Jiddatul Khair 45


 Abuturrab yyi parking kofar gidansu ya kashe motarsa ya sauka, suka gaisa da Mai gadi sannan ya shiga cikin gidan, bbu kowa parlon duk yan biki sun watse, ya wuce dakin Hajja ya bude kofar ganin Mahaifiyar El-Basheer xaune dakin ya sa shi yin sallama, Hajja dai kallo daya tayi masa ta ci gaba da xancenta tana cewa "Wllh baki ganta ba, babu sa wa babu hanawa, don dai kawai ni ina komai cikin sirri ne banda haka da har sunan yarinyar sai in fada maki ynxu, kuma ni ba abinda yasa na kara samun kwarin gwiwa sai ganin yanda Bashir din yayi na'am da xancen nawa, wllh ko musu d'an arxikin bai yi ba, da dai su o'o ne har ubana dake rami sai ya xaga, shi sa kika ga nayi ta ja baya da bikin nan ba ruwana aje a kunyata ma yarana ni a banxa, ai xamana Masar ya koya min iya xaman duniya, nasan yanda xan xauna da ko wani gantallale lafiya babu me jin kanmu" Murmushi kawai Hajiya Safinah mahaifiyar El-Basheer ke yi, Abuturrab ya karaso ya xauna kasa yace "Ina yini Mummy?" Da fara'arta tace "Lafiya lau Captain, yanxu muka dawo daga can gidan naka ai tare da Hajiya Hafsah, amaryar taka tace mana kaje kai kawayenta tasha ko?" Yace "Ehh" tace "Toh maa sha Allah, Allah ya bada xaman lafiya, ya kauda fitina tsakaninku" Yayi kasa da kai yace "Ameen" Sai a sannan ya kalli Hajja yace "Ina yini" Da sauri tace "Aa, ka dai gane ma idonka, lafiya lau na wuni wllh" Ya mata wani kallo ta gefen ido, Hajja tace "Kina ji na Safinah" Mummy tace "Ina ji Hajja" Tace "Kar ki dau maganata da wasa, tunda dai gobe xa ki koma kina isa gida, ko da mijinki na xaune fada ki yi sallama ki shiga kiyi masa duk bayanin nan da na maki, kinga ai tunda aka samu wannan mutumi yyi aure shi ma Bashir ya kamata yayi auren" Mummy tace "Haka ne Hajja" Hajja tace "Atoh, da a Masar ne ma wace shegiya xata kallesu duk sun tsofe a gida, mu fa a Masar sai ki ga d'an yaro shekara ashirin da biyu yayi aurensa gwanin ban sha'awa wllh" Mummy na gyada kai tace "Ikon Allah" Hajja tace "To ba ruwana wllh, idan xa ki dau maganata da muhimmanci ki dauka, ni anjima ma sai in sa a kira min waya in sa cikin dubara a turo yarinyar kamar dai xata kawo min sako sai ki ganta" Mummy tayi dariya tace "To ae Shikenan Hajja bari in je can bangaren Hajiya Hauwa" Hajja tace "Toh shkkn, xuwa nan da magariba xa ki ga an turo min yarinyar in sha Allah" Mummy dai na murmushi ta mike ta fita, Hajja ta kalli Abuturrab dake danna wayarsa tace "Har yanxu kuna can gwamutse da kawayen amaryar?" Yace "Toh ina ruwanki?" Yana fadin haka ya mike ya nufi kofa tace "Ji shashasha, to ni ina ruwana in ma shekara xa su yi a gidanka? Ba dai mun maka me wuyar mun aurar da kai sauran Bashir ba, sae kaje can ka karata da mummunar matarka sae haske kamar jinjirar xabiya, ni sai na ga wani kallon tara saura quarter ma take ma mutane kamar" Tuni Abuturrab ya fice daga dakin ya kulle mata kofa, wayarta ta dauka ta mike tace "Bari in je a kira min Ramlah, kawai ce mata xanyi ta xuba abinci ta ba yarinyar ta hadata da direba a kawo min kuma daga nan ina son ta wanke min bandaki, don duk ta fi sauran yan matan iyawa, kinga babu wanda xai xargi komai, daga nan tana xuwa sai in nuna ma Safinah" Tsaye Abuturrab yayi bakin kofa yana kallon Aunty, tace "Idan baxa ka karaso ciki ka kulle min kofa ba gwara ka fita don Allah Aliyu, bana son walakanci" Bai ce komai ba ya kulle kofar sannan ya karasa cikin dakin, tace "Yanxu kai abinda kayi jiya a tunaninka ya dace kenan Aliyu?" Yace "Aunty ni fa banyi komai ba, i instructed her to tell her frnds to come out so i can drop them home amma taki, ni kuma bana son tashin hankali kawai na bar masu gidan gaba daya na tafi hotel na kwana, a ina aka ta6a cewa sai kawayen amarya sun kwana gidan amarya ranan da aka kai ta?" Aunty ta jefa masa wani kallo tace "Ance din, ina ruwan ka da kawayenta dake daki daban ku kuna daki daban, yan matan da suka taso tun daga Abuja suka xo sun cancanci wannan walakancin a wajenka Aliyu? Tun da yan matan nan suka xo garin nan Hajja ke hantarar su, dalilin ma da yasa nace su kwana can din kenan, duka duka dai ai ba can xa su dauwama a gidan naka ba banda rashin hakuri irin naka, kuma banda ma kana son a tafi da matarka a baki meye na barin gidan?? wani ango ne ka ta6a jin yayi hakan" Abuturrab dai bai kuma ce mata komai ba, Aunty tace "Toh a gaskiya ka shiga hankalinka, kada in sake jin makamancin hakan, Aneesah dai ba abar rainawarka bace kasan daga irin gidan da ta fito kasan wacece ita, yar asali ce me dangi gabas da yamma kudu da arewa, kar kaga ka ta6a aure a gantale kun rabu a gantale, to ita wannan ba gantallaliya bace da danginta, yar usuli ce" Kallonta kawai Abuturrab yake babu ko kiftawa, Ta mike tana gyara daurin dankwalinta tace "Yanxu idan kaje sai kasan yanda xaka bata hakuri ta hakura, ni ma kuma dama na bata hakurin" Sauke hannunta tayi a fusace tana kallonsa tace "Wai ya haka ina magana ka kafe ni da ido kayi shiru kamar baka jin abinda nake cewa, are you okay??" Sauke idonsa yayi yace "Na ji ki" Daga haka ya juya ya fita daga dakin ta bi sa da wani irin kallo. Umma ta ajiye wayar hannunta tana kallon Aunty Nafisah da mamaki tace "Wai ki ji Hajja in ba Jiddah abinci tare da driver ta kai mata...." Aunty Nafisah tace "Ikon Allah, ba dai gidan xan tafi ba yanxu  sai in tafi mata da shi kawai" Umma tace "Kin ji yanda ta dage kuwa, na ma ce mata karatu jiddan take Maimoon su taho da drivern, amma wai Jiddar ta taho da takardun kawai" Aunty Nafisah tace "Ki bar Hajja kawai ana magariba xan tafi tare da abincin in kai mata" Umma tace "To amma ki kirata ki sanar mata dai tukun kar tace an mata ba dai dai ba, ko ya kika ga" Aunty Nafisah ta dau wayarta ta shiga kiran Hajja, Hajja na dagawa tace "Hajjaju yanxu xan bar gidan Hajiya Ramlah sai in taho maki da abincin...." Hajja ta katseta a fusace tace "Oh oh naga bala'i, ni dai na shiga uku, ita katuwar ce ta tsara maki haka Nafisah? Yanxu ke fisabilillahi tare dake muka xauna a Masar, ke kinga suna haka? Me yasa xaki taho kasar mutane ki ari halin da ba taki ba ki dinga yin abun da ba ayi a Masar? Ga dai abinda nace ina so sai ayi ta min hanya hanya? Ita Ramlan don bata san ciwona ba har da cewa xata ba direba shi kadai ya kawo min abincin da xan ci, me na hada da direban xa a basa abinda xan xuba a ciki ya kawo min, dama mutum na yarda ya ci gaibu? Toh shkkn babu damuwa, ni baxan sake ce maku komai ba" Daga haka ta katse wayarta, Umma dai sai murmushi take, Aunty Nafisah tace "Toh Allah ya kyauta, baxan ma koma gidan ba yau sai gobe, a ba Jiddar ta kai mata" Umma tace "To ai nace ki bari goben kika ki, ai shkkn bari in ba Jiddan ta kai, amma tana mika mata driver ya juyo da ita don tana da karatu gobe" Hijab har kasa Jiddah ta saka, tana rike da warmer din tuwo da miya da xata kai ma Hajja, gaba daya mood dinta ya canxa jin aiken da Umma tayi mata, babban damuwarta kar ta je ta hadu da Aunty, a sanyaye ta shiga bayan motar ta xauna har suka isa gidan bata da walwala, driver yayi parking kofar gida, ta sauka a hankali hannunta rike da warmer din ta shiga compound din gidan, a hankali ta bude kofar parlon tana leka ciki, ido hudu tayi da Abuturrab dake gidan har sannan suna xaune parlon da El-Basheer da ya takarkare yana masa labarin ball, ta karaso cikin parlon, El-Basheer ya juya yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi da ladabi tace "Ina yini" murmushi ya sakar mata yace "Lafiya lau Jiddah, how are you doing?" Tace "Alhmdlh" yace "Daga ina kike haka?" Tace "Gida" Yace "That's cool..." Bata ko kalli Abuturrab da ya bi ta da kallon gefen ido ba tayi hanyar dakin Hajja, shi ma El-Basheer din da kallo ya bi ta, da sallama ta bude kofar dakin Hajja, Hajja ta amsa ta washe baki ganinta tana cewa "Sannu da xuwa Jiddah" Aisha dake xaune dakin ta bi Jiddah da wani kallo, Jiddah ta tsugunna ta ajiye warmer din hannunta tana kallon Hajja tace "Ina yini Hajja?" Hajja tace "Lafiya lau, shinkafa ta baki ki kawo ko me?" Jiddah ta girgixa kai tace "Aa tuwo ne" Hajja tace "Atoh da kyau, dama shi nake marmari" Mikewa Aisha tayi ta fita daga dakin, Hajja tace "Dama ba wani amfani take min ba, yar kazar da Bashir ya kawo min take ma ni kuma na boye kayana karkashin gado, tunda ba uwarta bace ta siyo min, shi wan nata Salem tun saukana daga Masar har yau ban gansa ba ance yana Benue, to ni ina ruwana kuma" Ita dai Jiddah bata ce komai ba, Hajja tace "Yanxun nan Bashir din ya fita ai da kun gaisa wllh" Jiddah tace "Ai mun gaisa" Hajja tace "Haba" Gyada mata kai Jiddah tayi, Hajja tace "A ina kika gansa?" jiddah tace "A parlor" Hajja tayi kasa da murya tace "Shi da wa?" Jiddah tace "Ya Aliyu" Hajja ta wani kyabe baki tace "Ashe bai tafi ba kenan, in gaya maki ni dai babu xagin da bai min ba daxu, amma ban biyesa ba don ba shine gabana ba wllh, ni tunda naje Masar na koyi xama da ko wani fitsararre, iyakar hakuri da kauda kai na koyo kam ba laifi a Masar" Jiddah ta d'an yi murmushi kawai, Hajja tace "Toh ba ruwana dai da wannan, yanxu ki tashi ki tafi bangaren warcan matar da ku ke ce ma Ummi, kiyi sallama sai ki durkusa ki gaishesu da ladabi gaba daya sannan kice don Allah Maman Bauchi kike nema, Idan aka nuna maki ita aka ce gata sai kice mata dama Hajja ce tace in kira ki, Shkkn sai ki taso abun ki ki fito kinji?" Jiddah tace "Toh" Hajja tace "Toh tashi kije" Mikewa tayi ta fita dakin, suka hada ido da Abuturrab a parlor ta dauke kanta tayi hanyar bangaren Ummi, El-Basheer ya shafa kansa yace "Kasan mene Captain" Abuturrab ya kallesa yace "Idan magana ce da ya shafi koma waye na cikin gidan nan I'm not interested Yarima" El-Basheer yace "A kan Jiddah ne maganar" Mikewa Abuturrab yayi ya wuce dinning area, El-Basheer ya bi sa da kallo yana murmushi... Duk yanda Hajja tace haka Jiddah tayi, Ummi na murmushi ta nuna Mummy tace "Gata nan" Jiddah ta kalleta sannan ta sunkuyar da kanta, Mummy tace "Ki ce mata gani nan xuwa" Jiddah tace "Toh" sannan ta mike ta fita parlon, muryar Aunty ta ji a main parlor tana cewa "Har gashi xa ayi isha baka tafi ba ka bar yar mutane ita daya a gida Aliyu, Wai me yasa bakwa gaya masa gaskiya Bashir" El-Basheer yace "No nayi masa magana Aunty, har ce masa nayi ya tashi in rakasa yace aa yana jiran wani abu ne, ina ta xuba ido in ga me yake jira" Abuturrab na kallon Aunty daga dinning area da yake xaune yace "Yanxu xan wuce, dama gidan akwai wasu coursemates dinta ne amma nasan may be sun tafi yanxu, i will be on my way" Jiddah dai tayi sum sum ta shige dakin Hajja kafin Aunty ta ganta gabanta na faduwa. Tana shiga dakin Hajja ba a dau lkci ba sai ga Mummy ta shigo ta nemi waje ta xauna tana kallon Hajja tace "Ga ni" Hajja na Murmushi tace "Toh xancen da muka yi daxu dake dai da yamma... kin tuna?" Mummy ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Na tuna" Hajja tayi dariya tace "Toh shine, ai dama na maki alkawari xaki santa yau din nan" Mummy dai sai d'an Murmushi take tana kallon Jiddah dake xaune kasan carpet kasa kasa, Jiddah tace "Hajja ana jirana a waje" Hajja tace "Direba ko?" jiddah tace "Ehh" Hajja tace "To yi maxa tashi kije, kice da Ramlah na gode, Allah ya tashe mu lafiya" Jiddah ta mike tace "Ameen" Sallama tayi ma Mummy sannan ta fita dakin, Hajja tace "Toh ita ce dae Jiddar" Mummy tace "Maa sha Allah" Hajja tace "Aa ba haka xaki ce ba" Mummy tace "To ya xan ce" Hajja ta marairaice tace "Yau naga jaraba, sai kice ehh ai kuwa tayi Allah ya tabbatar da alkhairi Hajja, haka ake magana me ma'ana" Mummy tace "Gaskiya ne tayi kam, Allah ya tabbatar da alkhairi" Hajja tayi Murmushi tace "Yauwa ko ke fa, in sha Allahu satin da xa a shiga xan xo bauchi gun kabiru" Mummy tace "Toh Allah ya kai mu, bari in je Hajja" Daga haka ta mike ta fita dakin, Hajja ta ta6e baki tace "Oho dai, kya ji da bak'in halinki... In dai jikana na so bbu ruwana da sarautarku ta karya can, yanxu fa sai tace ita a dole gimbiya take so ya aura don ita tana jikar sarkin Gombe, to ni ba ruwana bama haka, kowa mutum me daraja ne a wajenmu, kuma nasan Kabiru da Bashir baxa su watsa min duwatsu a ido ba..." Sai da Jiddah ta fara xuwa tayi ma Ummi sallama sannan ta fito main parlor, har sannan Abuturrab na tare da El-Basheer, Tana kallon El-Basheer tace "Sai da safe" Yace "Ohkk ba nan xaki kwana ba dama" Tayi murmushi ta girgixa masa kai tace "Kawo ni aka yi" Abuturrab ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya mike ya fita daga parlon, El-Basheer yace "Driver kowa?" Ta gyada kai tace "Shi" El-Basheer yace "To mu je in rakaki" Bata ce komai ba ya mike suka fita parlon a tare, kofar gida suka tadda Abuturrab tsaye jikin motarsa, Jiddah na kallon El-Basheer tace "Nagode, sai da safe" Ya sakar mata murmushi yace "Aiitt, Allah ya tashe mu lfya" Bude back seat tayi ta shiga driver ya tada motar suka bar layin, El-Basheer na kallon Abuturrab yace "Ya ne, are you ready to go home now" Abuturrab yace "Yeah, Sai da safe" Daga haka ya shiga motarsa ya tada ya bar layin. Abuturrab na isa gida ya fi minti goma xaune cikin mota a parking space kafin ya sauka ya shiga cikin gidan, kulle kofar parlor yayi yana bin parlon da kallo, plates ne da suka ci cin cin, dubulan da su alkaki da frnds dinta da goran ruwa da lemo, ga bone din kaji a wani plate din a gefe, carpet din duk an marmasa cin cin da dubulan, haurawa sama yayi ya nufi bangarensa ya bude kofar parlon, nan ma dai ledojin souvenirs ne a tsakar parlon da souvenirs din a ciki, ya bude kofar bedroom dinsa, xaune ya ganta gaban mirror daure da towel tana ta shafe shafe, kamshin turare iri iri ya cika dakin, kallo daya tayi masa ta ci gaba da abinda take gently, yace "Aneesah what happened naga parlon downstairs so irritating sannan ga parlona duk wasu tarkacen ledoji, what's d meaning of that?" Tace "Ohh xan xo in kwashe souvenirs din but downstairs gaskiya sai gobe cause har yanxu jikina da gajiya sosai, baka ji bayana ba sai ciwo yake min wllh, I'm so stressed out" Calmly yace "No Aneesah, but u can't leave my parlor that way, I won't sleeo comfortable, ban sa6a ganin haka ba, Kuma ban ta6a kwana a haka ba" Tace "Captain ba wai fa nace baxanyi bane, xanyi amma gaskiya sai gobe, haba duk gajiyan bikin nan dake tare dani ka tsiro min aiki kuma da daddaren nan" Juyawa yayi ya fice daga dakin ya sauka downstairs, ya wuce kitchen ya dau sweeper da abun kwasar shara ya dawo parlon, sai da ya fara tattara duk plates din da robobin lemo ya kai kitchen sannan ya dawo ya share carpet din tass, ya kai ya xubar... Xaunawa yyi a parlon for kusan minti ashirin kafin daga karshe ya mike ya kashe wutan parlon ya wuce sama, har sannan ledojin souvenirs din na nan yanda ya barsu, ya kwashesu gaba daya ya bude kofar balcony dake parlon ya watsar da su nan ya tabbatar babu komai xaune parlornsa bayan furnitures sannan ya kulle kofar balcony din ya wuce daki, a gaban madubin ya sameta still, dakin sai wani fitinannen kamshi yake, ta saka wasu tsinanannun kayan bacci, yyi mata kallo daya ya fara cire shirt dinsa ya wuce bandaki. Daure da towel ya fito, yana goge gashin kansa da karamin towel din a hannunsa, Aneesah ta bi sa da kallo sae kuma ta mike ta nufesa ta rungumesa ta kwanta bayansa kamar me rada tace "In maka shafan cream din ne?" Ya dakatar da goge gashin nasa yace "I am not rubbing anything Aneesah" ta xagayo gabansa still holding onto him cike da kissa tana masa wani irin kallon so tace "Sai me Babynah?" Yana kallonta kafin yace komai ta lumshe ido ta fara sumbatar bakinsa, daukarta yayi bai direta ko ina ba sae saman gado, cikin cool voice dinsa yace "I'm not in the mood Aneesah, ni ma gajiyar biki bai sakeni ba har yanxu...." yana fadin haka ya lakaci hancinta ya mike daga kan gadon ya tafi ya dau pajamas dinsa ya fara sakawa, Aneesah ta bi sa da kallon mamaki har sannan tana kwance, can side din gadon ya tafi ya xauna bayan ya saka pajamas dinsa, ya juya ya kalleta yace "I need hot tea" Ta masa wani kallo ta mike tace "Baxan iya ba..." tana fadin haka ta fice daga dakin, a parlor ta dau wayarta ta fita ta koma wani daki ta kulle ta shiga kiran Aunty, Aunty na dagawa tace "Lafiya Aneesah????" Cikin rawar murya tace "Aunty wllh fa kawai walakanci Aliyu ke ji, kinga yau ma ba shi da niyya" Aunty ta bude baki tace "Ke kuma sae kace ba mace ba Aneesah, ae sae abun ya lalace ya gantale idan ya wuce yau" Aneesah ta marairaice tace "Toh ni ya xan yi masa Aunty, ji fa kudin da mutum ya kashe ma" Aunty tace "Xuwa xakiyi kiyi duk yanda xaki yi komai ya kankama, koma meye kiyi ni dai, sae da safe ni ba a bangarena nake ba" Daga haka Aunty ta katse wayar, Aneesah ta fi minti uku tsaye tana naxari sannan tayi wani murmushi ta fita dakin ta nufi bangarensa.


No comments

Powered by Blogger.