Jiddatul Khair 1
1.....
Slowly yake driving din idonsa a kan titi yana sauraron abokinsa, amininsa, kuma d'an uwansa dake xaune kujera me xaman banxa cikin motar, can dai ya ja tsaki ya girgixa kai, speaking calmly yace "Ni fa da ma ka canxa labarin nan naka Ahmad, in anyway ban ga amfaninsa ba..." Dariya abokin nasa Ahmad yyi yace "Toh ai ni yana da amfani gareni sosai tunda ina sonta and i want to marry her, look Captain don Allah ka cire son
xuciya ka gaya min meye aibun Maryam let me know" Wanda ya kira da captain ya shafa lallausan gashin kansa yace "Kasan mene?" Kallonsa kawai Ahmad yake yana jiran jin abinda xai ce, Captain yace "Ina son ka sanar dani me yasa ku Hausawa baku da xancen da ya wuce na soyayya, ga dai abubuwan ilimi iri iri masu ma'ana da mutum xai karu da su duniya... Amma ku dai soyayya kadai ku ka sa a gaba, did u know that it's just of recent ina wani karatu nayi discovering cewar Airplane water is riddled with bacteria, not even that, jiya jiyan nan na gano cewar...." Ahmad dake masa wani kallo ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Wannan kai da masu tunani irin naka ya shafa, what u are saying now will add no value to people like me gaskiya" Captain ya maida hankalinsa gaba daya kan tukin da yake, Ahmad yace "Duk sanda na kawo maka maganar Maryam you always have a way to get rid of the discussion ko me yasa?" Captain yace "Ohk you asked me of her flaws if i am not mistaken, right?" Ahmad yace "Yes so" Captain yace "To xaka ji ynxu.... first of all she is local, secondly she gat no qualities da xai sa ka makale mata dude, just imagine an undergraduate fa?? And worst of all she isn't even beautiful enough, ga dai big babes a garin da ka baro Abuja, sannan..... her hygiene is nothing to write home about, i mean nothing.... Shine ma babban damuwata ma ni" Da mamaki Ahmad ke kallonsa, da farko kasa ce masa komai yyi, can kuma yace "Wani rashin tsaftar kaga tayi??" Captain ya saci kallonsa yace "Oho, wataran xaka gani" Ahmad ya girgixa kai yace "You are talking off hook, Maryam tana da qualities din da ni nake so, I think that's all? Kuma dama kai idan baka son abu to fa baxa ka ta6a son abun ba, ka dingi discouraging mutum a kai kenan" Captain ya gyada masa kai yace "Ehh haka ne, plss close the chapter" Ahmad xai yi magana ya hango inda ake tuyar awara a gefen titi, da sauri yace "Captain plss ka d'an tsaya, I want to get this, na mance yaushe rabon inci awara, tun kafin in tafi Uk fa..." Captain ya d'an kalli wajen da ake tuyar awaran ya kara ma motarsa gudu yace "Allah ya kiyaye, domin na je dauko ka a railway station doesn't mean xa ka mayar da mu gantalallu a hayi.... Meye kuma awara?" Ahmad yace "Toh ka ajiye ni, ai bance sai ka xo ka daukeni a tasha ba dama, you offered to do so" Captain yyi kasa da murya yana rage gudunsa yace "Yanxu Ahmad kasan ta ynda suka yi processing abun nan da xaka ci? Hayi ne fa nan, ka bari kaje gida kasa ayi maka mana, ni Allah bana son locality din nan naka" Calmly Ahmad yace "Su 'yan hayin ba mutane bane Abuturrab?" Captain yace "Aa ba haka nake nufi ba, I mean... hygiene din, they don't value it, ka gane ai" Ahmad yace "Kai komai sai kace hygiene, to sannu sarkin 'yan tsafta, a haka kuma nake son in siya, ba ruwanka kuma" Captain bai kuma ce masa komai ba ganin wani waje da ake suyan yyi parking kafin ya karasa wajen yace "To sai ka sauka kaje ka siya, amma gaskiya you ain't worth being a Dr wllh, very careless Dr that looks down on Hygiene" Ahmad na hararansa yace "Ae ba dankali nace maka xan ci ba malam, Awara nace kuma nan dankali ake siyarwa" Captain ya kalli wajen masu tuyan yace "Toh ai ban san yanda Awaran yake ba, ba shi bane wnn din?" Ahmad yace "Ba shi bane" Captain ya ja motarsa yana tukin a nutse, can underneath his breath ya ja tsaki, Ahmad is just too local for his liking, Ahmad yace "I think ga wani wajen can" ta gefen wajen da ya nuna masa Captain ya gangara yyi parking yana kallon yarinyar dake tuyan awaran yana yamutsa fuska shi wnn ko yunwa xai kashesa xai iya cin abinda take yi kuwa, Ahmad ya bude motar ya sauka ya tafi gun ta, ita kadai ce xaune sai yara da almajirai dake tsaye suna jiran a siyar masu awara, Ahmad yace "Me awara nawa nawa ne awaran naki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Daya Ashirin" Ahmad ya buda ido ya rike waist dinsa yace "Ikon Allah, kamar dai muna fada da me awara irin wnn amsawan" Still bata kallesa ba ta ci gaba da sallaman yaran da ke gabanta, ta mota Captain ke kallonsu, shi dai Ahmad na tsaye bai sake ce mata komai ba ganin mood dinta, sai da ta sallami yaran gabanta ta daga kai ta kallesa tace "Na nawa xa'a sa maka?" Ya daga kafada yace "Na dari biyar kawai" Tace "Baxai kai ba, sai dai in xaka jira a soya wani" Yace "Toh ba damuwa xan jira a mota" Daga haka ya juya ya nufi motar ya bude ya shiga yana kallon Captain da ya kauda kai da sauri yana kallon daya side din. Leda biyu tayi masa sannan ta hadasu gaba daya a wani ledan daban, yajin ma ta xuba masa a wani ledan snn ta mike ta nufi motar ta mika masa ta glass dake bude, amsa yyi yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "Kamar dai an 6ata ma me awara rai" Ita dai bata ce masa komai ba, dubu biyu ya ciro a aljihunsa ya mika mata yace "Toh gashi" ta daga kai tana kallon kudin tace "Na dari biyar kace" Yace "Ehh sai ki rike sauran canjin ai ko" Ta sauke idonta kasa tace "Aa ka dai bani dari biyar din dai kawai" Ya bude ido yace "Dama ana maida hannun kyauta baya" ta girgixa masa kai tace "Ban san wa xance ya bani ba a gida" Cikin sanyin murya ta karasa maganan, yayi murmushi yace "Sai ki boye kayan ki" Daga haka ya saki kudin nan kasa yace "To sai anjima me awara, Allah ya kawo kasuwa" captain da ya ki kallonsu ya tada motar suka bar wajen. Sai da suka kusa fita titin hayi Ahmad yace "I imagine may be condition ne ya sa yarinyar tuyan awara a rana ko, the country is getting tougher and tougher for the less privileged everyday....." Captain dai bai ce masa komai ba, Ahmad yyi kasa da murya yace "On a serious note ina jin tausayin poor masses a kasar nan, yanxu banda situation me xai sa iyayenta su barta bakin titi tana wnn sana'a? Allah dai ya rufa ma kowa asiri" Still Captain bai ce masa komai ba har suka shigo Unguwan Sarki, yana kallon Ahmad yace "Mu je can gida ne kawai?" Ahmad ya gyara xama yace "Aa kai ni in ga Ummata tukun, da yamma xan shigo in sha Allah" Captain bai ce komai ba yyi driving har xuwa gidan kanwar Mum dinsa Hajiya Ramlah warce ita ce mahaifiyar Ahmad... A kofar gida yyi parking Ahmad na kallonsa yace "Baxa ka shigo ba?" Captain yace "Aa ni fa ko jiya na xo gidan nan" Ahmad yace "Sai dai idan Ummi ce ta aiko ka ba dai xuwan kanka ba" Captain ya shafa kansa yana xare manyan idanuwansa ya kasa cewa komai, Ahmad ya ta6e baki ya bude motar ya sauka, da sauri Captain na nuna masa ledan awaransa yace "Heyy ga kullinka ka mance min a mota" Juyowa Ahmad yyi ya jefa masa wani kallo ya dau ledan awaran ya nufi cikin gidansu, Captain ya bi sa da kallo yana murmushi, can ya kashe motar ya sauka ya bi bayansa walking slowly... Siyama ta sake yayanta da ta rungume ganin Captain da ya shigo parlon, tana murmushi tace "Yaya sannu da xuwa" Yace "How are you Siyama" tace "I'm fine" Yace "Ina su Maimuna?" Tace "Sun tafi islamiyya" Yace "Ke fa" Tace "Ka manta nace maka bani da lafiya jiya?" Yace "Ohhh ohk na tuna, Allah ya kara lafiya, Umma fa" Tace "She's in her room" Tuni Ahmad ya nufi dakin Mahaifiyarsa, Captain ya bi bayansa. Sai bayan Magrib Captain ya bar gidan tare da Ahmad xuwa nasu gidan a Malali, Babban gida ne duplex me wadatattcen tsakar gida.... Captain yyi parking a daya daga parking lot biyu dake katon compound din, suka sauka motar tare da Ahmad suka shiga ciki Ahmad na cewa "Amma Abba baya gari ko?" Captain yace "Ehh baya nan"Zaune take a d'an karamin tsukakken tsakar gidan nasu da kwanon tuwonta a gaba sae dai ba ci take ba duk da kasancewar hannunta cikin kwanon, wata matashiya ce xaune cikin daya daga kananun dakuna uku dake D'an tsakar gidan hannunta rike da mafici tayi daurin kirji, xaune a tsakar gidan kan tabarma wani middle aged man ne da baxai wuce 58 ba, daga cikin dakin matar ke cewa "Munafuka algunguma kawai, sae ana magana tayi mukui ta ki cewa komai, a haka xaki kare cikin nukurci da bakin hali, banda haka uwar me ya ci min naira hamsin a kudina, ko da yake dama ae kin saba halin bera, sae dai na yau yayi min ciwooo tunda ko biyar ubanki bai kawo min yace gashi kiyi cefane ba, to a kan me??" Ita dai bata iya ta ce komai ba har lkcn hannunta na cikin kwanon tuwon ta kasa ci, mikewa matar tayi tana gyara daurin kirjin jikinta ta fito a fusace ta janye kwanon tuwon jin almajiri na bara tace "D'an malam shigo ka amsa" Malam Isuhu dake xaune saman tabarma yace "Ita kuma ta ci me Hansatu??" Wani kallo ta jefa masa tace "Sae ta ci wanda ka nemo aka girka yau" tana fadin haka ta juye ma almajiri ta ajiye kwanon tayi shigewarta daki, shi dai bai kuma cewa komai ba, a hankali ta mike ta dau kwanon ta kai wajen wanke wanke ta shiga hada kayan wanke wanken tsakar gidan, sae da ta gama gaba daya ta mike mahaifinta dake tsakar gidan har sannan ya fiddo hamsin a aljihunsa yace "Gashi ki je ko dankali soyayye ki siyo ki ci Jiddah" karasawa tayi ta amshi kudin da ladabi tace "Nagode Baba" bata rufe baki ba Hansatu ta fito da gudu ta warce kudin tana kallonsa da kyau tace "Saura dari hudu da hamsin kudin cefane na na yau" tana fadin haka ta kulle kudin bakin xaninta ta shige akurkin dakinta, Jiddah ta juya a hankali ta shiga dakinsu ba tare da ta yarda hawayen dake makale idonta ya xubo ba.
Washegari da safe wata dattijuwa da baxata haura 55 ba ta shigo wani babban daki ta kulle kofar tana kallon wanda ke kwance yyi rub da ciki saman gado, karasawa ciki tayi ta buga gadon, juyowa yyi da sauri ya mike xaune ganinta yace "Aunty ina kwana?" Tace "Jiya da daddare ina kaje har bayan isha baka shigo ba" yace "Aunty ina gidansu Ahmad fa, kuma tare ma muka dawo nan da shi na xata kin yi bacci shi yasa bamu shigo ba" Tace "Ohk, jiya Ahmad din ya dawo" Yace "Ehh" Tace "Ai na xata tadi kaje" D'an murmushi yyi yace "Tadi kuma Aunty... Ai tana Abuja" Tace "Atoh na sani ko ka kyallara ido ka ga wata ka watsa min kasa a ido??" Bai kuma ce mata komai ba sai murmushi da yayi, ta juya ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita ta kulle kofar, mikewa tsaye yyi yana kallon agogo dake nuna karfe tara ya shiga bathroom. Kasancewar ranan asabar ce sai kusan karfe sha daya Abuturrab ya fito daga dakinsa sanye cikin kananun kayan da suka matukar amsar sa, lkci daya kamshin turarensa ya gauraye parlon gaba daya, kanninsa mata ne xaune Main parlor din gidan, duk kallo daya suka yi masa suka dauke kai, bangaren Mahaifiyarsa ya nufa, Ramlah ta bi sa da kallo tace "Ummi ta fita fa" Ya juyo ya wuce side din Stepmum dinsa... A parlonta ya sameta tana yi ma autarta Aisha tsifa, yace "Xan je gidansu Ahmad Aunty" Tace "Breakfast din fa?" Yace "Ni nayi breakfast da asuba fa" tace "Oh ka dawo breakfast din asuban kenan" Yace "Ehh" tace "Kawata xata tafi Lagos ranan Monday daga kano shine nace kilan ma you will be piloting the plane...." Yace "In dai flight din safe ne" Tace "Na safen ne ma ina ji" Yace "Allah ya kai mu" Daga haka ya juya yace "Sai na dawo" yana fita parlon, Hajiya Amina da suke kira da Aunty ta kalli autarta tace "Me yasa baki gaida sa ba?" Aisha ta buda hannu tace "Wllh Aunty ranan ce mana yyi mu daina gaishesa a gidan nan idan yana nan, and he was serious about it" Aunty tace "Me ku ka yi masa?" Aisha tace "Babu komai, ranan Thursday da ya dawo duk muna parlor da su Aunty Safiyya muka gaishesa bai ce komai ba, muka sake gaishesa, har ya tafi ya dawo on a serious note yace mana kar mu sake gaishesa baya so, and since then no one is greeting him again and he is very comfortable with that" Aunty ta ta6e baki tace "Toh ai shkkn" A daki Abuturrab ya tadda Ahmad bayan ya isa gidansu, Abuturrab ya nufi window din dakin ya dage curtains din ya bude windon yace "Allow natural ventilation mana" Ahmad yyi dariya yace "Gaskiya ne bature, to kashe Ac din ko?" Abuturrab ya xauna yace "Aa bar shi, how are you?" Ahmad yace "Fine, ya su Ummi" Abuturrab yace "Cool" Ahmad yace "Are you flying on Thursday?" Abuturrab ya d'an yi shiru trying to recall his piloting schedules, kafin yace "Yea, Kano to Lagos, Then Lagos to Abuja, on Friday kuma Abuja to port harcourt" Ahmad yace "Ohk dama Maryam will be going back to schl Thursday I tot kana nan mu kai ta tare" Abuturrab ya ta6e baki yace "Ahmadu Bello?" Ahmad yace "Ehh" Abuturrab yace "Ka kai ta tasha ka sa ta a mota mana, kawai yarinya karama tayi ta juyaka" Hararansa Ahmad yyi, Abuturrab ya fiddo wayarsa dake ring yana duba me kiransa. Bude kofar dakin aka yi Maimuna ta shigo da tray dauke da warmer din danwake da tamarind drink a jug, ajiyewa tayi ta gaida Abuturrab da murmushi fuskarta yace "Ya kike Moon?" Tace "Alhmdllh, Yaya xan je Abuja fa" Yace "To sae ki xo in makala ki a jirgi ko?" Dariya tayi sosai tace "To ai shi sa na gaya maka" yyi murmushi bai ce mata komai ba, ta mike ta fita, bude warmer din Ahmad yyi, Abuturrab dake ta kallon danwaken warmer din yace "Ya ma abin nan da ka siya jiya a hayin Rigasa? Kamar shi nake gani a nan" Ahmad ya wara ido ido yyi dariya yace "Ohh wannan danwake ne, wancan kuma awara, kamar kuwa kasan yau ma xan je in siya, kaji dadin awaran nan kuwa? Gaskiya sun iya sosai, har Umma sai da ta ci, ni uku kawai naci su suka cinye sauran" Abuturrab ya dinga kallonsa da mamaki, can yace "Har komawa xaka yi kenan ka sake siya" Ahmad yace "Yes, I had intention dama" Abuturrab ya gyada kai bai sake ce masa komai ba. Har yamma Abuturrab na tare da cousin din nasa kuma abokinsa.... Su yi fada su shirya, duk bayan sati uku Ahmad ke shigowa kd yyi weekend daga Abuja don a can yake aiki as a medical Doctor, throughout weekend din kuma tare suke spending dinsa da Abuturrab idan shi ma yana garin, karfe biyar saura Ahmad ya mike yace "Captain mu je ka rakani mana pls" Captain ya kallesa yace "In raka ka ina?" Ahmad yace "Hayin Rigasa" Abuturrab yace "Aa sae dai Hayin banki, kaga malam mu fita tare kawai kayi hanyarka inyi nawa, don gida xan wuce yanxu in sha Allah" Ahmad yace "Ae ko baka isa ba, wllh sae ka rakani" Abuturrab ya dau wayarsa xae dau makullin motarsa Ahmad ya dauke yace "Sae ka tafi da kafa ai" kallonsa Abuturrab yyi, lkci daya ya wani hade rai, Ahmad ya fita dakin yana murmushi. Driving Ahmad yake yi, ya kalli Abuturrab dake xaune gefensa yace "Wai Aneesah fa?" Abuturrab ya gyara xama yace "She's good, baka ji muna waya daxu ba" Ahmad ya girgixa kai yace "Kai ynxu da gaske mace da idanuwanta suke a bude da sunan wayewa kake so Captain...." Abuturrab yace "Look at you, kai baka san wayayyun sun fi tsafta ba, ni fa I don't care.... As far as xata yi tsafta 100%, wllh ko haduwa da mace kazama ban son yi a rayuwata, sae inji gaba daya hankali na ya tashi, u know how sensitive I am...." Dariya Ahmad yyi yace "Ita Aneesar tana da irin tsaftar da kake so kenan" Abuturrab yace "Kai ma kasan da ba don haka ba da tuni ae na rabu da ita, kawai sae kaga mace ta ci kwalliya iya kwalliya ta fito amma just check inside, ni in dai mace na da tsafta ko kyanta bai fi 80% ba i will manage her..." Girgixa kai Ahmad yyi yana kallon titin gabansa, Abuturrab yace "Ba ga wajen danwaken can mun wuce ba" Ahmad bai san lkcn da yyi dariya ba yace "Aa D'an gyero ne ba danwake ba" Abuturrab dai bai ce masa komai ba da ya lura u turn yake son yi, dai dai gun awaran Ahmad yyi parking, wata yarinya ce da baxata wuce shekara sha daya ba xaune a wajen tana juya awaran cikin kasko, Ahmad na kallonta yace "Ina me awaran?" Yarinyar tace "Ta je dauko canji a gida shine tace in tsare mata, ae sunanta Aunty Jiddah, a gidansu Bibalo take..." Ahmad ya koma jikin motarsa yace "Gidan ba nisa?" Yarinya ta nuna masa wani rubabben layi dake gefensu tace "Can karshen layi ne, gidansu daya da Bibalo" Shi dai Abuturrab na xaune kujera me xaman banxa yana kallonsu, Yarinyar tace "Lah ga ta can xuwa" Duk suka kalli direction din da ta nuna, Tafe take fuskarta daure hannunta rike da yar karamin bokiti dake a rufe, wanda ke dauke da dafaffen awara, sanye take da hijab ruwan kasa da iyakarsa gwiwa duk man awaran da take tuya yayi staining Hijab din, Abuturrab ya d'an yi tsaki ya hade girar sama da ta kasa yana kallon titin gabansa, tana isowa yarinyar ta tashi tace "Aunty Jiddah gashi xa a siya a awara, da motarsu ma suka xo" Ahmad ya wara ido yace "Aunty Jiddah a bamu kalan na jiya" Ta daga kai ta kallesa tace "Na nawa?" Yyi murmushi yace "Yanda kika sa jiya" Bata ce komai ba ta durkusa ta sa masa awaran sannan ta mika masa ledan, dubu daya ya ciro ya mika mata, tana kallon kudin tace "Yanxu na kai kudi gida na amso canji, ka d'an yi hakuri sai in koma in dauko..." Ya juya ya kalli Abuturrab yace "Ko a siya maka kai ma Captain?" Kallon Abuturrab din tayi ita ma suka hada ido, yyi saurin dauke idonsa yaki cewa komai, Ahmad ya kalleta yace "Toh kinsan abinda xai faru me awara? ki ajiye canjin...." Da sauri tace "Aa ka jira in tafi in dawo ynxu" yace "To tsaya ki saurareni mana, ajiyewa xa ki yi gobe idan Allah ya kai mu na xo sai a bani awara na canjin" tace "Toh" murmushi yyi ya nufi mota rike da ledan awaran, sae da ya shiga motar ta ga ledan yajinsa bata sa masa ba ta mike da sauri tace "Kayi mantuwa" motar ta nufa tana mika ma Abuturrab ledan yajin, da mamaki yake kallonta kamar dai mugun abu take mika masa, yace "Kai!! kinga na siya abu a wajen ki ne?" wani kallon cikin ido tayi masa snn ta xaga ta mika ma Ahmad ta koma gun xamanta tana juya awaran kan wuta, Ahmad ya tada motar suka bar wajen yana hararan Abuturrab da ko a jikinsa. Jiddah na xaune a d'an dakalin kofar gidansu bayan isha, dawowarta kenan daga bakin titi ta gama tuyan dankali da take yi, ta ta takure waje daya cikin hijab din jikinta, wani matashi ne da baxae wuce shekara ashirin da tara ba xaune d'an nesa da ita, yace "Kin yi shiru Jiddah" Ta d'an kallesa tace "Nace babu wata matsala" yace "Kin tabbatar?" Ta gyada masa kai, yace "To ki ci gaba da hakuri kin ji.... In sha Allah idan....." Kamar daga sama suka ji muryar Hansai, ta rike kugu tana kallonsa da kyau tace "Ta ci gaba da hakurin gyatuminka?" Ya kalleta ya duka har kasa yace "Ina yini Baaba" Ta wani sha kunu tace "Da ban yini ba xaka gan ni algungumi?? Ta ci gaba da hakuri a saboda ana cutarta ko? Sannan ban rabaka da kofar gidan nan ba? Dama tun da naga yara sun shigo da kayan tallanta ita bata shigo ba nasan da walakin goro a miya, shine nace bari dai in leko in ga ikon Allah" shi dai bai ce komai ba ya sunkuyar da kansa, tuni Jiddah ta mike ta makale da bango gabanta na faduwa, Hansai ta cire takalmin kafarta ta jefa mata a mugun fusace tace "Wuce ciki munafuka kawai, dama ban rabaki da wnn yaron mara tarbiya ba, ni xa ki ja ma abun kunya a unguwar nan?" Da sauri Jiddah ta shige ciki Hansai ta kai mata dundu da karfi, sannan ta maida dubanta kansa tana huci tace "Wllh na sake ganin ka tare da yarinyata gidan gayun garin nan yyi mana kadan da ni da kai, idan kuma karya ne mu xuba da kai" Tana kai wa nan ta shige ciki ya mike a hankali ya bi ta da ido....
Leave a Comment