Jiddatul Khair 39
Shirye shirye kawai ake babu kama kafar yaro a gidansu Abuturrab kasancewar kwana uku kacal ya rage daurin aurensa da Aneesah, kai kana ganin wannan shirin da ake kasan ba karamin biki xa ayi ba na first child of the family, tuni Umma ta dawo gidan da yan matan ta har da Huraira mai aikinta, yan uwa da abokan arxiki kuwa duk sun fara tahowa daga garurruka daban daban, Kamar yanda Aunty ta sanar ma yar uwarta godiya haka tayi a wannan period din, don sosai ta kwantar da kanta komai sai dai taje ta samu Umma taji yanda xa ayi, duk kuma yanda aka ce bata musu, har hakan ya ba Umma mamaki hatta idan wani shawara tayi da Abba sai taje ta tattago Umma ta xo taji ko shawaran yayi, ganin haka Umma ta sake gaba daya don da farko ko sakar mata fuska ta ki yi, ashe hakan ba karamin kona ma Hajja dake ta lura da su rai yake ba, ranan laraba wanda ya rage saura kwana biyu daurin aure Umma ta shigo dakin Hajja rike da babban cooler din soyayyan nama xata ajiye Hajja tace "Meye haka?? Aa ba ruwana da tarkace Ramlah, fita da shi gaskiya ki kai dakin Hafsah tunda naga dai ku ke aurar da yaro ke da ita" Umma ta tsaya tana kallonta, Hajja ta ci gaba da kakka6e gadonta fuska daure tace "Haka kawai kya shigo min da wani katon rubabben cooler daki kamar wata rubabbiyar tsohuwa, a ina xan sa shi? Kinga da ruwana da sha'anin bikin ku ne, ba dai kawai nasan ni na haifi uban Aliyun ba" Umma ta juya ta fita da naman, Hajja ta bi ta da wani shegen kallo tace "Idan ba gulma ba sai ki kama Hafsah ki rike hannu bibbiyu kuna abu gaban kanku bakwa sako kowa, in dai Hafsah ce ni nasan tana da wani mugun kudurin a ranta ne... Ahaf mu je dai xuwa, ni dai ba Allah ya so 'ya ta na hanya gobe ba, duk ita xan sa kan komai na bikin nan ai tafi ku kusanci da Aliyun tunda kanwar ubansa ce ita, sannan matan Kabiru duk suna hanya su ma gobe kwa sha mamaki ke da Hafsar, idan ma barbadensu na yan garin Benue tayi ta baki mu dai mun fi karfinta sai dai ke din da yayarki tunda naga ba a tsaye kuke ba" Tun da Jiddah suka xo gidan ko kallon inda take Aunty bata yi balle har tayi abinda xai sa ta 6ata likimon da tayi ma kowa, Jiddah ma bata yarda hanya ta hadasu, da ta ga Aunty a waje take barin wajen, duk Aunty na lura da hakan, sai dai tayi kwafa a hankali tayi murmushi, ita dai babban damuwarta yanxu a daura auren nan ran friday Aneesah ta xama mallakin Abuturrab tukun, yawanci Jiddah na gun Hajja tun xuwansu, don Hajja bata sa kowa aiki sai ita, a dakinta ma take kwana, da taga bata ji motsinta ba xa ta sa a kira mata ita ko a nemota, sauran yan matan kuma dama ta ce babu abinda ya hadata da su sun ma rainata. Washegari Thursday da safe Jiddah da Nafisa kanwar Abuturrab da ke boarding suna sharan parlor kamar yanda Umma ta saka su, Maimoon kuma na goge goge aka bude kofar parlon, duk suka daga kai El-Basheer ne ya fara shigowa sannan Abuturrab dake biye da shi a baya, Jiddah dai ta ci gaba da sharan da take, Nafisa ta gaida El-Basheer cike da murnan ganinsa yace "Ashe kin girma da yawa Feenah" Rungume Abuturrab tayi tace "Yaya sannunku da xuwa" Ya ja hancinta yace "Yaushe kika dawo" Tace "Tun ran Tuesday fa yaya" yace "To ya karatu?" Tace "Alhmdlh" Maimoon ta gaida El-Basheer ya amsa mata with smile, sannan ta gaida Abuturrab ya amsa a takaice, Jiddah ta dago tana kallonsu tace "Ina kwanan ku" El-Basheer yace "Lafiya lau, ya kike?" Tace "Lafiya lau" Dama Abuturrab bai amsa ba banda wayarsa da ya hau dannawa, Jiddah ta ci gaba da sharanta, kallon El-Basheer Abuturrab yayi ganin yanda yake kallon Jiddar, ya maida wayarsa aljihu ya nufi dakin Hajja, El-Basheer ya kallesa sannan ya maida dubansa gun Jiddah yace "Are you Asthmatic?" Ta daga kai ta kallesa amma bata ce komai ba, Maimoon tace "Aa bata da Asthma" yace "Ohk" daga haka ya bi bayan Abuturrab xuwa dakin Hajja. Hajja na ganin El-Basheer tace "Kai ma kaje kayi ma kanka fada Bashir, ba wai ka dinga yawo kana bin sabbin angwaye xalo xalo a baya ba, da ka san ciwon kanka yanxu ba cewa xaka yi a hadaku da wannan mutumi Aliyu ba, balle duka duka da watanni nawa ya girmeka? Amma ka tsaya shashanci kai a dole d'an sarki, to ko ni da nake uwar sarki bana abinda kake yi wllh" El-Basheer yace "Toh kin samar min matar ne nace maki bana so Hajja? Ni na xata Masar da kika je xaki samo min mata daga can fa" Ta marairaice tace "Wllh nayi niyya Bashir, Nafisah ce ta hanani wai su ba a haka a can, toh kaga kuwa ai sai inyi shiru in koma gefe tunda idan na botsare masu suka maido ni Najeriya sai inyi yaya, amma yanxu tunda har ka bani wuka da nama idan Allah ya yarda baxan baka kunya ba, yanxun ma na fara maka sha'awar wata yarinya wllh, baka ganta ba kyakkyawa doguwa jazur da ita kamar balarabiya, da ta bude min gashinta kuwa sai da na gigice, ga ladabi da biyayya sannan bata da kiwiya, komai aka sata yi take cikin dadin rai ga shegen hakuri, ai ni tuni na fara maka sha'awarta sai gashi ashe kai ma ni kake jira" El-Basheer yace "Toh fah, a ina kika samo min ita Hajja" Hajja tace "Sakin wawa ce..." Abuturrab dake danna wayarsa ya daga kai ya kalli Hajja, El-Basheer yayi dariya yace "Sakin wawa kuma Hajja, bazawara kika samo min kenan?" Hajja tace "ka ji ka da wani xance Bashir, wllh babu wanda xai ce ta ta6a aure, yarinya ce fa yar karama bata wuce Nafisah kanwar mutumin nan dake xaune ba, kuma ai ni na samu labarin wannan auren da tayi ba aure bane don babu abinda ya ta6a shiga tsakaninta da mijin, a gantale aka yi auren kuma a gantale aka yi sakin, yar yarinya ce karama fa nake gaya maka wllh, sannan kakan Aliyu nima ai a bazawarar ya aureni tunda sai da na auri kakanka aka haifi Kabiru da Aisha sannan kishiyoyi suka fiddani, Allah ya hadani da kakan Aliyu ya aureni sannan na haifi su Usman da Nafisah" Shi dai El-Basheer murmushi kawai yake yace "Toh shkkn ai ni nasan baxa ki min xabin da xai cutar da ni ba Hajjaju" Hajja tace "Haba haba ai na cuci kaina kenan idan na cuceka, in sha Allahu xabi ne har xabi na maka, kar ka ji komai a ranka, bari dai mu gama da bikin wannan mutumin tukun" Abuturrab dai bai daina kallon Hajja ba, El-Basheer yace "Toh baxa mu samu ko d'an ruwan shayi ba, ni yunwa nake ji fa" Hajja tace "Kaji ka, ai magana xaka yi, har abincin ma akwai naga sun dafa idan kuna so a xubo maku" El-Basheer yace "Aa shayin dai, bamu yi breakfast ba" Hajja ta mike tace "Toh bari in sa a kawo maku" Fita tayi dakin xuwa parlor, har sannan su Jiddah na parlor, Hajja tace "Yar nan ajiye masu sharan su ki xo in sa ki aiki kinji" Jiddah ta ajiye broom din hannunta ta karaso gun Hajja, Hajja tace "Xuwa xaki yi kitchen ki wanke hannu da kyau, don baya son kazanta Bashir, bayan kin wanke hannunki ki dau babban faranti da naga suke fafa da shi a gidan nan ki daura masa flask da cokali da kopi daya sannan ki ajiye kayan shayi a gefe, to shi kuma dayan mutumin ban san ko xai sha ba don ko gaisheni ma bai yi ba, amma dai baxa a biye ta halinsa ba, shi ma ki dora masa kofi da cokali daya mu mayar masa da aniyarsa, ki tabbatar duk ki dauraye kofunan don kinsan sarakan tsafta ne su, kuma duk a wajena suka gado, bayan nan idan akwai burodi ki daura kan tray din duk ki kawo masu" Jiddah tace "Toh" sannan ta juya ta wuce kitchen, Hajja ta koma daki tace "Toh ba shikenan ba bakina alekum, da wannan gantalallun 'ya yan na saka sai in samu me xagina ma tunda ba isasshen tarbiya garesu ba" Jiddah tayi duk yanda Hajja ta ce mata, tray biyu tayi ta daura kayan shayin da bread din a daya, dayan kuma ta daura cups da spoon sai flask din a kai, na flask din da cup ta fara dauka ta fito kitchen din suka kusa cin karo da Aunty ta koma gefe da sauri, Aunty ta hade rai ta ja gefe, Jiddah ta sunkuyar da kai ta bi gefe ta fita don tun sassafe ta gaisheta bata amsa mata ba, Jiddah na shiga dakin Hajja, Hajja ta mike ta shimfida rug da sauri tana cewa "Yauwa yar albarka, sannu kin ji, taho ki ajiye" Jiddah ta sunkuya ta ajiye tray din tace xanje in dauko dayan, Hajja tace "Toh yi maxa" Shi dai El-Basheer kallonta kawai yake, ta juya ta fita, Hajja tace "Wllh ba sawa ba hanawa, tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin nutsattsiya me tarbiya irin wannan yarinyar ba, gashi bata fushi ko kadan yanda ka san ni ce ina karama" El-Basheer yyi murmushi yana shafa kansa yace "Toh ko dai canje xaki min da sakin wawan da kika ce" Hajja tace "Aa kai dai kayi shiru kawai ka kyaleni yanda ka gan ni, ban fiye son surutu ba gaira ba dalili ba...." Abuturrab kallon wayar hannunsa kawai yake amma babu abinda yake da wayar, Jiddah ta dawo da tray din kayan shayin ta ajiye, Hajja tace "Yauwa er albarka, sannu" Sai kuma ta kalli El-Basheer tace "Ko ta soya maka kwai, naga ta iya, jiya da uwar rikonta ta sa ta soya mata naga tayi sa da kyau snn bbu karni ga albasa ta yankasa rimi rimi a kai abun zar sha'awa, ni dai har Ramlah ta gama cin kwan nan banji karni ba" El-Basheer yace "Aa ba sai na bata wahala ba ta bari kawai" Hajja tace "O'o Allah ina ruwanka da wannan batun, kai dai ba a soya maka kwai ba ka hada da burodi ka ci, da tana da son jikinta ai baxan ma fara sa ta ba, kaga na bi ta kan yaran gidan nan" Jiddah ta kalli El-Basheer tace "Xan iya" Yace "Toh je ki soya" kofa ta nufa ta fita, Hajja ta kalli El-Basheer murya can kasa tace "Ga tsafta kamar tsatsonmu wllh, ko kai baka gani ba?" Shafa kansa kawai yake yana murmushi, tace "To ni dai ba ruwana, kawai a barni yanda aka gan ni ba banxa nake ba" Bayan kusan minti goma jiddah ta dawo da kwai rufe a plate da fork biyu a kai ta dora, ta sunkuya ta ajiye plate din kan carpet, Hajja tace "Allah yayi maki albarka kinji" Jiddah tayi murmushi ta mike suka hada ido da Abuturrab da ya dago kansa, sunkuyar da kai tayi ta nufi kofa ta fita, El-Basheer ya sauko ya fara hada shayin yana kallon Abuturrab yace "Hey dude come let breakfast" Abuturrab ya mike yace "Alhmdlh" Daga haka ya nufi kofa ya fice. Da yamma Jiddah na dakin Hajja ita da Nafeesah, El-Basheer ya shigo da sallama yace "Hajja xa mu je dauko su Maman Farida" Hajja ta washe baki tace "Ehh wllh yanxu mijin ya kirani wai sun sauka ashe" yace "Toh dama xance maki sai gobe ne, don ni daga can baxan dawo ba" Hajja ta xare ido tace "Saboda mene?" Yace "Aliyu xai karaso da su ni xan sauka gida in huta ne" Hajja tace "Aa ba ruwana ba haka Kabiru yace min ba, bai ce min xaka sauka a wani waje ba nan ba, nan din ba gidanku bane, sannan ba ga dakin Aliyu ba idan ma bak'in hali Aliyun ke maka ba ga dakin wancan yaron da ya gantale ba Salem yake kowa, ni tunda na xo har yau ban dora ido a kansa ba idan anyi magana sai uwar tace yana benue, tsafin suke koya masa a can din oho mu dai ga mu ga Allah, bikin d'an uwansa guda ma gashi babu alamar xai xo, ni dama a tsorace nake da yaron tun asali" El-Basheer yace "Toh xan dawo" Nafisah tace "Yaya don Allah in bi ka?" Yace "Airport din?" Hajja tace "Ehh mana ku tafi da ita ai yar makaranta ce" El-Basheer yace "Toh idan da mijin Nafisan xamu dauko fa" Hajja tace "Toh ai mijin tun da muka dawo da shi bai koma ba, Nafisar ce kadai ta taho ko yaro daya bata xo da shi ba ta bar ma wata makociyarta balarabiya me kirki, mijinta kuma na Habuja" El-Basheer yace "Ohk" Nafisah na jin dadi ta dau mayafinta, Hajja tace "Toh gaskiya ni bana son kai, idan har xa aje dake sai dai a tafi da wannan yarinya Jiddah itama tunda tare kuke, ita ma kuma ba 6are bace" El-Basheer yace "Toh ta dau mayafinta mu je" Nafisah tace "Amma Hajja kar ya Abuturrab ya koro mu fa" Hajja tace "Xai ko aika, ku mu je gun motar gaba daya" A tare suka fita, suka tadda Aliyu xaune cikin mota yana jiran El-Basheer, ganinsu gaba daya ya daure fuska, Hajja ta bude ma su Nafisah bayan mota, Ita dai Jiddah gabanta sai faduwa yake don mayafi ne ita ma jikinta, kallon mamaki Abuturrab ke masu gaba daya, can yace "Ina xa a kai wa ennnan?" Hajja tace "Usman ne yace a tafi da Nafisah su hadu da takwararta a Iyapot, ni kuma nace a tafi da Jiddah tunda a kan kunnenta aka yi xancen kuma mu bama nuna banbanci a xuri'armu" Abuturrab yace "Aa ni baxanje da kowa ba sai dai El-Basheer yaje ya dauko Aunty Nafisar a Airport" Hajja tace "Amma kasan ina lura da yanda ka raina ubanka, shi fa ya fada bani ba, albarkacin daga bakinsa hakan ya fito ai sai kayi masa biyayya ko ba ta dadin rai ba kayi abinda yace, ba fa goyasu xaka yi ba balle kace aiki aka hadaka da, ko wacce xaunawa xata yi a bayan mota har kuje ku dawo, gaskiya ka sake hali Aliyu, wllh Bashir ba haka yake ba kai dai bar shi da tsokana da mugunta, amma kai wllh kana da bakin hali" Abuturrab yace "Duk naji su sauka kawai" Hajja tace "Allah ya tsine min idan sun sauka, a kira min Usman" El-Basheer dake dariya kasa kasa bayan ya shiga front seat ya kalli Abuturrab yace "Plss let them, it's Abba's instruction" Dama Hajja ko sake kallon Abuturrab bata yi ba tana kallonsu Nafisah tace "Ku shiga kawai" Nafisah ta turo baki ta shiga motar tana kallon yayanta, Jiddah tace "Hajja ni ai kince xan wanke maki bandaki ko?" Hajja tace "Aa wancan me fuskar uwar tata xata wanke min, wato Aisha" Jiddah ta girgixa kai tace "Hajja ni xan wanke kawai su tafi" A fusace Hajja tace "Oo Allah ya ana yabonki sallah sai ki kasa alwala, bayan nabi duk na barbada ma duniya cewar baki da musu kuma yanxu ki nemi karyatani gaban yaran nan??" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Toh kiyi hakuri" Daga haka ta shiga motar, Hajja tace "Yauwa, ku je Allah ya tsare, idan kinga yalo a hanya ki tuna masu idan sun ga dama sun siya min to" Daga nan ta kulle motar tayi wucewarta ciki tana cewa "Da ban masa haka ba koran min 'ya yan xai yi, gwara ma yayi aure kowa ya huta wllh yaje can su ci kansu da matar ni dai xan dinga kai masu ziyara kawai da d'an rakiya" Tada motar Abuturrab yyi fuska daure ya danna horn mai gadi na bude motar ya fita compound din ya dau hanyar titi, ta madubi El-Basheer ke kallon Jiddah da ya lura she is uncomfortable yace "How is ur studies going Jiddah?" Nafisah ta kalli Jiddah dake gefenta, Tana wasa da gyalenta tace "Alhmdlh" Ya dinga kallonta kafin yace "Hope u are assimilating what u are being taught?" Ta d'an yi murmushi tace "Ehh" ya langwabar da kai yace "Ni ai ba da Hausa na maki ba ko" sake kallonsa tayi suka hada ido, sai kuma tayi murmushi, yace "Do you have any idea of where we are heading to now?" Ta kalli Nafisah dake ta kallonta tana murmushi, Nafisah ta gyada mata kai alamar tayi magana, Shi dai El-Basheer na ta jiran respond dinta, ta d'an kallesa tace "Ka sake fadan abinda kace" Yace "Ohk.. Did u have any idea of where we are heading to now?" Ta d'an kalli Abuturrab da fuskarsa babu yabo bbu fallasa yana kallon titi yana driving, cikin sanyin murya tace "Yes i have" El-Basheer yace "So where are we going to now?" Tace "Hajja said we are going to take Aunty at the...." Sai kuma tayi shiru, ya gyada kai yace "Yess good, ci gaba" Tace "Airport?" Murmushi El-Basheer yayi sosai yace "Ohh yes, Hajja said we are going to pick Aunty Nafisa from the Airport" Ta sunkuyar da kai ita ma tana murmushi, Nafisah dai sai kallonta take, El-Basheer yace "So can you brief me about ur self?" Ta d'an yi shiru sai kuma ta kallesa yace "I am all ears" Tace "My name is Hauwa Jiddah yusuf, i was born and brought up in kaduna hayin rigasa, i lived with my step mum not until..." Da sauri Abuturrab ya kauce ma mai mashin da ya kusa bugewa, Nafisah da taga yanda abun ya faru tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da mamaki El-Basheer yace "How manage?" Abuturrab ya sauke glass ya ba ma mai mashin din hakuri ya ja motarsa ya kara gaba ba tare da ya tanka kowa ba, El-Basheer yace "Are u sure hankalinka na kan tukin nan Aliyu?" Abuturrab bai tanka sa ba still yana driving din, El-Basheer yace "Toh Allah ya tsare" Maida dubansa yayi kan Jiddah ta madubin gaba yace "Go on Jiddah" tace "I am currently living with Umma at Unguwar Dosa..." Sai kuma tayi shiru, kallonta kawai El-Basheer yake, tayi murmushi tace "Shikenan" Yace "Yea, kinyi kokari sosai Jiddatul Khair, maa sha Allah" Ita ma murmushin tayi tana daga kai suka yi ido hudu da Abuturrab dake kallonta ta madubi, ta sunkuyar da kanta, Nafisah ma duk tana lura da kallon da yake ma Jiddah ta dinga fatan Allah ya sa kada yaje ya sake buge wani kuma. Aunty Nafisah ta rungume takwararta cike da murnan ganinta tace "Haka kika girma Nafisah" Nafisah dake ta washe baki tace "Aunty me yasa baki taho da su Farida ba?" Aunty Nafisah tace "Suna makaranta ne amma in sha Allah xa su xo wani lokacin" Sai a sannan ta kalli Jiddah, Jiddah ta gaisheta da ladabi, Aunty Nafisa ta amsa da fara'a tana kallonsu El-Basheer tace "Wacece?" El-Basheer yace "Yarinyar Umma ce" Aunty Nafisa tace "To madallah" Tuni Abuturrab ya wuce da trolley dinta, duk suka bi bayansa xuwa mota, bayan ya saka jakan a booth ya shiga driver seat, Su ma suka shiga motar sannan ya bar airport din, hira kawai El-Basheer ke yi tare da Aunty Nafisah da ta fita harkan Abuturrab ganin yanda ya tarbeta a airport, shi dai driving dinsa kawai yake, suna fara shigowa gari, Jiddah na kallonsa tunda ita ce setin kujeransa ta d'an matsa, El-Basheer ya kalleta ta gefen ido, a hankali tace "Yaya... Hajja tace a taho mata da Yalo wai" Abuturrab da ya ji ta sarai don setin ears dinsa tayi maganan yyi shiru yana driving dinsa, El-Basheer yace "Kina son wani abu ne Jiddah?" Ta kallesa tace "Aa Hajja ce tace a siyo mata yalo" El-Basheer yace "Ohk idan an gani sai a siya mata" Luckily suka samu yalon El-Basheer yace "Oga ka samu waje kayi parking a siya ma Hajja yalo" Abuturrab yace "Wa ennan rubabbun abubuwan" Daga haka ya ja motarsa ya ki tsayawa, Aunty Nafisah dai bata ce masu komai ba, El-Basheer yayi wani murmushi shi ma bai ce komai ba, sai da suka kusa gida Abuturrab yace "Aunty ya baki taho da zee ba?" Tace "Ban sani ba" Murmushi kawai yayi ya shiga layinsu, a kofar gida yayi parking, El-Basheer ne ya fara sauka, Aunty Nafisah ta sauka, snn Nafisah, Jiddah xata sauka Abuturrab yace "Tsaya" kallonsa tayi, ya hade rai yace "Ke har wani nishadi kike kiyi ta hira da kattin maza kina washe baki don baki da kamun kai koh? To daga yau na sake jin kin wani bude baki kina ma wani turanci xan baki mamaki, sannan ki ci gaba da yawo da kananun gyale" Ita dai kallonsa kawai take, yace "Saukar min a mota" bude motar tayi ta sauka ta wuce cikin gida ya bi ta da kallo.....
Leave a Comment