Jiddatul Khair 4
4......
Jiddah ce xaune kusa da Abbanta dake kwance tsakar gida saman tabarma da wani pillow da ya yakune, hawan jininsa ne ya tashi tun daren jiya, magunguna ne ajiye daga gefensa wanda da kudin da take tarawa wajen Iyah ta samu ta siyo masa magungunan, ko bi ta kan inda ta samo
maganin Hansai dake ta yankan dafaffen awaranta bata yi ba, Sosai Abban nata ke jin jiki shi yasa duk hankalinta ya tashi, Hansai dai sai ta6e baki take, lkci lkci kuma tayi tsaki har ta gama abinda take yi ta mike tace "Yau ai sai ki xuba ruwa kasa ki sha tunda baxaki siyar min da awara ba kin wani makale kusa dashi wai bai da lafiya, to a duniyar nan yanxu wake da lafiya? Kowa ba lallaba kansa kawai yake yi ba, idan ka xauna ka fake da ciwo ai sai yunwa ta kar ka, ko da yake shi kwanciyar tasa ma da rashinta duk daya ai, Atoh duk daya mana tunda mace ce ke rike da gidan" Daga haka ta daura roban fentin dafaffen awaranta a kai da jarkan man gyada tace "Idan kinga dama in Bibalo ta dawo kice ta sameni bakin titi, tun safe ni ko ganin gilmawarta ban yi ba ko ina taje oho" kofa ta nufa da xaninta da yyi dukundukun xata fita, Jiddah ta goge hawayen dake makale idonta tana kallon Abbanta a hankali tace "Sannu Abba...." Bai iya yace mata komai ba, Hansai ta saka kai xata fita suka kusa cin karo da Iyah, Hansai ta koma baya tana washe baki tace "Sannu da xuwa Iyah" Iyah tace "Yauwa Hansatu, ya me jiki naji ance Isuhu bai ji dadi ba" Hansatu tace "Wllh da sauki kuwa, ga magungunan da na siya masa can ma, to ko kwayan hatsi bamu da shi a gidan shine nace Jiddah ta xauna tare da shi in fita in siyar da awaran nan, ba wata me yawa bace ta dubu uku ce kawai don dai a samu na cin abincin yau da gobe, kinga ai ba a xauna dukka ana jinya ba" Iyah tace "Gaskiya ne, Allah dai ya rufa asiri, yi maxa yamman ma tayi, Allah ya bada sa'a" Hansai tace "Ameen" Daga haka ta fita gidan, Iyah ta karasa ta dau kujeran tsugunno ta xauna tace "Sannu Isuhu" Da kyar ya gyada mata kai, Iyah ta rike ha6a tace "Farin mutum bafillatani duk ya kode kamar bai ta6a haske a rayuwarsa ba, Allah dai ya baka lafiya ya rabaka da cutan nan" Nan ma dai ya gyada mata kai, Iyah ta kalli Jiddah tace "Ya sha magungunan kuwa?" Jiddah ta gyada mata kai, Iyah tace "Toh Allah ya yaye masa" A hankali Jiddah tace "Ameen" Iyah ta bi d'an kuturun tsakar gidan wanda hansai ta mayar kamar na mahaukata da tarkacenta da kallo snn ta ta6e baki ta maida dubanta kansa tace "Amma kana ji na Isuhu" shi dai kallonta kawai yake yana numfashi da kyar, tace "Don muhammadurrasulillahi S.A.W.... ba a dai san gawan fari ba amma ka dubi Allah ka gaya ma wnn yarinya Jiddah inda dangin uwarta suke taje ta nemo su a fadin duniyar nan" Ya sauke numfashi da kyar muryarsa baya fita sosai yace "Iyah Mahaifiyar Hauwa 'yar Nijar ce...." Iyah tace "Kullum xancen ka kenan Mahaifiyarta yar Nijar ce, to a Nijar din bata da dangi ne Isuhu?" Ya sauke wani numfashin yace "Ni dai kowa yasan ni maraya ne ina almajiranci Uban gidana Alhaji Auwal ya daukeni ya rike kamar d'an sa sbda duk safiya xan wanke masa mota in share masa tsakar gida har ma in je masa aike, ni ban san garinsu Amina mahaifiyar Jiddah ba a Nijar din, ni dai tace min su 'yan Nijar ne, rana daya uwarta ta daukota suka dawo Nigeria wanda babu tantama kurciya aka mata, ko da suka dawo Nigeria basu walakanta ba don wata Hajiya ta amshe su hannu bibbiyu kakar Jiddah na masu aiki...." Iyah tace "To kai duk a ina kasan wannan labarin da ka kunshe ma cikin ka isuhu?" Yace "Mahaifiyar Jiddah ta bani labarin" Iyah tace "Toh ina ji" a hankali yace "A haka har Allah yayi haduwata da Mahaifiyar jiddah ranan naje kasuwa mai dakin uban gidana ta aikeni, ita kuma Jiddah Mahaifiyar ta aiketa, ban wani sha wahalan samun Mahaifiyar Jiddah ba sbda uban gidana ne ya tsaya min kan komai, a gidan da muka xauna wanda uban gidana ya kama mana haya a lkcn, muka hadu da Hansatu tana xuwa gun kanwar Mahaifiyarta, suka shaku sosai da Amina Mahaifiyar Jiddah duk da ko a lokacin Hansatu xata yi Shekara kusan talatin da wani abu amma bata ta6a aure ba, a lkcn kuma aurenmu ko shekara bai yi ba da Aminatu, ni dai nasan watarana na dawo daga kasuwa Amina ta sani gaba ai sai na auri Hansatu sun xauna tare yau Hansatu ta 6ata labarinta da irin tsananin da ake mata a gida duk don bata samu mijin aure ba kuma taji tausayinta sosai, wllh wllh Auren Hansatu kaddara ce daga Allah amma Amina ce sila, ta takurani, hatta iyayen gidana basu amince da auren ba a sannan, amma sbda son da nake ma Aminatu bana kuma son bacin ranta na lallabasu sai dai sun nuna min babu ruwansu a batun auren kuma babu biyar dinsu a auren, yawanci xannuwan da nayi ma Hansatu na lefe ma xannuwan Aminatu ce ta bani, kinji dalilin auren Hansatu, ni baxan ce sun yi xaman tashin hankali ba gaskiya don ko hakan ya faru Amina bata ta6a nuna min ba don har yau ban ga mace me hakurin Amina a duniya ba duk da xaman mu bai yi nisa ba don ta haifi Jiddah da shekara daya ta rasu, a lkcn Hansatu na da cikin Bibalo kin ji yanda rikon Jiddah ya koma gun Hansatu tun ba a yayeta ba, Uban gidana ya so Jiddah ta dawo wajensu bayan rasuwar Mahaifiyarta amma Hansatu ta saka mana kuka xa a rabata da jiddah, ita a bar mata ita xata raineta kamar yanda xata raini Habiba su taso tare, hatta Mahaifiyar Amina ta so amsan Jiddah bayan rasuwar 'yar ta, Amma Hansatu ta bi ta da dadin baki taki bata, ashe ita ma ba mai tsawon rai bace, don bayan rasuwan Amina da shekara uku ita ma ta rasu...." Jiddah dai kallon Abban nata kawai take don bai ta6a bata labarin nan ba sai yau, ta dai sha jin mutane na cewa Hansatu ba baabarta bace amma bata yrda sbda ita ta taso ta gani, Iyah sai girgixa kai take tana cewa "Allah me girma, ashe dai Hansatu baxata wanye lafiya da duniya ba... wuhuhu, Allahu akbar, To su iyayen gidan naka suna ina suka bar ka ka walakanta ka gantale haka, ai ko ba komai nasan sun ci moriyarka dai ba adadi" lkci daya Hawaye ya kawo idonsa yace "Hansatu ce dae ta rabamu, Alhaji Auwal ya bani kudi miliyan 2 in kai masa banki ban samu xuwa bankin a ranan ba sbda ruwan da aka yi kamar da bakin kwarya ina tsoron bin hanya da kudi haka, sae na dawo gida da kudin, Hansatu ta xare dubu dari biyu a ciki, kudi ko sama ko kasa, sbda Alhaji Auwal din yace bai yrda ba bayan na sanar masa 6atan kudin da naga bani da mafita, shine matar nan taje har gida ta ci masu mutunci ba na wasa ba, basu yi mata komai ba amma shine har yau, kudi kuma yace ya yafe min ya dai amshi sauran kudinsa, to kinji abinda ya faru... Wnn gidan ma da muke ciki ai shi ya siya min wllh, yau shekara bakwai kenan da ya bar kaduna suna Abuja da iyalansa" Iyah tayi tagumi tace "Yau naga tsinanniyar mata, dama ance ita ta talauta ka da ba haka kake ba, ilai ga magana ta fito...." Yace "Duk ta bi ta siyar min da filayena biyu da gonata daya, da wnn gidan kadai na tsira...." jiddah ta goge hawayen dake makale idonta duk jikinta yyi sanyi, Iyah tace "In sha Allahu xa mu ga karshenta kuwa, abinda Allah baya bacci, ynxu damuwata inda wnn yarinya jiddah xata samo danginta, to gidan da kakarta tayi aikatau a ina yake?" Yace "Wnn ai sun fi shekara sha biyar da barin kaduna, idan ko ba barin kaduna suka yi ba to sun sauya wani gidan ne don xuwana biyu duk akan haka amma aka sanar min sun tashi" Iyah tace "Abu ya lalace kuwa, banda haka ai baxata rasa basu labarin kanta da garinsu ba, kaga da ko su sai suyi ma jiddah hanyar xuwa dangin uwarta ita ma ta dawo mutum, amma ina mutum a nan ba dangi" girgixa kai kawai yyi, Iyah tace "Toh Allah ya rufa asiri, xaka ci tuwon masara da miyar kubewa in tafi in yi maka yanxu?" Jiddah tace "Xai ci iyah, tun safe bai ci komai ba sae kunu da ya sha" Mikewa Iyah tayi tace "Toh bari in je in hura gawayi yanxu ina da komai a gida, yanxun nan xan gama, to ae mayyar ba wani damuwa da rayuwarsa tayi ba, ehh Hansatu ba" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta ta ido har ta fita, murya can kasa yace "Kiyi ta hakuri kin ji Jiddah, wataran sai labari, nasan ban ta6a cutan wani tsawon rayuwata ba, ina fatan Allah ya dubi hakan, albarkacin hakan kada ya bari ki walakanta, Allah ya yanke maki wnn wahala da kike sha cikin gaggawa yayi maki abinda yafi alkhairi a rayuwarki, ina maki addu'an Allah ya baki hakuri da juriya da kauda kai irin na Mahaifiyarki Amina, kar ki kaga ana maki abubuwa ina shiru Jiddah, har gobe bani da kamar ki a duniya jiddah tun bayan rasuwar mahaifiyarki, Ban yi shiru a kan batun aurenki da wannan takadirin yaron da take ba, don har yanxu ban furta komai ba hakan ba yana nufin na aminta da auren bane, idan anyi duniya domin manzon Allah xaki auri mijin da xai kula dake yayi maki abubuwan da mu muka kasa maki, xaki auri wanda xai rike ki bisa gaskiya, wanda xai yanke maki wannan wahala da kike ciki in sha Allah" Hawaye ya shiga sakko mata ta kasa ce ma Abban nata komai, amma taji hankalinta ya kwanta sosai, da kyar ya ci gaba "In sha Allahu wannan takadirin ba mijin ki bane Jiddah..." ta gyada masa kai tana gyara masa kwanciyar kansa, ya lumshe ido yace "Tashi ki je kiyi wanke wanken da ta sa ki kar ta dawo kin ji" Ta goge idonta cikin sanyin murya tace "To Abbana Allah ya baka lafiya" Yace "Ameen Jiddah" Mikewa tayi ta tafi gun uban kwanukan da Hansai ta tula bakin kwararo k'uda sai fareti suke a kai, sbda yawan kwanukan sai kusan la'asar ta gama ta mike ta dau buta ta xuba ruwa jin ana kiran sllh ta ajiye inda Abbanta ke alwala ta koma kusa da shi ta durkusa tace "Abba ka daure ka tashi kayi alwala" Jin yyi shiru ta kai hannu jikinsa tace "Abba la'asar yyi...." hannunsa taga ya xamo kasa daga jikinsa, ta kamo hannun tace "Abba...." Shiru bai amsa ba, komin bacci ko rashin lafiya shi din ba me nauyin bacci bane, hakan yasa ta sake kiransa nan ma shiru, jijjigasa tayi taga dayan hannun ma ya xame, bata san lkcn da ta kwala wani ihu da karfi ba kan kace me mutane suka shigo gidan da sauri jikinta na rawa tace "Ku taimakeni Abbana yaki tashi" Wani makocinsu wanda har da shi ya shigo ya kai hannu jikinsa lkci daya ya saki salati yace "Isuhu ai rai yyi halinsa" Daga wnn Jiddah bata sake jin komai ba ta dai bude ido ta ganta kwance saman tabarma dare yyi ga mutane cike tsakar gidan. Bayan kwana uku, Jiddah na xaune tsakar gida da idonta da yyi bulu bulu ga wani rama da tayi don har sannan bata iya cin komai, Hansai sai faman yankan awara take tana cewa "Ke kadai aka ma mutuwa idan ba munafurci ba, Ita Bibalo ba ubanta ne ya rasu ba halan, munafuka kawai me neman suna, kin taso kin fita da kayan awara bakin titi ko sai na taso na nakada maki shegen duka, idan bamu yi awara ba yau ubanki xa mu kwakulo a kabari mu ci?" Hawaye kawai Jiddah take ta mike ta dau kaskon awara da coal pot da wasu kananun kayan ta fita xuwa bakin titi, Hansai tace "Ni wllh idan ba binsa kabarin kika yi ba bansan kina yi ba, bayan mutuwan da yyi ya bar ni da wahalan yi maki kayan aure duk da dai katifa da robobin kitchen kadai Allah xai hore min inyi maki, to ince me wnn wahalan da ya bar ni da shi, ina ta sintirin xuwa gidan Saude xaman makoki miji ya rasu ashe nima nawa na kan hanya xai tafi ya bar ni da wahala, to banda dai dama ya gaji da duniyar daga tashin hawan jini sai mutuwa Allah na tuba, shi dai yaji da munafurcinsa kawai dama ya gaji da duniyar ne, to ba dai ya mutun ba dai ai shkkn, yanxu ga aurenki dake ta karatowa ya gudu ya bar ni da wahala" A haka jiddah ta dawo ta sameta tana ta kumfar baki ta dau robon awaran ta fita, har sannan jiddah taki dawowa dai dai, gani take kamar mafarki take xata farka taga Abbanta bai rasu ba, har yau da aka yi uku abincin kirki ta kasa ci, don ma Iyah na tsareta sai ta sha kunu, banda tsine ma Hansai babu abinda yan anguwan ke yi ganin Jiddah bakin titi tana tuyan awara, daga mutuwar miji da kwana uku har ta ci gaba da awaranta wnn wani irin xuciya gareta, yawanci duk Jiddah ake tausayi don shkkn ta xama marainiya gaba da baya yanxu.... Abuturrab na kallon Ramlah dake yankan ma Umma Fruits yace "Umma ta ci abinci kuwa?" Ramlah tace "Aa bata wani ci ba, Amma Aunty Zainab taje gida xata yi mata tuwo yanxu" Ummi dake xaune kan farin kujera a ward din tace "Ga farfesun hanta ma da nayi mata bata ci ba" Abuturrab ya kalli Umma dake kwance da drip a hannunta yace "Umma ko a siyo maki awara?" Ta d'an yi shiru kafin a hankali tace "Toh Allah ya sa in iya ci, bana jin dadin komai a bakina" Ummi tace "Toh wannan ai dole ne Ramlah... Kawai daurewa xaki yi kici ko kadan sai kiji jikin ya maki kwari" Abuturrab yace "Toh bari in je in siyo maki yanxu" Daga haka ya fita, Slowly yake driving din har ya karasa hayi, dai dai u turn din wajen ya juya ya nemi waje yyi parking yana kallonta ta glass din motar, kanta a kasa tana juya awaran cikin man kaskon a hankali, ya sauke glass din motar yace "Ki bani awaran dari biyar" Dago kai tayi tana kallonsa, kallon idanuwanta da suka kumbura yyi, bata ce komai ba ta saka masa awaran yanda yace snn ta mike ta isa gun motar tana mika masa ledan, bai amsa ba yace "Kukan me kika yi haka??" Ta sauke idonta kasa, lkci daya xuciyarta yayi mata rauni wasu sabbin hawayen suka cika idonta, da mamaki yake kallonta, bata san lkcn da ta fashe da kuka sosai ba tace "Abbana ne ya rasu" Daga nan kuma kamar warce aka tunxura ta jingina da motar ta dinga rera masa kuka, a hankali underneath his breathe yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Kuka kawai take so painfully, ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya bude motar ya sakko ya xagayo yace "Yaushe ya rasu?" Cikin kuka sosai tace "Yau aka yi uku" Da mamaki yace "Shine kika fito suyan wannan abun" Cikin rauni tace "Baabarmu ce tace sai na fito" Dauke kansa yyi, can yace "Awaran na nawa ne gaba daya?" Ta juya ta kalli roban awaran cikin shessheka tace, wai na dubu biyar tace min" Ya girgixa kai bai ce komai ba, can ya juya ya bude motarsa, kudin da ya ciro xa ayi masa delivering eye glasses da yyi ordering online ya dauko a motar, kamar wanda ya tuna wani abu ya fasa fito da kudin a haka sai da ya saka a wani ledan turare snn ya juyo yana kallonta, har sannan kuka take sosai, ya mika mata ledan kudin yace "Gashi ki kai mata kice ance kada ki sake fitowa sai an kwana biyu" Kallon ledan ta dinga yi da yyi mata dishi dishi sbda hawayen idonta ya kamo hannunta ya mika mata ledan ya amshi ledan awaran ya saka a mota yace "Allah ya gafarta masa" daga haka ya xaga ya shiga motarsa ya tada ya bar wajen, share hawayen idonta tayi ta leka ledan taga dari biyar sababbi dal a rafe, sosai gabanta ya fadi, ta kasa kwakkwaran motsi, wani almajiri ne yace "Awaran ki na konewa" Da sauri ta juya ta sauke awaran, ta xauna xuciyarta na bugawa da karfi, muryar Hansai taji a bayanta, Hansai ta ajiye bokitin wani awaran tana cewa "Ta dari biyar ce wnn, gaba daya ya kama dubu biyar da dari biyar...." ganin awara ya kone a mai tayi tsit tana xare ido, lkci daya ta saki salati da karfi tace "Na shiga uku awaran kika kona min Jiddah???" A mugun tsorace Jiddah ta mika mata ledan kudin tace "Baabarmu wllh wani ne ya xo ya kawo min wnn wai in kai maki kar mu sake fitowa sai bayan kwana biyu...." Hansai ta karbi ledan tana duba ciki da sauri, xaro ido tayi tana kallon tulin kudin cikin ledan, lkci daya ta dinga bin anguwan da kallo, murya can kasa tace "Daga ina yake?" Jiddah ta buda hannu har sannan jikinta na rawa tace "Wllh ban sani ba" Hansai tace "Dauko jarkar man da roban awaran mu wuce gida ai ya kare ma" A haka Jiddah ta kwashi kayan awaran ta bi bayan Hansai dake tafiya da sauri da sauri, A bakin kofar dakin Hansai Jiddah ta makale tana kallonta tana ta faman kirgan kudi duk ta hada xufa, har ta gama kirgen tana xaro ido tace "Dubu dari a wannan marran ni Hansatu, Allah yyi ma bawan Allahn nan albarka, yanda ya taimaki marayu Allah ya taimakesa haka shi ma, kaiii a duniyar nan ma dai xaman wasu toshe hanyar alkhairi kawai yake, banda haka daga rasuwan Isuhu kamar daga sama Allah ya jefo bawan Allah ya bamu dubu dari cif cif, yaushe rabon inga dubu ashirin da idona ni Hansatu" Jiddah dai ta sunkuyar da kanta xuciyarta na mata xafi bata ce komai ba, Hansai tace "Maxa ki sa ruwa kiyi wanka kema ko kya ji dadin jikin ki, kinga dai mutuwar nan alkhairi ne garemu sai kiga Allah yyi ta bude mana hanyoyi iri iri, aa ni dai wllh gwara da ya bamu hanya mu san me muke ciki a duniyar, to da ya baki kudin sai yace maki me?" Cikin sanyin murya tace "Yace kar in sake fitowa sae bayan kwana biyu" Hansai ta fashe da kuka tace "To dama banda talauci me xai sa mijina ya mutu in fara awara a ranan da aka yi sadakan uku, ai sai dai talaucin dama" Ta kara rushewa da kuka tana matsar kwalla da bakin xaninta, juyawa jiddah tayi a hankali ta bar bakin kofar tana dada jin mutuwar mahaifinta kamar a mafarki wanda hakan yasa hawaye kawowa idonta.
Leave a Comment