Makauniyar Kaddara 11


*Page 11*


............Alhaji dake dubansu yace, “Lafiya kuwa naga tana kuka?”.

       “Humm lafiya ƙalau wlhy, daga tambaya fa shine sai kukan nan. Gani nai ya kamata musan matsalar data barota daga gida. Idan ya dace mu nema mijinta saimu nemesa kuma”.

       Murmushi Alhaji yayi yana zama a kujera, cike da nazarin Zinneerah yace, “Uhm inaga bata wannan hanyar ya kama mu saniba Hauwa'u, ki barta kawai ta huta dan yanzun farin ciki da kulawarmu tafi buƙata. Sauran maganar idan na dawo zamuyi ni da ke”. Bai jira amsar Maman Sadiq ba ya maida dubansa ga Zinneerah dake kuka har yanzu. 

     “Ɗiyata kinga share hawayenki kinji, banason na sake ganin kinyi kuka a gidan nan dan ALLAH. Ki fahimci mamanki kuma, batai miki wannan tambayar bane danta ƙuntataki. Wannan shine halin girma daya kamata kowacce uwa ta nuna ga matsala irin wanna. Ina fatan kin fahimceta”.

     Kai Zinneerah ta ɗaga masa alamar eh.

      Yace, “Alhmdllh, to share hawayenki kinji, ki kuma saki ranki a gidan nan dan baki da maraba da sauran yaran gidan, ALLAH yay miki albarka ya saukeku lafiya. Mikikeso na sayo miki idan zan dawo?”.

     Ƙasa Zinneerah ta karayi da kanta cike da girmamawa da ƙaunar wannan bawan ALLAH.

     Shima sai ya miƙe yana murmushi, “Shikenan tunda kin kasa faɗa, kafin dai na taso ki faɗama mamanki saita kirani a saya miki komi kikeso ɗin”.

      “Nagode Abba, ALLAH ya tsare ya bada sa'a”.

     Murmushi ya sakeyi cike dajin son yarinyar a ransa. Ya amsa idonsa akan matarsa.


___________________★


         Tun daga wannan ranar babu wanda ya sakema Zinneerah magana akan sanin uban cikin jikinta da dalilin barowarta gida. saima kulawa ta musamman da Maman Sadiq, Abba, Maman Halima suka sake ninka mata. Koyaya aka ganta a damuwa sai anbi ba'asinta domin son kauda mata. Duk da Maman Sadiq na kawaici a kanta cikin hikima take jan abarta a jiki idan sun shige ɗaki, hakan yasa shaƙuwa mai ƙarfu ke sake shiga tsakaninsu, tana sake sakin jikinta sosai kuma. hakama ƙannenta idan ka gansu saika ɗauka dama can tare suka tashi. 

      A wajen ƴaƴan Maman Sakina (Saude) ne kawai Zinneerah batajin daɗi da ita kanta Sauden. Dan ko ranar girkinta bacin Maman Sadiq nakai zuciya nesa da sun dinga tafka rigima akan abincin da ake zubama Zinneerah ɗin. Amma sai bata cewa komai ta barta da halinta. Tadai gargaɗi Zinneerah ɗin akan koda wasa karta shiga hurimin Maman Sakina da ƴaƴanta inhar ya wuce gaisuwa da girmamawa. Sannan duk wanda zai sakata aiki a gidan tai masa indai ya girmeta.

     Dayake Zinneerah ɗinma bamai kwaramniya bace sai tabi huɗubar mahaifiyarta aka zauna lafiya. Dan duk da cikin dake tare da ita da gadara Maman Sakina ke sakata aiki a gidan, itako babu musu takeyi koda batajin daɗin jikinta. Saima idan Maman Halima taga abin yayi yawane takanyi magana kota hana Zinneerah ɗin. Haka yakan saka Maman Sakina taita masifa a gidan da gori tana kiran Zinneerah da suna agola kinfi masu gida.

          Maman Sadiq bata taɓa tankawaba, bakuma ta taɓa gayama mai gidanba. Ta kuma roƙi Maman Halima akan karta faɗa itama, dan tasan duk dai iya zaman Zinneerah a gidan naɗan lokacine kafin ta koma gidan mijinta.


     Haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa Zinneerah na rainon cikinta dake bata wahala. dan bata taɓa ƙulla kwana biyu babu ciwo. Sai dai yanda cikin ya fito ɗas a jikinta ba ƙaramin ƙyau yasa tayi ba. Gashi tana samun kulawa sosai yanzun.

       Dan hatta da zuwanta asibiti Naziru ke zuwa ya kaita kamar yanda Khalipha ya bar masa sallaho. A ranar farko da suka fara komawa asibitin domin ganin likita Zinneerah ta samu damar ƙare masa kallon tsaf bayan ta karanta sunan asibitin tun daga waje. *_SHIRA HOSPITAL_*.

       Sosai take jinjina ƙoƙarin maginin wannan asibiti, dan yayi ƙyau sosai kuma an zuba masa kayan aiki bana ƙaramin kuɗiba. Ga likitoci ƙwararru da basa wasa da aikinsu kuma babu wulaƙanci. Sai dai abinda ke matuƙar bata mamaki yanda asibitin yay matuƙar haɗuwa zaka ɗauka sai wane da wane ne masu iya shigarsa neman lafiya, amma saika shigo ciki kai gamo da masu karamin ƙarfi bila-adadin suna amsar magani hankalinsu kwance. 

     Samun damar ganin likita akan lokacine ya katse mata dukkanin tunaninta. Sai dai yanda aka karɓesunne ya sake bata mamaki, amma jin zancen Khalipha a bakin likitan kuma sai ta fahimci a dalilin shine ake mata wannan tattalin da kulawar. An bata magungunan da suka dace da ita, tare da sake gargaɗinta akan daina duk wani aiki dan cikin jikin nata yana buƙatar hakan saboda ƴar matsalar da suka hanga tattare da shi.

    Ƙuruciya tasa batako damuba suka dawo gida. Sai dai bayanin da Naziru yayi na maganar kula da hutun nata a gaban Yayansa da bai kai ga fitaba yasa Abba gargaɗin kowa na gidan akan yasa ido kar Zinneerah ta sake wani aiki. Baki maman Sakina ta taɓe cikin ƙunƙuni take fadin, ‘Wayaga agola kinfi ƴaƴan gida’.

        Babu wanda ya tanka sai shi Alhajin ne ya dubeta rai ɓace, “Saude mikike faɗa?”.

       A zabure ta mike tana yarfar da hannaye da tafasu, “A'a kaga Alhaji bance komaiba nikam, karkuma a bugamin gangar ɗan bazakuɗa babu gaira babu sabar”.

     Daga haka tabar wajen fuuu. Ƙwafa yay kawai batare da yace komaiba.


       Tun daga wannan zuwan sai yazam Naziru kanzo ya kaita asibitin ganin likita kamar yanda akan rubuta musu. 

       A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai ga cikin Zinneerah ya shiga watanni na takwas. Zuwa yanzu ta saki jikinta sosai a gidan, musamman ma da mahifiyarta da kannenta dake faɗaɗa farin cikinta a koda yaushe. Idan ka ganta bazaka taɓa dauka ita bace, bakinta ya buɗe sosai alamar dama can rashin samun ƴancin kai ke sakata zama mai sanyi. Ita kanta maman Sadiq har mamaki take a ranta dama Zinneerah nada surutu haka? Ta tabbatar nan gaba idan ta sake warwarewa sai tafima haka kauɗi. Danma lalurar cikin kanɗan taƙaita mata wasu abubuwan.

         Duk da waɗanan sauye-sauye da Zinneerah ta samu a rayuwarta hakan baisa ta manta da Khalipha a rantaba. Koda yaushe yana nan maƙale a ranta, wani lokacin har mafarkinsa takeyi, kota zauna zugum tana tunanin yaushene zai sake dawowa gareta ne ko dan ta masa godiya akan ɗawainiyar da yayi da ita?. Idan kuma Naziru yazo gidan har ALLAH ALLAH take taji yace Khalipha na gaisheta, dan yana kiransa lokaci-lokaci idan ya samu dama. Sai dai bai taɓa cewa a haɗasuba dan shi duk zatonsa tanada aure ne.


       Yauma kamar kullum suna baje a falon Mamansu suna cin gyaɗa dafaffe da Zinneerah ta ƙwallafa rai sai da aka sayo aka dafa mata, kallo suke suna kwasar dariya. Maman Sadiq dake ciki tana shirin tafiya sashe Alhaji ta fito falon da kwalliyarta. Kallon yanda suke cikin nishaɗi tayi daɗi da farin ciki na ratsa ranta itama. Ta ɗauki tiren data shirya abincin Alhajin tana faɗin, “Zinneerah tashi ki tura muku ƙofar ni zanje na kaima Abbanku abinci, idan kunji barci kafin na dawo kimasu Aliyu addu'a karsu kwanta babu addu'a. Wannan sarkin fitsarin Abdull ki tabbatar ledan katifan bata zameba a inda zai kwanta. Ga kuma magungunanki nan kisha kema kafin ki kwanta”.

       “To mama sai kin dawo”.

Ta faɗa fuskarta washe da murmushi. Suma sauran yaran duk adawo lafiyar sukai mata ta ɗauki tiren ta fice. Yayinda Zinneerah ta saka Sadiq zuwa ya tura ƙofar suka cigaba da kallonsu.


     A can ɓangaren maman Sadiq ko bayan Alhaji yaci abincinsa ya ƙoshi take dubansa da damuwa. “Yaya dan ALLAH karkace na takura, baka ganin kuwa ya dace mijin yarinyarnan yasan wani abu game da ita”.

      Murmushi Alhaji yayi na manya. Ya gyara zamansa da cewa, “Eh kina kan gaskiyarki Hauwa'u, nima bawai hakan baya raina bane. Dama inason dai ta gama sakin jikintane sosai ta manta da duk wani ɓacin ran da yabarota daga gidan sannan. A yanda kuma nake tunani bata wajenta ya kamata muji komaiba. Nine zan shirya da kaina naje Danya ɗin domin ganawa da Baban nata da Mijinta. Kinga idan mun samu bakin zaren saimu yanke hukuncin daya dace. Dan indai ba rabuwa tai da mijin nataba tofa sai dai yasan mai yuwuwa”.

        Murmushi kawai taɗanyi, “To duk hukuncin daka yanke ai shine dai-dai Yaya. ALLAH yay mana jagora”.

     “Amin” ya faɗa yana maijin daɗi a ransa na yanda duk ta sakar masa ragamar rayuwarta batare da jin ko ɗarba garesa.


       ★★★


Bayan sati ɗaya dayin wannan magana Alhaji ya shirya zuwa Kusada ƙauyen Danya batare da sanin Zinneerah ba.

        Kasancewar a ranar yaje ya dawo kuma bata san komai akaiba tunda tasan yana fita kasuwa dama. Abinda dai kawai ta fahimta ranar Mamansu ta kwana cikin wani irin yanayi na tsantsar baƙin ciki. Dan harta kai washe gari ma sai da aka kwantar da ita asibiti. Kwananta ɗaya aka sallamota ta dawo gida. Zinneerah ta shiga damuwa da ganin yanayin na mamansu daya kaita ga kwanciya asibitin. Amma sai rashin wayo ya hanata tambaya koda suka dawo. Kallo ɗaya zakai mata itama dai ka fahimci tana cikin damuwar.

      Kusan kwanaki goma tana ganin Maman tasu a wannan bahagon yanayin, kafin kuma taga ta warware ta cigaba da harkokinta a gidan cike da ƙarfin hali.

        Abinda Zinneerah bata saniba shine mummunan labarin da Alhaji yaje ya samo a garinsune yakai ga mahaifiyarta kwantawa asibiti saboda motsawar hawan jininta. Sai dai kamar yanda Alhaji ya gargaɗeta yin gum da bakinta kar Zinneerah da abokan zamanta susan wani abu game da cikin Zinneerah ɗin yasata shanye komai a rai ta fawwalama UBANGIJI ikonsa da amsar ƙaddara. Musamman daya kasance duk wanda Alhaji ya jiyo labarin cikin Zinneerah a bakinsa saida ya yabi kyawawan halayyarta da wahalar data dinga sha ga matar ubanta. Harma takai wasu na ganin Inna ce silar komai akan cikin na Zinneerahn.

           Hakan yaɗan sake girmama danganarta ta shanye komai ko a fuska basu taɓa nuna Zinneerah sunsan komaiba daga ita har Alhaji. matan gidan kuma sun sanar musu cewar ashe mijin Zinneerah ɗinne ya mutu kawai, ruɗanin rasuwarne ya sata baro gida cikin gushewar hankali. Maman halima ta tausaya mata, Maman Sakina kuwa ko'a jikinta. saima ƙorafi data dingayi akan kenan an ƙara ma mijin nasu nauyi tunda dai nan Zinneerah zata cigaba da zama ita da abinda zata haifa.

     Babu wanda yabi takanta dan idan da sabo kowa ya rigada ya saba da halinta a gidan ai.


         Zinneerah ta cigaba da rainon cikinta aɗan tsakanin nan cikin rashin jin daɗin jiki, dan tunda ya shiga wata na tara komai ya sake mata wahala. Harma takai randa suka koma asibiti dole Doctor ɗin ya riƙeta akan zata cigaba da zama anan har saita haihu.

     Hakan baima Zinneerah daɗiba. Amma yaya zatiyi tunda ance wannan ne samun sauƙi a gareta. Yanzunma dai Maman Halima ce tare da ita, sai Mamanta dakanzo duk bayan kwana biyu ta amsheta ita kuma taje gida ta huta. Abba kam babu fashi kullum sai yazo safe da dare dubata. Ko'a fuska bai taɓa nuna ƙyamar cikin jikintaba balle bakinsa ya suɓuta wajen faɗama matansa dalilin samuwarsa.

       A randa ta cika kwana tara a sibitinne da Naziru yazo dubata yake faɗa mata kwana biyu bayajin Khalipha kwata-kwata. Yayi ƙuru ya gwada kiransa ranar kuma bata shigaba. ya tura masa saƙo babu reply har yanzun.

       Murmushi kawai Zinneerah tai na ƙarfin hali batare da tace komaiba. Hakan yasa shima bai sake cewa komaiba akan batun.

  

      Washe gari data cika kwana goma cif a asibitin jikinta ya ƙwaɓe ta fara zubar jini (bleeding). Hankalin likitocin ya tashi harma da su Maman Sadiq dan sun fahimci naƙudace tazo mata a bahagon yanayi. Tun suna ganin zata iya haihuwa da kanta har al'amarin yasoyin tsamari suka yanke shawarar mata cs kawai.

     Babu wani ja'inja Abba ya saka hannu matsayinsa na uba gareta. Daga haka suka shiga da ita ɗakin theatre su kuma suka koma gefe suna mata addu'ar rabuwa lafiya da abinda ke a cikin nata.


        Awa kusan uku Doctor Mansura ta fito fuskarta da murmushi. Duk miƙewa sukai suna mai sauke ajiyar zuciya ganinta a yanayi mai daɗi. Ta sake faɗaɗa murmushin da faɗin, “Alhmdllhi, an ciro baby boy ƙyaƙyƙyawan gaske, mai kuma lafiya insha ALLAH”.

        Basu gaza wajen ambaton Alhmdllh ɗinba suma, dan sunyi imani akan duk abinda kaga UBANGIJI ya jarabceka da samu ta hanyar da kai baka buƙatarsa ya fika sanin dalilin yin hakan. Basu isa canja ƙaddarar Zinneerah ba komai son hakan da zasuyi, sai dai su tayata da addu'ar ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Duk da har cikin ransu suna tsananin tausayin uwar da ɗan.

       Abbane yace, “Yaya jikin ita Zinneerah ɗin kuma?”

       “A Alhmdllh Alhaji. Itama dai insha ALLAH komai zai dai-daita zuwa nan gaba kaɗan. Kuyi haƙuri sai zuwa anjima zaku samu ganinsu koma da safe”.

       Godiya sukai mata. Ta wuce su kuma suka koma suka zauna kowa da abinda yake saƙawa a ransa.


    ★★★


     Kamar yanda likita Mansura ta faɗa basu sami ganin Zinneerah ba a ranar dai kam, sai dai zuwa yamma an fiddo musu da jariri ƙaton gaske kuma ƙyaƙyƙyawa kamar yanda Dr Mansura ta faɗa ɗazun.

     Abba ne ya fara amsarsa yana mai yin godiya ga ALLAH tare da jin tausayin yaron da baisan wanene shiba. Bayan ya masa addu'a ya miƙama Maman Halima daketa faman washe baki. Tace, “Masha ALLAHU mijin nawa kam dai-dai ni. ALLAH ya rayaka ya albarkaci rayuwarka. Ya jiƙan mahaifinka kaji”.

        Da amin suka amsa. Kafin ta miƙama Maman Sadiq dake kukan zuci. Bata musaba ta amsa itama ranta fal tausayin yaron dabaijiba bai ganiba. Ta ƙura masa idanu na tsahon lokaci zuciyarta na suya akan samuwarsa ta hanyar da ba ita sukai fataba. Sai dai a gefen zuciyarta na gargaɗinta da ambaton Alhmdllh. Dan babu maima UBANGIJI dole akan abinda yaso. Babu kuma mai sakashi saɓanin hakan.

     Itama dai addu'ar tai masa tamkar kowa ta sake miƙama Maman Halima dake kusa da ita. Ita kuma ta miƙama Matar Naziru. Bayan sun gama ganinsa da masa addu'a Nurse Salima tazo ta amshesa tana faɗin, “To waye zai zauna a wajenta? Dan an kaita ɗakin hutu yanzu haka. Sai dai likita tace wadda zata zauna da ita kawai za'a kai sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zaku ganta”.

        Dukansu sun gamsu da hakan, kafinma kowa yay magana Maman Halima tace ai bama sai anja zanceba itace zata cigaba da zama da ɗiyarta. 

    Wannan karamcin na Maman Halima kesa Maman Sadiq jin daɗi sosai da sake ganin girmanta da kimarta a koda yaushe, dan mace ce data cancanci girmamawa kodan ƙyawawan halayenta.

         Sallama tai musu tabi bayan Nurse Salima. Su kuma suka fito domin komawa gida.


★★


        Koda suka shigo gidan Maman Sakina batako leƙoba balle ta tambayesu yaya jikin Zinneerah ɗin tunda batabisu asibitinba. Duk da kuwa sanda Matar Nasiru tazo ta sanar musu ruɗewar jikin Zinneerah ɗin itama tana zaune a tsakar gidan. Amma taƙi bin Maman Sadiq. Bayan tafiyarta kuma bata kira waya taji halin da ake cikiba. Gashi yanzu sun dawo bataleƙo tajinba kuma.

      Hakan bai dami Maman Sadiq ba. Dan halin da take ciki ya wuce na matsalar Saude a yanzun. Tana shiga ɗaki fashewa tai da kuka, kamar Alhaji yasan za'ai haka ya biyo bayanta kuwa. Ganinta tsaye gaban mirror kanta a ƙasa tana shashshekar kuka ya sashi ƙarasowa cikin ɗakin sosai.

       “Haba Hauwa'u, minene kuma abin kuka anan dan ALLAH? Kenan bazaki iya karɓar ƙaddaraba? Ki tuna UBANGIJI ya fimu sanin abinda ke a ɓoye. Sannan yarinyar-nan mutane da yawa sun shaideta akan ba yarinyar banza bace. Kowa na ƙyautata mata zaton cewar tsautsayine kawai da ƙaddara da babu wanda ya isa kankaresu a rayuwarta. A ganina yanzu kamata yayi mu sake nutsuwa da janta a jiki wajen samun gaskiyar zance game da samuwar cikin, dan a yanda na fahimci zantukan jama'a a inda taje kwana da kwanaki ba'a saniba acan koma minene ya faru. Ina son ki kwantar da hankalinki ki karɓi komai a mashayin ƙaddara da jarabawa. Karki bari yarinyarnan ko wani a gidan nan yasan gaskiyar zance gameda yaron nan saboda gudun matsala, kokuma ita mu sakata  a wani halin da har zata iya tunanin sake sulalewa ta gudu daga nan kamar yanda ta baro can”.

     Cike da gamsuwa da bayanin mijin nata ta share hawayenta. “Nagode Yaya, nagode sosai da rufa asirina dana yarinyarnan. Lallai kaiɗin masoyine na gaskiya abin alfaharin kowacce mace. Insha ALLAH zanyi kamar yanda kace, sai dai ka tayani addu'ar jurewa wannan al'amari”.

       “Insha ALLAHU zan tayaki Hauwa'u. kema kuma kisa a ranki zaki iya ɗaukar komai kamar yanda kika ɗauki na baya da suka shuɗe. Kuma in ALLAH ya yarda inhar yarinyar nan bata da hakki duk inda uban yaron nan yake sai ya bayyana kansa watarana. ALLAH kuma zai wanketa ga idon kowa da izininsa”.

      “ALLAH ya tabbatar da hakan Yaya”.

      “Amin” ya amsa yana juyawa ya fita. Itama saita sake share hawayen da ke sake zubo mata. Zuwa tai ta leƙa yaranta taga harsun kwanta. Dama tasan Sadiq akwai ƙoƙarin kulawa kamar yanda ta horesa. Ɗan gyara musu abinda baiyiba tayi ta fito. Bayan tayi wanka itam ta kimtsa zuwa ɗakin maigidan dan girkintane.

     Sosai ya sake mata nasiha da tausarta akan komai, ya kuma sakata sukai salla da mikama UBANGIJI kukansu da bukatunsu. Sai gashi Alhmdllh ta wayi gari zuciyarta sakayau. Harma da jin zumuɗin komawa a sibitin taga halin da ƴarta ke ciki da baƙon duniya da baisan wanene shi ba.


     

       A asibiti kam da daddare ansha rikici, dan ɗan jinjiri dai kuka ya dinga tsula musu na yunwa gabannin asuba. Haka dai Maman Halima taita ƙoƙarin bashi ruwan zam-zam da aka haɗa da zuma a ciki. Zinneerah kam tanata faman barci batare da tasan wace wainar ake toyawaba. 

       Koda suka tashi aɗan barcin daya figesu bayan lafawa da kukan jaririn sai maman Halima ta samu sun makara. Lallaɓawa tayi domin gabatar da alwala. Tana kabbara salla tamkar jira yake ya fara raira kukansa da muryarsa dake cauy-cauy masha ALLAH. 

      Sosai maman halima ta rikice, tana a raka'ar ƙarshe taji shigowar mutum cikin ɗakin, ba'ayi maganaba dai, sai wani irin ƙamshin turare mai shegen daɗi daya gauraye ko ina na ɗakin. Tana ƙoƙarin sallamewa taji an fice da jaririn da har yanzu kukan yakeyi. Saurin sallamewa tai ta miƙe zaram ta biyo bayansu. Wayam babu kowa a wajen, sannan babu kukan yaron kuma. Hankalintane yay masifar tashi sanin duniyarnan fa babu gaskiya a cikinta. A cikin matuƙar ruɗani ta shiga leƙe-leƙe na neman inda aka nufa da yaron..............✍


No comments

Powered by Blogger.