Jiddatul Khair 33

 


Abba ya ajiye masa takarda da biro din hannunsa ya koma ya xauna yace "Tunda kana kokwanton auren da ake ce maka babu tsakaninku upon sanarwa da ka dinga yi ka saketa, to ni yanxu na umarce ka da ka kara wanda baxa kayi kokwanto ba a ranka" Kallonsa kawai Abuturrab ke yi kamar bai gane me yake nufi ba, Abba ya daka masa tsawa yace "C'mon my frnd ina sauraronka" Ya sauke idonsa a hankali yace "Toh ai Abba ni bance baxan xauna da ita ba, ban ta6a maku musun xama da ita ba, tuni na riga da na hakura...." Da karfi Aunty tace "Wllh karya kake munafuki... har ce min kayi kawai sbda Abbanka kake xaune da ita bayan ka saketa don kar ya samu labari yayi fushi da kai, kuma mu baxa mu xuba maka ido kuna xaman haram da yarinya ba, banda ma dai ni da na damu da lamarinka, ina ce ranan da na gano irin xaman da ku ke na xo na sanar gwaleni Abbanka yayi, to Alhmdlh ai yanxu tunda Hajiya Ramlah ce ta xo da batun da kanta" a kufule Hajja tace "Waye wannan dallah... Ya xa ki cika ma mutane kunne haka, ita uwar yaro ma ta ja bakinta tayi gumm kamar sabuwar kurma sae ke xaki dinga daga jijiyoyin wuya kina hak'i uwa dai kin hada wani abu da Aliyun, iyakarki fa matar ubansa, waye bai san auren cin amana ku ka yi da Usman din ba, daga dai ke da uwarki kuna fama da bakar talauci kuna tuyan masa da miyar taushe a daya daga gidajen hayana dake Tudun wada, shi kuma Usman na aikesa yaje ya fatattaki wani kato da yaki biyana haya kusan sati uku da karewar kudinsa, shkkn fa mata kika makale ma d'a na har da kullo masa yar wainar shinkafa a leda, to mu muka san abinda aka barbada a kai sai ga Usman ya birkice shi xai kara aure bayan ko shekara biyu da auren wannan Bafillatanar Hauwan bai yi ba, a takaice dai wllh tsallake maganata yayi ya aureki don na hanasa yaki ji ya bada toka a ido xai xageni, to ba dole in yafe masa ba tunda kowa dai yasan ku 'yan Benue ne, Mu dai babu abinda muka sani da ya wuce wannan, to yaushe ma xa a ga haka a Masar? Aa wllh basa haka...." Alhaji Umar yayi kasa da murya yace "Hajja ai ina ga ba wannan xancen muke yi a nan ba, duk ba shine ya kawo mu nan ba" a fusace Hajja tace "Toh don ba xancen ake ba sae in yarda ta gigita min jik'a, ni dai har gobe ina danasanin basu gidan hayata, daki daya ma fa suka kama suke rayuwa a ciki, kafin ma in basu dakin cewa suka yi gidan da suka baro watsi aka yi da kayansu bakin titi a unguwar mu'axu, gashi suka dinga ban wahala da kyar suke biyan kudin hayan a lkcn ma wllh.. to  ni duk na wannan ba don Allah ma bai ce ayi tone tone ba, wanda kuma ya rufa ma d'an uwansa asiri Allah ma xai rufa masa asiri, amma ai an cuci Usman, to kuma ni ance min Aliyu ya auri yar hayi lkcn ina Masar, tsoro ya kamani na fita hayyacina na gigice da naji wannan xance sbda ni nasan ina ne hayi, kuma ni nasan mutanen cikinta, to sae gashi kabiru yace min ae suna xaune lafiya lau da matarsa, hakan yasa na saki raina duk da ban samu xuwa bikin ba, toh ynxu abinda ban gane ba wannan yar farar dake xaune ce yar hayin koko?" Umma tace "Ita ce" Hajja tace "Ikon Allah... toh kai Usman ya kake son kashe masu aure kamar kai ka halicci auren?" Alhaji Umar yace "Hajja babu wannan auren fa yanxu musulinci, don ya riga da ya saketa da bakinsa, sannan kuma ya saketa a rubuce, ni ba mijinki bane ae dai dai yake da na sake ki...." Hajja ta rike ha6a tace "Naga jaraba, a gabanka aka yi sakin kake wnn ciccijewan ko kawai karere, Sannan kana min gatsal gatsal idan shafa'atu ce xaka mata haka yau?" Abba yace "Don Allah Hajjaju kiyi shiru muyi abinda ya kawo mu nan, baki san komai a kan maganar nan da ake a nan ba, yaushe rabonki da kasar??" Hajja ta rungume hannu hade da ta6e baki tace "Nayi shiru, amma mu a masar wa xai yi haka? Wllh ba a haka, ayi aure kuma a dawo ana cewa ya mutu bai mutu ba" Ta gefen ido Abuturrab ya kalli Jiddah da ta kasa dago kanta, Aunty dai ta wani sha kunu a parlon tun bayan xancen Hajja a kanta, ita dai Ummi kallonsu kawai take ba um ba um um, a fusace Abba yace "U are wasting our time Aliyu, saki me hujja nake so kayi ynxu tunda duk wanda kayi a baya baka aminta da su ba..." Ya dago kansa yana kallon Abbansa yace "Abba ni nasan na aureta sannan ina xaune tare da ita saboda inyi biyayya gareka, bayan hakan babu wani abu kuma...." Abba ya katse sa yace "Toh an dauke maka wannan biyayyan, write d divorce now, sai ka tashi ka tafi Allah ya baka ladan taimako, ae kayi me wuyan tunda ka rabota da tsananin da take ciki" Abuturrab bai kuma cewa komai ba, bayan few seconds yace "Yanxu sakin xan rubuta mata?" Abba yace "Ehh, baxa ka mayar da mu kananun yara ba mu xuba maka ido, har yau mun rasa gane xaman me ku ke da yarinya" Abuturrab ya sunkuyar da kansa ya fara rubutu a takardan, d'aga kai Jiddah tayi tana kallonsa, ya gama rubutun ya mike da ladabi ya mika ma Abba, Abba ya amsa yana duba content din takardan, Abba yace "Good, Allah ya maka albarka, ya baka ladan taimako, daga yanxu kuma babu ruwanka da duk wani harka da ya shafeta, xa mu yi mata komai in sha Allah, kai ma kuma kayi iya naka kokarin don ta dalilinka duk muka santa, Allah ya maka albarka...." Abuturrab ya amsa da "Ameen" Sannan ya juya ya fita daga parlon jiddah ta bi sa da kallo, Abba ya nuna ma brothers dinsa biyu takardan, Alhaji Umar yace "To maa sha Allah, kaga yanxu babu wanda xai ci gaba da kokwanton xaman da suke, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, shi kuma Allah ya saka masa ya basa ladan taimakonsa, ku kuma Allah ya baku ikon riketa da gaskiya" Aunty da taji jikinta na wani tsumma don farin ciki gaba daya ta mance abinda Hajja tayi mata sae jiran takardan take ya xo garesu, ai ko ana miko mata bayan ta karanta tayi wani murmushi ta mika ma Umma, Umma ma ta mika ma Ummi bayan ta karanta, Hajja tace "Amma na tsorata da lamarin Aliyu, Kunga da yana sonta da gaske ai kuka xai sakar mana a nan yace shi baxai saketa ba, amma almurin kamar jira yake gashi ya cike takarda da rubutu, aa gaskiya ba sonta yake ba, ku duba fa babu wani gardaman a xo a gani ya rubuta takardan, Lahh wanne mutum a masar, to amma ai shkkn sae a bani ita mu tafi Bauchi don kwana biyar xanyi a can kafin in koma Masar, idan ma kunga xaku iya biya mata jirgi kawai sai mu tafi tare, ai d'a na kowa ne bawa sai mai shi..." Umma ta kalleta da sauri tace "Hajja karatu xa a sata ai" Wani kallo Hajja ta watsa mata tace "Shi kuma masar din duk jahilae ne ba a karatu.... Banda neman magana ina ruwanki Ramlah, ni fa da d'a na nake kika tsomo baki, ko Ahmad ne ya tsintota a hayi?" Ta gefen ido Ummi ke kallon Hajja, Abba yace "Dama haka ake tafiya Masar din Hajja, ina laifin ma kice idan kin tafi a turo ta?" Hajja tace "Kai ba ruwana ni ku rabu dani, xa a Wani min caaa, dangin uwa ko na uba, meye hadina da ita banda Aliyu da ya aurota a gantale ya saketa kuma a gantale, kuma ma wasa nake, haka kawai inje in daura masu nauyi nima da ya ake bani yar gurasar da ake ban balle na tafi da wata?" Mikewa tayi tace "Banda Najeriya ina ake aure a gantale ayi saki a gantale, Hauwa taho ki bani sakon da na baki" Tana kai wa nan ta fita, Ummi ta mike ta bi bayanta, Aunty ta bi ta da harara, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Alhaji xan tafi da Jiddah ta koma gidana ta fara karatu" Caraf Aunty ta amshe tace "Me xai hana tayi a nan din, ga dai sa'aninta su Aisha" Abba yace "Da nan din da can ai duk daya ne, Allah dai ya bata ilimi mai amfani"  Ko kadan Aunty bata ji dadin haka da Abba yace ba, Umma tace "Toh nagode Alhaji, Allah ya tayani riko" Duk suka amsa mata da "Ameen" amma banda Aunty da ranta ya baci, can dai tace "Amma ai xata dinga xuwa nan din ko" Umma tace "Aa me xai hana kuwa" Umma na fadin haka ta mike tana kallon Jiddah tace "Mu je Jiddah" Jiddah ta mike a hankali ta bi bayanta, Aunty ta bi ta da kallon tsana, shi kam Abba tausayinta kawai yake ji, banda rashin gata ya xa ayi hakan ya faru gareta ma. Bangaren Ummi Umma ta kai ta, Ummi na xaune parlonta da Hajja dake mata magana kasa kasa, amma ganin Umma sai tayi shiru, Umma tace "Toh yaya mun tafi sai da safe" Ummi tace "Baxa ku yi isha ba?" Umma tace "Eh to bari inyi" Daga haka ta karasa bedroom din yayarta, Jiddaj dai na rakube jikin kujera, Ummi ta kalleta tace "Kije kiyi sallan ke ma" Mikewa Jiddah tayi ta fita, Hajja ta tabe baki tace "Toh ai gwara ma da aka kashe wannan auren don ai Aliyu d'an usuli ne, ita kuma bamu san yaya ba" Ummi tace "Ai babu wanda bashi da usuli Hajja" Hajja tace "Aa Hafsat dai bata da shi, an rasa gane ko kwatakwali ce har yau, duk da tace uwarta yar Benue ce" Ummi dai bata ce komai ba, Hajja tace "Shi yasa gashi duk ta amshe gida tayi bake bake, komai sai inji Usman yace Hafsa, to wacece kuma Hafsa, dama Hadiza ta bani labarin irin xaman da ku ke yarda ce kawai ban yi ba, gashi duk ta rufe maki baki ta amshe gida, wa ya sani ko ma har da ya yanki? Tunda na xo naga take takenta komai sai ace sai ita, to a kan me?" Ummi tace "Aa Hajja kowa ai da matsayinsa a gidan" Hajja tace "Toh kunga lalacewa ko? Wani matsayi matar da ta kwace maki miji ta karfi, me yasa kike abu sakwa sakwa kamar warce aka ce ma je ki kya gani Hauwa, komai fa na bikin nan naga sai dai ace Hafsat to wacece kuma Hafsat, gashi ana maganan tabargaxan da yaro yayi mata tayi bake bake a kan xancen kamar d'an ta, to ni tunda na xo ma ba sau daya Salem ya shigo gaisheni ba, duk sun tsotsa a nono wllh, dubi fa Aisha kamar yar karuwai Allah na tuba, to ba dai komai tunda duk jikokina ne, amma idan xaki tashi tsaye ki amshi gidanki ki tashi" Fitowar Umma yasa Hajja tayi shiru, Umma tace "Toh sai da safe Hajja, yaya sai mun yi waya" Hajja tace "Toh Allah ya ba yara xaman lafiya ya kauda fitina amma ki dai je asibiti kiga kibar ta mecece kika narka haka kinji" Umma bata tankata ba har ta fita, Hajja tace "Toh sai da safe" Sai da Jiddah ta sake shigowa tayi ma Ummi da Hajja sai da safe sannan suka bar gidan tare da Umma, har driver ya maida su gida Jiddah bata cewa komai, duk tayi sanyi sosai, ta rasa ko farin ciki take ko bakin ciki, Wajen karfe tara Umma ta xaunar da ita a dakinsu Maimoon tace "Kina ji na Jiddah?" Jiddah ta daga kai ta kalleta, Umma tace "Kin dai ga yanda abubuwa suka kasance, ni nasan Abuturrab bai da niyyar cutar dake a ransa, kuma har abada ina son ki daukesa da girma da mutunci don ya maki abinda ba kowa xai iya maki ba a rayuwa, duk abinda xaki xama a rayuwa nan gaba Allah ne ya tabbatar da hakan amma Abuturrab ne sanadi, ina son kuma ki maida hankalinki kiyi karatunki, kin san wacece ke kinsan daga inda kika fito" Hawaye ne ya shiga xarya idon Jiddah tana kallon Umma, Umma tace "Ni kuma ina fatan Allah ya bani ikon yi maki duk abinda ya kamata a rayuwarki Jiddah" Cikin rawar murya tace "Toh Umma baxan sake ganinsa ba kenan?" Da mamaki Umma tace "Don me baxa ki gansa ba, in dai Allah ya kawosa gidan nan ai xaki gansa, sannan xaki dinga yawan xuwa gida Ummi, idan baku hadu a nan ba xaku hadu a can, balle ma nace tsakaninki da shi kawai girmamawa ki daukesa kawai a matsayin babban wan ki, nasan shi ma a matsayin kanwarsa xai daukeki" Jiddah ta share hawayen idonta a hankali tace "Toh Umma nagode" Umma ta sakar mata murmushi, har ranta taji tana son Jiddah tana kuma son inganta rayuwarta, Umma tace "Gobe da safe sai mu je can gidan a kwaso duk wani abu naki" Jiddah ta gyada mata kai kawai, Umma ta mike tace "Toh sai da safe" Daga haka ta nufi kofa Jiddah ta bi ta da kallo wasu hawayen na kawowa idonta, Umma na fita Maimoon ta shigo dakin. Washegari misalin karfe Goma Umma ta kira Abuturrab, miss calls tayi masa kusan uku kafin ya daga, bata amsa gaisuwan da yake mata ba tace "Kana gidanka ne?" Yace "Ina nan" Umma tace "Ohk i am coming now" Bai ce komai ba ta katse wayar, tare driver ya kai su gidan Abuturrab da Jiddah da Maimoon da safiyya, mai gadi ya bude masu gate driver ya shiga da motar cikin compound, Umma ta sauka motar sannan su Jiddah, Hijab ne har kasa jikinta, suka bi bayan Umma xuwa entrance din parlon, a bude suka tarda parlon, yana kwance saman doguwar kujera da jallabiya, suna hada ido Jiddah tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na bugawa da karfi, sanye yake da jallabiya ya mike xaune a hankali yace "Ina kwana Umma?" Tace "Lafiya lau, ya gajiyan jiya?" Yace "Alhmdlh" Maimoon ta gaishesa ya amsa, Jiddah ma tace "Ina kwana?" Sai dai taki yarda ta kallesa, bai amsa ba ita dai ta xauna kasa kusa da kujeran da Umma ta xauna, Umma tace "Jiddah xata debi kayanta na nan ne" Ba tare da ya kalli Umma ba yace "Ohk" Umma ta mike tana kallon Jiddah tace "Mu je" Mikewa Jiddah tayi ta nufi stairs Umma na biye da ita Maimoon ma ta bi bayansu, da ido Abuturrab ya bi su har suka haura sama, Kaf sai da Umma ta kwashe duk abubuwan Jiddah dake dakin, Maimoon ce ke kai wa booth din mota, Ita dai Jiddah na tsaye jikin kofa sai kallonta take, ta rasa dalilin da yasa taji tana son tayi kuka, Umma ta mika mata babban ledan da ta hada duk abubuwan gaban madubi a ciki tace "Ki kai wannan" Jiddah ta karasa ta amsa ta nufi kofa ta fita, a stairs suka hadu da Maimoon, Maimoon tace "Kawo in kai toh" Jiddah ta kirkiri murmushi tace "Xan kai" Maimoon ta shiga dakin ita kuma fita, satan kallon parlon ta dinga yi taga baya nan, ta fita balcony, sosai gabanta ya fadi da ta gansa a xaune kan kujera yana danna wayarsa. Xata sauka stairs din balcony din taji yace "Toh ni dake wa yyi lose?" Ta juya tana kallonsa don bata gane me yace ba, yayi wani murmushi ya mike, speaking calmly yace "Kema kinsan wllh idan ba kaddara ba babu abinda xai hadani dake a rayuwa balle har in aureki bisa kuskure, aurenki da ni babban kuskure ne wanda nayi sbda in taimaki rayuwarki.. banda haka ai ni nafi karfin ki, komai da ya faru ya faru ne sbda haka Allah ubangiji ya tsara, duk da fin ki komai da nayi haka na hakura na xauna same roof dake sbda biyayya da kuma xuciyar musulinci, amma wai har ke xaki je ki sanar ma iyayena na sakeki? Toh yanxu da na maki sakin me hujja akwai wani abu da xai ragu a rayuwata ko kuma wani asara xan yi?" Ita dai kallonsa kawai take ko kiftawa babu, yayi wani murmushin kuma yace "Toh na maki duk abinda na maki saboda Allah ba don ki nuna kin san ni wataran ba, kai ni ko a hanya kika gan ni kar ki ta6a nuna kin ma san ni don kunya hakan xai bani, kiyi wucewarki inyi wucewata, na kuma fi kowa farin ciki da murnan xuwa karshen wannan al'amarin, i am now free like every other...." Jiddah dai kallonsa kawai take bbu ko kiftawa, ganin ya koma ya xauna cikin sanyin murya tace "Toh nagode" Daga haka ta juya ta kai ledan mota... Tare suka fito gidan da Umma bayan duk an kai komai mota, Har sannan yana xaune balcony, Umma tace "Toh sai anjima, yaushe xaka koma aikin" Yace "Anjima in sha Allah" Tace "Toh Allah ya tsare" Daga haka ta nufi mota, Maimoon tace "Sai anjima yaya" Yace "Ohk" Sai da Jiddah ta sauka balcony ta d'an kallesa tace "Sai anjima...."


No comments

Powered by Blogger.