Jiddatul Khair 48
Lkci daya Abuturrab ya saketa ta dalilin hasken wuta da ya dawo kitchen din, ta rufe bakinta a rikice ta juya ta bude kofar kitchen din ta fice da gudu, Aneesah na tsaye parlor bayan ta kunna solan gidan, ta bi jiddah da kallon mamaki barin yanda taga ta rufe bakinta da hannu har ta wuce sama, can ta kalli kofar kitchen din, sai kuma ta tafi can da sauri ta tura kofar xata shiga suka kusa cin karo da Abuturrab xai fito, ya d'an buda ido kafin yace komai ya juya mata baya, walking toward the gas yace "Na xata kinyi bacci ai...." Daga sama har kasa ta dinga kallonsa, yana tsaye gaban gas din bai yarda ya juyo ba tace "Me kake yi a kitchen Captain?" Yace "Gyaran kitchen din da kika bari kaca kaca" Sai a sannan ta bi kitchen din da kallo taga sai walkiya yake, ko ina yayi fess, sake kallonsa tayi tace "Who just left the kitchen now?" Ya dau lighter kamar xai kunna gas din yace "The person that helped in transforming the kitchen back to it normal sef..." Tace "To wannan juya min bayan da kake na meye haka?" Wani boyayyen ajiyar xuciya ya sauke ya daga wayarsa da ya fara ring duk da Ahmad ne ke kiransa ya kai kunne still backing her, Aneesah ta gaji da tsayuwarta ganin ba gama wayar xai yi ba gashi yayi backing dinta ta juya ta fice daga kitchen din, sai a snn ya d'an waiga, ya dau mug ya bude flask ya xuba ruwan xafi ya saka Lipton, sannan ya dau lime din da yake siyowa a kitchen din ya yanka uku yayi squeezing a ruwan lipton din... Hajja ce tsaye kan Jiddah dake xaune kasan dakin ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, rai bace Hajja tace "Naga abinda ya fi karfina ni Dije, yanxu baxa ki bude baki ki gaya min me aka maki ba in san ta inda xan fara, matar gidan ce ta maki wani abun koko?" Jiddah taki dagowa hawaye sai sauka idonta yake duk jikinta yayi sanyi, Hajja bata sake ce mata komai ba ta juya ta fita daga dakin ta tafi can bangaren Abuturrab, da karfi ta kwankwasa kofar, Aneesah dake xaune saman kujera a parlon tana kokarin dialing number Aunty ta kalli kofar, jin an sake kwankwasa kofar kamar xa a cire ta mike a d'an fusace tace "Wai waye wannan" Tura kofar parlon Hajja tayi ta shigo ciki, tana huci tace "Ni dai kafin ince komai ina son sanin waye mai gidan nan tukun??" Aneesah tace "Haba dai.. ai ba girmanki bane shigowa wannan bangaren Hajja, duk abinda kike so da sai ki jira a fito....." Wani xagi Hajja ta mulmula mata tace "Ke har kin isa ki gaya min yanda xanyi a gidan jikana? Kaji min yar banxa, Ashe dama bayan bak'ar kazanta har da rashin kunya da fitsara kika iya ban sani ba? To wllh na fasa komawa wannan gantalallen Masar din dai tunda ba uban da na hada dasu, ina nan kasata Najeriya sai na nemo ma jikana auren tsaleliyar mata me bama tsafta hakkinsa, yar gayu me kamshi xan samar masa ba irinki kazama me wari ba, mata daga aure ko wata biyu ba ayi ba kin hallakar min gidan jika da kazanta ko ina banda tsutsa babu abinda yake fita, ko irin kamshin turaren nan na amare gidan nan bai samu gatan yi ba, to tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin mace kazama aminiyar dauda irin ki ba, amma duk ba wannan ya dameni ba, ya xan sa yarinya karama wanda kika kusa haifa ta tsaftace kitchen din da kika halaka yake fitar da tsutsa kuma ki saka min ita kuka babu gaira babu dalili??" Aneesah dai na tsaye sai kallon Hajja take baki bude with shock, Hajja tace "Ba kya kalleni kamar shashasha ba dama, wllh dole in nemar ma Aliyu mata me tsafta da son kamshi dai dai shi, ina ta kallonsa ganin ya d'an rame ashe kaxantar ki ne ke tsotse mana shi, to Allah ya isa wllh, mu kaf xuri'armu babu kazami...." A fusace Aneesah ta nufi kofa ta fice fuuuu, Hajja tace "Uwar kazaman Najeriya kawai, mata haka kazama na bugawa a jarida, dubi farin kafet din parlon nan fisabilillahi yanda ya fara fita hayyacinsa, parlon ma naji kamar karni yake wllh, ko da yake dai ba ruwana bari inyi shiru, ba abinda Usman ya aikoni inyi a gidan nan ba kenan, amma da yau kinji maganganu a kan kazantarki wllh" Aneesah na sauka downstairs ta tadda Abuturrab xaune ya gama shanye cup din Lipton da ya hada, tana shigowa parlon ta rushe masa da matsanancin kuka tace "Aliyu dama grandmum dinka xuwa tayi ta ci mun mutunci ta ci xarafina har gidana? Dama haka kuke ban sani ba?" Kallonta ya dinga yi don bai san me ya faru ba, sai ga Hajja tana sakkowa tana cewa "Wllh kinci albarkacin ba abinda Usman yace in xo inyi a gidan nan ba kenan, amma yau da na maki bankada iri iri, kuma gida muna nan babu yanda kika iya da mu tunda ba wani ya haifo min Usman din ba har Allah ya basa Aliyun" Da mamaki Abuturrab ke kallon Hajja yace "Me ya faru Hajja?" Tace "Me kuwa baxai faru ba Aliyu, daga na tura Jiddah ta farfado da kitchen din da ta fara hallakarwa kawai sai ta saka min ita kuka na rasa abinda tayi mata, yanxu haka yarinyar na can tana rusa kuka ta inda take shiga ba ta nan take fita ba kuma taki gaya min menene, da kyar fa Ramlah ta amince ta biyoni, yanxu in maida mata yarinya idanuwa a kumbure me kake tunanin xai biyo baya matar da ba mutunci gareta ba kowa ya san da haka..." Abuturrab ya d'an saci kallon Aneesah, lkci daya ta sake fashewa da kuka tace "Wllh baxan kwana gidanka ba yau Aliyu, ni ai bansan bayan duk hakurin xama da nake da kai a yanda kake akwai wani kalubalen dake tunkaroni ba...." Tana fadin haka ta wuce sama kamar xata tashi sama, Hajja tace "Oho dai Allah ya ishi Jiddah, kai kuma kayi ta istigifari don wnn ba karamin laifi ka aikata ma mahaliccinka ba ya jarabe ka da mata kazama, ni wllh kawai nayi shiru ne amma tun daxu da na shigo parlon nan naji yana wari" Tana fadin haka ta juya ta koma sama, Abuturrab ya d'an yi murmushi, shi dai ya ki tashi har sannan, Aneesah na komawa sama ta saka kayanta ta dau kaya kala biyu a karamin akwatinta ta dau hand bag ta yafe gyalenta ta fito, tana saukowa downstairs bata ko kalli Abuturrab ba ta nufi Kofa, ya bi ta da kallo yace "Ina xaki je Aneesah?" A mugun fusace tace "Wllh baxan kwana gidan nan da tsohuwar nan a ciki ba, baka ce min bayan hakurin da xanyi da kai har ita ma xanyi hakuri da ita ba, sannan ita wannan yar iskar mara asali da ta kawo min gida...." Dakatar da ita yayi yace "Tafi kije, Allah ya tsare" Bude baki tayi tana kallonsa, tace "Kace in tafi inje?" Fuska daure yace "Ehh, sai da safe" Kofa ta nufa fuu ta fice, ko kulle kofar bata yi ba ta nufi gate, ya mike ya karasa kofar ya kulle ya sa makulli. Hajja na komawa daki ta tadda Jiddah kwance ta takure waje daya, Hajja tace "Kiyi hakuri duk ni na ja maki don uwar rikon ki ma da kyar ta amince kika biyoni, ban san gidan er iska xa mu xo ba da ban fara xuwa da ke ba, amma kema wannan simi simin da kike baxai fissheki ba, gwara ki samu kiyi baki ki dinga kwatar kanki, naga kin cika wani sanyi kamar kankara, ai yanxu idan kace xaka yi sanyi sanyi a duniya kullum cikin cutarka ake, da kin gaggasa mata magana kin gaya mata irin kazantarta ai da ta kama kanta amma kin wani taho sama kina kuka kamar er yarinya, ni sai yanxu ma kika bani haushi wllh, da ba don Allah ya takaita aurenku da Aliyun ba ai kishiyarki fa xata xama, to a haka xa ki xauna kina mata kuka kullum??" Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, har sannan xuciyarta bugawa yake, scene din abinda Abuturrab yayi mata ya ki daina dawo mata, ganin abun yake kamar afresh, Cike da damuwa Hajja tace "To ko dai wani mugun abun ta maki naga duk a firgice kike wllh, ki gaya min gaskiyar me ta maki Jiddah" Jiddah ta lumshe ido ta bude a karo na farko ta bude baki a hankali tace "Bata min komai ba" Hajja tace "Oho dai ita da Allah ni dai na gaya mata duk abinda ya kamata ta sani" Tana fadin haka ta sake fita daga dakin, Jiddah ta ji hawaye ya kawo idonta ta kai hannu bakinta da take jin kamar bai cire nasa ba har sannan, ita idan ba a tv ba bata ta6a sanin ana haka a reality ba ma, hancinta ta kai kayanta jin kamshin turarensa ya cikata, ta wani turo baki ta mike ta fara cire kayan, sai da ta cire tas sannan ta saka hijab ta kwanta tayi lamo saman gadon, scene din da bata so na sake dawo mata kamar a lkcn yake faruwa. Aneesah na xaune parlon kawarta Chef Salma, Salma tace "Kan bala'i!!! to ai ni duk a xancen ki babu abinda ya tsaya min irin yarinyar da kika ce ta biyo kakar tasa... Ita yar kauyen da ya saka ce ake miki sintirin xuwa gidan ki da ita? Sannan kuma ta bi ki da sharri haka? To me hakan ke nufi?" Aneesah ta fyace majina da handki din hannunta tace "Ai shine nake jiran kiran stepmom din tasa, wllh ni rabona da su gaba daya tun xuwansu da rana da nayi shigewata parlonsa, ban ganta ba balle har wani abu ya hadani da ita, amma ban san me taje ta gaya ma makirar tsohuwar ba ta shigo har bangaren mijina tayi min wankin babban bargo ta ci min mutunci" Salma tace "To kuma ai kinyi wauta barin gidan da kika yi, bar masu gidan fa kika yi kenan" Aneesah ta fashe da kuka tace "Captain din fa ce min yayi in tafi sai da safe" Salma tace "Toh ai dadi kakar da ita tsinanniyar yarinyar xa su ji, ke dai wani lkcn idan kinyi wani abun kamar er fari, ke da gidanki kawai ki hado kaya ki bar masu, wato sun ma ci nasara a kanki, sannan karyar da ita yarinyar tayi ma kakar Captain din ya xama gaskiya kenan tunda har kika bar gidan" Aneesah tayi wani murmushi tana girgixa kafa, Salma ta ta6e baki tace "Wllh sakwa sakwan da kike ma wnn pilot din yayi yawa, sai kace shine autan maza? Shi yasa har ya iya budan baki ya maki maganar banxa, banda kilan suna da wani kudurin a ransu meye na xuwa da yarinyar da ya saka gidan tun tale tale? Me ya kawota bayan ga kanninsa da cousins dinsa da xasu iya rako tsohuwar, to wllh ki farka daga wnn slumber din naki kina da aiki ja a gaba, da kyar idan ba sake cusa masa me dankali da doyan xa su yi ba" Aneesah ta sakko da kafarta daga saman kujera da sauri alamar xancen ya gigitata tana kallon Salma, er dariya tayi tace "Ka ji ki da wani xance, to babu wani aure tsakaninsu sai in ta sake wani auren, ya mata saki sau uku kenan, daya a lkcn auren na farko farko, sannan suna tare ma ya saketa, sai na karshen da Abbansa ya umarcesa da ya saketa kuma ya saketa din" Salma tace "Ke wa ya gaya maki haka?" Ta gyara xama tace "Aunty, kuma Aunty Safara'u ma taje wani waje haka aka ce mata babu aure tsakaninsu har abada, don haka mu kwantar da hankalinmu, balle ma captain ba class dinta bane shi ma ya sha fada, me xai ci da ita?? yar hayin rigasa ce fa bama birnin hayi ba kauyen hayi, ko numfashinta baxai so ya shakka ba balle wani abu ya hadasu" Salma tace "To har naji hankalina ya kwanta maki, da kika ce babu auren, amma duk da haka sai kin taka burki a daina taho maki da ita gida gaskiya, ba fa dangin iya ba na baba" Aneesah tace "Ita kanta tsohuwar xuwanta na farko da na karshe kenan tayi idan anyi duniya don manzon Allah, wllh ko da kudi aka hadota ta taho gidan Aliyu baxata sake xuwa ba" Salma tace "Yauwa, haka nake son ji dama, ki tashi xaune daga kwancen da kike wllh... Yanxu kowa ta kansa yake duk inda kika ji ance aiki na kyau ki cire kyashin kudi kije" Aneesah ta jawo wayarta ta daga ganin Aunty ke kiranta ta kai kunne da sauri, kuka ta sakar mata, nan kuma ta bata labarin duk abinda ya faru, Aunty da ta kakance idonta tace "Kina nufin tare da shegiyar taje maki gida?" Aneesah tace "Wllh kuwa" Aunty tace "Toh ke banda shashanci meye na barin gidan, wato Hajjar taji dadi kenan ma kin bar masu gidan" Aneesah tace "Aa wllh Aunty ni baxan iya xama ba suna ci mun mutunci kuma babu abinda Aliyun yace, sannan da kansa yace in tafi" Aunty tace "Toh abinda xai faru yanxu ki dauko jakar taki ki taho nan gida, Abbansa na gari ai, maza ki taho yanzu, kuma wajen maida magana duk ki san abubuwan da xaki kara a xancen, ai in sun san wata basu san wata ba" Aneesah tace "Toh" Aunty tace "Wai ya ma baki wannan kudin kuwa?" Aneesah ta tabe baki tace "Ina fa, ce min yayi sai sabon wata da xa a shiga..." Aunty tace "Anya Aneesah kinyi amfani da maganin karshen da na baki a daren ku na farko kuwa?" Aneesah tace "Aunty sai dai na xo gidan, yanxu xan fito dama gidan Salmah na taho" Aunty tace "To na gane, taho gidan maxa yanxu" Driver Salmah ta saka ya kai Aneesah can gidansu Abuturrab. Har wajen karfe sha daya Abuturrab na xaune downstairs tare da Hajja da babu irin labarin Masar da bata masa ba, with much interest yake sauraronta yake biyeta duk da labarin ba dadi yake masa ba, ya gyara xama yana kallon agogo yace "To ai nan ma akwai turarruka masu kamshi ba can kadai ba" Hajja tace "Inaaa har yau banji turare me kamshi irin ta Masar ba, akwai wani turare da Usman ya bani wai dubu hamsin ya siya ni dai yana can na jefa cikin kwambodi.... to ba kamshi" Yace "Toh bari in dauko maki wani turarena yanxu ki ji kamshinsa ko ya kai na Masar din" Mikewa yayi yace "Ki jirani yanxu in dauko maki" Hajja tace "Toh yi maza, kaga idan kamshin ya min sai ka bar min kawai" Yace "Ba damuwa" Daga haka ya haura sama, gently ya murda kofar dakin ya bude, kwance take saman gadon ta rufe duk jikinta da hijab dinta idonta a lumshe, ya karasa cikin dakin ya kulle kofar, kallon switch din dakin yayi kafin ya nufeta walking slowly ya tsaya kusa da gadon yana kallonta, ya kalli kayanta da ta linke ta ajiye sannan ya kara kallonta, daga hijab din da ta lullube jikinta yyi yaga babu abinda ke jikinta sai undies, lkci daya ya sake hijab din ya juya ya fita dakin ya tafi bangarensa yana shiga bedroom dinsa ya kashe wutan dakin ya fada saman gado yayi rub da ciki. Hajja ta gaji da xama, ta sha gyangyadinta har ta gode Allah sannan ta mike wajen karfe daya ta wuce sama tana cewa "Gantalallen ba sai yace min bacci yake ji ba sai da safe, me hali dai baya fasa halinsa kawai..." Tana bude kofar daki taga Jiddah durkushe kusa da gado ta hade kanta da gadon, Hajja tace "Meye haka?" Ta dago da kyar tana kallonta ta girgixa mata kai, a fusace Hajja tace "To meye kika wani rungume gado kamar me nakuda?" Jiddah dai ta kasa ce mata komai, Hajja tace "A gaskiya da na sani baki biyoni ba, daga abun arxiki? Me ya sameki?" Jiddah ta kara girgixa mata kai kawai, Tabe baki Hajja tayi ta Kashe wutan dakin tace "Baxan iya da wahalanki ba bacci xanyi wllh, babu wanda xai shiga hakkin bacci na" Tana fadin haka ta kwanta daga kwanciya kuma sai minshari, Jiddah tayi ta juye juye... tun tana daurewa har ta kasa ta dinga hawaye tana yarfe hannu, rabonta da irin ciwon nan da take ji yanxu tun tana gun Babaarta, har karfe biyu Jiddah na durkushe yanda take, da ya lafa mata sai ya fara kuma... Shesshekarta ya farkar da Hajja, Hajja ta mike xaune sai kuma ta tashi ta kunna wutan dakin, xaro ido tayi ta kalli agogo ta kalli Jiddah sannan ta bude kofa ta fice, bangaren Aliyu ta nufa ta buga kofa, Abuturrab dake xaune saman kujera a parlon ya rike kansa ya juya da sauri yana kallon kofar, Hajja ta sake bugawa, xai mike daga kan kujeran yayi kicking ruwan Lipton din lemun tsami dake cup a ajiye daga kasa kusa da shi, lkci daya ya malale saman carpet din parlon, tsallakewa yyi ya nufi kofar ya bude, cikin tashin hankali Hajja tace "Aliyu awa uku kenan wancan yarinyar bata ko rintsa ba, sai kuka take na rasa me ke damunta, ni fa tsorona Allah tsorona tijaran da Ramlah xata min a kanta" Da mamaki yace "Me ya sameta?" Hajja tace "Ina xan sani Aliyu ko kwanciya taki yi, tana can duke kamar me nakuda nayi nayi ta gaya min meye taki" Abuturrab yace "Ina xuwa" Daga haka ya koma daki ya dau jallabiyarsa ya saka sannan ya fito, yana gaba Hajja na biye da shi suka isa dakin, Yana bude kofar dakin suka ganta durkushe kofar bandaki tana kwarara amai, Hajja tace "Na shiga uku ni Dije ta kashe bandakin, wani aman arxiki ne baxa ta shiga can ciki ba sae a bakin kofa?? Tirrrrr" Abuturrab ya karasa da sauri ya duka kusa da ita yace "What's wrong with u?" Ta kasa basa amsa ya dagata xuwa cikin bandakin, Hajja ta fice daga dakin hankali tashe tace "Baxan iya ba wllh, ko ni ya na kare da nawa aman balle na wani..." Abuturrab ya wanke mata fuskarta bayan ya xuba ruwa gun aman, xai cire mata Hijab din jikinta ta rike gam tana xaro ido amma taki yarda ta kallesa, hade rai yayi yace "Cire hannunki" Da kyar cikin kuka tace masa "Aa bana so wllh" lkci daya ya fixge hijab din a jikinta da karfi, ta turasa ta durkusa a kasa hankali a tashe tana cewa "Wayyo na shiga uku don girman Allah ka bani hijabina ka fita" Yana kallon ko ina na jikinta yace "Me yake damunki?" Duk a gigice take tace "Ai naji sauki" Yace "Saukin me" Taki yarda ta kallesa tace "Don girman Allah kayi hakuri ka fita" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tana kara rufe jikinta, shi dai kallonta kawai yake, can ya d'an shafa kansa ya ajiye mata hijab din saman washing machine ya juya ya fita bandakin, banda rawa babu abinda jikinta yake, tun da take bata ta6a ganin irin wannan iskanci ba, ko a gaban mace bata ta6a tsayawa a yanda take yanxu ba, gaba daya ta nemi ciwon cikin da take ta rasa, ta kalli jikinta ta kara takurewa waje daya xuciyarta na bugawa, ta fi minti biyar a haka kafin ta mike da sauri ta figi hijab dinta ta saka gabanta na faduwa, ta makale jikin kofa sannan ta leka dakin a hankali, ido hudu tayi da shi yana tsaye har lkcn a dakin, da karfi tayi banging kofar bandakin ta sa makulli, ganin haka ya shafa kansa ya juya ya fita, xaune yaga Hajja a corridor din ta shimfida darduma sai xuba gyangyadi take, yayi mata kallo daya ya wuce bangarensa, throughout daren nan Abuturrab bai rintsa ba, banda juye juye babu abinda yake, idan ya gajiya da kwanciyar saman gadon ya koma kujera a parlor, har aka kira sallah. Karfe takwas Jiddah ta lallaba ta saka kayanta da Hijab tana kallon Hajja dake kwance kan darduma tana bacci, ta dau jakarta ta nufi kofa a hankali ta bude ta fita, kallon direction din bangaren Abuturrab tayi kafin ta sauka downstairs da sauri, mai gadi ne ya bude mata gate ta fice fittt daga gidan....
Leave a Comment