Jiddatul Khair 31

 


Aunty ce ta shigo parlon Ummi duk da mutane da ke parlon ta ra6a xuwa cikin daki, Ummi na ciki tana bada sako, Aunty ta ja gefe ta jira har ta gama bada sakon sannan tace "Jiya kaina ya dau xafi kika xo kina tambayar Jiddah, to kin dai ganta ko?" Ummi tace "Mijinta ne ya dauketa" Still Aunty tayi tana kallon Ummi, trying to assimilate tace "Abuturrab din?" Ummi tace "Eh" Juyawa Aunty tayi ta fita daga dakin xuciyarta na tafarfasa, lallai Abuturrab ya gama rainata... Through out ranan da ya kasance mothers eve Jiddah na gida ita kadai, kuma ko a jikinta, sai yanxu ta gane xaman gidan da take ita kadai ma gata ne ashe, xamanta 24/7 a gida babban Rahama ne gareta, tun da Abuturrab ya ajiyeta ya tabbatar ta shiga ciki ya tafi bata sake ganinsa ba. Karfe shiddah saura na yamma bayan sun dawo daga babban event center din da suka yi booking against tomorrow's dinner, su biyar ne a motar, wani abokinsu Umar ne ke driving motar, Abuturrab na kallon Umar kafin su isa hanyar da xai kai sa gidansa yace "Umar ka samu waje ka ajiye ni a restaurant din gaba..." Ahmad ya kallesa da sauri, kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace "Me xaka yi a restaurant bayan abincin da muka ci yanxu?" Abuturrab ya gyara xamansa babu yabo babu fallasa yace "Eh xan amshi abinci in wuce gida" Ahmad yace "Me xaka je kayi a gida?" Abuturrab yace "Kamar ya me xanyi a gida? Naga it's almost magrib yanxu ko kana nufin saboda gobe daurin aurenka sai in bar gidana in kwana a wajenka?" Murmushi Ahmad yyi yace "Kai dai ka fadi gaskiya, dama Ummi ta shaida min abinda kayi masu, kawai dai baka son ka bar matarka ta kwana ita daya a gidan, shine xaka amsar mata abinci yanxu ka wuce gida" Abuturrab ya d'an yi shiru idonsa a kan titi yana sake comprehending abinda Ahmad ke ce masa, Umar yace "Ni kuwa yau sai naje gidan Captain naga matar nan tasa mun gaisa" Najeeb ma yace "Same with me... matar da har yau ba wanda ya santa" Da sauri Abuturrab yace "To ai tana gidan biki, sai dai idan can xa mu je" Dariya Ahmad yayi yace "Tana gida bata wani gidan biki, mu je kawai Umar ai nasan gidan" Lkci daya mood din Abuturrab ya canxa amma ya kasa cewa komai, Ahmad na nuna ma Umar hanyar gidan har suka isa, horn Umar yayi mai gadi ya bude gate din bayan ya hango Abuturrab da ya sha kunu cikin motar, Umar na parking Ahmad ya fara sauka, sannan Abuturrab, sauran frnds din nasu uku ma duk suka sauka, tafiya kawai Abuturrab ke yi xuwa entrance din gidan, Ahmad na leading din frnds din nasu yana cewa "Wannan ai ba adalci bane ba a sanar maku biki ba kuma a ki kawo ku gidan amarya" Har wani nishadi yake suna dariya da frnds din suna biye da Abuturrab, Abuturrab na shiga parlon ya dinga bin ko ina da kallo, kamshin girki ne ke tashi a parlon wanda ko ina fess alamar har goge goge tayi bayan dawowarta, kitchen ya nufa ya ganta tsaye kusa da gas, ga miya tana yi a gas din, daga sama har kasa yake kallonta, wanda riga da skirt ne na atamfa jikinta amma ba ankon da ta saka da safe ba, har xai juya ya fita sai kuma ya sake juyawa yana kallonta babu yabo babu fallasa yace "Dama kar ki kuskura ki fito daga kitchen din nan" Bai jira cewarta ba ya fita parlor, su Ahmad na xaxxaune parlon har da kunna TV, Najeeb yace "Duk girkin amarya ne ya cika gidan nan haka, ashe yau xa mu kwashi girki" Ahmad ya hadiye dariyar da ke damunsa ganin fuskar Abuturrab, Abuturrab dai bai ce komai ba ya wuce sama, sai gashi ya sauko rike da folded hijab dinta ya wuce kitchen, mika mata yayi yace "Ki fito ki gaishesu, kuna gaisawa kuma ki wuce sama har su tafi kada ki kuskura ki sakko, saura kuma idan kin xo gaishesu ki xube kasa kamar kina neman gafara" amsan Hijab din tayi tace "Toh" ya juya ya fita, bayan ta saka hijab din ta bi bayansa, kanta a kasa har ta karaso cikin parlon, gaba dayansu kallonta suke, ta tsaya nan bayan kujera, sai kuma ta kasa gaishesu a tsaye don bata saba ba, xagayowa tayi ta xauna saman lallausan carpet din ta gaishesu ba tare da ta kalli kowa a cikinsu ba, amsawa suka yi gaba daya Umar yace "Yau Allah yayi xa mu ga amaryar captain, ashe shi yasan me yasa bai ta6a gayyatomu mu ganta ba" Ita dai kanta na kasa, Abuturrab sai danna wayarsa yake bai ce masa komai ba, Ahmad yace "Toh a kawo mana ruwa matar captain" Kallonsa tayi jin muryarsa, ta d'an yi murmushi sannan ta mike ta nufi kitchen, tray ta dauka ta daura ruwan gora uku da glasses hudu sannan ta fito ta ajiye nan tsakiyar parlon, daga kai Abuturrab yyi ya kalleta ganin tayi abun hankali, he was thinking a hannu xata rike goran ruwan ta kawo, Najeeb yace "Toh ni kuma girkin amarya xan ci" Sosai gaban Abuturrab ya fadi, don ko shi bai ta6a cin abinda jiddah ta girka ba, har Ahmad sai da ya ji faduwar gaba, can dai yace "Bayan wanda muka ci yanxu?" Umar yace "Wanda muka ci daban, wannan kuma na amarya ne" Jiddah dai tayi shiru, Najeeb yace "Ko baxa a bamu ba amarya?" Mikewa tayi tana murmushi ta nufi kitchen, Abuturrab ya kalli Najeeb yace "Yanxu fa ka ci abinci bawan Allah, sannan gwangwani daya ta dafa... ba daga kitchen din na fito ba yanxu, ai bata san xa ku xo ba" Dariya Najeeb yyi yace "Sai ta tsam mana a gwangwani dayan, duk wannan kamshin mu tafi bamu ci abincin amarya ba" Ahmad dai bai sake cewa komai ba, Abuturrab ya d'an saci kallon hanyar kitchen din, bai san lkcn da ya mike ya bi bayanta ba, plate ta dauka ta xuba shinkafar, tana tunanin ko a kai xata sa miyan, amma gidan umma taga waje daban ake sa miya idan an xuba ma baki abinci, hakan yasa ta dau wani bowl din me xurfi ta xuba miyan, tunda ta xo gidan bata ta6a girki da nama ba sai ranan, duk da ba wani girki ma take yi ba tun xuwanta, ganin Abuturrab ya shigo kitchen din ya kulle kofa ta juya da sauri tana kallonsa tace "a saman shinkafar xan xuba miyar?" Ya watsa mata wani kallo yace "Ko kuma a sama kaina ba, ke har wani girki kika iya xaki wani xo ki xuba masu abinci maimakon kice babu kare, ni kike son ki kunyata gabansu?? Ko ruwan shayi ma baki bari ya tafasa ballantana ki iya girki me dadi" Kallonsa kawai take ko kiftawa babu, ya nufi tray din da ta daura shinkafa da miyar, ya dau spoon ya debi miyar kadan ya sa a gefen shinkafar ya juya, sannan ya debi shinkafar ya kai baki, ita dai kallonsa kawai take gabanta na faduwa, ya fi second biyar trying to figure out the taste of the food, sai ya ji girkin kamar na gidan Umma, ko don sbda spices din da tayi amfani da ne, wanda umma ta bada a kawo mata, sake dibar shinkafar yyi ya kai baki, da gefen idonsa ya bi kitchen din trying to be sure ba Umma bace ta aiko mata da abincin, bai ga warmer ko wani abu da xai nuna kawo abincin aka yi ba, ya sake diban shinkafar ya kai baki, rungume hannunta tayi tace "Toh xaka cinye abincin ba a kai masu ba ai" cire spoon din yyi a baki da sauri, ya jefa mata wani kallo, ta koma baya ta turo baki, yace "Wa yayi girkin nan?" Bai san lkcn da yayi tambayar ba, sai yaji tambayar made him sound stupid, daukar tray din yyi ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, Najeeb ya sauke ajiyar xuciya yace "Ai har mun cire rai nace su tashi mu tafi kawai" Ahmad couldn't hold it any longer, banda dariya babu abinda yake, Abuturrab ya ajiye masu abincin nan middle of carpet yace "Ae nace maku d'an kadan ta dafa, gashi nan tunda yunwa ku ke ji" Najeeb ne ya fara sauka sannan Umar, shi dai khaleel murmushi kawai yake, Ahmad ya mike ya isa gun abincin ya ci spoon daya gabansa na faduwa, exactly tunanin da Abuturrab yyi shi ma shi yyi, kamar daga gidansu aka kawo mata abincin, komawa yayi ya xauna yana murmushi yace "Nima na ci abincin amarya" Najeeb yace "Kafin ka ci na taka amaryar kenan" Umar yace "Wllh u are missing Khaleel kaji dadin abincin nan kuwa" Tasowa Khaleel yyi shima ya ci spoon daya, sosai suka dinga yabon girkin, shi dai Abuturrab na xaune yana kallonsu, sai da suka cinye abincin duk da ba yunwa suke ji ba, sannan duk suka fita xuwa masallaci, Ahmad ne last din fita, kafin ya fita ya nufi Abuturrab yyi kasa da murya yace "Amma daga gidanmu aka kawo abincin nan ko?" Abuturrab yace "What did u mean?" Ahmad yace "Ba Jiddah bace ta girka" Abuturrab yace "Haka ta ce maka??" Juyawa Ahmad yyi ya bi bayansu Umar, Abuturrab ya mike ya dau tray din abincin ya wuce kitchen, har sannan jiddah na tsaye ta jingina da bango, ya ajiye tray din yana kallonta yace "Wa ya aiko maki da abincin nan?" Ta kallesa, a hankali tace "Abincin ya fi karfin ace ni na dafa ko??" Naxarin maganarta ya shiga yi, ta tattara plates da xata wanke a sink sannan ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Sake kallon pot din miyan yayi ya karasa ya bude sannan ya bude na shinkafar, rufewa yayi ya juya ya fita daga kitchen din xuwa masallaci. Ko da suka dawo mosque sun so Abuturrab ya kira jiddah suyi sallama da ita yace ai sallah take, haka nan ko wannensu ya basa kudi ya bata ladan girki, gefen kujera ya ajiye yace "Ta gode" sannan yayi masu rakiya har bakin mota yana kallon Ahmad yace "Xan shigo da safe in sha Allah" Ahmad ya hararesa yace "Kar ma ka shigo mana" a haka suka wuce a mota, Abuturrab ya juya ya koma cikin gidan, dubu sha biyar ne kudin da ya kirga, bayan kusan minti ashirin ya mike ya wuce sama ya bude kofar dakinta, xaune ya ganta kan darduma, ya nufi gaban mirror dinta ya ajiye kudin yana kallonta ta madubin yace "Gashi nan sun baki, dubu sha biyar, amma ban mance turarena da kika fasa ranan ba" juyawa yyi yana kallonta da kyau yace "Kinsan nawa turaren da kika fasa?" Kallonsa kawai take, yace "Dubu arbain da bakwai kika fasa ranan, don haka xaki ajiye wannan dubu sha biyar din har ki samo dubu 32 ki cika min kudin turarena" Yana fadin haka ya bar kudin gaban madubi ya nufi kofa ta bi sa da kallo, can tace "Toh ka tafi da kudin" Ya juyo yace "Sai kin cika" daga haka ya fita dakin. Karfe tara jiddah na wanke wanke a kitchen ya shigo, bin kitchen din ya shiga yi da kallo, ita dai tunda ta kallesa sau daya ta ci gaba da wanke wankenta, kettle din dafa ruwa ya dauko ya bude fridge ya fiddo goran ruwa daya ya xuba a kettle din sannan ya jona, satan kallonta yayi ganin hankalinta na kan wanke wanken da take, ya kai hannu a hankali ya bude murfin tukunyar shinkafar dake kan gas har lkcn, dai dai nan ta juya yayi saurin sakin murfin tukunyar, dauke kanta tayi ta ci gaba da abinda take, ya sosa kansa, sai kuma ya hade rai yace "Shi kuma sauran shinkafar wa kika bar ma??" Ta kallesa tace "Kai mana" ya kauda kai bayan few seconds yace "Na fara wasa da ke ko??" Bata ce komai ba ta dauraye hannunta bayan ta gama wanke wanken ta dau plate ta nufi gun tukunyar ta debi shinkafar duk da ta ci, ta ajiye pot din gun wanke wanke, ta bude miyar ta sa d'an dai dai da nama yanka uku sannan ta rufe sauran miyan ta dau wani plate me xurfi ta rufe shinkafar da shi ta dau spoon ta nufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita, shafa kansa yyi yana tunanin wani eatry xai kira yyi ordering abinci da daddaren nan a kawo masa, shayi ya hada bayan ruwan ya tafasa sannan ya fita kitchen din, yana haurawa sama ya kalli kofar dakinta sannan ya wuce bangarensa, bude kofar parlon yayi ya shiga sannan ya kulle, still yyi yana kallon plate din dake ajiye kan center table, ya karasa ya ajiye shayin hannunsa sannan ya bude plate din yana kallon abincin, ajiye murfin yyi ya mike, can ya kalli kofa, sai kuma ya xauna, kamar me contemplating sai kuma ya dau spoon din ya fara cin abincin. Washegari karfe takwas da yan mintuna Abuturrab ya bar gidan xuwa gidansu Ahmad, Umma bata amsa gaisuwar da yake mata ba, ya shafa kansa ya wuce dakin Ahmad, Ahmad na ganinsa ya mike yace "Let's talk" Kama hannunsa yyi ya fita suka tafi bangaren Abbansa, Abuturrab dai kallonsa kawai yake, Ahmad ya kulle kofar parlon yace "Me yasa ka dauke jiddah daga gidan su Ummi jiya?" Abuturrab ya hade rai yace "Gani nayi she isn't comfortable, sannan Aunty duk ta bi ta takurata duk ba wanda yace komai, shkkn saboda ba matata bace ita sai in xuba ido a cuceta?" Ahmad yace "Har Ummi ma cutarta take kenan?" Abuturrab ya shafa kansa ya xauna yace "Ni bance haka ba, wllh da kaga yanda na ganta shekaranjiya ko kai baxa ka bada shawaran in bar ta ba, ita Ummi bak'i sun mata yawa, babu abinda xata yi noticing, and Aunty sai aikenta take tana fita titi, what for?? I hate it when someone is being maltreated kai ma ka sani" Ahmad yace "Hmm, ka gano wani abu kuwa Abuturrab?" Abuturrab na kallonsa yace "Me kenan?" Ahmad yace "You are starting to develop feelings for Jiddah, na lura da hakan tun ba yanxu ba, wannan ya wuce tausayi da kwatar mata 'yan ci, gashi kayi gaggawar rabuwa da ita, don babu aure tsakaninka da ita believe it or not, ko da kuwa baka saketa ba shelan da ka dinga yi kana sanar ma kowa cewar ka saketa, ta saku babu wani kwaskwarima... Babu wani aure tsakaninku ynxu Captain, sannan kar ka manta babu idda a kanta..." Katse sa Abuturrab yyi yace "Nigerians have a very very poor thinking mentality, me yasa baxa ku yi koyi da wasu kasashen da suka fi ku wayewa ba, Shikenan ba dama mutum ya nuna rashin jin dadin abun da ake yi ma mace sai ace yana sonta? Ohk fine... Yanxu in xuba ido ayi ta cutarta kenan tunda ba sonta nake ba, ina ce ita ma mutum ce kamar kai, kamar ni, kamar kowa ma? To don me baxan kwatar mata right dinta ba, ko ka mance akan kwato mata right din nata yasa har naje na aureta? Sannan still a kan kwatar mata right din nata ne yasa na datse auren dake tsakaninmu, and duk wannan wa'axin da kake min ni na ta6a bude baki nace maka da aure tsakaninmu ne?? Ko kuma idan ma da auren gaya maka aka ce xanyi" Ahmad yyi murmushi yace "You are just confusing and disorganizing ur self, shi lamarin da ya shafi addini babu wayo a ciki dai, anyway Ummi is jet angry at you, gwara ko koma yanxu ka dau jiddah ka kai ta can gidan tunda dinner xa ayi yau, daga wajen dinner din sai ka wuce da ita gida, gobe Saturday ka kawota yini tunda baxa ka iya barinta a gidan ba, amma kasan me? Kawai ina ji a jikina xamanku tare da ita ya kusa xuwa karshe" Da ido Abuturrab ya bi Ahmad har ya fita. Motoci biyu ne lafiyayyu suka yi parking kofar gida, El-Basheer ya juya yana kallon warce ke xaune bayan mota ta sha glass yace "Toh ai sai ki sauka mun iso" Da mamaki tace "In sauka fa kace, a kan titin xan sauka d'an nan, motoci sun daina shiga get din gidan ne xan sauka a bakin titi" Yace "Toh ai babu wajen parking a ciki, ke baki ga mutane bane...." Tace "Toh ina ruwana da mutane, har yanxu dama Najeriyan bata canxa ba, mu ba haka ake yi a Masar ba wllh, idan ana biki ko wani shagali wllh dai daikun mutane ake gayyata da daddare, sai a tarfa ma kowa yar gurasar alkama a gefen faranti, a daura kofin madara a gefe, idan da yar cinyar kaza a saka a gefe shi ma, Allah ba a taro irin haka kamar ana yunwa, shi Kabirun yasan haka mutane xa su cika gidan xai bada mota a kawoni nan salon in gantale? wllh mu bamu saba haka a Masar ba, a gaskiya idan baxai yiwu ba a juyar dani kawai a mayar dani Bauchi, daga baya kada Usman ya kullaceni sai in dawo inyi Allah ya sanya alkhairi, amma wllh baxan sauka bakin titi ba duk k'ura ta kare min abinda babu a Masar, ko shi Usman din bai san ina hanya ba ai Aliyu ya sani tunda na sanar masa ta waya.... Aa gaskiya ba dole Allah ya sanya alkhairi juya mu koma kawai... Mu ba haka ake a Masar ba, komai bisa tsari ake yin sa" Kashe motar El-Basheer yyi yace "Kinga Hajja idan xaki sauka ki sauka ni xan tafi gun daurin aure ne, ga ki ga gate kice baxa ki sauka ba" Bude baki tayi tana kallonsa, can tace "Aa toh gaskiya Najeriya ba wajen xuwa bane, tunda nake a masar ba a ta6a min rashin da'a irin wannan ba, sun san girma da mutuncin tsoho..." Tana kai wa nan ta ciro wayarta fuska tsuke ta mika masa tace "Kira min Kabirun, ai shi na haifa ba kai ba" Bude motar El-Basheer yyi ya sauka yayi wucewarsa cikin gidan, ta bi sa da kallo baki bude, sai kuma ta sauko ita ma ta bi bayansa. Jiddah ce xaune bedroom din Umma kanta a kasa tana wasa da gefen hijab dinta, Umma tace "Jiddahh" dago kai tayi a hankali tana kallon Umma, Umma tace "Ina sauraronki, idan kika min karya kuma kar ki manta Allah na kallonki, kuma nasan kinsan makomar makaryaci" Lkci daya hawaye ya kawo idonta, Umma tace "Ina jin ki"


No comments

Powered by Blogger.