Jiddatul Khair 17

 


Karfe hudu saura Abuturrab na xaune parlor wayarsa ya fara ring, kallon wayar ya dinga yi ganin Ahmad ne ke kiransa ya ki dagawa har ya katse, bayan few minutes ya ji wayar na ring kuma, dauka yayi xai yi silencing phone din ya ga Aneesah ce ke kiransa, sosai gabansa ya fadi, ya gyara xamansa da sauri yana kallon wayar har ya katse, ya lumshe ido hade da jinginar da kansa da kujera, mikewa yayi daga karshe walking slowly ya wuce sama, bude kofar dakin da Jiddah take yayi, da sauri ta dago kanta daga kan gwiwanta ta jawo ledan abincin, kallon idonta da yayi jajir sbda kuka ya tsaya yi, ta fara bude abincin ba tare da ta yarda ta sake kallonsa ba, she looks sad and scared, karasawa yyi cikin dakin ya xauna kan stool din dake gaban mirror looking at her directly, kasa kunce ledan da abincin ke ciki tayi, cikin cool voice yace "Kukan me kike?" Ta girgixa masa kai kawai wasu hawayen na taruwa idonta ba tare da ta yarda ta kallesa ba still, yace "Tambayarki nake" Nan ma ta girgixa masa kai, shiru yayi yana kallonta, ta bude ledan abinci ta ciro ta fara ci a hankali, ya mike yace "Xan tafi masallaci, kafin in dawo ki tabbatar kin gama cin abincin" Ta gyada masa kai, ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita dakin... Ko kafin ya dawo ta rufe sauran abincin da ta rage, ba cikin dadin rai ta ci abincin ba, ko rabi bata iya ci ta kai ba, lemon ma bata bude ba tunda ba iya sha tayi ba, ruwa kawai ta sha, tunani ta shiga yi ko ta kai sauran kitchen kar ya dawo kuma yayi mata ihu, a sanyaye ta mike ta dau ledan abincin ta fita, kitchen ta shiga ta fiddo takeaway din abincin ta ajiye gefe daya, sannan ta ciro ruwa da lemon ta ajiye tana kallon ledan hannunta wanda bata san inda xata wurgar ba, window din kitchen din ta dinga kallo sannan ta karasa a hankali ta bude ta jefar da ledan ta kulle windown, bin kitchen din ta dinga yi da kallo, babban ne kitchen din sosai, ga kuma store a ciki, cabinet din yayi kyau ba kadan ba sai dai babu komai a kitchen din sai electric heater da gas cooker, wanda bata ma san meye shi ba, sai fridge da deep freezer, a hankali ta juya xata fita ta gansa tsaye bakin kofar shigowa kitchen din ya rungume hannunsa yana kallonta, komawa baya tayi a tsorace tana kallonsa, ya nuna mata kofa wanda xai yi leading dinka to the back of the house, calmly yace "Bude kofar nan ki fita ledan da kika wurgar ki kwaso su" Da sauri ta nufi kofar tana murda makullin amma ta kasa budewa, karasawa yyi hakan yasa ta koma gefe da sauri, gaba daya a tsorace take, ya bude kofar ta fice, ledojin ta kwaso ta dawo ta tsaya bakin kofa tana kallonsa rike da ledan, ya karasa ya sa ma kofar makulli yace "Daga yau kada ki sake jefar min da komai wajen nan, don ba bola bane, ko kinga yayi maki kama da bola?" Ita dai bata ce komai ba ta sunkuyar da kanta, ya nuna mata wani waste bin a cikin kitchen din yace "Nan xaki dinga ajiye bola from henceforth" A hankali ta karasa shigowa ta saka ledojin a waste bin din, ya juya ya fita yace "Ki sameni sama" Bin bayansa tayi... ganin ya shiga dakin da take ta bi sa xuwa cikin dakin, gefen kofa ta tsaya bayan ta shigo, yana kallon tulin ledojin kayan da ta jera a kasa yace "Ga press can da xaki xuba kayanki" Ta kalli abinda yake nuna mata amma bata ce komai ba, yace "Yanxu xaki fara sa kayan ina gani...." Yana fadin haka ya ja stool ya xauna yana kallonta, ta karasa gun kayan ta bude, rasa ta yanda xata fara jera kayan tayi she look so confuse and Afraid at the same time, ta marairaice tana kallonsa amma bata ce komai ba, hakan yasa ya d'an yi tsaki bai ce mata komai ba ya mike, tun daga kananun kaya, undies, nighties, ya fara arranging dinsu a press din tana tsaye gefe tayi jigum tana kallonsa, har ya gama, ya bude akwatin da suka taho da shi jiya, atamfofin ciki dinkakku wanda baxa su wuce kala biyar ba ya ciro, linkin guga aka yi masu hakan yasa ya ajiye su cikin press din, da hijab biyu da suka rage suma gogaggu, sauran kananun abubuwan ciki duk ya samar masu maxauni cikin press din, gaban mirror yaje duk turarrukan ya jera su da mayukan shafawa da kayan kwalliya, lkci lkci yake kallonta ta madubin gabansa, Jiddah dai ta dinga kallon turarrukan da take ta tunanin su wa da su wa xasu dinga amfani da su haka da yawa, sun yi yawa sosai ba kadan ba, bayan ya tabbatar komai ya samu maxauni ya hade uban ledojin waje daya sannan yana kallonta ya nuna mata turarrukan yace "Kinga turarrukan nan?" Ta gyada masa kai, yace "They are not there for decoration?" D'an rufe idonsa yayi after he realized what he just spoke, sai kuma ya bude idanuwansa ya d'an hade rai yace "Kin gane abinda nace?" Ta girgixa masa kai yace "Ohk, cewa nayi ba don jere na siya maki su ba, watanni kadan na baki duk su kare, idan kuwa basu kare ba xan sa sai kin shanye su, na siya maki ne don ki dinga amfani da su a kai a kai, safe, rana, yamma, dare, bbu takamaiman lkcn saka turare, sannan ba kadan kadan aka ce ki dinga fesawa ba, idan kinga dama xaki iya feshe gaba dayansu a lkcn daya, infact ba ma sai kin ga dama ba, haka nake son ki dinga yi, gaba daya xaki dinga fesawa a lkci daya, wata daya na baki in ga duk sun kare..." kai kawai take gyada masa, ya nuna mata body cream din yace "Wannan xaki dinga shafawa duk kika yi wanka, sannan wanka da safe, rana, dare.... kullum haka xaki dinga yi, ga sabulun nan xan kai maki bandaki, idan kina so ma xaki iya wanka sau goma a rana akwai enough ruwa a gidan" Nan ma ta gyada masa kai, ya hade rai yace "Ba ki gyada min kai kamar lizard ba malama, sau nawa nace xaki dinga wanka daga yanxu?" A hankali tace "Sau uku, idan ina so ma inyi sau goma" Yace "Idan ma baki yi ba ina da camera a gidan ai xan gani...." Xaro ido tayi tana kallonsa, yace "Wanke baki kuma duk kika ci abu ki tafi bayi ki matsa MacLean ki wanke bakin ki, sannan ga na kuskura baki ma, bayan kin wanke bakin shi ma sai ki kuskure baki da shi, duk dare kada ki kuskura ki kwanta baki wanke bakin ki ba, da safe kafin kiyi alwala sai kin fara wanke baki, idan xaki yi wanka ki sake wankewa da safe... haka da rana sannan da yamma, ina son cikin sati biyu maclean dinki ya dinga karewa" Ta gyada masa kai, ya nuna mata mayukan gashi yace "Kullum sai ki shafa wannan a gashin ki, ki gyara..." Cikin sanyin murya tace "Toh" Nail cutter ya dauka gaban mirror din yace "Kinsan meye wannan?" Shiru tayi tana kallo, ya isa gabanta yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi ta fara komawa baya a hankali, tsayawa yayi yana kallonta, lkci daya ya daure fuska yace "Meye haka?" Taki kallonsa gabanta sai faduwa yake, yace "Baxa ki dago kanki ba" Da kyar ta dago kanta amma ta kasa kallon cikin idonsa, ya daura nail cutter din a kan finger dinsa wanda babu farce yace "Shi ake yankewa da, duk ranan juma'ah ki tabbatar kin yanke faratanki, kar ki kuskura ki yarda in ga farce a hannunki, bana son ganin haka..." A hankali ta gyada masa kai, yace "In ga hannunki" a hankali tayi masa stretching dogayen fingers dinta wanda ita ma bbu farce, lkci daya kuma ta sauke kasa, ya dau shaving stick dake cikin leda yana kallonta yace "Kinsan wannan?" Sau daya ta kalli abinda yake nuna mata, ta Smsunkuyar da kanta, yace "Duk Jumma'ah xaki dinga amfani dashi shi ma" ita dai bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, Sabulu ya dauka da Listerine mouthwash ya nufi bathroom, da ido ta bi sa, xai shiga ya juyo ganin bata taho ba yace "In dawo in dauko ki ne??" Da sauri ta bi sa, wajen da xata ajiye towel dinta ya nuna mata, ganin undies dinta da ta wanke a bandakin yace "Xa a sa maki igiya a baya, daga yau kada ki sake shanya a nan ki kai rana, nan ba wajen shanya bane, am i clear?" Ta sunkuyar da kai a hankali tace "Toh" da ido ya bi bandakin ganin it's clean ya juya ya fita ta bi bayansa, ya jingina da bango ya rungume hannunsa yace "Kinsan abinda yasa nake nuna maki duk abubuwan nan?" Ta girgixa masa kai tana kallonsa, yace "Saboda ba lallai wani abun ya sake hadamu a gidan nan ba, ba lallai ki sake samun privilege din tsayawa waje daya tare da ni ina maki bayani ba, ke kadai xaki dinga rayuwarki gidan nan babu wani da xai xo balle ya nuna maki wani abu shi sa nake bata lkci na yanxu, kina da ikon shiga ko ina a gidan nan amma banda bangarena.... sannan idan ina gari ba ke ba fitowa daga dakinki, kwana biyu xuwa uku kawai nake yi a kaduna shi ma sai karshen mako, don haka a wannan lkcn iyakar ki dakin ki, sai kuma probably kitchen, sannan baxan lamunci ki bar min gida da kazanta ba, kullum ki tabbatar kin yi shara kin yi mopping kin goge ko ina, nasan kin ga yanda ake yi a gidan Umma, tunda kin fi sati a can" Ji tayi hawaye ya kawo idonta, ta daga kai tana kallonsa, ya hade rai yace "Kin ji abinda nace?" Gyada masa kai tayi tana kokarin ganin hawayen bai karasa xubowa ba, Ya rungume hannunsa yace "Gobe xan koma wajen aiki, kafin in tafi xan siyo kayan abinci da komai da xa ki bukata a kitchen, don haka duk abinda na gaya maki yanxu baki da wani da xai sake gaya maki a gidan nan, it's better ki tabbatar kin gane komai...." Kallonsa kawai take tana jin wani kuka xai taho mata, ya ki yrda ya hada ido da ita, ya daga kafada kawai ya juya ya nufi kofa ya fita, ta sauke idonta a hankali wani hawaye me xafi ya shiga sakko mata. Abuturrab na dawowa daga masallaci da magrib ya shigo da abinci, sama ya haura ya kwankwasa kofar sannan ya bude, tana xaune saman darduma, ya ajiye mata abincin bakin kofar, ya d'an tsaya wanting to ask what she is even reciting in her prayers, sai kuma kawai ya fasa, ya ta6e baki yayi wucewarsa, karfe tara da rabi ta gama saka kayan da ya nuna mata yace ire irensu xata dinga sa wa da daddare, wando ne dogo da riga, sosai kayan ya mata kyau tana tsaye gaban madubi ta saka daya daga hulunan da ya siyo mata, har makogwaro ta dinga jin turarrukan da ta fesa abin ka da bata saba ba, ta nufi saman gado ta takure waje daya ta kwanta ta lumshe ido... Abuturrab ya fito daga bangarensa rike da lallausan duvet, kana ganin duvet din kasan me tsada ne sosai, kamshin turarruka ne ya gauraye ko ina na upstairs din, ya isa kofar dakin, ya fi second biyar a tsaye kafin ya bude, ko motsi bata yi ba alamar ta fara bacci, ya karasa ciki ya bude duvet din ya rufeta da shi, da sauri ta bude ido, yana kallonta yace "Daga yanxu idan xa ki kwanta ki dinga kashe wuta" Ta gyada masa kai, gun switch din ya nufa ya kashe wutan dakin sannan ya fita ya kulle kofar dakin, Jiddah ta lumshe ido gabanta na faduwa don bata saba kwana ita kadai ba. Washegari Abuturrab ya tabbatar duk wani abinda Jiddah xata bukata a kitchen ya siya, tare da Ramlah suka tafi siyayyen, duk ita ke fada masa abinda xa su siya na foodstuffs, har da filling din gas sun yi, kitchen din ya dawo well stocked up with foodstuffs, few pots, and some kitchen utensils, Jiddah dai na xaune parlon tun bayan dawowarsa da Ramlah, shi ma ya aika Ramlan taje ta kirata ne, yana tsaye kitchen din Ramlah ta jera komai, yana kallonta yace "Ahmad ya koma Abuja ne?" Ta gyada masa kai, ko ranan ma Ahmad ya kirasa amma yaki dagawa kamar dai shi ya aura masa jiddah, Ramlah na gamawa Abuturrab ya bata 2k transport ta fito daga kitchen din tana kallon Jiddah dake ta xaune, da murmushi fuskarta tace "Aunty amarya xan koma" ko lura da kallon da Abuturrab ke mata bata yi ba don jiddah kawai take kallo, Jiddah kam ta ga kallon da yake ma kanwartasa, cikin sanyi tace "To sai anjima" Ramlah ta nufi kofa.... bayan ta fita, Jiddah ta d'an kallesa suka hada ido, daure fuska yayi yace "In rokeki ki taso?" A hankali ta mike ta nufesa, komai na kitchen din ya shiga nuna mata da inda suke ajiye, ya koya mata kunna gas ya tabbatar ta iya kashewa ta iya kunnawa, yana kallonta da kyau yace "Anjima kafin in tafi xaki kunna min in gani" Tace "Toh" fita yyi daga kitchen din ya bar ta tsaye, ta bi sa da ido sannan ta bi bayansa. Abuturrab na komawa bangarensa ya ga calls din Umma har biyu, kiranta ya shiga yi bayan ta daga ya gaisheta, ta amsa tana tambayarsa ya gida, ya amsa mata, tace "Jiya naji ka je kun yi siyayya da Jiddah ko?" Yace "Ehh" Tace "Toh Allah ya saka da alkhairi" Ya amsa da "Ameen" tace "Yanxu meye babu cikin kayan, don xan taho anjima ne, sai in ga ko xa a iya tahowa da su" Ya d'an shafa kansa yace "Kawai Hijabs, bayan shi babu wani abu" Tace "Toh xuwa wani satin sai a dinka mata su" Yace "To Allah ya kai mu" Tace "Shi kenan dai ko?" Yace "Ehh" Tace "Toh sai na iso" Yace "Kamar yaushe xa ki taho Umma?" Tace "Xaku fita ne?" Ya girgixa kai yace "Xan koma aiki ne yau" Da mamaki tace "Xaka koma aiki kuma? ni na xata tunda ansan baka ji dadi ba xaka dau wani satin off?" Yace "Aa ni naji sauki, yau xan koma" Sake baki tayi, can tace "To ita Jiddar fa? Ko tare xa ku tafi?" Ya xaro ido kamar warce ta fado masa wani mugun abu yace "Aa" Tace "To ina xaka barta?" Yace "Nan gidan" Umma tace "Ita kadai?" Yace "Ehh babu komai" ta xaro ido tace "Aa gaskiya ka kawota nan kawai" Abuturrab yace "Aa xata xauna nan Umma" Umma tace "A kan me xaka bar yar mutane ita kadai a wannan gidan, ae baxai yiwu ba Abuturrab" Ya d'an shafa kansa a hankali yace "Umma tace fa xata iya xama, kuma ma xa a kawo mata mai aiki, ni nafi son ta xauna nan din kawai, and ranan laraba da safe xan dawo ai" Umma tace "Yaushe xa a kawo me aikin??" Da sauri yace "Ermm yau, in sha Allah" Umma ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Ni dai na fi gane ka kawota nan gida Abuturrab, ina ga xai fi wllh, it's not advisable to leave her all alone a gidan nan, she is too young for that, beside bata saba xama ita kadai ba" Trying all he xan to convince her yace "Umma xafa ta iya xama wllh, u shouldn't worry pls..." Umma tace "Toh amma is there anything wrong idan ka dawo da ita nan din, idan ka dawo weekend ba sai ka xo ka dauketa ba" Yace "Umma makaranta fa xata fara soon, plss u need not to worry" A hankali Umma tace "Toh shkkn wai dama don in dinga nuna mata wasu abubuwan ne, yasa nayi insisting" Ya girgixa kai yace "Ai bata da wani lkcn Umma, xata fara boko sannan islamiyya" Umma tace "Toh shkkn" ya d'an sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yace "Toh sai kin xo Umma" Tace "Kai xan ba Maimuna sakon kawai ta kawo, next week din xan shigo in sha Allah" Yace "Umma me yasa kika fasa kuma, ko fushi kika yi" Tace "Not at all, let me leave it next week kawai" A hankali yace "Toh shkkn Umma" Sallama tayi masa ta katse wayar tana mamakin irin taurin kan Abuturrab, wanda tasan da Aunty ce tayi masa wannan maganan baxai mata musu ba xai yi yanda tace, girgixa kai kawai tayi don kwata kwata bata ji dadin haka ba,  Abuturrab ya sauke wani ajiyar xuciyar ya ajiye wayar. Bayan la'asar ya gama shirinsa don driving xai yi xuwa kanon, komai da yasan ya kamata jiddah ta sani ko ta iya amfani da shi a gidan sai da ya tabbatar ya nuna mata a gidan nan, abinda ya kara bata masa lkci kenan, xaune yake parlor waiting for Maimuna don baya son sai ya tafi ta xo, tana ring din bell ya mike ya bude kofar, gaishesa tayi da fara'a, ya amsa yace "Ya gida" Tace "Alhmdlh yaya, ina Aunty Amarya" Babu yabo bbu fallasa ya amshi ledan hannunta, sannan ya ciro dubu daya ya mika mata yace "Ki yi transport" tace "Tare da driver muke" Yace "Ohk" dubu daya ya kara xarowa aljihunsa ya hada ya mika mata yace "Ki saka kati" Tana murmushi tace "Aa ka bari nagode yaya" Ya hade rai yace "Amsa ki tafi" Amsa tayi yace "Sai anjima" Tayi masa godiya sannan ta juya a hankali, amma duk jikinta yyi sanyi don bai bari ta ga Jiddah ba, ya kulle kofar, kujera ya koma ya xauna yana duba abinda ta kawo, turarrukan wuta ne a kwalbansu kusan kala hudu sai burner, da wasu turarrukan na jiki, tabe baki yyi ya mike ya wuce sama, dakin jiddah ya bude ya ganta xaune duk ta dawo wani iri, tana ganinsa ta sauke kanta kasa, ya ajiye ledan yace "Umma ta bada a kawo maki" ta bi sa da kallo har ya jona burner din a socket, sannan ya bude turaren wutan guda daya ya diba ya xuba yana kallonta, bayan d'an lkci kamshi ya fara tashi, yace "Safe da yamma xaki tabbatar kin ma dakinki da parlor haka" Ta gyada masa kai kawai, waya karama ya ciro aljihunsa yana kallonta ya mika mata, ta mike ta isa inda yake ta risina ta amsa, yana kallonta yace "Number da xaki dinga samuna ne kadai a ciki, sai ki koyi yanda xaki yi amfani da shi ke kadai" cikin sanyin murya tace "Toh" Yace "Sannan ba ace ki xauna ke daya kiyi wani shiru kamar me xaman makoki ba, ga kayan kallo duk na koya maki yanda xaki kunna" Ta sunkuyar da kanta, kofa ya nufa yace "Na tafi" Ta kallesa da sauri tace "Ina xaka je" Yace "Garin da nake aiki" bude kofar yyi ta bi sa da ido, sai da taga ya fita kafin ya kulle kofar cikin sanyin murya tace "Allah ya tsare" Ya amsa da Ameen a takaice, da sauri tace "Yaushe xaka dawo?" Yana kallonta yace "Wannan bai shafeki ba, ko da wani abu da xaki bukata bayan duk wanda na maki??" Daga haka ya kulle kofar hawayen dake makale idonta ya silalo a hankali, ta fi minti goma tsaye yanda ya bar ta, jin an tada mota ta kalli window da sauri sannan ta karasa window din ta d'an bude labule tana lekan waje, tana ganinsa ya fita da motar, a hankali ta fara kuka ta xauna nan kasa, sai kuma ta fashe da kuka kamar ana dada tunxurata, Abuturrab ya sauka motar yana kallon gate din gidan, he just dont have any option then to close the gate from outside, don bai ma son ya gwada mata yanda ake kullewa daga ciki balle ya sa ta kulle ta ciki, yasan probably kafin ya dawo weekend an samar masa mai gadi kamar yanda yayi requesting ayi, ya kulle gidan ya koma ya shiga motarsa yana karasa addu'o'in da yake yi tun daga compound a ransa ya bar layin.....


No comments

Powered by Blogger.