Jiddatul Khair 37


Slowly Jiddah ke tafiya kamar bata son yi a compound dinsu Abuturrab, su Maimoon duk sun yi gaba tare da Umma, ita ce karshen shiga parlon, tsaye tayi bayan kujera ganin Abuturrab dake sakkowa cikin parlon waya kare a kunnensa, tayi bakin kokarin ganin bata kallesa ba, bayan ya shigo parlon ta

xaga ta bayan kujera tayi wucewarta part din Ummi ya bi ta da kallo, Bayan Jiddah ta gaisa da Ummi, Ummi tace "Ki tafi dakin Hajja suna can" Mikewa tayi tace "Toh" sannan ta fita xuwa dakin Hajja, Umma na xaune su Maimoon na ta bude akwatunan da aka jera a dakin, Hajja tace "Yanda kika san wata yar gwal xa a auro, haka aka hada lefen har da na Allah ya isa..." Akwatuna biyar ne set biyu each da kit, Umma ta dinga kallon uban kayan da aka hada na lefen bayan su Maimoon na ta budewa, Hajja tace "Aa kar ki ji komai Ramlah ai nace duk xan dibar ma kanninsa abinda ya sauwaka a ciki, mu ba 6arayi bane da xa mu kai masu wannan ubansun kayan, ni kaina xan cire atamfa me tsada daya da jaka, takalmin ma baxai min ba sbda me tsini ne kar in je in karye shi sa baxan dauka ba, amma duk wa ennan yan matan xan cire masu duk abinda Allah yayi wllh" Umma tace "Aa Hajja ki bar masu kayansu kawai, Allah ya sanya alkhairi, ya bama yan baya haka" Hajja tace "Kaji wata magana irin ta 'yan kasar nan, wllh wllh babu shegen da xai yi haka a Masar, sannan me yasa baki bari Ahmad ya hada ma Ramlah irin wannan lefen ba? Ba shi ma yana da dukiyar ba na samu labari?? to shine ni xaki ce jikana ya dauka ya kai ma su gaba daya sbda sata yake yi a sararin samaniya? Aa wllh duk xan bi in rage ni ba gantalalla bace" Umma bata kuma ce mata komai ba, ita dai Jiddah na xaune ta rakube jikin kujera tana bin akwatunan da kayan ciki da kallo. Abuturrab ne tsaye parlon step mum dinsa da duk ta firgice masa, yayi kasa da murya yace "Toh ke ba dai kinsan duk abubuwan da kika xuba a ciki ba Aunty, komai kika ga yayi missing kar ki damu xan bada kudi ki siya wani ki saka" Aunty tace "Ni dai cewa nayi ka tafi ka xauna a dakin, idan aka ganka babu wanda xai ta6a komai cikin kayan, kafi kowa sanin Hajjan nan fa" Abuturrab ya girgixa kai yace "Aunty don girman Allah ki bari su yi ta daukan duk abinda suke so ni xan sake replacing, i just can't go to that room" Aunty ta wani hade rai tana kallonsa tace "Wato ban isa da kai ba Aliyu, ban isa in sa ka abu kayi ba??" Yace "Toh shkkn, bari in je" Daga haka ya juya ya fita parlon, sai da ta bisa ta tabbatar ya shiga dakin Hajja sannan ta koma parlonta, Ya d'an shafa kai bayan sun hada ido da Umma da ladabi yace "Ina yini" Banxa tayi masa, su Maimoon suka gaishe sa yace "Lafiya lau" Jiddah dai tunda ya shigo bata kalli inda yake ba idonta na kan akwatuna, Hajja dake ta fiddo kayan akwatunan tare da Safiyya ta mike tana kallonsa tace "Lafiya ka shigo kayi mana sandandan a kai Aliyu?" Yace "Takardan da na baki nake so in amsa yanxu" Hajja ta kalli Umma tace "Kinga jaraba ko, tun fa ban tafi Masar ba ya bani wasu shegun takardu da ban san isilinsu ba yanxu, shekaranjiya ya xo nace masa yayi hakuri ban san wani shirgin suka shigw ba amma har gidana xan sa aje a bude mu shiga mu bincika ko da rabon a gani, a haka muka rufe kess din da shi, to meye yanxu xai dawo ya tsaya min in basa takardu kamar wasu takardun jaraba, to gaskiya ban san isilinsu ba ka rabu da ni, ni bance ka dauko takarda ka bani ba" Daga haka ta ci gaba da abinda take, Umma ko kallon direction din Abuturrab bata yi ba banda daure fuska da tayi, Hajja ta dauki wani gyale me kyau ta jefa ma Maimoon tace "Gwada wannan" Umma ta girgixa kai tace "Hajja nace ki bari don Allah, wannan bai dace ba..." Hajja ta mike ta katseta tace "Kinga baiwar Allah tashi kiyi wucewarki in gama abinda nake, babu ruwanki da harkana, kin wani narka uban kiba kina bani oda kamar yar ki, nace ki tafi asibiti a dubaki kin ki, Da a Masar ne da tuni an kai asibiti wllh, to kuma ina ruwanki da abinda nake banda dai kawai kina kanwar uwar Aliyun uwa daya uba daya" Umma ta mike tace "Toh Allah ya sanya alkhairi na ga lefe sun yi kyau Maa sha Allah, Allah ya nuna na yan baya haka" Hajja tayi banxa da ita, Umma ta nufi kofa ta fita, Hajja tace "Banda kema cutar Aliyun xaki yi tunda ba ke kika haifesa ba kuma haushinsa kike ji kamar ki kashesa, wacece ita wannan yarinya da xa a kai ma lefe guda sha biyu komai na ciki kuma dozen dozen, ina kokarin ragewa kuma xaki kawo min raini, to wllh baxai sa6u ba, Dukiyar Aliyu ba banxa ba..." Rungume hannu Abuturrab yyi yana kallon Hajja, ta dau atamfa daya me tsada ta jefa ma Jiddah tace "Yayi maki kyau ko a canxa?" Jiddah ta bude ido sosai tana kallon Hajja, ta dau jaka ta jefa ma Maimoon ma, a takaice dai sai da ta ajiye ma Jiddah atamfa, mayafi, da jaka da takalmi da kayan kwalliya, su Maimoon ta basu kayan kwalliya da mayafai kawai duk don sbda haushin abinda Umma tayi mata, Jiddah dai gabanta sai faduwa yake tana kallon kayan gabanta, Hajja ta nemi waje ta xauna tana kallonsu Maimoon tace "Toh ku kulle masu kayansu, Allah ya sa albarka a abinda suka rage" Maimoon da Safiyya duk suka rufe akwatunan, Sai a sannan Abuturrab ya juya ya fita daga dakin, sai bayan da ya fita Hajja ta nemi ledoji duk ta sa ma kowa abinda ta basa a ciki, Jiddah dai duk jikinta yayi sanyi ta ma kasa ta6a ledan da Hajja ta ajiye mata a gabanta, Hajja tace "Ki tafi kice ma Zubaida take ko wa, kice mata baxata bani ruwan xafin bane in shiga makota in samo?" Jiddah ta kalleta don bata san ko da wa take ba, Hajja tace "Da ke nake, tunda barinsu kika yi da rufe akwatin kin xauna kamar sarauniya, banda dai Allah ya rufa maki asiri Usman ya rufa maki asiri ai da ke xa ayi ma kishiya yanxu, to kamar ya san da haka yasa aka sakeki" Mikewa Jiddah tayi ta nufi kofa ta fita, xaune ta tadda Abuturrab shi kadai a main parlor, duk da sun hada ido tayi wucewarta xuwa kitchen, bata tadda mai aikin a kitchen din ba, tayi ta tsayuwa daga karshe kuma ta fito, taki kallon inda Abuturrab yake ta wuce dakin Hajja, tana kallon Hajja tace "Hajja bata kitchen din" Hajja tace "Toh ta ci kanta, tafi da flask dina idan kin ga an daura ruwa ki juyo min ko bai yi xafi ba, tun daxu nake bin bakar matar ta ban ruwan xafi in sha shayi ta ki, Da a Masar ne wnn ruwan da aka tsuga yau ko wani gida kya ga butan tafasasshen shayi da kofuna kowa na ta sha" Jiddah bata ce komai ba ta dau flask din ta fita, har sannan Abuturrab na xaune parlon, tayi wucewarta kitchen, ta bude tukunyar da ta gani kan gas taga ruwa ne amma bai tafasa ba, ta dau cup kenan xata fara xuba ruwan cikin flask aka bude kofar kitchen din, sosai taji gabanta ya fadi wanda hakan yasa bata san lkcn da ta saki flask din hannunta ba, da sauri ya karasa ya amshi cup din ruwan xafin hannunta shi ma kar ta sake, iyakar rikicewa ta rikice a lkcn, cikin rawar murya tace "Ina yini" jin bai amsa ba ta durkusa ta dau flask din ta ga ya fashe, sae a sannan ta kallesa hankali tashe tayi narai narai da ido tace "Na shiga uku flask din ya fashe, me xan ce mata?" Yace "Ni kike tambaya?" Ta goge hawayen da ya kawo idonta, yace "Toh yanxu da kika hadani da Umma da Every of my family sae aka yi yaya?" Bata tsaya basa amsa ba tabi gefensa rike da flask din xata fita kitchen din ya jawota, kallon mamaki tayi masa yace "Ki bani amsata" Tace "Ni bani da amsan da xan baka" ya dinga kallonta, taki yarda ta kallesa, ya karbi flask din hannunta ya fita ta bi sa da ido, Hajja ta dinga kallon Abuturrab bayan ya shigo dakin, ya ajiye mata flask din gefenta yace "Ga flask dinki ya fashe sai ki fadi nawa kika siya a biyaki...." Da farko Hajja bude baki tayi tana kallonsa, sai kuma ta dauka da sauri ta jijjiga, lkci daya ta sake flask din ta mike sai kuma ta fashe da kuka tace "A Masar fa mijin Nafisa ya siya min flask din, waye yayi min wannan aika aikan??" Abuturrab yace "Ni ne, kuma shi yasa nace ki fadi nawa yake" Tace "Toh Allah ya isa wllh, don kaf dukiyarka baxasu siya min flask din ba tunda a Masar aka siye sa ba a kasar nan ba, sannan me ya kai flask dina hannunka bayan wancan matar na ba ta juyo min ruwan xafi?" Yace "In dai kin tambayi nawa aka siya sai ki gaya min" Daga haka ya juya ya fice daga dakin, ta fashe da kuka tace "Allah ka dai ga wannan xaluncin da aka min, a ina xa a samo flask irin wannan yanxu a kasar nan" Komawa gefe Jiddah tayi da sauri bayan Abuturrab ya fito don tana labe bakin kofar, ta bi sa sa kallo har ya wuce sannan ta shiga dakin gabanta na faduwa, a fusace Hajja tace "Ke garin yaya flask dina yaje hannun wancan mutumin da ya tsaneni?" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Dauka yayi Hajja" Hajja tace "Toh yaje shi, ni ba yafewa nayi ba, kuma bari Usman ya dawo tunda shi na haifa" Ita dai Jiddah bata ce komai ba. Bayan magrib Umma ta ajiye ma Ummi duk abinda Hajja ta ba su Jiddah da Maimoon na kayan lefe, Ummi tace "Ki bar masu kawai tunda ita ta basu" Umma tace "Aa maida masu da kayansu yaya, a ina aka ta6a haka" Ummi tace "Wai ba ni nace ki bar masu ba??" Umma tace "Toh Allah ya kyauta bari in je in ma Hajja sallama" Daga haka Umma ta fita bangarenta, a corridor suka hadu da Aunty xata sakko parlor, Aunty tace "Aa Hajiya Ramlah ashe kun shigo, mun wuni lafiya?" Umma tace "Alhmdlh" Aunty tace "Tun shekaranjiya nake ta ce ma Ummi ta kiraku an gama hada lefe wllh..." Umma tace "Ai kam kaya maa sha Allah, Allah ya sanya alkhairi" Aunty tace "Toh ai ni na xata kin xo kenan sai mun dawo daga kai lefen, kin san gobe ne xa a kai fa da safe" Umma tace "Aa sai kun dawo Hafsah, ni ba wani dadi nake ji ba, Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lfya" Aunty tace "Ehh tun da ma da ni xa aje shkkn kawai, Allah ya kara lafiya..." Umma dai ta wuce dakin Hajja, Aunty kuma ta sauka parlor, Ummi na kallon Jiddah dake parlonta ita kadai, su Maimoon kuma na daki wajen Ramlah tace "Kwashi kayan ki kai mota Jiddah" Jiddah ta mike ta dau ledojin kayan da Hajja ta basu ta fita, Aunty dake xaune parlor da wata bakuwa da tayi, Abuturrab ma na parlorn don kudi ta kirasa xai tura ma bakuwar wai na zoben gwal guda biyu da xa a sa ma Aneesah a lefen, ta bi Jiddah da kallo tana kare ma ledojin hannunta kallo, shi ma Abuturrab kallonta yake, Jiddah ta gaisheta ta nufi kofa ta fita, mikewa Aunty tayi tace ma bakuwarta tana xuwa sannan ta fita da sauri, shi dai Abuturrab bai ce mata komai ba, a compound ta tsayar da Jiddah ta amshi ledojin hannunta tana duba abubuwan ciki,  kwace dayan ledan tayi da karfi tace "Ubanki ne ya siya kayayyakin da aka baki ki kai mota??" Jiddah dai tayi shiru tana kallonta, Aunty tace "Baxa ki daina kallona cikin ido ba sai na tsole idanuwan?" Sunkuyar da kai Jiddah tayi, Aunty ta juya kamar xata tashi sama ta koma cikin gida, Abuturrab na kallon Aunty bayan ta xauna a parlor ta ajiye ledojin da ta amso a gefenta yace "Aunty da baki amsa ba ai ni nace xan siya duk abinda babu a ciki" Aunty tace "Rufe min baki, kai xaka gaya min abinda xanyi da wanda baxan yi ba, duk wanda bai rike girmansa ba xai ga rashin girma a gidan nan wllh, a kan me xa a debe ma yarinya kaya wannan ai karanta ne wllh, wannan abun kunya har ina kawai a bude lefen yarinya a yashe mata kaya??" Umma da ta shigo parlon tare da Ummi ta kalli Aunty amma bata ce mata komai ba suka fita parlon tare da Ummi Aunty tace "A gaida gida" a compound suka ga Jiddah a tsaye, Umma tace "Ina kayan? Kin kai mota?" A hankali Jiddah tace "Aunty ta karba" Juyawa Umma tayi ta koma parlon, Ummi ta bi ta da kallo sai kuma ta bi bayanta, Umma na kallon Aunty tace "Kayan da kika amsa xa ki bani Hafsah" Aunty tace "Wllh baxan bada ba Hajiya Ramlah, wannan ai ba girmanku bane daukan kayan yarinya, wannan ai karanta ne, ku idan aka ma 'ya yanku haka xa ku ji dadi??" Ummi ta kalli Abuturrab tace "Aliyu" ya daga kai ya kalleta, tace "So nake ka kwashe akwatunan nan gaba daya ka kai su gidan Ramlah da daddaren nan" Aunty tayi wani shewa tana tafe hannu tace "Gidan Ramlah? To ai naga ba Ramlah bace ta hada lefen, don haka xan ga me kwasan akwatuna ya fita da su gidan nan yau...." Shi dai Abuturrab kallon Ummi ya dinga yi ya kasa cewa komai, Hajja ta fito rike da fasasshen flask dinta tace "Me ke faruwa na ganku cirko cirko a tsaye?" Aunty na kallon bakuwarta tace "Xa a tura maki kudin na biyun ki tafi gida kawai Salaha" Daga haka ta bar parlon kamar xata tashi sama, Salahan ta mike ta fita parlon, Ummi na kallon Abuturrab strictly tace "Kaji abinda na gaya maka?" Yayi kasa da murya yace "Ummi duk bai kai haka ba, don Allah..." Wani tsawa tayi masa tace "I said take away the boxes to Ramlah's home" Hajja tace "Naga ikon Allah, na tambayi me ke faruwa an min shiru" Ummi tace "Cewa nayi ya kwashe akwatunan ya mayar gidan Ramlah daga can xa a kai su" Hajja tace "Atohh a kira mai gadi ya fitar da su xuwa motar mana me ake jira" Kallonta Abuturrab yyi fuska daure, Ummi tace "Ya fita ya kira mai gadin da kansa, idan ba haka ba wllh wllh baxa a kai kayan nan ba, kuma kudin da aka kai sai dai a yafe shi...." mikewa Abuturrab yyi yana kallonta, Ummi ta juya ta bar parlon Umma na biye da ita. Hajja ta nufi kofa don kirawo mai gadi tana cewa "Aa bai kai haka ba Hauwa ni da kaina sai in je in kira mai gadin a fito da akwatunan" Abuturrab ya koma ya xauna ya rike kansa ya rasa tunanin da xai yi, mikewa yayi ya nufi bangaren Aunty....


No comments

Powered by Blogger.