Jiddatul Khair 15


Umma ta sauka motar bayan drivernta yayi parking, Jiddah ma ta sauka tana kallon babban gidan, Umma ta kalli driver tace "Ka je kawai idan xan dawo anjima xan kiraka..." Cike da ladabi yace "Toh Hajiya" ta kalli Jiddah tace "Mu je" Bin bayanta Jiddah tayi tana tafiya a hankali har suka isa main parlor din gidan, kasancewar ranan asabar ne su Ramlah duk sun tafi islamiyya, Mai aiki ce

kadai parlon tana aikace aikace, ban da kamshi babu abinda ke tashi parlon, mai aikin ta gaida Umma da ladabi, Umma ta amsa da fara'a tana mata sannu da aiki sannan ta kalli Jiddah tace "Toh xauna Jiddah" Xata xauna kasa Umma tace "Aa tashi ki hau kujera" Mikewa tayi ta xauna saman kujeran Umma ta nufi bangaren yayarta, sai a sannan Jiddah ta gaida mai aikin, matar ta amsa mata da murmushi tana ci gaba da abinda take, Muryar Abuturrab Jiddah ta ji ta d'an saci kallon gefenta amma bata gansa ba, slowly yake tahowa waya kare kunnensa yana waya tare da wani colleague dinsa da ya kirasa don jin ya jikinsa, murmushi Abuturrab yyi yace "Wato the sky misses me, not my co pilots" Murmushin kawai yake, daga karshe suka yi sallama da Captain Ishaq ya katse wayar ya nufi kitchen, 3 quarter ne jikinsa da farin T shirt, Mai aikin gidan Naja'at ta d'an risina ta gaishesa with respect ya amsa without looking at her, Jiddah ta bi sa da ido, har xai shiga kitchen ya juya coz he saw someone sitting amma bai kalli ko waye ba, suka hada ido, da farko bai ganeta ba sai da ya tsura mata ido, ita dai tayi kasa da nata idanuwan tace "Ina kwana" daga sama har kasa yake kallonta, Naja'at tace "Tana gaisuwa ranka shi dade" Juyawa yayi ya shige kitchen abun sa, Naja'at ta sunkuyar da kai sanin kadan daga abinda xai iya aika kenan, can ta d'an yi murmushi tana kallon Jiddah tace "Ina jin bai ji ba" Jiddah tayi murmushin karfin hali bata dai ce komai ba, Umma ta shigo parlon tare da Ummi, Ummi na kallon Jiddah tace "Sannu da xuwa" Jiddah ta gaisheta da ladabi, Ummi ta amsa da d'an murmushi fuskarta, Ummi na kallon Naja'at tace "Tafi dakin Hajiya Hafsah ta xo su gaisa da bakuwa" Naja'at tace "Toh Hajiya" daga haka ta wuce da sauri, Ummi ta xauna Umma ma ta xauna, gaba daya Jiddah sae taji ta kasa sakin jiki, duk ta takura, Ummi tace "Ya kika kara ji da jiki?" A hankali Jiddah tace "Alhmdlh" Abuturrab ya fito daga kitchen rike da cup din shayi yana juyawa da cokali, Umma ta dinga kallonsa, sannu da xuwa kawai yayi mata ya nufi dakinsa ya ajiye cup din shayin, ba a dau lkci ba sai gashi ya fito, ya karaso cikin parlon ya xauna yace "Ina kwana Umma" Da murmushi tace "Lafiya lau Abuturrab, ka tashi lfya?" Yace "Alhmdlh" Umma ta kalli Jiddah tace "Kun gaisa kuwa" Jiddah na kallonsa tace "Ina kwana" Ba tare da ya kalleta ba yace "Lafiya lau" Ummi dai kallonsu kawai take, Aunty ta shigo parlon ganin Umma tace "A'a Sannu da xuwa Hajiya Ramlah" Umma na murmushi tace "Yauwa, mun same ku lfya?" Aunty tace "Alhmdlh wllh" Aunty na kallon Jiddah tace "Sannu yan mata..." Jiddah ta gaisheta tana kallont, Aunty ta amsa ta nemi waje ta xauna, Ummi na kallon Abuturrab tace "Sai ka kai ta parlon Abbanku su gaisa tunda Kawunnanka na ciki" Abuturrab mood dinsa ya sauya lkci daya, Aunty dai sae murmushi take a xatonta ko 'yar uwarsu ce Jiddah warce bata sani ba, ganinta fara sosai kamarsu Ummin, Mikewa Abuturrab yyi, Umma na kallon Jiddah tace "Tashi ki bi sa" Ta mike a hankali ta bi bayansa, Ummi ta bi su da kallo, ba karamin kyau hijab din yyi mata ba har kasa kuma yake ja, Wani boyayyen ajiyar xuciya ta sauke, Aunty na gyara daurin dankwalinta tace "Bakuwa aka yi, kamar yar uwarku naganta ita ma fara, amma ban santa ba" Ummi na kallon Aunty tace "Ita ce yarinyar da yaje ya aura ae" Da sauri Aunty ta bi Jiddah da kallo idanuwanta kamar xa su fito, Daga Umma har Ummi kallonta suke, da wani confusion tace "Ita ce yar hayin??" Umma tace "Ita ce fa" Aunty ta hade rai lkci daya, can ta girgixa kai tace "Toh meye fa'idar kawota nan din tunda dai sakinta xai yi, haba ni dai ina ta kallonta ganin halin gidadanci a tare da ita, to yanxu meye amfanin xuwa da ita har ace taje ta gaida kawunnansa??" Wani kallo Umma tayi mata ta dauke kai, Ummi dai bata ce komai ba, Aunty ta ja wani tsaki ta mike ta fice daga parlon. Da sallama Abuturrab ya shiga parlon Abbansa Jiddah na biye da shi, Abba na xaune tare da yayansa da kaninsa, Abuturrab ya xauna kasa ya sunkuyar da kai, d'an nesa da shi ta xauna ta takure cikin Hijab, cikin sanyin murya ya gaishesu gaba daya, ko wannensu ya amsa mata da fara'a, Alhaji Lawal na kallon Abuturrab yace "Ita ce?" Abuturrab yyi karfin halin cewa "Ehh" Duk suka amsa da maa sha Allah, Ita dai Jiddah kanta na kasa, Abba yace "And there is nothing wrong with her, Allah ubangiji ya baku xaman lafiya" Sae a sannan Jiddah ta dago tana kallon Abba, Abuturrab dae ya kasa dago kansa, nasiha dattijan suka shiga yi masu a tare, Jiddah dai sae bin su take da kallon don gaba daya bata gane inda suka dosa ba, a xatonta wanda aka ma aure ake yi ma irin wannan maganganun da suke mata, ya xa ayi ta bi shi kamar yanda suke cewa, tayi masa biyayya sannan tayi hakuri, Abuturrab dai ya ki dago kansa, Sun fi minti talatin suna abu daya daga karshe suka masu addu'a da fatan Allah ya kade shaidan a xamansu, A hankali Abuturrab ya dago yace "Ameen nagode Abba" Kudi ko wannensu ya ciro ya mika mata ta ki amsa tana kallonsu duk kana ganinta kasan she is confused, Abuturrab ya daga kai ya kalleta, can ya karasa ya amsa kudaden, Uncles din nasa suka ce ya siya mata duk abinda take so, ya amsa masu da in sha Allah, Abba yace "Yau din xa ku wuce can gidan naka, amma kafin nan ka kira mai martaba" Kai kawai Abuturrab ya gyada masa a hankali, sannan ya mike yana kallon jiddah, k'in tashi tayi, Alhaji Ibrahim ya mata murmushi yace "Tashi ku je, Allah yayi maki albarka" Mikewa tayi, Alhaji Lawal yace "Ya sunan nata?" Ta sunkuyar da kanta Abuturrab ya d'an fara kame kame yace "Ummi ce..." Abba ya d'an yi murmushi yace "Hauwa sunanta" Duk suka amsa da maa sha Allah, Alhaji Lawal yace "Baki da matsala a rayuwa idan kika yi halin me wannan sunan ta gidan nan, A very simple life" murmushi kawai Abba yayi, Abuturrab ya nufi kofa Jiddah ta juya ta bi bayansa, sai da suka fita ya kulle kofar yana mata wani irin kallo yace "Ke wace irin dakikiya ce ana maki magana kiyi ta kallon mutane kamar wawuya kiyi shiru..." Kallonsa kawai take da manyan idanuwanta ko kiftawa babu, ya nuna mata parlon fuska daure yace "Koma kiyi masu godiya ko ajiya kika basu kudin da suka baki?" Ba musu ta juya ta bude kofar ta shiga parlon, duk kallonta su Abba suka tsaya yi, ta tsugunna hawaye har ya kawo idonta cikin sanyin murya tace "Abba nagode Allah ya saka da alkhairi" Duk suka amsa mata da Ameen, suka kara sa mata albarka sannan Alhaji Lawal ya umarceta da ta tashi ta wuce, mikewa tayi ta nufi kofa ta bude ta fita ta rufe masu kofar, tsaye ta tadda Abuturrab bakin kofar yana jiranta, ta sunkuyar da kanta, ya fara tafiya, bin bayansa tayi tana tafiya a hankali, babu kowa parlon, ganin xai hau sama ta nemi waje parlon ta xauna, kamar ance ya juya ya ganta ta xauna a parlor, hade rai yayi sosai yana kallonta, ta mike tsaye ita ma tana kallonsa, yace "Xo ki wuce" Ta nufesa gabanta na faduwa, sai da yaga ta kusa iso shi sannan ya fara tafiya, tana biye da shi har suka isa dakin Aunty, Kulle kofar yayi bayan Jiddah ta shigo, Aunty ta tamke fuska ganinta, ya xauna kan stool din gaban mirror yana kallon Aunty a hankali yace "The lady..." Aunty ta wani ta6e baki hade da tafe hannu tana kallon Jiddah, lkci daya ta girgixa kai tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wllh ka cuci kanka  Aliyu, me xaka yi da bagidajiya domin Allah, sai ku ce sai kunyi taimako, taimakon da yanxu idan mutum yayi yake xame masa sharri, to dai ga naka nan ya xamar maka sharri babba, da ajinka, da kyanka, da ilimin ka da kudinka, ina xaka kai wannan fisabilillah? Ina kai ina wannan Aliyu? Wllh wllh banyi baccin kirki a kan lamarin nan ba jiya" Sunkuyar da kai Jiddah tayi har lkcn ta kasa gane kan komai amma duk jikinta yayi sanyi har hawaye ya kawo idonta don saurin kukanta, Abuturrab ya lumshe ido, bai ji dadin maganganun Aunty a lkcn ba, he wish she was even speaking just English at that moment, ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "U need not to worry Aunty as soon as possible i will find a solution, I've told u everything, you just have to trust me aunt" Yana fadin haka ya mike yana kallon Jiddah kafin yace komai ta juya ta bude kofar ta fita daga dakin, Aunty taji har ranta ta tsani Jiddah, and she will do everything Abuturrab ya datse auren nan balle ma tasan tunda yace xai saketa xai saketa din... Suna fitowa Abuturrab ya fara tafiya, bin bayansa Jiddah tayi a hankali tace "Umma fa?" Ya juyo ya kalleta bai bata amsa ba ya ci gaba da tafiya sai ga Umman ta fito dakin Ummi, ganinsu tace "Yauwa dubawa xanyi dama ko kun fito" Jiddah ta nufeta, Umma tace "To mu shiga ciki" Umma na juyawa Jiddah ta kalli Abuturrab, hararanta yyi ta bi bayan Umma suka shiga parlon Ummi, jingina yyi da bango ya rufe idanuwansa, idan ba avoiding yarinyar nan xai dinga yi ba ko da suna xaune gida dayan ae wataran bubbugeta xai yi a banxa, she is just too dopey for his liking, kwafa yayi ya bude ido ya bar wajen.... Har bayan magrib Jiddah na part din Ummi, a lkcn kuma Umma ta shirya xata wuce don har ta kira Driver, Suna bedroom tare da 'yar uwarta Jiddah kuma na parlor tana kallon tv dake ta aiki, duk ta kagu Umma tace mata su tashi su wuce, duk yan matan gidan kowa ya shigo kallon sama har kasa yake mata sannan ya fita, Ramlah ce kawai ta tsaya suka gaisa, Ummi na kallon Umma tace "Toh ki kara mata fada ni dai kinsan babu abinda xan ce, har yanxu Ramlah i am finding it hard to believe Aliyu is married, ganin abun nake kamar mafarki, i still don't have the courage to start telling this to relatives and frnds, to me ma xance masu Ramlah? Waliman da Uban nasa yace ayi yace baxai yi ba shi, nima dama I'm not in support of that" Umma ta kwantar da murya tace "Yaya kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki, in sha Allah xa mu yi alfahari da wannan auren gaba dayanmu, duk mu yi hakuri mu bar ma Allah komai, Ae Allah ya ga xuciyar mu gaba daya, bama nufin d'an kowa da sharri mu bi su da addu'a kawai" A sanyaye Ummi tace "Ikon Allah, idan wani yace min haka xae ta6a faruwa a household dina baxan yadda ba wllh, duk burin da aka ci a kan bikinsa a haka ya tarwatse??" Umma tace "Haka Allah ya so, ynxu duk abinda Allah ya hore maki sae kiyi mata yaya kinga marainiya ce, nima xan yi nawa, amma kar ki manta da kayan Ramlan don bata da wanda xata sa idan sun tafi yau din" Ummi bata sake cewa komai ba duk jikinta yayi sanyi sosai, Umma tace "Xan sake yi mata nasiha yanxu kafin driver din ya karaso" Daga haka ta fita Ummi ta bi ta da kallo ta girgixa kai tace "Ikon Allah, so all this isn't a dream" Jiddah na ganin Umma hankalinta ya kwanta a tunaninta xa su wuce, ta mike Umma tace "A'a xauna" Xaunawa tayi tana kallon Umma, Umma tace "Abuturrab ae ya maki bayanin komai jiya ko?" Kallonta kawai Jiddah ke yi, can tace "Na me Umma?" Umma tace "Auren ku" a sanyaye Jiddah tace "Ehh yace min an daura min aure da wani, amma wanin xae sakeni sae in dawo wajenki kuma in xauna" Innocently ta fadi hakan tana kallon Umma, Umma ta d'an yi murmushi, lkci daya taji tausayinta ya rufeta, can tace "Bai gaya maki da wanda aka daura maki auren ba?" Jiddah ta girgixa kai tace "Aa bai gaya min ba" Shiru Umma tayi tana tunanin ya kamata tayi breaking mata news din ma kuwa, ajiyar xuciya ta sauke sannan tace "Toh shkkn, d'an xaman da muka yi dake Jiddah naga kina da hakuri da kawaici, sannan kina da hankali, to ki ci gaba a haka kinji, me hakuri shi ke cin riban xaman duniya sannan ki xama me rikon addininki sallah a kan lkci, tsaftar jikin ki, duk ae na nuna maki yanda xa ki dinga yi a gida, kinsan daga inda kika fito Jiddah, ki rike maraicinki, kiyi hakuri a duk halin da kika tsinci kanki" Jiddah ta gyada mata kai lkci daya hawaye ya kawo idonta, abinda Umma bata so kenan duk mutum xai yi hawaye gabanta sae taji xuciyarta ya karaya, tana da rauni sosai, hakan yasa ta mike tace "Drivern ma na kirana ya iso ina jin" Jiddah ta mike da sauri cikin rawan murya tace "Umma ba da ni xa ki koma ba?" Umma ta kasa kallonta tace "Abuturrab xai dawo dake, ae baku yi sallama da Abba ba, Abban na dawowa bayan kunyi sallama xai dawo min dake" Umma na fadin haka ta shiga daki gun yayarta, Jiddah ta bi ta da kallo hawaye me xafi na sauka idonta, ba a dau lkci ba Umma ta fito, murmushi tayi tace "Toh idan baxa ki daina kukan nan ba sae ince ya bar ki nan ki kwana biyu kafin ya dawo min dake" Da sauri ta share hawayenta, Umma tace "Toh ko ke fa, yanxu Abban xae shigo sae Abuturrab din ya dawo dake a motarsa" Gyada mata kai Jiddah tayi, Umma tace "Sae kun karaso" Daga haka ta fita, Jiddah ta koma kasa ta xauna a hankali wasu sabbin hawayen na sauka idonta.... Karfe takwas da few minutes Abuturrab ya shigo parlon, tun tafiyar Umma Jiddah ke ta xaune parlon ita kadai, Ummi kuma na bedroom dinta, kallo daya yayi ma Jiddah ya karasa dakin Umminsa, Jiddah ta shiga saka hannun hijab dinta hoping ynxu xai ce mata ta tashi ya maidata gidan Umma, Abuturrab ya karasa gun Umminsa dake xaune ita kadai dakin, kasa kallonta yayi kansa a kasa yace "Ummi xan wuce" Tace "Allah ya kiyaye" Bai iya yace komai ba, Ummi ta ci gaba da duba littafin hannunta, a hankali yace "Sae da safe" Tace "Allah ya tashemu lafiya, ga akwatin kar ka manta" Ya kalli trolley din ya karasa ya daga ya juya ya fita dakin, yana shigowa parlon ya kalli Jiddah dake jiran taji yace tashi mu tafi yace "Ki shiga kiyi ma Ummi sai da safe" Ba musu ta mike ta shiga dakin Ummi, ta sunkuyar da kai tace "Ummi sae da safe" Ummi ta kalleta tace "Allah ya tashemu lafiya" Juyawa Jiddah tayi ta fita, har sannan Abuturrab na tsaye yana jiran fitowarta, ganin ta fito ya fara tafiya, Bin bayansa tayi har suka fita, ko da wasa bai yi tunanin shiga bangaren stepmom dinsa ba sanin wani maganan da xai bata masa rai xata yi, yana fita su Safiyya da Aisha dake xaune parlor suka dinga kallon jiddah, kofa ya nufa duk suka yi masa sai da safe bbu warce ya tanka cikinsu, Basu ce ma Jiddah ba ita ma bata ce masu ba, a tare duk suka ta6a baki banda Ramlah da ta bi Jiddah da kallo, a booth ya saka trolley din, ya bude driver seat ya shiga ya tada motar, Jiddah dai na tsaye bata ma san inda xata shiga a motar ba, ya wani hade rai ya sauke glass din yana kallonta yace "Rokanki xan yi ki shigo?" A hankali tace "Toh ban san inda xan shiga ba" irin kallon da ya dinga yi mata ya sa ta bude back seat ta shiga ta rufe motar, gaba daya sae taji ta tsorata da shi, amma lkcn da yake xuwa can gidansu ae baya hararanta ko yayi mata ihu haka, sunkuyar da kanta tayi har hawaye ya kawo idonta, yayi horn mai gadi ya bude masa gate ya fita gidan, driving kawai yake amma gaba daya yyi nisa tunanin da yake, wai shi yau xai tafi gidansa da yaki budewa wishing to go in with his wife first, sai gashi da wannan yarinyar xai je, wannan yarinyar fa, tunanin hakan yasa yaji kamar ba a ta6a abinda ya cucesa a rayuwa irin wannan lamarin ba, ya runtse ido ya bude still driving, ae idan ya kwana ma da auren yarinyar nan yau yana da ra'ayin rayuwa tare da ita kenan, Ahmad ne ke ta kiransa tun fitowarsa amma yaki daga wayan haushin kowa kawai yake ji shi yanxu, tafiyar minti talatin da biyar yayi ya isa gidansa dake U dosa, dai dai gate din gidan ya tsaya ya dau makullin gate din ya karasa ya bude gate din sannan ya dawo ya shigar da motar compound din gidan, Jiddah dai sai bin gidan take da kallo don bai yi kama da gidansu Umma ba, sauka yyi motar bayan ya kashe ya karasa ya rufe gate din ya cire makullin ya koma gun motar, ya bude booth ya sauke trolley din, har sannan Jiddah ta ki sauka daga motar, bayan ya rufe booth din ya bude side dinta yana kallonta fuskarsa ba fara'a, sauka tayi tana sake bin gidan da kallo ta kara tabbatarwa ba gidan bane duk da shi ma din gidan sama ne, ta marairaice tana kallonsa tace "Ae ba nan bane gidan" Wani kallo yyi mata ya ja trolley din, bin bayansa tayi da sauri a d'an tsorace tace "Gidan Umman fa??" Ganin har ya shiga parlon ta shiga ita ma ya kunna wuta da ya haska ko ina na parlon, komai na parlon sabo ne, ba kuma karamin haduwa parlon yayi ba, ta dinga bin babban parlon da kallo kamar idanuwanta xa su fito, rufe kofar yayi yasa makulli, sae a sannan ta fashe da kuka a hankali tace "Gidan Umma ae aka ce ka kai ni fa" Biron da ya saka a aljihunsa tun daga gida ya ciro sannan ya wuce sama sanin baxai rasa takarda a bedroom dinsa ba, bin bayansa jiddah tayi hawaye na xuba idonta, ganin hanyar da ya bi bayan ya hau saman ta bi da sauri ita ma don tsoron gidan take, wani kofar da taga ya shiga ta bude taga wani babban parlon hadadde, tsaye tayi bakin kofar gabanta na faduwa, bayan few seconds sae gashi ya fito rike da farar takarda......


No comments

Powered by Blogger.