Jiddatul Khair 50

 


Murmushi kawai Jiddah tayi bata ce komai ba, Ahmad bai kuma ce mata komai ba shi ma, suna isa wani babban pharmacy yayi parking yana kallonta yace "I am coming let me get u pain reliever, Umma tace kina ciwon ciki ko?" Ta gyada masa kai ya kashe motar ya sauka ya shiga cikin pharmacy din, ba a wani dau lkci sosai ba ya fito da ledan magani, ya shiga motar yana kallonta ya ajiye mata kusa da ita yace "Ko kina bukatar wani abun daban, akwai Supermarket a nan..." Ta girgixa kai tace "Aa bana bukatar komai" Yace "Ohk" sai da suka hau saman titi ta d'an kallesa amma bata ce komai ba, ganin haka yace "Say what is in ur mind Jiddah, be free with me and take me as ur elder brother" Ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Ni yanxu baxan iya xuwa in ga Baabarmu in gaisheta ba?" Da d'an mamaki yace "Baabarku? Me xaki yi mata idan kinje, ko kuma me xata maki ita?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Babu amfanin xuwa wajenta a yanxu dai Jiddah, idan kinyi hakuri wataran babu wanda xai hanaki xuwa gareta, when the rightful time comes da kanki ma xaki je ba sai wani ya kai ki ba kin ji?" Cikin sanyin murya tace "Toh, amma kuma akwai wata tsohuwa a layinmu ana ce mata Iyah, tana da kirki sosai, ko ita ma baxan iya xuwa in gaisheta ba?" Yace "Baki tunanin xata gaya ma Baabarku kin je?" Ta girgixa kai da sauri tace "Aa baxata fada ba, ai ita ba haka take ba, ita ce fa ke taimakona lokacin da nake gun babarmu, har abinci tana bani idan tana da shi" Yace "Toh yanxu kina son a kai ki can kenan?" Ta gyada masa kai a hankali, ya d'an yi shiru yana ci gaba da driving dinsa, kallon agogon wrist dinsa dake nuna karfe hudu da wani abu yayi, sannan yace "Kinsan me Jiddah?" Jiddah na kallonsa ta girgixa masa kai, yace "Ki bari ko gobe da daddare in kai ki, tunda kina gidana, i think it will be more safer..." Jiddah tace "Toh nagode" Yayi mata murmushi kawai. Suna isa gidansa yayi parking a space din parking sannan ya sauka motar ita ma ta sauka, tana biye da shi suka shiga gidan, Xaunawa tayi a parlor shi kuma ya wuce bedroom dinsa sanin Ramlah na can tana bacci, xai shiga dakin sai gata ta fito, ya d'an buda ido yace "Ashe ba bacci kike ba" Ta turo baki tace "Ina ice cream din?" Yace "Ohh kinga na mance wllh, I'm sorry anjima xan fita sai in siyo maki, fito ku gaisa da Jiddah" Ramlah tace "Da gaske?" Yace "Ehh" a tare suka dawo cikin parlon, Ramlah ta xaro ido tace "Lallai sis Jiddah ce yau a gidanmu, ashe xa ayi ruwa da kankara" Jiddah tayi murmushi tace "To ai ina xuwa" Ramlah ta karaso ta xauna kusa da ita tace "Aa sau biyu ina ga kika taba xuwa, ina fa sane, to ya su Umma?" Jiddah na murmushi tace "Lafiya lau, ya jiki?" Ramlah tace "Naji sauki Alhmdlh" mikewa tayi ta dau jakar Jiddah tace "Mu je ciki to" Jiddah ta mike ta bi bayanta, Ramlah ta kai ta dakin visitors, sosai Ramlah taji dadin xuwa Jiddah gidanta, Ramlah tace "Gashi ni banyi girki ba wllh, ko in dafa maki indomie kafin a daura dinner?" Jiddah tace "Daga gida fa muke, ai na ci abinci" Ramlah tace "Toh bari in kawo maki ruwa" Bata jira cewar Jiddah ba ta fita dakin, sai da Ramlah ta daura ruwan shinkafa a gas snn ta dau tray ta daura Chivita drink da ruwan gora sai glass cup ta dawo daki ta ajiye tana kallon Jiddah tace "To ga ruwa ki sha sis Jiddah" Jiddah ta d'an yi murmushi tana kallon hancinta dake shige da na Abuturrab, har idanuwansu iri daya ne, dama kuma duk a cikinsu ita tafi kama da shi, Ramlah ta xauna tana ta jan ta da hira, tun Jiddah na shiru shiru har dai ta fara biye mata, lkci daya Ramlah tace "Ohh na manta na daura ruwan shinkafa a gas, bari in xuba shinkafar in dawo" Jiddah tace "Toh bari in wanke in xuba maki" Ramlah ta nufi kofa da sauri tace "Aa wllh... Ai ba wani aiki bane" Daga haka ta fita, xaune ta tadda Abuturrab a parlor da Ahmad, Ta d'an buda ido sai kuma ta washe baki tace "Yaushe ka xo yaya?" Karasawa tayi ta duka gefensa tace "Welcome Yaya, ina yini?" Ya kalleta yace "Lafiya lau, ya gida?" Tace "Alhmdlh, ya aiki?" Yace "Fine Alhmdlh" mikewa tayi ta wuce kitchen, Ahmad dake shafa beard dinsa yana kallon Abuturrab yace "ina jin ka great Captain" Abuturrab yace "Kana jina na me wai, kai fa idan kaga mutum na neman abu a wajen ka ka dingi walakantasa kenan" a takaice Ahmad yace "Toh ka tafi asibiti kawai" Abuturrab ya dinga kallonsa, Ahmad yace "Yes, nasan kana da mata baxan rubuta maka wannan maganin da kace ba, ko dai Hygiene din ne bai kai yanda kayi expecting ba? Abu d'an sauki tunda kana da wadata sai ka kara aure kawai" Da dariya Ahmad ya kare maganar, Abuturrab dai ya kasa ce masa komai, Jiddah ce ta fito parlon rike da tray din lemon da Ramlah ta kai mata don xuwa kitchen ta taimaka ma Ramlah da girkin da tace xata yi, Tsaye tayi bakin corridor din dakunan ganin Abuturrab a parlon kafin ya ganta ta juya da sauri har tana tuntube ta koma ciki ta shige daki ta kulle kofar gabanta na faduwa sosai, Abuturrab ya kalli direction din don rufe kofa kawai yaji, can ya kalli Ahmad yace "Who is there?" Ahmad yace "Bakuwa muka yi" Abuturrab yace "Ohk" Ramlah ta fito kitchen ta ajiye masa ruwa da drink tace "Amma yaya ba yau xaka koma kano ba ko, naga yamma yayi" yace "Gobe da safe in sha Allah" Yana fadin haka ya dau bottle water daya ya bude ya sha ya mayar ya ajiye sannan ya mike yace "Sai anjima...." Ahmad dai sai murmushi yake yana kallonsa, Ramlah tace "Yaya ka tsaya ka ci abinci mana pls..." Yace "What are u cooking?" Tace "Shinkafa da miya ae bai da wahala" Yace "Idan naje can gida xan ci, yanxu gida xan wuce" Daga haka yayi ma Ahmad sae da safe ba tare da ya kallesa ba ya nufi kofa ya fita. Gidansu ya tafi, direct ya tafi bangaren Umminsa, fitowa tayi daga bedroom jin an bude kofar parlor, ganin shi ne ta koma dakin, ya bi ta har can, xaunawa yyi gefen gado sannan ya gaisheta, ta amsa tana kallonsa, bai kuma ce mata komai ba tace "Me ya hadaka da matarka?" Ya kalleta yace "Ummi ita da Hajja ce, ni ban mata komai ba wllh" Tace "Why did u create room for that, me yasa baka dakatar da Hajjar ba?" Yace "Sanda suka yi ma ni bana gidan, and na bata hakuri but she didn't listen to me tayi tafiyarta kawai" Ummi dai tayi shiru tana kallonsa, can tace "Are you okay?" Daga kai yayi ya kalleta sai kuma yayi murmushi yace "Did u notice anything mum?" Tace "Are u answering my question with a question?" A hankali yace "Kawai ki taya ni da addu'a Ummi" tace "Me ke faruwa?" Ya girgixa mata kai yace "Ba komai addu'a kawai nake bukata" Tace "Saboda ni ai bani da matsayin da xaka gaya min matsalarka ko?" Ya kalleta a hankali yace "Ko daya Ummi, ni kaina ban san me ke damuna bane" Tace "Toh Allah ya yaye maka" Yace "Ameen" Yace "Ummi in a month time xamu fita waje fa..." Tace "Xuwa yin me?" Yace "Aa wani babban mutum xa mu yi piloting" Ummi tace "Toh Allah ya kai mu, sai ku dawo yaushe?" Yace "Ban sani ba dai, sai yanda suka ce" Ummi tace "To Allah ya tabbatar da alkhairi" Yace "Ameen" tace "Yanxu ka tashi kaje ka ba matarka hakuri ka dauketa ku tafi gida tare, ba sai an sake wani xaman ba" Shiru yyi, Ummi dai na lura da shi, can yyi kasa da murya yace "Ummi Aneesah bata son xaman lafiya tare da ni, I don't know why she changed all of a sudden from who I knew her to be, kamar ana xugata kullum, kinga bata mutunta ni bata kunyar gaya min ko wani magana ya xo bakinta, sannan i wish u can come one day ki ga yanda ta mayar min da gida, kawai fa sai dai tayi wanka ta fesa turare abinda ta iya kenan, tsaftace muhalli Zero, girki Zero, ibada Zero, kullum sai nayi fama da ita a kan sallah, I'm so tired and fed up Mum, ko wata biyu fa ba ayi ba, har xullumin dawowa weekend nake wllh Ummi" Ummi da tayi shiru tana kallonsa taji tausayin d'an nata amma taki nunawa, can tace "Toh me yasa baxa ka daukar mata mai aiki ba?" Da sauri ya kalli Ummi yace "House help kuma Ummi? Warce ta xauna kafin ita a gidan duk da karancin shekarunta da rashin wayewarta ai ban daukar mata mai aiki ba, kuma komai na gidan ita ke yi, sannan ni ban ta6a dawowa weekend naga ba dai dai ba" Ummi dake kallonsa kasa kasa tace "Wacece ta xauna kafin ita?" Shiru yayi bai ce komai ba, Ummi tace "Wai Jiddah kake nufi?" ya daga kai yana kallon Ummi amma bai ce komai ba, Ummi ta tabe baki tace "Ni a iya sanina warce ta xauna kafin ita ai ba matsayin mata ka dauketa ba a lokacin ko? Wannan kuma matarka ce ta sunna...." Shi dai bai ce komai ba, Ummi ta ci gaba tace "Don haka sai kayi hakuri da duk abinda ka gani, da yanda ka gani, na farko dai ba wani ya nemo maka yarinyar nan yace ka nemeta ka aura ba..." Ya marairaice mata yace "Ummi to ai ni da muka hadu da ita da farko ba wai soyayya muke ba, kuma ni ban ta6a tunanin xan ma aureta ba, kawai dai ta kan kirani mu gaisa ne time to time, sai kuma WhatsApp chat, a airport din Abuja muka hadu taje gun uncle dinta, ni kuma mun sauke jirgi, and she requested my digit na bata kawai don ban iya walakanci ba, sai kuma coincidentally na dawo wani weekend na ganta a gidan nan ta xo gun Aunty da aunt dinta ashe Mum dinta close frnd din Aunty ce" Ummi dake ta kallonsa tace "Sai aka yi yaya? Sai aka ce ka so ta dole har ka aureta?" Yace "Aa Ummi but Aunty ce ai..." Sai kuma yayi shiru, Ummi ta tabe baki tace "Kaga Aliyu rabani da wannan labarin da na sani, yanxu dai kawai kayi hakuri ka nema mata house help, da xata dinga tsaftace maka gidan ka, sai kuma ka ci gaba da hakuri da sauran halayen nata tunda dai auren soyayya ku ka yi ba auren kiyayya ba" Bai iya yace komai ba, Ummi dai sai kallonsa take, amma can kasan xuciyarta tausayinsa take, she understands what he is going through, barin shi da yayi detesting kazanta with passion, ita har ta mance rabon da ya shigo dakinta balle har ya dade haka yana xance da ita kai tsaye, Ya d'an ja tsaki underneath his breathe yace "Karamar yarinya ma da ta kusa doubling age dinta warce ta tashi a ghetto bata irin abinda take yi na kazanta wllh, tun daga balcony nake jiyo kamshi lkcn da yarinyar ke gidan idan na dawo gida, for once ban ta6a shiga kitchen naga dirty utensils ko daya ba, ni har kunyar wani nawa nake ya xo gidana yanxu, dama a garin nake sai in dinga gyarawa ni kullum, kawai ita abinda ta sani sai tayi wanka ta fesa turare ta xauna tana danna waya, sai tara kawaye a gida" Ummi tace "Toh wai ita kuma wannan karamar yarinyar da kake sa wa a baki kake comparing da matarka meye hadinka da ita ne, why don't u face ur life ka daina mentioning dinta a lamarin ka, did she have anything to do with u again xaka sa ta a bakin duniya" Ya kalli Ummi amma bai ce komai ba, Ummi tace "Ni ka tashi kaje ka same matarka ka bata hakuri ka dauketa ku tafi gida, Allah ya ci gaba da daidaita ku, ba ruwana da matsalar cikin gidanku, it's something u should have known before marrying her"  Abuturrab yace "But how mum, kullum fa fes fes xaka ganta a titi, waye xai san xata yi haka?" Ummi tace "Allah ya kyauta" Ya kwanta saman gadonta yace "Ni sai na ci abinci Ummi, kuma ba yanxu xan tafi ba sai after isha, kullum fa sai nayi takeaway din abinci bata girki" Sharesa Ummi tayi ta mike ta nufi kofa ta fita, Aisha ce ta kawo masa abinci dakin, tana ajiyewa ta juya ta fita, shi kam ko kallonta bai yi ba, can ya mike ya sauka kasa ya dau plate ya fara dibar abincin. Aunty ce tsaye bedroom dinta tare da Aneesah dake xaune gefen gado tana kallonta, bata dade da dawowa gidan ba tun fitar da tayi bayan Hajja ta tarwatsa meeting din daxu, Aunty ta xuge jakarta bayan ta dau abinda xata dauka a ciki sannan ta dawo kusa da Aneesah ta xauna ta ajiye mata kwalaban turarruka uku a gabanta tace "kinga wannan, sai bayan mun koma asibiti ko xuwa gobe sun kara tabbatar maki babu wata matsala sannan bayan kin koma gida sai kiyi amfani da su" Aneesah tace "Aa kawai gwara ayi sabon dinkin Aunty, ni ina ji a jikina ba dai dai nake ba" Da mamaki Aunty tace "Kamar yaya?" Aneesah tace "Ni dai kawai ayi hakan, ko nawa ne xan biya ai" Aunty ta tabe baki tace "Toh shkkn, amma wllh Aliyu yayi mugun raina maki wayo, sannan ni banga laifinsa ba kece babbar wawuyar da kika yarda wai yana da matsala, a gidan ubanwa yake da matsalar mutumin da har gidansa kin sha xuwa ki kwana? Ko ke duk xuwan da kike gidansa a Abuja kin ga alamar yana da matsala?" Aneesah ta tabe baki tace "Ban ta6a ganin haka ba wllh, kawai shi dai baxai yi intercourse ba sbda gudun sa6on Allah amma ba don bashi da lafiya ba ko wani abu, amma babu abinda baya min ai, ce min yayi of recent ya samu matsalar" Aunty tace "Wllh ni ban yarda da kanwar uwar nan tasa ba don ita ma waye bai san tana shige shige ba kilan taje ta hango aikinmu ne tasa aka lalata, shine yake ta maki hanya hanya..." Aneesah tace "Toh ai da kin tambaya inda kika je daxu" Aunty tace "Wllh na manta shaff ban tambayi mutumin ba, amma akwai wani da xan kira anjima a benue, xai sanar da ni komai, yanxu kuma sai ki kirgo dubu talatin na turaren nan ki bada" Aneesah tace "Ina na gansu Aunty, har yau fa nace maki kudin nan da kika ce in tambayesa sai min yawo da hankali yake, yace yau yace gobe" Aunty tace "Rabu da shi don ubansa, xa muyi maganinsa nan ba da dadewa ba, muna nan dake sai account dinsa ya dawo hannunki gaba daya" Kwankwasa kofar dakin aka yi, Aunty ta jawo pillow ta ture kananun kwalaban turaren a karkashi da sauri, Aka bude kofar Abuturrab ya shigo da sallama kansa a kasa, Hade rai Aunty tayi ta mike ta dau Hijab dinta ta saka ta shimfida darduma ta hau sallahn isha, Aneesah dai sai wani cika take tana batsewa tana danna waya, ya ja stool ya xauna ya fiddo nasa wayar yana dannawa, yana ta xaune har Aunty ta idar da sallah, sannan ya kalleta yace "Ina yini Aunty" a takaice Aunty tace "Lafiya lau, sai yanxu ka ga damar shigowa bayan ina ganin sanda ka shigo gidan tun kafin magrib?" Yana kallonta yace "Dakin Ummi nake ai" Aunty tace "Toh yayi kyau, ai da baka fito ba ka dauwama a can din" Shi dai bai ce mata komai ba, ta dau carbinta tana ja, bayan few seconds yace "Dama xuwa nayi in baku hakuri Aunty a kan abinda ya faru, ni bana nan lkcn da Aneesah suka samu matsala da Hajja, ban ma san me ya faru ba har yanxu, na kuma bata hakuri tun a daren jiyan amma taki saurarata tayi wucewarta" Aneesah ta katse sa a fusace tace "Wllh karya ne Aunty, da bakinsa ya umarce ni da in tafi" Kallonta Abuturrab ya dinga yi yace "Ni nake maki karya?" Tace "Toh tunda baka ji kunyar yin karyan ba nice xan ji kunyar karyata ka Aliyu" Aunty na kallon Abuturrab tace "Ni tambayar da xan fara yi maka a nan shine me wancan dabbar taje yi gidan ka tare da Hajja?" Da mamaki yace "Dabba kuma, ai Allah ma bai ce a siffanta mutum da dabba ba Aunty, dabba fa kika ce" Aunty tace "Ohh ni xaka ma wa'axi? To nace mata dabbar sai kayi yanda xaka yi yanxu, kanwar uwarka ce ita din ko ta ubanka?? Ko uban meye hadinka da ita xaka ce kar in kirata da dabba? Ka bani amsar tambayata uban me ya kaita gidanka Aliyu?" Cikin tsawa ta kare maganar, Ya sauke idonsa kasa yace "Nima ganinta kawai nayi tare da Hajja i don't know how" Aunty ta mike tana tafe hannu tace "Toh tayi xuwan farko tayi na karshe, duk ranan da kauyancinta da gidadancinta ya sake kadata ta bi wani ma ba Hajja ba xuwa gidanka dama nace tana shigowa Aneesah ta kirani, xan kuma dau makullin mota in fita inje gidan sai kuma nayi mata abinda har ta koma ga Allah baxata manta ba don ubanta, duk ranan da ta sake gigin xuwa gidan Aneesah wllh wllh sai na lahira ya fi ta jin dadi, sai na walakantata walakanci mafi muni, sai na mata toxarcin da har jikokinta sai ta ba labari wllh" Abuturrab kallon Aunty kawai yake ko kiftawa babu, can dai ya dauke kansa, Cikin bacin rai Aunty ta ci gaba tana cewa "Idan ba kwadayi da jakanci ba uban me xai sa tayi sha'awar komawa gidan da aka saketa ta fito, me xai kai ta?? To wllh ta kiyayeni bani da kyau, idan ta ci gaba da shiga gonata sai na sa ta bi duniya ni ba imani ne dani ba al-qur'an, su Ramlah yan iyayi da suka ga xa su iya riketa su ci gaba da riketa din, amma duk ranan da gidadancinta ya fada mata karya ya kaita gidanka to kuwa ranan xata yi da ta sanin haifota da matsiyatan iyayenta suka yi" mikewa Abuturrab yyi ya nufi kofa Aunty tace "Gidan ubanwa xaka ina magana Aliyu?? Aliyu ba da kai nake ba??" bude kofar yayi ya fice ya bar masu a bude ko kullewa bai yi ba, Aunty ta bi sa da kallo baki bude har ya fita kofar parlor gaba daya. Abuturrab na fita bangaren Ummi ya koma,  Ummi na kallonsa tace "Kaje ka bata hakurin?" Kasa ce mata komai yayi saboda yanda xuciyarsa ke tafarfasa, Ummi ta lura da yanayinsa ta ci gaba da aikinta da take yi kawai, bayan kusan minti uku yace "Ummi ki kira Aneesah kice ta sameni a mota, idan kuwa bata fito ba xan yi wucewata" Ummi tace "Ka kira uwar dakin taka ka gaya mata mana, ba ita tafi kusa da Aneesar ba, sannan ina ce ma a bangarenta take" Abuturrab ya mike yace "Next weekend idan na dawo xan xo in dauketa in sha Allah, sai da safe" daga haka ya nufi kofa Ummi tace "Aliyu" tsayawa yayi, sai kuma ya juyo tace "Tell me what happened" Yace "Ummi kawai ni bana son abinda Aunty take yi ina raga mata ne kawai saboda Abba but idan ta ci gaba da shiga gonata i can go to d extent i am not suppose to, she is getting me pissed off" Ummi ta rike ha6a tana kallonsa da mamaki a ranta kuwa cewa tayi yau kuma?? Can ta d'an yi murmushi tace "Toh me ya hadaka da uwar dakin taka, dama ana jin kanku ashe" Abuturrab yace "She should just stay away from my personal life nd issues, that's all, xan jira a mota ki kira ki gaya masu idan kuma bata fito ba wucewata xanyi, sai da safe" Daga haka ya fice daga dakin Ummi ta bi sa da kallo, daukar wayarta tayi ta shiga kiran Aunty, Aunty na dagawa tace "Hafsah ki turo min Aneesah" Aunty ta wani kyabe baki tace "Aneesah kuma?" Ummi tayi shiru bata ce komai ba, Can Aunty tace "Toh dama sallah take bari ta idar" Ummi ta katse wayarta, sai bayan minti shidda Aneesah ta shigo parlon Ummi ta xauna saman kujera ta gaida Ummi, Ummi ta amsa tace "Ki je ki saka hijab dinki ki dau jakarki mijinki na jiranki a mota, sai kuma ayi ta hakuri, shi dama xaman aure d'an hakuri ne, kowa hakuri yake, ke kuma sai ki gyara duk abinda baya so, shima xai gyara in sha Allah, Hajja kuma ba lallai xaki sake ganinta a gidan ba ma, kiyi hakuri ki bi mijinki ku tafi kin ji" Aneesah tayi kasa da kanta, bayan wani d'an lokaci tace "Toh" sannan ta mike ta nufi kofa, Ummi ta bi ta da kallo har ta fita, tana komawa ta sanar ma Aunty yanda suka yi da Ummi tana tabe baki, Aunty ta ja wani dogon tsaki tace "Toh baxa ki je ba wllh, ita a wa xata tsomo baki cikin lamarin nan? Ina ruwanta! A cikin kayan miya wacece ita a lamarin Aliyu??" Aneesah dai sai ta6e baki take, can tace "Kinsan me Aunty tunda har kirana tayi ta min magana ki bari kawai inje kar ta saka ni a baki" Aunty tace "Ta saka 'ya yanta a baki dai ba ke ba wlh, kamar tana wani tabuka abun kirki a kan lamarin Aliyun da xata wani tsomo baki a wannan case din, ta ma ji da mugun abinda ke cinta kullum a xuciya mana da shiru shirun da take na algungumanci" Aneesah ta mike tace "Ko kayana ma baxan dauka ba Aunty xan dai tafi da turarrukan cikin hand bag" Aunty tace "Toh ya xancen xuwa asibitin gobe, ni fa dalilin da yasa nace baxa ki tafi yau din ba kenan" Aneesah tace "Sai in taho idan ya koma aiki gobe da safe, nasan da sassafe xai wuce kano ai, yawanci yanxu haka yake yi, ni bana son wancan matar tace nayi disrespecting dinta ne amma da sai in tsaya" Aunty ta ja tsaki ta xauna gefen gado tace "Dama goben ki xo da wuri, Kinga dai dai kenan kafin ya dawo wani weekend din anyi duk abinda xa ayi an wuce wajen" Aneesah ta saka hijab dinta ta xuba duk turarrukan a jaka sannan tayi ma Aunty sai da safe ta fita. Har suka isa gida Abuturrab bai ce ma Aneesah komai ba ita ma haka, banda danna wayarta babu abinda take, ta sauka motar ta bi bayansa xuwa cikin gidan, xaunawa parlor yyi yana kara regretting furnitures da aka xuba ma Aneesah a bangarensa, ko kallonsa bata yi ba ta haye sama ta wuce bangaren nasa, kwafa yyi ya mike ya haura sama ya bude dakin da su Hajja suka sauka ya shiga ciki, tsaf Hajja ta gyara dakin kafin su fita neman jiddah daxu da safe, don cewa tayi babu inda xata tafi bata gyara dakin ba haka kawai ta shiga hakkin tsafta, har bandaki sai da ta wanke, banda kamshi kuma babu abinda dakin yake, cire kayansa yayi ya shiga bandaki dake cikin dakin, bayan yayi wanka ya jima xaune dakin kafin ya sauka downstairs ya shiga kitchen, har sannan kitchen din fess tun gyaran da Jiddah tayi masa, ya dinga bin kitchen din da kallo kafin ya dau mug ya tafasa ruwan xafi ya hada shayi ya fito, a parlor ya sha shayin, yana ta xaune har kusan sha daya kafin ya mike ya wuce sama, babu yanda ya iya ya nufi bangarensa don daukar jallabiyarsa, Aneesah ce durkushe dakin hannunta rike da karamin towel tana goge turarrukan da suka fashe da sauri, har wani rawa hannunta yake, jakarta ta dauka xata ciro charger bata san a bude yake ba duk kayan ciki suka jirkice ciki har da turarrukan da aunty ta bata daxu wanda nan take biyu suka fashe wani kamshi ya gauraye dakin, tana ganinsa ta mike da sauri ta wuce bandaki da towel din, ya bi ta da kallo....


No comments

Powered by Blogger.