Jiddatul Khair 38


 Waya Abuturrab ya tadda Aunty na yi a parlonta rai bace, ko ba a fada ba yasan da wanda take wayar, yana dai tsaye har ta gama ta jefar da wayar kan kujera tana huci, ya kwantar da murya yace "Aunty duk bai kai wannan extent din ba, pls i want u to calm down...." A fusace tace "Ya kai har ya wuce extent din da kake fada, kuma wllh xan ga uban da xai fitar da kayan nan a gidan ga yau, sun san da nuna ikon me ya hanasu wahalan hada lefen? Tun da na fara hada kayan nan kullum sai na fita kamar yar iska, kuma bani xan shigo gidan nan ba sai karfe takwas din dare, to a kan me ba a ce min Allah ya shi min albarka ba xa a dinga bata min rai ana sa ni a bakin duniya?? To wllh wllh Ramlatu ta fita harkata, ta fita idona in rufe idan kuwa ba haka ba xan kai kararta ba wani shege, ko kuma in kai ta gani ga ka ayi min iyaka da ita" Abuturrab dai kallonta kawai yake, wayarta ne ya fara ring ta dauka ta shige daki a fusace ta kulle kofar, Abuturrab ya shafa kansa sannan ya juya ya fita daga dakin, bangaren Umminsa ya shiga, ya kasa kallonta ya xauna saman kujera cikin sanyin murya yace "Ummi don Allah kiyi hakuri, duk bai kai haka ba" Ummi tace "Inyi hakuri da me??" Kasa cewa komai yayi, Ummi tace "Wllh in har akwatunan nan suka kwana gidan nan sai dai ka nemi wata yarinyar da xaka aura ba wannan ba Aliyu" Umma dai na xaune tana danna wayarta tana girgixa kafa, Abuturrab bai kuma cewa komai ba ya mike ya fita parlon, a main parlor ya tadda Hajja tsaye bakin kofar parlon da su Maimoon, sai ga mai gadi ya fito daga dakinta rike da akwatuna biyu a hannunsa, Hajja ta basa hanya tace "Yanxu saura nawa?" Mai gadin yace "Saura hudu" Hajja tace "To yi maxa..." Mai gadin yayi kofar gida da akwatunan ya saka au booth din mota da driver din Umma ya bude sannan ya koma ciki da sauri, Hajja ta kalli Jiddah dake tsaye wajen balcony din tace "Toh ke wa kike da suna, ki kwashi kananun da ya ajiye a nan ki kai mota da tsayuwar nan, ki daina lagwai lagwai kamar ba mace ba kinji??" Jiddah bata ce komai ba sbda bata son mata musu ta dau kit din biyu ta nufi gate, Banda hararan Hajja babu abinda Abuturrab yake daga inda yake tsaye, can ya nufi kofar kamar xai tashi sama, Hajja na ganin haka ta basa hanya da sauri, bayan ya fita ta kalli su Maimoon tace "Kun ga d'an banxan ko? Kunga irin dabancin nasa ko?? Da ban kauce ba bangajeni yayi niyyar yi fa, anya wannan Aliyun da na tafi Masar na bari kenan shekaru uku da suka wuce? o,o to baxan biyesa ba, ba ruwana ni ba yarinya bace, kuma sai dai ya bangaje Hauwa ko Usman, ko kuma yar Benuen can, amma ba ni ba tunda ban hada komai da shi ba ai" Jiddah na ajiye kits din bayan booth taki komawa cikin gidan tana tsaye jikin gate har ranta bata jin dadin abinda ke faruwa, Abuturrab ya fito compound din, kallon driver din Umma yayi yace "Wa yace ka saka akwatunan a bayan mota?" Drivern ya xagayo da sauri yace "Aa kawai ni bude booth nayi ake xubasu a ciki" Calmly Abuturrab yace "Toh sauko da su" Kallonsa Jiddah ta dinga yi da mamaki, Driver ya koma gun booth da sauri xai sauke kayan, kafin driver ya fara sauke kayan ta daure tana kallon Abuturrab tace "Ina son in maka wata tambaya don Allah..." Sai a sannan ya kalleta, tace "To ka d'an ce masa ya jira kafin ya sauke kayan, kaji?"  Driver ya kalli Abuturrab din dake ta kallon Jiddah da mamaki, Ta koma gefensa tana kallonsa, kana ganinta kasan she is afraid of talking to him, gathering many courage ta fara magana tana wasa da fingers dinta "Dama ina son in san wacece Baabarka a cikin Aunty da Ummi, ni har yanxu ban sani ba" Daga sama har kasa ya kalleta, ta ci gaba da magana ba tare da ta yarda sun hada ido da shi ba tace "In dai Aunty ce Baabarka to kayi dai dai idan kace a sauke akwatunan nan, tunda ai ba a wasa da maganan uwa, idan kuma Ummi ce Baabarka...." Sai kuma tayi shiru, yana kallonta da kyau yace "Ina jin ki" Cikin sanyin murya tace "Kaga ni ban samu gatan sanin mahaifiyata ba, na taso cikin maraicinta, saboda maraici da rashinta yasa na taso cikin rashin gata da kula..." Hawaye ya kawo idonta tana gogewa tace "Da mahaifiyata na nan duk abubuwan da suka faru dani da nasan baxa su faru ba, ko yan uwanta ni ban samu daman sani ba, bansan ko tana da yayyi ko kanni ba, ban ma ta6a ganinta ba" Ta kasa ci gaba tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, shi dai kallonta kawai yake, cikin sanyin murya tace "Toh kaga duk wanda baya ba Baabarsa muhimmanci baxai ji dadin rayuwarsa ba, kuma xai hadu da fushin Allah" Sai kuma ta daga kai ta kallesa tace "Albarkacin haifanka da Ummi tayi kaji maganarta na yau kawai mana, tunda tace bata son a bar kaya a nan ka bari a tafi da su xai fi, ko kai baka son ka xauna lafiya da matar da xaka aura?" Hajja ce ta fito gate din gidan tana yafa gyalenta da yar jakarta a hannu tace "Ina matukin motar yake mu tafi" Drivern Umma ya xagayo da sauri yace "Gani Hajiya" Tace "A ina xan xauna a motar?" Bayan motar ya bude mata ta shige ba tare da ta kalli su Abuturrab ba tana cewa "Bari in fara yin gaba da kayan" tana shiga ta kulle motar, Drivern dake ta kallon Abuturrab yana jiran wani instruction din jin bai ce komai ba ya xaga ya shiga motar ya tada suka bar layin... Jiddah ta daga kai ta kallesa ganin kallonta yake ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, ya gyara tsayuwarsa yace "Ohk, shikenan kin gama?" Shiru tayi da farko, sai kuma ta girgixa masa kai a hankali tace "Aa, yanxu don Allah kaje ka ce Ummi tayi hakuri ta yafe maka, sai kace mata Hajja kuma ta riga ta tafi da kaya" Yace "Koh?" Ta d'an kallesa, sai kuma ta sauke kanta ta gyada masa kai, yace "Ohk, kalleni" Kin yarda ta kallesa tayi, yace "Kalleni nace" Ta dake ta dago kai ta kallesa yace "Toh daga yau... Kika sake sako min baki a abinda ya shafi rayuwata sai na mareki, ke har xaki gaya min abinda xanyi da wanda baxan yi ba? " Jiddah dai bata ce komai ba, kawai ta juya ta nufi gate ya bi ta da kallon mamaki yace "Kee" ko waigowa bata yi ba, yace "Ba magana nake maki ba" Tayi shigewarta gate, shafa kansa yayi sai kuma ya bi bayanta. Parlor ya tadda ta xaune tare da su Maimoon, bai kalleta ba ya wuce bangaren Ummi, har sannan Ummi na xaune da Umma dake ta bata hakuri, kansa a kasa ya xauna kan rug din parlon, da kyar yace "Ummi don Allah kiyi hakuri ki yafe min, in sha Allah duk yanda kika ce xa ayi hakan xa ayi, kaya kuma na sa Hajja ta tafi da su can gidan Umma" Dama bai sa ran Ummi xata basa amsa ba, hakan yasa ya kalli Umma ita ma yace "Ku yi hakuri Umma, in sha Allah hakan baxai sake faruwa ba, duk yanda ku ka ce haka xa ayi, kaya kuma duk ranan da ku kace a kai sai a kai, kuyi hakuri don Allah" Yana kai wa nan ya mike ya nufi kofa duk suka bi sa da kallo, ba Ummi ba har Umma tayi mamaki sosai ba kadan ba, abinda bai ta6a yi ba kenan duk rayuwarsa karkari ya je ya ba stepmom din tasa hakuri ya bar gidan sai kuma randa aka gansa, Ummi tace "Wannan ba xuwan kansa bane..." Umma tace "Aa nima nayi mamaki, ko Hajja ce dai..." Ummi ta kalleta da sauri tace "Wacce Hajjar? Shi dai ya san what he is up to shiyasa ya shigo bada hakuri, amma this is so unusual of him, ni bai ma ta6a bani hakuri ba" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh koma dai menene tunda ya shigo kuma yace ayi hakuri, sannan yace Hajja ta tafi da kaya kawai kiyi hakuri yaya" Ummi dai bata ce komai ba. Abuturrab na fita Bedroom dinsa ya shiga ya sa makulli, wayarsa dake hannunsa ya fara ring ganin Abba ke kiransa ya daga, Abba yace "Kana ji na Aliyu?" Abuturrab ya xauna gefen gado yace "Ina ji Abba" Abba yace "Plss ka lallaba iyayenka duk yanda xa ayi kar a fitar da kayan nan daga gidan nan... It should remain their gobe a kai su" Abuturrab ya shafa kansa yace "Abba Hajja ae ta tafi da su" Abba yace "Ta tafi da su?? Amma baka yi making ko wani effort na hana tafiya da su ba Aliyu??" Yyi kasa da murya yace "Abba Ummi ta dau lamarin da girma ne, tayi fushi sosai, and...." Abba ya katsesa yace "And what nonsense? Ita kuma Hafsah fa? Ni nasan yawancin abubuwan dake faruwa gidan nan duk Ramlah ke xuwa ta hada, a kan me su basu hada lefe ba kuma su 6ata ma warce ta hada rai kana kallo Aliyu??" Shi dai Abuturrab yyi shiru, Abba ya katse wayarsa, kallon wayar Abuturrab ya dinga yi sae kawai yaji bai ji dadin abinda Abba ya fada ba har ransa, can ya mike ya koma parlon Ummi..... Hauka ne kawai Aunty bata yi ba bayan Aisha ta kai mata rahotun ai har an fitar da akwatuna xuwa gidan Umma, ta fito parlor tana kai koma inda take shiga ba nan take fita ba, xage xage ta dinga yi kamar yar maguzawa, su Maimoon da Jiddah dai na xaune parlorn, Umma da Ummi duk na jin ta, Abuturrab dake parlon Umminsa yace "Umma muje in ajiye ku gida yanxu tunda driver din bai dawo ba" Umma ta ki tashi, Sanin at anytime Umma na iya tanka Aunty yasa Ummi tace "Ramlah dare nayi ku tafi a ajiye ku a gida" Umma ta mike ta dau wayarta tace "Sai mun yi waya yaya" daga haka ta fita Abuturrab na biye da ita bayan ya ciro makullin motarsa a aljihu, Umma bata ko kalli Aunty ba tana kai xuciyarta nesa tace ma su Jiddah su taso su tafi, daga haka ta fita parlon, Mikewa Jiddah tayi ta xaga xata wuce ta bayan Aunty dake tsaye tsakar parlon dab da ita tana kumfar baki, Aunty na ganin haka ta fixgota a fusace ta sauke mata lafiyayyen mari tace "Don uwarki ta bayana xaki bi ki wuce duk ga hanya a gidan sbda ni sa'ar uwarki ce fitsararriya?? An aiko ki wajena ne xaki bi ta bayana, to koma wa ya aikoki ki koma kice masa na fi karfin sa, baki gan ni ba, kaji min dai yarinya xaki xaga ta bayana duk ga hanya a parlo??" Bude baki Abuturrab yyi ya tsaya yana kallon Aunty, Jiddah ta kasa motsawa tana dafe da kuncinta ta rufe ido, hakan ya kara tunxura Aunty ta fincikota tana jan kunnenta tace "Ooo rashin kunya xaki min?" Karasowa Abuturrab yyi parlon cikin annoyance yace "This is mean of u Aunty, me ta maki xaki mareta haka? Who does that? Akan me xaki mareta a fuska, what offense did she commit?" Sake baki Aunty tayi tana kallonsa, can tace "Ni kake tambaya me yasa na mareta Aliyu?" Ko kallonta bai yi ba ya kalli Jiddah dake shessheka yace "Fita...." Taki motsawa hawaye na xuba idonta ya Fixgo hannunta ya nufi kofa, Aunty ta bi sa da kallo baki bude, sae bayan da suka fito balcony ya sake hannunta ta nufi gate tana goge idonta, Umma na tsaye jikin motar Abuturrab dake waje tana jiransa, har suka isa gidan Umma babu wanda yace komai a motar, Abuturrab yyi parking kofar gida Umma ta bude motar ta sauka, ta nufi gate Abuturrab ya bi ta da kallo, Safiyya dake gaban motar ta sauka, Maimoon ce karshen sauka a motar, yana kallon Jiddah kafin ta wuce yace "Dawo ki rufe min motata da kyau" Dawowa tayi ta bude motar ta sake rufewa sannan tayi wucewarta ciki. Washegari lahadi da yamma Jiddah na xaune balcony tare da Yousuf hannunta rike da Literature da ya sa ta karanta masa, mota ce ta shigo compound din, tunda ta kalli motar sau daya ta ci gaba da karatun da take Yousuf na kallonta, Ummi ta fara saukowa motar sannan Abuturrab ya sauka, suka nufo entrance din gidan a tare, tun basu kai balcony din ba Abuturrab ke kallonsu, Da ladabi Yousuf ya gaida Ummi ta tsaya Balcony din ta amsa da fara'arta, Abuturrab bai ko kallesa ba ya shige parlon, Jiddah ta gaida Ummi sannan ta mike ta amshi ledan hannunta, Ummi tace "Ki xauna kiyi karatun ki Jiddah... Don't worry my dear" Jiddah tace "Bari in kai ciki Ummi" Daga haka ta amshi ledan ta shiga parlon Ummi ta bi bayanta, dakin Umma ta nufa tare da Ummi, bayan ta ajiye ledan ta fito parlor, satan kallon Abuturrab tayi taga idonsa na kan TV, sai ta kasa wucewa bata gaishesa ba, hakan yasa ta d'an tsaya tace "Ina yini" Bai ko kalli direction dinta ba balle ya amsa fuskarsa daure, tayi wucewarta waje, tana dawowa balcony din ta dau literature din da ta ajiye sannan ta xauna Yousuf na kallonta, murmushi tayi tana duba page din da take, sai ga Abuturrab ya fito, ya nufi motarsa ya shiga yayi horn mai gadi na bude masa gate ya fice daga gidan, Yousuf ya kalli Jiddah yace "Is he alright?" D'an murmushi tayi tace "Nima ban dai sani ba" Yousuf yace "Naga baki gaishesa ba" Tace "Aa na gaishesa a parlor" Yousuf yace "Go on with ur reading" ba musu ta ci gaba da karatun yana kallonta. Aunty ce kwance kan gadon sister dinta godiya, Aunty ta mike xaune tace "Ni fa duk abubuwan da aka yi a gidan nan bai dameni ba don Alhaji ya tsaya min kuma ya dawo yayi ta bani hakuri wllh, ita ma Hauwan taga bacin ransa wllh kuma komai ya xo da sauki tunda uwarsa ba gidan ta kwana ba, abinda ya dameni shine yanda har yanxu Aliyu ya ki ce min komai a kan lamarin, tun da ya shigo sau daya ina waya da Abban nasa a daren har yau da nake maki magana bai sake ce min komai ba, ko a waya kuwa, abinda bai ta6a min ba, bayan xuwa ya bani hakuri sai ya sake kirana ya ban hakuri sannan ya tura min text kuma to wannan karan wllh duk babu" Godiya tace "Kuma yana gidan?" Aunty tace "Jiya Monday dai ya koma bakin aiki da safe, kuma ko baya gidan ma ai yana kirana a waya, to ni duk ba wannan ba, abinda ya bani shock shine yanda yake querying dina a kan dalilin marin talakan nan da ya je ya kwaso mana a hayi...." Godiya tace "Wai ba kince an gama case dinta ba har ma ya saketa? To me kuma ya hadasa da ita" Aunty tace "Toh ai har yanxu tana gun kanwar uwarsa, ta amsheta wai xata riketa har sun sa ta a karatu" Godiya tace "Toh sai ya maki magana don kin mareta ko ko?" Aunty tace "Wllh kuwa Kyauta, cikin bacin rai ya gaggaya min magana wai a kan me xan mareta sannan ya kada keyarsa ya fita, ni tsabar shock ma ban samu bakin ce masa komai ba" Godiya tace "Aa to da akwai lauje cikin nadi a wannan batun naki, me yasa xai ji haushi har yyi magana don kin mareta" Aunty dai bata ce komai ba ta ta6e baki abun na sake dawo mata ranta na k'una, Godiya tace "Toh ko dai bai saketa din bane dai Hafsah" Aunty tace "Haba dai ga takarda ubansa ya sa ya rubuta kowa ya gani, kowa ya shaida babu wani aure tsakaninsu, kawai toxarta ni yake da niyyar yi dama, amma ba komai in dai ni ce ya xuba ido" Godiya tace "Gaskiya kam, to yanxu ranan juma'ahn da munafukar kanwar Hauwan xa ku je kai kayan??" Aunty tace "Aa Alhaji yace in bar masu kawai suje su kai kayan ba sai naje ba, kuma ina ga da wannan takadiriyar tsohuwar xa a, kinga gwara ai inyi xamana, abu dai namu, ta wani bangaren fa uwa nake a gun amaryar, iyaka kawai ki shirya ki bi su don ki kwaso min rahotu" Godiya tace "Aa gwara kam kiyi xamanki ni inje, don na lura da take takensu so suke wani abu ya billo daga bangarenki a sa yaron ya fasa auren Aneesar tunda ai an san uwar Aneesar aminiyarki ce" Aunty tace "Yauwaaa ashe kin gano godiya, haka suke so ni kuma ba shashasha bace duk xan bi su a nutse ayi auren, shi sa kika ga na fara ja baya, ayi komai a gama su ga ko xasu sake iko da Aliyu kuma a rayuwar nan, ba uwarsa ba, wllh har ubansa sai ya nuna baya yinsa, balle wata kanwar uwarsa can, don tun farko ma shi bai dauketa mutum ba, su da Aliyu kuma sai dai hange daga nisa al-qur'an" Godiya tace "Shkkn kuwa Hafsah" Aunty ta d'an yi dariya tace "Allah dai ya kai mu lokacin lafiya, ai ni yanxu ido xan xuba ma kowa in ta binsu a samu a daura auren cikin aminci Aneesah ta tare" Godiya tace "Amma fa hankalina bai kwanta da xaman wannan yar hayin ba tsakaninku, tunda kinga dole dai Ramlah xata dinga xuwa da ita wajen yayarta..." Aunty tace "Toh sai me idan tana tahowa da ita, shi fa Aliyu bayan auren nan ko gidan ba xuwa xai dinga yi ba, tsaf xan masa iyaka da gidan wllh, kawai dai idan ina bukatar wani abu in shirya in tafi gidansa amma shi da gidan nan sai hange daga nesa.." Godiya tace "To da kyau hakan, Allah ya nuna mana auren nan lafiya" Aunty tace "Ameen, satu biyu kamar gobe ne ai in sha Allah" Godiya tace "Haka ne, bari in dubo mana girkin ko ya nuna" Daga haka ta mike ta fita dakin. Ranan Juma'ah Umma da frnds din Ummi biyu sai wasu yan uwan Abba da Godiya suka tafi kai lefen Aneesah garin Abuja, Hajja ta so xuwa amma Abba ya hanata don kar ya kullaceta ya sa ta hakura kawai suka tafi, sai ta 6ige da cewa su Jiddah ai ita ba yarinya bace dama da xa aje kai lefe da ita, banda ma an rainata ai bai kamata ayi mata xancen kai lefe ba tunda dai ita ba yarinya bace, iyayen Aneesah sun amshi su Umma da mutunci ganin uban kaya na gani na fada da aka yo ma yar su, ga zobunan gwal manya har biyu a ciki, Godiya dai na ta kwashe rahotun kai ma Aunty, aka yi komai cikin mutunci da girmama juna sannan su Umma suka juyo xuwa Kaduna..... Abuturrab na kwance dakin hotel dake cikin garin Lagos idonsa a lumshe kafin lkcn da xa su yi piloting jirgi xuwa kano yayi wayarsa dake gefensa ya fara ring, ya bude idanuwansa ya dau wayar ganin Aneesah ce ya daga ya kai kunne yayi shiru, cikin wani salo tace "Mijinaaa" Calmly yace "Ya aka yi?" Ta lumshe ido tace "I love you my Captain... Ina sonka fiye da yanda kake xato a ranka, I can't wait in ga na mallakeka a matsayin mijina" Shi dai sauraronta kawai yake, ta kanainaiye murya tace "I can't wait a daura in 2 weeks time, I can't wait to be ur wife officially My captain" Yace "Amma kin san wajen aiki nake Aneesah, i tot it's something serious u want to say" Tace "Ban gane something serious ba, wannan da nake gaya maka ba something serious bane?" Yace "Amma ba da rana ina wajen aiki ba" Tace "Ohk haka xaka ce min captain?" Yace "Ohk, i love you, idan na sauka kano xan kiraki..." Katse wayar yayi ya sa flight mode yayi rub da ciki ya lumshe ido.


No comments

Powered by Blogger.