Jiddatul Khair 42


Jin yanda take kuka Abuturrab yayi kasa da murya still holding onto her yace "Gaya min abinda aka maki kike kuka...." Ganin ba amsa xata basa ba sai shessheka take, ya rufe idonsa ya bude cikin tsawa yace "Ya isa haka nan" kokarin kwatar kanta ta fara yi da karfi amma ta kasa... hakan yasa tayi lamo jikinsa tana kukan a hankali, gaba daya scent dinsa ya cikata, hannunsa taji a idonta ya goge mata hawayen sannan ya bude mota xai shigar da ita ta fara turjewa, ya d'an hade rai yace "Baxa ki shiga ba??" turasa tayi da duk strength dinta bata ankara ba kawai taji ya dauketa kamar ya dau yar shekara biyar, ta hadiye kukan da take tana xaro ido tace "Na shiga uku, meye haka..." Cikin motar ya shigar da ita ya xaunar ta kamo hannunsa tana sake fashewa da kuka hankali tashe tace "Don girman Allah kayi hakuri kar ka sake kulleni a nan, ina hada ka da Allah kayi hakuri...." Ya daure fuska yace "To rufe min baki" Hadiye kukan tayi da sauri ta rufe bakinta tana gyada masa kai, don har ranta take tsoron kada ya sake kulleta cikin motar, sai da ya ga tayi shiru snn ya shiga bayan motar shi ma ya kulle yana kallonta, ta sunkuyar da kanta yana kallon yanda kirjinta ke sama da kasa, yace "Yanxu tun daga gida kika taho a haka babu mayafi?" Ita dai bata ce komai ba xuciyarta na bugawa, a fusace yace "Tambayarki nake" Ta jawo jakarta a hankali tana nuna masa tace "Yana ciki" Yace "Amma ke baki ji kunyan tahowa a hakan ba maxa na kallonki a hanya?" ita dai bata ce komai ba, gaba daya a tsorace take fatan ta kawai kar ya sake kulleta cikin mota yayi tafiyarsa, yace "Tambayarki nake..." ta marairaice tace "Ai a mota muka taho, ni ba wanda ya gan ni" Yace "Wa ya kawo ku a motar?" Tsoron ce masa Yousuf take bata san dalili ba, yace "Baxa ki bani amsa ba?" Ganin yanda take kallon kirjinsa ya sunkuyar da kansa yana kallo shi ma, da sauri ta dauke kanta, xaro ido yyi ganin yanda farin rigarsa ya bace da powder da janbaki, ya kalleta yace "Kinga abinda kika min ko??" Ta kallesa tayi narai narai da ido tace "Kayi hakuri" Ya d'an hade rai yace "Inyi hakuri? Sai in ce ma matata me idan ta gani?" Ta kallesa amma bata ce komai ba, handkerchief ya ciro aljihunsa ya mika mata yace "Maida min rigata yanda take" Tana kallon handkerchief din tace "Xai goge kuma?" Yace "Oho" karba tayi ta fara goge shaddar a hankali, ya jinginar da kansa jikin motar yana kallonta babu ko kiftawa, ita dai taga sai kara bajewa powdern yake, bata san lkcn da wani dariya ya taho mata ba ta rufe bakinta da sauri ya dinga kallonta, ta marairaice tace "Allah baxai fita ba" Yace "Ba ruwana" Bata kuma cewa komai ba tana ta gurje wajen da handki din hannunta tana kuma jin yanda xuciyarsa ke bugawa, daga kai tayi a hankali suka hada ido, fuxgota yyi ta kusa fadawa jikinsa cikin husky voice dinsa yace "Daga yau kika sake fita da gyale xan sa6a maki, sannan karatu kike yi yanxu babu ruwanki da ko wani namiji ko waye shi" wayarsa ne ya fara vibrate a aljihunsa ya saketa ya ciro yana duba screen din wayar, lkci daya ya bude motar ya sauka ta bi sa da ido kafin ya rufe ta riko hannunsa da sauri cikin rawar murya tace "Don girman Allah kar ka sake kulleni" kulle motar yayi ya xaga ya bude driver seat ya shiga, sai a sannan taji hankalinta ya kwanta... Har suka iso gida bai ce mata komai ba, can nesa da gate din gidansu yayi parking, kashe mota yyi ya juyo yana kallonta cikin duhun motar yace "Dama kar ki kuskura ki ambato ni idan aka tambayeki daga inda kike" ita dai bata ce komai ba sai kallonsa take, yace "Fito da mayafinki" A hankali ta bude zip din jakarta ta ciro mayafinta, yace "Sauka" Bude motar tayi ta sauka ya bi ta da kallo har ta isa gate ta shiga cikin gidan, Umma ce ke kokarin fitowa parlor da wata kawar Ummi da Aunty Nafisah, Umma na ganinta tace "Daga ina kike Jiddah?" Jiddah da gabanta ya fadi tace "Umma ni ban ga su Maimoon ba kuma baxan gane gida ba" Umma tace "Wa ya dawo da ke yanxu?" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Ya Aliyu" Da mamaki Umma tace "Aliyu?? A ina kika ga Aliyu kuma?" Cikin sanyin murya tace "Aa kawai nagansa ne ya koma can wajen shine muka hadu ya taho da ni gida" ita kanta Aunty Nafisah kallon mamaki take ma Jiddah, Umma dai ta juya bata ce komai ba ta koma ciki, Kawar Ummi ta bi bayanta, Aunty Nafisah tace "Toh shigo" A sanyaye Jiddah ta shiga parlon, babu kowa parlon sai few guess da yaransu, Aunty Nafisah ta wuce dakin Hajja, ita kuma ta wuce dakin da ta san su Maimoon suke, Tana shiga dakin Maimoon ta mike da sauri tace "Jiddah ina kika je, ko wajen dinner ban ganki ba" Jiddah ta cire gyalen jikinta ta ajiye jakar hannunta tace "Toh ai baki nemeni ba" bandaki ta wuce don yin alwala... Washegari tun asuba aka tashi gidan aka fara girke girken breakfast, su Maimoon da su Jiddah kuma duk aka hadasu da gyaran gida, Safiyya da Nafisah parlorn gidan suke gyarawa, Tun da Jiddah taga sun gama gyaran part din Ummi xa su na Aunty taji hankalinta ya tashi, tana kallon Maimoon tace "Ko dai inje in dinga gyara dakin Hajja don mu yi sauri" Maimoon tace "Aa wllh muje mu gyara na Aunty tare, Na hajjan ma muyi tare" Jiddah bata kuma cewa komai ba ta bi bayan Maimoon xuwa part din Aunty, yawanci duk yan uwan Aneesah ne a parlonta, Aneesah da kawayenta kuma na can bedroom dinta, Jiddah ta gaishe da manyan da ta gani a parlor suka wani amsa da kyar kamar dai sun santa, Maimoon dama bedroom ta wuce direct bata ko kallesu ba Jiddah ta bi bayanta, Aneesah da kawayenta suka daga kai suna kallonsu, Maimoon tace "Xa mu yi gyaran daki" wani kallo Aneesah tayi masu daga sama har kasa tace "Da mutane a ciki xa ku yi gyaran?" Maimoon tace "Atoh saka mu aka yi mu ma ai" Aneesah tace "Toh sai ku koma kuje kuce ma duk wanda ya aiko ku da akwai mutane a ciki" Jiddah dai bata ce komai ba tana tsaye, Maimoon ta wani ta6e baki tace "Toh mutane" Daga haka ta juya tayi ficewarta daga dakin, Jiddah suka hada ido da Aneesah da ta wani murtuke fuska kamar ta ga mugun abu, juyawa Jiddah tayi ta fita daga dakin ita ma, kawar Aneesah Naja tace "Wai wacece wnn da tsohuwar can na jiya ta dage sai mai make up dinki ta mata make up, sannan sai in ga tana ta wani shan kamshi tana daga kai ko kanwar Captain din ce ita ma" Aneesah ta jefa mata wani kallo tace "Kanwar Captain? Tab... Amma kin so neman magana, wa ya bata matsayin kanwarsa? Ke baki ga yanda take dari dari ba kice wani daga kai da shan kamshi, ai karere ce ita a gidan Awara da doya fa take soyawa a hayin rigasa inda train station yake, cin arxiki fa take kawai a gidan, ya talakawa ce nan ku ke gani mara galihu" Naja tace "Ke Aneesah, wllh na xata yar gidan ce yanda na ga an dage sai me kwalliyanki tayi mata" Aneesah ta ja wani dogon tsaki tace "Ni ki bar ma xancen raina baci yake wllh" Fauziyya tace "Toh Allah ya kyauta, nima dai ban xata karere bace a gidan, kuma na ganta fara kamar dai..." A fusace Aneesah tace "Don Allah ku bar xancen nan haka nan, nace maku yar Hayi ce, doya da dankali take siyarwa, kuma yar talakawa ce" tana fadin haka ta mike ta shige bandaki. Bayan azahar Jiddah ta fito sanye da Hijab dinta har kasa ta dalilin kiran da Yousuf yyi mata ta wayar Maimoon, yana tsaye jikin motarsa ta karasa gun motar da ladabi tace "Ina yini?" Yace "When did u leave the event center yesterday?" Tace "Ni ban duba agogo ba" Yace "Na kira Maimoon tace baku tare, where were u?" A hankali tace "Ba waje daya muka xauna ba" Yace "Toh wa ya dawo da ke gida" D'an murmushi tayi tace "Masu dawo da jama'a gida mana" Da ido suka bi motar da ya wuce su, motar yayi parking d'an gaba da nasu, Ahmad ne ya sauko sannan El-Basheer, Abuturrab ya bude back seat ya sauka shi ma, kallo daya yyi ma Jiddah ya nufi gate, El-Basheer ma ya bi bayansa, Ahmad ya karasa ya mika ma Yousuf hannu yana murmushi bayan sun gaisa yace "Ba mu ganka wajen Dinner dinmu ba jiya" Yousuf yace "Yeah naje amma ban dade ba" Ahmad yace "To madallah" sallama suka yi Ahmad ya shiga gidan, Yousuf ya jingina da mota yace "Guys din gidan nan i think suna da karancin ilimin mu'amalah da mutane" Jiddah ta kallesa kawai tayi murmushi yace "Yahhh, that pilot... i don't know but i wont call him an introvert, kawai dai bai san mutuncin d'an Adam bane, and i guess shi ma farin d'an uwansa ne ko?" Jiddah tace "Ehh" yace "Bird of the same feathers" Jiddah dai bata ce masa komai ba, Yousuf yace "Yaushe xaku koma gida da su Umma?" Jiddah tace "Kilan idan an kai amarya da yamma" Yace "Toh Allah ya kai mu, xa mu yi waya with Maimoon's phone" ta gyada masa kai kawai, yace "Take care Jiddah" Ta yi murmushi tace "Nagode" daga haka ya xaga xuwa driver seat ita kuma ta shiga cikin gidan, dakin Hajja ta nufa don dama aiki take mata Yousuf ya kira, tana shiga dakin Hajja dake xuba ma su Ahmad abinci ta daga kai tana kallonta tace "Toh wai saurayinki ne ya xo halan, naji shiru shiru" Jiddah ta nufi kayan da take linke mata don ta karasa, Hajja ta kalli Maimoon dake dakin tace "Halan dai saurayinta ne?" Maimoon tayi dariya tace "Ehh" Hajja tace "Atoh shi kuma baya gaida mutane ne, ai da sai ya shigo ya gaishemu yayi mana Allah ya sanya alkhairi haka ake yi" Jiddah ta ci gaba da linkinta, Hajja ta gama xuba abincin ta mike tace "Toh a kai masu can dakin, idan ba ni ba babu wanda xai masu haka, kowa na ta kansa a gidan" Maimoon ta mike ba tare da ta tsaya gyara plates din abincin kai ba ta dau tray din sai ga plate daya ya rikito kasa, Hajja ta amshe tray din da sauri tace "Je ki Allah ya isa" Wani kallo Maimoon tayi mata tace "Toh na sani ne?" Hajja tace "Nace maki wani abu ne, cewa nayi kije ke da Allah kawai" Maimoon ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, Hajja tace "Algunguma kawai, wllh da gangan ta kifar, dama bata yi niyyar xuwa ba, yar mummuna da ita kawai, uban me na hada da ita banda dai uwarta kanwar matar d'a na ne, gayyar tsiya kawai, da a Masar ne dama babu wani dangantaka tsakanina da ita nan ne dai komai sai anyi karere" Ita dai Jiddah linkinta kawai take, Hajja ta sake xuba wani shinkafar tana ta mita, har ta gama sannan ta kalli Jiddah tace "Ki dauka ke ki kai masu, nima na so raina ya baci ne, banda haka ga ki, er arxiki irin albarka" Jiddah ta ajiye xanin hannunta ta karasa ta durkusa a hankali ta dau tray din ta nufi kofa, sai a sannan ta juya tace "A ina xan kai masu?" Hajja tace "Suna can parlon Usman" Jiddah ta fita dakin ta kama hanyar parlon Abba, sai da ta fara ajiye tray din ta murda kofar a hankali hade da sallama sannan ta dau tray din ta shiga ciki, waya na kare kunnen Abuturrab yana magana, El-Basheer kuma na xaune saman kujera idonsa a kan phone dinsa, karasawa ciki tayi ta ajiye tray din tana kallonsu tace "Ina yini" El-Basheer na kallonta da murmushi yace "How are u?" Tace "Lafiya lau" Daga haka ta mike ta nufi kofa El-Basheer yace "Who were u speaking with outside Jiddah" ta juyo tace "Yaya Yousuf ne" El-Basheer yace "Who is he?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Family frnd din su Yaya Ahmad" El-Basheer bai kuma cewa komai ba, ta d'an kalli Abuturrab taga yanda ya sha kunu, juyawa tayi ta fice daga parlon. Bayan la'asar aka fara shirye shiryen kai amarya, gidan cike yake dam da jama'a yan kai amarya, motoci sun fi ashirin a compound da kofar gida duk na yan kai amarya, wajen Hajja aka fara kai Aneesah dake sanye da alkyabba fuskarta a rufe, aka xaunar da ita saman carpet Hajja na daga xaune kan tabarma ta daura kafa daya kan daya, tana kallon Aneesah tace "Ni dai bani da abinda xance, amma da a Masar ne kawai ce maki xa ayi ki bi yan uwansa da iyayensa sau da kafa, to sai ki ji dadin xama da shi, duk abinda yake so shine abun sonki.... Kinga dai shi me yan uwane barkatai kuma duk baxa su ki xuwa gidansa ba don haka kika iya allonki ki wanke, ko ni nan duk sanda na ga dama xanje gidansa tunda ni na haifi ubansa kuma a hannuna ya taso daga bisanni ya fita waje koyon tukin jirgin sama..." Aunty dake tsaye daga bakin kofa sai hararan Hajja take kamar ta kifa mata Mari, Aneesah dai sai satan mutanen dake dakin take da kallo duk da fuskarta a rufe yake, Jiddah ta gani xaune gefen gado rike da jakar da Hajja ta bata, ganin kallonta Jiddah ke ta yi ta wani tsuke fuska kamar tana ganinta, ita dai har ranta taji ta tsani jiddah, bata ta6a jin tsanar mutum yanda take ma Jiddah ba, she just hate her with passion, Hajja ta gama surutanta mara tushe aka daga Aneesah dake ta kallon Jiddah har lkcn, aka fitar da ita daga dakin, next aka kai ta gun Ummi, Ummi ma tayi mata duk nasihar da ya kamata, Umma ta daura da nata, daga karshe aka kai ta gun Abba da Uncles din Abuturrab, sai wajen hudu da rabi aka kai amarya mota, Hajja ta saka ma kofarta makulli ta mika ma Jiddah tace "Jefa min a jaka sai Allah ya mana dawowa kuma, mu xa mu kai ta" Saurayin Safiyya ne ya tafi da su Maimoon da Jiddah da safiyyar sai Nafisah gidan Abuturrab, tun da yayi parking out side gate Jiddah ke kallon gidan, kamar bata ra6a rayuwa a gidan nan ba, kofar gidan cike yake da motocin kawo amarya, Maimoon da su Jiddah suka samu suka shiga compound din, Jiddah dai na biye da su a baya har suka shiga parlon, taji gabanta ya fadi, komai na parlon an sauyasa xuwa sabo, jama'a ne cike parlon ana ta gud'a, Maimoon ta ja su Jiddah suka wuce sama, dakin da Jiddah ta xauna ta bude taga few mutane a ciki, kayan dakin ma duk an canza suka fito suka bude sauran dakunan da duk aka xuba ma furnitures, duk da Abuturrab ya sanar ma Aneesah ta gaya ma iyayenta ba a bangarensa xa a xuba mata furnitures din daki ba, taki sanar masu, can kuma suka kai kayan dakinta, Jiddah dai sai kallon parlon Abuturrab take, har sannan hotonsa na kayan pilot na parlon, ta rasa me yasa memory ke ta dawo mata, ba karamin kudi iyayen Aneesah suka kashe mata na kayan daki ba, don duk dakuna hudun dake gidan sun xuba kaya, can karshen gado ta xauna fuskarta a lullube Jiddah dai kallo daya tayi mata ta fita daga dakin ta bar su Maimoon a can ta koma downstairs ta xauna a parlor tana bin ko ina da kallo. Sai kusan karfe shidda aka fara watsewa daga gidan amarya shi ma Hajja ce ta fara sallaman mutane su tafi kada a 6ata ma yarinya gida, gidan ya rage daga Umma, Aunty, Aunty Nafisah da frnds din Ummi, sai wasu family, Jiddah dai sai jiran lkcn da Hajja xata tafi ta bi ta take don taga alamar su Maimoon basu da niyyar tafiya don har Saurayin Safiyya ya wuce, tana ta xaune parlor har magrib hakan yasa ta mike ta shiga bandakin dake parlor tayi alwala ta fito tayi sallah, bayan ta idar ta tafi sama ta bude dakin da take tunanin su Maimoon ke ciki xaune ta gansu suna ta hira, Tace "Wai baxa mu tafi gida bane?" Nafisah tace "Aa mu dai kila ma a nan xa mu kwana" Xaro ido Jiddah tayi, can tace "Toh ga jakar Hajja ni xan tafi" Maimoon tace "Toh wa xai maida ki gidan?" Jiddah tace "Akwai dari biyar din Umma a jakana xan yi amfani da shi" daga haka ta fita, xata sauko downstairs suka kusa cin karo da Aunty sake haurowa sama rike da abinci, sosai gabanta ya fadi ta koma gefe da sauri, Aunty ta kalli downstairs taga babu kowa parlon, fuska murtuke tace "Uban me kika taho yi gidan nan ke kuma?" Jiddah dai ta kasa cewa komai gabanta na faduwa, Aunty tace "To don ubanki sauka ki kama hanyar ki, ke a wa xaki biyo yan kawo amarya, munafuka kawai mayya, nace ke a wa??" Jiddah ta fara sauka a sanyaye, hankadeta Aunty tayi har sai da ta kusa faduwa, cike da tsanarta tace "Maxa fita, ke da gidan nan ai sai dai hange daga nesa" Jiddah bata ce komai ba ta sauka da sauri ta nufi kofa ta fita compound din gaba daya, duk jikinta yayi sanyi, slowly take tafiya a dogon layin wanda ko wani gida da fitilu farare da ya haska layin kamar rana, mota ne ya dallareta ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da tafiya a hankali, reverse taga motar na yi yana komawa baya, ta kalli motar don bata ta6a ganin irinsa ba, lkci daya aka sauke glass din motar, ta dinga kallonsa, murmushi ya sakar mata yace "Hi...." Ta fara wasa da hijab din jikinta ta sake satan kallonsa, bude motar taga yyi ya sauka ya xagayo ta inda take yace "Assalamu alaikum" amsawa tayi a hankali, yace "Sorry na tsayar dake a layi ko?" Tace "Um" yace "Kin ganeni kuwa" ta sake kallonsa, d'an murmushi kawai tayi bata ce komai ba, Yace "Ina xa ki da daddaren nan?" Tace "Gida" da mamaki yace "Ba can bane gidan ku dama" ta kalli gidan Abuturrab da yake nuna mata, sai kuma ta girgixa kai tace "Aa, gidan yayanmu ne" Ya wara manyan idanuwansa yace "Ohh, shi yasa na daina ganinki kenan" murmushi tayi masa nan ma, yace "Toh mu je in ajiye ki gidan naku ynxu" Tace "Aa ai ban sanka ba" Yace "Really? Duk sanin da kika min a balcony?" Murmushi tayi tana kallonsa, ya bude mata front seat yana kallonta, sauke idonta tayi ta shiga motar ya kulle sannan ya xaga ya shiga driver seat, reverse yayi suka bar layin yace "Ya sunanki?" A hankali tace "Jiddah" As if counting his words yace "Jeedderh!!" Ta kallesa ya sakar mata murmushi wanda har sai da dimple dinsa ya lotsa ya kai fuskarsa dab da ita yace "I am Ali" 


No comments

Powered by Blogger.