Jiddatul Khair 20


Babu kowa babban parlon, Ahmad ya xauna saman kujera yana bin parlon da kallo snn ya kalli Abuturrab yace "It looks very good.. " Kitchen Abuturrab ya nufa ya bude fridge ya dau ruwa, fruits din da ya bar mata na cikin fridge har sannan, ya juya ya fita ya dawo parlor ya xauna yana bude ruwan hannunsa, Ahmad yace "Mu yi magana ta fahimta

Captain..." Abuturrab ya kallesa bayan ya sha ruwan hannunsa, Ahmad yace "Tell me ur plan on this innocent girl" Abuturrab yace "I have no plan then to make her somebody useful in life, daga nan kuma sai tayi aurenta idan ta samu miji...." Ahmad ya masa wani kallo yace "How Captain? By locking her up for days ita kadai a gida?" Abuturrab yace "I wanted enrolling her in a schl but ni fitan ne gaba daya bana so ma, so it's better i get a lady with better teaching qualification ta dinga koyar da ita a nan gida, i will also get another lady da xasu dinga karatun islamiyya tare duk a gida" Bude baki Ahmad yyi yana kallonsa, can yace "Why? Why dont u want her to go to school and islamiyya with her mates?" Abuturrab ya mike yace "Haka nan kawai, ra'ayina ne" Daga haka ya haura sama, Ahmad ya bi sa da kallon mamaki kafin ya kauda kai, a nan kuma yaji ya fara tantama anya Abuturrab ya saki yarinyar nan ma kuwa, but kuma yasan Captain to be someone that is very straightforward in yayi xai ce yayi, idan kuma bai yi ba xai ce bai yi ba, baya karya. Abuturrab na tafiya sama ya kwankwasa kofar dakin nata kafin ya bude, tana tsaye jikin window ta juyo da sauri, suna hada ido ta sunkuyar da kai, yace "Ki sameni kasa" Daga haka ya juya ya fita, Abaya ne jikinta blue, sosai kayan ya amsheta, a kwanaki kadan din nan da take shafa cream da Abuturrab ya siya mata tana wanka da shower gel ainahin haskenta yake kara fitowa ko ina na jikinta yyi smooth, wanda rashin fita ta shiga rana ya kara contributing da kyan fatar nata, slowly ta nufi kofa kana ganinta kasan she isn't happy, yau gaba daya ta tashi da kewan yan gidansu duk da basu ta6a nuna mata so ko na minti daya ba amma har kukan kewansu sai da tayi daxu, Abuturrab na komawa parlor ya xauna, Ahmad dae sai kallonsa yake, bayan some minutes ya mike da sauri  tunawa da yyi ba karamin aikinta bane ta sakko ba hijab, ganinta yayi tana saukowa stairs, Ahmad ya juya yana kallonta, Abuturrab ya koma ya xauna, ta karaso cikin parlon ganin Ahmad ta sunkuyar da kanta ta rakube kasa jikin kujera cikin sanyin murya tace "Ina yini" Yana kallonta babu ko kiftawa da murmushi fuskarsa yace "Lafiya lau Jiddah ya kike?" Tana wasa da gefen mayafinta, ita ma tana d'an murmushi tace "Lafiya lau" Ta d'an saci kallon Abuturrab dake kallonta suna hada ido ya jefa mata wani kallo ya dauke kansa ita kuma ta sunkuyar da kanta a hankali tace masa "Ina yini?" Bai amsa mata ba, Ahmad dake kallonta yace "Amma kin ci abinci?" Cikin sanyin murya tace "Eh na ci" Abuturrab ya kallesa yace "Is that question necessary??" Bai jira cewar Ahmad ba, ya kalli Jiddah babu yabo bbu fallasa yace "To sai anjima, tashi ki tafi" Mikewa tayi ta wuce sama tana tafiya a hankali, Ahmad ya bi ta da kallo, sosai yaji tausayinta har ransa, he can see she is sad, she looks so unhappy, ya dawo da dubansa kan Abuturrab dake hararansa, Daure fuska shi ma yyi yace "Abuturrab ka taimaki yarinyar nan sbda kaga ana neman cutarta right?ka taimaketa because she is sad, frustrated and almost depressed a gidansu, to ka gaya min bambancin gidansu da wannan gidan ynxu, didn't u notice how sad she looks fisabilillah, how on earth will u lock a being for days ita kadai a gida bata ganin kowa, ai sai wani cutar ya kamata wllh, baka san babu abinda ya kai wannan yanayin da ka barta ciki saurin kashe mutum ba ko, she have nobody to share anything with, just reason it fa, ta yaya xata yi ta rayuwa ita kadai, plss think of a more better solution tunda baka son kaita gidanmu ko gidanku..." Abuturrab yace "Idan ta fara karatu she won't look unhappy anymore" Ahmad bai kuma ce masa komai ba, Abuturrab yace "Ni fa can gidanmu xan wuce yanxu" Tabe baki Ahmad yyi ya mike yace "Dama idan abu ya samu yarinyar nan Aliyu kada ka kirani da sunan kana neman shawara ko wani abu" daga haka ya nufi kofa, Abuturrab ya mike ya bi bayansa. Sai bayan isha Abuturrab ya dawo gida, yana shigowa parlor ya kulle kofar parlon ya wuce sama, part dinsa ya fara wucewa ya ajiye ledan hannunsa, sai da yyi wanka ya canxa xuwa pajamas dinsa, mintuna ba da yawa ba yyi yana waya da Aneesah daga bisanni yace "Xan kira ki anjima" Daga daya bangaren ta marairaice tace "Ni ban yarda da xan kiraki anjiman nan dinka ba, just tell me karfe nawa xan sake kiranka" Yace "Wani d'an aiki nake son yi a system, idan na gama ai nace xan kira" A hankali tace "Toh Allah ya sa, but it's always xan kiraki anjima daga nan kuma shikenan sai gobe" Yace "Uhn xan kira don't worry" Daga haka ya katse wayar, mikewa yyi ya dau ledan abincin ya fita bangarensa, sai da ya fara knocking din sannan ya bude kofar dakin ya shiga, kwance ya ganta ta takure waje daya ta rufe har kanta, ya ajiye ledan hannunsa ya karasa ya bude duvet din, rufe fuskarta tayi da hannunta taki juyowa, tsayawa yayi yana kallonta, can yace "Kee" Still taki juyowa, ya hade rai yace "Baki ji na ne?" A hankali ta dago ta mike xaune amma bata yadda ta kallesa ba, kallon idanuwanta da suka yi ja ya dinga yi, can yace "Kuka kika yi?" Wasu hawayen suka taru idonta, ta ki yarda ta kallesa, yace "Ba magana nake maki ba" Ta fashe da kuka ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, da mamaki yake kallonta, ganin irin kukan da take, ya xauna gefen gadon yana kallonta yace "Gaya min me ya faru" Ta girgixa masa kai kawai tana kukan a hankali, dauke kansa yayi, yayi shiru, bayan wani d'an lkci ya sake kallonta yace "Dago kanki ki kalleni" Taki dagowa, ya mata tsawa yace "Dago kanki nace" Da sauri ta dago hawaye na sauka idonta amma ta kasa kallonsa, ya mike ya koma side din da take kallo suka hada ido, a hankali ta sauke idonta, speaking very calmly yace "Toh gaya min me yafaru, kina son wani abu ne?" Ta girgixa masa kai yace "Kukan me kike yi then?" A hankali tace "Babu komai" Bai kuma ce mata komai ba, can ya kalli ledan da ya ajiye yace tashi kije ki dau abinci ki ci, ganin bata tashi ba ya hade rai yace "Tashi nace" Mikewa tayi ta nufi gun ledan ya bi ta da ido, yau ma riga da wandon ne na bacci jikinta, tana isa gun ledan yace sa darduma ki xauna a nan ki ci, ta tafi gun darduman ta dauka sannan ta dawo ta shimfida ta xauna a kai, daurewa kawai take amma ji take kamar ta fashe da kuka, ta bude ledan taga tuwo ne da miyar kubewa irin na ranan, sauke idonta tayi ta kasa kallonsa, ganin bata da niyyar fara cin abincin yace "Malama abinci nace ki ci" A hankali tace "Xan dauko ruwa" Ya mike ya fita xuwa kitchen ya dauko mata ruwan ya dawo, yana ajiyewa ya koma ya xauna, tashi tayi ta tafi bandaki ta wanke hannunta sannan ta dawo ta fara cin tuwon a nutse, shi dai kallonta kawai yake, he just have a special pity for women, bai son ganin hawayensu even by mistake, it get him weak, and sure yasan maganganun da Ahmad yyi masa daxu babu karya ko daya a ciki but he cannot let her stay with his mum or Ahmad's mum, he will get another solution.... Tana gama cinye tuwon daya xata rufe yace "Daya kika gani a wajen?" Ta girgixa masa kai tace "Baxan iya cinyewa ba" Yace "Kara daya" Bata masa musu ba ta fara cin wani dayan, amma bata iya ta cinye ba kuma bai tilastata ta cinye din ba, ta mike ta dau sauran abincin da ruwa ta fita daga dakin, mikewa yayi ya bi bayanta ya xauna main parlor ya kunna Tv, bayan few seconds ta fito kitchen din xata wuce sama ya nuna mata kujera yace "Dawo ki xauna nan" Tace "Xan wanke baki" yace "Je ki wanke ki dawo" Tafiya tayi saman ya maida dubansa kan tv, tana sakkowa ta tsaya tana kallonsa ya nuna mata kujera yace "Xauna" xaunawa tayi, ya ci gaba da kallonsa, tun tana daurewa sbda baccin da ya fara damun idonta gashi ta kasa gaya masa har daga karshe ta d'an kwanta still pretending to be watching d movie da bata ma san abinda ake a nan ba, da haka bacci ya dauketa, duk yana lura da ita amma bai ce komai ba, he gets she's so lonely, abinda ke damunta kenan, shi kuma he doesn't have intention of spending any of his time together with her, yau ma don kawai kukan da yaga tana yi ne yasa ya kasa jurewa, har karfe sha biyu yana kallo parlon, sai a sannan ya tuna da Aneesah da yace xai kira ya lumshe ido ya jinginar da kansa da kujera, sai kusan karfe daya ya bude idon don bacci daukesa yyi a hakan, kallon 2 sitter din da take kwance yayi yaga baccinta kawai take, mikewa yyi ya kashe switch din wutan parlon gaba daya sannan ya kwanta kan 3 sitter ya kashe tv da remote din kusa da shi ya lumshe ido.... Kiran sallahn farko Abuturrab ya tashi, ya fi minti goma xaune kafin ya duba wayarsa ya kunna fitila yana haskata, mikewa yyi ya karasa inda take kwance ya buga kujeran a hankali, bude ido tayi da sauri yace "Tashi ki wuce sama" tana lullumshe ido ta mike xaune sannan ta tashi ya haska mata hanyar stairs, ta fara tafiya sannan ya bi bayanta, tana shiga dakinta ko rufe kofar bata yi ba ta fada kan gado ta ci gaba da baccinta, yana tsaye daga bakin kofar bayan ta shiga, ya kulle kofar sannan ya wuce bangarensa. Sae kusan karfe tara da rabi Abuturrab ya sauko downstairs, kamshin girki kawai yake ji a gidan, ya tabe baki ya xauna saman kujera, sae ga ta tafito kitchen, turus tayi ganinsa, sae kuma ta juya ta koma kitchen din, shi dai idonsa na kan tv da yyi powering, can sai ga ta ta fito ta karaso cikin parlon, kallonta yyi... Her expression today isn't of someone that is sad, ta xauna kasa ta sunkuyar da kai, dimples dinta na lotsawa tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya lau" Ya gane da magana a bakinta ganin yanda take wasa da fingers dinta, can yace "Me xa ki ce?" Ta kallesa tace "Dama cewa xan yi in kawo maka kumallo?" Da mamaki ya dinga kallonta, can yace "Na me kenan?" Tace "Dankalin turawa na soya na soya kwai, sai na tafasa ruwan shayi" Yace "Ohk mun yi da ke xan ci ne?" Ta girgixa masa kai yace "Toh baxan ci ba, kayan abincin da kika gani a kitchen don ki girka ke kadai na siyosu na ajiye ba don ki girka ma ni da ke ba" Sunkuyar da kanta kawai tayi, bayan few seconds ta mike a hankali xata bar wajen yace "Tsaya" Tsayawa tayi amma bata yarda ta kallesa ba, yace "Dama kin iya soya Dankalin da kwai kike tsayawa da yunwa?" Bata ce masa komai ba, ya tabe baki yace "Je ki" Juyawa tayi ta koma kitchen din. Tana komawa ta fara kuka a hankali, sae da tayi me isarta sannan ta goge idonta ta fito xata wuce sama, ya bi ta da kallo yace "Kin karya?" Ta gyada masa kai xata haura sama yace "Dawo nan!" Ji tayi wani sabon hawayen na shirin xubo mata, ganin tsayawa tayi yace "Ba kya ji na ne?" Dawowa tayi ta sunkuyar da kanta, yace "Wuce ki xuba abinda kika yi ki xo nan ki xauna ki ci" xata yi magana ya jefa mata wani kallo, kitchen din ta nufa trying hard kar ta fara rusa kuka, a haka ta debo abinda tayi ta dawo parlon ta xauna tana turawa da kyar yana kallonta yana kallon TV sai da ya ga ta gama sannan ya bar ta ta wuce sama, shi kuma ya fita xuwa siyo fastfood.... A ranan mutumin da Abuturrab ya sa ya nemo masa mai gadi amma mai mata ya kirasa ya sanar masa an samu, Abuturrab ya masa izinin kawosa gida amma wajajen biyar na yamma. Yana xaune parlor yana jiran Jiddah bayan azahar, he is been sitting for almost 20 mins now, daga cewa ta shirya shine har ynxu, mikewa yayi ya haura sama ya bude kofar dakin suka kusa cin karo don xata fito ne ita ma, ta koma baya da sauri, ya wani hade rai yace "Baki da hankali ne xaki shanya ni a parlor?" Ta marairaice tace "Na kasa rufe rigar ne?" Yana kallonta daga sama har kasa yace "Wani riga?" Hijab ne jikinta har kasa sai atamfa daga ciki, tace "Zip din rigar" Ya jefa mata wani kallo ya juya, bin bayansa tayi, har suka sauka parlor, ya dau makullin motarsa ya nufi kofar fita ta bi sa da sauri, yana cikin motar ta  iso parking space din xata bude back seat yace "Kinsan meye ma'anar mutum ya shiga bayan mota bayan su biyu ne kawai a motar?" Tayi shiru tana kallonsa, bai kuma ce mata komai ba, ta xagayo xata shiga motar sai a sannan ya ga how obvious zip din da bata kulle ba yayi cikin hijab din, bayan ta shiga gaban motar yace "Daga hijab din nan" a hankali tace "A bude zip din yake" ya hade rai yace "Daga nace" kamar warce xata yi mugun abu ta fara daga hijab din, sai kuma ta kallesa kamar xata yi kuka, ganin yanda ya hade rai ta daga hijab din kawai, bayan ta yake kallo da bra strap dinta, ta sunkuyar da kanta, yace "Da a haka xaki bi ni don baki da hankali?" Ta girgixa masa kai, yace "Koma ki canxa kayan" Ta buda ido tana kallonsa, ganin irin kallon da yayi mata ta bude motar ta sauka, sauka yyi ya bi bayanta to check another clothe for her, sai bayan da suka shiga parlon ta kallesa tace "Xaka iya taya ni jan zip din fa, ba lalacewa yayi ba" yace "Ban yi niyya ba" bata kuma cewa komai ba ta wuce sama ya bi ta. Bude press din nata yayi yana kallon kayan ciki, abaya baki ya ciro mata da mayafinsa ya ajiye gefen gado, ta dan xaro ido tace "Wannan ai yana kama jiki" ya harareta yace "Baya yake kamawa ba jiki ba, minti uku na baki ki canxa kayan nan ki dawo kasa ki sameni" Bai jira cewarta ba ya fice daga dakin nata dake ta kamshin turarurruka, a balcony ya tsaya yana jiranta, sai gata ta fito, sosai bakin abayar ya haska farin fatarta ta dawo kamar balarabiya, flat show ne kafarta, she looks so beautiful and neat, kawai dai ta rame ne ba kadan ba, ganin ta tsaya ta wani sunkuyar da kai yace "Tsayuwar me kika min a nan?" Tafiya ta fara yi, ya bi ta da kallo kafin ya bi bayanta, front seat ta bude ta shiga, sai da ya fara bude gate sannan ya dawo ya shiga motar suka bar gidan, ya sauka ya kulle gate din, gidansu Ahmad ya nufa don xuwa gaida Umma, ya lura kamar she is a bit angry at him, don gashi wannan satin ma bata ce masa xata xo ba, a parking space din yayi parking, Yana sauka motar Jiddah ma ta sauka tun da taga gidan da suka shigo farin cikin fuskarta ya kasa boyuwa, shi dai ko kallonta bai yi ba, kallonsa tayi a d'an tsorace bayan ta sauka tace "Don Allah xan iya xuwa in gaida maman Abdallah?" Ya fara tafiya xuwa cikin gidan yace "Ki je mana" Da sauri ta nufi dakin Maman Abdallah, sai da ta gaida mai gadin ya amsa da fara'a yana mata sannu da xuwa tace "Maman Abdallah fa?" Yace "Ki shiga tana ciki" Da sallama ta shiga dakin, Maman Abdallah na ganinta ta rungumeta cike da farin cikin ganinta tace "Idonki kenan Jiddah, kai kai kai kinga yanda kika yi kyau kuwa, sannu da xuwa amarya" Wannan kalmarta na karshe ne ya d'an sa mood din jiddah ya canxa don tasan dai ita ba amarya bace, Xaunawa tayi tana ta kirkiran murmushi tace "Abdallah na bacci" Maman Abdallah tace "Wllh kuwa, ashe ku ne kuka shigo gidan a mota, sannunku da xuwa" Jiddah na ta murmushi tace "Bari inje in gaida Umma" Maman Abdallah tace "Toh maxa ki tafi, amma fa don Allah ki leko kafin ku koma kinji?" Jiddah tace "Toh" fita tayi dakin dai dai sanda Ahmad ya shigo compound din, ya buda ido sosai ganinta, sai kuma ya hango motar Abuturrab, da ladabi ta gaishesa ya amsa da fara'a yace "Yaushe ku ka xo?" Tace "Yanxu muka shigo" yace "Maa sha Allah sannunku da xuwa" Tafiya take yana gefenta shi ma yana tafiyan, can yace "Amma baki da damuwa ko Jiddah, kar ki boye min komai ki gaya min" Ta sunkuyar da kanta cikin sanyi tace "Ina son dawowa nan wajen Umma" Shiru yayi bai ce komai ba, don yasan taurin kan Abuturrab ya wuce ya amince Jiddah ta dawo nan gidan, a hankali yace "Kar ki damu Jiddah, nasan xama ke kadai ne baki so ko?" Ta gyada masa kai, yace "Kar ki damu nasan me xanyi" Da damuwa tace "Amma kar kayi masa magana ihu xai yi min" Murmushi Ahmad yyi yace "No baxan yi masa ba" Abuturrab suka gani bakin kofa tsaye alamar lkcn ya iso wajen ganin jiddah bata shigo ba, Jiddah sai da taji gabanta ya fadi ganinsa, shi kuwa sai ya hade rai, suna isa balcony din Ahmad yace "Sai ga amarya yau ta xo gidanmu, kun xo gaida Umma kenan" Abuturrab da yayi masa wani kallo underneath his breath yace "Half-wit" daga haka ya juya ya koma parlon. Rungume Umma jiddah tayi, sosai tayi farin cikin ganinta kamar yanda Umma ma taji dadin ganinta, Shi dai Abuturrab na yi yana kallon agogo don bai ma son la'asar yayi masu a gidan, Kitchen Jiddah ta tafi bisa umarnin Umma na cewa taje ta taya su Siyama da mai aiki girki, Umma na kallon Abuturrab tace "Why is she this lean? Bata da lafiya ne?" Ya sunkuyar da kansa yace "Eh tayi xaxxabi kwana biyu, amma ta samu lafiya yanxu" Ahmad dai sai wani kallo yake masa, Da damuwa Umma tace "Toh Allah ya sauwake, ita kadai din ce a gidan kenan yanxu?" Da sauri yace "Aa Umma ai nace akwai me aiki, kuma ma yawanci one day on, one day off nake yi" Umma tace "Toh shkkn Allah ya taimaka, karatun fa?" Yace "Xata fara in sha Allah" Umma tace "Toh maa sha Allah, Allah ya taimaka" Abinda Abuturrab bai so bane ya faru don sai da la'asar din yayi yana gidan, dakin Ahmad ya tafi yin alwala, Ahmad dake ta jiran ya shiga alwala ya jawo makullansa na gida bayan ya shiga bandaki, cikin few seconds yayi abinda xai yi ya ajiye sauran sannan ya fita dakin....


No comments

Powered by Blogger.