Makauniyar Kaddara 1
*Page 1*
..............“Inada tabbacin wannan itace tashar da zaki iya samun motar duk wani gari da kike buƙatar zuwa”. Mai napep ya faɗa dai-dai yana samun wajen fakin, da ɗan karkato kansa yana duban yarinyar dake a baya zaune.
Batace da shi komaiba. Sai ƙoƙarin kwance haɓar zaninta da takeyi jikinta na rawa. Ta miƙa masa ɗari biyar ɗin dake a ƙudundune saboda uban ƙullin da tasha a cikin zani. Baki ya buɗe kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya ɗan fisgi ƙudundunanniyar ɗari biyar ɗin daga hannunta yana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa.
A yanzu ɗinma batace da shi komaiba, sai hawayen dake famar zarya daga idanunta zuwa kumatu.
Tsohuwar ɗari biyu guda biyu da naira talatin a sama ya miƙa mata fuska a tsuke.
“Nagode”.
Ta faɗa a karo na farko tana amsar kuɗin. Batare da ta jira amsarsaba ta fito daga Napep ɗin tana kalle-kalle da ƙoƙarin sake maida kuɗin daya bata a haɓar zani ta ƙulle kamar ɗari biyar ɗin ɗazun.
A kallo ɗaya zaka iya fahimtar ƙarancin shekarunta. Dan kuwa bazata wuce shekaru sha huɗu ba. A tsarin halitta batai kama da mai taɓin hankaliba, amma a yanayi zaka iya kiranta da mai ƙarancin hankalin. Duk da kuwa babu wani datti ko makamancin hakan a kaf illahirin jikinta.
Ƙara kai hannu tayi ta share hawayenta a karo na babu adadi, cikin rauni da alamun tsoron dake tattare da ita ta furta, “ALLAH gani gareka. Da kai na dogara, a gareka kuma nake buƙatar taimak......”
“Ƙanwata ina zakije?”.
Karaɗin wani kwandasta ya katseta batare da takai ƙarshen addu'arta ba. Kallonsa tai da jajayen idanunta dake a kumbure saboda kuka tace, “Danya”.
“Danya? Ƙanwata sai kinyi ƙarin bayani, dan nikam bamma taɓajin sunan wannan garin ba”.
Shiru tai alamar nazari, ‘Gaskiyar kwandasta ɗin nan. Danya dai garinsu motama bata shiga sosai. To amma idan bata mantaba lokacin da zasu taho da Hajji Lanti bayan sun fito daga Danya a mashin, a Gozarki suka kwana, washe gari kuma daga Gozarki sukazo kusada, anan suka sami motar Katsina’.
“Wai kodai bakisan ina kika dosa bane ƴammata?”.
Kwandasta ɗin nan ya sake katseta. Da sauri tace, “Kusada zanje”.
“......Kusa da kano, nesa da birnin katsina” kwandasta ya faɗa cike da barkwanci. ita dai batace da shi uffanba, sai ma faman waige-waige da takeyi, har yanzu akwai tsoron ko wani zai iya biyo bayanta tattare da ita.
“Kinga ga motar da zaki hau can ta kaiki Gidan mutum ɗaya. Inada tabbacin daga can zaki samu motar kusada ƴar ƙyaƙyƙyawa”.
“Nagode sosai” ta faɗa tana ɗan risinawa. Daga haka tai gaba da sassafa batare data sake bi takansa ba.
Tana isowa motar daya nuna mata ko jiran ba'asi bata tsaya yiba saboda jin kwandasta ɗin motar nata faman faɗin, “Charanci, kankia, Gidan mutum ɗaya, Tsanyawa, Bichi, har kano.
Can baya ta shige inda wata mata ke zaune ita da yaranta biyu da bazasu wuce sa'annintaba. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya dasa hannu ta gyara ɗan labulen jikin gilashin yanda take fatan ko su Hajiya biyota sukayi bama zasu iya ganinta ba. Duk da hakan kuma roƙon ALLAH take a ranta ALLAH yasa motar ta cika da wuri su tafi.
Addu'ar tata kuwa ta amsu. Dan ko cikin ƙanƙanin lokaci motar ta cika. Ita dai tana duƙunƙune cikin hijjab har kanta. Ko wanda ya shigo ya zauna a gefenta bata kallaba sanda ya shigo. Ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya jin motar ta ɗaga alamar zasu bar cikin tashar.
Sunyi tafiya mai ɗan tsayi data tabbatar sunbar cikin birnin katsina ta tsinkayi maganar kwandasta na ambaton kowa ya bada kuɗin mota. Ciro kanta tai daga hijjab ɗin bayan ta kunto kuɗin data ɗaure a haɓar zaninta na canjin mai napep. Jin matarnan mai ƴaƴa na tambayar “Nawane gidan mutum ɗaya” ya sata tsaida hankalinta tana jiran amsar kwandasta ɗin itama.
“Ɗari huɗu ne kuɗinki hajiya”. Ya bata amsa yana amsar kuɗin na kusa da shi.
Matar tace, “Haba ɗana adai duba. Wlhy jiya a ɗari uku-uku mukazo. Yaran nanma ɗari bibbiyu na biya musu”.
“Ai jiya kikace hajiya. Jiya kuma ba yau bace. Dan haka kuɗinki keda yaranki dubu da ɗari biyu ne”.
Zatai magana wani dake can gaba yay saurin amshewa. “A'a fa gaskiya ɗari uku ne, ni kaina ɗazun nan da safe nazo a haka”.
A take rigima ta kaure tsakanin kwandasta da matarnan da mutumin da yay maganar da safe yazo a ɗari uku. Da ƙyar dai aka tsaya akan ɗari uku da hamsin.
Ita dai yarinyarnan dama bata tanka ba. Ta miƙa masa ɗari huɗun da mai napep ya bata canji.
“Ƙanwata ina zakije?”.
A taƙaice tace, “Gidan mutum ɗaya”.
Canjin hamsin ya miƙo mata. Batare datace komaiba ta amsa ta maida a haɓar zaninta. Sai dai bata koma cikin hijjabinba tabi ayarin masu kallon hanya. Kasancewar motar mai lafiya ce bayan sallar la'asar kaɗan suka iso gidan mutum ɗaya. Danma sun ɗanyi tsaye-tsaye a hanya na sauke mutane.
A gidan mutum ɗayarma dai a rikicen take. Dan ba taɓa yin tafiya irin haka ba sai wannan karon. Sanda zasu tafi kuwa hajji Lanti ce tai musu komai. Da ƙyar ta samu ta tambayi wani yaro mai saida biredi inda zata sami motar kusada. Shine ya nuna mata. Tai masa godiya.
Ta iske ƙananun motoci kusan huɗu dake jere a kan hanyar da yaron yace mata itace hanyar kusada. Lokacin da suka tafi su tun daga cikin kusada suka shigo motar katsina.
“Ƴammata kusada ne?”.
Wani tsamurmurin saurayi ya faɗa yana nufota. Saurin ɗaga masa kanta tayi alamar eh. Cike da jin daɗi yace, “Yauwa taho muje, dama mutum ɗaya muke nema”.
Har cikin ranta taji daɗin hakan. Ya nuna mata jar motar data gama fita hayyacinta. “Yauwa shiga nan. Bayin ALLAH a matsa mata mu kama hanya ko”.
Cike da mita fasinjojin suka shiga muskutawa dan sama mata waje. badan wajen zai wadacetaba ta shiga ta zauna. Sai dai kasancewar ta mai ƙaramin jiki yasa bata takuraba matuƙa. Sai dai waɗanda ta tarar a ciki sunata faman mita sukam an takura musu. Direban ya cika haɗama da son kuɗi. Yanda direba bai tanka musuba itama bata tanka ba. Sai dai acan ƙasan ranta daɗi takeji zata koma gida taga Babanta da su Yaya Tinene, duk da su ba son ganinta sukeba.
Tsabar rashin isashshiyar lafiyar motar basu iso ba sai gab da magriba, dan sun kwashe kusan awa ɗaya da rabi a hanya. Ga tsaye-tsaye da suka dingayi ana sauke wasu da ɗauka a ƙananun ƙauyika har kusan sau uku.
Hankalinta bai tashiba sai da suka iso taga kowa na miƙawa direba ɗari da hamsin kuɗin mota. Cike da tashin hankali da fargaba ta miƙa masa naira tamanin ɗin da suka rage mata. Wani banzan kallo yay mata sheƙeƙe yana nuna kuɗin.
“Naga kina miƙamin murtala huɗu (80n), bakiga abinda kowa ke badawa bane?”.
Cikin rawar murya da cikowar ƙwalla a idanunta tace, “Wlhy su kaɗaine suka ragemani, dama ɗari biyar ce na taho da ita da ga katsina, to sai naba mai ƴar ƙurƙura......”
“K! dakata. Wannan damuwarkice ba tawaba. Inda kinsan baki da kuɗin mota da baki bari nayi jigilar ɗakkoki ba ai. Dan haka ni kuɗina kawai na sani ba wai yanda kika taho daga katsina ba”.
Sharr hawaye suka shiga sakko mata. Ta durƙusa a ƙasa zata fara roƙonsa, hayayyaƙo mata yayi da masifa. A take hankalin mutane ya fara dawowa kansu. Ita dai duƙe take tana kuka da roƙonsa.
A mutanen da suka taru wajen duk basu bata goyon bayaba. Acewarsu miyyasa bata faɗa masaba kafin ta shigo. Idan data faɗa in yaso saiya taimaketa. Suma ɗin haƙuri take ta basu ita dai, dan harga ALLAH batasan adadin kuɗin motar ba. Hakama direba da zugar mutane ke sake harzuƙawa yana mata tujara.
Tun tana roƙonsu a duƙe harta koma gurfane abin tausayi. A haka wani saurayi da tausayinta ya kamashi ya ciri naira ɗari ya bama mai motar. Daga haka suka sama mata lafiya. Har ƙasa ta duka taima saurayin godiya. Yace karta damu, tadai daina shiga mota babu kuɗi. Gara ma idan bata da shi ɗin ta dinga faɗa kafin ta shiga zaifi sauƙi. Godiya nanma tai masa ta miƙe riƙe da naira talatin ɗin daya sake rage mata tunada an biya mata ɗari.
A kusada ɗinma ba sanin ina zata gano hanyar garinsu tai ba. Dan tunda tasan kanta bata taɓa zuwa cikin Kusada ba. Iyakarta ƙananun ƙauyukan dake gefen ƙauyensu kawai.
Tana son tambaya tanajin tsoro, ga wani azababben ciwon ciki da takeji yana taso mata kaɗan-kaɗan. Duk yanda taso cigaba da tafiya sai ya gagara. Da ƙyar taja ƙafafunta zuwa wata runfa ta zauna. Da alama runfar mai yin faci ne. Kasancewar magriba tayi harya tashi.
Zama tai ta duƙunƙune kanta cikin kafafu jikinta na rawa. Ga wata irin zufa na keto mata ta ko ina saboda azabar ciwon ciki. Tun tana zaune har sai da takai kwance a wajen tana juye-juye. Bata damu da cinnakun daketa galla mata cizo ba a jiki, dan ciwon da cikin nata ke mata ya danne komai.
Tsahon lokacin data ɗauka a yanayin ciwone yasa har dare ya rufa bata saniba. Sai jin garin tai ya rage hayaniyar jama'a. Ba ciwon cikin bane kaɗai matsalarta harda Yunwa da ƙishi. Dan rabonta da abincin kirki tun jiya a gidan Hajiya. Abincin da aka bata a gidan da aka kaita ƙinci tayi sosai, dan tana tsoron taci su yanke mata kanta kamar yanda zuciyarta ke bata danshi suka kaita gidan.
Tashi tayi zaune a hankali tana ɗan waige-waige. Titin babu haske. hakama jama'a duk sun nufi gidajensu sai ɗai-ɗaiku. Duk yawan motoci da mashinan ɗazun yanzu babusu. Sai wasu da basu wuce uku ba. Mashinanma bazasu gaza haka ba. Sai fitilar mai shayi da take hangowa can a wajen da motocin ke tsayawa (Tasha).
Komawa tai ta kwanta. Dan haka kawai taji wani shegen tsoro ya turniƙeta. Ta rufe idanunta gam tana karanto abinda ta sani na addu'a. Cikin amincin ALLAH kuwa sai ga barci ya kwasheta. Da alama hakan nada nasaba da gajiyar dake tare da ita ta wahalar tafiya da gudun da taci kafin samun Napep..
★★★★★
Tun kiran sallar farko na asubahi ta farka da wani irin ciwon ciki. Murkususu ta dingayi tana kuka. Ta jima tana shan azaba kafin ya lafa mata. Zuwa lokacin anata ƙoƙarin shiga sallar asuba. Tashi tai a jikkace, dan yunwa takeji sosai. Ta taka a hankali zuwa inda massallacin tashar nan yake. Butocin da akai alwala ta dinga taɓawa harta sami mai ruwa. Ɗakkowa tai ta dawo wajen rumfarnan. Ta zagaya bayanta tai fitsari da yin alwala. Sauran ruwan kuma ta shanye. Sai a yanzune ta tuna ko sallar La'asar ɗin jiya batayiba. Rabonta da salla tun ta azhar da bayan idarwarta ta gudo.
A take ta fara maka sallolin nan batare da tabi tsarin daya dace na mai ramuwaba. Sai da ta gama jerosu har asubahi. Zuwa lokacin mutane nata fitowa, hakama masu mashina da motoci.
Da farko zaman kallonsu tayi. Daga baya kuma saita mike bisa shawarar zuciyarta. Ƙarasawa tai wajen mai shayin nan daketa ƙoƙarin ɗora tukunyar garwar shayinsa yana raira waƙar shata. bayan ta masa sallama ya amsa ta gaishesa da girmamawa dan babbane ba laifi.
“Baba dan ALLAH tambaya nake?”.
Ɗago kansa yay ya kalleta a karon farko. “ALLAH yasa na sani ɗiyata”. Ya faɗa da kafeta da kallon ƙurilla.
Kanta a ƙasa tana ɗan juya yatsun hannunta cikin juna tace, “Baba dan ALLAH inane hanyar Danya?”.
“Danya! Danya!?. To indai Danya dana sanice ta kusa da Gozarki hanyarta na nan gabas da mu”.
Jin sunan Gozarki ya sata kallonsa cike da jin daɗi. Ta kaɗa kanta fuskarta na sauyawa alamar farin ciki tace, “Eh itace baba”.
Yace, “To zaki zauna ki jira masu mashina dake shiga kenan. Idan kuma bazaki iya jiraba ki samu mai mashin anan ki biyasa talatin ya kaiki ainahin Gozarki ɗin anan zaki samu ƴan mashinan Danya”.
Taji daɗin shawararsa. Hakan yasata masa godiya. Duk da talatin din ta rage mata a jiki, kuma yunwa takeji gara tabi shawararsa. Babu wani jimawa kuwa ta samu mai mashin. Kamar yanda mai shayi ya faɗa talatin mai-mashin din yace zata bashi. Sai da ta bashima sannan ta hau.
Cikin mintuna ƙalilan suka iso Gozarki. Amma sai da ya kaita har hanyar ƙauyensu Danya. A take farin cikinta ya ƙara bayyana. Harta zauna da nufin jiran masu mashin dan babu wanda ya fito saboda akwai sauran safiya, sai kuma ta mike. Ba komai ta tunaba sai nasihar saurayin jiya daya cika mata naira ɗari. Bata da ko sile. Mizaisata zaman jiran mashin? Gara ta taka da ƙafa, duk da kuwa tasan akwai nisa. Amma ɗokin gata a kusa da gida sai ya gusar mata da komai har yunwar da takeji da rashin daɗin jiki.
Tafiya ta fara a doguwar hanyar jan birjin da batasan iyakar lokacin ƙarewarsa ba. Ga ɗan sanyin safiya na busawa kaɗan-kaɗan.
Tayi tafiya mai nisa ciwon cikin nan da batasan dalilinsaba a kwana biyun nan ya ƙara turniketa. Ƙarƙashin bishiyar dalbejiya ta samu ta zauna. Taci murƙususnta da kuka na wani lokaci kafin ta tashi ta cigaba da tafiya. Zuwa lokacin ƴan mashinan garinsu nata fitowa ɗai-ɗai da fasinjoji akai.
Kafin ta gama ankara rana ta ƙwalle. Ga yunwa na cigaba da ragaɗar hanjin cikinta. Haka ta cigaba da jurewa tana jan ƙafafu tamkar mai tsohon ciki. A lokacin da dukkan wani ƙarfinta ke gab da ƙarewa ne ta hango rufin ginin makarantarsu dake da matuƙar tsaho fiye da duk gine-ginen gidajen garin. Ta saki murmushin yaƙe idanunta dake ganin duhu-duhu na lumshewa. Sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi da sauri-sauri. A hankali hajijiya ta fara juya mata hanyar, saiko gata ƙasa yaraf babu numfashi..........✍
Leave a Comment