashi akwai sanyin safiya”.

       Cike da kunya ta juya ta koma. babu jimawa ta dawo da zanin goyon a hannu. Maman Sadiq ce ta amshesa ta saka mata a baya dan har yanzu ba wani iya goyon tayi da ƙyauba. Kusanma wannan shine karo na uku kacal da zata goyashi. Dan mafi yawancin lokuta su ƴan biyune ke goyashi ko Maman Halima ko ita Maman Sadiq ɗin. Har Sadiq da Abdull goyamusu akeyi, ƴaƴan maman sakina ma sukan faki ido suzo su ɗaukesa saboda kusan shine ɗan ƙaramin yaro yanzu a gidan, sai yazan abin sha'awa ga kowa banda maman sakina da ko sau ɗaya bata taɓa ɗaukarsaba ma ita.

     Da ƙyar Maman Sadiq ta samu goyon yayi dai-dai tanata ma Zinneerah ɗin faɗa. Ita dai batace komaiba sai dariya takema a ranta wai mama ta dage da masifa akan ɗan aljanu, sai randa sukazo suka ɗauke abinsu taga yanda kowa zaiyi a gidan ai.

          Bayan fitar Abba da Maman Sadiq Zinneerah ta hau gyaran ɓangaren nasu kamar yanda ta saba, Sadiq kuma suka shige suna shirin makaranta dan an koma hutu.


★★★★


       Haka rainon Little Abdull ya cigaba da gudana kusan kaso biyu a hannun Maman Sadiq da maman Halima ne. Kaso ɗaya kuwa Zinneerah na rabawa dasu Sadiq. A haka sukai arba'in yaron yay ɓulɓul masha ALLAH, ga ƙyawunsa na sake fitowa. Yaro gaba ɗaya bai ɗakko kamannin Zinneerah ba ta fuska sai halittar yatsunsa na ƙafa da hannu da abinda ba'a rasaba. Amma daga basuba kamanninsa daban da nata. Takan zauna ta dinga kallonsa da shiga dogon nazarin ko zata iya gano da wanda yake kamar. Amma sam bata iya hasaso komai ga kamannin nasa.

        Sosai jikinta ya warke, idanma baka saniba bazaka taɓa ɗauka cs akai mataba. Musamman da yazam bayan dawowarsu gida maman Sadiq da Maman Halima kulawa da gyara na musamman suke mata wanda ita bawani gane inda suka dosa take ba. Abinda kawai ta sani tanajin daɗin jikinta sosai balle yanzu barci take sosai tamkar kasa. Ga lafiyayyen abinci da take samu kuma ga kwanciyar hankali. Sam bata wani tunawa da Inna. Garama Babanta da Yaya Sa'a da Yaya Gajeje. Takanyi kuka a duk sanda sukazo mata ranta koda a boyene. Sai ko Khalipha da har yanzu yake maƙale a zuciyarta. Gashi yanzu Naziru ko gidan yazo baya mata maganarsa ma. Itako kunya ta hanata sake tambayarsa ko yanzu yana samunsa.  


     Bayan tayi arba'in da kusan wata ɗaya Maman Sadiq taga zaman nata baida wani amfani. sai dai taci ta ɗanyi aikin gida ta kwanta barci. Samun Abba tai da shawara akan Zinneerah ɗin ta shiga wata islamiyya dake anan kusa da su ta ƴanmata, inda su Sakina ke zuwa da yamma. To sunayi da safe kuma zuwa ƙarfe ɗaya ga yaran da basa zuwa boko.

      “Eh shawaranki mai ƙyau ce Hauwa'u, nima kuma maganar fara karatunta dama yana raina. Na bartane kawai Abdul-Mutallaf ɗin ya ƙara ƙwari sannan. To amma tunda dai naga bama itace ke rainonsa ba gara ta fara islamiyyar kawai itama bokon sai a nema mata inda zai dace da ita dan nasan da wuya ace acan tayi karatunma”.

       Cikin gamsuwa da bayaninsa Maman Sadiq tace, “ALLAH ya saka da alkairi yaya, sai dai duk da bamu taɓa maganar karatu da itaba sai naga kamar taɗanyi acan, dan naga wasu lokutan idan su Abdull na Assignment haka takan saka musu baki harma tayi gyara a wani wajen”.

     “A'a ikon ALLAH, to kinga kiramin ita dai muji ta bakinta, kinga ai sai mu sami madafar kamawa ko”.

     Miƙewa tai tana amasa masa da to. Babu jimawa kuwa sai gasu sun dawo tare da Zinneerah. Bayan ta gaida Abba sai yake tambayarta ajinta nawa a makaranta?.

       Duk da a bazata tambayar tazo mata sai gashi ta saki murmushin da ya basu mamaki. Kanta tsaye cike da zumuɗi tace, “Abba nayi jsce ma ai”.

      “Ikon ALLAH, to to Alhmdllh. Ashe ɗiyar tawama ƴar boko ce bamu da labari. Amma gaskiya naji daɗin hakan sosai, kuma na yaba ƙoƙarin babanki anan....”

     Cikin suɓutar baki tace, “Lah Abba ai bama shine ya sakaniba. Inagama Baba fa baisan ina zuwa makarantaba, dan shifa babu ruwansa dani a gidan. Ni saima nayi kwana hudu biyar ban gansaba wani lokacin”.

      Duk idanu suka zuba mata, a ransu kuma cike suke da zumudi da jin daɗin yanda ta fara sakin jiki da faɗa musu abinda ke ranta.

     Maman Sadiq ce tace, “To wani guri yake zuwa da har kike kwanaki baki gansaba?”.

      “A'a mama, yana nan a gidan, kawai dai bansan miyasaba shi bayason ganina ne wani lokacin, wani lokacin kuma daga sallar asuba idan ya fita bai dawowa sai munyi barci”.

        Babu wanda ya iya magana tsakanin Maman Sadiq da Alhaji. Maman Sadiq dai rayawa take a ranta yaushe al'amarin baban ya taɓarɓare haka kuma?. Dan tasanshi a da mutumne tsayayye akan iyalansa da gidansa. Dan ko talla wannan bai yarda yaronsa ya fita ba. Duk inda akai sallar isha'i kuwa yana gidansa, bazai sake fitaba sai asuba. Da an idar da salla zai dawo gida ya karya sai rana ta haska zai fita kasuwa wajen sana'ar sai da dankalinsa ɗanye da makani.......

         Tambayar da Alhaji ya jefama zinneerah ce ta katse tunanin Maman Sadiq ɗin ta maida hankalinta garesu.

       “Karki damu yarinyata, haka rayuwa take kullum cikin tsere-tsere da jarabawa. To amma wanene ya kaiki makarantar?”.

       Kunyar wanda zata ambata ɗin ya sakata jan lokaci kafin ta bashi amsa. “Abba Babawo ne ya kaini kafin ya koma yace Yaya Karima yake so”.

       Duk da a dunƙule tai maganar kasancewarsu manya masu hangen nesa sai duk suka gano inda ta dosa kai tsaye. 

     “ALLAH ya saka masa da alkairi”.

Abba ya faɗa dajin daɗi. Amin sukace ita da maman Sadiq. Daga haka Abba ya sallameta suka cigaba da tattaunawa shi da matarsa.


       “Hauwa'u kinga fa'idar shiru da mukai mata akan son sanin bayanta ko? Ina mai tabbatar miki inhar zamu cigaba da binta a haka harma abinda bamuyi zatoba sai munji daga gareta wataran. Kinsan shi yaro tamkar dabba yake, mai kula dashi da mai sake masa shi yake sakewa da shi shima. Dan haka ki sake nutsuwa wajen fahimtarta a hankaki komai da muke buƙata zai fito. Domin a fahimtar danai mata rashin samun sake a inda ta baro ya sakata kasancewa shiru-shiru kamar mara wayo. Amma ras take kuma tanada kwaramniya, sai a hankali zakiga ta hau bisa hanya da ƙyau”.

     Murmushi maman Sadiq tayi har haƙoranta na bayyana. “Maganarka haka yake Yaya. Dan yanda ma zakaji tana faman shagali dasu Sadiq idan na barsu su kaɗai ya isa tabbatarwa. Idan kaji bakinta cauy-cauy baka taɓa cewa itace ke zuba zance”.

     Dariya shima Abban ya sakeyi. “Ahaf kaɗanma kenan. Bayan takurar data taso a can harda cikin yaron nan ya sake dankwafe dukkannin kuzarinta da karsashi. Amma zata ware tsaf ta bama kowa mamaki. Naga alamar kuma tanason karatu ma sosai, dan jin daɗinsa ya sakata bamu labarin abinda bamu tambayetaba ma”.

      Haka suka cigaba da hirarsu cike da fahimta dajin daɗi. Yayinda Zinneerah kecan tana tsallen murna zata koma makaranta. Harda ɗaukar Little dake barcinsa ta hau masa rawa. Aiko ya farka ya birkuce mata kuma. Da ƙyar ta lallashesa tana dungure kansa da goyasa wai karya tona mata asiri Mama tazo tai mata faɗa ta tada ɗan aljanu kuma.


       Kwana uku dayin maganarnan aka saka Zinneerah islamiyyar safe zuwa 2 sun taso. Kusan dai-dai da yaran gidan kenan amma ƴammatan kawai dake shirin gama secondary. Su Sadiq kam sai shidda suke tasowa makarantarsu haɗe take da islamiyya.

      Faɗa muku irin kalar farinciki da Zinneerah tayi ɓata lokacine. Sai da akaje makarantar kuma ta raina kanta dan batasan komaiba. Amma tayi alwashin nutsuwa sosai ta fahimci komai ɗin kodan ta ribantu a duniya da lahirarta

        

                


_________________★


       A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI. Yau ga Abdul-Mutallaf (Little) da wattani bakwai a duniya. Yaro ƙyawunsa nata ƙara fitowa fili da lafiya ingantacciya. Bazaka taɓa cewa ba abincinsa yake samu daga mahaifiyarsa ba. Dan ma zazzaɓin haƙora kan girgiza kuzarin nasa wasu lokutan. 

        Amma da yake zuwa yanzun cin abubuwa yake sosai, dan su Aliyu komai suka yayo kimsa masa suke shiko ya cinye abunsa sai hakan ya ƙara taimaka masa aynun. Rarrafe yake ko ina ga ɓarna, inda yana waje kowa kaye-kayen kayansa yake inba hakaba yazo ya tarar an canja musu sabon tsari.

      Babu ruwansa da Zinneerah, hasalima ƙyuya yake mata wani lokacin. ba komai ya jawo hakanba sai itama rashin kulashin da takeyi sosai. Dan komansa Maman Sadiq ce sai kace itace uwarsa. Shi da su Sadiq kuwa ai da kuka ake rabuwa idan zasu makaranta. Dasun dawo kuwa zakaga walwalarsa ta daɗu.

       Zinneerah nata karatun islamiyyarta wanda a yanzu tayi matuƙar yin nisa dai-dai gwargwado, dan ko a Alkur'ani ta kusa kai izifi biyu, ta saka himma sosai. Hakama sauran littatafai bata wasa. Bokon dai ce ba'a kai ga sakataba har yanzu saboda wasu ƴan dalilai da suka riƙe Abba. Amma yanata shirin hakan batarema da sanintaba.


         ★★★★★★


   Little nada shekara ɗaya cif a duniya da ƴan kwanaki ALLAH ya bashi ikon fara takawa. Ranar zokaga murna wajen su Aliyu. Zinneerah na zaune a falon ita da Mama suka dinga ihunsu na murna mama na tayasu da dariya. Zinneerah dai ta murmusa ta kauda kanta ga abinda takeyi, sai dai a kallo ɗaya zakai mata ka fahimci kawaicine kawai takema mahaifiyarta, amma har cikin ranta tanason ɗanta da jin daɗin duk cigaban da zaizo masa a rayuwa. Duk da kuwa har yanzu tunaninta na nan akan aljanu suka saka matashi a ciki ta haifa musu. Wataran kuma zasuzo su sace abinsu.

    Maman Halima dake tsakar gida tana girki ta leƙo tana tambayar lafiya su Sadiq ke ihu haka?. Cike da murna Abdull yace, “Mama little ya fara tafiya”.

     Dariyar itama tayi, tare da shigowa ɗakin sosai ta ɗauka Little tana juyi dashi. Dariya su Sadiq suka sake sakawa. Amma banda Little da kowa ya fahimci miskilancin yaron tunda ya fara wayo. Sam baida yawan fara'a, akan daɗe ba'aga yana dariya ba. Garama idan su Aliyu ke masa wasa zakaji har ƙyalƙyalewa yanayi abunsa. Zinneerah ma catai ita daya rainama ko dariyar yake idan ya ganta dainawa yakeyi.

   Duk sanda ta faɗi haka mama kan girgiza kai kawai da faɗin, “ALLAH ya kaimu randa zakiyi hankali dai, harshi Abdul-Mutallaf ɗin miya sani da sai ya zaɓa wanda zaima dariyar? Kawai dai zuciya nason mai ƙyautata mata, keko ko wasa bayimasa kikeba”.

      Idan mama ta faɗi hakan Zinneerah bata ƙara cewa komai kuma, dan dai kam da gaskiyar mama. Idan kaga tama yaron wasa sai inba idon Mama a wajen. To kafin hakan ta faru kuwa akan jima musamman daya kasance yanzu itama ta fara makarantar boko a sukul ɗin su Sakina.

    Duk da Sakina nashan zubar mata da mutunci ga abokan karatunsu na cewar ai bazawarace ta taɓa aure harda ɗa. Da farko ƴan ajinsu kan ƙaryata ta sukeyi, dan a ganinsu nawa Zinneerah ɗin take da za'ace ta haihu, a yanzunefa suke shekaru sha biyar suna farkon shiga sha shida. Tsabar son ƙara wulaƙanta Zinneerah saita ƙirƙiri dinga gayyatarsu gidansu dan aga little. Wasu ko sunje sun gansa basa yarda, amma yau da gobe sai suka fara amincewa da Sakina ɗin har suna tsokanar Zinneerah.

     A farko takansha kuka. Amma zuwa yanzu da take neman watanni kusan biyar a makarantar sai hakan ya bar ɓata mata rai. Tama sake ɗammarar maida hankali akan karatunta kamar yanda a kullum Mama ke jaddada mata ta dage wannan karatun sai ya zame mata ado mai ƙawata tarihinta watarana.

     Ba fahimtar Mama takeba kai tsaye akan furucin, dan ita a shirmenta har yanzu Mama batasan yaya aka samu Little ba. Bayan sun gama darerakunsu akan fara tafiyar little ɗin Mama ta fice. Su kuma suka cigaba da hidimarsu a ɗakin kasancewar lahadice yau islamiyya kawai yaran zasuje da yamma.

     Ganin Little ya ɓingire ƙasa alamar barci zaiyi yasa Zinneerah ajiye buk ɗin hannunta da take Assignment ta ɗaukesa ta goyashi, dan Mama ma ta shige ciki kanta na ciwo. Fita tai tsakar gida dan ta taya Maman Halima aiki kasancewar yau ranar girkintace.

        Maman Sakina kawai ta samu zaune dasu Luba dake wanki a bakin rijiya. Ba wani shiga sabgarta suke a gidanba shiyyasa itama bata matsawa kanta na shiga tasu. Dan wasa-wasa Zinneerah ma akwai miskilanci da tsiwa idan taso. Sai dai yanayin rayuwar data tashi a cikine ya sakata komawa sanyi-sanyi.

     Yanzu ɗinma Maman kawai ta gaida taja kujera ta zauna a bakin rijiyar itama inda aka tara wanke-wanke. Cikin neman tsokana Luba ta dubeta taɗan taɓe baki, sai kuma a bazata ta bushe da dariya. Kallonta Aliya tayi, hakama Mamansu. “Luba lafiyarki kuwa da wannan dariya kamar wata mara hankali?”.

     Cikin dariyar tace, “Mama bazaki ganeba. Wlhy wannan agolance take bani dariya. Idan ta fita waje samarin anguwarnan suyita wani rawan kai a kanta su sun sami budurwa, shashashun basusan harda surƙumemen ɗa gareta a gidaba. Jiyafa Faisal ɗin gidan Alhaji Zubair bakiga yanda ya nacemin da tambaya akan wacece ita ba? Niko na ce masa bazawarar agolan gidanmuce”.

       Dariya suka bushe dashi su duka har Maman. Maman Halima dake kicin ta fito a fusace tana kallon Luba mai zancen. “Haba Luba wane shirmene haka da girmanki. Zinneerah ba ƙanwarki bace amma kike wannan sakarcin?”.

     Da kunƙunin rashin tarbiyya Luban tace, “A'a Umma nikam ba ƙanwata bace, dan bamu haɗa komaiba banda agolanci datazo gidanmu cin arziƙi”.

       “To sannu mara kunya, yanda kikejin nan gidankune itama haka gidansu ne. Dakike aibantata wajen mutane cewar bazawara kuma agola kina tunanin hakan zai hana wanda ALLAH yasa ya zama mijinta zuwa har gidan nan neman aurenta. Kubar wannan banzan halin dan baida ƙyau, ku matane gidan wani zakuje wataran kuma.......”

     A fusace Maman Sakina ta tare zancen. “A'a Maman Halima kinga, miye na wannan dogon alkaba'in bayan gaskiya yarinyar ta faɗa. Daga ni har ke kowa yasan ai ita agolarce a gidan. Kuma bazawara. Luban ai taimakonta takeyi wajan faɗar gaskiya dan kar bayin ALLAH suzo a rufesu a basu budurwa bayan gata harda ƙurmusheshen ɗa a baya”.

       Maman halima zata sake magana Maman Sadiq da hayaniyarsu ta sakata fitowa dole tai saurin faɗin, “Yaya dan ALLAH abar maganar dan bata da amfani. K kuma Luba ki kwantar da hankalinki ko baki faɗa musu ba dama idan sunzo ɗin zasu sani ai. Cin arziƙi kuma da tazoyi gidanku naɗan lokacine insha ALLAH ”. Daga haka ta juya ta koma ɗaki idanunta na cika da ƙwallar tausayin ɗiyar tata da babu ranar da zata fito ta koma ga ALLAH Saude da ɗiyanta basu yadda habaici akanta ba a gidan. Sai dai suna musu shirune daga ita har Zinneerah ɗin saboda tana ƙwaɓarta akan karta kulasu komai mai wucewane. Sai dai na yau ya mata zafi har tanajin kamar tasa Zinneerah tabar gidan ko itama ta huta da wannan gorin.

       Maganar Maman Sadiq sai gashi tabar baya da hazo. dan dama irin wannan damar Maman Sakina ke jira ta dirje Maman Sadiq ɗin akan haushin zaman Zinneerah da ɗanta a gidan. Aiko ta zauna ta fara zuba tijara har su Luba na iƙirarin dukan Zinneerah wai. 

     Shiru Zinneerah dai bata kulaba, tamkarma batasan anaiba tanata wanke-wankenta. Sai da cikin suɓutar baki Aliya ta zagi Maman Sadiq ne Zinneerah ta miƙe batare da kowa ya luraba. Sai saukar sautin mari kawai sukaji akan fuskar Aliya a bazata..........✍


No comments

Powered by Blogger.