Jiddatul Khair 21

 


Jiddah ce xaune bedroom din Umma dake mata tambayoyi, ita dai ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Kar kiji komai ki fada min gaskiya Jiddah" Tayi murmushin karfin hali ta dago kanta tana kallon Umma tace "Da gaske ba komai Umma" Umma tace "Kin tabbatar?" A hankali Jiddah ta gyada mata kai, Umma tace "Yace ya kawo maki mai aikin haka ne?" Ta kalli Umma sannan cikin sanyin murya tace "Eh" Shiru Umma tayi tana kallonta don sai take ganin kamar ba gaskiya take fadi ba, tausayin Jiddah take a xuciyarta, ta kwantar da murya tace "Ni baxan ce masa mun yi maganan komai da ke ba Jiddah, ki bani amsan tambayoyina kafin su dawo masallaci yanxu" Jiddah ta kuma wani murmushi tace "Umma na baki amsan ai" Umma tace "Toh kina jin dadin xaman gidan?" Kallonta Jiddah ta dinga yi ta kasa cewa komai, Umma tace "Ina saurarenki..." Lkci daya hawaye ya kawo idonta, dai dai nan aka bude kofar dakin, Ahmad ya shigo tare da Abuturrab, sosai gabansa ya fadi, ya kalli Umma sannan ya kalli Jiddah, Umma dai ta daure fuska tana danna wayarta, Ahmad dai na tsaye bakin kofa bai karaso ba, ya dinga fatan Jiddah ta sanar ma Umma bata boye mata komai ba, Abuturrab ya shafa kansa a hankali yace "Umma dare na yi xa mu wuce gida" Umma tace "Ohk" wasu sabbin hawayen ya dinga sauka idon Jiddah, gaba daya Abuturrab ya kasa nutsuwa, kana ganinsa ka ga mara gaskiya, Umma na kallon Jiddah tace "Tashi ku je sai da safe" Ta kalli Abuturrab tana goge idonta, ya jefa mata wani kallo a fakaice, a hankali ta mike hawaye yaki tsaya mata tace "Sai da safe Umma" Umma bata iya ta amsa ba Jiddah ta nufi kofa, Abuturrab na kallon Umma yyi kasa da murya yace "Sai da safe Sai Umma" Ba tare da ta kallesa ba tace "Allah ya kai mu" Ya kalli Ahmad that is still standing wanda har ransa yake jin hawayen da jiddah take, Abuturrab ya ki ce masa komai ya fita dakin, Maimuna da siyama ne suka dau ma Jiddah abubuwan da Umma ta hada mata tun daxu xuwa motar Abuturrab, Jiddah dai na xaune gaban motar kamar ana dada tunxurata da kukan da take, Abuturrab ya tada motar ya bar gidan, sai a sannan ya sauke ajiyar xuciya, he even love it da Umma taki ce masa komai, har suka isa gida bai ko kalli Jiddah ba,  yana parking ya sauka ya tafi ya kulle gate din gidan ya dawo, tsaye ya ganta jikin motar fuskar nan nata kamar warce aka aiko ma da sakon mutuwa, ya hade rai yace "Ni xan dauko maki kayan naki dake cikin motar" ta juya ta bude bayan motar tana goge guntun hawayenta ta dau ledan hijabs din da Umma tayi mata da warmer din tuwo da miyar kuka da Umma ta sa a xuba mata, da harara ya bi ta yace "Xaki ga ko xaki sake leka kofar gate din gidan nan balle har in kai ki gidan Umma ki samu daman hawayen iskanci" Kamar jiran jin hakan take ta fashe da kuka sosai tana kallonsa tace "Don girman Allah kayi hakuri, wllh kewarta nake bana son in rabu da ita shi sa nake kuka, don Allah kayi hakuri" ko tanka ta bai yi ba ya nufi kofar shiga gidan ta bi bayansa da sauri tana kuka, ko tsayawa bai yi a parlor ba ya wuce bangarensa, ta shiga dakinta ta ci kukanta me isarta bayan ta sannan ta kwanta. Karfe sha daya da kusan rabi yayi knocking kofar dakin ya shiga, ganin tayi bacci ya bude warmer din abincin da ta ajiye kasan dakin, yaga bata ta6a ba duk da yasan ta ci abinci a can gidan, ko kayan jikinta bata cire ba, wannan dalilin ne yasa ya tasheta, mikewa xaune tayi da sleepy eyes dinta tana murxawa, yace "Me ya hanaki wanka kafin ki kwanta?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Dama bakya wankan daren da nace maki kenan?" Da sauri ta bude ido sosai tace "Wllh ina yi bansan sanda nayi bacci ba" Yace "Toh tashi kije kiyi wankan" Kallon agogo tayi da sauri, ya hade rai yace "Tashi nace" A sanyaye ta mike xata shiga bandakin yace "Da kayan xaki yi wanka?" bata ce komai ba, amma ta ki cire kayan a gabansa, ya daure fuska yace "Ba magana nake maki ba" Ta d'an kallesa tayi narai narai da ido tace "Tawul din yana bandaki ne" tana fadin haka ta shige bandakin, gefen gadon ya xauna yana naxarin maganganun da Umma tayi masa a waya bayan sun dawo gida, he is finding it hard to forget her words and move own, yasan no matter what Ahmad baxai ta6a gaya mata xaman da yake da Jiddah a gidan nan ba, yasan baxai ta6a ce mata ma bbu aurensu da Jiddah kamar yanda ya sanar masa ba, but her words carried weight this night, he have a very good intention toward jiddah, ba shi da nufin ya cuceta ko ya walakantata ko ya saka rayuwarta a garari, his intentions are nothing but pure, dafe kansa yyi, lkci daya ya dago jin wayar dake hannunsa yayi vibrate ya duba ya ga Aneesah ce ke kiransa, bai sake kallon wayar ba coz sun yi magana not too long, bayan kusan minti sha biyar jiddah ta fito daga bandakin sanye da kayan da ta cire, kasa kallonsa tayi ta ja gefe ta tsaya, wani kallo ya dinga mata kafin yace "Meye hakan kika yi?" Ta ki yarda su hada ido tace "Ni baxan iya fitowa babu kaya ba bayan kana xaune dakin" Daga sama har kasa ya dinga kallonta yana mamakin abinda ta fada, can dai yace "Ke kina da wani abinda xaki boye min a jikin ki dama, kwaila da ke?" Ta d'an turo baki ta juya masa baya, Tsaki yyi ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo, murya can kasa tace "Eh amma ai ni ba muharramarka bace da xan cire kaya...." Ganin ya juyo tayi tsit, ganin impression din fuskarsa gabanta ya fara faduwa, yace "Kika ce me?" Ta girgixa kai da sauri tace "Ban ce komai ba" Dawowa dakin yyi, ta marairaice tana kallonsa tace "Don Allah kayi hakuri ni bance komai ba" Yace "Kika ce ni ba muharraminki bane?" Ta girgixa masa kai da sauri bakinta na rawa tace "Aa bance haka ba" Sai da ya iso gabanta ya tsaya, sbda tsoro taji ta ma kasa tsayawa, calmly yace "A ina kika san wanda muharraminki ne da wanda ba muharraminki ba?" Jin taki cewa komai ya mata wani tsawa da yasa ta duka hawaye ya kawo idonta, yace "Idan baki bani amsata ba na fara ball dake sai kin ganki downstairs yanxu" Cikin rawan murya tace "Ai da ina xuwa islamiyya" Ya gyada kai yace "A islamiyyan kuma basu sanar maki hukuncin wanda yace xai kashe kansa ba?" Kasa cewa komai tayi, ya wani hade rai yace "Mike ki cire kayanki" Ta sake marairaice masa amma ganin kallon da yake mata ta mike da kyar, ta gefen ido ta kalli bandakinta, lkci daya kamar kiftawan ido ta shige ta sa makulli hannunta na rawa, ya dinga kallon kofar, can yyi murmushi yana shafa kansa, lkci daya kuma ya hade rai ya fice daga dakin, bai karasa bangarensa ba wayarsa yyi vibrate ganin me kiransa sai da gabanaa ya fadi, har ya katse bai dauka ba, sai da aka sake kira sannan ya daga, murya can kasa yyi sallama yace "Ina yini Aunty" ba tare da ta amsa ba tace "Aliyu kana ina??" ya d'an bude ido yace "Aunty ai ina kano, ban dawo ba..." Bude kofarsa yyi ya shiga ya kulle hade da lumshe ido jin abinda take cewa. Washegari da safe wanda Abuturrab ya sa ya samar masa mai gadi ya iso gidan da mai gadin, Abuturrab na kallon matashin mai gadin yace "Yaranku nawa da matar taka?" Mai gadin yace "Daya ne kawai Alhaji, sabon aure ne" Abuturrab yace "Ba damuwa, yau nake son xaka fara aikin sai ka koma ka taho da iyalan naka" Mai gadin ya risina da ladabi yace "Toh nagode Alhaji, xan je kauyen namu yanxu sai in taho da su in sha Allah, Allah ya saka da alkhairi" Abuturrab yace "Ameen, amma kada ka wuce karfe biyar na yamma don xan koma gun aiki a yau" Mai gadin yace "In sha Allah Alhaji" dubu biyar Abuturrab ya basa kudin motar xuwa taho da iyalan nasa, shi ma wanda ya kawo sa ya basa dubu biyar, bayan sun tafi ya koma cikin parlor.... jiddah na kitchen tana dumaman tuwon da umma ta bata jiya, yatsine fuska yyi yana kallon kitchen din don ko by mistake baya son warin miyar kuka, barin ma yanxu da take dumamawa, hakan ya sa ya dau makullin motarsa ya bar gidan xuwa inda xai je yyi breakfast, jiddah na jin fitan motarsa ta jigina jikin bango tunda taji yana waya ko minti sha biyar ba ayi ba yace yau xai koma gun aiki ta ji duk mood dinta ya canxa, gaba daya bata son xama ita kadai a gidan, a sanyaye ta kashe gas din ta xuba tuwon amma ta kasa ci, Duk da xamansa a gidan da rashin xamansa kusan daya don ba wai wani magana me tsayi yake mata ba, kuma ba waje daya ma suke xama ba amma idan yana gidan bata jin kadaici da kewa na damunta, duk sonta da tuwon saboda yanayin da ta shiga sai ta kasa ci da yawa, haka nan ta mike ta kai kitchen ta wanke plate din, sama ta wuce ta wanke bakinta, komai da take yi a gidan tayi, turaren wuta ne kawai bata sa ba, ta dau turaren ta sauka parlor ta sa sannan ta xauna tana kallon yanda yake fita a hankali, kana ganinta kasan jikinta a sanyaye yake, bude kofar parlon aka yi Abuturrab ya shigo ta daga kai ta kallesa sannan ta sauke idonta, sai da ya karaso cikin parlon tace "Sannu da dawowa" Bai amsa ba yyi wucewarsa sama ta gefen ido ta bi sa da kallo har ta daina ganinsa, a sanyaye ta mike ta wuce sama ta shiga dakinta ta kwanta tana kallon fuskarta ta madubin press din dakin.  Da yammacin ranan tana tsaye jikin window aka bude kofar dakin, tunda ta kallesa sau daya ta dauke idonta, yana bakin kofar a tsaye yace "Shuka kika yi wajen nan da kike tsayawa ko da yaushe?" Tana wasa da fingers dinta ta girgixa masa kai, juyawa yyi ta bi sa da kallo ganin jakar hannunsa, da sauri ta bi sa tace "Tafiya xaka yi?" Ya juyo yace "Kina bukatar wani abu ne?" Lkci daya jikinta yyi wani sanyi, shi dai kallonta yake yana lura da ita duk a lkci daya, sauke idonta tayi saboda hawayen da ya kawo idonta, yace "Nace kina bukatar wani abu ne" ta girgixa masa kai hawayen dake makale idonta ya gangaro ta juya da sauri ta koma ciki, da ido ya bi ta, kafin ya bi bayanta xuwa dakin, durkushe ya ganta ta daura kanta saman gado, da mamaki yake kallonta, can yace "Ke kina da lafiya kuwa" kin dagowa tayi tana shessheka, ajiye jakar yyi yana kallonta, can ya karasa kusa da ita ya tsaya yace "Tambayar ki nake, kina da lafiya kuwa?" Still taki dagowa, ya daka mata tsawa yace "Baki ji na ne" mikewa tayi hawaye na kai koma a idonta, ya dinga kallonta kafin yace "Me aka maki?" Ta girgixa masa kai, ya mata wani kallo yace "Me aka maki nace?" Cikin rawar murya tace "Ba komai" rungume hannu yyi yana kallonta, can yace "Kina bukatar wani abu ne" Wasu sabbin hawayen na xubo mata cikin rawar murya tace "Tafiya zaka yi ka barni ni kadai babu kowa, alhalin tsoron gidan nake ji" kallonta kawai yake ya ma rasa me xai ce mata, can dai yace "Shine yasa kike kuka?" Ta gyada masa kai tana kallonsa with tears in her eyes, yace "Ohk, ynxu in tafi da ke kenan?" Tayi shiru still crying tana kallonsa, yace "Bude baki ki bani amsa, in tafi da ke kenan yanxu?" A hankali ta gyada masa kai, daga sama har kasa yake kallonta, tausayinta yake ji har kasan ransa amma bai nuna hakan ba, to ina ma xai kai wannan yanxu wani yayi xaton matarsa ce?? Ta ina xai fara tafiya da ita? Ita dai kanta na kasa, bayan few seconds yace "Ina wayar da na baki" juyawa tayi a sanyaye ta nufi gaban madubi ya bi ta da kallo, har ta dauko wayar ta dawo, ta mika masa, amsa yyi ya shiga call log, yace "Matso" ba musu ta matso kusa da shi tana kallonsa, ya hade rai yace "Wayan xaki kalla ba ni ba" Kallon wayar tayi, ta madubin press din dakin ya kallesu, duk tsayinta iyakarta kirjinsa, jin bai ce komai ba sai kallon wayar take ta daga kai a hankali ta d'an kallesa, ganin inda yake kallo ta kalli madubin ita ma, a hankali ta d'an koma baya ganin dab take da shi ta sunkuyar da kanta, dauke idonsa yyi daga madubin, as if bai son maganan yace "Ga number na nan, duk idan kina son wani abu ko kina da wani magana sai ki danna nan sannan ki sake dannawa ki kirani" Kai kawai ta gyada masa ya jefar da wayar kan gado ya nufi kofa ta bi sa da kallo sabon hawaye na taruwa idonta har ya fita, yau din ma ta waje ya kulle kofar parlon duk da kasancewar mai gadi da matarsa da yaronsu dake gidan yanxu. Kuka sosai Jiddah tayi bayan tafiyarsa, taji komai bai mata dadi a duniyar ynxu, kullum ita kadai kamar mayya a gida babu kowa, tun tana tsoro sosai har tsoron ya ragu, tana sallan isha ko abinci bata ci ba ta kwanta ta takure cikin duvet, nan da nan bacci ya dauketa.... Abuturrab na xaune saman gadon hotel wajen karfe goma da rabi, ya gama abinda yake a laptop ya ajiye yana duba agogon wayarsa, call log dinsa ya shiga har yyi dialing number sai kuma ya katse, mikewa yyi ya kashe wutan dakin ya kwanta yana karanto addu'ar kwanciya, jawo wayar yyi ya d'an yi dube dubensa, sai kawai ya shiga call log din yyi dialing number, he just can't because he have a problem with conscience, abu kadan ke sawa conscience dinsa yyi judging dinsa... Karan wayar ya farkar da Jiddah, bacci ne sosai idonta haka dai ta dau wayar dake saman gadon tayi picking sannan ta kai kunne ta rufe ido bata ce komai ba, jin shirun yyi yaww Abuturrab yace "Ni xan gaisheki" ta bude ido cikin muryar bacci tace "Aa" nan da nan ya gane ta fara bacci, ya dai ce "Me kika ci?" Shiru bata amsa ba, yace "Kee?" Tace "Uhn" yace "Kin yi bacci ne?" Kai kawai ta gyada masa ba tare da tace komai ba kamar yana ganinta, shiru yyi, bayan wani d'an lkci yace "Amma sae da kika yi wanka??" Tuni Jiddah tayi nisa baccinta, bayan few seconds yace "Jeeddarh" jin shiru ya katse wayar kawai ya ajiye sannan yayi rub da ciki nan da nan shi ma baccin ya daukesa. Washegari Jiddah na kitchen yau dai shinkafa da miya take yi tunda ya koya mata yanda ake amfani da blender, ji tayi kamar ana bude kofar parlor, ta tsaya kitchen din tana saurare har taji an shigo parlon, da sauri ta fito, ido hudu tayi da Ahmad tare da Maimoon, kallonsu kawai take da mamaki, ya sakar mata murmushi yace "Toh ko dai mu koma ne?" ta girgixa kai da sauri tace "Aa sannunku da zuwa" Duk suka karasa parlon yana kallonta yana murmushi, Maimuna na kallon Jiddah ita ma tana murmushi tace "Sannu da gida Aunty Amarya" Murmushi jiddah ta kirkira ta karaso ita ma cikin parlon, har ranta taji dadin ganinsu, Ahmad ya xauna yace "Ya gidan Jiddah?" A hankali tace "Lfya lau, ina yini?" Yace "Fine Alhmdlh, dama an kawo mai gadi gidan ne?" Kallonsa kawai Jiddah ke yi kafin tace "Nima ban sani ba ai" Tausayinta Ahmad ya ji, can yace "Toh baxa a kawo mana ruwa ba?" Tashi Jiddah tayi tana murmushi a kunyace ta wuce kitchen ta kawo masu har da lemo, tun jiddah na kin sakin jiki, har daga karshe ta sake gaba daya, Ahmad ya dinga mamaki ganin ashe tana da baki, ga zakin murya kamar zaabiya, sosai Maimoom taji tana son Jiddah, har abinci sai da ta kawo masu, ana kiran azahar Ahmad yace mata xasu wuce don yau ma xai koma Abuja, lkci daya mood dinta ya canxa, Maimoon sai taji tausayinta, makullin gidan Ahmad ya mika mata yace "Su Maimoon xasu dinga xuwa taya ki hira a kai kai idan captain din baya gari so kar ki damu kinji" kasa basa amsa tayi don har hawaye ya kawo idonta, dariya ta basa, yyi kasa da murya yace "Amma fa kar ki sanar masa xuwan mu kinji? Wataran idan naxo tafiya xanyi dake daga gidan gaba daya" Ta gyada masa kai, a haka suka tafi duk yanda ta so daurewa ta kasa sai da tayi kuka. Bayan la'asar wajajen karfe biyar ta gaji da xaman dakin da tsayuwar window ta fito, kallon hanyar da xai kai ta part din Abuturrab tayi, tun ranan da suka fito daga wajen bayan ya nuna mata takarda bata sake bin hanyan ba, tsaye tayi tana ta kallon direction din, can dai ta karasa tana tafiya a hankali har ta isa kofar parlonsa ta bude tana lekan ciki, komai na parlon fess ko alamar datti bata gani ba sai wani kamshi ma da take ji, shiga parlon tayi tana bin ko ina da kallo gabanta ya dinga faduwa, can ta karasa wani kofa da ta gani, bude kofar tayi a hankali tana lekan ciki, daki ne da wani babban katifa da bedsheet a kai, babu abinda bbu a babban dakin, karasawa tayi ciki tana kallon wani table da jirgi a kai, xaro ido tayi tana kallon karamin jirgin, dauka tayi da hannu biyu tana jujjuyawa ta kai idonta tana leka d'an windows din jirgin, hotonsa ta gani jikin bangon dakin da fararen kaya ya rike hula tsaye kusa da wani katon jirgi, a ranta tunani ta shiga yi kilan shi ya ta6a ganin jirgi tunda gashi yayi hoto kusa da jirgin, ita dai a sama kawai suke hangosa dan mitsili, kallon fuskarsa ta dinga yi, lkci daya gabanta ya fadi tana ganin kamar xai iya magana a hoton, a hankali ta juya, taga wani kofa ta karasa ta bude ta ga wani makeken bandaki da abu kamar katon glass a ciki har tana iya hango ciki, kwata kwata bandakin ba irin nata bane, ga shi da girma sosai, ko ina a bushe yake sai kamshi bandakin yake, a hankali ta rufo kofar sannan ta bude wani kofar da ta gani daga can end, xaro ido tayi ganin view din, karamin balcony ne, ta dinga bin gidan da kallo daga kasa wanda ke shimfide da carpet grass ga wasu flowers a gefe, sosai wajen ya mata kyau ba kadan ba, ta kalli wani babban gidan dake opposite dinta suka yi ido hudu da wani dake xaune shi ma a balcony, laptop ne gabansa da drink, shi dai kallonta kawai yake, ta Sunkuyar da kanta da sauri ta juya ta koma ciki ta kulle kofar, da sauri da sauri ta koma dakinta. Daren ranan bayan isha Abuturrab na Abuja a gidansa sbda weather bai bari sun koma kano ba, Aneesah ce xaune kusa da shi a dakinsa, yace "Kince kina da lectures da safe, why not sleep now?" Ta hade rai tace "Toh ae it's not a crime idan nayi bouncing lectures din ko?" Ya gyada mata kai yace "Haka ne...." Lamo tayi ta lumshe ido kusa da shi, ya ci gaba da abinda yake, bayan few minutes ta bude ido tana kallonsa tace "In tambayeka mana captain" Yace "Ina jin ki" tace "This days kamar u are not longer eager being with me, why?" ya buda ido sosai yace "Why do u say so?" Ta marairaice tace "Haka naga alama, or do u have anything in mind?" Murmushi yyi yace "Yaushe rabon mu hadu? It's almost 10 days now" ya ja hancinta yace "And ke kin fiye ma mutum jan aji ne" Rungumesa tayi cike da shagwaba tace "Wallahi ba haka bane, ae kai din ne sai ka xo Abuja kake neman mutum" ya cire hulan kanta yace "Ohh really??" Dariya tayi tace "Aa wasa nake my captain ni kadai...." yyi murmushi yace "In few days time su Abbanmu xa su je gidanku in sha Allah" ta wara ido tace "Da gaske my captain?" Yace "In sha Allah" Rungumesa tayi tace "I can't wait Babynah" ya d'an hade rai yace "Baby kuma?" Dariya tayi sosai tace "Au.. to yi hakuri na manta baka son sunan, amma fa kada wataran ka xo kayi ta rokana in kiraka da Baby" yace "Sai kace wani jariri" Dariya kawai take tana kallonsa don tun ba yau ba tasan bai son irin wannan soyayyan da yawanci yake kiransa da na yarinta, ta daura kanta saman shoulder dinsa tana jin wani sabon sonsa na fixagarta...  Karfe daya saura few minutes Abuturrab ya fito bedroom dinsa bayan yayi wanka ya shirya cikin jallabiya, xaunawa yyi parlor yyi dialing number ya kai kunne, sae da ya katse ba a dauka ba sannan ya kalli agogo, ajiye wayar yyi ya kwanta saman doguwar kujera ya lumshe ido... Throughout week din nan Jiddah bata ji kadaici sosai ba don ranan laraba ma sai da Maimoon ta xo gidan, A ranan kuma Abuturrab yyi niyyar dawowa amma cikin ikon Allah sai bai samu dawowan ba, ranan alhamis Maimoon ta kara xuwa tare da Ramlah da abinci wanda Umma ta basu su kawo ma Jiddar, sosai Jiddah ta sake da su don ba kadan suke debe mata kewa ba, Ramlah ta dinga mamaki kamar yanda Ahmad yyi ganin ashe dai Jiddah na magana haka, ga dariya kamar me, xuwan su ya sa har ta samu confidence din fita suka xaga cikin gidan gaba daya tare da su, a nan ne ma tasan da mai gadi da matarsa a gidan, sai bayan magrib Umma ta aika driver ya je ya daukosu, Jiddah ranta fess ta ci sauran abincin da suka rage sannan tayi wanka tayi isha ta shirya ta kwanta, nan da nan bacci ya dauketa. Karfe tara saura Abuturrab dake xaune hotel room dinsa a kano yyi dialing number nata, har ya gama ring bata daga ba, da mamaki ya dinga kallon wayar, ya sake kira nan ma no answer, sake kira yyi ya sake ringing ya gama ba a daga ba, da yamma ma ya kira sau biyu no answer, a lkcn kuma Jiddah na can compound tare da su Ramlah, ajiye wayar yyi, can ya mike ya shirya within few minutes ya dau makullin motarsa da jakar laptop dinsa ya fita dakin, abinda bai ta6a yi ba xai yi ranan, wato driving to kaduna at night, dama da asuba yyi niyyar komawa kaduna sbda throughout gobe ba shi da duty, amma yanxu yyi deciding din tafiya kawai, sai kusan sha biyu da wani abu Abuturrab ya shiga gida yyi parking mai gadi ya taho da sauri yyi masa sannu da xuwa, amsawa yyi ya wuce ciki, makulli ya ciro ya bude kofar dake a kulle, Jiddah bata mance warning din Ahmad na cewar duk wanda ya xo kar ta mance kulle gidan da makulli bayan ya tafi ba sannan ta boye makullin, bin parlon ya dinga yi da kallo, ya kashe wutan dake a kunne ya wuce sama, kofar dakinta ya bude, kwance ya ganta tana bacci cikin nutsuwa, karasawa cikin dakin yyi still looking at her da wani expression can ya juya ya fice daga dakin ya tafi bangarensa. Washegari da safe bayan Jiddah tayi wanka ta shirya ta fito daga dakinta, cak ta tsaya jin kamar tana jin murya a can daya part din, to ko tv ne a kunne, ko ma ita ce ta ta6a abu da ya kunna tvn ranan da ta shiga dakin bata sani ba, gabanta na faduwa ta fara tafiya xuwa can din a hankali, har ta isa sannan ta bude kofa cikin nutsuwa tana lekan parlon, babu wani tv dake a kunne ta dinga bin parlon da kallo, sai taji ba tv bane karatun qur'ani ne, har xata juya ta d'an yi jim kamar me shakkar shiga ciki, can dai ta karasa ciki tana kallon kofar bedroom din da ba a rufe ba gaba daya, tunani ta dinga yi ko ita ta bar kofar haka jiya, a hankali ta kutsa kai ciki, wani kara tayi a tsorace ganin mutum kwance with short and singlet yana bacci, ta juya da sauri ashe ta mayar da kofar ta ci karo da kofar, wani ihun ta kuma yi ta dafe forehead dinta....


No comments

Powered by Blogger.