Jiddatul Khair 18

 


Jiddah ce tsaye kitchen  bayan magrib tana ta kallon kayan abincin dake cikin store, yunwa take ji tun daxu amma bata san me xata girka ta ci ba, gashi tsoron gas din take, don yace mata yana kona mutane idan ba a maida hankali wajen amfani da shi ba, a hankali ta bude fridge tana kallon ciki, lemo ne a ciki da ruwan gora, sai apples, grapes, banana da dai wasu fruits din a ciki, a hankali ta rufe ta bude deep freezer, taga naman cow, kayan ciki, kifi, da naman kaza, a hankali ta rufe shima, kwalin indomie da ya riga ya bude mata ta nufa ta dau daya a ciki, ta bi tukwanen dake ajiye da kallo snn ta dau wani karami, da kyar ta iya kunna gas din tana ja da baya don duk a tsorace take, ganin wutan ya dawo kamar na risho da take gani gidan iyah yasa ta daura tukunyar, tun da take idan banda icce da gawayi bata ta6a girki a kan wani abu ba, ba ita ta bar kitchen din ba sai ana isha a masallaci, ta cika ma indomien uban ruwa sai swimming yake a plate din, da kyar dai ta tuttura ta cinye indomien da bai mata dadi ba a baki don ita bata ta6a ci ba ma, tura plate din tayi hawaye ya kawo idonta don kewar tuwon masara take da miyar kuka, cimar da ta saba da kenan iya rayuwarta, don ko shinkafa kwana biyun nan da take ci duk taji ya isheta. Abuturrab na kwance hotel room da ya saba sauka, dawowarsa kenan daga eatry yaje ya ci abinci, vid call suke yi da Aneesah wanda har yanxu bata san abinda ke faruwa ba, bai yi mamakin da har lkcn Aunty bata sanar ma kowa ba, tunda ita bata yarda da auren ba dama from start, Aneesah na kwance saman gado daga ita sai wata yar rigar bacci, komai na jikinta na waje, ganin yanda Abuturrab ke lumshe ido tace "Kar kace min har ka fara jin bacci My captain" Ya bude idon yana kallonta yace "Sure, i will be piloting 8am flight tomorrow in sha Allah" Ta marairaice tace "Wllh ban gaji da jin muryarka ba mine" a hankali yace "Yi hakuri, early to bed early to rise..." Tace "Toh shkkn sweetheart, sleep tight, and dream of me" Ya kashe mata ido sannan ya katse wayar, har ya ajiye ya juya baya hade da lumshe ido sai kuma ya bude idon a hankali ya jawo wayar, dialing number yyi ya sa handsfree yana kallon screen din, Jiddah ta kwanta kenan ta takure waje daya tsoro duk ya cikata, da ta tuna ita kadai ce gidan sai hankalinta yyi mugun tashi, ko wutan dakin ma taki kashewa kamar yanda yyi instructing dinta, sai taji kamar abu na motsi a dakin, ring din wayar dake gaban madubi yasa ta mike a mugun firgice tace "Wayyoo Allah na, nq shiga uku" Sosai jikinta ya dinga rawa tana kallon wayar, sai kuma ta nufi gaban madubin ta dau wayar tana kallo, button din left side din ta danna, tunda iyah na da waya kuma ita ke daga mata ma idan ana kiranta, Shiru Abuturrab yyi yana kallon wayar tasa bayan yaga ta dauka, can jin bata ce komai ba yace "Kin ci abincin ko ba ki ci ba?" Ta sauke idonta kasa a hankali tace "Na ci" Bai ta6a xaton xata yi magana da irin wannan natsuwar a waya ba, can yace "Me kika ci?" Tace "Taliyar indomie" Yace "Ohk.... Sai da safe" Da sauri tace "Ka kai lafiya?" Yace "Eh" kamar xata yi kuka tace "Amma ni tsoro nake ji wllh" yace "Tsoron me?" Ta fashe masa da kuka kamar jira take tace "Ni kadae fa a gidan, gashi sae inyi ta jin motsi" Ya gyara kwanciyarsa, calmly yace "Ehh dodon da na ba ajiyar ki ne ke motsi, ko kar yayi??" Ta wani gwalo ido tana bin dakin da kallo tana sake maimaita abinda yace a ranta, ko ina na jikinta ya dau 6ari a lkcn, cikin rawar murya tace "Dodo fa kace?" Yace "Ehh ko dai ya bari kin gansa ne?" Wani ihu ta kwala da ya sa shi mikewa xaune da sauri, ta rushe da wani kuka tana salati, da sauri yace "Ke wasa fa nake maki" ko sauraronsa bata yi ba ta cika masa kunne da kuka, tsayar da kukan tayi ganin duhu ya gauraye ko ina na dakin, da ta dage ta kara kwala wani ihun sae da Abuturrab ya mike tsaye, cikin bargo ta shige har sannan wayar na hannunta tana rusa kuka, Abuturrab ya dinga cewa "ki tsaya ki saurareni nace maki wasa nake, i am only joking" ko ina na jikinta na rawa cikin tashin hankali tace "Wllh ya kashe wutan gidan, na shiga uku na, don Allah ka xo ka taimake ni, xan iya mutuwa ni kadai" Komawa Abuturrab yyi ya xauna jin tace ba wuta, gaba daya ya mance ya gwada mata yanda xata dinga kunna solar idan an dauke wuta, yayi kasa da murya yace "Ki saurareni nace, ni wasa nake maki, wa yace maki akwai dodo a duniyar nan, ke baki san wasa ba? babu komai fa wuta kawai suka dauke, ko ba a dauke wuta a Hayin ku??" kuka kawai take tana shessheka tace "Don girman Allah ka dawo ka fitar dani a gidan, ni wllh baxan iya kwana ni kadai ba, Allah baxan iya ba" Hade rai yyi sai dai bai ce komai ba, jin yanda take rera kuka da karfi, yyi kasa da murya yace "Kinsan inda nake da kike cewa in dawo ynxu" Taki ce masa komai sai kuka, cikin kwantar da hankali yace "Wllh babu komai kawai zolayarki nake yi, amma tunda kina tsoro shkkn baxan kashe wayar ba har gari ya waye, idan da wani abu sai ki min magana, kina ina yanxu?" Tana shessheka a hankali tace "Ina kan gado" Yace "Toh kwanta" Ta gyada masa kai tace "Na kwanta" Yace "To kulle idonki" Cikin rawar murya tace "A kulle yake ai" Yace "Toh fara bacci" Yana jin yanda take kuka a hankali, ya lumshe ido ya bude, can yace "In kashe wayata ne?" Da sauri ta bude ido ta girgixa masa kai tace "Aa don Allah" Yace "Toh daina kukan nan" a hankali tace "Na daina" Yace "Kiyi baccin ki, ni karatu xan yi..." tayi shiru bata ce komai ba tana sauke ajiyar xuciya, jingina yyi jikin pillow ya fara karantun Al-qur'ani cikin cool and calm voice dinsa, tun jiddah na jin sa har bacci ya dauketa, ya kai ayar karshe a suran da yake karantawa, shiru yyi.... bayan few seconds murya can kasa yace "Jeedderh" jin shiru ya kara tabbatar da tayi bacci, a hankali ya katse wayar ya sauke ajiyar xuciya sannan ya kwanta yana karanto addu'a.... Kiran Sallan asuba ya farkar da Jiddah, ta mike xaune da sauri tana bin dakin da kallo da hasken fitilun ciki ya haska tarrr, kallon wayar dake kusa da ita tayi ta dauka ta danna tana kallon screen din, a hankali ta mayar ta ajiye sannan ta mike, kamar me tsoron tiles din dakin ta sauke kafarta sannan ta mike tsaye, dodon da yace mata ne ya dameta a rai, amma kuma yace wasa yake, cikin sanda ta nufi bandaki ko rufewa bata yi ba tana leko dakin ko xata ga abu me kama da dodo... Karfe tara da yan mintuna Abuturrab na lagos bayan sun sauka kiran Ahmad ya shigo wayarsa, kallon screen din ya dinga yi kafin ya dauka daga karshe, Ahmad yace "What nonsense Aliyu, ni na turaka hayi kayi ma kanka aure da xan dinga kiranka ka ki dauka all this while?" Abuturrab yace "Ka kirani ne ka ci xarafina daga inda ka tsaya?" Ahmad yace "Abinda ya fi xarafi... Ance maka farin ciki nayi da auren nan naka Captain, ae ko a mafarki ban ta6a tunanin xaka riga ni aure ba, which means xaka riga ni fara ajiye iyali, may be next year warhaka duk muna gidanka suna, to kaga kuwa ae ni ba haka na so ba, tunda ni aka fara sa ma rana" rasa abinda xai ce masa Abuturrab yyi sae bin mutanen cikin eatry da yake xaune yake da kallo, har ransa yaji xafin abinda Ahmad ke gaya masa, gashi ya ma rasa amsan da xai basa, Ahmad da tsaf ya san ya kular da abokin nasa, ya dinga dariya kasa kasa kafin yace "Toh ya Amarya me sunan Umminmu, ka dai min bakin cikin xuwa ganinta a gidanka kafin in koma aiki, hope a hankali dai ake cin amarcin??" Abuturrab ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya cire wayar a kunnensa ya yi tapping button din katse kira sannan ya jefar da wayar kan table din gabansa, ya jingina da kujera xuciyarsa na ci gaba da tafarfasa, haske wayan ya sake yi ganin El-Basheer ke kiransa ya dinga kallon wayar bbu ko kiftawa, har ya katse bai yi attempting din dagawa ba, he knows the news of his marriage has circulate, but what's d essence, auren da babu yanxu.... Mikewa yyi daga bisanni ya dau wayar da ruwan gora ko breakfast din bai cinye ba ya fita eatry din back to airport. Yana Abuja that same day da rana, which in few hours xa su yi piloting xuwa port Harcourt, kasa daurewa yyi ganin da sauran lkci sannan Co-pilots dinsa suna preflight preparations kawai ya fita xuwa hospital din da Ahmad ke aiki, many patients ne xaune reception din hospital din, ya nufi gun wata nurse bayan sun gaisa yace "Dr Ahmad na nan?" Tace "Eh, do u have any appointment with him sir?" Abuturrab yace "Yea ynxu muka yi waya..." Daga haka ya nufi hanyar office dinsa, nurse din ta bi sa da kallo, can tace "But he is attending to a patient" ko juyowa bai yi ba har ya isa kofar office din ya murda, Ahmad na xaune attending to his patient, ya daga kai, ganin Abuturrab ya bude ido, Abuturrab bai ce komai ba ya nemi kujera ya xauna, murmushi kawai Ahmad ke yi har ya sallami patient din ya fita, sannan ya kalli direction din da Abuturrab ke xaune, smiling broadly yace "Latest ango in town" mikewa Abuturrab yyi yana kallonsa yace "In ur life Ahmad.... I mean in ur life don't ever abuse me the way u did earlier today, i felt really bad at that" Ahmad ya masa Wani kallo kafin ya fara dariya irin wanda ke kufular da mutum yace "Toh Alhaji Ibrahim, ae da ka xo da bulala koh?" a fusace Abuturrab yace "You caused me all this mess sannan ka fi kowa yi min dariya?? Who does that Ahmad?" Ahmad ya buda baki hade da xaro ido yace "Ta yaya na janyo maka?" Abuturrab na huci yace "Ohk, i will tell u now, ka xata da baka fara kai ni gun yarinyar nan ba da akwai wani abun da xai hadani da ita balle taimakona ya dawo min sharri?" Ahmad yace "Da na kai ka gun yarinyar sai nace ka xaga ka bi ta baya ka dinga xuwa wajenta ba tare da na sani ba? Ina ce ranan har Umar sai da yace yana ganinka a unguwar Hayi ka mu sa don kada ma in dago komai" Dariya sosai Ahmad yyi har da gyara xama yace "Gaskiya na dade banga me abun dariya irin ka ba Captain, da naje siyan awara sai nace ka dinga xagayawa kana xuwa gun me awara?? just take a look at the distance daga cikin gari xuwa Hayin rigasa amma haka kullum kake jan motar kaje shine xaka xo nan yanxu kayi wani blaming dina, ni da ma aka munafurta ana ta xuwa tadi ta baya ban sani ba, ban ji haushi ba sai kai?" Kallonsa kawai Abuturrab ke ta yi yana jin kamar ya shakosa, Ahmad ya sake wani shegen dariya har da buga table yace "Toh ai dai yanxu ka rigani sanin aure hankalinka ya kwanta, mu ma Allah ya nuna mana namu da wuri wuri haka..." Komawa Abuturrab yayi ya xauna xuciyarsa na mugun tafarfasa, Ahmad sai satan kallonsa yake yana yar dariya, Calmly Abuturrab yace "Dama Aunty na yawan tagging taimako da xama sharri a rayuwar nan, and i have seen that clearly now don ya faru a kaina, assuming i ignore and act as if i didn't see anything da duk hakan bai faru da ni ba, kuma am making this vow today.. ni Aliyu duk inda na ga wani na neman taimako idan ya wuce na kudi, shi ma kudin sai nayi naxari me xurfi a kai, to wllh wllh i will never ever render that help" Ahmad yace "Calm down man, wannan taimakon fa bai xame maka wani sharri ba illa ma lada me yawa da ka kwasan ma kanka idan Allah ya yrda, da ma nine na kwashi wannan ladan wllh, i cant imagine how happy i will be, sannan sharrin dake ciki a naka tunanin ba dai auren yarinyar dake kanka bane??" Abuturrab na kallonsa da kyau yace "Babu wani aurenta a kaina yanxu, ni d'an iska ne da xan bar aurenta a kaina" Da mamaki Ahmad ke kallonsa, can yace "Ban gane ba" Abuturrab yace "U heard and assimilate me right, babu wani aurenta a kaina" Ahmad ya mike yana kallonsa da mamaki yace "Kana nufin ka saketa Aliyu?" Abuturrab yace "Toh me xan jira, ko don dariya da jest making irin naka da mutane ire iren ka ai dole inyi hakan in samar ma kaina kwanciyar hankali" Ahmad ya fito ya xauna gefen Abuturrab on a serious note yace "Stop it plss captain, da gaske ka saketa?" Abuturrab yace "To wai jiran me xan yi, idan ba ina da intention din auren nata bane dama, i have nothing to do with that girl as a wife, gwara kawai in xama guardian dinta, and that's what i am doing right now..." Ahmad ya dafe kansa yace "Ya salam... amma da baka yi haka ba Captain, why will u do that pls???" Abuturrab yace "You are not to tell me what to do and what not to do, so ka ke in cuci kaina in kwari kaina, ina aka ta6a irin wannan taimakon, i just have to saboda kwanciyar hankalina" Kallonsa kawai Ahmad ke yi gaba daya expression dinsa ya nuna ko kadan bai ji dadin sakin jiddah da yace yayi ba, Bayan few seconds yace "Kuma ta sani, i mean ta san ka saketa?" Abuturrab yace "Of course a gabanta nayi na mika mata sannan na amsa na ajiye" Ahmad ya girgixa kai yace "Wllh banji dadin hakan ba Abuturrab" Wani kallo Abuturrab yayi masa sannan ya ja tsaki ya mike ya nufi kofa, Ahmad ya bisa da kallo yace "Amma kuma xamanku a gida daya baxai ta6a yiwuwa ba, ko don hakan ma ni da kaina xan sanar ma su Umma cewar babu aure tsakaninka da Jiddah, I can't pretend over this in cuceta, idan baka san addini ba ni na sani" Dawowa Abuturrab yyi yana kallonsa da kyau, calmly yace "And this will bring the end of our friendship Ahmad, i told you my secret because i trust u, and I'm sure u won't betray my trust, addini kuma da kake cewa ina ga sai dai mu goga a kan saninsa da ni da ke, bbu abinda xaka nuna min... Baka isa kuma ka koya min yanda xanyi da rayuwata ba" Daga haka ya nufi kofa ya fice ya kulle masa kofar. Daren ranan Abuturrab na xaune hotel room dinsa dake kano after isha yana shan shayi a hankali, tunawa yyi daxu da yamma ya kira wayar wajen Jidda bata daga ba, ya sake kira da magrib ma no answer, ya kalli wayarsa dake gefensa ya dauka ya sake dialing number, har ya katse no answer, haka nan kawai yaji his mind has lost rest, kallon wayar ya dinga yi, can ya sake kira nan ma har ya katse no answer, kallon agogon jikin wayar yyi yaga takwas ya wuce, sake dialing yyi nan ma har ya katse no answer, ajiye cup din hannunsa yyi, ya shiga kiran wani pilot hoping to reach him don yasan he might be up in the sky now, jin captain Musa ya daga, ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yace "Captain baku tashi har yanxu ba?" Captain din yace "About to... in few minutes time, ya gajiya?" Abuturrab yace "I think i will have to follow you to kaduna now" Da mamaki pilot din yace "Baxa kayi piloting jirgi gobe da safe ba, and hope all is well?" Abuturrab yace "Sure alhmdlh, jirgin gobe na sha daya ne, i don't have early morning duty" Musa yace "Toh shkkn, ka taho yanxun nan kasan basu fiye son jira ba, in some minute time xamu yi take off" Abuturrab yace "In sha Allah" Cikin few minutes ya shirya cikin kananun kaya Hoping not to miss the private flight going to kaduna, cikin ikon Allah ya isa, kuma suka daga sama, within some minutes suka sauka a garin kaduna, a motar Musa dake airport din kaduna suka shigo cikin gari, Musa ya kawo Abuturrab har layinsa ya sauka yana masa godiya, Musa yace "Sai mun hadu Wednesday in sha Allah" Abuturrab yace "Sure in sha Allah, thank you" daga haka suka yi sallama ya karasa cikin layin da kafa, makullin gidan ya fiddo a aljihunsa ya bude sannan ya shiga, har ya isa main entrance nan ma ya bude sannan ya shiga parlor, wutan parlon a kunne yake parlon sai kamshin turaren wuta yake, ko ina na nan ynda ya barsa jiya, kuma babu alamar ana xama cikin parlon ma, karasawa yyi sama yana kallon kofar dakinta ya murda a hankali ya shiga, babu kowa cikin dakin ya bude ido sosai sai dai lkci daya yayi calming kansa jin kamshin sabulu a dakin, coz he is a very sharp percipient, bin dakin ya dinga yi da kallo yana duba inda xai ga wayar amma bai ga alamarsa ba, can kusa da window ya nufa ya tsaya hade da rungume hannunsa ya daure fuska, bayan few seconds ta bude kofar bandakin, ta fito daure da towel, bata ko kalli direction din da yake ba ta nufi gaban mirror, sai a sannan ta ga mutum ta madubi wani ihu ta fasa da karfi ta nufi bandakin a guje ruwan kafarta ya sa tsantsin tiles ya kwasheta ta fadi nan bakin kofar bandakin, da sauri Abuturrab ya nufeta ya durkusa kusa da ita ya dagota yace "Ke nine fahh" wani kuka ta fashe da bayan ta kare masa kallo ta tabbatar shi din ne, tana rike da towel din jikinta gam tace "Wayyo kafata, wllh kila nayi targade, wayyo Baabarmu" Komawa baya yyi yana kallon kafar,  ya mike yace "Tashi tsaye" Tana girgixa kai hawaye na sauka idonta tace "Ni baxan iya ba wllh" Ya kamata ya dagata, lkci daya ya hade rai yace "Wani kafar ne kika yi targade" Ta nuna masa right leg dinta, gefen gado ya xaunar da ita ya duka yana kallon kafar, ita dai hawaye kawai take tana hade laps dinta tana kallonsa, wani kallo ya mata ta sunkuyar da kai da sauri, mikewa yayi ya nufi gaban madubi don yasan ya siya mata man xafi ranan da suka yi shopping incase she will need it, a hankali tace "Don Allah ka yi hakuri ka miko min hijabi na" Ya dau man ya juyo ya dawo kamar bai ji ta ba, ta marairaice tace "Hijabina nace" Yace "Ki bari in duba maki kafar in ga babu targade, yau duk kukan karyar nan da kike ma mutane sai ya dawo na gaskiya, kuma xaki gaya min inda kika jefar da wayar da na baki" Shiru tayi bata ce komai ba, ya duka ya bude man ya diba sannan ya kama kafar da tace, wani ihu tayi ya ja kafar da karfi, har kasa sai da ta sauko tana kokarin kwace kafarta sbda axaban da take ji, ganin da gaske ta ji ciwon yasa yace "A hankali fa nake maki amma wllh idan kika sake ta6a ni xan yi da karfi" hawaye na sauka idonta tace "Wllh xafi yake min sosai, don Allah ka rufa min asiri kayi hakuri" Ya daure fuska ganin xata sake kai hannunta kan nasa yace "Kin xata wasa nake maki" Da sauri ta dauke hannun, duk da yanda yake mata a hankali haka ta dinga kuka tana neman birgima a wajen, shi dai kallonta kawai yake, don a fuska bata yi kama da warce xata yi shagwaba ba, ko warce baxata iya jure xafi ba ko yaya ne, dauke idonsa yyi ganin tawul din na neman sauka a kirjinta, ya sake mata kafar ya mike, sai a snn ta ankare, tana shessheka ta kankame abarta, ya ajiye man xafin hannunsa ya nufi kofa ya fita.


No comments

Powered by Blogger.